HEEDAYA CHAPTER 17 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 17 BY By Khaleesat Haiydar

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mumy ta mike da sauri ganin Karime ta dawo tace “Ya, har kin xuba?” Karime tace “Korata tayi wllh, har cewa tayi 

xata sa a sallameni” Mumy ta xaro ido tace “Me kika mata????” Karime tace “Ban mata komai ba wllh, haka nn 

kinsan dama bata sona” Mumy tace “Toh baki bata hkuri ba kika fita ke kuma?” Karime tace “Cewa tayi bata son 

ganina” Mumy ta xauna tayi tagumi tana tunanin to ynxu ya xa ayi ta samu ta juye maganin nan cikin kayan shayin 

Heedayah, ta kalli Karime tace “Ba ni kayana ki fita” Karime ta fiddo kullin cikin rigarta, kin amsa Mumy tayi tace 

“Ajiye min kan kujera” ta ajiye, Mumy tace “Je ki sae na neme ki” fita tayi parlon Mumy ta bi ta da wani kallo, leda 

ta dauko ta rufe maganin da shi tana yatsina fuska sannan ta dauka ta wuce daki. A ranan Mumy ta shiga dakin kaka 

yyi sau biyar kafin yamma, fitarta na karshe kaka tayi mitsi mitsi da ido tace “Da kyar idan matan nan tana da 

gaskiya, na lura tun safe take min xarya kmr me nakuda…. Ni dai bari Amadu ya dawo in ji dalili gaskiya, Allah na 

tuba duniyar nan yanxu ko wanda ku ka fito ciki daya kaga yana maka xarya bbu dalili toh kayi ta kanka kawai” 

Heedayah dai na dakin tana jin abinda kaka ke cewa, Kaka ta mike ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri 

tace “Gani kaka” Kaka tace “Kasko xa ki dauka kije duk inda xaki samo gawayi ki hura min garwashi ki kawo min 

yanxun nan” Sajida tace “Toh sai dai inje kasuwa yanxu a siya gawayin” Kaka tace “Toh ni dai bani da ko sisi, tafi ki 

kira min Maryam” Sajida tace “Toh” sannan ta wuce, ba a dau lkci ba sai ga Mumy tana murmushi tace “Gani kaka, 

aiki xa a maki” Da sauri kaka tace “A’a, aikin me kuma kamar kuturwa, dari biyar xa ki ba Sajida xata je min 

kasuwa ynxu” Mumy ta d’an juya lkci daya ta daure fuska, sai kuma tace “Anya xa a samu kuwa, da yake jiya da 

naje can gida na kai Salima asibiti to bbu kudi wajena ynxu” Kaka tace “Toh kira min Amadu, shi baxai rasa yanda 

xai yi da ni ba ai” Mumy dai bata ce komai ba, Kaka tace “Ki kira min shi da wayarsa” Barin dakin Mumy tayi 

murya can ciki tace “Toh” tana tsaye daga bakin kofarta ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri, Mumy ta 

jefa mata dari biyar din fuska a murtuke ta shige parlonta ta kulle kofa… Sajida na dawowa da gawayin ta rura ma 

kaka a Kasko, sannan ta kai mata dakinta, kaka na xaune tsakar dakin ta baje kayan wani tsohon jakarta, kullin 

magunguna ne iri iri kai kace boka ce, Sajida ta ajiye kaskon saman tiles tace “Gashi kaka” Kaka tace “Allah maki 

albarka….” Tace “Ameen” sannan ta fita, kaka ta xuba uban turaren icce a wutan, Tuni Heedayah ta mike ta fara tari 

tace “Kaka meye shi?” Kaka tace “Toh haka kawai aka ce maki xan xauna a kashe ni, jiya fa wani mummunan 

mafarki nayi…” Heedayah xata fita dakin kaka ta rufe kofar tace “Toh ko dai ke mayya ce ba mu da labari…” 

Heedayah ta fashe da kuka tace “Kaka yana shiga hancina” kaka tace “Ai dama ta nan din xai shiga, Ina xa mu tsaya 

a cuce mu, kowa fa ya lalace da mugun abu a xuciyarsa, tun ina gidan mijina nake tsare kai na, Rakiya ma idan ta 

dawo daga gantalin aikinta sai ta xo in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne fa…” Heedayah ta toshe hancinta, 

Kaka na ta surutunta tana kara cika iccen cikin wutan kaskon, sai da ta tabbatar ya ratsa ko ina na dakinta sannan ta 

fitar da shi parlor ta ajiye tace “Toh dama kada wanda ya dauke min kayana a nan” Mami ce ta bude kofar da 

sallama, tana shigowa ta fara yatsine fuska don hayaki ya cika ko ina, Ta karaso gun kaka tace “Meye wnn din kaka” 

Kaka tace “Ke ma idan xa ki samo leda in debar maki ki samo, duniyar ynxu ba gaskiya, Maryam ma idan ta ga tana 

so ta samo leda in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne” Mami ta gaida kaka xata wuce kaka tace “Yauwa 

Rakiya dama Ina jiran ki dawo ki gaya min me wnn me aikin taki take tsinana maki a gidan nan” Mami ta juyo tace 

“Aa ba komai kawai dai suna aikin gidan ne tare da dayar mai aikin” Kaka tace “Toh a gaskiya ki sallameta Sajida 

kawai ta ishe mu a gidan nan, baki ga ba kullum fa naso take, kazama ce fa da kyar idan ruwa na ta6a jikinta haka 

kawai wata cuta taje ta kama mu ta dalilinta bayan mu duk muna wanka muna tsafta” Mami tayi murmushi tace 

“Naga kamar aikin ya ma Sajidar yawa ne” Kaka tace “Sai a samo wata me tsaftar amma a gaskiya a sallami wnn, 

idan ko ba haka ni a sallameni” Mami na kallonta tace “Ta maki wani laifin ne kaka?” Kaka tace “Aa ko daya kawai

na gaji da kazantar ta ne” Mami bata kuma cewa komai ba ta juya ta nufi bangarenta… Da daddare Abba na parlonsa 

sai ga kaka ta shigo da sallama, Mumy da ke yanka masa watermelon tace “Sannu kaka” Kaka ta xauna tace “Yauwa, 

Amadu ashe ka dawo” Yace “Ehh na dawo, Ina yini” tace “Dama xuwa nayi naji wa ke biyan kudin aikin matar da 

Rakiya ta dauka” Yace “Aa ita ke biya” Kaka tace “Au haba, to bari in bar mata mai aikinta kar ta kullaceni, wai da 

cewa xan yi a sallameta” Abba yace “Tayi wani abu ne?” Kaka tace “Oh oh kawai dai ni bata kwanta min bane ga 

kazanta malam, amma tunda ba kai ke biya ba ai shikenan, ae Rakiyar ma me kudin kanta ce, ba xaman banxa take 

ba kamar wasu, baka ga gidan wan tsohon mijinta ba da Junaidu ya kai ni shekaranjiya, Kai kace wani shugaban 

kasa ne” Mumy dai ko kallon kaka bata yi ba sai sauri take ta bar parlon, ko yankan kirki bata ma kankanan ba ta 

mike tace “Xan je in duba ruwan shayin da na sa a kitchen” daga haka ta fita, kaka ta kalli kankanan tace “Dubi wani 

yanka da tayi ma kankanan kamar bakatafiya…” Shi dai Abba bai ce komai ba, kaka tace “Toh ni dai na hada kayana 

tun ranan da ka min xancen tafiya gyaran idon Deedayah a india” Abba yace “Mutane biyu kacal xa su je tare da ita 

fa Baaba” Kaka tana kallonsa da kyau ta gyara xama tace “Ban gane mutane biyu ba, su wa da su wa kenan mutane 

biyun?” Yace “Aa ba ni nace ba, ka’idar wajen ne haka, Doctor ne ma ke gaya min” Kaka tace “Toh ba sai ni da kai 

mu kai ta din ba, ko akwai wani wanda ta hada wani abu da shi banda ni da kai din” Abba yyi shiru yana kallonta, 

kaka tace “Toh dama ai ni da kai ne dolenta, ita Rakiya yaushe ta xo gidan ko yaushe ta san Deedayar da xa ayi 

marmarin tafiya da ita?” Shi dai Abba bai ce komai ba…. Mumy na fita sai da ta fara wucewa bangarenta snn ta fito 

da sauri, ta dinga bin main parlon da kallo kamar munafuka sannan ta shige dakin kaka ta kulle, hannunta na rawa ta 

isa gun kayan shayin ta sauke gwangwanin madaran amma ta rasa da me xata bude na milon, kan Fridge ta hango 

cokali cikin cup, ta tashi da sauri ta dauko ta bude gwangwanin ta ciro ledan dake rigarta, hannunta na rawa ta bude 

kyallen ta juye bakin content din cikin gwangwanin ta gauraya da cokalin snn ta rufe gwangwanin ta mayar Inda 

yake ta tashi, ta goge cokalin da xaninta shi ma ta mayar cikin cup din, gaba daya a rikice take, ta fice daga dakin 

kamar xata tashi sama, sai da ta shiga parlonta ta sauke wani ajiyar xuciya ta juyo tana kallon yaranta tace “Uban me 

ku ke jira ba ku tafi kun kwanta ba? Maxa a kashe min tv tunda bance ku lalata na dakinku ba” Sai da suka fita 

parlon snn ta wuce cikin dakinta tana wani murmushi…. Washegari da sassafe kaka na share sharen lungu da sako na 

dakinta ta dauke gwangwanin madara da Milo ta tabe baki tace “Mayyar ma bata sha shayin jiya da daddare ba, 

dama fa gulma ce, a gidan uwarta da ubanta ina xata samu haka, ita dai kawai ta samu d’ana sai kashe mata kudi 

yake a banxa a hofi, sbda ita abubuwa da yawa an daina min, tasa sai maneji muke yi, ga uban kudi xa aje a gyara 

kaddararrun idonta nan da kwanaki kadan, mu dai kawai Allah ya bamu lada, bafa dangin iya balle na baba” Tana 

ajiye gwangwanin milon taga murfin ya fadi, ta dau murfin tana kallo da mamaki, can ta ajiye tace “Ikon Allah, ni fa 

na hada mata shayin jiya da yamma, to wani barawo ne ya xo ya bude ya sata ya manta bai rufe ba, gashi har Milon 

yyi kasa, ni dai ba haka na bar sa ba wllh, sata aka fara yi gidan amadun bani da labari??” Ajiye tsintsiyar tayi ta fice 

daga dakin, direct parlon Abba ta nufa ta kwankwasa kofa, Mumy ce ta fito, kaka tace “Amadun fa?” Mumy tace 

“Yana ciki” Kaka tace “Ce masa gani a tsaye” Abba na fitowa kaka tace “Amadu wllh shigar min daki aka yi aka 

yashe milon Deedayah tass, ynxu ba sai ace ni ke shanyewa ba ko da ba a fito fili an gaya min ba ayi ta xagina a 

xuciya, toh gaskiya ni dai a san matakin da xa a dauka ynxun nan” Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace “Ikon 

Allah, toh bari in debo na wajena sai a kara mata a kai tunda yyi kasa, ba abun tada hankali bane kaka” Kaka tace

“Oh oh ba wani debo naki da xa kiyi, ko ma waye ya diba sai ya maido wllh, xan fara ta kan masu aikin nan tass sai 

na bincike kayansu don nasan ba shan lkci daya xa ayi ma milon ba deba xa ayi a leda a boye, Kai har kayan 

Deedayar ma sai an bincika da nasu Rabi’ah” tana fadin haka ta nufi dakin masu aiki tana kwala ma Mami kira ita 

ma ta fito, kayan Sajida ta fara dubawa ta xaxxage gaba daya Ghana must go din bata ga komai ba, Kaka ta kalli 

Karime dake ta xufa tace “Ke ina jakarki” Karime ta nuna mata ghana must go din, ba komai ya sa hankalinta ya 

tashi ba sai kullin Madara da millo na Mumy da take diba a leda idan Mumy tace taje ta hada shayi, har na Mami ma 

tana diba, snn ga kullin soyayyen nama na jiya da ta boye a kayan, ga kuma Cornflakes a leda shima duk ta boye, 

kaka ta yatsina fuska tana xaro kayan kamar Kashi tana ajiyewa kasa, da ledan naman ta fara cin karo, ta kunce 

ledan ta saki salati ta yar a kasa tana kallon naman, Mumy ma xaro ido tayi tana kallon naman, Kaka ta ci gaba da 

xaro kayan sai ga ledan cornflakes, Kaka ta kara gwalo ido ta ajiye Cornflakes din, ta ci gaba da xaro kayan sai ga 

ledan milo sannan Madara, kaka tayi wani dariya irin na boss, Mami ma na tsaye bakin kofa ta kasa cewa komai, 

Kaka tace “In ji dai kun tabbatar cewar ba banxa nake ba ynxu, duk wanda Allah ya daukaka ya riga da ya daukaka 

sa, to a kira Amadu shi ma ya gane ma idonsa, nasan da naje na samesa nace gashi gashi a ransa cewa xai yi ohh 

Allah ya hadani da fitinanniyar uwa, to yau ga ranan fitinata, ni dai nasan shigar min aka yi aka debi milon nan 

dama” Karime ta durkusa tana matsar kwalla tace “Wllh wllh wllh kaka ba milon ki bane wnn, ki duba ki ga wnn har 

fa ya daskare….” Kaka ta kwala mata ledan milon da ya daskare a fuska tace “Ke dai bakya tsoron Allah, to kin saka 

sa cikin jaka duk wari ya baxai daskare ba?? Ai da kyau tunda ba tsutsa ya fitar ba, ni dai a kira min Amadu ya xabi 

ko ni ko kazamar nan, don in har xa a yafe mata ta ci gaba da xama a gidan nan gwara in tafi duk inda Allah yyi” 

Mami ta sauke ajiyar xuciya tace “Yau kwana nawa da biyanki kudin watan aikin ki?” Karime ta fashe da kuka tace 

“Sati daya” Mami tace “Toh ki hada kayanki, ki taho ki sameni in baki kudin aikinki na sati daya da kudin mota kiyi tafiyar ki, Allah ya bamu alkhairi” daga haka Mami ta fita dakin, Karime ta kara rushewa da wani matsanancin kuka 

ta daura hannu a ka tana kallon Mumy tace “Don girman Allah Hajiya ki taimakeni wllh aiki wahalan samu yake yi 

ynxu, ki saka baki a maganan nan don Allah a barni in ci gaba da aikina” Mumy ta ki kallon ko da Inda take, can ta 

juya kamar munafuka ta fita, kaka tayi wani shewa tace “Aje can wani gidan kuma ayi tayi masu naso ana wari 

amma ba gidan d’a na ba” daga haka ita ma ta fice daga dakin, Dubu goma Mami ta ba Karime kudin mota dubu 

biyar, dubu biyar kuma na aikin sati daya da tayi, sai kuka Karime take tana cewa “Don Allah Hajiya kiyi hakuri kar 

a koreni, wllh sharrin shaidan ne” Mami tace “Da ni ce kika debar ma abu na kamaki, sai dai in maki nasiha kuma in 

gargadeki da cewar kar ki kuma, amma kinga ya fi karfina ynxu, kinsan yanda tsofaffi suke lamarinsu, don haka kiyi 

hakuri ki tafi, Allah xai kawo maki wani hanyar” tana kuka sosai ta fita, Tsaye ta ga kaka da gwangwanin madara da 

milon a hannunta, tana ganin ta fito ta nufeta ta ajiye mata su tace “Ga nawa gudunmawar, a gaida mutan Doguwa” 

Mumy dake tsaye bakin kofarta ta shigo parlon da sauri kuma a rude tace “A’a kaka ya xa ayi haka? Ki bata tayi me 

dasu kuma???” Kaka ta katseta tace “Toh Ina ruwanki, so kike in ba Jikata gaibu ta sha, nasan barbadin da ya shiga 

ciki a yayin satar? Kazama ce fa bata wanka, to Deedayar xan ba ma sauran milon da ta jagwalgwala ta sha kamar 

uwata tace min je ki kya gani, kawai wani cutar ya kamata Amadu da Rakiya su kullaceni?? Aa wllh ta tafi da su tayi 

ta shan shayi a kauyen nasu” Karime sai kallon Mumy take tana hawaye, Mumy na rawar baki tace “Aa kaka idan ba 

xa a bata ba ni a bar min xan yi amfani da su wllh” kaka tace “Toh banyi niyya ba, ita dai barauniyar xan ba ta tafi da 

su, kinga dai ai baxata kullaceni sosai ba tunda na sallama mata sauran kayan shayin” kaka na fadin haka ta jawo 

katon Ghana must go din Karime ta xuge ta xuba gwangwanin biyu a ciki sannan ta rufe tana kakkabe hannu tace 

“Gudunmawata kenan, anjima kuma sai a kira min Junaidu in sa ya siyo mata wani bbu ruwana da wahala” Karime 

ta dau Ghana must go din ta nufi kofa tana matsar kwalla, Kai kana ganin Mumy kasan duk a rude take don hakan 

ya fito kiri kiri a fuskarta, Mami kuwa sai kallonta take, Mumy ta koma part dinta da sauri ta dauko Hijab sai ga ta ta 

fito ta bi bayan Karime tana cewa “Mu je in raka ki ai baxa ayi rabuwar tsiya ba….” Hada idon da suka yi da Mami 

yasa tace “Au to ai ba sai na raka ki ba ma….” Sai kuma ta koma bangarenta da sauri, Mami ta bi bayan Karime da 

har ta fita, Karime ta juyo ganin Mami ta tsaya tace “Hajiya kiyi hankali da kishiyar nan taki, bata sonki bata son yar 

da kike riko, wnn milon da kaka ke batu a kai ita ce ta xuba abu a ciki don da farko ni ta ba in xuwa ban samu nayi 

hakan ba shine taje tayi da kanta amma ta mance bata rufe murfin ba….” Tana fadin haka ta ciro milon ta mika ma 

Mami tace “Gashi don tana iya biyoni tace xata amsa idan na bar gidan nan” amsa Mami tayi tana kallon milon, 

Karime ta nufi gate da sauri tana goge idonta, sai ga Mumy ta fito, Mami ta mayar da gwangwanin bayanta, Mumy 

tace “Lahh har ta wuce? Canji na fa na jiya da yamma na wajenta bata bani ba, har dubu uku fa….” tana fadin haka 

ta nufi gate kusan da gudu, Mami tayi wani murmushi ta juya ta koma ciki, parlonta ta shiga ta bude milon tana 

kallon content din, ta girgixa kai ta wuce bandaki nan ta xubar da gaba daya a Bathtub ta bude ruwa ta juya ta fita 

rike da gwangwanin. Mumy ce xaune dakin Sadiya sai rusa kuka take, Sadiya tayi tagumi ta kasa cewa komai, Can 

tace “Kai kema dai wllh sai kace dakikiya, toh garin yaya ma xaki bar murfin gwangwanin a bude, ke meyasa baki 

yin abu da hankali, ynxu da ace abun nan na backfiring fa? Sannan uwa uba ga kudin da aka kashe, Kai ni dai wllh 

idan abun nan bai bata min rai ba shegiya nake” Mumy na Shessheka tace “Wllh kakan nan mayya ce kawai ki 

yarda” Sadiya ta ta6e baki tace “Toh ita na Rakiyan fa?” Mumy na goge idonta tace “Aa dama cewa nayi bari in fara 

gamawa da na yarinyar tukun, gashi kuma komai ya tashi a aikin banxa” Sadiya tace “Toh Karimen ke kina tunanin 

a layin ta jefar da gwangwanin milon?” Mumy tace “Wllh kaf bbu flawan da ban duba ba a layin amma banga komai 

ba, rashin kunya fa sosai yarinyar ta min har tana neman dambe da ni a titi xata tara min jama’ah, har da kirana 

shaidaniya, toh ni kuwa ai bana biyeta ba sum sum sum na juyo, amma sai da na bincika jakar banga komai ba wllh 

sai gwangwanin madaran” Sadiya ta sauke ajiyar xuciya tace “Ikon Allah… Yanxu dai sai ki saka rana mu koma 

Zarian tunda haka Allah yyi da mu” Mumy ta marairaice tace “Toh amma ynxu ya xanyi da na wannan Rahinar, ni 

kinsan ba shiga bangarenta nake ba haka yarana, dama da kariman na nan ne nasan idan na bata xata yi ynda nace to 

gashi bbu ita ynxu” Sadiya tace “Toh aikuwa dole a san yanda xa ayi a shiga bangarenta kawai…” A hankali Mumy 

tace “Toh shkkn, Yau laraba ranan juma’ah sai mu koma Zarian” Sadiya tace “Toh Allah ya kai mu” Kaka na yanke 

ma Heedayah farce a dakinta sai mita take ita an maida ta boyi boyin yarinya duk wa enda suka tsintota darewa suke 

su barta da ita tayi ta wahala har dare, Heedayah dai sai turo baki take tana sauraronta, kaka tace “Toh bakya turo 

baki ba dama tunda gani naynny ki, ni kenan kullum a wahale inyi ta fama da maki bauta bakya gani balle ki gode 

min, bari Rakiyar ta dawo ayi ta takare yau, xanji amfanin aurota da Amadu yyi” Bude kofar parlon aka yi Salima ta 

shigo da sallama tana kas kas da cingam, kaka ta kalleta ta ci gaba da abinda take, Salima ta xauna tace “Ina yini 

kaka?” Kaka tace “Lafiya lau, ke dai har yau bbu matayi ko Salima? Toh Allah ya fiddo maki da na gari” Salima ta 

d’an harareta bata ce komai ba, kaka tace “Toh ai Ina jin Maryam din ma bata nan ta fice” Salima tace “Ehh na sani” 

Kaka tace “Ayyo, to tafiya xakiyi sai ta dawo ki dawo kenan?” Salima tace “Aa xan d’an kwana biyu a nan” kaka ta 

kalleta da sauri tace “Kwana biyu kuma? Toh… Allah dai ya ba Amadu ladan ciyarwa, amma ynxu ai abinci ya xama 

abinda ya xama a kasuwa, ynxu fa mun kusa mu ashirin a gidan nan” Mikewa Salima tayi tana taunar cingam dinta 

ta fita, kaka tace “Karuwanci dai a sarari ni ‘ya su” A hankali Heedayah tace “Kaka wacece?” Kaka tace “Kanwar Maryam uwa daya uba daya, ai bin otal take tana kwana, kinsan uwarta ta rasu haka ma ubanta to bata da wani 

mafadi ynxu sai makwabta, Maryam ita ma da ba don auren dake kanta ba xata yi fiye da haka ina tsammani, kinsan 

kafin Amadu ya aureta har xuwa Abuja take wai yawon bude ido a can ma suka hadu da Amadun….” Heedayah tace 

“Meye yawon bude ido” Kaka tace “Toh ke ina ruwanki da xancen manya kina ‘yar yarinya da ke” Heedayah ta turo 

baki Kaka ta ci gaba da yi mata yankar farcen tana cewa “Banda lalacewa ma ina ni ina hiran nan da ke” Bayan 

La’asar Salima na kwance parlor tana kallo aka bude kofa, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, ta mike xaune a 

hankali tana kallonsa, Tunda suka hada ido ya dauke kai, ta bi sa da kallo tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau, ya 

gida?” Tace “Alhmdllh, nima yau na xo” yace “Ohk” parlon kaka ya shiga, ko gama gaisawa basu yi da kaka ba sai 

ga Saliman ta shigo, ta d’an xauna gefen kujera tace “Kaka bbu abinda xa ayi maki?” Kaka tace “Ehh to wankin bayi 

ne, daxu ban yrda da wanki Sajida ba, kinsan na sa an Kori dayar me aikin, ta saci milon Deedayah ni ko na sa aka 

sallameta, shine aka kira min Junaidu yanxu ince masa ya tafi ya siyo mata wasu….” Salima tace “Toh bari a wanke” 

cire karamin mayafinta tayi ta ajiye nan kan kujera ta nannade skirt dinta har saman Gwiwa, duk fararen 

kafafuwanta a waje, shi dai Junaid tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, ta nufi cikin bathroom din, kaka tace “Ae 

Salima yar albarka ce, ga haxaka wajen aiki, da fa idan ta xo gidan nan har kwaleman dakina tana min, kwana biyu 

ne kawai ta guji gidan nan, kasan yayartata bata da hali tsangwamarta kawai take shi yasa bata son xuwa ma” Junaid 

ya kalli kaka yace “Wacece yayarta?” Kaka tace “Kishiyar uwarka mana Maryam” Junaid bai ce komai ba, 

Heedayah tace “Kaka ko xaki basa ya yanke min kina min da xafi” Kaka ta jefar da nail cutter din a jikinta tace 

“Algunguma sai kije yyi maki da sanyi, yarinya sai sharrin jaraba kawai” murmushi Junaid yyi ya dau nail cutter din 

yana kallon Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka, ya ja hancinta a hankali yace “Don’t Lolly….” kaka ta mike tana 

kakkabe jikinta tace “Ni idan ta bata min rai ma sai ince ma Amadu na fasa xuwa gyaran idon da ita sai in ga ta 

tsiya” Murmushi Shuraim yyi ya gyada kai yace “Toh Allah ya tsare” Kaka tace “Atoh yanxu kayi magana, Ameen dai….. 

Allah ya kai mu lafiya ya dawo da mu lfya kawai” Juyawa yyi ya fita dakin still smiling ya kulle kofar, Baffa dai na 

ta xaune bai iya yace komai ba, lkci lkci yake kallon wayarsa waiting for his son Sudais don kafin ya iso gidan sai 

da ya kirasa yace ya samesa gidan Abba, Kaka na kakkabe jakarta ta tabe tace “To su matan naka basu da niyyar 

xuwa yi min sallama ne Umaru?” Baffa yace “Dama ba wanda xai yi tafiya ake xuwa yi ma sallama ba Baaba, amma 

ai xa su xo sallaman” kaka da bata tsaya ta fahimci farkon maganansa ba tace “Toh kar ma su xo mana, xuwansu da 

rashin sa duk daya ai a wajena, meye hadina da su banda kai da ka auro su, matan da suka kusa kashe ni da kwai duk 

karni Allah yyi da sauran kwanana a gaba” Baffa na kallon Heedayah yace “Baaba meyasa ake bari tana baccin 

yamma haka?” Kaka ta daga hannu sama tace “Haka aka saban mata tun daga gun iyayenta wllh, sakakku ne iyayen 

nata duk sun sangartata sun lalatata, Banda haka katuwa kamar yarinyar nan ace tana tashi shan shayin dare, baka ga 

gwangwanayen kayan shayin da na tara ba xan ba ‘yan gwan gwan, wllh xa su siya dubu biyu ko uku kila, kana 

maganan baccin yamma ai ko xaka shekara kana tashinta magagi kawai xata yi ta maka, to ni baxan iya wahala ba 

shi yasa nake barin ta, kuma bana rabo da tofa mata addu’a ba don halinta ba” Baffa ya gyada kai yace “Hakan na da kyau ai” Bude kofar dakin aka yi Sudais ya shigo da sallama, Kaka tayi tagumi tana kallonsa tace “Ta janye 

tsinannen bakin da tayi maka na xuwa gidan nan kenan, Kai dai kam baka yi sa’ar uwa ba Sudess, yau kusan wata 

daya kenan rabona da kai fa” Sudais da idonsa ke kan Heedayah ya xauna ya cire face cap din kansa, Baffa ya fara 

gaidawa sannan ya kalli kaka yace “Ina yini kaka” tace “Lafiya lau Sudess muna ta shirye shirye ashe da rabon xa 

mu hadu, kai ma ka xo sallaman kenan?” Yace “Sallama da wa?” kaka tace “Ni mana, gashi har na gama hada 

kayana” Yace “Hada kaya xuwa Ina?” Ta ja tsaki tace “India mana, ko baka da labari ne? Au da yake uwarka ta 

hanaka xuwa gidan kilan shi yasa baka da labari, ae ni da Rakiya xa mu kai ta indiyan” Ya wara ido yace “Toh ai 

naga ba da ke xa aje bane Hajiya Kaka? ko wani ya bude baki yace maki har da ke ne a tafiyar kika hada uban kaya 

haka?” Kaka tayi shiru tana kallonsa bayan ta hadiye wani yawu da kyar, ya danne dariyar sa yana xare mata 

idanuwansa yace “Mami da Shuraim ko Junaid ne ai xa su yi tafiyan ai, ko mafarki kika yi xa a je da ke ne baki ba 

mu labari ba kika tsiri hada kaya” Kaka ta juya a hankali tana kallon Baffa dake danna waya, Sudais yace “To ba a 

ma barin tsofaffi su shiga asibitin, don su ma tsoffin kansu ai cutane….” Baffa ya jefa masa wani kallo, ba shiri yyi 

shiru trying hard not to laugh, kaka dai magana ya makale mata sai ‘yan idanuwa, Baffa yyi gyaran murya yace 

“Kina ji kaka, kece baki fahimci abun nan ba tun farko, kinga dole ana son a samu masu ilimi sosai su je tare da ita, 

sannan kin san ynda xaman asibiti yake kuma a gaskiya baxa ma su barki ki xauna ciki ba tunda kin manyanta, shine 

muka yanke shawara da Amadu cewar Hajiya Rahinah da Shuraim ko kuma Junaid su tafi can din tare da ita don shi 

Sudais baxai je ba yace, Kinga ai duk masu ilimi ne, komai xuwa xai yi da sauki tare da su, ke kuma daga baya ko 

kafin a sallame su ne sai a kai ki ki sauka hotel a dinga kai ki asibitin kullum kina dubata….” Kaka ta sauke ajiyar 

xuciya a hankali tace “Toh daga kai har Amadun da duk wanda ya kawo wannan shawaran ku je na bar ku da 

Allah….” Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta kwantar da kanta saman katon akwatinta, Baffa ya bude baki 

yana kallonta ya kasa cewa komai, Sudais duk irin yanda yake dakewa bai san lkcn da ya fashe da dariya ba har da 

kyakyatawa, Baffa ya juya fuska daure yana kallonsa, Mikewa yyi da sauri yana kokarin hadiye dariyar sa yace 

“Meye kuma abun barin jama’ah da Allah kaka?? Daga fadin gaskiya?” Cikin rawar murya ta dafe kirjinta tace “Ae 

sun cuce ni ne sun toxarta ni sun kunyata ni Sudess, yanxu da wani idon xan kalli duniya ince masu ba da ni xa aje 

ba? Dama ashe Deedayah na da wani me muhimmanci bayan ni a rayuwar nan bani da labari? Ashe dama Rakiya 

munafuka algunguma ce ita ma bani da labari?” Wani kukan ta kuma rushewa da kai kace yarinya ce, Sudais yace 

“Toh ai ba ace baxa ki je ba fa kaka, cewa aka yi su fara yin gaba daga baya sai ke da Abba ku bi su” Kaka ta dakatar 

da kukan da take yi ta daga hannu sama da sauri tace “Aa wllh na yafe suyi ta tafiya har bangon duniya idan da 

matsallaki su tsallake bangon duniyar ma bbu abinda ya sha ma Patuu kai, dama ai ban hada uban komai da shegiyar 

makauniyar ba karambani na ne” Mikewa Baffa yyi ya fita dakin gaba daya ransa a bace, Sudais na nunata yace “Ke 

dai kin fiye wahala da neman fitina, tsofe tsofe da ke ina kike son a kai ki? Jinyarki xa aje india ayi ko na 

Heedayah?” Kaka na nunasa ita ma tayi fici fici da ido tace “Wllh tllh idan ka bari na maka baki sai ya bi ka, uwarka 

ce tsohuwa ba ni ba, to sae me don su Umaru da Amadu sun munafurce ni? Ae dama munafukan ne tun suna yara, 

Ga dai gari da yawa maye ae baya ci kansa ba, dama yanxun nan xan bar gidan nan inga shegen da xai hanani in 

tsine masa bbu ruwana” Tana fadin haka ta mike ta fara neman gyalenta tana matsar kwalla, Sudais sai kyalkyala 

dariya yake yace “Sai ki fi ruwa gudu ai, mu ba mun huta da wahalar ki ba ma, dama duk kin addabemu kin dame 

mu” Kaka ta juya tana kallonsa ta nufesa ta cakumosa tana huci tace “Don kaza kazan ka nice wahalalliya??” Gwalo 

yyi mata ta kara rushewa da kuka ta sakesa ta xauna nan kasa tana rera kuka, suka yi ido hudu da Heedayah da 

hayaniyar kaka ya tasheta ta mike xaune tana bin ko ina da kallo, a mugun fusace kaka tace “Munafuka maxa sauko 

min saman gadon kar in jefar da ke” Turo baki Heedayah tayi xata sauka, Sudais ya karasa yana dariya ya kama 

hannunta ta sauka, kaka tace “Dama duk a xo a fitar min da kayanta daki na kada in konasu wllh wllh” Sudais ya 

nufi kofar fita da Heedayah yace “Baxa dai kije India ba idan xa ki sa ma ranki salama ki saka, ance maki tsofaffi na 

fita India ne, ke a dole xa a hau jirgi, to sai a dau na annabawa dai” Daga haka ya fice da sauri kafin ta ce komai, ya 

nufi part din Mami. Baffa na tsaye compound tare da Shuraim da ya ki shiga dakin kaka shi dai, Baffa ya kalli 

Shuraim yace “Me yasa baxa ka bi su Shuraim? Barrister ya ce min da junaid xa su tafi” Shuraim ya shafa kansa 

yace “Haka nan kawai Baffa” Baffa yace “But you need to go as your father’s representative tunda shi baxai samu 

xuwa ba, shi Junaid can go anytime” Shuraim yayi murmushi kawai bai ce komai ba, Muryar Mumy suka ji ta leko 

tace “Ni na hanasa tafiya Doctor, tunda ba a maida uwarsa bakin komai ba a gidan uban me xai je yi masu India?” 

Baffa ya juya yana kallonta, can yace “Wnn ba girman ki bane Maryam” bata tanka sa ba ta juya ta koma, Baffa ya 

girgixa kai bai ce komai ba, Suna tsaye har Abba ya dawo ya samesu wajen, Abba na ganin yanayin yayan nasa 

dama bai ce komai ba duk suka shiga cikin gidan, parlor suka tadda kaka tana jan akwatin ta fuska a tsuke, Mumy na 

daga dining tana dariya kasa kasa dadi kamar ya kasheta, Abba yace “Ina kuma xa ki Baaba?” A mugun fusace tace 

“Rufe min baki algungumi, Ina ruwan ka da inda xa ni??” Ya kwantar da murya yace “Kinga Baaba, tafiyar ma an 

fasa har sai an maki visa sai duk ku tafi tare” Tace “Oh oh ba ruwana su yi tafiyarsu, kada wanda yace min komai, ni 

dai an walakanta ni an cuce ni, Allah ya hada mu a kiyama gaba daya kawai….” Xaunawa Baffa yyi saman kujera ya 

jinginar da kansa yana kallonta, Abba dai bai ce komai ba, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, Kaka ta saki jakarta tayi mitsi mitsi da ido tace “Junaidu ashe dama uwarka bata da kirki ban sani ba, Ashe sai a hada baki da ita a cuceni 

ban sani ba, ni tunda nake Maryam bata ta6a min abinda Rakiya tayi min ba wllh” Da farko tsaye yyi bakin kofar, 

sai kuma ya karaso yace “Me ya faru kaka?” Kaka ta sakar masa kuka tace “Da hadin bakinta aka yanke shawarar 

baxa a je India da ni ba wajen gyaran idon Deedayah” Junaid ya d’an bude ido yace “Aa kaka ai dole ma xa ki je, ga 

visa nan ana maki, idan ya so bayan an gama ni da ke sai mu bi su daga baya, nima ai ba binsu xanyi ba ynxu…” Ta 

marairaice tace “Toh ai su basu ce min haka ba cewa suka yi ban da ni kawai, wani har ce min yyi nima kai na cutar 

ce me xai kai ni India, wato wai nice cuta, har da ce min wahalalliya, abinda ni dai nasan ubansa ya xaga ba ni ba” 

Junaid yace “Aa kiyi hakuri don Allah, tafiya kam xa ayi da ke in sha Allah, kawai dai daga baya ne xamu bi su” 

Kaka tace “To da wa da wa xa a tafi din yanxu?” Yace “Mami da Shuraim” Mumy dake dinning har sannan ta sakko 

xuwa cikin parlon cike da gadara tace “Nace Babu inda Shuraim xai je, a nemi wani amma ba shi ba, indai har ni da 

na haifesa ban cancanci xuwa ba to shima bai cancanta ba, kada a sake ambaton sunansa a masu tafiyan” Kaka ta 

bude baki tana kallonta tace “Waye wannan kuma? Daga gidanku kika xo da Shuraim din da xaki nuna mana iko a 

kansa ko kuwa shakiyanci ke damun ki? Kaji min jarabbiyar mata dai, to wllh sai an je da Shuraim, Kai idan xuciya 

ta debeni ma sai ince shi kadai xai kai ta gyaran idon kada wanda ya bi su, ke a wa xaki ce baxai je ba wahalalliyar 

mata kawai, nan nan kanwarki ta xo nan gidan ranan kamar abun arxiki amma sbda tambadewa na samu labarin ba a 

gidan take kwana ba sai ta fita da daddare ta dawo mana da safe, to gidan ubanwa take kwana, baki dau mataki kan 

wnn lamarin ba sai don ance Shureen xai je indiya da Deedayah? ” kaka ta kalli Abba a fusace tace “Kai Amadu da 

wa da wa xa a tafi goben?” Yace “Rahinah da shi Shuraim, daga baya sae ke da junaid ku bi su” kaka tace “Toh dole 

da Shuraim xa a tafi, idan ma kowa bai je ba sae Shuraim yaje wllh” Mumy tace “Ohk, ya tafi bakina ma ya ishesa 

ai” Kaka ta nufeta tana tafe hannu tace “Bakin ki na banxa na hofi, bbu abinda bakinki xae mashi, ae ubansa xai yi 

ma biyayya don hka a gantale bakin ki xae xaga duniya ya dawo ya fada kanki ba dai kan jikana ba, gantalalliya 

kawai” a nutse Mumy tace “In har Shuraim ya taka ya fita gidan nan xuwa wani kasa wllh sae na tsine masa” tana 

fadin haka ta bar parlon kamar xata tashi sama, Shuraim dai na tsaye gefen Abbansa, kaka tace “ke kuma tsinuwar 

Allah ya tabbata a kan ki ba na mutum ba, xan ga uban da ya isa ya hana Shuraim xuwa India” Abba da gaba daya 

ransa ya gama baci ya bi bayan Mumy, Baffa dai ya ta6e baki bai ce komai ba, kaka na kallon Junaid tace “Ni dai ko 

xaka kai ni gidan kawun ka ynxu, wllh raina baci yake idan Ina ganin mutan gidan nan, Ka kai ni can ko xa a 

kwantar min da hankali” yyi murmushi yace “Toh mu je kaka” tace “Amma ae abun ba hauka bane bana kai masu 

katon akwati ba bari in bude in dau kayana kala ko goma ne” Shi ya ja mata akwatin har dakinta tana biye da shi 

tana goge guntun hawayenta… Washegari da asuba Mami ta gama duk shirinta, ta shirya Heedayah, suka fita xuwa 

parlon Abba, Abba da ya gama hada duk medical report din Heedayah a envelope ya mika ma Mami yace “Amma 

xa mu tafi ku yi ma Kaka sallama tukun koh” Mami ta amsa tace “In sha Allah” Abba ya kalli agogo yace “We need 

to hurry up, sbd kar ku yi missing train din” Mami tace “Haka ne” Abba ya dau wayarsa yana mamakin rashin ganin 

Shuraim a masallaci don bai dde da shigowa daga masallacin ba shi ma, Dialing number sa yyi ya ji switched off, ya 

kuma kira a kashe, Mami dai kallonsa kawai take bata ce komai ba, Abba ya dinga kallon wayar tasa, can ya mike 

yace “Mu tafi kawai in kai ku gidan Honorable din daga can Junaid ya kai ku Train station” Tace “Shuraim din fa?” 

Yace “Don’t worry about that” Mai gadi ne ya shigo ya dau kayan Mami da Heedayah ya sa bayan motar Abba, 

Mami tace “Toh baka yi ma daughter din taka Addu’a ba Allah ya sa ayi aiki a sa’a” Abba yyi murmushi yana kallon 

Heedayah dake sanye da kananun kaya sai baby Hijab dake kanta tana rike da hannun Mami, kamo hannunta yyi 

yace “Safe trip dear, Allah ya kai ku lafiya ya sa ayi komai a sa’a, ya baki lafiyan idon ki” Ta kamo hannunsa a 

hankali tace “Abba xan fara gani nima?” Yana murmurshi yace “In sha Allah Dear” ta d’an yi shiru sai kuma tace 

“Toh baxan fara ganin Ammi na ba?” Abba da Mami duk suka yi shiru suna kallonta, hawaye ne ya kawo idonta tace 

“Tace min ita xan fara gani fa” Abba ya jawota jikinsa yace “Xa ki ganta in sha Allah daughter, Mami ma ai Ammin 

ki ce” Ta gyada masa kai, ya share idonta suka nufi gun mota Mami na biye da su a sanyaye, Sai bayan da ya shigar 

da Heedayah motar Mami tace “Baxa ayi ma matarka sallama ba?” Yace “No, rabu da ita” Mami bata kuma cewa 

komai ba ta bude front seat ta xauna suka fita gidan xuwa gidan Alhaji Imran Baffansu Junaid, Dakin da aka sauke 

kaka Mami ta shiga da Heedayah bayan sun gaisa da Hajiya Zuwaira a dakinta, kaka na xaune ko haske gari bai yi 

ba ga kayan karin kumallo iri iri a gabanta tana hada shayi cikin katon mug, Mami ta xauna saman carpet tana 

murmushi tace “Ina kwana kaka” Kaka tace “Lafiya lau, to Ina xan samu haka a gidanku??” Murmushi Mami kawai 

take, can tace “Toh mu kaka xa mu tafi ayi mana addu’a, Allah yasa mu je a sa’a ayi a sa’a, ku kuma Allah ya kawo 

ku lafiya” Kaka tace “Toh Allah ubangiji ya kai ku lafiya, ya sa wnn marainiya ta fito lafiya, Allah kar ya bamu 

kunya yasa idanuwan nan su rufa mana asiri su budu” Mami ta yi kasa da kanta tace “Ameen” Kaka tace “Toh matso 

da ita in yi mata addu’a” Mami ta maida Heedayah kusa da kaka, kaka tayi duk suran da ta sani da su ayatul qursiyyu 

da Amanar rasulu duk ta tofa mata tace “Allah ubangiji ya sa ayi aikin a sa’a, ya rufa mana asiri ki fara ganin kowa 

kamar yanda ake ganin ki, daga karshe kuma Allah ya bama d’a na ladan uban kudin da ya kashe maki, Allah yayi 

masa albarka yasa kema ki ji k’an sa wataran kada ki yi mana butulci…” Heedayah dai tayi shiru staring into space, 

kaka tace “Kaji gantalalliya, baxa ki ce Amin ba, ko kina da niyyar butulcin ne ya sa kika yi shiru bamu da labari

” Mami tayi murmushi tana kallon Heedayah tace “Say Ameen daughter” a hankali Heedayah tace “Ameen” Kaka tace 

“Toh maxa ku tafi kada jirgin ya tafi ya bar ku ba mutunci ne da su ba haka suka so min xuwa umrana na karshe 

Allah ya fi su” Mami tace “Toh Kaka, mun gode da addu’a, baxa ki fito ku gaisa da barrister ba” Tace “Waye kuma 

Barrister? Don Allah ki rabu da ni kada raina ya baci, yyi ta kansa inyi ta nawa kawai” Mami ta mike tace “Toh 

Allah ya sada mu da alkhairinsa kaka” Kaka tace “Kiyi addu’a sosai kafin ku hau wnn bala’in na bature wai jirgi” 

Mami tace “In sha Allah” kaka tace “Da Shuraim din dai xa a je koh?” Mami tace “In sha Allah” Kaka tace “Toh duk 

Allah ya tsare ku, yayi maku albarka, ya sa ayi wnn aiki a sa’a sai mun xo ni da Junaidu” Mami tace “In sha Allah 

kaka” daga haka ta fita dakin, Abba na xaune parlor da Alhaji Imran, Ganin Mami yace “Lkci fa na wucewa kada 

kuyi missing train” Mami tace “Ka samu Shuraim din?” Abba yace “No tare da Junaid xa ku tafi” Shiru Mami tayi, 

Ya mike yace “Yeah, na kira junaid din ya shirya ynxu” Mami ta xauna tare da Heedayah, Alhaji Imran yace “Allah 

ubangiji ya tabbatar da alkhairi a tafiyar” Mami tace “Ameen Baffa” Ba a dau lkci ba sai ga Junaid da traveling bag 

dinsa ya sakko kasa, Abba na kallonsa yace “Hope baka ce ma kaka komai ba” junaid yace “Aa ban shiga ba” Abba 

yace “Good” Har motar Abba dake parke waje Alhaji Imran da matarsa suka raka su, Alhaji Imran na kallon junaid 

yace “Nayi maka transfer yanxu Incase da bukatar wani abun a can, Allah ya kai ku lfya, ya sa ayi aikin a sa’a” 

Junaid yace “Toh Baffa Allah ya saka da alkhairi” Abba yyi ma Alhaji Imran godiya haka ma Mami sannan suka dau 

hanyar train station na Hayin rigasa, Junaid na xaune back seat da Heedayah, ta kwantar da kanta saman shoulder 

dinsa a hankali tace “Good morning….

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

One comment

  1. I value this informative blog. Im searching on search engines for this type of info last but not least got a high quality one. This will assist with what I am considering regarding my research for my personal college task.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *