HOD’IJAM CHAPTER 10 BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 10 BY NOORIEEYAH

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

*

Cikin yanayi na qwarewa yake murza sitiyarin motar ta shi me qirar honda accord 2021,kasantuwarshi ma’abocin son farar kala,idan ka debe yanayin suturar shi ta zuwa aiki da suke kasancewa a kusan ko wanne lokaci baqaqen suits ne,inka debe wadannan toh kusan ko da yaushe cikin fararen kaya zaka iskeshi,be it natives or english wears,kai harma abubuwan da suka danganci sauran kayan amfanin shi,kama daga motar hawanshi da sauran wasu abubuwan da baa rasa ba.+

Ko da ma can munsan waye Mukhtar Gaya a shekarun baya,mutum ne wanda ko a wancen lokacin yanayin dabi’unshi na nuni da zallar isarshi da kamewa,wanda hakan yake taka muhimmiyar rawa wajen sanyawa mai kallonshi yabashi shekarun da suka zarce nashi,yana da wani irin kwarjini da cika ido,mussaman yanzu da girma yazo mashi akan shekarun baya,har yanzun kuma wasu dabi’un nashi na nan kamar dai sanin da akai mashi a baya,sai ma qarin wasu da baa rasa ba,wadanda zamu iya cewa sun sake samun gurbin zama ne sakamakon sauyi iri iri da rayuwa ta miqa shi,sai dai duk da haka zai yi wuya a kallo na farko zuwa na biyu da zakai mashi ka hango wata damuwa ko tawaya a tattare da shi,qila hakan nada nasaba da qwarewarshi wajen ganin ya adana duk wasu rauni da ka iya bayyana gazawar shi a fannoni da yawa na rayuwarshi.

Lalurar dake damun shi tana damunshi kwarai,sai dai ita kanta lalurar koma baya ce ga babban raunin da zuciyar shi ta dade tana jinya,lalura ce da har gobe ,jibi ko gata bayajin zai samu waraka daga ita,duk da wani bangare na zuciyar tashi na cigaba da haqiqancewa akan cewa yau ko gobe din Allah zai dubeshi ya amshi addu’o’in da bai taba gajiya ba wajen neman alfarmar Allah ya amsa daga gareshi ya sake hada fuskar shi da rayuka biyun da a kullum zuciyarshi na bugawa ne da tunanin su,yanaji ko ba dade ko ba jima zasu sake haduwa,yanaji a jikin shi Allah zai ara mashi damar gyara kurakuranshi da ya aikata masu,sosai yakeji a jikin shi cewa ba shakka Allah na sane da kukanshi a kullum,kuma zai amsa daga gareshi.

Isowarshi gidan nasu ya sanya shi yin horn,cikin en qananan daqiqa maigadin dake da haqqin kula da shige da fice ya wangale mashi get din,shikuma ya cusa hancin motar cikin gidan,bayan yasama mata matsagunni ne a gurin da aka tanada don aje motoci ne ya ankare da motar Fadwa,mamaki yake me ya akwota gidan nasu,don bai tuna lokacin da sukai da ita zata zo ba,hasalima a iya sanin shi yau kusan kwana tara kenan gaisuwa ta fatar baki kadai ke hadasu,haka zalika yana da tabbacin ba shakka da safe kafin yafita yabarta a cikin gidan,don har haduwa sunyi lokacin d ayake shirin barin gidan domin tafiya gurin aiki,kuma bayajin sunyi wata magana da ta danganci zuwan nata gidan su,kawai girgiza kai yayi ya dauki hanyar shiga cikin gidan.

Ba kowa a main falon gidan,zamu iya cewa kusan ko yaushe haka gidan nasu yake shiru babu wani motsin kirki,in ba matan gidan sunzo yini ba da yayansu shine fa zaka samu gidan yazama lively,harma hakan yataimaka wajen dawo da nishadin Mammyn ta su,sabida a kusan ko da yaushe zamu iya cewa cikin quncin zuciya ta ke da tunani iri iri,ba komai ya jawo hakan ba kuwa sai wannan lalura ta rashin haihuwa da ta samu dan nata kwaya daya tal da a da take mafarkin diyoyinshi za su cika mata gida da bari bari,domin dai ita kanta tasan cewa jikokin nata na bangaren diyoyinta mata ba nata bane kai tsaye,maana bata da qarfin da zatai iko ko tutiya da su kai tsaye,dama dai daga bangaren Mukhtar dinne take da wannan qarfin ikon,toh ashe mafarkin nata ba mai zama gaske bane ba,zamu iya cewa ko shi mai dauke da lalurar yafita dauriya da rungumar qaddarar da Allahn ya dora mashi,sau tari ma shi dinne mai tausar ta a kusan ko wani lokaci da zaizo ya sameta cikin wannan quncin.

Kai tsaye bedroom din Mammyn ya nufa,kasantuwar ba dadewa zaiyi ba yasanya shi binta can makwancin nata,yasan ma dai still dayan biyu baa rasa Fadwan a can din,tun da sawun shi ke qara kusanta shi da dakin baccin yakejin er shessheqar kuka,haka kuma yakasa fahimtar wa ke kukan ko ma a ce me ya kawo abun kuka a gidan,a iya abinda zai iya tunawa kowa lafiya yake a gidan,kama daga Mammyn har Fareeda,tunda dama dai su biyu ne ke rayuwa a gidan,sai ko in sunyi baqi a wasu lokuta na yau da kullum.

STORY CONTINUES BELOW

Bude qofar dakin yayi dai dai da jiyo abinda ya sanya shi idasawa ba tare da shi kanshi ya san yayi ba,idanuwanshi a qanqance,haka kuma ba wai mamakin hakan yake ba daga wacce ke maganar,abu guda ne ya sanyashi mamaki ganin yanda Fadwan ta tasa mashi uwa tana gaggasa mata magana kanta tsaye babu wani daar ko alamun jin rashin kyautatawa,hasalima bayyanuwar shi a dakin bai sanya ta sarara daga maganganun da take ba marasa dadin ji,ai d ayana dauka Mammy itace mutum ta qarshe da Fadwan ka iya yi wa fitsara,duba da irin qwarya qwaryar gudummuwa da kuma rawar gani da Mammyn ta taka wajen ganin ta cika wa Fadwan burin ta na mallakarshi a shekarun na baya,a tunanin shi wannan kadai ya isa ya sanya Mammyn ta tsira daga ire iren haukar dake damunta.

“What is happening here?”

Ya ida maganar yayin da yake zuba idanuwanshi kan Fadwan da ke zaune a bakin gadon Mammyn tana kwararo zance hankalinta kwance,yayin da Mammyn ke gefe kan lallausar daddumar da antanade ta ne dama don hutawa,duba da tim tim da suke zube a kan carpet din mai dan girma domin sakaya kai,kai tsaye kusa da Mammyn ya qarasa ya zauna,lokaci guda yana qoqarin fahimtar abinda ya sanyata kuka,duk da dai dama a kwanakin nan ta fara qulla abota da kuka,ganin yanda al’amura ke a sake jagule mata ba yadda ta so ba,kuma ta gaza yarda da canjin da rauyuwar ta zo mata da ita,ita dai burin ta ko ma ta halin qaqane Mukhtar ya haihu.

Fyace majina Mammyn tayi cikin tissue din dake hannunta,lokaci guda hawayen idanunta na cigaba da shatatar hawaye kana tacigaba da cigaba da maganar da ta keyi da Fadwan tace,

“Fadwa sau nawa kike so in baki hakuri ne?nasan kinfini gaskia ta wani fannin amma dai still me zai hana bazaki qara hakuri ba uhmm Fadwa?kinfi kowa sanin baa zaune nake ba kullum cikin neman maganin nan muke,saboda Allah meaysa bazaki qara haquri ba har Allah yakawo mana qarshen abun nan?besides inkika ce zaki bar Mukhtar Fadwa ta ina kike tsammanin wasu zasu yarda su bashi aure bayan sanin lalurar d ayake dauke da ita?kiyi hakuri mana don Allah”

Ko rufe baki Mammyn batai ba ta amshe,murya cike da tsiwa tace,

“Gaskia Mammy sai yanzu nake qara tabbatar da selfishness dinki,just look at abinda kike cewa Mammy,incigaba da zaman da bani da tabbacin ranar sauyawar lamura har mai afkuwa ta afku ko?saboda Allah meyasa Mammy kike da son kanki ne?saboda Allah idan diyarki ce a halin da nake ciki zaki yarda ne?nafi dan dakon tasha sanin ba zaki taba lamuntar hakan ba,sai ni don kin rainani kice incigaba da zama da mutumin da dashi da babu daya suke don son zuciya irin taki,toh wlh angama wannan iskancin da ni.”

Ta ida maganar tana murguda baki,ko dama can da biyu take wannan rashin kunyar,qwarai d agaske so take ta tunzura ta ko wane hali ne,sanin halin nashi d atayi yasa ta qara zage dantse wajen ganin ta kauda duk wani abu da ka iya sawa taji kunyar Mammyn ta riqa kwararo fitsara son ranta,a ganinta hakanne hanya daya d ata rage mata da zaisa ta samu ‘yancin ta a gurin Mukhtar Gaya,taga dai itama mutum ce kamar kowa,na menene da da uwa zasu nemi zauta ta akan abinda take ganin kamar ba adalci bane a gareta.

Har alokacin fuskar shi bata nuna jin haushin abinda take yi wa mahaifiyar ta shi ba,hasalima sai bai tankata ba,yai qoqarin adana bacin ranshi wajen ganin ya lallashi Mammyn daga irin hawayen dake ta kwarara daga idanunta,lokaci guda kuma tana mamakin yanda a en watannin nan gaba daya Fadwan ta canza daga Fadwan da ta sani mai yi mata  biyayya daidai gwargwado,duk da sanin cewar Fadwan dama can dai ba wai kanwar lasa bace ba,sai kuma ta juya murya cike d arauni tacewa Mukhtar din,

“Mukhy kanajin me Fadwa ke cewa?shin baka nuna mata girma da muhimmancin aure ne?Don Allah ka riqa nuna mata muhimmancin daraja aure,tell her komi na rayuwar nan dan haquri ne,kuma ma ai naga komi lokaci ne,cuta ai ba mutuwa bace ba,zaka warke,besides an tabbatar mani da cewa ma duk hakan yakusa zama tarihi nan ba da jimawa ba,please ka cigaba da lallabata Mukhtar,banaso asirin ka yatonu.”

STORY CONTINUES BELOW

Zuwa wannan lokacin Fadwan ta miqe sabe da mayafinta da jakarta a hannu,cikin yanayi na kallon banza ta dubi d’a da uwar ta mele baki gaba tace,

“Lallai Mammy yau naqara tabbatar da rashin imaninki,watau ni ga er iska incigaba da zaman jiran gawon shanu ko?sabida hadisi ne ko aya ce da tace dole sai ni zan zauna da nakasasshen danki?wai ni don Allah Mammy meyasa baku da imani ne wai?ko da yake kika iya raba shi da d’an da shi kadai ya taba mallaka a dunia ba tare da kinji d’ar ba ma,ai inajin by now yakamata selfishness dinki ya dena bani mamaki,toh bari kiji Mammy ko kisa danki ya sahale mani wannan qadararren auren ko kuwa ni da ke a garin nan shege ka fasa,ko banza dai ai inajin danki ne ya zabi ai hakan,tunda d ayana ganin qimarki da darajar ki da tuni yai maganin abun.”

Ta ida maganar tana juya idanu gami da watsawa Mukhatat din kwandunan harara kamar idanunta sa fado qasa,ita kuwa Mammy ai zuwa yanzu ba baka sai kunne,an sake soso mata inda yake mata qaiqai,har yanzu tambayar kanta take meya kaita aikata abinda ta aikata din har Ni’imah ta samu ikon guduwa da tilon dan da ita kanta sai dai taqi Allah amma jikinta na bata shi dinne kadai jinin Mukhtar din da zata gani a ban qasa,ba tun yauba take danasanin bacewar tasu,mussaman a en watannin nan da al’amura ke sake cunkushewa,ha rayuwar sai gudu take ba tare da bata tabbacin zata ga diyoyin Mukhtar din ba.

Sake bude baki tayi domin cigaba da baiwa Fadwar baki amma Mukhtar din ya dakatar d ahakan ta hanyar rufe mata baki,kana ba tare da ya dauke idanuwanshi da suke matuqr qoqarin danne bacin ran d ayake ciki ba yace wa Mammyn,

“Mammy please ya isa haka ku dena magana,kunsan condition dinku ba isashshiyar lafiya gareku ba,one thing that i want to assure you is that,zaman Fadwa a gidana tamkar zaman gidan kaso ne da yazame wa mai laifi dole,ba zata iya gujewa hakan ba tunda ita d akanta ta aikata abinda ya miqota duniyata,ai inajin bai kyautatu ba in saba alqawarin da na daukar maku na zama da ita har iya zuwa lokacin da Allah ya ara mana rayuwa,Mammy kinsani fiye da kowa,i am a man of my words!!!”

“Ahayyeh!”

Duk suka juyo suna kallonta,Mammy na binta da kallon tsantsar mamaki yayin da Mukhtar ke binta da kallon wata aba da bata da daraja ko qima a gurin shi,duk kuwa da amsa matsayin da ba kowacce mace ke amsawa ba a rayuwar shi,matsayin mata.

“Ni kuma a yau ba sai gobe ba zan tabbatar maka da sunana Fadwa Hisham Mommadou  Agadez!”

Ta juya ta fuskamci Mammy,lokaci guda tana sake dauke sassaucin fuskarta,kana tace,

“Idan har kin amsa sunanki Hajia Khaltume,inaso yau ba sai gobe ba ki sanya danki ya sakeni,naga dai da ni nace inayi,toh yanzu nace banyi,haba ko ana dolene?”

“Fadwa ni kike kallo kika fada wa baqaqen maganganu irin wadannan?ai inajin ban cancanci qasqanci irin wannan daga gareki ba?ko banza nai maki halarcin da duk dunia ba wanda yataba yi maki irin shi”

“Indai wannan kike kira halacci toh Allah wadaran shi,halacci ko masifa,halarcin da bai tsinana man komi ba sai bacin rai,toh ni this is not what i signed for,ehe nima inason inga jinina,saboda ayiman abinda nake so a samu zaman lafiya.”

Ta ida maganar tana juya kai gefe,itafa a shirye take da uban kowa,duk abinda zai faru yadade bai faru ba indai akan neman ‘yancin ta ne,yawwah.

“Mukhtar duk da banason fadin abinda zanfada din a yanzu,amma zanso kayiwa Fadwa abinda take so tun kafin munin al’amarin yafi haka,kana dai ji yau da kunnenka irin tijarar da wannan butulun yarinyar ke man,ba shakka yau na shaida cewar en bororoji ba abun yarda bane ba,dangin tsiya dangin mayu,dama inbanda qaddara Fadwa me zai kai mu hada jini da irinki?”

“Eh koma zakice Mammy yau kindade baki fadeshi ba,besides ni ba er qabilar baroroji bace ba,sau nawa zanfada maki ni er qabilar Tuareg ce?Ko a jikina inzaki kwana dubu kina aibata bororoji,wannan ba matsalata ba ce,nidai abinda nasani shine kisa danki yabani takaddata,abinda nasani kenan.”

STORY CONTINUES BELOW

Miqewa Mukhtar din yayi kana ya dubeta ido cikin ido,har a lokacin facial impression dinshi is hidden,amma duk d ahaka ba zaka fasa karanto tsanar Fadwan ba a cikin idanuwan shi,qwarai ya daure wajen adana duk bacin ranshi  da har bai daidata bakin rashin kunya ba,duk fishin shi ko hannu baitaba tsira wa mace ba,ballantana akai ga batun bugu,daace kam baida wannan self control din ya tabbata da yau Fadwan sai dai ta tashi ta tsinceta a asibiti ana bata taimakon gaggawa.

“Saki kike so ko Fadwa?”

“Kwarai shakka babu!”

Ta bashi amsa kanta tsaye.

“Toh kije ai kinsan hanyar inda ake badawa,kije a amsar maki.”

Daga haka ya nuna mata qofa.

“Now get out,and don’t even think of stepping your leg in my house,kitafi gidan ku.”

Zuqunnawa tayi tana kurma ihu.

“Wallahi babu inda zani sai ka bani takaddata Mukhtar.”

Bai sake bi ta kanta ba ya juya gurin Mammy bayan yayi mata kallon nasan me nakeyi,kana yace mata,

“Mammy ki shirya jibi zamuje Katsinan kan maganar da mukayi last week,dazu Kabeer din ke sanar dani likitan yadawo qasar jiya,kuma ya riga yai mana booking appointment da shi,so jibi in sha Allahu zam tafi,abu na gaba kuma Mammy ina hadaku da Allah karki bari kalamen wannan matar su zauna maki a rai,da sannu zanyi wa tufka hanci.”

Daga haka ya juya gami da fizgo Fadwan gaba daya yai waje da ita tana zunduma ihu bai tsaya ko ina ba sai bakin gate din gidan,sai d aya tabbatar da ya ajetaa waje,kana ya juyo ba tare da damuwa da haukar Fadwan ba,a ranshi kuma yadena mamakin abinda yasa Fadwan bata ci exams din medical school ba,qarshema dropping out tayi tace bata yin karatun lokacin giyar soyayyar Mukhtar din na walagigi da ita,hakan ya sake tabbatar mashi da qaramar qwaqwalwa ke gareta,sam bata da hankali.

Bayan ya shiga gidan ne ya tabbatar da yaiwa maigadi kashedin sake barin wata mai kama da Fadwan da shigowa gidan,kana ya wuce ida yai parking din motarshi ya shiga yai mata key maigadi ya wangale mashi get ya fice,can ya hangota tsaye ta tare inda zai wuce,ba don tsoron Allah ba bi ta kanta zeyi ya wuce,qila hakan yarage mashi radadin haushinta d ayake ji,amma sai ya tsaya yana danna mata harara,da sauri ta zagayo tana ambaton ina motarta yabarta ta dauko motarta,sai yanzunma yatuna a she be amshe keys din motar ba,hakan yasa shi fitowa daga motar ya miqa mata hannu

“Bani keys din mota ta.”

Baya tayi tana mazurai,ina zata bari yarabata da motar nan,ita akdai ce abinda zatai tutiya da ita,tunda ta tabbata tunda yace kar yaga qafarta a gidanshi tasan illar qin bin maganar shi.

“Bani keys dina tun kafin ranki ya baci.”

Wannan karon da sauri ta juya domin barin unguwan,ai gara daga baya ta dawo ta dauki motar,amma wlh ba zata bashi keys din ba,ai da sunanta ya sai motar,bai bi ta kanta ba yakoma cikin tashi motar yai mata key ya wuce ta,yana da tabbacin in hauka take taqama da ita,bala maigadi yadameta ya shanye.

***

Katsina,Nigeria.

1:44 pm

Hankalin shi rabi na kanta rabi na kan tuqin da yake,haka suke a kullum duk da irin fadan da take akan illar hakan,amma sai dai yai murmushi yace kinsan tun yaushe nake juya sitiyarin mota kuwa?tun ban wuce 15 years ba,kinga kenan shekaru kusan ashirin baya,so you are safe with my in sha Allah baby mamaa.

Yauma kamar kullum tafe suke zaije ya ajeta a asibiti,wannan din normal routine ne indai yana gari,shi zaije ya kaita kuma ya daukota regardless of shift din da take,haka shima regardless of wani abu da yake,yana matuqar qoqarin ganin ya inganta tarayyar su ta hanyar kyautata mata,even the smallest of things matters to him indai yadangance ta,haka itama ta bangarenta,soyayyar su qwarai mai burgewa ve da tarin tsafta,inka debe wancan qalubalen da ya ke taka rawa wajen son daqile burin su toh kam babu wasu tangarda a tafiyar ta su.

Isowarsu cikin asibitin yayi daidai da shigowar kira akan wayar shi,hakan yasa ya gyara packing gami da daukar wayar a lokaci guda,wayar bata dibesu wani dogon zango ba,aje wayar yayi daidai da kasheta da murmushin da ya zame mashi jiki inhar zai daga ido ya dubeta,tana sanya mashi wata iriyar nutsuwa,nutsuwar da daga kallonta kawai yake samunta.

“Ni da MG ne,yanzu yake sanar dani jibin suna tafe in sha Allah shi da Hajiyar shi.”

“Allah sarki Allah yakawo su lafiya.”

Itama tabashi amsa tana murmushi,lokaci guda kuma tana kimtsa jakar hannunta,a ranta kuma duk taji ta qosa ta hafu da wannan MG da Kabeer din ke zuzuta kirkinshi,duk da dai ta tabbata lallai mai kirkin ne,don Kabeer din baka taba samun shi yana mu’amala da mutanen banza,duk da kasantuwar cewa dama can shi ba mutum bane mai tara abokai,zata iya cewa abokan shi biyu ta sani qwarara,daga Dr Nurayn da dama shi ba a nan katsinan yake zama ba,sakamakon aiki da ya wullashi can birnin tarayyah sai kuwa Moh Kaita,shima dai din likita ne,yana zaune a garin katsinan da matarshi da diyoyin shi biyu,ta taba tambayar shi yanda aminan nashi biyu suka kasance likitoci yayin da shi kuma yake chattered accountant,ta kan tuna a lokacin dariya yayi,amsar shi kuma a gareta itace,duk da abokantaka da aminta dake tsakaninmu kowa path dinshi dabbane,asalima ni ba accounting naso karanta ba,tun ina qarami nake da shaawar zama matuqin jirgin sama,sai kuma hakan yai akasi da abinda ubangiji ya nufe ni da zama,so here we are after na rungumi accounting din da fatan yazame mani mafi alheri a gareni,and Alhamdulillah it was never a bad option after all. Kwarai it wasn’t a bad choice,because zata iya rantsewa kudin da yake earning him as chattered accountant in bai doke na likitocin ba toh kuwa zasui kunnen doki,kowa yasan yanda duk wani mai aiki da FIRS(federal inland revenue service) ke daukar salary mai tsoka.

“What time zaki tashi?nasan ki da nawa.”

“Kai Daddy.”

Ta fada cikin yanayin muryarta mai kama da shagwaba.

“Qarya nayi?ai kinsan dai shirirtarki duk fadin garin nan,inbakizo ta daya ba zaki zo ta biyu that i have no doubt.”

Tana dariya take bashi amsa.

“Toh nidai Allahumma yahdeeniii kawai.”

“Khalas!you needed it kam.”

Ta qarasa kyalkyalewa da dariya don tasan dama amsarshi kenan a duk lokacin da zatai wa kanta adduar shiriyar,bayan ta fita daga motar ne ta leqo kanta ta windown motar bayan ya sauke glass tace,

“Daddy don Allah yau muyi chatting,ni gaskia kowa na chatting da saurayin shi banda ni.”

Harararta yayi bayan ya tada motar,kana cikin sigar tsokana yace,

“Kice dai yau so kike kiman kiss.”

Wannan karon kwantowa tayi bayan ta zuro kanta sosai cikin motar tace tana qara sautin dariyarta kadan tace,

“Laifine don mata taiwa mijinta kiss?”

“Karki bari infito daga motar nan Ni’imah,zaki ba masu garinku labari.”

Janye kanta tayi gami da yin baya tana idasa dariyar maganar da yayi,wai don kawai tana tura mashi da emojis din kiss shikenan yataso ta gaba,wai kiss take so,shikuma bayason na en aljanun nan,nagaske yake so,don haka karta kuma tara mashi na qarya.

“I will see you later beautiful.”

Ta tsinkayo muryarshi bayan yayo ribas domin ficewa daga asibitin,ita dinma bye bye tayi mashi tanajin zuciya da gangar jikinta na kewarshi already,a hankali kuma bayan taga bacewar motar ta shi ta juya ta nufi cikin asibitin zuciyarta cike fal da soyayyar Kabeer Sambo Kaita.17

***

About AIS

Check Also

HOD’IJAM CHAPTER 6 BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 6 BY NOORIEEYAH                    Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *