HOD’IJAM CHAPTER 5 BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 5 BY NOORIEEYAH

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Birnin Dikko.

Zuwa yanzu da suke da kwana daya da yini daya a cikin gidan Justice Sambo Kaita,a dan mizanin hankali irin nata,ta fahimci mutane ne masu tarin karamci da yakana,bayyanuwar ta cikin gidan bai sanya sun matsanta mata da tarin tambayoyi ba,sai dai qalilan wadanda suka zama dole a sani,misali sunan ta,da kuma sunan babyn ta,babyn da tun zuwansu gidan yasamu dukkan kulawar da yake buqata daga shi har uwar,bugu da qari har asibiti Ammyn ta kaita aka duba lafiyar su,mussaman ita Niiman da take cikin danyen jego.

Kwarai Ammyn take da tarin tambayoyin da take buqatar yiwa Ni’imar,har yanzu qwaqwalwarta ta gaza fahimtar yanda zaa ce qanqanuwar yarinya irin wannan haihuwa,duk da cewar ba abu bbane sabo,sai dai a yanayi inka dubi Ni’iman ba zaka danganta ta da irin yaran da suka fito daga karkara ba,ballantana ace auren wuri akai mata,sai dai kuma bata tsananta bincike ba,abu guda ta sanya wa ranta shine,bata yi wa yarinyar mummunan zato,haka kuma tana zaton cewa wani gagarumin abu ne ya rabota da gida,koma tace da mijin ta,toh koma dai menene tana jin time will tell.

Gidan Justice Sambo Kaita,gida ne mai girman gaske,domin kuwa gida ne mai dauke da zuri’ar gidan gaba daya,mussaman idan mukai duba da cewa mata hudu ringis Justice din ya mallaka,manya manya parts har shidda ne a cikin gidan,ciki kuwa harda BQ na en mazan gidan da ba su kai ga gaciyar aure ba.

Hajia Binta itace matarshi ta farko suna kiranta da Hajia Mama,wacce zamu iya cewa itace tun auren saurayi da budurwa,ikon Allah kuma ba ta taba haihuwa ba,sai dai a koda yaushe baka raba sassanta da yaran en uwa da abokan arziqi ta kowanne fanni,mace ce mai hakuri da tarin kirki,kuma ba ma’aikaciya bace.

Sai kuma Hajia Khadi,wacce suke kira da Doctor Mommy,itace matar shi ta biyu,macece er boko kuma er kwalisa,babbar lecturer ce a jami’ar bayero dake kano,tana da yara biyar mata hudu,sai namiji daya,kuma shine na biyu,ukun duk sunyi aure,saura autar ta guda d’aya Fa’izah,tana da nata kirki itama,amma fa macece mai fadan tsiya ga ta kuma no nonsense ce.

Mai bi mata itace Hajia Nana wacce ake kira da Mama,isashshiya kakeji,ko don tanajin kamar itace uwar garke a kafatanin gidan ne oho,domin kuwa tafi kowa ‘ya’ya a gidan,yaranta goma sha biyu,maza bakwai mata biyar,matan gaba dayan su sunyi aure,mazan ne dai uku sunyi aure,sauran hudun na nan a gida,biyu suna aiki,yayin da biyun kuma ke final year a jami’ah,kasancewar gwanne da ta riqa yi lokacin da take haihuwar ta,ya sanya mafi yawan yaran suke kai daya,idan ana neman mafadaciya mata aka samu Hajia Nana to anzo wajen,fitinanniya tun a wancen lokacin da suke da quriciyar su,har ko zuwa yanzu da girma yazo masu,babbar er kasuwa ce.

Sai kuma ta qarshe Hajia Barrister Safiyyah,wacce suke kira Ammy,amarya a gidan Justice Sambo,mace mai tarin kirki da yakana,gata kuma wayayyiya mai tarin ilimin addini da na boko wacce ta iya zama da mutane,yaranta hudu duk mata ne,biyu sunyi aure,Zainab da Rahma,saura Ummita da auta Yusrah,amma anfi kiranta da auta.

Sai kuma oganniya kwata kwata,mahaifiyar shi kanshi Justice Sambon Hajja Daada,tsohuwa mai ran qarfe,ga kirki ga fada duk ta hada,tana matuqar son zuri’ar ta,macece mai son kyauta,babu ruwanta kowa nata ne,kama daga baqo ko dan gida,part din dake kusa da na Justice ne part din ta,mafi akasari kuma baka raba sashen nata da matasan gidan a ciki suna chapter,esp da dare,dama dai Yusra ce er gidan ta,ta hannun daman ta kuwa,domin hasalima a wajen ta take gaba daya, acewar ta kuma kaf gidan babu mai kama da justice sambo din sak sai ita,shikuma justice Sambo din kowa yasan carbon copy din Daadan ne,farar bafullatana mai tarin kyau kuwa har yanzu da tsufa ya murqushe ta,sai dai daqauqau take,babu inda bata iya sanya kafarta.

Gidan Justice Sambo gidane da ya qunshi kwanciyar hankali da mutane masu tarbiya gwargwadon hali,gidane kuma na ‘yan bokon gaske,nasan kowa yasan su waye katsinawa?mutane ne wayayyu kuma masu tarin ilimi,haka dai ta kasance da wannan zuri’ah,duk da munsan cewa yau da gobe tafi gaban wasa,babu inda baa samun tsaiko na dan wani lokaci,amma dai gidan Justice gidane da ya samu shedar arziqi a fadin garin katsina da kewaye.

STORY CONTINUES BELOW

***

Wanka ta fito daga makewayin dake manne da dakin baccin Ammyn,fitowarta lullube da tawul a kanta yayi daidai da shigowar Yusrah,a kallo guda da zaka iya yiwa Yusran zaka iya bata shekaru kamar sha shidda zuwa sha bakwai,tana da tsayi kuma siririya ce sosai,hakan ke bayyana tsantsar kamananninta da Daada,fara ce qal,don har wani yalo yalo take,a taqaice dai kyakkyawa ce ajin farko,may be hakan yasa take dan fama da guntun rawan kai,domin samsam halayenta da na Ummita sun banbanta,Ummita akwai nutsuwa qila kuma hakan na da nasaba da girma da wayau da tafi Yusran.

“Ni’imah Ammy tace in kin shirya ki fito palour kici abinci,tace kuma ki hanzarta kar abincin ya huce,ta lura bakya son cin abinci.”

Murmushi Ni’iman tayi tana mai gyada kai,lokaci guda tana sake jinjina girman karamcin mutanen gidan,zuciyarta fal tunanin dunia ta hanzarta shiryawa cikin wata plain green abaya da ta gani aje bisa gadon,domin tun zuwanta ta fahimci sayayyar kayan da Ammyn ta sanya Ummita taje tayi masu ita da Fawaad,hakika ko haka nan mutanen nan suka barta ba zata dena gode wa karamcin su ba.

Tunda ta doso palourn gaban ta ke faduwa,yau palourn a cike yake sabanin yanda ta saba ganin shi,domin kuwa sashen na Ammy shine bai cika daukar hayaniya ba,most of the time hhayaniyar tafi yawa a sashen Hajia Mama ko kuma sashen Daada.

Baqin fuskokin da ta fara gani ya qara sanyata dan diriricewa,hakan yasa jiki a sanyaye taqarasa kusa da Ammyn ta zauna,lokaci guda tai qarfin qara sautin muryarta domin gaishe da baqin falon,wadanda suka kasance yawancin su maza ne.

A tare kusan dukkan su suka amsa,sabanin wani guda daya dake can kan 3 sitter din da suka qawata falon miqe da qafa yana daddana waya,babu alamun fara’ah ko annushuwa a baqar fuskarshi dake kallon waya,girar nan kuwa a hade domin daya har ta hade da dayar tsabar cikar girar,ita dai Niiman ba ta san ya akai ba,ba kuma tasan dalilin da yasa tai sakato ba tana cigaba da zura mashi ido a fakai ce ba.

Sauke idanuwan ta tayi kan uban gashin da ya kewaye fuskar shi,hakan ya samar da wani irin dogon gemu kai kace qanin osama bin laden neh,hancin shi da idanuwanshi sunfi komai kyau a baqar fuskar tasshi,eh baqa mana,domin kuwa baqi ne sosai,irin baqin nan mai sheqi da kyau,wanda tsabar hutu har wani yar yar yar yakeyi a idanuwan masu kallon shi,lokacin kuwa da ya d’ago idanuwan shi ji tayi gabanta yayi wata iriyar faduwar da batajin ta taba yin irin ta.

A qasan zuciyarta ta riqa ambataon “Fa tabarakallahu ahsanal kaliqeen,tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya qagi wannan halittar,dama akkwai baqaqen mutane masu kafirin kyau haka?masha Alla,masha Allah!

Daga can gefen ta tajiyo muryar Yusrah.

“Niimah meet my able brothers.”

Sai tai nuni da wanda take zaune kusa da shi tace,this is my fav Yaa Saddiq,ga kuma Yaa Bilal ta nuna wanda ke gefen Ammy,ga Yaa Usman usyy,ta nuna na kusa da Ummitah,and then Yaa Kabeer,watau Kabeer Singh namu na nigeria,ta qarasa maganar tana dariya yayin da take nuni da wancan na kwanshe Mr blacky.

Gyada kai take yayin da take sake gaishe su,bata fuskanci wata matsala ba daga sauran ukun,mussamman Yaa Usman wanda shi din ta lura mutum ne mai barkwanci,domin kuwa har jan ta yafarayi da hira,mussaman da yaji ance Babyn dake hannun Mammy nata ne,idan har sunyi mamaki ma toh ba su bayyana mamakin nasu ba.

Hira sosai ce ta kacame cikin falon,bakajin muryar kowa sai ta Yusrah da Yaa Saddiq,domin da alama tasu tafi zuwa d’aya,sai kuma Ammy da su Usman,Bilal,da kuma Ummita ke ta su hirar,hirar dai duk akan matsalolin da qasar ke ciki ne,mussaman wannan kidnapping din da ya addabi al’umma.

Shi Malam Blacky dama tun shigowarta palourn har yanzu bataji muryar shi ba,babu abinda yake yi inbanda latsa waya,kwata kwata hankalin shi ma baya kansu ballntana ya san wace wainar suke toyawa,hakan yasa daga ita sai shi dinne baa jin muryoyin su a cikin hirar,ita dai tai zugudi tana satar kallon shi ba tare da ita kanta tasan tanayi din ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Af,nikau Niimah ba abinci nace kifito kici ba,kinganni hankalina yayi gaba,kema kuma naga kin sha’afa,maza tashi kije kici abinci,banason ganin kina wasa da cikin ki,mussaman domin yaronki,kinga kuwa inkina so kiganshi yayi bulbul yai girma yai kyau tofa kema sai kina daurewa kina cika tumbin ki,ko ba kyaso yazama abin shaawa a idanun mutane?”

Murmushi Niiaman tayi yayin da take sunne kanta cikin tafin hannun ta,ita dai Allah yasani ba qaramin nauyi take ji ba in ana hirar Fawaad a matsayin d’anta.

“Haba tanaa so mana,ai ni zaa baiwa yayen shi ma ko Ammy?lokacin nasan kun aura mani Chicago,sai mu riqa bashi abinci da yawa yazama qatoto kamar Fu’ad din Aunty Bahijjah.”

Cewar Yusrah tana rausaya wuya.

“Chicago?”

Ta tunano sunan da kuma fuskar mutumin,ita sai yanzu ma da aka ambaceshi ta tuna shi,toh amma meyasa tun daga ranar ba ta sake ganin shi a gidan ba?bata jin ma dan gidan nan ne,domin shi kamannin shi daban suke da na sauran mutanen gidan,kasancewar duk en gidan kusan duk kammanin su daya,duk suna yanayi da juna kwarai,sabanin shi da sam basa kama ko kadan.

“Toh er wahala zaki fara soki burutsun naki ko?” Cewar Ummitah tana hararar ta.

Zumbura baki gaba Yusran tayi,lokaci guda tana mai hade rai.

“Eh naji koma me zaki ce kice din,duk baqin cikin mutum sai na auri Yaa Chicago,ehe!”

Ta murguda baki yayin da take qoqarin miqewa domin rantawa ana kare,domin tafi kowa sanin dundun da Yaa Saddiq ke tiqa mata matuqar ta fara yiwa Ummitan rashin kunya,ilai kuwa har ya daga hannu yana shirin damqo ta aikuwa ta arce da gudun ta,ta bar sashen gaba d’aya.

Girgiza kai kurum Ammyn tayi,can qasan ranta kuma tana fatan hakan yazamana yarinta ce daga cikin yarintar Yusran,domin tafi kowa sanin cewa aure tsakanin ta da Chicago ba abu bane mai yiwuwa ba.

Kukan da Fawad din ya fara ne ya dakatar da Niiman daga kunun gyadan da take zubawa tumbin ta dagacan saman dinning table din dake kusurwar falon,sai dai bata waigo ba kasancewar kunyar hakan da take ji,ba tare da tayi tsammani ba ta jiyo Muryar Ammyn na kiran sunan Kabeer din.

Sai a lokacin ta waigo domin ganin ko me kenan,wannan karon a tsaye yake hannun shi sanye cikin wandon track suits din dake jikin shi,farar armless t shirt ce a jikin shi mai v-neck,hakan ya taimaka wajen bayyanuwar gargasar jikin shi,sannan kuma awannan lokacin ta sake tantance tsayin shi,duk da dama ta gama yarda dogo sosai mussamman lokacin da yake kwance kan 3 sitter din,sosai figure din nashi ya cinye tsayin kujerar,amma yanzu ganin shi a tsaye yasa ta qara amanna da tsayin nashi,a da tana ganin tsayin Mukhtar sosai,amma yau sai take ganin tamkar wannan din yakere Mukhyn,qila kuma haka nada nasaba da rashin qibar wannan dinne,domin Mukhtar ya danfi wannan er qiba kadan.

“Ka ga tayani miqawa Ni’imah yaron nan Kabeer,inajin yafara jin yunwa ne.”

Babu musu ya nufo Ammyn,sai dai kuma ba nan gizo ke saqar ba,goganku malam Kabeeru bai iya daukar jarirai ba,duk kuwa da showel din dake nannade da Fawad din mai laushi,amma saigashi ana faman daga wajen saisaita yanda zai riqe babyn,uta kanta Niiman dake can saman dinning juyowa tayi gaba dayan ta tana kallon abun daria da al’ajabi,ai ita ta dauka kowa ya iya daukar jariri,ganin yanda Ya Mukhtar ya kware da daukar Fawad din tamkar wani mace,ko ita batajin ta kaishi iya riqe Fawaad din.

“Toh bari dai in miqa mata shi da kanta Kabeer,yi tafiyarka,wannan haka zaa haifi maka babyn aita faman daga dakai wajen daukar Babyn?haba Babana kadena badani mana.”

Sai yanzu tajiyo muryar shi,irin deep husky voice dinnan gareshi,daga jin sautin muryar tashi wani abu ya dunqule yadaki qirjin ta,abunda bata tabaji ba,sai kuma ta sake samun kanta da sake wara kunnuwa tana zuqar sautin muryar tashi,wacce ta riqa jin duk dunia babu mai dadin ta(a kunnuwan ta amma).

STORY CONTINUES BELOW

“Ammy kawoshi zan iya mana,you know gara infara koya before hand.”

“Garaf kam ka koya,amma ba yanzu ba kar ka yada mani jika qasa.”

Cewar Ammyn tana daria,yayin da take miqewa domin kaiwa Ni’iman Fawad din.

Maimakon ya fita kamar yanda yai niyyah sai ya fasa,duk da bai bayyana mamakin shi ba,but deep inside him yana mamakin ace qaramar yarinya irin wannan da haihuwa.

Amsar Fawad din Niiman tayi a hannun Ammyn,kana ta fara shirin juyawa domin komawa daki tabashi abincin shi.

“Zo dawo nan Niimah,kingama cin abincin ne zaki tafi?”

“Ah ah,dama so nake idan nagama bashi,sai inzo inqarasa cin abincin.”

Ta ida baiwa Ammyn amsa yayin da take jin idanuwan wasu daga cikin falon akan ta.

“No zauna kina ci kina bashi,ai babu mai hangoki daga can,ko kuma in kinga zaki takura ki tafi dakin,sai in sanya Ummita ta biyoki da abincin,don Allah kibar wasa da cikin ki Niimah kinji ko?”

“Toh Ammy in sha Allahu zanci,nagode bari in shiga cikin.”

“Toh shikenan jeki.”

Sai ta juya tana kwalowa Ummitah kira akan tazo ta bi Niiman da abincin ta.

Zaman Ammyn a falon yayi daidai da tambayar da Kabeer ya jefo mata,tambayar da bata da amsar ta,tambayar da kuma kwarai yakamata ace tayi wa Niiman tuntuni,kuma mma sai yanzu da Kabeer din yai tambayar taji ma ai ya cancanci taji labarin Niiman,ba don komi ba sai akan abinda ka iya zuwa ya juyo.

“Ammy ina fatan yarinyar nan bazawara ce?”

Ta sake nanata tambayar cikin sakannin da basu gaza goma ba.

Bilal ne ya dubi Kabeer din ya kwashe da daria,lokaci guda Usy da Saddiq ma suka dauka,ranar yau yakamata ta shiga cikin dimbin tarihin gidan nan,yau Kabeer ne ke buude baki yana tambayar marital status din wata?watan ma baquwa waccce basu da haqiqanin sanin ainihin wacece ita,lallai yau inama Daada na gurin nan.

“Are you for real?”

Bilal ya furta cike da mamaki.

“As in how?did i say something wrong?”

Shima ya tambayi Bilal din fuskar shi dauke da mamaki mabayyani.

“Kambuuu!”

Cewar Ussy yana mai sake gyara zaman shi,yayin da Saddiq inbanda murmushi yana girgiiza kai babu abinda yake,yau shikam ina zaikai wannan kayan dariyar?

“Wallahi bani da wannan masaniyar Kabeer,but nafi tunanin hakan,tunda babu namijin da zai bar matarshi da yyaro sabon haihuwa su riqa walagigi a titi,there must be something.”

Cewar Ammy tana mai sake jinjina al’amarin a ranta.

Miqewa yai tsaye hannuwan shi sanye a aljihun wandon shi,kana ya sake maida hankalin shi kan Ammy yace,

“Ammy ku tayani addu’ah ta kasance bazawara,because i don’t think i can be able to survive if she still happen to be someone’s wife.”

Yana gama maganar ba tare kuma da ya damu da kallon mamkin da dukkan ilahirin falon ke makamashi ba ya dibi tsayin shi yai gaba,mamakin shi bai gama sakin su ba ya sake harbo wata katob’arar.

“Ammy help me tell her,bata da miji sai ni din nan da take ji kuma take gani,tabar ganina ‘dan baqi,nafi kowa na duniyar nan iya soyayyah!”2

“Ahhhhh e don happun!”8

Muryar Bilal din ta karade palourn,yayin da su duka suka saki baki suka rakashi da idanu yuuuuuuuuu….

Ba wai mamakin maganganun shi suke ba,abu guda suke mamaki,abh guda ne,bakomi bane sai sanin da kowa yaiwa Kabeer a cikin gidan nan shine,qaramar yarinya kamar Ni’imah is the last thing da zai iya kallo,talk less of azo ga batun aure,bai taba soyayyah da wacce yagirma ba,sai wadanda suka girmeshi,inkinci saa ne ma ace shi din age mate dinki ne,saboda haka mafi yawancin yammatan shi manya ne irin shi ko kuma wadanda suka fishi,shi kuma haka yake,kuma kowa yyasan da hakan.

“Kai Bilal,bi mani Kabeer zuwa dakin shi kaga bai fara shaye shaye ba?”3

Cewar Ammy fuskar ta har yanzu dauke da mamaki.

Cikin dariya Saddiq yace,

“Ammy wallahi garas yake,ke kinsan drugs is the last thing Kabeer zai iya shaaa,kawai lets just assume Allah ne ya fara kamashi!”

“Lallai kam Allah ne zai kamashi,because i don’t want to imagine what type of chaos this could lead us to,Allah dai ya iya mana!”

Gaba dayan su suka ce amin! Zukatansu dauke da tunane tunane iri iri.

“Kabeer calm down,Kabeer calm down,Heyy you asshole calm the heck down”+

Wannan karon dakatawa yayi ya dafe gefen zuciyar shi,sai kuma ya koma ya jingina da bango sashen Hajian shi,yanajin zuciyar shi na wani irin bugu,gaban shi na wani irin fad’i,like what is all this?gaba d’aya lamarin ya susuta shi,har yanzu yakasa fahimtar wani irin nauyi ne wannan.

“Matar aure ce Kabeer,kana da hankali kuwa?”

Sashen zuciyar shi sake tuna mashi,al’amarin da ya sanya shi runtse idonshi yana fatan hakan ya zama qarya,meyasa yakejin tamkar ze iya mutuwa in be mallaketa ba?sake runtse idanuwan shi yayi yanajin wani irin nauyi da kunya na lullubeshi,this is unlike him!

“She might be someone’s wife!”

Ya sake tunawa,wannan karon zamewa yai qasa yana maida numfashi,lokaci guda ya bude maqoshi ya riqa ambaton sunayen Allah yana sambatu.

“Yaa Allah karka jarabceni da wannan baiwa taka,ya rabbi na roqeka kai mani wannan alfarmar,ya rabbi na tuba,na tuba ya Allah….”

Kamar an tsunguleshi ya miqe,haka kuma without any second thought ya koma baya ta sashen Ammyn,amma maimakon ya shiga sai ya miqa gaba inda zai iya sadaka da windown dakin baccin ta,in be manta ba yaji Ammyn na bata umarnin shiga dakin ta,sabida haka ba tare da wata tantama ba ya isa jikin windown ya tsaya,he just can’t wait for Ammy ta sama mashi confirmation, qila zai iya yin bindiga saboda fargaba.

A hankali ya zuge windown,lokaci guda yan mai hadawa da gyaran murya,kana babu wani emotion da zaka iya karantowa bisa fuskar shi,sosai yai matuqar saita kanshi kafin yayi abin kunya.

Zaune take kan carpet a gefen gado tana shayar da Fawad,da’alama ma hankalin ta gaba daya baya jikin ta,domin babu alamun taji motsin bude windown da yayi,ganin yanayin da take duk da ta dan juya baya ya sanya shi juya kanshi gefe guda kana ya sake sakin wata gyarar muryar da tafi ta dazu sautiii,aikuwa wannan karon taji,domin a dan firgice ta waigo zuwa saitin da tajiyo gyaran muryar.

Gabanta ne ya dan fadi bayan sun hada ido,kana cikin azama tai maza ta gyara zamanta gami da daga Fawad din daga qirjin ta,ba tasan meyasa mutumin ke mata kwarjini ba.

Ganin ya danyi mata quri da idanuwa ya sanyata fara waige waige,atunanin ta wani abu yake so,daqyar tai qarfin halin cewa

“Ina wuni,wani abu za’a kawo maka?”

Muryarta ta tai nasarar fargar dashi,hakan yasa shi hanzarin saisaita kanshi,gyaran muryar ya sake yi kafin ya yafito ta da hannu.

“Oyaa,come over here.”

Da sauri kamar wacce ke jira ta miqe gami da saba Fawad din a kafadarta ta nufi bakin windown tana mamakin kiran da wannan miskilin ke mata.

“Ke ina mijin ki yake?”

“Mijina kuma?”

Ta sake nanata tambayar itama cike da mamaki a fuskar ta.

Saida ya harareta kana yace

“Yes your husband,where is he?”

Ba ttare da wani tunani ba kuma bilhaqqi da gaskia tace,

“Ni bani da miji.”

Wannan karon ji yai wani abu daya tokare mashi maqoshi ya wuce zuquut,har da yarfe wani dan guntun gumi a gefen goshin shi,madallah da wannan Rahma ta ubangijin shi,madallah da tarin alkhairan sa da tausayin shi ga bayin sa,yau kam dolene ya kwana godewa tarin Ni’imomin ubangijin shi a gareshi.

STORY CONTINUES BELOW

Ba tare da yasake cewa komi ba ya saki labulen windown ya juya fuskar shi dauke da wani irin annuri,yanajin tamkar Allah ya yafe mashi dukkan zunubanshi,yau da yarinyar nan matar wani ce har yanzu da bayajin zai iya yafe wa kanshi abinda zai aikata.

“Errmm don Allah kaji nace ba….”

Ya tsinkayo muryarta bayan ya juya,da kamar ba zai juyo ba don ze iya yin abin kunya,amma sai yafasa ya haqura ya juyo din,juyowar tashi yayi daidai da had’a idanuwan su,a qasan zuciyarshi kuwa ya riqa jinjina hikimata ubangiji,domin yanzun ne ma ya wara idanuwa dakyau ya kalli ainihin yaya fuskar ta take.

“She is the true definition of beauty, she is freaking beautiful.”

“Don Allah dmaan tambayar ka zanyi.”

Ta furtta cike da yarinta,yayin da shi kuma ya riqa jin yarintar ta sabon abu a gareshi,domin har cikin qwaqwalwarshi tta shige lokacin da take tambayar tashi tana dan tapping bayan Fawad,ga kuma murmushi shimfide akan fuskar ta.

“Uhmmm go ahead.”

Yai qarfin halin furtawa.

“Dama i just want to tell you kana da kyau,and to ask if i can crush on you?because kana burgeni.”9

“Yesssss!” Ya furta daga qasan makoshin shi,wanda shi kadai daya furta shiyasan me yace,amma a bayyane sai ya hada rai ya dubeta sheqeqe yace mata

“Maza nawa kika taba furtawa hakan?”

Ai sai ta diririce ta rasa ma me zatace,ita har ga Allah babu wani wanda ta taba ce ma haka,hasalima ita bata taba ganin kyan wani namiji ba inbashi ba,infact ita maganar nan ma da take its from the bottom of her heart,bata dauka laifi tayi ba,hakan yyasa muryarta na dan rawa tace

“Kaine na farko,and im hoping you’d be the last,because ni a duk iya zamana a america da nigeria babu wanda ya taba burgeni har na fada mashi inba kai ba,ko na fadi wani abu ne da ba daidai ba?”

Sai da ya dage girar shi sama,qasan ranshi kuwa dadi ne fal cikin shi,bbayan yayi qasa da muryarshi yace.

“You mean har shi tsohon mijinki bai taba burgeki ba or what are you trying to tell me?”

“Naam?tsohon mijina ku….?”

Muryar Ammy ce tai nasarar katse ta.

“Ah ah Niiima ke dawaye kike surutu a jikin window?”

Da sauri Ni’iman ta danyi baya tana jin kunya na lullubeta,ko kafin tace wani abu goganku ya sake turo kai cikin windown.

“Ammy Kabeeru Blacky ne yazo tadi wajen Ni’imah er fara kyakkawa,nasan kema abun zai burgeki.”7

“Oh Allah,yanzu Kabeer dama ba tafiya kayi ba,inace i told you sai munyi magana da ita tukunna?”

“Ammy kiyi hakuri,ji nai wallahi zan iya mutuwa in ban san matsayina ba,ki gafarceni Ammy.”

Ya ida zancen yana langabar da wuya,lokaci guda kuma yana kashe wa Ni’iman ido,al’amarin da yasanyata yin sakato da baki da hanci tana kallon shi,gaskia ita kam taga crush,shi dai yaji dadi wannan,matarshi ta more.

Girgiza kai kurum Ammy tayi,sanin halin Kabeer din,ba tare da ta bari ya sake wata magana ba tace toh naji tafi saina nemeka.

“Angama Ammy,don Allah ki mani campaign dakyau,na lura diyar taki bahaguwa ce,sai ana dorata a layi.”

Daquwa Ammyn tai mashi tace

“Zaka wuce ko sai na zonan na sameka.”

Ta baya baya ya tafi yanayi wa Ni’iman bye bye,lokaci guda kuma yana jefo mata pecks,yana faman lallangabe kai,itakuma yanda kasan doluwa haka ta riqa miqa wuya tana kallon ikon Allah,gaba daya abun sai ya burgeta,ta riqa jin zuciyarta na mutuqar jin dadin abinda yakeyi din,can qasan ranta kuma ta dinga fadin dama akwai maza masu kirki haka?meyasa shi Yaa Mukhtar baida kirki haka?bai taba yi mata dariyar minti uku ba,kullum sai dai ya riqa tsareta da qananan idanuwan shi kamar baqin maye.1

STORY CONTINUES BELOW

Tsabar leqenshi har sake zura kai take ta window,yayin da itama ta dage ta riqa yi mashi bye bye,kai qarshe da taga yana shirin bacewa ganinta sai ta d’aga murya iya yanda zaiji tace,

“Kana burgeniiiiiiii wallahiiiii!”3

Dariyace ta kwace mashi,yayin da yariqa jin haushin kanshi tuntuni da qaddara bata hadashi da wannan cutieyn ba,she is freaking amazing!

“Kana burgeniii wallahiii.”

Caraf a kunnen Daaada ita da Yusra,daidai lokacin sunzo wucewa ta baya zasu shiga sashen Ammyn,hakan yasa Daadan dakatawa tana rarraba ido.

“Auta me nakeji a cikin gidan nan?ko en wasan diramar hausa ne suka shigo mana gida bani da labari?”

Yusran ce ta hango Kabeer din na billewa ta baya,hakan yasa ta ruga jikin windown dakin Mammyn da ta hango a bude,domin inba kunnenta kemata qarya ba,muryar da suka jiyo tayi mata kama da ta Ni’imah.

Ilai kuwa Ni’iman ce ke shirin sakin curtain,mamaki ne yacika ta,tofa,itakuma wannan haka take?tama rasa wanda zatace yana burgeta sai Yaa Kabeer?mutumin da kafirin son girmanshi ma bai barshi yayi soyayya da er qasa da shekarun shi ba sai wadanda suka girme mashi?lallai wannan er wahalace.

Ammy kuwa mamakine itama ya lullubeta,tun dagajin kalamen Niiman ta qara sakankancewa da yarintar ta,ta kuma tabbatar wa kanta da cewar bata da aure,amma duk da haka dole tana buqatar yi mata wasu tambayoyin,amma zata barta sai dan nan gaba kadan.

“In yagama burgekin toh kizo kibani Fawad din kafin ki jefashshi.”

Sai a lokacin ta tuna ma da ashe Ammyn na dakin,hakan yasa da sauri ta sunkuyar da kai tai hanzarin zuwa ta miqa wa Ammyn Fawaad din,qasan zuciyyarta kuma ta kasa tantance me takeji,abu guda tasani shine a duk lokacin da zata ga wannan dan baqin,ko zata tunano shi,ko zataji muryarshi,toh kuwa rabi da kwata na daga cikin damuwar ta yayewa suke,infact mantawa ma take da wasu obstacles da rayuwarta ke fuskan a yanzu.

Wannan kenan.

***

Wayewar garin be sauya komi na daga qunci da bqin cikin da ahalin gidan suka kwana suka wuni da shi ba,mussaman Mukhtar da bayajin akwai sauran digon wani abu mai suna farin ciki da yai wa rayuwar shi saura,a daren ya kwana yana raya daren,in zai iya tunawa ma bayajin yayi wa kanshi addua’ah,addu’arshi daya ce,addu’arshi ga Ni’imah ce da gudan jinin shi,yana fatan a duk inda suke su kasance a hannu nagari,bayajin zai yafewa kanshi in wani abu ya samesu.

Anan bisa dadduma barcin wahala ya kwashe shi,qarar wayarshi ta tashe shi da misalin qarfe tara da kwata na wayewar garin,wani cousin din su ne Habib.

“Habib how far?”

Ya furta bayan ya dauki wayar,daga dayan bangaren aka amsa da

“Kai babaa share,meke faruwane naga Mammy da sassafen tazo gidah,a taqaice dai gasunan zasu zo gidan ita da Daddy,and wani rumor nakeji wai aure zaa daura maka a yau din,is this some kind of joke?”

“Co ask Habib,co ask!”

Daga hakka bai kuma cewa komi ba ya latse wayar ya aje a gefe,ba tare kuma da ya raba jikin shi da jallabiyar da yake sanye da ita ba ya juya ya nufi bangaren Mammyn,bai damu da yai knocking ba,kai tsaye ya shige cikin bedroom din,kamar yanda yai tsammani kwance yya sameta duqunqune cikin blanket tana kwasar bacci hankalin ta kwance,takaici ya sake kamashi,har yanzu yakasa gane dalilin da yasa har yabar Fadwa take numfashi a cikin gidan su,ko da yakke ba laifin ta bane.

“Keh,keh,keh get up!”

Ya daka mata tsawarda ta sanyata zabura gami da yin qarshen gadon da sauri tana mutssike idanu,kallon shi take fuskarta dauke da mamaki,yayin da a tun kallon farko da tai mashi taji en hanjin cikin ta sun juya,bata jin ta taba ganin shi a yanayi irin wannan.

STORY CONTINUES BELOW

“Tell me,tell me for the last time Fadwa,me kike so dani neh?”

Ya tsura mata idanun shi masu kama da na mmai jin bacci tsabar qaanqantar su,idanuwan kuma da suka fi komai sanya Fadwan cikin shauqin son shi.

Rauusayr da kai tayi gefe tana narai narai da idanuwa.

“Mukhtar i believe by now kafi kowa sanin cewa inayi maka son da ko Mammy ba tayi maka rabi rabin shi,i can do anything to have you,even if that means zubewar duk wata qima ko mutuncina ne!”

“Shame on you!Shame on you Fadwah,you know what?”

Ya tsareta da idanuwanta,ita kuma babu alamun risinawa a tattare da ita ta gurgiza kai gami da cewa “sai ka fada!”

“I hate you,daidai da second daya bantaba jin kin burgeni ba,hasalima you are the last person i can share my bed with,in fact you r disgusting!”

Dama beyi tsammanin jin haushi daga gareta ba,saboda shegiyar zuciyar tata ta wurga wa kare ya lamushe,hasalima murmushi ta riqa yi tana jinjina kai,alamun insults din nashi suna kai mata yanda take so.

“Bana buqatar ka soni Mukhtar,ko na taba ce maka ka soni?abu daya na nema ko a wancen lokacin,just marry me,idan ka aureni a lokacin zamu tantance waye mai qarya tsakanin ni da kai.”

Ranshi ne ya sake baci,gaba daya yarinyar nan er rainin wayau ce,shiasa ba tare da wani second thought ba ya nuna mata qasa alamun ta sakko daga gadon,babu musu kuwa ta yaye bargon jikin ta ta taho,tsabar yanda idanun shi suka rufe da tsanarta bai sanya ya lura da bingilar rigar baccin dake manne da jikin ta ba,haka nan kuma kafin ya ankare sai jinta yai a jikin shi tana mai sakin kuka da qarfinta.

Baisan da shigowar Mammyn ba,sai da sukai ido hud da Mammyn lokacin da yake qoqarin hankade Fadwan daga cikin shi a sannan ne ya fahimci tuggun da Fadwan ta qulla mashi,take yanke kuma ya san babu mai fiddashi cikin wannan halin sai Allah.

“Da kyau Mukhy,da kyau,iskancin naka ya girmama har cikin makwancina,ni Mukhtar?ni?”

Kalamen Mammyn suka jefeshi tamkar saukar guduma,a yanzu kam bbashi da wata mafita,hakan yasa ya dafe kanshi yana jin sabuwar tsanar Fadwan na ninkuwa cikin ranshi,ita kuma dama tuni ta boye bayan Mammy tana rera kuka munafinci.

“Yi shiru Fadwa,yi shiru kinji ko?wuce ki sanya hijabin can kije kiyi wanka,da yyardar Allah yau komi zaizo qarshe.”

Babu musu ta zari hijabin ta sanya kana ta fada makewayin dakin zuciyarta fal dadi,ko banza wannan dan qaramin action din nata zai taka muhimmiyar rawaa wajen assasa wutar aura mata Mukhtar din,kira take habawa Malam inkasan wata ai bakasan wata ba.

“Baqin munafuki,a haka kake ikirarin baka son er mutane,amma ka iya lallabowa kabiyo yarinya har makwancin ta,wai nikam Mukhy yaushe kazama mutumin banza ne ne?”

“Mammy please stop all this,ban aikata abinda kike tunanin ina aikatawa ba,saboda Allah u riqa yi mani kyakkyawan zato mana.”

“Kai ni da Allah gafara can…..”

Ta katseshi kamar tana shirin rufeshi da bugu.

“Baka da sauran wata kalma da zaka yaudare ni da ita,ai ni Mukhtar sai dai kuma kabi wani sarkin,amma nikam ai kashani na warke,aure kuma a yau yau dinnan sai an daura shi,wannan karon bazan lamunci iskanci da iya shege ba,kaji nagaya maka.”

Wannan karon kasa ce mata komi yayi,sai dai bacin ranshi bayyananne,can qasan ranshi kuwa qara godewa Allah yake da wannan jarabawar dake bibiyarshi cikin dan qanqanin lokaci.

“Mammy shin yin auren nan shine farin cikin ki?”

Tambayarshi ta jefeta cikin muryar da bata sanshi da itaba,sosai yaso yabata tausayi mussaman yanda taga gaba dayan shi a yamutse yake,amma dake zuciyarta ta qeqeshe,burinta kawai ta cimma burinta yyasa bata bari tausayin nashi yayi tasiri a kanta ba tace…

“Idan ka yarda ka amince ka fanshe duk waani laifi da kai mani Mukhy,da gudu zan yafe maka.”

Cikin murmushin qarfin hali yace,

“Mammy na yarda na amince zan auri Fadwah idan har yin hakanne farin cikin ki.”

“Masha Allah ko kaifa Mukhy,don Allah kar inji kar in sake gani an kamanta abinda yafaru a baya ba kaji ko?in bbanda abinka mai mata irin Fadwah har mi zai kalla a jikin wata sakarya can wai Ni’imah?haba ka riqa reasoning mana.”

“Hakane Mammy,Allah yashige maa gaba.”

Tana washe baki ta amsa da amin amin,lokaci guda ta riqa sanya mashi albarka,tsabar jin dadi ma har qara jaddada mashi irin son da Fadwan take mashi ta riqa yi,shikam jinta kawai yake yana gyada kai tare da murmushin yaqe,bba shakka da tana da masaniya akan abinda ya qudira a ranshi da bata bata bakinta gurin wadannan zantuttukan ba.

“Muje maza ka je ka shirya,domin ga kawunku can Uncle Yusuf na tattago shi tare da babban limamin unguwar su,gara a daura auren nan a wuce gurin.”

“Amma Mammy Fadwa bata da waliyyii,waye zaizama waliyyin ta.”

Dariya Mammyn tayi kana tace,

“Sha kurumin ka,nayiwa baba maigadi magana shi zai zama waliyyin ta.”

A lokacin kuma daidai da fitowar Fadwan daga bathroom,baba maigadi daidai aa kunnen ta,butar shayin can,a rasa wanda zai zama waliyyin ta sai megadi?kambbbuuu

“Mammy bangane maigadi ba?maigadi ne zai zama waliyyi na duk fadin garin kaduna?haba Mammy gaskia da sake!”

Murmushi Mammyn tayi lokaci guda kuma tana qoqarin maida komi ba komi bane a kalamen na Fadwa.

“In banda abinki Fadwa,ke dai ba a daura aure ba,meyashefi da koma waye zai wakilci auren naki ba?maza kije ki shirya gaf kike da zama amaryar Mukhtar Gaya.”

“Hakane fa kuma Mmmy!”

Ta amshe yayin da take kwantar da kanta bisa kafadar Mammyn tana daria qasa qasa,lokaci guda kuma tana jifan Mukhyn da kallon ka kusa zuwa hannu.

Toilet ta shige bayan tagama noqe noqen abun kunyan da take tunanin ta aikata,duk da dai Ammyn bata ce mata komi ba bayan dariya da tayi ta amshi Fawad din daga hannun ta.+

“Idan kingama noqe noqen kya fito hakanan ko Ni’imah,ko kuwa wata sabuwar naqudar kikeyi a bandakin?”

Ta tsinkayo muryar Ammyn na tsokanar ta,ita har ga Allah bata dauka tayi wani abu ba,abu guda tasani ita kam abinda ke ranta ta furta,ko shiyasa mutane da dama ke cewa she is too straight forward, eh gaskia kam bata daga cikin mutane masu qumbiya qumbiya,daurewa dai tayi ta fito din tunda tasan kwarai ta dauki dan dogon lokaci cikin bandakin.

“Ammy kiyi hakuri don Allah.”

Ta furta cike da kunya,sabida gani take lallai abinda ta furta din kammar abun kunya ne,mussaman yanda taga Ammyn na murmushi lokaci guda tana girgiza kai.

Maida wardrobe din da ta sanya kayan Fawad din tayi ta rufe,bayan ta rufene ta samu bakin gado ta zauna,kana ta umarci Niiman da ta zo ta zauna kusa da ita.

Riqo hannuwan Niiman tayi gaba daya,lokaci guda tana sauke idanuwan ta akan fuskar Niiman dake sunkuye tana dan murmushi a hankali.

“Ni’imah dube ni nan.”

Ammyn ta furta bayan ta sake sanya wa fuskarta seriousness a karo na farko tun bayyanuwar Ni’iman a gidan.

“Da farko kafin ince maki komi Niimah inaso ki fahimci wani abu guda d’aya zuwa biyu,na farko dai nasan ke baquwa ce a cikin gidan nan namu,baquwar da baki da masaniya cikin ko wane irin zama muke gudanarwa a tamu duniyar,wanda hakikanin gaskia mu kanmu bamu da masaniya akan wace iriyar rayuwa kika gudanar a baya ba,sai dai inason ki san wani abu guda,mussaman da na lura da cewar ke din yarinya ce sosai,shi komi na duniar nan da kika gani dan abi a sannu ne,if im not mistaken nasan a qarancin shekaru irin naki kin fuskanci kadan daga cikin qalubale da rayuwa kan iya miqa mutum,misali a yanzu kinga ke din uwa ce,kinga kenan akwai wasu responsibilities sosai da yanzu suka hau kanki a matsayinki na uwa,bansan mi ya rabaki da mijinki ba,amma dai nasan ko menene abu ne mai tarin girma…..”

Dakatawa tayi da magana ganin Ni’iman na kuka,sai dai tunanin ta abu guda ne ka iya sanyata kukan a yanzutuno da gida,rayuwarta ta baya da kuma may be dalilin daya rabota da dangin ta da gidan su take.

“Kiyi hakuri Niimah,nasan me ke sanyaki kuka,inayi maki zantuttukan nan ne domin isar maki da wani saqon da nake ganin yakamata in isar,duk kuwa da cewar ban ji labarinki ba tukunna!”

“Ammy kiyi hakuri duk laifi na ne!”

Niiman ta fada cikin sheshsheqar kuka,ta cigaba da cewa….

“Ammy kunyi mani halaccin da ba zan manta ba a rayuwata,kwarai koda yau nabarku zan dawwama ina godewa karamcin ku,and i know ya kyautatu a gareni in sanar dake labarina,sai dai ina matuqar tsoron yin hakan,qila hakan nada nasaba da tashin hankalin dake rataye da labarin nawa ne.”

Zuwa yanzu kukan nata ya qaru,tanajin tamkar ba zaa yarda da ita ba,labarin rayuwarta labari mai tsaurin gaske,fahimtar shi kai tsaye al’amarine da ka iya daukar dogon zango,amma duk da haka tanajin Ammy ta cancanci sanin ko wanne bigire na daga tarihin ta,kwarai ta cancanci sanin wacece ita,daga ina ta fito,kuma mi ya fito da ita.

“Ammy da farko dai ni bantaba aure ba,hasalima ni bantaba saurayi ba a rayuwata!”

Yanayin da ta gani a fuskar Ammyn bai bata mamaki ba,ai tanajin duk wani wanda zaiji batu irin nata ya halasta ya nuna tsagwaron mamaki ko kuma kokwanto,wataqilama in ba ai sa’a ba mai sauraren labarin na iya b’igewa da nuna bayyanannen tashin hankali,duk babu laifi ga mutumin da yasan ko ita din wacece.

STORY CONTINUES BELOW

“Inayi maki kyakkyawan zato Ni’imah,haka zalika zancigaba da binki da wannan zaton har zuwa lokacin da zanji karshen labarinki,menene ya sanyaki yin shiru?ko kina tunanin zan tuhumeki ne biisa abinda bansani ba?zan tuhumeki ne kadai idan naji labarin da ba shikenan ba,mussaman in baki boye mani komi ba,kuma ya kasance ke din kece ke da llaifi akan zancen da bana fatan kkasancewar abinda nake tunani…..”

Ta numfasa kana ta cigaba….

“Ke nake saurare Ni’imah,garin yaya baki da aure amma kika haihu?har ga ma dan naki kwance a gefena?tell me what i don’t know please.”

Sauke ajiyar zuciya Ni’iman tayi,lokaci guda tana sanye tafin hannayenta tana dauke hawayen dake faman zarya daga kuncin ta,a yau ta shirya fada ma wani yanda qaddarar rayuwar ta ta fara!

“Kamar yanda na fadi maki ne Ammy…”

***

Sunanah Ni’imah Sulaiman Gaya,sai dai ina amfani da Ni’imah Dambatta sakamakon riqon mahaifina da akayi a garin na dambatta,hakan yasa mahaifina yake amfani da Dambatta a cikin jerin sunan shi.

Malam Junaidu Gaya shine kakana,kuma mahaifin Abbana da yayyenshi guda bita Alh Qassim da Gwaggo Bilkisu,tun a wancen zamanin kakana mutum ne mai rufin asiri,a duk fadin garin namu yana daya daga cikin dattijai masu rufin asiri,kuma yana daga cikin qalilan dattijan da suka san darajar karatun boko,hakan yasa duka yaranshi guda uku ya jajirce shi da maidakin shi don ganin sunyi karatun boko da na muhammadiya.

Mahaifina shine auta,hakan yasa duk wani son duniar nan iyayensu sun daura shi akanshi,mussamman Innah,watau mahaifiyar su,Alh Qassim shine babba,kana sai ita Gwaggo Bilkisu,sannan mahaifina,bayan gama karatun sakandire da Qassim yayi sai Malam Junaidu ya aika dashi garin kano wajen wani aminin shi domin ya samu gurbin shiga jami’ah,a lokkacin itakuma gwaggo bilkisu tana aji biyu a sakandire,kasancewar akwai tazara sosai a tsakanin haihuwar da Inna keyi ya sanya doguwar tazarar shekaru tsakanin yaran su,tunda a lokacin shi kuma mahaifina aji uku yake a primary.

Ana tsaka da haka ne watarana Inna ta tashi da ciwon ciki,ciwon cikin da ba dauki dogon zango tanayi ba yakaita ga kushewarta,kwarai dagaske Malam Junaidu ya girgiza da mutuwar matarshi,girgizawar da sai da tayi nasarar tafiyar da duk sauran farin cikin shi,haka kuma har yakoma ga mahallicin shi bai sake yin aure ba,ganin cewa ita kanta Bilkisun a wannan lokacin batai wayon da zata kula da kanta ballantana ta kula da qanin ta ba ya sanya qanwar Inna dake aure a dambatta ta nemi alfarmar riqe su ita da mahaifina,Malam junaidu ya hakura ne sanin wacece Baba Hajaran da kuma maigidanta,shekarun su sama da sha biyar Allah bai basu haihuwa ba,hakan yasa dole ya hakura aka tafi da Gwaggo bilkisu da kuma mahaifina garin na dambatta,nan suka cigaba da rayuwa a hannun Baba Hajara da maigidanta Malam Salihu cikin aminci da amana,sai dai a kodayaushe sukan shirya in sun samu hutu suje suga mahaifin su,ko kuma idan Yayansu Qasimu yazo Gayan sai ya dauko mahaifin nasu yakawoshi su gana,wanda zuwa yanzu Qasimun gaf yake da qare karatun shi na jami’ah a fannin Electro petro chemical engineering.

Bayan wasu shekaru masu dan tsayi al’amura da dama sun sauya,kama daga girma da wasu canje canje da rayuuwa kan miqowa dan adam,hakance ta kasance da mahaifina,domin a yanzu yana da kimanin shekaru ashirin da takwas a dunia,zuwa wannan lokacin ya dade da baro garin Dambatta yai qaura zuwa kano wajen yayanshi Qassimu,wanda yanzu yake aiki da matatar man fetur ta qasa,alhamdulillahi kuma arziqi yafara zama,ba arziqi na dukia ba harda arziqi na iyali,domin har matarshi da ya aura diyar abokin Malam Junaidu da Qasimun ya zauna a wajen shi ta haifa mashi yara biyu,sunan ta Ummu Khultum,su din en asalin dakata ne dake jihar ta kano,amma mazauna kano ne tun tale tale,auren soyayyah sukayi ita da Qasimu,domin kuwa ko a lokacin bawai ta isa aure bane a idanunsu aka aura wa qasimun ita,sai dai soyayyar da suka fuskanci tana tsakaninta da Qasimun mai tsanani ce,hakan yasa tana gama sakandire aka aura masu juna,bayan iyayensu sun gamsu da hadakar zumuntar a tsakanin su.

STORY CONTINUES BELOW

Mahaifina matuqin jirgin sama ne,domin sosai malam junaidu da yayanshi qassimu suka tsayamashi har yasamu shaidar shiga collage of aviation dake birnin na zariya,dake mutum ne mai qoqari sosai ya maida hankali yayi karatun shi cikin nutsuwa da kamala,kasancewar shi mutum maras hayaniya da kuma bala’in qoqari ya sanya tashi tai matuqar zuwa daya da wani lecturern su,wanda shine yataimaka mashi bayan yagama bautar qasar shi yai masshi hanyar samun aiki a Alaska Airlines dake birnin america Washington DC.

Zuwa yanzu kudi sosai sun fara zamawa mahaifina,abinda yai mashi saura iyali,iyalin da har Malam yagaji da mitar ya fidda mata yai aure,baa maganar Alh Qassim da yai mashi rantsuwa zuwa shekara mai zagayo in bai fidda mata ba shi zai nema mashi da kanshi.

Ana hakane watarana aka kawo sabuwar air hostess(flight attendant) nan company na Alaska airlines and group din,Mutuniyar Niamey ce dake jamhuniyar Nijar,Khadeejatu Hameedu sunanta,a lokacin matashiyace mai kimanin shekaru ashirin da shidda,tserayarta da mahaifina yazamana baifi shekaru hudu ba,domin shi a lokacin ya tasamma shekaru talatin a dunia,a farkon ganinshi da ita soyayyah mai zafi kuma mai tsafta ta wanzu tskaanin su,basu dauki dogon lokaci ba suka gabatar wa iyayen su da nufin su,sai dai ba nan gizo ke saqar ba,iyayen Khadeejatu sunyi rantsuwar ba zata auri bahaushe ba dan najeria,kasancewar banbanci qasa da kuma yare dake tsakanin su.

Hankula sun tashi kwarai dagaske,mussaman daga bangaren masoyan,a inda a lokacin soyayya ta riga da ta rufe masu ido ruf ya sa basa ji kuma basa gani,a haka ne Khadeeja ta daka tsalle takoma gefe tace sai dai a kasheta amma ita kam babu ita babu rayuwa in baa barta ta auri Sulaimanu ba,qarshe dai gudowa tayi aka daura aurensu da Sulaiman ba tare da sanin iyayenta ba,Khaltume wacce ake kira da Aunty Mammy kuma matar Alh Qassimu uta tazame wa Khadeejatu uwa,er uwa kuma aminiyah sakamakon korar karen da iyayen khadeejatun sukayi mata bayan ta koma masu da zancen auren ta da masoyinta Sulaiman,suka kuma yi rantsuwa babu su babu ita har dunia ta nade.

Wannan shine babban dalilin da yasa bansan dangin mahaifiyata ba ko da kuwa mutum daya ne,abu guda nasani ita din mutumniyar niamey ce dake Nijer,daga haka bani da masaniyar kowa na daga dangin ta.

Wannan kenan.

***

Ammy tunda na girma na budi ido a garin america,a america aka haifeni,anan na budi idanu nake ganina,domin daga baya iyayena gaba daya zama maidosu yayi birnin na america,lokkaci lokaci ma Uncle dina,uncle Qassim sukkanzo hutu american,anan ne na saba da cousins dina yaran Uncle Qassim din da matarshi Mammy,duk da bawani dadewa sukeyi ba amma nasan cewar en uwana ne kuma akwai wannan er shaquwar tsakaninmu,mutum daya ne ma zance jininmu bai wani hadu ba a lokkacin Yaa Mukhtar babu duka babu zagi tsakanin mu,sai dai babu wani good vibes a tskanin mu,Fareeda itace age mate dita,sabida haka a kodayaushe da ita nake maraba in sunzo,duk kuwa da qarancin shekarunmu a lokacin.

Ba zan manta ba akwai wani zuwa da sukayi american hutu,lokacin ba zan wuce 12 years ba,tun bayan da nasamu labarin zuwansu wajen Ammyta na hau zakwadin son zuwa gidansu da suke sauka,dama qaida ne da sunzo tofa can zankoma da zama har su koma,makaranta ma daga can gidan ake kaini a maidoni,zakui mamakin yanda nake son zuwa gidan duk kuwa da halin ko in kula da nake fuskanta wajen Yaa Mukhtar,a lokacin ba zai wuce shekaru goma sha tara ba,amma dake yana da tsayi sosai da garin jiki yasanya nake mashi kallon wani babba,mussaman yanda yakejin shi shikadai ne namiji a duk ilahirin gidan yasa yake jin kanshi kamar me,duk da cewa shine na hudu a bayan su Adda Bilkisu da Aunty Sakeena da Aunty Bena bai sanyashi rusunawa ba,shegiar zuciyar shi da kowa yasanshi da ita yasa ake lallabshi ake yin abinda yakeso a gidan,bai cika kirki ba mussamman in bai sonka,haka kuma qiri qiri yake nuna maka tsana matuqar baka cikin category din mutanen dake burgeshi.

Toh zan iya cewa nima bani da sa’a ta wannan fannin domin kuwa na fado cikin category din mutanen da baya viben da su,duk da qanqantar shekaru na na fahimci kallon banzan da yake jifana da shi a duk lokacin da zan gifta ta gaban shi.

STORY CONTINUES BELOW

Yau ma kamar kullum bayan wayewar gari idan antashi kowa zai shirya a fito dakin cin abinci na cikin gidan,a qa’ida kuma baa cin a binci har sai kowa ya hallara,yau kuma unfortunately sai natashi da wani irin azababben ciwon mara,dama ni da Fareeda ne a dakinmu,toh kawai saita bani paracetamol nasha na kwanta bayan nayi wanka,itakuma ta fito zuwa dinning arean domin cin abinci tunda ni nace bani iya zuwa.

Toh mistake dinta daya data isa bata fadi condition din danake ciki ba,tana can tana danna wayan Aunty Bena tana game,daddy sai ya umarci Yaa Mukhyn da yazo yakirani tunda ni kadai ake jira,gogan naku dama a qule yake yagaji da jira,asalima shine first din zuwa teburin cin abincin sakamakon tashi da yayi da wata kafirar yunwa,duk kuwa da coffee din da ya kwankwada bayan yayi sallah,toh ga kuma takaici an aikoshi kirana duk sun taru sun mishi yawa,shiyasa ya fado dakin ba tare da ma yadamu da yai sallama ko knocking ba,hasalima da ya shigo yasameni baccin wahala ya sureni sai yai tunanin iskanci ne ma ya hanani fitowa,ashema bacci nake.

Kafin insani sai ji nayi yadage iya qargin shi ya d’aka mani tafi aa cinyoyina danai rubda ciki ina baccin wahala,a firgice natashi ina zare ido,lokaci guda zafi da kuma mamakin wanda zaimani irin wannan bugun nake,don zan iya rantsewa ko dungurina baa taba ba tunda uwar da ta kawo ni dunia,hada idanunmu yayi daidai da sakkowar wasu hawaye masu zafi daga idanuna,lokaci guda nagama yanke wa zuciyata wannan din maqiyina ne ba d’an uwa ba,saboda dai ni har yau narasa me na tsare mashi ya tsaneni haka.

“Very useless girl,don qaniyanki sabida kin raina mutane zaki zonan ki saki teba kina bacci,while kinsan anacan ana jiranki ko?will you get the hell down ko sai nazo nan na kakkaryaki a banza a wofi?”

Bansan ya akai ba,nadai tsinci harshena na maida mashi magana a karo na farko,duk kiwa da tsoronshin da nake.

“Wallahi nikam bbanyafe maka ba,ta yaya zakazo kawai ka hau buguna don kawai ka tsaneni?”

Rufe bakina yayi daidai da hayo gadon da yayi gaba daya,kafin ingama sanin menen sai ji nayi yasa hannunshi guda ya mangareni na kifa,ban gama saituwa ba ya damqi kunne na da mugun qarfi,al’amarin dayasani tsanyara wata iriyar qara na hau bashi hakuri,domin dai bantaba ji ko ganin azaba irin wannan din ba aa kafatanin tsayin da nayi a ban qasa.

Sai da yagadama bayan yagama rarranqwashina kana ya sakeni yana mazurai,ba tare kuma da yadamu da kukan da nake ba ya iza qeyata mukai waje,ganin yanda yatasoni ina kuka ya sanya Daddy miqewa tsaye yana tambayar baasi,ba tare da ya bari na bude baki ba yai caraf ya amshe yana ba Daddyn amsa.

“Daddy wai kanta ke ciyo,shine ta ishi mutane da burarin banza.”

Ya lailayo qarya sakamakon tunawa da yai na cewar yaga sachet na pcm da robar ruwa kan bedside din su.

“Ayyah sorry my daughter,zauna mugama cin abinci sai Mukhtar yai dropping dinki a clinic.”

Cewar Daddy yayin da Fareeda ke qoqarin ja mani kujera.

“Eh wallahi Daddy,dama harda ciwon ciki takeyi,mantawa nayi danazo infada maku.”

Hararta AuntyBena tayi kana tace,

“Inafa dama zaki tuna tunda kinsamu abin yi,kar inkuma ganin hannunki a kan wayata wallahi,if not zan mugun saba maki.”

Mammy ce ta cab’e.

“Kinga karki takurawa auta ta,inkuka ban haushi sai inbata wayar itama a dena mata gori,ki kiyayeni Bena.”

Tana shirin bude baki tai magana,Mukhtar din ya katseta a hasale.

“Haba don Allah,wai sai yunwa tagama cinye mutum sannan za ai serving dinmu,for goodness sake tun dazu nake hakuri ina jurewa amma kamar bama a san me nake ciki ba,toh gaskia ni im starving, ha’aaan mana….”

Ya ida maganar yana huhhura hanci,al’amarin da ya sanya Aunty Benan yin shiru tana harararshi,ta san yanzu inta sake ta sake cewa tak toh ta shiganga a hannun Daddy,domin kwarai ba so na wasa yakeyi wa Mukhtar din ba,qila haka nada nasaba da kasancewarshi shi kadai ne da namiji da Allah yabasu ne oho.

Adda Bilkisu ita tai serving kowa akai bismillah muka fara cin abincin,wanda ni azabobi biyu ne suka hadu sukai mani rubdugu,na daya ga dai azabar ciwon mara da nakejin tamkar zan shide,na biyu kuma ga kaina da yau dau ciwo sabida kwandunan ranqwashin da wancan azzalumin ya zuzzuba mani,hakan yasa ko abincin nakasa kaiwa bakina,bansaniba ashe yana nan yana sanya mani na mujia.

“Keh nunar rana,meke damunki?”

Dama sunan da yake kirana dashi kenan inyagadama,duk da cewa ma akwai wasu sunayen banzan ma na daban da yakan laqaba man da zarar yana tsaka da jin haushi.

“Cikina ke ciwo,kumaaa….kum….”

Harshena ya sarqe sabida wata murdawa da cikina yayi,a daidai lokacin kuma najk wani danshi na biyo mani qafafu mai dan yawa,ai saina wage baki na hau rusa ihu,dama tuni nayi qasa ina birgima ina kiran sunan Ammy da Abbuna,hankulan kowa yatashi sukayo kaina,a tunanin su wani gagarumin abune ya sameni,sai da Mammy ta hangi stain a jikin farin skirt din dake jikina ne ta fahimci me kenan,ashe period ne na fara,shine ya jaza manj duk wadannan masifun danakejin tamkar dunia ta juya man baya ne saboda azaba.

“Ke dai kincika rakj,dubi duk ya da kika birkita mu gaba daya,ke Bilkisu kamata kuje daki ki kimtsata sai ku fito kuje Mukhy ya kaiku clinic subata magani,ke kuma irin naki period din kenan mai sanya pain.”

Duk da inacikin azaba bai sanya ni jin wata iriyar kunya ba,yanzu dama period nafara shine nake fuskantar wadannan azabobin?amma Mammy babu wanj sakayawa sai rattafo zance take gaban Daddy da Mukhy?gabana ne ya fadi rass bayan da na tuno da zancen Ammyna da take yawan yi mani akan cewar innafara jinin al’ada.

“Shiyasa nake son ki aje wannan at the back of your mind kinji ko babyna?daga ranar da kika fara period,ko dan yatsanki namiji ya taba shikenan ciki zakiyi,kuma dai kinsan hukuncin wanda yai ciki?ba abu bane mai kyau ba,toh ki kiyaye babu ruwanki da wasu maza,ko su waye kuwa,kina jina?”1

In ban manta ba alokacin cikin mamaki na sake daga kaina dake kan cinyar Ammyn tawa nace…

“Ammy na wai cikin haihuwa kike nufi?ciki yai qatoto a haifo mutum jariri?”

“Eh shifa nake nufi,amma idan kika kiyaye babu abinda zai sameki.”

Tunani na ne ya katse lokacin da Daddy ke cewa Mukhtar yakamani akaini daki domin kintsawa,bangama tunani ba najiyo tsakin shi a hankali,kuma lokaci daya da kai hannun shi da yayi gaba daya ya sunkuce ni yana gunguni ya nufi hanyar daki dani.

Ji nayi duk wata hanya dake sadar da jini ta jikina sun tsaya,kalamen Ammyna kawai ke mani yawo qwaqwalwa,shikenan ni yau tawa ta qare,shikenan nayi cikin shege,tunda ba ma yatsana kadai mukhtar yataba,gana dayana ya sunguma,ai kuwa tuni na barke da kukan tashin hankali da danasanin zuwana gidan nasu ma gaba daya.

Kira nake,nashiga uku naaa Ammyy shikenan Yaaa Mukhtar yayi mani ciki,wallahi babu ruwana,ni bansan zai tabani ba,wayyoo nabanu na lalace…..”1

***

About AIS

Check Also

HOD’IJAM CHAPTER 7 KARSHE BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 7 KARSHE BY NOORIEEYAH                 Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *