HOD’IJAM CHAPTER 4 BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 4 BY NOORIEEYAH

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da tunanin maganganun Mammy tayi bacci,har zuwa lokacin da baccin yai nasarar kwasheta kuwa ta kasa dena mamaki da jinjina girman labarin na Mammy,sai kuma k’wak’walwarta ta riqa kokarin tai comparing tsakanin maganganun da sukai ita da Ra’is,shine me hakan ke nufi?Mukhtar yasan da labarin Niimah amma still he went ahead wajen aikata abinda ya aikata din?Me hakan ke nufi?har bacci yatafi da ita bata samu nasarar samo amsoshin ta ba.5

Wayar Najma ta tasheta,kallon time tayi don ta tabbatar da lokaci,tun zuwanta gidansu Mukhtar dib sau d’aya sukai waya da Najman,ba wai kuma don Najman bata kiranta ba,ah ah ita dince dai bata son yin wayar da Najman,ba don komi ba sai don isarta da Najman keyi kan karatu,taga dai karatun nan dai ko ba dade ko ba jima zata gama ne,na menene zaa bi a isheta.

“Hello Najma,lafiya da farar asuban nan?”

Tsaki Najman tayi daga d’ayan bangaren,inda sabo yaci ace ta saba da wannan halin na Fadwan.

“Hey don Allah hang it there, ke fa ba mutunci kika cika ba,amma ba laifin ki bane,laifi nane da har nadamu nake kiranki.”

Lallai tasan ta kai Najman baango tunda har take bata amsa cikin jin haushi,hakan yasa ta sassauto da muryarta ta shiga bata hakuri.

“Yi hakuri mutumniyas,dama dai mamakin ganin wayarki da asubahin nan ne yasanya ni tankawa,it is not that deep naaa.”

“Keh ni rabani,naga alamun dadin ganin masoyi yana sanyaki manta time difference da muke dashi tsakanin america da nigeria da kike nema ki manna man hauka.”

Dariya Fadwan ta hau yi,ita wallahi shaf ta manta da wani banbancin lokaci,gaba d’ayanta rasa control dinta take akan duk abinda zai shafi Mukhtar ne.

Bayan sungama gaisawa ne Najman ta fara mata magana kan dalilin kiran nata.

“Wai halan kin manta date din yau ne?”

“Innalillahi,wallahi Allah na manta Naj,ya akai baki tuna man ba don Allah?”

Ta mike zaune hankalin ta a tashe,kwata kwata ta manta da ziyarar da babban yayansu kuma mariqinta a wani fannin ke kawo mata a duk qarshen shekara sanadiyar medical check up da yake zuwa american,hakan yasa yake using opportunity din wajen zuwa domin tabbatar da yanda take tafiyar da rayuwarta a k’asar,both academically da kuma personal life din ta off campus.

Tsaki Najman tayi,lokaci yayi da zata tunasar da Fadwan abinda take shirin aikatawa,duk da tasan cewa opposing issue din tamkar yankar tikitin batawa da Fadwan ne,but she doesn’t care,gaskiar nan da bata so uta din zata cigaba da fada mata.

“Ta yaya kike expecting na tunasar dake abinda ke din yashafa,kuma ma that aside,banyi tsammanin kin damu da duk wani abu da ka iya faruwa ba,mussaman ya da kike shirin yin aure ba tare da sanin iyayenki ba.”

Ta numfasa,kana tacigaba,mussaman yanda ta lura Fadwan ta maido dukkan hankalin ta kanta,duk da bata da masaniyar cewa ko maganganun nata zasui wani tasiri akan ta,amma duk da haka tacigaba da cewa,

“Fadwa,bance karki auri Mukhtar ba tunda kinsamu damar yin hakan,bt still kafin ki aikata abinda kike shirin aikatawar yakamata iyayenki su san me kike ciki,su san me ke shirin faruwa,haqqin su,haqqin su ne Fadwa,kada so ya rufe maki idanuwa ki aikata abinda zaki zo daga baya kina nadamar shi,ba baki nake maki ba,illah qoqarin tunasar dake abinda nake ganin kamar kin manta,a matsayina na qawa kuma aminiyar ki,and u hope,i really hope maganganuna basui nasarar bata maki ba,coz nasan halinki qanqanin abu ke nasarar bata maki rai.”

Shiru ne yabiyo bayan maganganun Najman,bayan kamar wasu tsirarun mintuna sai Fadwan ta tanka,duk da Najman bata expecting nadama take yanke daga Fadwan,still batai expecting jin abinda Fadwan tace ba,hakan yasa ba tare da ta sake furta wata kalma ba ta katse wayar,kasan ranta tana sake sanya alamar tanbaya akan sabbin halayen da Fadwa ta ara ta yafawa kanta.

STORY CONTINUES BELOW

“Najma,wallahi billahi ba zan taba wasa da wannan damar da Allah yabani ba,me kike expecting?i should give up my dream?my love life?just sabooda iyayena?iyayen da im very sure ba zasu taba approving al’amarin nan ba,abu ne da ke kanki kika sani ne,sabida haka indai akan wannan issue dinne ina roqonki da ki riqe duk wasu wa’azin ki,coz babu tasirin da zasu iya yi a kaina!”4

Ko bayan da ta fahimci Najman ta katse wayar hakan bai hanata cigaba da mita da masifa ba,Haka kawai zata nemi ta gaya mata magana akan mutanen da tafi dan dakon tasha sanin halin su,shi kuma Hamma Aboubakar d’in tasan qaryar da zatai ta rufe bakin shi,aure ne dai in sha Allahu babu fashi da ikon Allah,domin kuwa sosai jikin ta ke bata nan da wani dan lokaci zata zama mallakin Mukhtar Gaya.

***

Yau kam d’aukacin mutanen gidan sun so su makara daga sallar asuba,in ka debe Fadwa da tun bayan wayarta da Najma bata sake samun sukunin komawa wani baccin ba,misalin qarfe shidda da minti biyu Mammy ta shigo dakin,kasancewar ba dakin take kwana ba,ta dauki kacokan dakin nata tabarwa Fadwan me shirin zama surukarta nan ba da jimawa ba.

Mamakin sanya Fadwan a idanunta ba wanka take,a tunaninta zata shigo ne ta sameta ta gama shiryawa koma ace ta gama cancara ado da hadadden leshin da ta sanya akaje aka tsantsaro mata uban ubansun dinki,duk da aure ne da zaayi a sirrance,hakan ba zai hana ta tauye surukar tata daga looking good ba,ko banza ai tana ganin yau din tamkar wata rana ce dake shirin shiga cikin ranaku masu muhimmanci na tarihin rayuwar su.1

“Mammy barka da safiya,ina kwana?”

Fadwan tai hanzarin mikewa zaune tana gaida Mammyn.

“Lafiya lau Fadwa,ya kwanan kadaici?nasan ba wani baccin kirki kikai ba yau babu wancan a koken kuusa dake.”

Dariya ce taso kwacewa Fadwan,ita wallahi billahi ta manta da rayuuwar wani abu wai shi Fawad,wannan shine ba kanta,sai tai sauri wajen canza yanayin fuskarta zuwa kalar damuwa,gwanace dama a bangaren iya pretending,haka yasa ta marairaice fuska tace,

“Mammy banson in nuna damuwata aga kamar na zaqe,kamar kuma na nuna rashin kunya,mussamman a al’amari irin tamu qaddarar,duk da nasan Mammy kin fahimce mu,kuma kin mana uzuri bisa kuskuren da muka riga muka tafka,amma still a duk kallo na dunia da zan maki da tarin nauyi da danasani nakeyin su,ki qara yafe mamu Mammy.”

Sai kunga yanda ta lankwashe kai da murya tana rattafo zance tamkar mai shirin tsagewa da kuka,al’amarin da ya sake nasarar cusa tausayi da qaunar ta cikin zuciyar Mammyn,ko ba komi ai Allah ma nasan masu tuba,kalli tun daga muryar Fadwan zaka fahimci tsantsar nadama da danasani a cikin ta,hakan yasa cike da kulawa ta dubi Fadwan tace,

“Karki damu Fadwa,tuni na dade da yafe muku,nasan qaddara irin wannan bawa bai isa ya guje mata ba,fatana dai zaku taru ku rufawa juna asiri,ku kuma zama sanyin idaniyan juna,yanzu tashi maza maza ki shiga wanka ki gasa jikinki da kyau,kinsan jirgin qarfe shidda zaku bi.”1

Rungume Mammyn tayi tana faman gode mata,ko banza matar tayi nasarar sadata da dadden burin ta,ba zata taba manta wannan alherin nata ba,duk kuwa da cewar ta fahimci tsantsar sonkai cikin lammarin na Mammy,amma ai ita hakan ba damuwar ta bace,hasalima ita gaba ta kaita gobarar titi a jos.

Muryar Mammyn ce ta jefeta yayin da take qoqarin shiga bandakin.

“Bari inje in dauko Fawad din,nasan ma kila basu tashi ba,kinsan Niiman ma ba laifi akwai son bacci.”

Amsa mata tai da toh,can qasan zuciyarta tana cigaba da babbaka dariyar mugunta,ita har yau bata taba ji ko ganin sokuwar yarinya irin wannan Niimar ba,shiasa ma ta dena bi ta kanta,ashe yarinyar ma muguwar sakarya ce,ga tarin yarinta da hauka dake dawainiya da ita,ba ta jin ko uta da take auta a duk kafatanin gidan su tayi sakarci kwatankwacin irin wanda Niiman keyi,amma don tsabar rashin sanin ciwon kai irin na Mukhtar,ya rasa wa zaiso sai ita,kwafa tai azuciyar ta tanajin komi gaf yakeda zuwa qarshe,duk kuwa da jikin ta na bata akwai babban aiki a gabanta,sanin waye Mukhtar din.

STORY CONTINUES BELOW

“But she still won’t give up,ai bature yace if there is life,there is hope!”

***

30 Minutes Later.

Parlorn gidan ta nufa kanta tsaye,bayan ta tabbatar da ta sanya kayan da Mammyn ta aje mata,duk da bata cika yiwa fuskarta kwalliya ba,hakan baisanya yau taqi yi ba,kasantuwar ta mace mai bayyanannen kyau,kyau kuma mai daukar hankali yasa ita kanta asara take gani ta tsaya bata lokacu wajen fente fuska,amma yau sai takejin rashin dacewar hakan,ko banza yau din rana ce mai muhimmanci a gareta,hakan yasa ta dan tsantsara very light make up da yai matuqar amsar ta,gurin daura dankwali ne dama ake samun matsala da ita,babban dalilin da yasa bata fiye sanya natives ba kenan,duk da kasancewar ta buzuwa mutumniyar jamhoniyar nijer,tana son natives,especially ankara/atampa,sai dai bata taba daura dankwalin a kanta,sai dai ta sagalashi a kafada yayin da dogon gashin kanta zai maye gurbin dankwalin.

Yauma hakan ce tafaru,hankalinta kwance ta nufo falon cikin doguwar rigar bubun da aka dinka domin ta,kan nan babu dankwali,sai gashin nata da yai mata rumfa tun daga wuyanta har bayan ta,hakan yasa,tunda ta doso falon idanuwan mutanen falon suka dawo kanta,mussaman Fareeda da zuwan su gidan kenan ita da Adda bilkisu,domin tun ranar da tai tsautsayin yin subul daa baka ta arce tabi Addan gidan ta,hakan yasa sam bata taba sanya idanunta a idanuwan Maman Fawad din da akace tazo ba.

Kusa da Adda Bilkisun ta zauna,fuskar nan dauke da bayyananniyar fara’ah,lokaci guda ta sanya hannayen ta biyu ta dauki babyn Addan da bata wuce watanni biyar da haihuwa bata rungume,kana kuma cike da fara’ah ta shiga gaida su,ciki kuwa harda Fareedan da ta girma,don in bata bata shekaru biyar ba zata bata shidda.

Kunsan aka ce mai d’a wawa,hakan ce ta faru da Addah,lokaci guda taji yarinyar ta kwanta mata,duk kuwa da cewar da shirin tawaye suka diro gidan,sabida har ga Allah su basa maraba da wannan auren da Mammy ke shirin qullawa.

“Aunty Sakeena ina su Haniif din?na ganki ke daya?”1

Mamaki duk yagama lullubesu,mussaman su aunty Sakeenan,yanda akai cikin taqaitattun kwanaki har ta bi ta haddace mutanen gidan baki daya.

Cikin murmushin yaqe Aunty Sakeenan ke bata amsa,

“Su Haneef na school Fadwah,shiasa bamu zo tare ba.”

Fadwan na shirin maida akalar tambayar ta kan Fareeda ne suka ji shigowar shi,a kallo na farko da zakai mashi zaka hango ttashin hankalin da yake matuqar qoqari wajen dannewa,amma duk da hakan mutum ba zai kasa gane yanda hannun shi na dama kedan rawa ba,bai dubi kowa ba a parlorn sai Mammy,kanshi tsaye yace mata.

“Mammy ina kuka aiki Ni’imah ne?zuwana dakinta na biyar kenan bana samun ta.”

Sai a lokacin Mammyn ma ta tuna da abinda take ta son fadawa Fadwan cewa dazu da taje dakin Niiman bata sameta a ciki ba,toh sai tai tunanin ko kitchen ko wani guri taje.

“Bangane baka ga Niimah ba,nikuwa ina zan aiki Niima da safiyar nan,ni kaina dazu naje dakin nata some few minutes back bansame ta ba,thoughts ma ta shiga wani gurin ne shiasa ma ban maida hankali a kai ba.”

Zuwa yanzu tashin hankalin dake fuskar shi yagama bayyana baro baro,cikin wata iriyar murya mai dauke da amon tsoro yace

“Toh Mammy ina kuke tunanin Niimah zataje da sassafe irin haka?tun bayan da na dawo sallar asubah fa nake zaryan dakin nata,but babu ita babu Fawad,me hakan ke nufi?”

Zuwa yanzu gaba dayan su duk sun miqe,kafin kace me duk sun duru sun ggarzaya dakin Niiman hankulansu a tashe,sai dai kamar dazun ne,babu ita babu dalilin ta.4

Wata iriyar faduwar gaba ce ta same shi,ji yai gaba daya jikin shi na saki,bugun zuciyar shi ya yawaita,yayin da yakejin tamkar zuciyarshi zata faso qirjin shi,baya so ko kadan ya gasgata abunda zuciyar shi ke sanar dashi,no it just cant be,ya ilahi,ya fara ambaton Allah a can cikin zuciyar shi

Sautin ihun kukan Fareeda ne ya maido dashi hankalin shi,baya son tabbatar da zarginshi har yanzu,bayason yardarwa kanshi cewa Niiman shi ta guje shi,Niiman shi babu ita a wayewar garin na yau,dadin dadawa babu ita babu yaron da yake jin ko zai iya qara rayuwa ba tare da shi ba.

“Mammy look here,she left a letter.”2

Ya tsinkayo muryar Fareeda na yi mashi quwwa a kunne.

“She left a letter?she left a letter?”

Ya riqa maimaita kalamen da sukai nasarar tarwatsa duk wani guntun hope da yai mashi saura.

“Niimah left a letter, letter dake dauke da bayanan cewa tagaji da hakuri da shi ta tafi?ta tafi mashi da babyn shi?sun tafi sun barshi?bata duba ko wane hali zai iya shiga ba ta tafi ta barshi?bata damu da rusa shi da hakan zeyi ba,bata damu da tarwatsa shi da hakan zeyi ba?shin yaune take nufi da kalmomin ta na zeyi nadamar sanin ta a duniyar shi?”3

Ya sulale qasa yayin da wasu hawaye masu zafi ke tsartowa daga kwarmin idanun shi.

Abinda bata sani ba shine,yau ba nadamar sanin ta yayi ba,abu daya yayj shine nadamar abinda ya aikata mata,nadamar rashin nuna mata dukkanin qaunar shi gareta,nadamar rashin nunawa duniya how much she meant to him,how much he love and needs her all by himself, how his selfishness needs and yarn nothing but her,nadamar shi kenan,nadamar da bazai dena ba har qarshen numfashin sa.1

“I’m soa sorry Hayatiey.”3

Ya rika furtawa da dukkan qarfin shi,yayin da hawayen so da qaunar ta ke samun nasarar bulbulowa daga idanuwan shi,qila ya samu sauqi.

Ni kaina i do hope ya samu sauqin!Katsina,Nigeria.1

11:45 am.

Kimanin awannin kusan bakwai da isowar ta birnin na Katsina,har yanzu bata gusa daga cikin tashar motar ba,tun bayan fasinjoji sun sauka itama kuma tabi ayarin su rungume da Fawad din a qirjinta,duk da har ta iso garin na katsina bata gama gane dalilin da yasa ta zabi garin ba a duk iya tarin garuruwan dake nahiyar arewacin najeriyar,abu guda ta sani,abu guda kuma take da yaqinin sa shine labari da take dashi a kan karamci da kara irin na al’ummar jahar,harma takanji sau da yawa anaiwa garin kirari da ta dikko dakin kara,kunya gare su tsoro babu,kenan za ta iya cewa wannan din na daga dalilin da ya sanya ta zabi garin,mussaman don tayi nesa da nahiyar da Mukhtar da sauran en gidan su suke.4

Maganar fadar irin yunwar da takeji ma b’ata baki ne,ba wai kuma babu kudi a hannun ta ba,kawai dai bata jin tana da sauran kuzari ko kuma kwanciyar hankalin da zata sanyawa tumbin ta wani abu,mussaman a guri irin wannan da bata saba da yanayin ba,lokaci lokaci ta kan duba agogon wayarta,domin shi kadai ne abu mai amfani da ya rage a wayar,ksantuwar ta cire simcard dinta ta balla takuma watsar,sannnan kuma duk wasu hotuna da sauran wasu abubuwa da kayi garajen tuno mata da mutanen can ta tabbaatar da ta goge su a wayar,jikinta na bata goge su a wayar na nufin shafe su daga duniyar ta.

Wani d’an kamasho ne dake ta kai da kawowa tun bayan da ya fahimci da zamanta a bakin wata bishiya dake dan nesa da inda motoci ke lodi,da farko bata lura da shi ba,sai bayan wasu taqaitattun kai da komowar da suka sanyata sanya mashi alamun tambaya,hakan yasa ta qara riqe Fawad din sosai a jikin ta,lokaci guda tana sake qanqame jikin ta cikin hijabin ta,domin a kallo guda da tai wa mutumin bai kwanta mata ba,duk kuwa da qarancin shekarun ta.

Wannan karon da ya dawo kai tsaye nufota yayi yana wage baki,daalama murmushi yake sakar mata,hakan kuwa ba qaramin tasiri yai a zuciyar Niiman ba,kawai sai ta sadaqar shi din mutumin banza ne mai shirin cutar ta.

“Barka dai,sannu baiwar Allah.”

Dan matsawa tayi baya tana zare idanu,gogan kuwa banajin ya fahimci yanayin da Niiman take ciki,domin daga haka kai tsaye yanemi da ya zauna kusa da ita kamar wadda ya dade da sani.

“Malam please lafiya?yaya zakazo inda nake ka nemi damuna?”

Dakatawa yayi yana kallon ta baki sake,lokaci guda mamaki na lullube ilahirin fuskar shi mai matsakaicin fad’i,a kallo guda da zakai mashi zaka san cewa fari ne,amma daalama wahalar rayuwa ta sanya shi komawa baqin dole.

“Ikon Allah,toh aike baiwar Allah tayaki zama zanyi,naga tun isowata tashar nan misalin qarfe bakwai na ganki a zaune a gurin nan,kyma gashi sama da awanni biyar baki da alamun barin gun,toh ganin kar kadaici yai maki yawa na aje aikin da nake nazo in tayaki hira.”1

Ya ida maganar yana washe hakora,hakoran da sungama mutuwa da dattin sigari da goro,dama ya dade da sanya mazaunen shi a gefenta,hakan yasa tai hanzarin mikewa tana mai jin tashin hankalinta na dawowa,ba kuma ta sake wani tunani ba tai baya baya ta fara ttafiya da sauri,ko kadan bata shirya wa wani iftila’in rayuwar ba,duk datasan akwai yiwuwar hakan mussaman a irin yanayin da take ciki yanzu.

Jiyo muryar shi tayi yana binta,lokaci guda yana mai kwala mata kira

“Baiwar Allah dakata mana,kinji,jimana.”

Aifa shikenan sai ta sake rudewa ta qara sanyawa sawun qafarta mugun sauri,sosai take da yaqinin mutumin nan dan iska ne,kuma abinda zai baka mamaki shine yanda mutanen tashar ke al’amuran su ba tare da sun lura da abinda ke faruwa tsakanin su ba.1

STORY CONTINUES BELOW

Bata san ya akai ba,ita dai ta ganta a wajen ttashar,duk ta hada gumi,ttsayuwar tata yayi daidai da isowar dan kamashon shima,lokacin ta fara waige waigen inda yakamata ta bi,hakan yasa batayi aune ba sai jin saukar hannun shi tayi a kafadar ta ta baya,hakan yasanyata sakin ihu da uban qarfi tamkar wacce wutar lantarki taja,haka kuma qiris ya rage ba ta saki fawad din dake hannun ta ba shima a jigace kuma a gajiye.

Daidai nan kuma wata dattijuwar mata da bazata wuce shekaru hamsin ba zuwa hamsin da biyar ta fito daga wani qaramin mall dake gefen tashar,a gefen ta kuma wata budurwa ce da bazata wuce shekaru ashirin zuwa ashirin da biyu ba,saukar hannun dan kamashon a kafadun Niiman yayi daidai da dagowar idon matar,hakan yyasa duk wani tashun hankali da Niiman ta shiga a idanunta ne.1

“Ke dallah can ana maki magana kinai wa mutane yanga,banza kawai nunar rana ma dake,da ganinki ma kila cikin shege kikayo aka koroki daga gidan ku,shine har ana maki magana zakiy mana iyayi er rainin wayau kawai da ke.”

In banda rawa babu abinda jikin ta keyi,hakan yasa bata damu da zantuttukan shi ba,ita dai burin ta a lokacin shine ta samu tsira daga mutumin da takeda tabbacin yau qila sai dai wata ba itaba,mussaman yanda taga yakoma mata kalar mayu marasa imani,take yanke kuma ta riqa danasanin sanya qafafun nata a birnin na katsina,domin kuwa bata shaiida karar da ake yamadidin suna da ita ba.

“Don Allah kayi hakuri,ni bansan me nayi maka ba bawan Allah kake ta bina.”

Zuwa lokacin hawaye ne ke zubowa daga idanun ta,ga kuma Fawad shima da azabar zafi da gajiya ta taru tai mashi rubdugu sai faman canyara ihu yake,hakan yasa sai faman jijjigashi take itama tana nata kukan,sosai take nadamar zuwanta garin,dama Nijar din ta ta wuce taje ta nemi dangin mahaifiyar ta,tasan ko ba dade ko ba jima kila ta gansu,daga nan ta nemawa mahaifiyar ta gafarar su.1

Yana shirin sake kai hannu jikin ta ne ya ji saukar jaka a kanshi,ko kafin ya dago ya sake jin wata,jakar kuma mai dan girma ce da kauri,ga kuma wani dan qarfe da akaiwa jakar ado da ita,hakan yataimaka wajen bubbuge mashi gingimemen kan nashi mai dauke da sanqo.1

Juyowa yayi a fusace don ganin isashshen dake yimashi wannan iskanci,had’a idanun nasu yayi daidai da ja baya da yayi yana muzurai,ba shakka yasan yau tashita qare,babu kuma wata kalmada zai furta da zata fiddashi.

“Da kyau Yaquba,da kyau,watoh kai dai ba zaka dena saida hali a duk inda zaka tsinci kanka ba ko Yaquba?ka sani tun dazu nake a gurin nan,kuma ina kallon duk wan iya shegen da ka riqa aikkatawa yarinyar mutane,kasan Allah wannan maganar a kunnen Abbu.”

Sai ta juya gefen da budurwar da suke tare take tana qunshe dariyar bakin ta,hararar da matar ta sakar mata ya sanyata maida dariyar da sauri,toh ita me tayi?

“Ummitah fiddo wayata ki daukar mani hoton shi a yanda yake dinnan.”

Da sauri Ummitan ta zaro wayar domin yin abinda Ammyn ta sata,dama haushin shegen take ji,mussaman yanda jiya yasa Abbun ya sanya dokar karta qara kawo wan aboki namiji cikin gidan shi,duk kuwada qoqarib fahimtar dashi da tai qoqarin yi.

Ita dai Niiman kallon su kawai take,bangare guda ta riqa godewa Allah domin kobanza zuwan su gurin ya tseratar da ita daga sharrin mutumin da taji ankira da suna Yaquba.

“‘Yawwa zo ke kuma d’iyata.”

Ta yafito Niiman kusa da ita,kana lokaci guda ta nemi jin baasin abinda ke sa jarirn kuka.

“Kukan me yake haka?aiken ku akayi hala wannan shashashan ya nemi yi maku sakarcin shi da ya saba?toh da’alama ma zafi ne ya dameshi,ah ah ikon Allah wannan ai jaririne ma danye,garin yaya mamarku ta aiko ki kasuwa koma ince tasha da wannan lab’ub’un abun?haba!”

Duk ta jero mata tambayoyin da ba ta da amsar su,ita dai yanzu burinta shine tta bata Fawad din ta qara gaba,kila ta daceda inda zata nemi koda aikatau ne da kuma gurin kwana,domin sosai hankalinta yake tashi inta tuno da dare.

STORY CONTINUES BELOW

“Ko bata jina ne?yaya sunanki ne ma?”

Muryar Matar ta dawo da ita hayyacin ta,ko kafin tai qoqarin ba ta amsa sai jiyo Yaquba sukai ya fara makyarkyata,lokaci guda yafara yi wa matar magana yayin da yake kallon gefen da wani mutumi ke kusanto su.

“Toh nidai Ammyn yara kiyi hakuri,wallahi tallahi kingani dama wayar ta ce ta manta shine na biyo ta inbata taqi tsayawa,kuma ma ni taimakon ta nakeson yi dama,ganin awanni kusan shidda ta kwashe a cikin tashar nan zaune ita kadai sai wannnan jaririn,ki taimakeni ga Chicago nan tahowa nan,kuma kinsan makomata inhar yaji zancen nan,don Allah Ummita ki saka baki,daga yau ba zata sake samuna a abu irin wannan ba.”

“Awanni sama da shidda zaune a tasha?”

Ta sake maimaita maganar da Yaquban yayi?sai a lokacin ta sake sanya nutsuwarta wajen kallon yarinyar da kyau,gaba dayanta she look disturbed,she look tired,she look exhausted, she look pale,she infact she look like someone who gave birth,ta yi kama da mai jego a fizge,sai dai ta sanya alamar tambaya a jegon da take tunanin ta nayi,batajin wannan qaramar yarinyar ce ta haihu,qila dai qanin ta ne,toh meyasame su?ko uwar ce ta rasu ta barsu?ko b’ata sukai?tasake kallon fuskar Niiman,ba tayi mata kama da bahaushiya ba,tafi yanayi da irin sadakar yallan nan en Nijer,ko kuma irin inyamuran cross rivern nan,kila kuma idanun ta ne ke mata gizo da wata fuska da ta sani,amma ta mantaa ina.

“Ammyn yara don Allah kittaimakeni ga Chicago nan.”

Ta tsinkayo muryar Yaquban,hakan yakatseta daga kallon da take yi wa Niimar,hakan yasa ba tare da ta kalleshi ba tace,wuce ka tafi zamu hadu a gida anjima,ko kafin ta idasa rufe baki Yaquba ya arce,fiiit haka ya fella yabar gurin da mugun sauri,domin ya gwammace zancen nan yaje kunnen Abbu akan yaje kunnen Chicago.

“Ammy for God’s sake ku rika tuna dan adam mai rai kuka bari a mota yana jiranku,haba Ammy daga ku sayi ruwa you almost spend awa daya a wajen nan.”

Bata damu da ta dago kai ta kalli ko waye ba,amma daga en zanttuttukan da suka wakana tsakanin Ammyn da Yaquba ta fahimci ko waye mai maganar,qila shine Chicagon,sunan da tunda aka fara fadar shi yai mata tsaye a rai,shi kuma wannan ya rasa sunan da ya zabi jama’ah su kirashi da shi sai Chicago?sha take Chicago sunan wani garine a united state of america,but here comes wani da irin sunan,kuma ma musulmi.

“Sorry my Dear,wani dan problem ne yataso nake qoqarin sorting din shi out,ke Ummita wuce ku tafi cikin mota ganin nan zuwa.”

Ummitan ba ta qara cewa komi ba da ya wuce toh kawai tai gaba abin ta,shi kuwa malam Chicago dama ba wai yabi ta kan Niiman ba ne dake gefe sunkuye da kai,kawai dai jaririn dake hannun Ammyn ne ya janyo hankkalin shi,hakan yasa ya dan leqa fhskar jaririn,aikuwa daidai ya bude ido,sai kawai yadena en qananan kukan da yake yai zuru yana kallon Chicagon,sai karantse da Allah ganin shi yake,ah ah toh nace jaririn kwanaki tara nefa kacal,yaushe idanunma suka fara ganin gari?

“Ammy this baby is cute,don Allah ki bani shi mana.”

Harara ta buga mishi kana tace tohya dauka yatafidashi anbashi,yana daria ya sunkuya yai mashi peck a kumatu ya juya domin komawa cikin motar su,bai sani ba ya dan takata,hakan yasa shi dan dakatawa yana bata hakuri.

“Please im so sorry ban kula bane.”

Kanta a sunkuye tace,

“Karka damu babu komi,nagode.”

“Nagode kuma?”

Ya maimaita kalmar a ranshi,ya dauka shi ke da hurumin godia?mussaman don ganin shine yai laifi kumaa a kace anyafe mashi?ashe kenan shine ya cancanci ya gode mata?

“Nima nagode.”

Ya furta yyayin da yake kallonkanta dake sunkuye taqi dagowa,daga haka baice komiba ya wuce,yayin da yakeji wani shashen jikin shi na matuuqar son ganin fuskar wannan yarinya mai tarin hakuri da karamci.

Muryar Mammyn ta dawo da ita,bayan tagama kallon abinda ya wakana tsakanin ta da Chicagon.

“Menene sunanki?”

“Ni’imah!”

Ta bata amsa a hankali.

“Well,Ni’imah bansani ba,ban kuma san labarin ki ba,amma abu guda na sani,gaba dayanki kina buqatar taimako,shin kina son taimako daga garemu?”

Dagowa tayi da dan sauri tana sake kallon fuskar Matar da aka kira da Ammy,a kallo na farkon da tai mata yanzu sai kawai taji tana son yarda da ita,kila hakan nada nasaba da halin da take ciki ne,toh koma dai menene matar look harmless,and tanajin tamkar Allah ne ya dubeta ya yanke mata rabon shan wahala ya aiko mmata da wannan baiwar tashi zuwa gare ta,shin bai cancanci ta gode mashiba?1

Ya cancanta,Allahn ta mai ji kuma mai gani ne,mai kuma tausayi ne ga dukkan bayin shi,Allah abin godia.1

Kanta a sunkuye tace,

“Zan dawwama ina godewa karamcinki,sosai nake da buqatar taimako,ni baquwa ce anan,bansan kowa ba!”1

Rufe bakin ta yayi daidai da jin tafin hannun Ammyn cikin nata ta kama sun fara tafiya,ga kuma Fawad sabe a dayar kafadar ta,ba tare da ta kalli fuskar Niiman ba tace,

“Let’s go home Ni’imah,ke da Babyn nan na buqatar hutu.”

Bata ce komi ba a bayyane,illa qasan ranta ta riqa jin batai kuskuren zaben katsina a jerin garuruwan da ta sani ba!lallai akwai tarin mutane masu karamci da yakana!1

Ya yama taken yake?ta tambayi zuciyar ta,daidai lokacin dasuka iso gaban qatuwar jeep din dake girke a bakin titin,idanun ta suka sauka kan plate number din.

“Katsina home of hospitality.”

***Kaduna,Nigeria.

Sakanni sun koma mintoci,yayin da mintuna suka juye zuwa awanni,awanni kuma suka taimaka wajen hauhawar samuwar kwana,hakan ce ta faru yau kwana d’aya da bacewar Ni’imah da jaririn ta,bacewar da har yanzu Mukhy ke fama da radadin azabar faruwar lamarin,ilahirin gidan al’amarin ya tabasu,mussaman Fareeda da Adda Bilkisu,baa maganar oga kwata kwata,ganin cewar shi tunda ya shige dakin shi babu wanda ya sake ganin keyar shi,gara ma lokacin da su Addan zasu tafi gida sunyi nasarar tausasa shi,gami da bashi shawarwarin da suka dace,duk kuwa da suna jin yiwuwar samuwar kwanciyar hankalin nashi ba abu bane mai sauqi.

Wayewar garin ya qara zafafa lamarin,domin kuwa babu wani cigaba ko wani labari mai dadi daga guraren da aka bada cigiyar su,al’amarin da ya sake dugunzuma hankalin Fadwa,takuma riqa tsine wa Ni’iman sau ba adadi a cikin zuciyarta,sabida tana ganin ta zama shedaniya mai toshe hanyar alheri,eh mana shedaniya mana,tunda gashi nan tayi nasarar dakatar da babban burin ta dake gaf da cika,kaico da er iskar yarinya irin Niimah,kaico! A cewar ta kenan!

“Mammy yace in maido abincin ba zaici ba,kuma kinga na jiyama haka yace in maido ba zaici ba,don Allah Mammy ki sa baki yaci abincin nan kafin ulcern shi yatashi.”

Cewar Fareeda bayan da ta shigo cikin madafin gidan ta tarar da Mammyn a ciki ita da Fadwa tana faman aikin lallashinta akan taci abinci.

“Au yanzun ma cewa yayi ki maido breakfast din?wai ni don Allah don Annabi me ke damun yaron nan ne for goodness sake?kawai daga yarinya ta kama gabanta ta tafi shine zaibi ya tsangwami kanshi ya hana kanshi sakat?wace iriyar masifa ce wannan ne ne ni?”

Daga Fadwan har Fareedan babu wanda ya iya tanka mata,gara ma Fareeda da lokaci guda fuskarta ta qara sauyawa da alamun jin haushi,ita kam har ta kan kasa tantance wace iriyar mutum ce mahaifiyar su?gaba dayan ta bata cika alqibla ba.

“Haba Mammy,b’acewa fa Niiman nan tayi,ga jariri a tare da ita,a tunani na duk wani mai imani dole hankalin shi yatashi duba da sanin cewa qasar gaba daya ma ba guri ne da Niiman ta gama sani ba,don Allah Mammy ku riqa reasoning.”

Tsaki Mammyn tayi ta fice,lokaci guda tanajin yakamata ta kawo qarshen lamarin nan,ai tanajin tana da wannan ikon ko?hakan yasa direct dakin Mukhtar din ta dosa,yayin da can qasan ranta ta qudiri aniyar yi mashi wankin bbabban bargo,wannan iskanci da iya shegen ba a muhallin ta ba.

Zaune ta iske shi kan carpet ya maqure,kallo guda zakai mashi ka karanto tsantsar damuwar da yake ciki,lokaci guda kuma ga wata iriyar rama da yayi cikin yini guda,ba shakka Niima ta tafi da kaso mafi yawa na daga walwala da jin dadin shi.

Shigowarta bai sanya ya dago kanshi ba,hasalima sake sanya kan nashi yayi cikin guiwowin sa tun fahimtar shigowar Mammyn,ko kadan baya maraba da bayyanuwar ta cikin dakin,ko tantama ba yayi yasan ba alheri ne ya shigo da ita ba.

“Mukhy what is wrong with you eyeeh?”

“What is wrong with him?” Ya riqa maimata tambayar a cikin ranshi,yana ganin idan za ai mashi adalci,bai cancanci ko da tambaya mai kama da wannan bane.

“Mukhy dakai fa nake,meke damunka kake nema ka illata kanka?ina sane da jia babu abinda ka sanyawa cikin ka,haka zalika yanzu ma ka maido abincin da aka hada maka,duk a wani dalili?a dalilin banza dalili maras tushe?kana tunanin babbar budurwa kamar Niima zata bace ne?ko kuwa wani ne zai shigo har gidan nan ya dauketa?nakan rasa gane wannan banzar dabiar taka ta rashin kan gado….”

STORY CONTINUES BELOW

Ta numfasa kana ta cigaba.

“Toh let me tell you one thing, wallahi tallahi ba zan zura ido ba ka nemi salwantar da taka rayuwar akan yarinyar da bata da hankali da tunani ba,yoo eh mana in ba rashin hankali da tunani ba ta yaya zata dauki yaron mutane ta sanya kafa ta kama gabanta kamar tasan wahalar haihuwar?duk wannan haqilon da kaga inayi akan cigiyar Niiman ba don kowa nakeyi ba sai don kai da Fadwa,mussaman sanin zafin d’a da ni din nayi,duk kuwa da cewar naku yaron ga shi ga irin shi nan,baa kirashi da kai tsaye kamar kowa ba.”

Har yanzu da ta rufe baki bai dago ba ballantana yace mata kanzil,hasalima fata yake inama akwai abinda zai uya rabbashi da numfashin shi ko ya huta da wannan musibar dake bibiyar shi,a iya kwana daya kacak da bai sanya su a idanuwan shi ba ji yake tamkar shekara daya ce,yanaji a jikin shi ba zai jima ba a ban qasa matuqar rayuwa ta cigaba da wanzuwa ba tare da sanin inda hasken idaniyanshi suke ba.

Ganin babu alamun zai tanka,ko kuma ya nuna yaji fadan da take mashi ya kara assasa wutar bacin ranta,take yanke kuma ta kudiri aniyar ko ta wani hali ne sai ta rabashi da Niiman da a tunanin ta ta yakice ta a ranshi,ashe ihu take bayan hari,hakan yasa ta sake dubanshi da kyau tace,

“Mukhy nasan kana sane da aurenka da zaa daura kai da Fadwa ko?a inda faruwar lamarin nan ya sanya anyi biris da lamarin,toh kuma sai nake ganin tafiyar Niiman ai bai isa dalilin da zai sanya a fasa d’abbaqa sunnar ma’aiki ba koh?ko banzaa ina ganin hakan shi dinne gatan da zan iya yi maka a yanzu,hasalima hakanne kadai hanyar da zata taimaka wajen sassauto da duk wani qunci da zuciyar ka ke dako,nasani,nasani kwarai bacewar d’a ba abu bane mai sauqi ba,mussamman in akai duba da hannun da jaririn yake,amma duk da haka ba zan fasa ganin na sauqaqa maka baqin cikin ka ba gwargwadon iyawata,ko banza ni din uwa ce mai son ganin farin cikin d’iyoyinta.”

Ya rasa da wata kalma zai dangata mahaifiyar tasu da ita,abu guda ya sani,abu daya yasani shine she is too selfish,her selfishness is on another level,wanda har yanajin wani sashe na zuciyar shi na jin haushin ta,duk kuwa da sanin cewar hakan bai kamata ba.

“Ba neman amincewar ka nake ba,asalima inayin abinda nake ganin zai amfani rayuwarka ne,because nasan kasan ni uwa ce,hakan ke nuni da cewa ba zan aikata abinda zai kaika ga halaka ba,so as of now nagama yanke shawara,zaa daura aurenku da Fadwa kamar yanda yake a tsare,daga nan kuma sai mu fuskanci inda rayuwa ka iya miqa mu.”

Daga haka ba ta sake wata magana ba ta juya domin ficewa daga dakin,juwayar tata yayi daidai da kai idanun ta bisa farar takardar da Niiman ta bari,wacce Allah bai sanya ta maida hankalin sanin me ta qunsa ba,mussaman don ganin yanda Mukhtar din yai magajiya da lettern.

Dakatawa tayi ta nufi stool din da takardar ke yashe akai,bata san meyasa hankalinta ya miqa akan son sanin me ke k’unshe da takardar ba.

Ga abinda ke qunshe da wasiqar.

“I’m writing this letter with a very heavy heart,which i can’t really tell how my heart is aching right now,and im very sure i will live with this burden till end of time.

This is for you Yaa Mukhtar,you’ve always been a nuisance to my well being which im so sure you knew it yourself,till date i couldn’t comprehend what i ever did to deserve such cruelty from you,i don’t have to mention how you completely shattered me into pieces, how you actually made me into who i am today,a mother out of wedlock,ya rabbi!i will never forgive you for this Yaa Mukhtar.

And this is for you Mammy!

Mammy all my life i thought, i really thought you were that one person i can lean on,that one person i can look up to,that one person i can actually call a mother with my chest,but unfortunately i was mistaken,therefore im so sorry for being a burden to you and the rest of your house hold,i promise i will make a long distance between us,and im also sorry for peaking at your room,privacy to be precise,which actually made me realize who i really am!all thanks to you Mammy!

Lastly i’m using this medium to apologize for anything ive ever done to all of you,and to also thank you for bearing with me despite you knowing who i am,i know i will be long gone when you will notice this letter,do not bother looking for Fawad,coz i know he is your only priority, as he is to me,because he is my son too.

…Ni’imah. “

STORY CONTINUES BELOW

“Because he is my son too!”

Kalmar ta riqa yi mata amsa kuwwa cikin kwakwalwar ta,ba ta damu da sanin cewar Ni’iman taji hirar su da Fadwa ba,ba wannan bace damuwar ta,damuwar ta daya ce a yanzu,damuwar ta daya ce jinin Fawad na gudu ne hade da jinin Niimah da Mukhtar din ta,kenan tayi nasarar gurbata mata zuri’ah kenan?

Ai sai ta dafe kai,yayin da kan nata ke wata iriyar sarawa,kana lokaci guda dukkan ilahirin jikin ta daukar rrawa tamkar mazari,yau ita kam ta shiga uku ta lalace,watoh duk kaffa kaffan da take sai da Mukhtar ya watsa mata k’asa a idanuwan ta,sai da yai nasarar gurbata mata zuri’ah,kaii ba zai yiwu ba!

Zuwa yanzu ta sulale k’asa tana rafka gumi ta ko wane lungu da saqo na jikin ta,duk kuwa yanayin sanyi da ake ciki,yau ita kuwa wace iriyar baqar rana ce wannan a gareta,shikenan kuma sai taji wani kuka na taso mata,shin meyasa Mukhtar zeyi mata haka?innalillahi wainna ilaihirraju’oon.

Jiyo sautin sheshheqar kukan Mammyn ya sanya shi dago kai da sauri,shi be mayi tunanin tana dakin ba,tsabar tunanin da yai mashi yawa,jiyo sautin kukan nata ya qara tayar da nashi hankalin,hakan yasa ya taso da sauri domin jin dalilin sauyin yanayin nata.

“Mammy lafiya?me ya faru?please Mammy ku dena kuka don Allah,in sha Allahu zanci abincin,zanyi abinda……”

Maganar shi ce ta datse sakamakon hango farar takardar a hannun Mammyn,hakan yasa da sauri ya maida kallon shi bisa stool din da yake tunanin nan ya saki lettern da zaiyi alwala dazu da asubah,kenan taga me ke kunshe da wasiqar?hakan yasa ya saketa yakoma ya zauna dab’ar yana dafe kai,abubuwa sunyi mashi yawa,yanajin tamkar zai iya shurawa a kowanne lokaci.

Kafin ya ankara sai ji yai Mammyn ta ciyo kwalarshi tana kikkifa mashi mari,lokaci guda tana hadawa da antaya mashi zagi ta ko ina,al’amarin da yai nasarar janyo hankulan Fareeda da Fadwa,wadanda dama kusa suke,hakan yasa suka fado dakin da gudun su jin yanda Mammyn ke kuka tana marin Mukhtar din.

Rirriqeta sukayi ganin Mukhtar din bashi da niyyar matsawa daga lodi lodin tafin da Mammyn ke antayawa fuskar shi,fuskar da har ta yi fushi ta suntume,abinka kuma da jar fata,sai ta yi jawur abin ta.

“Mammy don Allah,Mammy please stop it,you are hurting him.”

Cewar Fareeda cikin muryar kuka.

“Rabu dani in qarasa shi,tunda shi din dan banza ne mai kunnen qashi,upon all the warnings ive been giving this boy, sai da ya daka tsalle ya watsa mani qasa a idanu,oh ya rabbi,ni Mukhtar har nawa kake ma da har kasan kai wa mace ciki,la’ilaha’illalahu!”

Ai sai ta sake saka kuka tanajin wani sabon bacin rai na dibar ta,ba shakka Niimah ta cuceta,ta kuma zalunce ta,lallai ya wajaaba a kanta ta nemo ta duk inda take domin hukunta ta daidai da laifin da ta aikata a gareta,domin kuwa sosai take da yaqinin cewa itace zata yaudari Mukhtar din har su aikata abinda suka aikata.

Fadwa kam babu bakin magana,tuni cikinta ya tsure tun fahimtar abinda ke sanya Mammyn kuka,shikenan asirin ta ya tonu,hakan ke nuni da cewar burin ta na auren Mukhtar din tafe yake yana dabo,ba shakka ko sama da qasa zata hade ba zata taba hakura da son da take wa Mukhtar ba,a shirye take da ta fuskanci duk wani qalubale daka iya kawo mata hari,gama tunanin hakan ya sanyata zubewa kasa gami da riqe qafafun Mammyn gamgam tana kuka,lokaci guda ta fara rattabo zancen neman afuwar Mammyn,gami da nunawa Mammyn tsantsar soyayyar da ttake wa Mukhtar din ne ya sanyata aikata abinda ta aikata din.

Tsabar tsana da kuma haushin Niiman da Mammyn ke ji ya sanyata kasa ganin kuskuren da ita Fadwan tayi,dama idanunta sungama rufewa,hakan yasa babu bata lokaci ta yafewa Fadwan,hada qarin cewa ba laifin ta bane,shi so babu haukar da baya sanya dan adam.

Anan take kuma ta tabbatar wa Fadwan cewa gobe babu gudu babu ja da baya sai Mukhtar ya zama angon ta,ba don komi ba sai don ta qara jaddada tazara tsakanin danta da tsinanniyar yarinya irin Niimah,a ganin ta hakan itace kadai hanyar da zata rage takaicin da ta kunsa mata,tai kwafa cike da baqin ciki maras misaltuwa.

Furucin na Hajia ya sanya Fareedan tsoma baki cikin maganar tasu,

“Amma Mammy kunajin kunyi wa Yaa Mukhy adalci keenan?atleast a barshi yaji da batan yaron shi mana,sannan kuma baku damu da jin raayin shi akan lamarin nan ba kawai sabida wani dalili naku maras tushe zaku aikata abinda ina ganin zai iya kaiku ya baro.”

“Toh uwata zoki bugeni kawai,ashe baki da kunya Fareeda?ni zaki gaya wa abinda ya kamata da abinda be kamata ba?how dare you?”

Cikin hawaye Fareedan tace,

“Ni ba nufi na ba kenan ba Mammy,amma kuyi hkri in ranku ya baci,but still Mammy in baki manta ba yanzun nan kika gama furta cewar Ya Mukhtar din nawa yake,idan har ko zaki iya furta hakan toh ni banga amfanin matsa mashi akan auren da bashi da raayi ba,maganar gaskia fa Mammy.”

Ta ida zancen tana hararar Fadwan,gaba daya matar ta sure mata,dama can ba wai ta wani yi mata bane,a ganin ta wace iriyar tabewa ce wannan budurwa ki taho gari ya gari tun daga wata qasa ki biyo saurayi gidansu ki tare,hakan bai isheki ba sai kin tursasashi aurenki,wannan rashin aji har ina?

“Zoki fita ki bar dakin nan kafin na saba maki,sakarya wacce batasan abinda dunia ke ciki ba.”

Ba tare da ta sake furta wata kalma ba ta zumbura baki tai gaba,lokaci tana mai bangaje Fadwan dake gefen Mammyn a zuqunne.

“Karki damu da Fareeda kinji?aure dai babu fashi indai ina raye.”

Cewar Mammyn a loakcin da take dannawa Mukhtar dake can makure da kai harara,gana dayanshi haushi yake bata,har yanzu ta rasa wacce masifa ce ta sanya shi aikata abinda suka aikata din.

“Idan kagadama ka hadiyi zuciya ka mace,aure na rantse da Allah babu fashi,zakasan ka tsallake magana ta.”

Daga haka ta yunkura Fadwan ta kama ta suka nufi hanyar barin dakin,sai dai muryar Mukhtar din ce tai nasarar dakatar da su,lokaci guda Mammyn ta riqa jin yau inama zata ga Niimah,toh da ba shakka sai ta gwammace bbata taba sanin ta ba a dunia!

“Mammy i thought labarin nan zai sanyaki ki rusuna,nadauka lamarin nan zai sanyaki ki san annabi ya faku? A wauta da tunani irin nawa hakanne zai sanyaki sakar mani mara domin nunawa macen da nafi so kaf dunia bayan ke soyayyah?ashe ba haka bane Mammy?shin in tambayeku mana,why are you so selfish?please please tell me Mammy,meyasa kike da son kanki?a mizani na hankali banajin akwai wani laifi da Niima ta taba yi maki,ko akwai?babu!laifinta guda ne,laifin ta daya ne Mammy,laifin ta shine samun ta ta hanyar da ke kanki kike da kamasho a ciki,Mammy kina cikin sanadin qaddarar Niimah,kin taka muhimmiyar rawa wajen assasa tata qaddarar,amma a yau kece mutum ta farko dake qyamar ta saboda laifin da bata da masaniya a kai,laifin dada tana da iko da ta hana wanzuwar shi a ban k’asa,Mammy why are you like this don ya rasulillahi?”

Ya nunfasa yayin da yake dauke ragowar hawayen dake fita ta bayan idanun shi,kana ya cigaba.

“Mammy duk abunda na aikata,na aikata su ne domin ke,na aikata su ne domin in nuna maki ishara,na aikata su ne domin kiji me akeji,inaso ki dandana kema,kiji ya akeji idan aka kiraki da kakar shege maras asali,jinin nan da bakya qaunnar haduwar shi da nawa,ni din na jajirce wajen haduwar su,ba don komi ba sai don in nuna maki ba zan taba iya rayuwa babu Niimah ba,sannan kuma yazamana ko babu ni babu Niimah a ban qasa,jinin zai cigaba da gudana cikin zuri’arki!”

Wannan karon da ta juyo rufeshi tai da bugu tana faman rusa ihun kuka,ba shakka Mukhtar ya cuceta,yakuma zalunce ta,shin anya zata iya yafe mashi kuwa?

***

About AIS

Check Also

HOD’IJAM CHAPTER 7 KARSHE BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 7 KARSHE BY NOORIEEYAH                 Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *