KALLON KITSE CHAPTER 11

KALLON KITSE CHAPTER 11

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Toh Allah ya bada sa’a, saiki shiga kicin a samo abunda za aci ko? Cikin jakarta ta zaro atamfa tana nunawa inna, inna ya kika ga wannan zanin?.”

“iye! Waya baki?

“inna wazai bani? Anko nefa na kawo miki, sai kimin.”

“nawaye, wacece zatayi aure?

Balaraba ce, a islamiyarmu take, inna kinsanta tare muka sauke da ita.” hala ta wuce ku a boko ne?

A’a ajinta ma uku, makarantarmu daya da ita ai.”

“ikon Allah haka zataci gaba ko shikenan?

“nima ban saniba, ko zataci gaba, amma a makarantarmu akwai masu aure.”

“Toh Allah nuna mana lokacin, nawa ne?

“dubu daya ne inna ba yawa.”

“uhm hakane Allah yaba da ikon biya.”

wannan hutun bataje ko nan da can ba, tana tare da inna, sun koma makaranta abun ba a cewa komai, domin a kullum inna burinta ta gyara uwaninta, ita kuwa gimbiyar sai kara kyau take,

ta kara cika sosai, dai ta cika budurwa, dan gashi har suna neman su koma term na karshe, wato promotional exams, kwanakin baya a wannan hutun ne salaha ta aiko musu da kudin jirgi, ita da inna, acan sukayi sati biyu, sannan sukaje gusau da mota, nan abu yafi ma uwani dadi, dan sun hadu da hafsat tace,

“nifa har yanzu kinsan uncle mamaki yake bani, yace wai ke yake so! Uhm ke abun yaba mamaki koni, ni ina zanje da wannan gogaggen dan duniyan. Wallahi ko a kafa aka daura minshi bana so.”

kai uwani kinsan fa ya hadu, kowace mace zata so ace mijinta ne, toh ko matan ma bani ba wallahi, bana son shi, ko kadan. Ku kyau kuke hange ba hali ba? Wato shiyasa muke da matsala a wurin fidda gwani.”

“hakane wallahi da yawan mu, abunda ke cutar mu kenan, koma ba haka ba wallahi kinga uncle son ‘yan mata, in kin shiga dakinsa, in banda wasiku da hotunan ‘yan mata babu komai, musamman wata durowa gareshi, na wadannan tarkacen, Allah kiyaye in so namiji irin wannan.”

“kai uwani anya ba sharri kike son yiwa uncle ba? Wallahi gaskiya na fadamiki, sau nawa yana sani gyaran dakinsa, ai ba haka kawai zan shirya magana ba, ban fadawa kowa ba kuma saike, dan haka nima nayi mursisi naki ba yadda za ace in cuci kaina, dan inna ma ba so takeyi ba, itama tasan halinsa ne shiyasa.”

“uhm kinsan ba wanda zai yadda da wannan labarin akan uncle, dan haka abarta haka karta wuce dakin nan.”

nima nasan haka idan ka ganshi kamar bazaiyi ba, Allah dai ya shiryemu baki dayan mu,(ameen)

a yau su uwani sun koma makaranta cike da jindadi, dan sun shiga S.S 3, abun kamar a mafarki suke gani, kowa na yaba yadda uwani tayi kyau, fatar jikinta kamar tarwada, akan tambayeta, wane irin mai take shafawa?

“baseline, amsarta bata wuce hakan, ba komai bane kuwa, illa girma ne ya shigeta gadan-gadan.

Hamza kuwa yanata shirin tafiya service, soyayyar su sai karuwa yakeyi.

Sun sami kamar wata daya da rabi da komawa makaranta, jafar ya shigo gari. Uwani ta shigo gidan, ta iske wata dankareriyar wata mota a tsakar gida, batayi mamaki ba, dan dama ana irin wadannan bakin, da taso taki shiga dan ta gane jafar ne, taji gabanta yana faduwa da sauri, da sauri, tayi ta maza ta shiga falon.

Yana zaune suna hira da inna, tadan dubi inda yake zaune tace, “uncle ina wuni, sannu da zuwa.”

ya amsa yana kallonta ta kara girma, dan watannin da ya tafine har ta kara kyau haka. Lallai kuwa dole ne kuwa yasan yanda zaiyi ya auri yarinyar nan, dan gaskiya dashi ta dace.

Nan da nan yaji hirarsa da inna ta fita kansa, zumbur ya mike.

“inna ina zuwa, bari inje in gaida baba yunusa.”

toh saika dawo.” ta fada itama tana mikewa. Inna ta karasa daki tana yiwa uwani sannu da zuwa, “inna sannu da gida. Ta amsa cike da fara’a

“inna yaushe uncle ya dawo?

Acewarsa yau satinsa uku da dawowa, saida sukayi summiting report. Sannan aka basu iznin tafiya.”

gaskiya inna yadan fada, lallai aikin soja sai mai hakuri, ai shi yaji zai iya dan haka yai ta fama.”

jafar kuwa ya isa dakinsa yayi wanka, yayi shiri tsab, har ya fito sai ga muzamil kanin jafar ne, amma shikam yayi aure, harda ‘ya’yansa biyu, suna ganin juna sukayi musabaha cike da farin ciki ganin juna, dan dama suna dan taba shiri tsakanin su.

“a’a saukar yaushe captain?

Yau din nan officer.” suka kwashe da dariya baki dayansu, “sunan daka lakabamin kenan?

“eh, to nima ai captain ka kirani dashi, wuri suka samu suka zauna, suna hira. A lokacin uwani ta fito cike da yanga, dama akwai shi, tayi kyau sosai a idon jafar, ya rasa dalili, bai taba jin abunda yake jiba in har yaga uwani, hakan sai ya manta abunda yakeyi

duk hankalinsa sai ya dawo kanta why? Ta dan rissina tana gaida muzamil, ya amsa yanayi mata saita dawo, ta wuce. Tana tafiya a nutse, sam jafar yama mance akwai mutum a kusa dashi, sai da ya tabashi yace, “dan uwa kana tare dani kuwa? Yayi ajiyar zuciya yace, “kasan mene muzamil? Wallahi yarinyar nan nakeso, amma sam inna taki amince min, wai bata yadda dani ba.”

muzamil yana girgiza kansa yace, naji komai jafaru, tun wacan zuwan da kayi baba ya fadamin,tun wancan zuwanka dakayi baba ya fadamin komai, toh ya kana ciki ko kuwa ka hakura?

“dole in hakura muzamil, inna bataso, inban hakura ba ya zanyi ne?.”

muzamil ya gyara zama yace, ‘dan uwa akwai wata hanya da za abi mai sauki, kuma itace abunyi.”

jafar ya kara maida hankali sosai ga muzamil yana sauraransa, “kayi mantuwa jafaru, da wani kakan da yake bunza, kanin mahaifin inna, wanda shikadai ya rage masu, ko ka manta dashi? Kasan Kuma kasan baba sabo yafi kowa rigima a kawunan inna, inace shine dalilin rashin zuwanka gunsa….. .”

jafar ya dada masa duka yace, gaskiya ne muzamil wallahi sam na manta da baba sabo, da tuni angama komai, kasan abunda yasa nadaina zuwa? Saboda maganar aure nefa. Kai Allah ya barka dan gobe, toh amma zaka rakani ko?

“insha Allahu kuwa

saika shirya gobe dan Allah muzamil.

Toh Allah kaimu goben

“Ameen

washe gari tunda safe suka bar kebbi, zuwa bunza, tafiyar kusan awa biyu da rabi suka isa, ba karamin murna Baba sabo yayi ba, dan ya kwana biyu baiga jafaru ba.

Sai dai kuma yayiwa jafaru fada sosai akan abunda ya faru a baya.

Jafaru kam hakuri yake badawa, sai kuma ya fado maganar matarsa marliya, ya kuma tambayi ‘ya’yansa nawa? Muzamil ne ke gaya masa bata haihu ba.

Toh me kake jira da ba zaka sake aure ba? Jafaru bafa yaro kake ba, ka duba ka gani, duk kanen ka da yara birjik, amma banda kai, wai kai bature ko?.”

a’a baba ba haka bane, inji jafaru, lokacine baiyi ba kawu.”

muzamil ya amshe maganar yace, ‘ai baba abunda ya hanashi auren inna ce taki bashi matar da yake so, shiyasa ma muka shirya yazo nan, dan ka roketa ta sauko ayi auren.”

“ita inna ta hana shi matar da zai aura?

Yayi tambayar cike da mamaki, “haka maganar take baba.” nan dai muzamil ya kwashe labari yaba baba sabo.

Baba sabo ya dubi jafar shin ka tashi yin auren ko baka tashi ba?

“wallahi baba na tashi.

“toh shikenan, inaso ran jumma’a da safe kazo ka daukeni muje gun ita shatun nida ita zanyi magana ba sai nayi da inna ba, sannan inaso kai muzamil ka kai mana Alh. Yunusa can jega, dan ya zama shaida dan da yardar Allah ranan zan daura maka aure, saika siyo goro ka kawo sadaki, kuma shikenan sai kunzo.”

jafar ji yake kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha dan tsabagen farin ciki, da ya cika masa ciki. Ai tuni ya cika baba sabo da naira, har yayi masa sayayyar kayan abinci.

Cike da murna suka isa kebbi, a wannan dare ko bacci ya kasa, dan murna. Haka yayi ta shirye-shiryen sa saboda jibi ne jumma’a, dan haka ko wuni baiyi gida ba, babu abunda bai tanada ba, wanda yasan zai bukata.

Ranar jumma’a da safe ya shiga gun inna, ya isketa ita kadai a falo, tana kari. Saida gabanta ya fadi, sabo da wani kwarjini na musamman da yake dashi a idonta, duk saita rikice, dan dama har yanzu tana jin tsoronsa fiye da dama. Gab da ita ya zauna, cikin manyan kaya yake, tunda take bata taba ganin yasa irin wannan kayan ba, sai a wannan ranar.

Lallai yau za ayi ruwa.” ta fada a ranta, gabanta kuma kamar zai fashe, saboda faduwar da yake, muryarta na rawa tace, ina kwana uncle?.” kallonta yakeyi cike da sha’awarta, bai amsa ba saiya dauke filet din data ke cin abinci, ya soma ci.

Tambaya ya jefo mata, “waya gaya miki ni uncle dinki ne?

“uncle wannan abinci na ne.” ta fada a shagwabe, dan bakinta ya kalla, ji yake kamar ya tsosesu, toh amma ba hali. Ya lashi labbansa na kasa, yace, shikuma zanci, sai dai ki debo wani.” toh ya za ayima ta mike, harta debo wanin, ya wani zauna haka, ya tare ko ina, da yake tana sanye da kayan makaranta ne, farar riga da wando marun, braziya ta saka, dan haka ana kusan ganin zanen bra din awajen rigar.

Tana mikewa idonsa sai a kirjinta, da sauri ta koma ta zauna, tana bakin cikin wannan hali na uncle din nata, wai meke damunsa ne? Duk kwanan nan saiya rika mata wani irin kallo da yake bata mata rai? Ita kuma sam bada gangan takeyin hakan ba, toh amma shi ko ajikinsa. Kallonta yaci gaba dayi

ita kuwa gabanta sai kara harbawa yakeyi, har yanzu muryarta rawa take, tace, uncle zanyi latti kuma ana duka,

ya juya yana ci gaba da cin abincin sa, “na tsare miki hanya ne? Ya tambayeta, “kizo ki wuce mana.”

tana nan dai zaune bata motsa ba, har saida ya gama, sannan ya juyo ya dubeta, suna kallon juna, duk da kanta na kasa, duk ta tsargu, ita haushin kanta ma takeji, data saka wannan bra, dama ita ba kasa fai take sawa ba, saboda kunyar asan ta saka bra….

Ya tsinka mata tunani, “kinaji na ko? Inaso muyi magana ta fahimta, nasan da banso in fara magana dake ba, har sai naga abunda zai yuwu, toh amma daga ke, har inna kun dau abun da zafi, so a yau inaso inji naki ra’ayin akaina, kina sona?

Nan da nan yanayinta ya canza, shima ya lura da hakan, ba zato ta mike hannayenta rumgume a kirjinta, abun dariya ya bashi, dole ta koma ta zauna, ta hada kanta da gwiwarta, tana kuka.

Dan nayi miki tambaya shine ya zama na kuka? Toh Allah ya baki hakuri, ina so ki sani, ina sonki, so na gaskiya kuma na amana…..” katse shi tayi, “wallahi ni bana sonka.” cike da tsiwa take magana,cike da tsiwa take magana, “kuma bana kaunarka, ni inada wanda nake so…. .”

da sauri yayi mata bal a baki, idonsa tuni sukai ja, abun ya bashi haushi, da sauri takai hanunta baki, wani kuka ta saki.

Kuma bakin nata bai mutu ba, “ni har abada ba zan taba sonka ba, mugu kawai.” ta mike zata wuce, ya rike hannunta, tayi iya fisge-fisgenta harta gaji, amma shi ko gezau.

Ke wai bakiji ina magana bane? Nace ki saurari abunda zan fada miki, kin sani bana son raini, ni ‘yan mata keso, dan ma kin samu harna furta miki kalmar So? Toh bari kiji nidin nan dole ki soni, dan dole ki aure ni, in Allah ya yarda.

Ya saketa tare da kuma tsareta, “saboda inna ta lalataki, har ya zama bakya shakkar fadawa gwarzon namiji iri na magana, an gaya miki inda nayi saurin aure, ai dana haifi kamarki, dan haka ki iya kanki, dan nace ina sonki, toh bazan yadda ki raina niba.”

ya kauce mata, a guje tabar falon, tana mita, “nidai nace bana sonka, kuma bazan soka ba.”

“yarinyar nan ta rainani sosai, koda yake yasan halinta, tun ba yanzu ba, tsiwanta dama yayi yawa, sai dai ba karfi. Hannunta daya rike ma kamar auduga, tun tana karama ya sha zuwa ya iske malamarsu, an kawo karanta tayi fada, kuma itace da tsokanar fadan, “toh amma ni zan gyarata ne.” ya fada afili, kuma saina aureki, insha Allahu yau dinan basai gobe ba.”

haka ya wuce bunza cike da tunanin, yarinya tana nema ta juya shi, yana mamakin yadda ya biye mata, shima ya koma sa’anta, amma lokaci yazo dazai goge raini tsakaninsu.

Karfe sha daya saura suka hadu jega, harma su muzamil sun isa, su kawai ake jira. Shatu babu abunda zatace, dan dama ai yarinya a hanunta take, dan haka aka shirya in ankidar da sallar jumma’a sai a daura.

Haka kuwa akoyo, ana kidar da sallar jumma’a aka daura auren jafar alkali bello da Aisha dalhatu. Mijin shatu mal. Tasi’u shine ya zama wakilin Aisha, shikuma Baba sabo shiya wakilci jafar. Haka aka tashi, anata zuba addu’a. Jafar ji yake kamar aranar ya fara aure, sam baya shakkar yaga inna, dan dai Allah ne yayi zai lamince duk wani abu dazai biyo baya, amma bazai rabu da itaba.

Wajajen karfe uku suka isa kebbi, harda Baba sabo dan yace, yanaso yaga inna da kansa ba sako ba.

Tana kicin kuwa suka shigo, da sauri ta isa gunsu tana gaishesu, yadda ta lura da yanayin Baba sabo tasan akwai muhimmin daya kawoshi, kuma abun ba karami bane, dan tasan halin kawun nata, tun suna yara shikam suna tsoron shi, dan baya daukar raini, toh amma meya faru haka da bata saniba? Ta nemi wuri ta zauna, bayan ta gama jera abinci agabansu,, tana kara gaishesu.

Baba sabo ya buda baki zaiyi magana, saiga jafar, yace yauwa, dama inaso inyi maganar kana nan, fatima.” ya fada, inaso in fada miki ta farin ciki.”Baidai ce mata ci kanki ba, ya wuce ya shiga dakinsa.

Yayi wanka ya shirya, ya fita wurin jamila ya nufa, da yake tunda sukayi fada ya raba musu wurin zama, dama tuni ya fada mata yana gari, dan haka ta shirya masa abinci, yana shigowa harabar gidan ta taho da gudu ta rungumeshi, tun a waje suka fara shegantakar tasu, har suka isa falo.

Nan suka baje, bayan ya gama cin abinci, ta jawoshi suka shiga daki, sukayi ta shedancin nasu. Allah dai ya shirya Ameen.

Sai sallar mangariba ya shiga yayi wanka, ya wuce masallaci, daya dawo ya isketa zaune bakomai ajikinta.

Wata sha’awarta ne ya bijiro masa, suka ci gaba da abinsu cike da nishadi, shiyasa yake son jamila, sam bata gajiya da irin wannan harkar, ga shi mabukacine kwarai da gaske, yana da sha’awar mace a tattare dashi.

Da aka neme shi yaje jaji completing din cos daya soma, kafin ya samu major, tareda jamila ya tafi, zaiyi kusan wata uku a can, ita dai marliya ta nan abun tausayi, duk tabi ta lalace, saikace ba itaba, duk ta rame ta zama kamar mai ciwon kanjamau, saika ce wanda iyayenta suka tsine mata. Ashe rayuwa na iya juyawa mace acikin kankanin lokaci?

Toh gashi dai marliya ta shiga,kuma taji abinda takeji, shin dama duk mai irin halina marliya wadda bata da wurin zuwa sai na bokaye da malamai a zatonta sune gatanta, toh sai gashi ita da banza duk daya, toh saimu dage mu roki Allah shine yasan abinda ya dace damu, dan haka mu rokeshi abin daya fi zama alkhairi, shine zai bamu.

Ubangiji yasa mufi karfin zuciyarmu(ameen)

a kebbi kuwa tunda aka daura aren jafar da uwani, sam inna ta kasa samun kwanciyar hankali, dan yadda ita uwanin ta tada hankalinta, abu daya inna ta fada ta kwantar mata da hankalinta, idan jafar ya dawo zatasa ya saketa.

Tunda inna ta furta haka, sai uwani ta koma sha’aninta kamar da, a makaranta kuwa lawisa ma bata san an daurawa uwani aure ba, dan ita a ganinta abun kunya ne ace tanada aure, kuma tana zuwa makaranta.

A haka ma saita rika hira da hamza, acewarta ai inna tace za a raba auren da aka daura mata, dan haka basai ta daina ganin hamza ba, yarinta kenan.

A yau watan jafar hudu rabonsa da kebbi, ita kuwa uwani ta samu hutun 1st term dinsu dan haka tana gida.

Tunda safe ta shirya ta tafi gidan su lawisa, a ranar jafar ya shigo gari. Yana isa cikin gida, inna ta tareshi da fada, ta inda take shiga bata nan take fita ba, a karshe dai cewa tayi ya rubuta takardar saki ya bata, biro da paper ta mika masa,

jafar bai amsa ba, kuma baice mata kala ba, amma duk yanayinsa ya canza, hardai kalaman daata fada na karshe, duk hankalinsa ya tashi, ya rasa inda zaisa kansa, sai a lokacin yace inna kiyi hakuri, amma bazan iya sakin uwani ba.” jin mari yay a fuskarsa, “ni kake fadawa magana? Toh wallahi baka isa ba, baka barin gidan nan saika rubuta mata sakin nan, inba haka ba kuwa, duk abunda na maka kai ka ja.

Har yanzu kansa a kasa, can dai yaga abun yana so ya zama haka, saiya karbi paper da biro tare da mikewa tsaye, cikin sauri ya fice daga falon.

Ta biyo shi tana fada, shikuma tuni ya bar gidan.

Gidan Alh. Yunusa ya tafi, yayi sa’a kuwa yana nan, dan haka ya zayyane masa abunda ke faruwa, lallashi Alh. Yunusa ya far dashi, dan yadda yaga jafar ya fita hayyacinsa, ya kuma saka aka kawo masa abinci, “bari inke in ganta.”

shi abun yana bashi mamaki, wai dama haka inna takeda taurin kai?

Bari insha Allah yanzu gunta zanje.”

daya je gunta, nunawa Alh. Yunusa tayi ita batayi kananan furuci ba, yadai zauna ya mata nasiha tare da tunasar da ita abubuwa da dama.

Nan da nan jikinta yayi sanyi, itama ta rasa dalilin data keyiwa jafaru haka, kodai abunda ya fada gaskiya ne, bata yafe masa ba? Ta tambayi kanta.

Toh Allah yafe mata, Allah ya shirye shi.” ta fada afili, Alh. Yunusa yace “amin, abunda ya kamata ki ringa yi masa kenan fatima, kiyi ta yi masa addu’a Allah zai amsa addu’arki, haka dai Alh. Yunusa yata bata baki, harta sauko, dan yanda yanayinta yayi.

Tunda ga ranar bata sake yiwa jafaru maganar takarda ba, amma kuma bata sake masa fuska, ita kuwa uwani tunda taji labrin yazo ta faman buya a tsakaninsu.

Yau kwanansa biyu da yini daya, amma baisa ido akan uwani ba, yanzu ma ya shigo cikin gidan yanata kwala sallama, amma shiru ba a amsa ba.

“toh ina mutanen gidan suka shiga ne? Ya tambayi kansa.

Can daga kicin yaji faduwar tangaram, ya isa kicin din da sauri.

Uwani ya iske tsugunne gaban tangaran din, a tsorace ta mike, saika ce wadda taga kura.

“dama kina jina ina sallama, amma kika yi banza dani? Ya shiga kicin din, ita kuwa sai ja da baya takeyi, can ta tsinci kanta da gaishe shi, ina wuni uncle?

Bata san sanda ya isa gabanta ba, waye uncle? Bata iya amsa masa ba.

Yaci gaba ina kika shiga kwana biyu ina nemanki a gidan nan ban ganki ba? Da sauri tace ina nan.”

ke baki san miji tattalinsa akeyi ba? Yayi tambayar cike da sha’awarta,

About AIS

Check Also

KALLON KITSE CHAPTER 10

KALLON KITSE CHAPTER 10                     Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *