HEEDAYA CHAPTER 16 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 16 BY By Khaleesat Haiydar

Parking Junaid yyi a compound din Baffan sa, ya sauka ya bude ma kaka bayan motar, ta fito tana kare ma 

kantamemen gidan kallo baki bude tace “Nan ne gidan kawun naka?” Junaid yace “Nan ne” kaka tace “Ikon Allah, 

to mu shiga, Allah ya sa bai fita ba dai….” Junaid ya shiga gaba tana biye da shi yace “Yana nan ai, ga motarsa” 

Kaka ta kalli motar da ya nuna mata tace “Kamar irin motar Umaru kuwa” Babu kowa parlon da suka shiga, Kaka ta 

xauna tace “Wato basu tashi ba kenan ana ta bacci” Junaid yyi murmushi yace “Bari in masu magana” daga haka ya 

wuce sama, kaka ta dinga bin parlon da kallo ta rike ha6a murya can kasa tace “Toh ai masu kudi ne su ma, ba gidan 

tsiya Shureen dina xai fada ba, ko gidan Umaru bai kai haka ba” Ba a dau lkci ba Junaid ya dawo tare da wata 

dattijuwa, Ta xauna tana kallon kaka da fara’a tace “Sannu da xuwa Mama, Ina kwana” Kaka ta kalleta tace “Lfya 

lau wllh, kece matar gidan?” Matar na murmushi tace “Ni ce Mama” Kaka tace “Atoh ya yara, ya gida” Matar tace 

“Alhmdllh wllh, fatan kun xo lfya?” kaka tace “Toh Alhmdllh, ba ma wanda yasan na fito sai shi Junaidun, nace dai 

yau bari in xo inyi xumunci ku san ni in san ku, bana biye ta Rakiya da Amadu ba, ko karyawa ban yi ba wllh na 

fito” Matar tace “Ikon Allah to bari a kawo maki kayan kari yanxu, tashi mu je daga ciki Mama, sannu da xuwa” 

Kaka tana washe baki mike tace “Toh” har parlonta ta kai kaka, ba a dau lkci ba aka cika gaban kaka da kayan karin 

kumallo, flask din ruwan Lipton me kamshi, soyayyen dankali da kwai da plantain, katon bread, sai wainar shinkafa 

da lafiyayyen taushe, ga farfesun kayan ciki a gefe, Kaka na kallon masu aikin dake ta jera mata abincin tace “Babu 

darduma in sauka kasa??” karamin carpet me laushi suka shimfida mata ta sauko kasa bayan ta cire Hijabin ta, 

komai sai da kaka ta diba ta ci a abincin, sai da taji tayi nak murya can kasa tace “Toh ko nan nace xan dawo da 

xama ai bbu me ce min komai tunda an xama daya yanxu…” Sallama aka yi kofar parlon Kaka ta amsa wani dattijjo 

da baxai wuce 65 ba ya shigo parlon, kasa ya xauna yace “Sannu da xuwa Baaba” Kaka na washe baki tace “Sannu, 

kai ne kawun Junaidun?” Yace “Ehh nine, Ina kwana” Kaka ta gyara xama tace “Lafiya lau, yau dai nace bari in xo 

in ganka ka gan ni, idan na biye ta uwar Junaidu baxa ayi xumuncin ba ma, kasan yaran ynxu basu san amfanin 

xumunci ba” Yyi dariya yace “Gaskiya ne Baaba, to ya ku ka baro mutan gidan?” Tace “Lafiya lau, ko sanin na fito 

ma basu yi ba, nace inyi maxa in xo kar ka fita, tunda shi Amadu na ga karfe takwas xuwa tara yake ficewa” Yace 

“Wannan gaskiya ne” Kaka tace “Toh bayan xumunci kuma a gaskiya har da alfarma na xo nema a gun ka” Ya xauna 

da kyau yace “Toh ina sauraron ki Baaba” Tace “Ba wani abu bane d’an nan, jikana Aliyu na xo nema ma auren ‘yar 

ka, wato Farida, kaga dai Aliyu ni na haifi ubansa Amadu, tunda nake ban ta6a ganin yaro da ya tashi bashi da 

matsala irin Aliyu ba, bbu ruwansa da kowa, ba shi da abokin fada, kai in takaice maka shi ba me magana bane ma, 

to shine na ya6a da hankalin farida tunda ta xo kuma ta xauna dakina, komai ita ke min wllh, ko nayi laifi da nayi 

wnn tunanin bawan Allah, amma dai ya ma sunan ka tukun” Yace “Sunana Aminu” Kaka tace “Toh ai sunan babana 

kenan, Allah sarki, to yanxu ya kaga…” Yace “Batu ne mai kyau wannan Baaba, amma sai dai Farida ynxu karatu 

take wllh” Kaka tace “Oh oh Allah, karatu na hana aure ne wai dama? Ku me yasa ku ka bari boko yyi maku kaca 

kaca haka, Shi kansa Amadun fa haka yace min, meye a ciki idan anyi auren ta ci gaba da karatun ta, ynxu 

shekararta nawa ma dai tukun?” Yace “Bata cika sha shidda ba ma” Kaka tace “Shine tayi girma haka? Toh kaga 

kuwa ai aurar da ita shine rufin asirin mu da ku, kaga dai takanas na taso da kafafuwana na sameka a gida sbda 

alkhairin da nake nema da ku, a gaskiya idan kace min A’a raina xai baci Aminu, da girmana na taho wajenka…. 

Kuma da Rakiya ta san gidan banxa ne gidan Amadu ai baxa ta shigo ba….” Yana murmushi yace “Gaskiya ne Baaba, 

in sha Allahu tunda ba fin karfina alfarmar da kika xo nema yyi ba xanyi bakin kokarin ganin komai ya tafi yanda kike so, amma sai Farida ta gama secondary in sha Allah” Kaka tace “Toh tunda dai ka amsa ai shkkn, kwana nawa 

ne xa a ga ta gama sakandarin, shi ma massers dinsa yake yi a Zaria, kaga sai su gama lkci daya kenan, bari anjima 

shi xan ma kira ya mayar da ni gida sai ka gansa, yana nan ko yatsa ka sa masa a hannu baxai ciza ba, yaron kirki 

me girmama na gaba da shi, Kai ni ko rashin kunya na jika da kakan nan ma ni bai ta6a min ba, tamkar uwarsa haka 

yake min biyayya” Shi dai murmushi kawai yake yace “Toh shkkn Baaba xan fita wajen aiki sai na dawo, ai kina 

nan?” Tace “Aa ina nan kilan har ka dawo, yanxu fa na xo” yace “Toh maa sha Allah, sai anjima” tace “Allah maka 

albarka” ya amsa da Ameen ya fita. Yana fita wayar kaka ya fara kara ta fiddo a jaka da sauri, da yake ta san Inda 

ake dannawa ta danna ta kai kunne, Muryar Mami taji, kaka tace “Ke ba fa wani waje naje ba, gidan ta salla na tafi, 

anjima in sha Allahu xan dawo” Mami tace “Toh shkkn, amma ba sallama kaka” Kaka tace “Ehh to da yake tafiyar ta 

gaggawa ce, anjima dai xan dawo in sha Allah” Mami tace “Toh Allah ya dawo da ke lafiya” kaka tace “Ameen” 

daga haka ta katse wayar ta ajiye ta jawo sauran farfesunta tana lasa. Har aka yi Magrib Kaka na gidan Baffansu 

Junaid, Matarsa kuwa Hajiya Zulaiha bata bar Kaka ita kadai ba, tare suka yini, a xamansu na yan awannin nan 

abinda kaka ta manta ne kawai bata gaya mata ba, tarihi iri iri, Wanda ya kamata da Wanda bai kamata ba, tun 

mijinta na da rai har sanda ya rasu, amma ko da wasa kaka bata gaya mata halin Mumy ba, Hajiya Zulaiha dake 

yanka ma kaka kankana bayan anyi sllhn Magrib tace “Na kirasa yana hanya ynxu Mama” Kaka tace “Toh kinsan 

shi xai mayarda ni gida kar in gigita ‘ya yana suyi xaton 6ata nayi shi sa na damu” Hajiya Zulaiha tayi dariya tace 

“Kila yana can gun budurwar sa tun da kika ga har war haka bai shigo ba” Kaka tace “Au, yana da budurwa kenan?” 

Hajiya Zulaiha na dariya tace “Kwarai kuwa” Kaka tace “ikon Allah, ko da yake ga Shureen ma Ina kokarin ganin 

yayi aure nan da ‘yan watanni balle Junaidu, da kyar idan bai girmi Shureen ba ma” Hajiya Zulaiha tace “Lallai 

kam” Kaka tace “Ko da yake ga Farida ma naji shekarunta ba wasu shekaru bane amma duk ta balaga, kusan sa’ar 

Khadijahn Amadu ce fa, Ita kuma Rabi’ah sa’ar Deedayah Ina jin, don duk kwailaye ne” Hajiya Zulaiha dai tayi 

dariya ta ajiye ma kaka kankanan tace “Bari in je inyi sllh Mama, amma da kawai kiyi kwanan ki a nan Mama” 

Kaka tace “A’a ba mutunci gare su Amadu ba sai su iya min fada ba ruwana, bari dai in tafi ba dai na ga gida ba” 

Hajiya Zulaiha tace “Toh shkkn Mama” daga haka ta fita parlon…. Tana fita da minti sha biyar Junaid ya shigo, kaka 

tace “Ashe kana da budurwa Junaidu, yanxu matar kawunka ke ce min tadi ka tafi” yace “Aa gidan abokina nake” 

tace “Au, to in tashi mu tafi kada su Amadu su yi ta nemana koh?” Yace “To mu je kaka, ai kin ci abinci” Kaka tace 

“Idan ma nace ban ci ba, ba sai Allah ya kama ni ba, Tuwo ce fa malmala uku aka saka min ga miyar kubewa duk 

nama da Ganda ga kifi, ga kuma lemo me sanyi… To ina xan samu haka gidan Amadu?? Gaskiya matar nan ta san 

mutunci, baka ga ba wllh sai ji take da ni, komai ta rarumo ta kawo min, daxu da rana har kwadon zogala ta min 

bayan shinkafa da miya da uban nama da ta xubo min, ni dai gaskiya an karrama ni a gidan nan, ai Rakiya sai dai 

ince Allah yyi mata albarka kawai, danginta sun san mutunci kam” Murmushi kawai Junaid yyi yace “Idan kin gama 

shiryawa Ina parlor kaka” Kaka tace “Toh, d’an Albarka” Sai bayan kusan minti ashirin kaka ta sakko da handbag 

dinta, tana kallon yan matan gidan guda uku dake xaune parlor tace “Toh ko Sudess ma idan ya samu daya daga 

cikin wa ennan bai gode ba, ynda yan mata ke wahala ynxu….” Har parlon Baffan Junaid kaka ta shiga, yace “Aa 

Baaba ai na xata kwana xa kiyi a nan” tace “Aa su Amadu xa su min fada” Yace “Ikon Allah, toh Junaid xai maida ki 

amma” tace “Eh yana jirana ma yanxu haka” mikewa yyi yace “Toh Ina xuwa Baaba” yashiga dakinsa sai gashi ya 

fito ya mika mata dubu goma da ladabi yace “A siya goro Baaba” Kaka ta amsa ta saka a jaka tace “A’aaahh ayi haka 

d’an nan, ai da ka bar shi wllh, toh Allah yayi maka albarka, nagode ka ji” yace “Godiya ya tabbata ga Allah” rakata 

yyi har xuwa parking space tare da Hajiya Zulaiha da ta bata atamfa da turarurruka, tayi ta daga masu hannu tana 

washe baki har motar ya fita gidan, bayan sun hau titi tace “Gidan ma babu wahalan ganewa kaga idan xan dawo 

baxan sha wahala ba koh” Yace “Haka ne kaka” Tare Junaid da Kaka suka shiga parlor, Rabi’ah dake kwance parlon 

tana kallon Tv tace “Sannu da dawowa kaka” kaka tace “Yauwa…. Junaidu tafi ka dauko min Deedayah ga sauran 

nama na kulle mata a leda” yace “Toh” daga haka ya nufi part din Maminsa, Rabi’ah tace “toh mu fa?” Kaka da ta 

nufi dakinta tace “Uwar me na hada dake banda dai ke jikata ce, idan Maryam ce ko Amadu kya gaishesu a 

kwance?” Daga haka ta shige dakinta. Mami na kallon Junaid bayan ya gaisheta tace “Daga ina ku ke?” Yace “Gidan 

Baffanmu” Mami tace “Baffan ku? Kai da kakan?” Yyi yar dariya yace “Da sassafe ta kirani wai in xo in kaita” 

Mami ta dinga kallonsa da mugun mamaki tace “Sai ka kai ta?” Yace “To meye a ciki Mami?” Mami ta mike tace 

“Why didn’t you call and ask for my opinion Junaid???” yyi kasa da kai yace “Mami naga ba wani abu bane, ai kowa 

ya san tsoho…” Xata yi magana aka bude kofar, shiru tayi kaka ta shigo tace “Ina Deedayan?” Mami tace “Sannu da 

xuwa kaka” Kaka tace “Yauwa Ina Deedayah ga nama na kullo mata” Mami tace “Suna parlon Barrister” Kaka tace 

“Kai Junaidu tafi ka dauko min ita, Ina iya shiga parlon yanxu Amadu ya rufeni da bala’i” Mikewa yyi ya fita parlon, 

Kaka tace “Wllh anguwa naje ke dai Rakiya, mutum yyi ta xaman gida kamar bashi da jama’ah” daga haka ta fita ta 

bi bayan Junaid da sauri, tun kan ya shiga parlon Abba ta tsayar da shi tayi kasa da murya tace “Kar ka gaya masu 

daga Inda muke, cewa kawai xakayi a bakin titi ka ganni ka dauko ni, har ita Rakiyan kar ka gaya mata kaji” Yana 

murmurshin karfin hali yace “Toh” daga haka ya shiga parlon ta koma nata dakin…. Washegari Sunday da safe 

Shuraim ya shiga gaida Abbansa, Abba na aiki system dinsa ya amsa yace “Anjima xaka ajiye Farida makaranta” Ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Abba yace “Before then, xan maka transfer ku je tare tayi shopping, da yamma sai 

ka ajiye ta schl din” yyi kasa da kai yace “Toh” Abba yace “That’s it, Kai yaushe xaka wuce Zarian?” Yace “Gobe da 

safe” Abba yace “Allah ya kai mu” mikewa yyi, ya ma Abbansa sallama ya fita, direct dakin kaka ya nufa, Kaka na 

ta gyara kayan da ta binciko a press din dakin, Heedayah kuma na kwance saman gado tana cin naman da kaka ta 

kawo mata, kaka kuma na bata labarin irin abubuwan da ta ci a inda taje jiya, Heedayah tace “Toh baki gaya min 

sunan wajen ba….” Kaka tace “Toh wai ina ruwanki, ke dai kawai ki bari, akwai abinci a gidan” Heedayah ta tallabi 

chin dinta tace “Toh shine ni baki je da ni ba?” Kaka tace “Ai kinsan a boye na bar gidan shi yasa, amma ba gashi na 

kullo maki sauran nama ba” Shuraim ya bude kofar ya shigo dakin, kaka tayi tsit da bakinta tana ci gaba da linkin ta, 

Murya can kasa Heedayah tace “Kaka waye?” Kaka tace “Iska ce ta turo kofa” Heedayah ta turo baki tace “Na xata 

wnn Shureen din nan ne….” Kaka tace “Shureen kuma, me xai shigo ya min, baki ga tun wayewar gari bai ko shigo 

gaidani ba” Heedayah tace “To kaka wai me yasa yake yi ma mutane mugunta? Ni fa bana son sa” Kaka tace “Haka 

nan Allah ya halicce sa, Kuma ya xa ayi ki so sa, ke da baki hada komai da shi ba….” Heedayah dai tayi shiru sbda 

kamshin turare da ta fara ji, kaka tace “Tun yana karami duk da baya magana haka yake narkan ‘ya yan mutane, yyi 

ta cin xali, uwarsa kuma tayi ta goyon bayansa” Heedayah dai bata ce komai ba, Kaka tace “Ya kika yi shiru kuma” 

Heedayah ta turo baki a hankali tace “Bayan yana dakin xaki ce min baya nan” Kaka ta kyalkyale da dariya, 

Shuraim da ya wani hade rai yana kallon Heedayah yayi kwafa ya juya ya fice, Heedayah dai bata ce komai ba ta

wani cinno baki, kaka tace “Atoh, yarinya sai fitsara da gulma wai don ma bbu ido…” Da rana Farida ba don ranta ya 

so ba ta shirya xa su je shopping kamar yanda ita ma Abba ya gaya mata, Heedayah ma ta sa Hijab dinta don tare 

Mami tace su je, can kofar gida yyi parking don ma kar Mumy tayi noticing xa su fita, Farida Ta bude ma Heedayah 

back seat tana rike da hannunta ta shiga, ita kuma ta shiga gaba, ko kallonsu bai yi ba ya tada motar suka bar layin. 

Wani shopping mall xai shiga Farida tace “A na gaban nake yi shopping, nan ba dukka abinda nake so suke da shi 

ba” Ya wani daure fuska bai dai ce komai ba ya shiga yyi parking ya kashe motar, Farida ta dauke kai ta ta6e baki ta 

bude motar ta sauka, ta bude side din Heedayah ta kama hannunta ta sauka, ta gefen ido yake kallon Heedayah da 

Hijab dinta ya wuce gwiwa da kadan, sae pink wandon dake jikinta amma bai kai ankle dinta ba, Farida xata rike 

hannunta su wuce ciki ya fixge hannun yace “Wa xata bi a hakan???” Farida ta kalli Heedayah daga sama har kasa, 

ya bude bayan motar yace “Maida ta ciki” Farida tace “But there is nothing wrong with her dressing, I dressed same 

also” Da kansa ya mayar da Heedayah da ta fashe da kuka cikin motar ya rufe, Farida ta rungume hannunta ta hade 

rai ta jingina da motar tace “Ni na ma fasa shopping din” Wani kallo yyi mata yace “Gaura maki Mari xan yi idan 

baki shiga mun wuce ba” Ta fashe da kuka tace “Toh why will u lock her all alone cikin motar, don’t you know there 

is heat, ni baxan bar ta ita kadai ba” Atm card dinsa ya ciro ya mika mata still frowning his face yace “Double five, 

double zero…. Tafi kiyi shopping dinki ke kadai” Ta leka motar tace “Toh xaka tsaya da ita ne” Kin bata amsa yyi, ta 

amshi ATM card din ya bude maxaunin driver ya shiga ya xauna, A hankali Farida ta nufi cikin mart din. Heedayah 

dai ta daina kukan da take sai share idonta take, ta gaban madubin motar yake kallonta, bayan kusan minti goma jin 

shirun yyi yawa ta matsa a hankali kusa da driver seat ta sa hannu xata lalabu ko akwai mutum a nan, Kirjinsa ta 

ta6a ta janye hannunta da sauri ta koma ta xauna tana turo baki… Bayan wani 15 mins din sai ga Farida ta fito da 

labourer dake dauke da ledojin kayanta, Bude booth yyi kafin su karaso, mutum ya saka kayan gaba daya a ciki ta 

bude jakarta ta ciro kudi ta basa sannan ta bude back seat ta shiga ta rufe tana kallon Heedayah tace “Didi na siyo 

maki chocolates and Biscuits har da teddy…” Heedayah ta wara ido ta kamo hannunta tace “Thanks Farida” Ya d’an 

ta6e baki ya tada motar yayi reverse ya bar shopping mall din. Karfe biyar saura Farida ta gama shirin komawa 

makaranta, Heedayah har da hawayenta daga Inda ta xauna ta takure kanta, Mami da ta ji tausayinta sosai tace “Ku 

tafi tare Farida, sai ya dawo da ita” Farida da duk jikinta yyi sanyi ta kama hannun Heedayah suka fita parlon xuwa 

dakin Kaka su yi mata sallama, Shuraim na xaune main parlor da makullin motarsa cox Mumy bata gidan, Ya bi su 

da kallo yace “If she is not changing that clothe she shouldn’t bother entering my car…” Farida ta juya tana kallonsa 

don tun da take bata ta6a jin yyi magana me tsayi hka ba, ta dauke kai ta ta6e baki, Heedayah ta rike hannun Farida 

sosai kamar xata yi kuka tace “Pls kice Mami ta bani dogon Hijab in sa” Farida ta d’an ja tsaki suka koma bangaren 

Mami, Mami na kallon Heedayah daga sama har kasa tace “Does he have any business with her dressing, ko ya siya 

mata Hijabs ne? Or is he stupid??” Farida dai bata ce komai ba ta dauko ma Heedayah wani Hijab din har kasa ta 

saka sannan tayi ma Mami sallama suka fita, Kaka har da kwallarta, ta daure ma Farida cin cin da bai fi kwaya 

shidda ba a leda ta mika mata tana cewa “Ashe baki nan xa a kai Deedayah India” Farida tace “Kilan muna jarabawa 

lkcn” Kaka tace “Toh ai shkkn, Amadu yace min nan da sati uku ne, ga kayana har na hada” Farida tace “Toh Allah 

ya kai mu” Kaka ta dauko maltina daya ta kara mata, ta rakasu har bakin motar Shuraim, tana kallon Shuraim tace 

“Toh ko in dauko gyale mu tafi tare Shureen?” Ya gyara xama yace “Ehh” Da sauri ta juya ta koma ciki, ya tada 

motarsa ya fice daga gidan, Heedayah ta rufe fuskarta a Hijab tana dariya a hankali, Farida kuwa sai hararansa 

take…. Suna Isa makarantar Shuraim yyi parking, tsadaddun motoci ne iri iri an kawo students, Farida ta kamo 

hannun Heedayah tace “Till I come back Didi…” hawaye ya kawo fararen idanuwan Heedayah, ta madubi Shuraim 

ke kallonsa, Jikin Farida yyi sanyi tace “Baxan dade ba xa mu yi hutu….” Heedayah ta fashe da kuka sosai ta daura kanta saman jikin Farida, Shuraim ya hade rai yace “Malama sauka ki bude booth ki sauke kayan ki” Ta galla masa 

wani harara tana share idonta ta sauka motar, sauka yyi shi ma don sauke mata kayan don ya san sun mata nauyi, 

Heedayah na jin haka ita ma ta bude motar ta sauka, Tsaye yake jikin black ride dinsa ya rungume hannu idonsa 

sanye da bakin space, he looks so gentle and calm, dai dai saukowar Heedayah, a hankali ya cire Glasses din idonsa 

yana kallonta, Shuraim kawai gani yyi ta ci karo da daya daga jakan Farida da ya sauke kasa Farida kuma tana gun 

booth tana fiddo kananun ledojin, kafin ya karasa ya riketa tuni ta fadi kasa, shi kansa Mutumin har ya taho da sauri 

kafin ta kai kasa ganin Shuraim sai kuma ya tsaya cak, Shuraim ya dagota yace “Wa yace ki sakko?” Ta fashe da 

kuka tana yarfe hannunta tace “Wayyo na buge kafana, and there is sand in my eyes” Tuni Farida ta durkusa kusa da 

su tana ma Heedayah sannu, da ma sauran mutanen wajen, Bude idon Shuraim yyi, yyi blowing mata iska gently, 

ganin yanda ake kallonsa kawai ya dagata ya bude back seat ya sa ta ciki, ya karasa sauke ma Farida kaya yace 

“That’s all” daga haka ya bude back seat din ya shiga yana kallon Heedayah dake ta murxa idonta matsawa yyi kusa 

da ita ya dafa forehead dinta yana kallon cikin idon, ta kauda kanta kamar xata yi kuka tace “Ya daina” Saketa yyi 

still looking at her eyes…. Tuni Mutumin ya shiga mota ya mance abinda ya kawosa bakin makarantar ya tada 

motarsa yana kallon motar Shuraim ta madubi, Shuraim ya daga hijab dinta ya kalli kafarta ya ga just little bruises 

ne a farin kneel dinta, Bude motar yayi ya sauka ya koma driver seat, ya tada motar yana fara tafiya Mutumin ya bi 

bayansa

Shuraim bai yi wani nisa ba ya kula da motar bayansa dake bin sa, slowly ya dinga tafiya to see idan motar xai yi 

overtaking dinsa ya wuce, but sai ya ga motar ya ki yin hakan sae ma rage nasa tafiyar da yyi shi ma, Shuraim ya 

samu waje yyi parking har sannan yana kallon motar ta madubi, Mutumin dake cikin motar dake ta lura da Shuraim 

shi ma kuma ya san Shuraim ya gano yana bin sa ne kawai yyi wucewarsa bai tsaya ba, Shuraim ya bi motar da 

kallo har da plate number din motar, juyawa yyi ya kalli Heedayah dake xaune bayan motar, she looks so sad kiris 

ya rage ta fashe da kuka daga ynda tayi da fuskarta, dauke kansa yyi ga mamakinsa har sannan motar bai bace masa 

ba, sbda a hankali me motar ke tafiya kan less busy road din, Shuraim ya kalli layin dake gefensa kawai ya karya 

kan motar ya shiga layin…. Sai kusan Magrib Shuraim ya isa gida, a hankali yake tafiya ganin motar Mumy dake 

tsaye bakin gate tana jiran me gadi ya bude gate din, sae da ta shiga snn yyi parking gefen flowers dake gaban gate 

din ya kashe motarsa, Mai gadi na ganin baxai shiga gidan da motarsa ba ya kulle gate din, Shuraim ya juya yana 

kallon Heedayah dake bacci bayan motar, sauka yyi motar ya kulle ya nufi cikin gidan, tsaye ya ga Mumy alamar 

shigowarsa take jira, ya karasa Inda take ya gaisheta tace “Daga ina kke da magariban nan” Yace “Asibiti” tace “Ohk, 

goben xaka tafi Zarian?” Yace “In sha Allah” tace “Toh nima xan je Zarian gobe, amma bance ka gaya ma kowa ba, 

karfe nawa xaka fita?” Yace “Takwas…” Tace “Toh kayi hakuri ka bari karfe tara, kafin nan Abbanku ya fita” Shi dai 

kallonta kawai yake don ya san basu da ‘yan uwa a Zaria, can yace “Me xaki je ki yi a Zaria Mumy?” Mumy tace 

“Yar Hajiya Sadiya ba can take aure ba, to ta haihu gobe suna, ko barka ban je ba, kuma idan na gaya ma Barrister 

ba lallai ya yrda ba, ni ko Sadiya ai ta wuce haka a wajena” Shuraim yace “Aa da dai ki fara sanar ma Abba Mumy” 

Mumy ta daure fuska tace “Toh ban yi niyya ba” Bai kuma cewa komai ba ta juya ta nufi cikin gidan ya bi ta da 

kallo har ta shiga parlon snn ya juya ya koma waje, Bude back seat yyi Heedayah ta bude ido da sauri, hannunta ya 

kama ya saukar da ita daga cikin motar ya kulle motarsa, har da xai mika ma Mai gadi hannunta ya kai ta ciki sai 

kuma kalli cikin compound din ya shiga yana rike da hannunta, yana isa balcony ya bude kofar parlon yana kallon 

ciki, bbu kowa hakan yasa ya shiga parlon da ita ya kai ta har kofar dakin kaka sannan ya juya ya fita xuwa 

masallaci, Kaka da ta fito daga bandaki tayi alwala tace “Waye wnn?” Heedayah tace “Ni ce” Kaka tace “Toh ai na 

ganki, sai yanxu ku ka dawo kai faridan makaranta?” Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace “To ina Shureen din?” 

Heedayah tace “Nima ban sani ba, ya wuce” Kaka ta ta6e baki tace “Toh me yasa kika yo min nan, Rakiyar bata nan 

ne” Heedayah ta turo baki tace “Toh ai shine ya kawo ni” Kaka tace “Toh ni dai na gyara dakina na share, na sa turaren wuta, gadon ma yau ko hawa ban yi ba tun da garin Allah ya waye” Heedayah ta turo baki ta juya tana laluba 

hanya da hannunta ta fice daga dakin, Kaka tace “Haka kawai ba kya ma mutum taimakon komai sai dai ki lalata 

waje gantalalliya” Mumy da fitowar ta kitchen kenan ta bi Heedayah da ido har sai da ta isa kofar parlon Mami, Dai 

dai fitowar Sajida dakinsu ganin Heedayah ta karasa don ta bude mata kofar, juyawa Mumy tayi ta wuce parlonta 

kafin Sajidan ma ta ganta… Sai da Heedayah ta shiga ciki sannan Sajida ta kulle kofar ta wuce. Karfe tara da rabi 

Mumy ta kira wayar Shuraim, yana xaune dinning da cup din shayi a gabansa, Ya daga kiran Mumy tace “Abbanka 

fa ya fita, baka gama shiryawa bane ko in tafi in hau motar haya kawai?” Yace “Na gama” katse wayarta tayi, ya 

mike ya tafi dakin kaka, Heedayah ce kwance saman gadon tana ma Doll din da Junaid ya siya mata kitso, Kaka 

kuma na bandaki tana wankewa, Heedayah ta dakatar da kitson da take ba Doll din jin an bude kofa tace “Waye?” 

Ya kalleta ya dauke kai, bata kuma cewa komai ba sbda kamshin da ta ji, Ya xauna yana jiran fitowar kaka, sai ga ta 

ta fito tana cewa “Masu aikin jaraba kawai sun bari bandakina xai dafe in shiga uku in lalace, Banda dai ma lalacewa 

ta sameni ina ni ina bar masu bandakina su dinga wanke min….” Shuraim dake ta kallonta yace “Xan wuce Zaria” 

Kaka tace “Tohhh da sassafe haka shureen” Yace “Eh” Tace “Toh Allah ya kiyaye hanya, ni dai ko kwandala bani da 

shi a dakin nan, dama Umaru ne me bani, gashi yau kwana daya bai xo ba” Mikewa yyi ya mayar da wayarsa aljihu, 

tace “Toh ko dari biyar baxa ka d’an bani ba Shureen, bani da ko sisi fa” Yace “Ni da bana maki komai kuma yau xa 

ki ce in baki kudi?” Kaka tace “Toh ai dama idan ba kai ba waye me min, shi Sudess yan matan da ya tara gabansa 

ma sun ishesa, Amadu kuma kaga ynxu ta kudin da xai kai makauniyar nan gyaran ido yake, da kyar idan ba sai an 

kashe kusan miliyan biyar ba tunda India ne, ai kaga ta kassara min d’a na kawai, wa gareni dama banda shi, shi din 

kuma ga uban abinda ke gabansa ba dangin iya balle na baba, Umaru dama yau sati rabona da kudinsa, sae dai ya xo 

ya karaci xamansa ya fice, toh ya ake son inyi da raina” Shuraim ya tabe baki yace “Toh nima bani da shi” Daga 

haka ya fita daga daki, kaka ta bude baki ta bi sa da kallo, can kuma tace “Toh kada Allah ya sa ka samu, marowacin 

banxa kawai solobiyo” Ko saurarenta bai yi ba, yana fita sai ga Mumy ta shigo dakin, Ta xauna ta gaida kaka, kaka 

ta amsa xata koma bandaki, Mumy tace “Kaka xanje gidanmu ne Salima bbu lafiya” Kaka ta dawo tace “Toh ba dole 

ba, yarinya sai gantalin duniya take an rasa me gaya mata gaskiya, kamar abun arxiki Amadu ya daukota kusan 

shekara sha biyu da suka wuce amma uwarki ta amshe ta wai autarta, to yau ina uwar taki take, ba gashi ta tafi ta 

barta ba, yarinya duk ta lalace wa yasani ma ko bin maxa take, da ynxu tana wajen Amadu har ya aurar da ita ta haifi 

‘ya yanta….” Mumy dai bata ce ma Kaka komai ba, Kaka tace “Amma wnn ai tafi karfin kowa ynxu, ta xama abar 

tsoro, na samu labarin ma ba kullum take kwana gida ba wai koh??” Mikewa Mumy tayi tace “Toh sai na dawo” 

daga haka ta nufi kofa ta fita, kaka tace “Toh Allah ma dai ya sa ba ciki ne da ita ba, tunda cewa kika yi bata da lfya, 

toh a dawo lfya Maryam” Mumy dai tayi wucewarta bata tanka ta ba Karfe Goma da rabi suka isa Zaria, 

Shuraim na kallon Mumy dake ta danne dannen waya yace “Ina ne gidan?” Tace “A’a kawai ka samu waje ka ajiyeni 

xan nemi adaidaita sahu, kilan kana da lectures kar in shiga hakkin ka” yace “Sai goma lectures din” Mumy tace “Ba 

dai ni nace ka ajiyeni ba wai” Bai kuma cewa komai ba yyi parking, Mumy ta sauka motar tace “Toh Allah ya bada 

sa’a” yace “Ameen, amma wani anguwar xa ki?” Tace “Saboda ga ka ubana?” Yace “A’a I was thinking ko anjima 

xan xo in maida ke kaduna ne” Tace “A’a, xan samu motar haya” Daga haka ta tsayar da adaidaita ta shige, ya tada 

motarsa ya wuce… A cikin adaidaitan Mumy tayi dialing number Sadiya tace “Toh ga fa ni na shigo Zarian Sadiya” 

Hajiya Sadiya ta gaya mata sunan wani filling station wai ta jirata a nan, Suna isa gidan man Mumy ta sauka ta ba 

Mai adaidaitan kudinsa tana jiran Hajiya Sadiya, bayan kusan minti ashirin sai ga Hajiya Sadiya, Mumy tace “Kin fa 

ce min kin fito gida ashe baki fito ba” Hajiya Sadiya tace “Wllh hatsari me Muni aka yi kafin Jaji, shine ya haddasa 

go slow” Mumy tace “Toh Allah ya ji k’an musulmi, ynxu ina muka nufa?” Hajiya Sadiya tace “Tashan da xa mu je 

mu hau motar garin mana” Wani adaidaitan suka samu ya kai su tashan, Mumy sae cewa take ni dai Allah ya sa 

kafin karfe hudu xa mu koma Kaduna, gidanmu nayi ma Barrister karya nace xan je” Hajiya Sadiya tace “Gwara ke 

an san baki gida, to ni Alhaji bai ma san na fito ba” Mumy ta biya masu kudin motar suka shiga suna jiran ya cika a 

tashi….. Tagumi Mumy tayi tana kallon katon Mutumin dake gabansu, Hajiya Sadiya na xaune gefenta ita ma tana 

kallonsa, bayan kusan minti goma Mutumin yyi gyaran murya yace “Toh ga dai abubuwa da yawa na gani, masu 

kyau da mara su kyau, da farko dai da fatan a shirye kike Hajiya Maryam don nan ba da dadewa ba babban d’an ki 

xai yi aure….” Mumy ta kalli Hajiya Sadiya da sauri, sannan ta kara kallonsa tace “Aure kuma Malam?” 

Yace”Kwarai kuwa gashi na gani” Tace “Toh ni dai bai ta6a ce min komai ba….” Mutumin yace “Ita kuma wnn 

yarinya Makauniya naga abubuwa da yawa tattare da ita da nake kan ganewa har ynxu, sai dai a sarari na ga har Mai 

gidan ki na shirin fita da ita kasar waje gyaran ido, haka ne ko ba haka ba?” Mumy ta marairaice tace “Haka ne 

wllh” yace “Toh nan da kwanaki kadan xa su fita, kuma idanuwanta kam xa su bude in dai an fita… Sannan ita 

wannan kishiyar ta ki, naga a gaba xata xama ita ce kan komai a gidanki, don ynxu ma maganar da nake maki sonki 

ya ragu sosai a xuciyar mijin ki, kawai dai yana xaune ne da ke ko sbda rabon tsakanin ku, amma ynxu wnn kishiya 

ta ki ita ce gabansa, ita kadai yake gani, sannan ita salonta xa a iya kiransa da na makirci don bata wani nuna ta 

damu da shi, nan kuwa duk karya ne” Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace “Allah Malam???” Shiru yyi yana 

kallonta da tikeken hancinsa, Hajiya Sadiya ta dinga bugeta alamar me yasa tace haka, da sauri Mumy tace “Tuba nake malam ayi hakuri” Mutumin yace “Ku fita ku dawo nan da minti ashirin” Hajiya Sadiya ta mike da sauri tace 

“Toh Malam, ayi hakuri….” Mumy ma ta mike suka fita waje da sauri, saukowa suka yi daga kan rock din suka samu 

karamin rock suka xauna Mumy ta fashe da kuka sosai tace “Kin ji ko Sadiya, dama ba na gaya maki har yau ni da 

Barrister ba kamar da ba, tun da yayi auren nan dama ko nemana baya yi, Kin dai ga abinda wnn makauniyar tayi 

ma rayuwata koh? Ta dalilinta ne fa dukka wannan abubuwan ke faruwa, ita fa ta lalata min gida na, ita ta sa kishiya 

ta shigo gidana har xa a kwace gidan a hannuna, ni ynxu me xan ma yarinyar nn in ji dadi???” Hajiya Sadiya ta 

sauke ajiyar xuciya tace “Ba tuntuni nake ta bin ki mu xo nan ba kinki, yo ai Allah ma cewa yyi tashi in taimake ka, 

ga dai shi kin jiye ma kunnenki komai, Amma bari mu koma ciki tukun mu ji sauran bayanin, shi kuma Shuraim duk 

rashin maganan nan nasa har wani neman aure yake yi dama baki sani ba” Mumy ta share idonta tace “Toh ae sai yyi 

auren mu ga, xae ma ajiye xancen auren nan ne, ce masa nayi ina son yyi aure yanxu” Hajiya Sadiya tace “Toh ai shi 

na gani, duka duka nawa yake da xai tsiri son yin aure” Mumy tayi tagumi bata ce komai ba don ba batun auren 

Shuraim ya fi damunta ba ita yanxu, suna nan xaune har minti ashirin din yyi sannan suka mike suka sake 

gurgurawa can sama, Hajiya Sadiya tayi kasa da murya tace “Toh ga mu mun dawo Malam, da fatan ka huce” Bai ce 

komai ba sai bayan kusan minti biyar yace “Tohh, yanxu me ku ke son ayi a kan lamarin, ita dai wnn makauniya 

naga xata warke nan ba da dadewa ba, sannan xata xame maki ciwon ido nan gaba ke Maryam….” Mumy ta 

marairaice tace “Toh Malam ya kaga ya kamata ayi, ni so nake gaba daya ta bace bat na har abada kuwa, in son 

samu ne ma ni kada idon ya bude malam ta dauwama a makance, Kai idan ma duniyar xata bari gaba daya ni dai 

oho in daina ganinta kawai, sannan shi kuma wnn yaro nawa ayi kokarin ganin an dakatar da batun auren nasa don 

ni ban shirya aurar da shi ba yanxu, ita kuma kishiyar ayi duk abinda xa ayi ta bar min gidana da mijina, in xama ni 

kadai ce a gidan, Kuma maigidana na da uwa fitinanniya, duk ta gallabe mu, so nake ita ma a rabata da d’an nata, ko 

biyayya ya daina yi mata, snn a rufe bakinta gumm ta xama kamar kurma ko bebiye, taji kuma bata son xaman gidan 

namu ta koma can gidan wansa har abada” Mutumin yace “Toh an gama….” Hajiya Sadiya ta gyara xama tace “Ni 

kuma Malam a kara rufe min bakin mijina a kan na da, duk da dai bbu wata matsala ynxu bai jin batun kowa sai 

nawa tun aikin da kayi min kwanaki, amma a kara min wani sabo ynxu dai” Mutumin yace “Toh a bani minti sha 

biyar a waje” Mikewa duk suka yi suka gungura kasa. Sai kusan magariba Mumy ta isa gida don ma ba ita bace da 

girki, a dar dar ta shiga parlon tana boye jakarta a Hijab, ganin bbu kowa kusan da gudu tayi bangarenta ta kulle 

kofar, ganin su Rabi’ah da Khadijah xaune suna kallo parlonta ta shige bedroom tana amsa sannu da xuwan da suke 

mata… Karfe goma saura na dare Mumy ta fito, Mami ce ta fito bangaren Abba, Mumy ta dauke kai kamar bata 

ganta ba ta shiga dakinsu Sajida, tana daga tsaye bakin kofa tace “Sajida me ya hanaki wanke min bandaki yau?” 

Sajida ta mike da sauri tace “Wllh Hajiya na wanke tun da safe” Mumy tace “Toh tafi ki ga bandakin da kika wanke 

ki dawo ki sameni yanxu” Sajida ta fita dakin xuwa bangaren Mumy, Mumy na kallon Karime tayi kasa da murya 

tace “Xuwa sha daya ko sha biyu ki taho bangarena ki sameni” Karime tace “Toh Hajiya” Daga haka Mumy ta juya 

ta wuce da sauri. Mumy na parlonta xaune tana ta jiran Karime sai ga ta kuwa karfe sha daya da rabi, Karime ta 

kulle kofar ta iso kusa da ita ta durkusa tace “Ga ni Hajiya” Mumy tace “Yanxu ita makauniyar gun Rahinar take ko 

gun Kaka?” Karime ta tabe baki ta gyara xama tace “Ehh toh, yau ta kwana dakin kaka, gobe ta kwana bangaren 

Rahinar, amma dai ta fi dai xama wajen kaka” Mumy tace “Ba naga tana yawan shan shayi da, ko ta daina?” Karime 

tace “Har yau tana sha, gwangwanin kayan shayin nata ma na dakin kaka, ta sha da safe wani lkcn har da rana 

sannan ta sha da daddare” Mumy tace “toh wani aiki xan baki Allah ya sa xa ki iya Karime” Karime tace “Haba me 

xai hana, ai bbu abinda baxan iya maki ba Hajiya, ke da kika rike ni tamkar ‘yar ki, Ina xan samu haka banda wajen 

ki” Mumy tace “Toh, ba wani abu bane garin magani ne nake son ki juye a gwangwanin milon gaba daya sai ki 

gauraya, don idan an sa a madara xa a gane” Karime tace “Hajiya amma dakin kaka fa kayan shayin suke ba dakin 

uwa rikonta ba” Mumy tace “Toh sai me?? Ba tana sa ki share share ba?” Karime tace “Ta fi sa Sajida, komai Sajida 

take kira tayi mata” Mumy tayi shiru sai kuma tace “Wani aikin take sa Sajida?” Karime tace “Irin su Shara, goge 

gogen waje sai wankin bandaki” Mumy tace “Da yaushe take sa ta?” Karime tace “Da safe haka take kiranta ta saka 

ta” Mumy tace “Toh gobe kafin ma ta kirata xan aiki Sajidar, tana kiranta sai ki je kice bata nan, nan kuma xa ki 

tambayeta me xa ki yi mata” Karime tace “Toh shkkn, xan yi iya bakin kokari na Hajiya” Mumy ta mike ta tafi cikin 

dakinta sai ga ta ta fito da Kullin magani a kyallen atamfa tace “Gaba daya xaki juye kuma kiyi a hankali kar ki bari 

ya xuba” Karime ta amshe ta tura cikin rigan mamanta tace “Toh Hajiya in sha Allahu” daga haka ta fice daga parlon 

da sauri, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta kashe wutan parlon ta wuce cikin dakinta. Washegari da safe bayan Abba 

da Mami sun fita, kaka ta kwalo ma Sajida kira, Karime ta mike da sauri tana ta6a mamanta don ta tabbatar kullin na 

nan don Mumy tun safe ta sa Sajida ta bar gidan, Tana shiga dakin kaka da sallama tace “Gani kaka, Sajida an 

aiketa” Kaka ta dinga kallonta daga sama har kasa sannan tace “Ni dai na ga jaraba, wai ke baki wanka ne, kullum 

cikin naso kike kamar d’an wake, mata kazama kawai duk wari, me xa ki min to da kika taho toh?” Karime tayi kasa 

da kai tace “Na xata aiki Sajidar xata maki shine na xo in yi” Kaka tace “Ehh lallai, da kuwa lalacewa ta sameni, a 

hakan xaki kama min aiki inje wata cutar ta kama ni a banxa a hofi, wai ma daga wani kauyen kike??” Karime tayi 

kasa da kai tace “Doguwa” Kaka tace “Ko da na ji, to yi tafiyar ki, kar ki sake shigo min daki da sunan xa ki min aiki ni ba gantalalliya bace, bari Rakiyar ma ta dawo xan ji ko meye sauran amfanin ki a gidan nan tunda dai ga ni 

nan ina ma Deedayah komai, ke kuma ba sai a sallame ki ba” Karime ta juya da sauri ta fita tana waigo kaka a 

tsorace, Kaka tace “Ni naga jaraba, mata duk naso kullum fisabilillahi tayi ta shigo min daki” Heedayah dake 

kwance saman gado tace “Kaka to aiki fa xata taya ki…” Kaka ta kalli Heedayah da sauri tace “Ta je can ta taya 

uwarki Rakiya aiki, ni ba ruwana cewa ma xanyi a sallameta ko xan daina ganin fuskarta”

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *