HOD’IJAM CHAPTER 6 BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 6 BY NOORIEEYAH

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

“La’ilaha’illahu,kai kai Mukhy dawo,maza dawo man da ita nan.”+

Muryar Mammy ta dakatar da Mukhtar din dake qoqarin billewa,nikuwa har yanzu ihu nake ina burari,tsakanina da Allah gani nake na riga nazama me ciki,shikenan haihuawa zanyi,kuma na tabbata Ammyna yankani zatai kamar yanda tasha fada mani.

“Yawwa sauketa maza kafin ta qarasa qulla maka sharri a bainan nasi,Niimah halan baki da hankali ne?ta yaya zaki nemi kira mana alkaba’i da farar safiyar nan?”

Nidau ba baka sai kunne,kukana kawai nake,ciwon marar ma nemaanshi nai na rasa tsabar tsurewa,can najiyo muryar Adda Bilkisu tana dariya,lokaci guda tana qoqarin baiwa Mammy amsa.

“Kai kuma Mammy inbanda abunku meyene abinda ma har zaku ke tankawa anan,ni nasan ina zancen Niiman yadosa,i bet irin tricks dinnan ne Ammynta tai mata out of protection,if i can eveb remember same issue yataba faruwa da Kausar din Gwaggo bilkisu,and daga baya duk mun fahimci cewa wasu kalamai ne da mstly iyaye mata ke amfani dasu wajen tsorata yaransu mata a lokacin da suka fara al’ada,and kowa yasan cewa abinda suke fada din bawai hakan bane,sai dai suna amfani da trick din ne don su tsorata yaran don ganin sun tsare qima da mutuntakar su,mussaman sanin cewa period shine sign mafi girma dake nuni da cikar matantakar diyoyi mata.”

Ta numfasa,tana mai cigaba da kallon kowa dake falon anyi zugudi ana sauraron ta,har ita Mammyn kuwa,duk da ita tsakani da Allah da farko ta tsorata,har ga Allah tama manta da ire iren tricks dinnan,ah ah toh,gani tayi lokaci guda yarinya na shirin kira masu ruwa,ina Allah yaranasu da mugun ji da mugun gani.

“Kinji har diyar cikin ki tafiki hankali,dubi dai yanda tayi bayani a nutse kuma kowa ya fahimta.”

Mammy dai shiru tayi,gakuma takaici da yake neman sake lullubeta,toh ita bataga wani aibu cikin abinda tace ba,maganar gaskia fa.

Daddy ne ya dubenu ganin zuwa wannan lokacin na dan sarara da kukan ina zazzare ido,daalama tsoron da nakeji din yadan ragu,duk da dai bangama yadda da bayanen da Addah bilkisu tagama rattafowa ba,ni gidanmu ma zanzo inkoma,domin ji nai gaba daya gidan ya fice mani a rai.

“Bilkisu kamata kuje ta kimtsa jikinta,daga nan sai ki qara yi mata bayani dakyau yanda zata gane,inkun gama sai ku fito Mukhtar ya ajeku a clinic.”

Daddy ya umarci Adda Bilkisun,toh kawai tace ta kama mani hannuna na miqe,Fareeda ma tazo ta riqe mani dayan hannun nawa muka kama hanyar dakin su Adda Bilkisun,sai a lokacin na kula ma da babu ko inuwar Mukhtar din a parlour din.

Toh koda muka shiga dakin su Addan dai abu daya ne aka cigaba dayi,bayanai sosai Addan tai ta mani,ta hada harda Fareedan ma,duk da cewa ita ba tariga da ta fara nata period din ba,ba laifi yanzu kam na gamsu sosai da bayanan na Adda Bilkisu,harma naa riqa jin kunyar katob’arar da na tafka,banga laifin Mammyn ba da take zunduma mani fada,eh mana wannan ai mugun alkaba’i ne ta bakin tata.

Shigowar Aunty Sakeena da Aunty Bena ne ya sake bude shhafin wasu hudubobin,tunda dai su a lokacin Yammatane sosai,don Adda Bilkisu she was almost 26 atime din,don anma kusa aurenta ita da Aunty Sakeena,tunda dama immediates ne su,Adda Bena itace take 22 a lokacin kuma tana lvl 300 a jami’ah,yayin da Mukhtar ke shirin tafiya lvl 100 bana.

Tambayoyi sosai sukai mani kan hukunce hukuncen jinin al’ada,bankuma basu kunyaba nai masu bayani gwargwadon abinda nasani,domin kuwa kwarai zamana a america bai sanya iyayena watsar da addinin su ba da al’adunsu,mussaman Ammyna ke koya mani abubuwa da yawa da suka danganci addini in tana off duty,kuma Abbuna baiyi qasa a guiwa ba ya hadani da gidan wani abokin shi ina zuwa daukar karatu tare da yaranshi,a gurin wani dan uwan matarshi dake zaune dasu anan american yana karatu shima,alhamdulillah nasan addini na gwargwadon hali da kuma shekaruna.

STORY CONTINUES BELOW

Fitowar mu domin zuwa clinic yayi daidai da fitowar Daddy zai fita zuwa wani meeting da zaiyi attending,mota daya ce a gidan Range Rover,shiasa indai wani yariga fita da ita tofa sai dai aje a tari cab,ganinmu ya sanya Daddy tunawa da fitar da zamuy,hakan yasa ya umarci Fareeda da taje ta kira Mukhtar ya tuqamu,idan yai dropping dinmu sai ya wuce yai dropping Daddy inda zeyi meeting sai yadawo ya maida mu.Fitowa yayi yana ciccin magani,babu wanda yakulashi in bannda Daddy da baya iya jure bacin ran shi.

“Mukhtar inafatan lafiya?ko wani abu ke damun ka?”

Sai da ya yamutsa fuska,cikin daurewa ya nunawa Daddyn babu komai,kanshi ne ke dan mashi ciwo,toh kuma sai Daddyn yai insisting in ba zai iya driving din ba yabari sai Adda Bilkisu ta tuqa,dama dai bai cika son suna tuqin manyan tituna irin na qasar nan bane shiasa,nikuwa kamar an tsungule ni nace

“Eh Daddy,dama yabarshi kawai sai Adda Bikkisu ta tuqa mu,ni nafison ta kaimu,banason shiga mota dama da Yaa Mukhtar dinnan,mugu ne ya tsaneni.”

Kaina tsaye nai maganata,batare kuma danaji daar ko wani abu ba,domin dai nikam iya gaskiata nake fad’i,kallon danaga yana wurgo man daga nesa ya sanyini hanzarin sunkuyar da kaina ina wasa da qaramin vail din dake nannade da kaina.

Daalama wasa Daddy ya dauki zancen nawa,domin kuwa yana er far’ah yai tapping kaina yace,

“No Niimah kar in sake jin kin fadi haka kinji ko?Mukhtar dan uwanki ne,ta yaya za ai ya tsaneki?ko kintaba ganin inda dan uwa ya tsani danuwanshi?”

Na girgiza kaina bawai don na yadda da cewar be tsanenin ba,domin har zuwa yanzu da Daddy ke magana ban fasa kallon unda Mukhtar din ke tsaye yana ballo man hararara ba,nasan da mukadai ne da tuni ya dade da mangareni.

“Toh kingani,kar insake jin kince ya tsaneki kinji ko?nida nake so ma in aura mashi ke domin ku haifo mana jikoki masu kyau,ko baki lura ba kunfi kowa kyau a duk gidan nan ba?”

“Eh wallahi Daddy,kuma ma suna kama sosai!”

Cewar Fareeda cikin doki da jin dadi.

Ni kuwa tuni nai kicin kicin da rai ina zumbura baki,Allah ma yakyauta ni me zanci da wannan Yaa Mukhtar din?wallahi ko zan mutu ba zan taba aurenshi ba.

“Allah ya kyauta,Daddy ni wallahi bana son shi,mugu ne mai baqin hali!”

Na furta da iya gaskiata ina shirin yin kuka,mussaman yanda naga shi kanshi mugun na wani irin tsuma kamar wanda zai tashi ya hau tamola dani,ina kallon yanda maqoshin shi ke sama da qasa yan huhhura hanci.

“Shima Allah yakyauta ya tsareshi,me zaici dake ni kuwa Niimah?da har saboda baki da kunya ki dubi tsabar idon mahaifin shi kice kin tsanar mashi d’a baki k’aunar shi?”

Muka tsinkayo muryar Mammy lokacin da take sakkowa daga stairs, tsaki kurum Daddy yayi lokacin da ya juya yana umartarmu damu taho mutafi,kana ya qara da jefa wa Mammyn amsa lokacin da yake gaf da ficewa daga main entrance din fita daga falon.

“Khaltume bansan ranar da zaki riqa banbancen zancen mai hankali da kuma wanda yarinta taiwa dabaibayi ba,Allah ya ganar dake wannan banzar dabi’ar taki.”

Nidai gaba mukak nida Fareeda muna aus qus dinmu,munma manta da nayi wata katobara,har ga Allah a lokacin bancika hango haushina da Mammyn ke qoqarin boyewa ba a gaban idanun Ammyta,ina dauka cewa ita din mai qaunata ce,ganin yanda Ammyna bata da wata aminiya kuma er uwa da ta wuce ita,ashe ba haka bane.

***

Tun bayan faruwar wannan abun sai na lura da sabon canjin abubuwa daga Yaa Mukhtar din,bai cika hantara ta kamar da ba,amma dai still ba wai nuna mani qauna yake ba a matsayina na er uwarshi,har kuwa hutun su yazo gaf da qarewa suka fara shirin komawa Nigeria,nasan kwarai zanyi kewar su kamar yanda nasaba a duk zuwan da suke.

STORY CONTINUES BELOW

Ammyna da Abbuna sukazo gidan a daren domin komawa dani gida,dukkanmu zaune muke a falon gidan ana hira,inka debe Mammy da Ammy da basa falon,suna can sama dakin Mammyn suna tasu hirar,ni da Fareeda kuwa wayar Aunty Sakeena ce a hannunmu mun hade kai muna kalle kalle a shafinta na Instagram, daga mu shiga wannan profile din sai mu shiga wancen profile din,Fareeda ce ta rada mani wata maganar da ta sani k’yakyalewa da dariya.

“Wallahi inna girma nima na zama ‘yammata,miji zan aura irin wannan gayen,dubeshi don Allah fari qal qal so fresh and cute.”

Na sake zooming hoton saurayin dake sanye da farar kaftan ta shadda yasha kyau abinshi,daganin shi kaga dan boko dan gayu,ba shakka yana da kyau kam,amma fa ni sam ko kadan be burgeni ba,domin ni banson namiji fari,haka kawai nakejin baqar fata sunfi kyau,bakina a tabe na rada mata nima a kunne.

“Ni kuwa nafi so inna girma na auri miji dogo,baqi,mai dogon gemu,gemu mai laushi,gemu mai santsi,gemu mai sheqi da bala’in kyau!gemu irin na saurayin Addah Bena uncle Saddiq,don Allah gemunshi bai burgeki keh?ni wallahi bala’in burgeni yake”

Gama zancen yayi daidai da kicibis da idanuwan mu da sukayi dana Yaa Mukhy,ban iya karanta facial expression din shi ba,kuma daga dukkan alamu yaji menace,amma a tunani na rad’a nakewa Fareeda,kuma naga da dan tazara a tsakanin inda muke zaune a kan kafet da inda yake zaune akan kujera yana danna system din shi,maida kallona nayi kan Fareeda,gani nai tai tsuru tana zazzare idanu,da idanu nace mata menene?

A hankali tace man.

“Ke banzace,duk yanda nake zungurinki bakiji ba,kin bude makoshi sai kwararo zance kike,wallahi Yaa Mukhy yagama jin duk abinda kika ce,innalillahi gashi can yana kiranki ma.”

Jinai cikina yace qulululu,ga kuma wani gudawa da nakejin kamar ze kamani, shikenan yau qaryata ta qare,don nasan yanda ya tsanenin nan tsaf zaije ya gaya wa su abbuna da Daddy abinda nace,nabanu na shige su.zungurin da Fareeda take mani ya sanyani yin firgigit nadawo hayyacina.

“Kitashi kije yana kiranki Ni’imah.”

Idanuna duk sunyo waje,sai zufa nake ina hasko irin dukan yau da Ammyna zatai mani,nasanj nasanj kwarai,er qanqanuwa kamata bai kamata ma na riqa tunanin yin saurayi ba,ballantana akai ga har rattaba yanda nakeson yazama nake,ai ni kuma yau tawa ta qare.

Dana maida kallona inda Yaa Mukhtar din yake sainaga ya miqe tsaye,ai ba shiri na miqe natafi zugui zugui tamkar wacce zaa ce kyaaat ta arce,a zuciyata kuwa ba irin adduar da bana kamowa domin tsira daga kaidin wannan baqin mugun,bai kalleni ba yadai yi mani nuni da in biyoashi da system din shi da ya aje,jikina na rawa na dauki system din nabi bayanshi salalau salalau,duniyata yau tangal tangal take,don qiris bake jira in kece da gudawa.

Maida qofar dakin nashi yayi ya sanya lock ya datse,baice mani komi ba ya shige bayi kanshi a d’age ba kuma tare da ya dubeni bba,nidai ina tsaye maqure da bango ina shirin mai aukuwa ta auku,baifi mintuna biyar ba yafito yana mazurai,gefen couch din dake extreme end na dakin ya zauna,kana ba tare da wani bata lokaci ba ya yafito ni da hannu,kai da ka kalleni kasan nayi surrender,kwata kwata bani da sauran wani courage din nasan matuqar asirina ya tonu yau sai Ammyna tayi mun bugun da bata taba yimani ba,runtse idanuna nayi ina hasasho yhanda zata dubeni intaji abubuwan da nace.

“Ehen lover girl,sake maimaita abinda naji kina cewa d’azu.”

Cikina ne ya sake hautsinewa,naji tamkar aasa ta bude na afka ciki,nabanu yau shegen surutu na yaja mani masifa,bakina na karkarwa nafara bashi hakuri ina magiya.

“Zanci gidanku,zaki bude baki ki fada abinda naji kina fadawa Fareeda ko saina ballaki into pieces?”

Jikina yacigaba da rawa,nafara kuka a hankali ina cewa.

“Dama ni wlh wasa nake ma Fareeda,kuma ma ni gaba daya na manta me nace mata,don Allah Yaa Mukhtar kayi hakuri karka bari su Ammyna suji,zaneni zatayi?”

Komawa yayi baya yana wani munafikin smirk.

“Stupid girl,ashe kinsan ba abu me kyau kikai ba?wallahi sai kin maimata abinda kikace,if not bayan nagama zaneki da kyau,inkuma je inhadaki da Daddy da su Ammyn daganan su suka san irin hukuncin da zasui maki,inma gidan kangararrun yara za’a miqa ki duk sai ayi hakan kowaya huta!”

Tashin hankali wanda baa sa masa rana,jinai gaba daya rayuwata ta juye daga fari zuwa baqi,nikuwa wai wane tsautsayima yakaini taba wayar Adda Bena?harma tsautsayin da ya kaimu shigar mata Instagram page duk na hade na riqa tsine masu a zuciyata,tsawar da yadaka mani ita tasani nafara zubo zance ba tare da nasani ba

“Dama cewa nayi,Ni nafi so inna girma na auri miji dogo,baqi,mai dogon gemu,gemu mai laushi,gemu mai santsi,gemu mai sheqi da bala’in kyau!gemu irin na saurayin Addah Bena uncle Saddiq,ni wallahi bala’in burgeni yake”

Idanunshin nan fici fici nakaina yana zuba mani harara,sai kuma naga kamar huhhura hanci yake,yanda dai yakeyi in yanajin haushi,cikina ya sake qullewa,naji na sake tsurewa gaba daya,ai ni yau kam bani da sa’a,baki na yaja mani masifa.

“Da kyau lover girl da kyau,oyaa clap for yourself.”

Sunkuyar da kaina nai qasa inajin duk na muzanta,aifa yau ranace da zata shiga cikin kundin tarihin rayuwata,what a hectic day?

“Ba dake nake ba?oyaaa clap for yourself kafin nazo nan na tattakaki.”

Ai ba shiri na hau tafi,ji kake raf raf raf inayi ba qaqaautawa,sai da yace man ya isa cikin tsawa kana na tsaya ina dauke hawayen da suka bata man fuska.

“Yanzu shekarunki nawa?”

“Last month nai turning twelve years.”

Nabashi amsa kaina a qasa.

“Imagine,a twelve years old girl ce har tasan kalar namijin da takeso?dubeta fiqi fiqi kamar wata mumina,sai iya shege fal cikinta,yau zakisan ni mugu ne,ba kwanaki kin iya fadawa Daddy ni mugune mai baqin hali ba?today you will testify to that for real!”

Na dade da fara kuka gadan gadan,ai nikuma tawa ta qare yau,ko kafin insan abinyi sai gani nai ya zaro chargern wayan shi ya janyoni gabanshi sosai.

“Oyaaa Kneel down!”

Jikina na rawa nai qasa ina ambaton Allah a zuciyata.

“Raise up your hands and close that your big big eyes masu kama da na jimina.”

Duk da banma san meye jiminan ba amma na haqiqance zagina yayi,ba shiru kuwa nnayi abinda yace din,shiru dakin ya dauka sai qarar ac dake aiki,nikuwa jira nake ta Allah ta sameni,ganin shirun yayi yawa ya sanyani dan bude idona kadan don ganin kome kenan,hada ido mukai yaman quri da ido yana kallo kamar maye.

“Uban wayace kibude idonki?”

Da sauri na maida su na rufe ina faman bashi hakuri,hakanan kuma jikina ya riqa bani kallona yake,sabida in banyi qarya ba inajin kallon nashi a jikina,saida ya tabbatar da hannayena sungajj kana yace in sauke su in bude idanuna,da sauri nasake ina zamewa qasa,jinake hannayen nawa kamar ansanya hammer an bubbuge man su.

“Zan rufa maki asiri base on one condition,kina jina?”

Da sauri na daga kai inajin zan iya yin komi domin tsira daga bugun Ammyna.

“Ehen from now henceforth, banyarda ko bayan bana nan ba kiqara tuananin ma wai kalar mijin da kike so ki aura ba,talklless of ki kula wasu mazan ko da kuwa class mates dinki ne,idanma kina ganin bana nan toh i assured you ni ina ganinki,ni dinnan dakike gani rabi mutum ne rabi aljani,babu abinda bana ganj koda kuwa bana gurin,saboda haka ki kula,wallahi inkika kuskura kika saba,ki kuka da kanki duk abinda ya biyo ba.”4

Yanda kukasan fadar Allah haka zancen Yaa Mukhtr sukai tasiri a garenj,gaba daya kuma naga yadda da dukkan kalamen shi,na kuma daukesu na rungume katamaumau,sune manyan dalilin da yasa koda wasa bantab bari nayi saurayi ba ko da da wasa ne har kuwa zuwa yau danake baki labari.

Farkon Labarin kenan.

***Rayuwa ta cigaba da gudana ban manta da threat din Yaa Mukhy ba daidai da daqiqa guda,saboda inaganin a kowanne lokaci zai iya ganina,kuma ganin nawa na nufin sabawa umarnin shi,sabawa umarnin shi kuma na nufin tonon asiri na,hakn yasa nai riqo da kalamen shi tamkar fad’ar Allah,mussaman inna tuna kalmar …+

“Ni nan da kike gani,rabi mutum ne rabi aljani.”

Yauma kamar kullum nadawo daga makaranta,dama da dokin zuwa in iske Abbuna nake,saboda nasan wannan satin gaba daya he will be off duty,Ammyna kuwa dama tana hutu,babu abinda nafi so da qauna irin koda yaushe in riqa ganina da iyayena a gidanmu cikin jin dadi da walwala,there was never a dull moment with those two’s,because a haqiqanin gaskia ni bani da wasu best friends da suka wuce su,i dont think ko a school dinmu ina da wata qawa shaqiqiya guda d’aya,hasalima a school ko hayaniyar kirki ban cika yi ba,mussaman ma da na fara riqo da kalamen Yaa Mukhy,hakan ya qara taimakawa wajen yin takatsantsan akan duk abinda ka iya kawo mani matsala ko tonuwar asiri na.

“Ammyyyna,Abbuuna your girl is backkkk….”

Na shigo gidan namu da dokin sake ganin Abbun nawa a karo na barkatai cikin rayuwata,sai dai shigowar tawa yayi daidai da jin wata sabuwar fad’uwar gaba,take kuma nai turus riqe da handle din qofa ina zare ido,Allah yasani i wasn’t expecting someone like him zaune a falon gidanmu yana wani daddage kai,shi kadai ne cikin falon,and daalama ma yadan jima da zuwa,don banga wani alamun gajia a tattare dashi ba.

“Ina wuni.”

Itace kalmar da na iya furtawa,ji nai kuma gaba daya ya mani spoiling mood,saboda har ga Allah nakasa comprehending abinda ma zai kawoshi america ba lokacin zuwan su ba,kuma ma sai naga shikkadai yazo this time around.

Kalmar lafiya da ya jefi qeyata dashi ta sani jan tsaki a hankali,Allah yafi annabi sani banji dadin zuwan mutumin nan ba.

“Ke zonan.”

Na tsinkayo shi yana kirana lokacin ina shirin shigewa corridor din da zai sadani da bedroom din Ammyna,takaici naji sanin cewar bani da ikon qin amsawa,mussamman sanin da nai ya riga yasan da cewar ban kai ga shigewa ba,haka nan nadawo baya ina sassaita bacin ran fuskata.

Sai da ya mula ya mule naci tsayuwa kana ya dago yana kallona a ya mutse yace,

“Halan kin maidani dan iskane mai shan taba ta qeya?”

Mamaki ne ya lullubeni nakasa magana,kawai dai nna tsinci kaina da hangame baki ina tunanin me kuma nayi ma wannan mutumin yanzu yanzu daga shigowata?

“Yaa Mukhtar me nayi maka?”

Na tambayeshi cikin qarfin hali.

“Sabida kin maidani dan iska zaki shigo mana gida kina wani fizge fizge,kina cika kina batsewa koh?ke waittt tell me kinyi watsi da maganganun da nai maki kafin mutafi right?”

Ai bai rufe baki ba na hau rantse rantse da iya gaskia ta,domin kuwa yau dai ni nake ganin qarfin hali da rana tsaka,azo har gidanku anemi fin qarfin ka.

Hararar da yake balloman ya sanyani sararawa da rantse rantsen da nake yi na kawai sunkuyar da kaina ina mai tsinewa zuwan nashi gidan mu,kwarai mutumin mugun mood spoiler ne.

“Ba zan fasa tuna maki cewar ni dinnan da kike gani rabi mutum ne ni kuma rabi aljan ba,mind you i can hunt you down whenever you disobey me.”

“Kayi Hakuri.”

Shine kadai abinda nake iya furtawa.

“Sai nazo na mutsike wannan bakin inbakiman shiru ba,mayyar maza kawai.”

STORY CONTINUES BELOW

“Kaiiiii…..!ni wallahi ba mayyar maza bace.”

Na furta a lokacin da hawaye ke son zubomani,cin mutuncin nashi kuma yafara yawa,sai kace dai wacce ke xuwa tana liqe wa maza?laifina guda don nafadi ra’ayina akan irin kalar namijin da nakeso.

“Toh nine mayen kenan?”

Bansan yaqaraso gabana ba sai da naji hucin shi na shigar mani kofofin hanci,tsabar tsayin shi sai narasa inama zan kalla a fuskar shi,gaba daya yai mani qerere a ka yana mazurai,hakan yasani takure jikina ina maakyarkyata.

“Toh ni ai ba haka nace ba,amma dai don Allah kayi hakuri.”

Banyi tsammanin zai qyaleni ba farad daya,na daiga yasa ya hannu ya mangare qeyata,kana yakoma ya zauna yana mai cigaba da mani kallon banza.

“Bace man da gani,da wani qaton kanta a gurin.”

Da sauri sauri na arce nai hanyar dakina,nama fasa zuwa dakin Ammyn,direct gaban mirrow dina na nufa lokaci guda ina cizge qaramar Barret din dake kaina,so nake in hango inda kaina yai qatoto,haka nai quri ina karewa kan nawa kallo amma ban hango girman da Yaa Mukhtar din ke kirawa kan nawa ba,hasalima ni banda yalwatacciyar sumar da ke kaina zan iya cewa ina daga cikin halittu masu qaramin kai daidai daidai,amma kunji wannan baqin mugun sharrin da yake man,tsaki nai nafada kan gado na,lokkaci guda nariqa fatan yayi ya tattara yakoma qasar su inda yafito.

Sai dai me?da daddare lokacin gaba d’ayanmu mun hallara wajen cin abinci kunnuwa na suka jiyo mani zancen da ya sanyani shaqewa da qarfi,dakyar da ya Allahu nasamu dakyar nadawo hayyacina,kana kuma take yanke naji appetite dina yatafi,bani kuma da sauran kuzari,dan ragowar hope din danake ciki kuma yai tsalle yakama gaban shi.

Muryar Abbuna ta sake dawo mani,

“Princesss Yayanki ya sanar dake yadawo nan America da zama?zeyi undertaking degree nashi a nan Harvard University Cambridge,zai karanci Criminal Law.”

“Abbuu amma ba nan gidan zai zauna ba?”

Na furta bayan nadawo daga hayyacina,nidai a yanzu babban burina shine inji cewar ba nan gidanmu zai zauna ba.

Kallon banzan da Ammyna ke wurgo mani ya sanyani sunkuyar da kaina,toh ba dole inyi wannan tambayar ba?ko don basu da masaniya akan masifar dake tunkaro duniyata neh?

“Haba princesss,instead of you to extend your hearty congratulations to him sai kuma ki fara mita akan inda zai zauna?wai sai yyaushe zaki dena yarinta ne?you are almost 13 fa princess.”

Nikam dai ina ruwana,ni yanzu haka duk neman sauran jin dadin da yai mani saura nai na rasa,zancen gaskia bana hango irin halin ha’ula’in da zan shiga matuqar zancigaba da rayuwa da Yaa Mukhy a cikin gidan,its unimaginable.

Tsaki Abbu yai suka cigaba da cin abincin su ba tare da sun sake bi ta kaina ba,nikam na dade da afkawa duniyar tunani,how can i be spending the rest of my life with this wicked man a gidan nan?na shiga uku kawai.

***

Da sassafe natashi nai shirin makaranta ta as usual,tun bayan barina dinning arean ban sake kallon parlorn ba,gaba daya kowa na gidan haushi yake bani,why not Abbu zaai bar wannan mugun ya zauna mana a gida?inaganin kamar baa kyauta man ba.

A taqaice dai ban dawo hayyacina ba sai bayan kwanaki biyar da faruwar abun nadawo gida na iske babu mugun a gidanmu,its a relief one could ever imagine,a bakin Ammyna naji labarin yakoma hostel da zama,ta kuma qara da ce mani shegen dogon bakina watarana sai yakaini yabaro,tunda muka dai ke da gida,ban fahimci baqar maganar da take mani ba don duk dadi yagama lullubeni,ko banza dai baqin mugun yatafi zai barni

Ba wai na tsira bane,domin kusan duk weekends din dunia a gidanmu yake spending din su,kuma abu guda da na lura dashi shine bawai don Allah yake zuwa ba,mussamman yake samun guri a balcony din gidan matuqar zaiga giftawa ta ya shiga sanyani aiki ko kuma ya sani kneel down haka nan kuwa ba tare da nayi mashi kl da tari a fuska bane.

STORY CONTINUES BELOW

A haka yagama aji daya,nikuma a lokacin ina aji uku a high school,a shekarar ne kuma mummunan qaddarar rayuwata ta fara sanyo kai,a shekarar ne dukkan farin ciki na yai balaguro,a shekarar ne na rasa manyan jigogin rayuwata,iyayena abin alfaharina!

Ranar sha biyu ga watan nuwamba shekara ta dubu biyu da sha biyar nadawo daga makaranta kamar kullum,a ranar ne kuma mukai sendoff party da mukanyi a duk qarshen shekara nagama wannan session din,murna biyu ce kuma a ttate dani a wannan lokacin,kwanaki sama da biyar Abbuna baya gari shi da Ammyna,a yau dinne kuma nake expecting dawoowar su kamar yanda suka sanar dani,Miss Florence itace matar da take zama dani a gidanmu a duk lokacin da iyayen nawa suke bakin aiki.

Isowata gidanmu kenan bayan school bus ta dire ni,tun daga get din shiga estate dinmu naaji gabana yafara fadi a hankali,haka nan kuma idan ba idanuna ke mani gizo ba na hango mutane masu dan yawa a gaban gidanmu,and alongside ga motar company na Alaska and group itama a gefe,ban dai kawo komi a raina,tunani na wasu baqine Abbun nawa yayi.

Hakan yasa kaina tsaye na tunkari gidan namu,daidai da sanyo kainaa cikin compound in namu na hango Yaa Mukhtar cikin mutanen da bangama sanin suwaye ba,a kallo na farko da nai mashi sai naga ya canza man,sannan abu na biyu dana kula dashi again shine bantaba ganin ya dubeni with so much remorse, care and concern irin yau din ba,its unlike him you know,amma dai still ban fahimci ko menene ba.

Isowarshi yayi daidai da kamo hannuna guda daya da yayi ya janyo ni sosai jikin shi,and i couldn’t help to show a bit of suprise because it is not something im used to,ha’an yau meke damun Yaa Mukhtar?he seems diaturbed.

“This is her,their only daughter!”

Na tsinkayo muryar wani mai jan kunne ya fada cikin harshen turanci,kuma lokaci guda yana kallona cikin jimami,zuwa yanzu jikina yafara sanyi,nafara shiga rudu duk da qanqantar shekaru na,this is unusual,atmosphere din seems a bit complicated.

“Ni’imah kiyi hakuri kinji koh?”

Inyi hakuri kuma?Na dago da kaina sama ina daidaita idanuwana cikin na Yaa Mukhtar din?yau kam menene ya hau kanshi?

Da kai ya sake jinjina abinda ya fada din,al’amarin da yasani sake bin mutanen dake tsaitsaye a qofar gidanmu da kallo ina son sanin abinda ke faruwa,sake maida kallona na yi kan Yaa Mukhtar daake jan hannuna a sanyaye zuwa cikin gidanmu.

“Yaa Mukhtar meke faruwa?Ina su Ammyna?are they not yet back har yanzu?”

Na furta a hankali yayin da nake binshi salalau salalau zuwa cikin gidan,jikina yagama bani basa gidan ma,mussamman yanda na hango Madam Florence a corridor din shiga falon gidanmu a zaune dabasss,bana taba samunta a gida a lokaci irin wannan,domin da iyayena sun dawo take tafiya gidanta,sai ka in basa nan kuma.

“Just pray kinji ko Niimah?and kiyita karanta innalillahiwainna ilaihirtaju’oon okay?”

Nikam sakato nayi ina bin bakinshi da kallo,tambayoyina maqare a zuciyata,su waye wadannan baqin fuskokin a cikin gidanmu?and that aside,where are my parents?yaune ranar da sukace mani zasu dawo,i can even remember wayan da nai dasu dazu da asubah.

“My princess get ready,wannan summer din Nigeria zamuje hutu.”

Na tuna babban albishir din da Abbun nawa yai mani,wanda duk safiyar yau da dokin abun na wanzar da yini na,sosai kwarai nakeson zuwa ganin Baffana wato kakana Malam Junaidu,its been long da naje Nigeria,tun bayan da nagama aji daya a high school,ga Fareeda ma da i can’t wait to see her too.”

“Yaa Mukhy ina su Abbu?yakamata by now sun iso gida,or is something wrong?”

“Yes Niimah!something is wrong!but i want you to please calm down okay?i know you are a strong girl,plea……”

STORY CONTINUES BELOW

Hankalin shi ne shima yakoma inda idanuna ke kafe da qatuwar tv din dake parlor din namu,a qarancin shekaru na na fahimci me headline din ke nufi,mussamman ganin jirgin Alaska Airlines din danagani a sashe biyu,hoton farko jirginne kafin ya tashi maana lafiyayye kuma ingantaccen jirgi,a yayin da hoto na biyu kuma hoton jirginne a qone qurmus ya gama ci da wuta,koma ince har yanzu yana kan ci da wutan.

Wannan shine tashin hankali na farko da na fara fuskanta a cikin qananun shekaru irin nawa,a ranar na fara sanin me ake kira da maraici!a ranar nasan gibin da duniata ta samu,wannan babin qaddarar tawa shine yha taimaka wajen miqani wajen wata sabuwar qaddarar dake a rubuce tana jirana,qaddarar da ta taimaka wajen hauhawata zuwa gareku,qaddarar kuma daa ta sake taimakawa wajen bankad’a sirrin ainihin kl ni din wacece,qaddarar da samar da ni ta kuma samar da nawa d’an!

***

Fadar irin kukan rashin iyayena da nayi bata baki ne,duk da qarancin shekaru na na fahimci babban gibin da rayuwata ta samu,nayi kuka,kuka ba kadan ba,kukan da a kodayaushe yakan ziyarceni,wala a bacci ko a yayin da nake sallah,ko kuma a lokacin da nake cin abinci,aa kowane yanayi na tuna da Ammyna da Abbuna nakan rasa nutsuwa da annushuwa,ba shakka nayi rashin da bazan taba maida kwatankwacin shi ba.

Banqara kwana uku ba a garin da ba namu ba,Daddy yazame mani kwatankwacin mahaifina da na rasa,ya soni,ya qaunaceni,ya fifita ni,yakuma yi matuqar qoqarin ganin ya zamemmani uwa da uban da na rasa da dukkan qarfi da ikon shi,sai dai shi dinma da nake gani nakejin sauqi ashe ba mai jimawa bane,shekara na zagayowa da rasuwar mahaifana shima Allah ya amshi abinshi,babu ciwo babu komi sai dai muka wayi gari da mummunan labarin shi,mutuwa ce da ta tabani fiye da yanda mai karatu zai qimasta,kwarai da gaske yanzunne ma na zama maraimiyar ta gaske,ba kuma don muzguna ko cuzgunawar wasu daga cikin mutanen gidan ba.

Asalima daga ranar da na rasa iyayena daga ranar na fahimci hakan samar mani da ‘yanci yayi gurin Yaa Mukhtar,na sake samun sassauci ne bayan tafiyar Daddy,ba zan iya tuna wata kyara ko hantara ba daga Mammyn da nake zata ba,abu guda nasani shine tai qoqarin takawa Mukhtar burki biisa zaqewar da acewarta take lura daga gareshi a akaina,a kullum dai amsar shi guda ce.

“Mammy Hayatiey needs a shoulder to lean on,tana buqatar kulawarmu,look at her she is just a small kid with so much burden.”

Tsaki Mammyn takanyi ta ce “Ai mu nan duk ba mutane bane da she can lean on,kaine mai kafadar zinari da sai taka zatai leaning on,kasan Allah ka kiyayeni Mukhy.”

A koda yaushe reply din shi kenan,ko da kuwa a wayane inya bugo daga america inda yake karatu.

***

A cikin shekarar qarshe da muka gama secondary school din dana cigaba a nan Nigeria ne bayan rasuwar mahaifana kuma wani issue yai arising wanda dole ni din ce zanje nai sorting din shi out a american.

Shekaru uku kenan da rasuwar iyayena,babu wata magana daga Alaska and groups din sai a kwanan nan,company din sun buqaci heir to the decease din staffs dinsu da suka rasa rayukan su a plane crash din da ya faru three years back da su zo suyi clearing duk wasu documents din su,sannan kuma suyi signing duk wasu haqqoqin su da suke bin company din,da duk wasu kudaden da suke haqqin mamatan ne.

Mammyn ta so Fareeda ta rakani,sai dai kuma rashin lafiyan da ta fara mai dan tsanani ya sanya tafiyar dole ni kadai nayi ta,nakuma tafi ne bisa warnings din da Mammyn ta dora ni akai,duk da tabbacin da take dashi ba zan zauna gidan da Yaa Mukhtar din yake zaune ba,amma hakan bai hanata jaddada mani rashin yardarta da zuwa gidan da zan sauka ba da ta haramta,duk kuwa da cewa gidane na Abokin Abbuna da muke makwabtaka a zaman da mukayi a american,na amsa mata da bata da wata matsala daga gareni,domin dama dai ba wai wata alaqa ce mai mugun dadi ba tsakani na da Yaa Mukhtar din da tabi ta tsangwami kanta da shi a kaina,domin da tun tana dan boye jin haushin abin har tazoma a bayyane take nuna adawarta ga duk wata er kulawa da yake bani,nakuma fahimci duk hana mani hakan ne saboda maraicina.

Jirgin Yamma nabi zuwa American,shekkaruna kusan na uku kenan rabona da qasar,tun rasuwar mahaifana da aka tafi dani bansake waiwayota ba sai yau din,isowarmu unguwar da nai rayuwa a da ya taimaka qwarai wajen taso mani da mikin da nake qoqarin binnewa a kullum,ina kallo cab ta wuce gidan dayake a da mallakinmu ne nida iyayena,hawayen da nake ta qoqarin dannewa ne suka zubo daga idanuwa ba,ba shakka nayi matuqar kewar su.

Daga Bangaren Dr grema kuwa(abokin babana) da iyalin shi sunyi matuqar murna da sake ganina,haka ka sun amsheni da hannu bibbiyu cike da kulawar da suka saba bani dama can tun filazal,Dr dinne kuma yataimaka mani da duk wasu activities da nake undergoing cikin qasar,na daauka abu ne da baifi ya daukeni satittika kamar biyu ba,sai gani ina neman shafe wata bangama yin abinda yakawoni qasar ba.

Tun zuwana sau uku kacal Yaa Mukhtar din yazo gidan dana sauka,wai exams yake baya samun time din zama,sai dai lokaci zuwa lokaci yakan kirani yaji lafiyata dakuma in ina buqatar wani taimako daga gareshi?nikuma nakan nuna mashi no babu komi ina samun dukkan wasu maximun help and support daga Dr grema and his family.

Wayewar garin ranar asabar shekara ta dubu biyu da sha takwas ce ta kasance rana ta biyu cikin ranakun da ba zan mance da su ba a ilahirin rayuwata ba,yau itace ranar da shafin qaddarata na biyu ya bude,ranar da Mukhtar Gaya yazama silar shigata duk wani tashin hankali da kuma gallafirin da dunia ta ingiza ni.

Na tab’a fada maki cewar shi din mugu ne koh?toh a yanzu ne asalin muguntar shi zata fara sanyo kai!A yinin Juma’ar ne bayan na idar da sallar la’asar yakira wayana.+

“Zan zo gobe muje in kaiki kiga doctor din kamar yanda Mammy ta buqata.”

Shiru na danyi bayan naji abinda yace,a iya sanina tun last week mukai maganar zuwa inga likita da Mammyn akan azababben menstrual cramps din dake damuna,and idan ban manta ba banajin munyi magana akan Yaa Mukhtar dinne zai kaini,i know gaisawar da ma muke danyi da shi din da tana da ikon hanawa da tuni ta hana.

“Ni’imah na jina kuwa?”

Muryarshi ta dawo dani cikin hayyacina,banyi kuma qasa a guiwa ba na nemi jin yanda akai yasan zanje inga likita,duk kuwa da nasan yawan tambaya na daga cikin abinda yafi tsana.

“Malama just be ready,gobe qarfe 10 na safe zanzo in kaiki.”

Nima kuma ba tare da na sake zafafa bincikien ba na amsa mishi da toh,na kuma kawai sanya wa raina qila Mammyn ce ta canza shawarar akan yazo yakaini,qila ta fara sakkowa ne,na furta hakan a zuciyata.

Misalin karfe takwas na dare ina kwance a qaramin parlour din gidan Dr Grema ina duba wani littafi Every Woman,littafin ya dauki hankalina sosai,qasan raina na riqa jinjina qudirar ubangiji,mussaman yanda naga marubucin littafin ya baje basirarshi wajen yin bayani filla filla akan duk wasu Anatomical and physiological aspect na diya mace,kwarai littafin ya kara mani haske sosai akan abubuwan da bansani ba,kuma banajin zan sansun in ba ta wannnan hanyar ba.

(Note:Every Woman a gynaecological guide for life littafine mai matuqar amfani da muhimmaci ga ko wacce diya mace,a ganina littafin yabayyana duk wasu aspects na diyoyi mata da suka danganci jikinta lafiyarta da kuma duk wasu matakai da mace kan taka tun daga yarintar ta zuwa matantakar ta,kamar su matakin balaga,haihuwa da kuma tsufa,a taqaice Every Woman littafi ne da nake jin ya cancanta ko wacce mace ta mallakeshi,musaaman domin qaruwar kanmu gaba d’aya.)

Soosai naa tsunduma ina bin littafin daki daki,duk da ina cikin sahun mata masu son jarirai sai da na jinjina yanda marubucin ya bayyana matakai daki daki wadanda suka shafi tun daga samuwar cikin,kwanciyar shi a mahaifa,rainon shi,girman shi,haihuwar shi da duk sauran al’amura da mace kan fuskanta a yayin da ta dauki cikin,domin kuwa take na riqa yi wa kaina tambayar anya nikuwa zanma iya haihuwa kuwa?domin abubuwan dana gani kuma na karanta din sunyi matuqar tab’a ni ba kad’an ba.

A taqaice sai da nakai kusan qarfe goma sha d’aya ina duba littafin,qarshe dai da najj bacci ya fara ribata ta na yunkura na rufe littafin gami da zuwa na sokeshi cikin book shelve din dana dauko shi,book shelve din da yazama amini kuma abokina tun zuwana garin,ba laifi ni din asalin bookworm ce,kwarai i so much love reading,mussaman yanzu da bana komi sai dai idan an buqaci ganina haka akan musabbabjn zuwana qasar ta America.

Direct kitchen na nufa domin shan coffee kafin naje na kwanta,tunawa da nayi qarshenta a daren yau ko gobe inyi ovulatinoya sanyani sassauta zuba sugarn da nayi niyyar zubawa a coffee din nawa,na taba fada maku ina cikin irin emmatan nan masu tracking ovulation period dinsu?ba don komi ba sai don wani abu ne dana taso kuma na girma naga Ammyna nayi.

In ban manta ba,har takoma ga ubangijin ta duk wata cikin circlen ovulation date dinta take,banda ovulation dinma hatta da menstrual circle din ta duk were on track, aand ba zan iya cewa ga dalilin da ya sanya take hakan ba har sai yanzu dana girma na danyi hankalin kaina naso in fahimci dalilin ta,sai dai nima bansan meyasa na bi sawun Ammyn nawa ba,abu guda nasani dai shine ina tracking ovulation dina ne in preparation for the undying pain din da nake fuskanta yayin da zan b’ule,and sosai abun yazame manj jikin da bantaba fashin yin hakan ba.

STORY CONTINUES BELOW

Kurban qarshe naiwa Coffee din a yayin da idanuwana ke faman rufewa,banajin zan iya yin wanka ma saboda irin baccin da ke neman cin qarfina,ina gaf da ficewa daga Kitchen dinne Aunty Madina ta shigo kitchen din,Aunt Madina sistersn Mummy ce matar Dr Grema,ta girmeni sosai don inajin za tai irin 22 dinnan,whilst ni im just 16 yanzu.

“Ah ah qanwata bakiy bacci ba kema har yanzu?ko kema mood swings dinne ke swinging dinki kamar ni?”

Tana da yawan fara’ah da barkwanci,duk da tazarar shekarun dake tsakaninmu baisa ta riqa jin ita din wata babba bbace akaina,asalima har zama take ta bani labarin mijin ta dake can South Korea yana Masters din shi,whilst ita tana nan America tana qarasa Degree din ta akan Psychology anan Stanford university.

“Wallahi kuwa Aunt Madina,inacan ina duba Every woman,gaba daya book din yatafi da ni har bansan its late ba,gaskia I’m in awe with the book,duk da ko rabi ma banyi ba.”

Sai sa ta gama taune loman sandwich din da ta riga ta gutsira kana ta bani amsa tana dan tari kadan.

“Ahh ai every woman yaci sunan nashi,infact nifa da zaabi ta tawa koh?a sanyya dokar cewa ko wacce mace a duniya ta mallaki na ta copy din on her own,ba don komi ba sai tarin ilimin dake qunshe da littafin,sincerely speaking the book is just for every woman din da gaske.”

“Gaskia kam Aunt Madina,wai yunwa ne ya tasheki ne?naga sai saka loma kike ba kama hannun yaro,kalla a tsaye ma kike fa.”

Na ida maganar ina dariyar yanda take ta fama cika baki da Sandwich,ga kuma fresh milk tana korawa loma bayan loma.

“Hmmm bari kawai Ni’imah,ai ina cikin wani yanayi a cikin gidan nan,come matso kiji wani sirri.”

Ta yafito ni da hannu daidai lokacin da take dan rage murya,aa hankalk nima na fasa ficewar nakoma baya ina er dariya qasa qasa,ko ba komi Aunty Madina ta iya buga chapter, nasan may be wani labarinne ke cinta,sai da ta kawo bakin ta kusa da kunne na kamar wanj zai iya jiyomu tace,

“Ke cikine fa dani wallahi.”

Haaaaaa!naja wata ajiyar zuciya,lokaci guda na nemi tsanyara ihun murna,amma hakan bai samu ba sakamakon toshe mani baki da tayi tana hararata.

“Ke tona mani asiri zakiyi neh halan?”

Ina dariya qasa qasa,na girgiza mata kai,kana a hankali na rage muryata nima nace,

“Kai Anty Madina,wai kina nufi baki gaya wa kowa wannan good news dinba?har Mummy?baby fa zaki haifo Aunty Madina?”

Tsaki tayi bayan ta jefa lomar qarshe ta sandwitch din,banga alamun kuma ta qoshi ba,ta dai dubeni ta bani amsar tambayata.

“Wallahi kunya nakeji Ni’imah,kinsan last da Babyna yazo Mummy hanani kebewa tayj dashi qiri qiri,wai bata so in samu cikj yanzu da nake final year,so ita duk nufinta i should avoid him by all .means don gudun shigar ciki,amma kinga dake kunnen qashine dani ga irinta nan nakwaso abinda baa so!”

Zugudi nayi ina dubanta,tofa ni bansan ma me zance ba,kawai dai sai nai dabarar shhare wancen zancen nace mata

“Nikam Aunty Madina ba ba’aso mai ciki nashan kayan sanyi ba?yanaga ke sai antaya wa tumbinki sassanyan madara kike?”

“Hmmm lallai yarinyar nan kin kau san me ake ce ma cravings?toh wannan shine,yoo iban sha fresh milk dinnan ba ai sai cikkn ma ya zube gaba daya,uhmm astagfrullah ba amin ba wallahi masiffar son cikin nan nake duk da cewar kuwa baifi two months ba.”

Rausaya na riqa yi a hankali,ni kaina bansan meyasa ba na riqa jin wata annushuwa da jin dadi,in banyi qarya ba ma har ji na riqa yi inama ni ke da cikin nam,wai!da ya zanji?like i want to feel abinda akeji idan ana da cikj,sosai mata masu juna biyu ke burgeni,i mean to be able to raise a human a cikin cikinka its something worth crushing on.

STORY CONTINUES BELOW

“Wuce kije ki kwanta Ni’imah,naga alaman gaf kike da tona mani asiri gurin Mummy,gashi Babyna ya ce kar ince mata komi,idan cikin ya fito ai zata gani,ah ah to nikam kuwa yanda yace haka zaayi.”

Ina dariya na nufj hanyar waje,

“Kai Aunt Madina,mudai fatan mu Allah yarabaku lafiya,yaci da en baya irin muuuuu……”

Na fella a guje ina dariya,nasan da kusa da ita nake harda dundu zata hada mani,amma duk da haka sai da najiyo muryarta tana fadin,

“Haba yarinya kamar gobe ne,what are eating na baka is falling down?”

***

I’m not a fan of make up,white powder kawai nake murzawa fuskana sai kwalli da kusan ko yaushe baka raba idanuwa na da shi,sai kuma chap-et da yazamemani tamkar addiction sanya shi,dashi nake yawo kuma nake bacci,domin labbana shine madai abinda ke tab’asu.

Abaya mai kalar maquba na sanya ma jikina,shigar da nafi yi kenan a rayuwata tun bayan dana fara zama emmata,kawai nidai i hold a very special something for Abayas,ko may be hakan na da nasaba da comfortability da nake samu a shigar ne oho!amma dai ina qaunar Abaya,qauna ba er qanqanuwa ba,don zan iya cewa rabin kayana sune.

Qaramar jakata na dauka tare da wasu tarkacen da ba’a rasa ba,jikina kwata kwata baya mani dadi sosai tun wayewar garin na yau,sai dai na danganta hakan da ovulating da nakejin zanyi yau din,in ba jikin ne ma ke fada mani qarya ba inajin sabbin feelings kadan a tattare da ni,andd feelings din ke qara tabbatar mani da tracking calender din nawa ba qarya bane.

A corridor na ci karo da Aunty Madina,hannunta qatoton kofin shayi ne mai kaurin tsiya,don ina iya hango yanda kalar shayin ya juye kalar Ovaltine din da tai matuqar cikawa a shayin,gefen hannun ta kuma wasu tiqa tiqan cookies ne jere ras ciki wani tray,aifa shikenan an bani kuma da Aunty Madina a cikin gidan nan,dama yaya lafiyan kura ballantana da tayi hauka?

“Goodmorning Aunty Madindin.”

“Morning Pretty,wai har zaki wuce?Yayan naki ya qaraso kenan?”

Ina gyara zaman mayafin Abayan a kaina nake bata amsa,

“Eh fa Aunty Madina,bai dai riga da ya qaraso ba,but yamani text wai gashinan qarasowa nan da 15 minutes,Aunty Madindin how is our baby doing today?”

Sai da na rage muryata can qasa kana na jefeta da tambayar,nayi expecting dundu ne,sai na tuna ashe duk hannayen nata akwai kaya,shiasa sai dai ta ballo mani hararara,amma duk da haka sai da aka kalli gabas aka kalli yamma kana akace man,

“Motso kiji,he kicked twice a wayewar garin nan!”3

Qwalalo idanuna nayi waje inajin dadi,dagaske kuma nagama yarda da abinda tace din,sai bayan na isa kusa da ita sosai ne domin sanya kaina akan cikkn nata ne ta sa qafa ta harbeni,

“Matsa ki ban guri er tusa,ke da nace maki cikin is just 2 months old ta yaha kike expecting zai fara kicking?”3

“Kai Aunty Madin wai dama wasa kike?”

Tana dariya tace, “Ah ah da gaske nake biyoni ki tabbatar!”

Ta ida zancen yayin da take nufar saman benen da zai kaita makwancinta,nima dariyar nayi na nufi kofar da zata sada ni da parlorn Dr Grema,zaune na iske shi shida Mummy,bayan na gaidasu na sake tuna masu asibiti da zanje yanzu,adduar a dawo lafiya suka bini da ita don sunsan bani da wata matsala tunda ma da Yayana kuma dan gari nake tafe.

“Hurry up,ina waje.”

Text dinshi yai popping akan allon screen din wayata,ko me ya hau kanshk yau da ture turen message,last i check shi din ma’abocin kiran waya ne fiye da tura saqo,sai dai bansani ba qila ni yakewa haka.

STORY CONTINUES BELOW

Motar tashi tinted glass ce,hakan yasa bana hangoshi kwata kwata har na isa inda motar ke a parke,ina qarasawa naji locks din motar sun bude,shiasa kai tsaye na bude gaban motar na shigo,nasanshi ma’abocin qamshi ne,shiasa banyi mamakin sassanyan qamshin dake fita daga motar ba da kuma mamallakin motar.

Ina idasa rufe murfin yai wa motar key,al’amarin da yasani na juyo ina kallon shi domin na gaishe shi,in ba idanuna ke mani gizo ba,he look tired,in fact yayi kama da wanda ke matuuqar buqaatar bacci da hutu,duk kuwa da alamu sun nuna babu alamun ma cewar beyi wanka ba a tattare da shi,and kamar something is wrong with him,sai dai a lokacin banyi figuring out ko meyene ba,sai daga baya na fahimci duk me hakan ke nufi.

“Ina kwana?”

Na furta a hankali,banaso ko kadan na kuskure dan sassaucin da nake samu daga gurin shi ya bace,banyi tsammanin ya amsani ba sai da na dan dago da shirin in kalleshi naga shima din kallo na yake.

“Appointment dinki da Dr Craig has been postponed!”

Na juyo da mamaki inajin abinda yace din,toh kuma yuasan da haka meyasa zai fito dani?he could have told me ma tun a waya ba sai na shirya ba,shiasa ma nai zugudi inajiran jin dalilin da yasa toh ya fito dani bayan yasan bbabu yanda za ai naga Dt Craig din yau,wanda shine Doctor din da muke gani tun ina qarama.

“Well karki damu,na maki booking appointment da wani Doctor din,yanzu haka yana jiran zuwan mu ne.”

Nikam bansan meyasa naji kwata kwata ganin wannan doctor din da ban sani ba bai mani dadi ba kwata kwata a raina,Allah ya sani nafi sabawa da Dr Craig,ko bayan da nakoma Nigeria na dade bangama sabawa da Family Doctor din su ba.

“I’m i communicating?”

Muryarshi ta maidoni,a hankali na girgjza mashi kai alamun eh,daga haka bai sake kallon gefen da nake ba ya cigaba da tuqin shi yana mirgina kai a hankali,a yayin da nikuma na maida kaina bisa murfin motar ina en tunane tunane na har muka isa asibitin da ke Baltimore,sannan naga an rubuta Johns Hopkins Hospital Baltimore a jikin signboard din dake girke a get din shiga asibitin.

Asibitin da anan ne na ci karo da qaddarar rayuwa ko kuma ince zabbabiyar qaddarar da Yaa Mukhtar ya zabi ya sanyani saboda wanj dalili nashi maras tushe,ashen dan adam zai iya zama mai son kai haka?har gobe nakasa yarje wa kaina wannan baqar qaddarar tawa zab’a mani ita fa akai,da qafata aka daukeni aka kaini,dan uwana,wanda kuma shine uban dana,shi ya dauki nauyi da ragamar yin wasa da rayuwata,wasan da bani da masaniyar ashe irin shine wasan da tawa mahaifiyar tai amfani wajen samar da ni a ban qasa!alhamdulillah da mutane irin Yaa Mukhtar da Ummana,Alhamduliah da dukkan qaddarorina,munanan da kuma kyawawaan!

***

Bude idanuwa na nayi ina ganin dusu dusu,in ban manta ba shigowar mu cikin OPD din ba da jimawa ba kira yazo kanmu,daalama likitan yasan da zuwanmu,domin fuska mai dauke da murmushi,kulawa da kuma sanayya ya amshemu,sai daj daga baya naga ya umarci Yaa Mukhtar din da ya dan bamu wuri.

Tambayoyine yayi mani masu qarancin yawa game da yanda nakejin cramps din,sosai nai mashi bayani da fatan samun sauqi,bayan en rubuce rubuce ya umarceni da in shiga bayi inyo fitsari,bayan na fita aka dibi blood sample dina,nidai ina zaune ina kallon su,bayan wasu mintoci kadan wasu nurses guda biyu suka umarceni da in shigo wani dan qaramin daki da yai mani kama da operating room amma ba shi bane,daga haka akai mani allurar da bacci ya sureni.

Bude idanuna yayi daidai da haduwar idanunmu da na Yaa Mukhtar din atsaye a gefen kaina,dankwalin kaina ya zame,inba mistake nayi ba kamar hannunshi ne bisa sumata yana dan shafawa a hankali sai dai bayan buude idanun nawa yai hanzarin dauke hannayenshi gami da bone fuskar shi.

“Ya dubaki ne sosai,yace infection ne sosai yai maki yawa,ko da yake yanzu zaizo yai maki qarin bayani.”

Bai rufe bakk ba,dogon likitan ya shigo da fara’ar shi,cikin kulawa yake tambayata yaya nake jin jikin nawa,lafiyata lau dai ni last i check,asalima da qafafuna na kawo kaina a sibitin,amma yanzu naji kamar cramps sosai na neman kamani,shiasa nafada mashi abinda nake ji din kaina tsaye.

Take kuma ya nuna mani ba wata matsala bace duk infection dinne,yanzu dai ga magunguna nan da allurai zai bani,bayan sati daya zamu dawo yaga improvement din da aka samu,zancen kenan muka tattara ya maida ni gida,a mota kuma ya riqa jaddada mani da shan magungunan da aka bani in inaso in samu lafiya,har ma yaso yabani haushi,haka ya riqa yi mani kullum zai kirani a waya safe,rana da dare yana tambbayar ko nasha magunguna na,da abu ya giga ma har takowa yake yazo gidan tsabar kulawa.

Sati na zagayowa da farar safiya ya dirar mana,nikaina har mamakin wannan masifa nake,amma duk d ahaka ban kawo komi a raina ba,a wannan ranar ne ya daukeni ya maidani asibiti kamar yanda likitan ya buqata,yadubani yace dole ina buqatar aikk,zaa kankaro infection din da yake nema ya toshe mani mahaifa,hankalina yatashi naji babu abinda nakeso sai lafiyata,hakan yasa nabada hadin kai domin ganin an rabani da cutar dake neman hanani sukuni.

Sai dai abinda bansani bane ashe,yau itace itace ranar da zaa dasa gudan jinin Ya Mukhtar cikin mahaifaata ba tare daa na sani ba,a satin da ya gabata,ashe qwayayena(matured eggs) aka diba domin ayi fertilising din su da sperm din Yaa Mukhtar,sati dayan da aka bamu muje mudawo shine duration din da suka diba domin completion na fertilisation din,don haka dawowar da mukayi yau itace ranar da aka dauko selected Embrayo(wato fertilised qwaina da sperm din Yaa Mukhtar din da aka hada a lab suka tashi Embrayo) domin a dasa shi a mahaifata.

A haka aka dasa mani cikin Yaa Mukhtar cikin mahaifata da sunan ana mani qaramar tiyata ne akan infection dake damuna,wannan shine sabon shafin qaddarar da aka tabo mani da ya girgiza qananun shekaru na,a yau ne na dauki cikin da bani da masaniya akan shi.

Wannan itace muguntar farko da nakeson kusan Mukhtar Gaya ya fara dora wa duniyata,shin kunajin ya cancanci in yafe mashi?8

***

About AIS

Check Also

HOD’IJAM CHAPTER 7 KARSHE BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 7 KARSHE BY NOORIEEYAH                 Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *