HEEDAYA CHAPTER 15 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 15 BY By Khaleesat Haiydar

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kaka dake ta kallon Umma baki bude ta saki salati tana tafe hannu, ganin Umma ta yanke wayar bayan ta gama 

magana kaka tace “Toh yanxu dai kafin ince komai so nake a fara gaya min munafukin da ya kai maki xancen nan, 

idan kuma baxa ki gaya min ba sai in sa a kira min Umaru ya kira ki ya tambaye ki nasan shi xa ki gaya masa, don 

gaskiya idan aka ki fada min wanda ya kai gulman nan kunnen ki, toh gwara in tafi duk inda xan tafi kawai….” Kaka 

na fadin haka ta tafi daki, Mami kuma ta nufi kofar fita Umma ta bi ta a fusace tana cewa “Kema ba ina ce kina da 

d’an ba, me yasa baki dinga makala masa makauniyar ba sai ‘ya yan mutane?? To wllh daga ke har shegiyar yarinyar 

ku fita harkan d’a na….” Mami ta tsaya so pissed off tace “Look plss woman, get back home, sit ur son down, warn 

him seriously to stay away from the little girl, or from this house as a whole, you can’t just come here and be 

displaying how mad you are plss…. behave like a literate for once, this is a very simple issue to address to alone 

without u causing commotion, komawa gida xa kiyi ki kira d’an ki ki xaunar da shi ki ja masa kunne cikin nutsuwa, 

in har ya dauke ki uwa to bbu abinda xai sake kawo sa gidan nan balle ya xo gun Heedayah, amma kawai kin xo 

kina ma mutane hayagaga a gida, why not behave like the elderly lady you are?? Wnn fa ba abun tada jijiyoyin wuya 

bane, in har d’an ki na jin maganar ki to fa baxai kusanci abinda baki so ba, plsss I have very important things a 

gabana than listening to ur bull shit… So excuse me” Mami na fadin haka ta fice daga parlon, Umma da ta saki baki 

tana sauraronta ta bi ta da sauri tana cewa “Toh ai asirin da kika masa kilan baxai ta6a barin ya saurareni ba, don 

naga ba iya Barrister kadai mugun abun ki ya tsaya ba, waye bai san da asiri kika shigo gidan nan ba, kuma wa ya 

sani ko ke kika lika ma barrister makauniyar duk don ya aure ki??” Mami ko juyowa bata sake yi ba balle ta tanka ta, 

Mumy da ta bi bayan Umma ta dinga cewa “Toh ai fada ma 6ata baki ne Amina, tuni aka shaida min ta asirce 

barrister sai yanda tayi da shi, shine ta koma kan Sudais….” Mami ta bude motarta ta shiga tana answering call da ya 

shigo wayarta, Kaka ce ta fito dakinta rike da wayarta, ganin Farida rike da hannun Heedayah xa su fita parlon ta nufeta tana mika mata wayar hannunta tace “Maxa kira min Umaru, yana nan xa ki ga ansa Dakta… Yi maxa kirasa” 

Farida ta amsa ta nemo number Baffa sannan tayi dialing ta mika ma Kaka jin ya fara ring, Baffa na dagawa kaka ta 

nemi kujera ta xauna ta fashe da kuka tace “Umaru ashe dama matarka Amina gantalalliya ce bani da labari, me nayi 

mata xata xo har gida ta min wankin babban bargo don wnn yaro naka Sudess ya yo ma Deedayah tsaraba?? Ni fa na 

ce yyi mata tunda ba wai gata gareta ba kowa na mata kallon yar tsintuwa, shi kansa Amadun da ya rabota da titi har 

yau ko tsinke bai ta6a siya mata ba, shi dai ya kawota kawai ya jibge mana ita, sai Rakiya ke ta siya mata kaya duk 

da dai ita ma kayan anna take siya mata wasu guntaye kmr ta6a66iya, to laifi ne don ynxu Sudess ya mata tsaraba 

daga kasan waje?? To wllh ka taho gidan Amadu yanxun nan ka titsiye Amina sai ta gaya maka uban da ya kai mata 

rahotun an ma Deedayah tsaraba, idan ba haka ba ni gaskiya an ci mutunci na kawai an keta min rigar mutuncina” 

Baffa dake ta sauraronta yace “Ikon Allah, haka ya faru?” Kaka tace “Aa karya nayi maka” Baffa yace “A’a ba haka 

nake nufi ba kaka, kawai gani nayi….” Ta katse sa da sauri tace “Baka ga komai ba Umaru, ba ruwana da bayanin ka, 

so nake kawai ka kamo hanya ka xo ka ritsa Amina ta fadi shegen da ya kai mata gulman Sudais ya yo ma Deedayah 

tsaraba, idan ko ba haka ba to xan tattara ya nawa ya nawa in san inda dare ya min, baxan xauna a ci mun mutunci 

ba kayi shiru” Baffa ya girgixa kai yace “Toh sai na xo” Ko amsa bata basa ba ta katse wayar, ta mike ta nufi kofa da 

sauri, Tijara iri iri Umma ke ma Mami a tsakar gidan Mami taki ko da kallon inda take har Farida da Heedayah suka 

karaso gun motar, Umma na kallon Heedayah tace “In sha Allahu a makance xa ki dauwama ki kare, tunda har kika 

shigo gidan mutane kika tarwatsa farin cikin da aka gina da dadewa, lkci daya kin tarwatsa komai, ae ko xuwan ki 

familynmu sharri ne ba alkhairi ba…” A nan Mami ta kalleta tana murmushi tace “Kya ga dauwamammen makanta 

kuwa a gidanki….” Umma tayi wani shewa tace “Bakin ki ya sari danyen kashi, sai dai a gani a naki xuri’ar, mu kam 

kaf dangi daga farko har karshe bbu nakasasshe…” Muryar kaka suka ji tana cewa “Toh Amina idan kin gama ki 

shigo daga ciki ki xauna, tafiya bai ganki ba, Umaru na hanya” Mami na kallon kaka tace “Kaka sai mun dawo” 

Kaka tace “Toh a dawo lfya Rakiya, da yake ke ba xaman banxa kike ba ina xa ki samu lkcn gantalallu da ko 

sakandarin basu kare ba, ita fa Maryam iyakarta aji biyu na sakandari Amadu ya gaya min, ita kuma Amina dama ko 

makarantar Ina jin bata ta6a yi ba don ko ‘yar turancin nn ban ta6a ji tayi ba shekarata biyu gidan Umaru, kawai dai 

Allah ya ba ‘ya yana jahilai sai xuba jahilci suke a gida ba kakkautawa” Mami ta tada motarta ta nufi gate da mai 

gadi ya bude mata tuni ta fita. Baffa ne xaune parlor a gidan Abba bayan la’asar, sai Umma da kaka sannan Sudais, 

Mumy sai kai komo take a parlon kamar me yin wani abu, Baffa yyi gyaran murya yace “Da farko dai xan fara baki 

hakurin rashin xuwa da ban yi da wuri ba sbda marasa lfya da na tsaya dubawa asibiti, sannan ina kara baki hakuri 

da abinda ya faru daxu da safe….” Kaka ta ta6a baki ta rungume hannu tace “Haka dai” Baffa ya kalli Umma yace 

“Ke me ya kawo ki gidan nan daxu da safe?” Tace “Kayan da Sudais ya kawo gidan na xo amsa” Baffa yace “Wasu 

kayan?” Tace “Ai shi ya san wasu kayan ne Dr….” Kaka ta dakatar da ita tace “Kafin a je da nisa, Ina son sanin 

wanda ya gaya maki Sudess ya kawo kaya gidan nan, don banda ni sai shi sai wannan sumu sumun yaron Shureen 

bbu wanda ya sani, har ita Deedayahn bata sani ba balle uwar goyonta Rakiya, to ynda kika samu labari kawai nake 

son sani yanxu” Baffa na kallon Umma yace “A ina kika ji xancen” Umma ta d’an yi shiru na wasu seconds kafin 

tace “Shi din da bakinsa ya gaya min ba kowa ba” Kaka ta kalli Sudais da sauri tace “Wai??” Yyi kasa da kansa yyi 

shiru, har sai da Baffa ya sake cewa “Plss kar ka bata min lkci malam, I have important things” Sudais ya daga kai 

ya kalli Umma dake hararansa yace “Ehh nine” Kaka tayi tagumi tace “Toh abu ya lalace kenan ai, kai kuma ashe 

haka kake bakin ka baya haila?? me ya kai ka don ka yi abun arxiki kaje kana terere kana fada ma duniya?? Aa lallai 

Sudess ya xama abun tsoro” Baffa dai ya jinginar da kansa da kujera so pissed off da wnn batun mara amfani garesa, 

Umma tace “Don haka ynxu idan bai maido kayan can gida ba ya nemi wata uwar amma ba ni ba” Kaka na kallon 

Baffa tace “Ni kuma idan har Sudais ya maida mata kayan ta sa hannu ta amsa baka sallameta ta tafi gidansu ba ka 

nemi wata uwar ba ni ba Umaru” Baffa ya kalli Umma da ta bude baki tana kallon kaka, Kaka ta mike tace “Duk 

shawaran da aka yanke ni dai ina daki, kaya na fita daga dakina dama Amina ta fita daga gidanka, to ni ba 

gantalalliya bace” Tana fadin haka ta nufi dakinta tana cewa “Kuma duk wanda yace Deedayah xai sa ma ido sai dai 

ya mutu muruss, ni ma ba gashi gantalallen bai min tsaraba ba amma na hakura ban ma yarinyar bakin ciki ba, to 

meye wasu xa su yi mata bakin cikin tunda har na kai xuciyata nesa ni ban mata ba, da ni azzaluma ce da ba cewa 

xan yi xan kai kayan kasuwar ‘yan koli in siyar ba, amma ae bance haka ba” Baffa ya mike yace “To shawara ta rage 

kuma gare ku, but let me tell u this Amina, duk ranan da kika sake janyo na baro gun aiki unnecessary ranan won’t 

be funny for me and you” daga haka yyi ficewarsa daga parlon, Umma ta dinga kallon Sudais da idanuwanta da suka 

kankance, shi dai bai iya ya kalleta ba, can ya mike a hankali ya nufi dakin kaka, yana shigowa tace “Meye kuma ka 

biyoni? Ae tunda ka fita har waje ka dawo baka kawo min ko tsinke ba to xaka iya bada min shinkafar 6era a abinci, 

wai Deedayah, to uwar me ka hada da Deedayar bani da labari?” Ya mata wani kallo yace “Toh ki fito min da kayan” 

kaka tace “Sae dai in fito maka da Umaru, kaya kam bbu wanda ya isa ya sa in fito da shi, Allah ya tarwatsa duk me 

yi ma marainiyar nan bakin ciki” Ya fi minti uku yana ta kallonta tana harkan gabanta, can ya juya ya fice daga 

dakin ta bi sa da harara tace “Da baki kmr gidan tsutsa, sae shegen surutu kmr mace” Tsaye ya ga Umma a parlor 

tare da Mumy ko wannensu rai bbu dadi, Umma tace “Kasan Allah Aliyu, wllh ka sake shigowa gidan nan ni dai ban yafe maka ba, bbu kai bbu gidan tunda Mahaukaci ka xama, ita makauniyar kanwata ce ko ta ubanka da kayi mata 

siyayya hka, to wllh ka sake kallon ko da inda take kai da Allah…. Kaya kuma basu ci bulus ba duk ma wanda yyi 

amfani da shi Allah ya isa wllh” tana kai wa nan tayi ma Mumy sallama a fusace ta fita, Mumy na kallonsa tace “Ni 

ka ban mamaki wllh Sudais, kana da dangantaka da yar tsintuwar ne?” Yace “Ina da shi mana, ‘yar uwata ce ita 

musulma” Mumy ta hade rai tace “Ohh wato ni kake da bakin mayar ma magana koh?” Yace “Toh Mumy fisabilillah 

meye don nayi ma marainiyar tsaraba, kowa fa ina masa idan na tafi….” A fusace tace “Kana masu uban me?? Shi 

biscuits din da chocolates ne tsaraban? Ka tashi ka cika akwatuna har uku kamar me kai lefe sai kace mara mafadi, 

to gidan ma gaba daya an hana ka shigowa sae in ga ta tsiya… Yarinyar kawai matsiyaciya mara gata duk ta 

tarwatsa gida” Ya girgixa kai yace “Ae kam tana da gata….” Yana fadin haka ya nufi kofar fita daga parlon, muryar 

kaka yaji tana cewa “Ni dai ban yafe rashin tsaraban da baka min ba” ko kallonta bai yi ba har ya fice daga parlon…. 

Heedayah ce xaune garden din gidan da malamin da ke mata karatu, a final year Engineering student, baxae wuce 

ashirin da shidda ba, tana xaune saman one of the two comfortable chairs da Abba ya siyo gidan don koya mata 

karatu, shi ma malamin na xaune saman guda daya da textbook din Basic science a hannunsa, bayanin topic din da 

ya mata ranan take masa, ko tsallaka word daya bata yi ba a abinda ya koya mata, a nutse take masa bayanin, 

directly yake kallon cikin idanuwanta without even blinking, duk wannan abun Shuraim na xaune balcony a sama 

doing nothing yana kallonsu lkci lkci, shi kansa malamin bai san yana wajen ba, can dai Shuraim ya mike ya tsallaka 

gwangwanin Coke da ya ajiye wajen ko budewa bai yi ba ya fita balcony din, cikin few minutes ya shigo garden din, 

tun daga nisa idonsa ke kansu, Heedayah ta turo baki tace “Toh ban yi dai dai bane, why don’t you want to 

compliment me?” Ta fadi haka ne sbda shirun da ta ji Malamin yyi bayan ta ce masa ta gama, Malamin na hango 

Shuraim yace “Yess, that’s excellent of you, I know u can do it….” Tayi murmushinta me kyau tace “Da gaske?” 

Shuraim na isa wajen yana kallon Malamin yace “Karfe nawa kake gama lesson din?” Malamin na kallon agogo 

yace “Saura minti ashirin…” Shuraim yace “All same, akwai hadari garin you can leave now, sae da safe…..” yana 

fadin haka ya kalli Heedayah ya wani hade rai yace “Tashi” a hankali ta mike tsaye staring into space, fuska daure ya 

fixgo hannunta ya bar wajen tana biye da shi kamar xata fadi, malamin ya bi su da kallo, Suna shiga parlor ya kai ta 

har kofar dakin kaka yyi abandoning dinta sannan yyi wucewarsa sama. Heedayah ta samu dai ta bude kofar ta shiga, 

Kaka xaro ido tace “Har kun yi me??? Anya wannan yaron ba 419 yake ma Amadu ba kuwa, ba fa a titi ake tsintar 

kudin ba, me ya koya maki haka da wuri har ku ka tashi?” Heedayah ta turo baki tace “Ko ba wnn bane ya dawo da 

ni wai akwai hadari ko gama karatun ba mu yi ba” Kaka ta mike tace “Wa?” Ta yatsina fuska tace “Ni manta sunansa 

nake, wannan din nan dai” Kaka tace “Atoh ce min xa ki yi wancan sumu sumun, me yasa ku ka biye masa, 

gantalalle ne fa, lkcn yana karami baki ga kukan da yake tsalawa ba idan xa a kai sa makaranta, kwata kwata bai son 

karatun, ya fi so yyi ta xaman gida yana kassara min Amadu da kashe kudin yagwat, to shine xai maki bakin ciki 

yanxu sbda d’an turancin da kike ji?? Bakin xuciya fa garesa ci gaban ki ne baya so….” Lkci daya kaka tayi tsit ganin 

Shuraim tsaye bakin kofa don a bude Heedayah ta bar kofar, kaka tace “Toh kuma ai hadarin idan ya kare maki sai 

ya sa maki wani cuta, ni kaina fa idan ana hadari bana yarda in fita ko nan da kofa balle ke me lalura, ae da kyau da 

ya koro ki….” Heedayah ta wani turo baki tace “Kaka karya fa yake yi bbu wani hadari wllh, ai banji kamshin ruwa 

ba, kuma bbu ko wani iska kawai dae shi mugu ne….” Kaka tace “Kul…. bar ce ma baba yana karya bbu kyau, kuma 

ba mugunta bace lafiyar ki yake ji shi sa yace ki shigo kar iskan yamman ya kare maki, abinda likita ne shi ma ya 

san illan haka…..” Heedayah ta laluba gefen gado ta xauna tace “To Ina ruwansa da ni? Ko English language fa ba 

mu yi ba ya dawo da ni, kuma sae sauri yake sbda in fadi inji ciwo” Kaka ta saci kallon Shuraim dake tsaye yana 

kallon Heedayah, tace “Ke kuma ya xa ki ce haka, ubansa fa ne ya tsinto ki a titi kina galantoyi, kinga kuwa ai da 

ruwansa da ke, ni dai ki bar rashin kunya, haka kawai kina fama da makanta kina fitsara, ni ban taba ganin inda aka 

yi haka ba” Heedayah ta daura kafanta saman gadon tace “Shi ma ba yana maki fitsaran ba kullum…. Kaka gaya min 

ma yanda yake” Kaka tace “Shureen din?” Ta gyada kai, Kaka tace “Tohh, yana nan dai wani dogo kamar fal waya, 

wani lagwai lagwai, shi dai baxa a ce masa fari ba kuma baxa ace masa baki ba, Sudess ya fi sa haske, snn a tsaye 

yake bai dai kai samudawa ba, kinsan da shi da d’an uwan nasa Sudess basu da aiki da sai xuwa gidan karafe suna 

dagawa, to ynxu duk sunyi hankali, yana nan kuma da kwala kwalan idanuwa kamar dai naki, amma naki ya fi nasa 

kyau, Inda Allah ya cecesa hancinsa har baka wllh, sannan bakinsa d’an tsut, shi ke hanasa magana kila” Heedayah 

ta juya ido tace “Toh meyasa sai yyi ta cin xalin mutane, haka ranan ya doki kawata Farida” Kaka tace “Toh wnn 

kuma sai dai mu ji daga garesa, kinsan yana tsaye bakin kofa… Kai Shureen me yasa kake cin xalin al’umma” 

Heedayah ta xaro ido tana komawa baya saman gadon kamar xata yi kuka a hankali tace “Kaka yaushe ya xo?” Kaka 

tace “Tun tambayar ki na farko amma kinga ai baxai yiwu in katse maki hanxari ba tambaya ance mabudin ilimi….” 

Shuraim sai kallon Heedayah kawai yake ya rungume hannunsa, can ya gyada kai ya juya ya fita dakin, kaka ta rufe 

kofarta tace “To ni dai ba ruwana Allah ya so ban fadi wani mugun abu a kansa ba, ke kuma kar ki iya bakinki da 

surutu, wllh karya ki xai yi ba ruwana, ko kanninsa baya wasa da su duk tsoronsa suke, ke kuma gashi har ce masa 

mugu kika yi kika ce karya yake, ni dai ba ruwana” Heedayah da har hawaye ya kawo idonta tayi shiru tana sauraron 

kaka. Bayan Magrib Heedayah na dakin kaka har lkcn bata koma bangaren Mami ba, a hankali Kaka ke daukan naman kwanon gabanta tana ci kar Heedayah ta sani balle ta bata, kaka tace “Toh ko uwar ce ta hanata shigowa yau 

gaba daya bani da labari, da ta shigo fa da ynxu kinga ta gyara min daki ta goge tace xata wanke bayi, yarinyar ba 

dai tsafta ba gata yar gayu kuma kyakkyawa fara, har da lotsa kumatu gareta, naga kamar ma har waya gareta, ‘ya 

yan Amadu kuma ga su nan dai wasu kolaye kazamai, Kinga da Shureen wani ne ae sai ya nemeta nasan ko don 

Amadu Rakiya baxata ce A’a ba, to ba a auren aka aureta, shi ma Shureen din ae d’an gayu ne, fess xaka gansa 

kullum cikin kamshi, ko kadan bai son datti, kinsan ni ya gada amma ba uwarsa ba, Kuma fa wllh auren yake so, ya 

rasa yanda xai fito ya fada ne amma wnn shiru shirun da yake duk aure ya saka a rai, kinsan indai shirun namiji yyi 

yawa kawai auren nan yake so wllh” Heedayah dake gefe xaune da plate din shinkafa da miya a gabanta ta ta6e baki 

tace “Kaka ni fa na san nama kike ci wllh….” Kaka ta fiddo naman da ta kai bakinta da sauri tace “Inji ubanwa, meye 

kuma nama da xan ci in hanaki kamar wata mayya?” Heedayah tace “Ni dai nama kike ci wllh” Kaka tace “To tashi 

ki yi ma kanki jagora ki fitar min a daki kada raina ya baci, aniyar ki kuma ya bi bayanki wllh, ni ya kamata in baki 

nama ko shi Amadun da ya tsinto ki, Kuma wllh ke mace ce ki raba kanki da sa ido gidan wani xaki, meye kuma 

kinsan nama nake ci, a ina kika ga naman kina fama da makanta” Heedayah ta mike tana turo baki tana ma kanta 

jagora da hannunta ta nufi kofa xata fita, kaka ta bi ta da harara tace “Aa kifi nake ci ba nama ba tunda Amadu kika 

ga ya kawo min nama….” Dai dai nan aka bude kofar Heedayah ta ja baya da sauri, Kaka ta saki salati ta mike tace 

“Junaidu?? Allahu Akbar saukan yaushe??” yana murmushi yace “Daxu kaka….” Yana magana yana kallon 

Heedayah da ta bude ido sosai, ya daga kanta yana murmushi cikin cool voice dinsa yace “Hey….” shigewa jikinsa 

tayi ta rungume sa tace “Yaya”Junaid ya dago kanta yana murmushi yace “How are you dear?” tace “I’m fine….” Kaka na washe hakora tace “Ae da 

ka gaya min kana hanya da nayi maka girki Junaidu, ga dai yara in aika su siyo min kayan miya da yar kaza” yana 

rike da hannun Heedayah ya karasa cikin parlon ya xauna yace “Aa bana son ki wahal da kanki ne, Ina yini kaka?” 

Kaka tace “Toh lfya lau Junaidu, to ya hanya?” Yace “Alhmdllh” tace “In ji dai baxa ka sake komawa ba” yyi 

murmushi yace “Saura kadan in gama kaka” kaka tace “Toh, shima dai Sudess hka na ji yace saura kadan, Shureen 

dai ne ban san isilin karatun nasa ba, anya ma yana karatun kuwa? Gani nake kamar budirinsa kawai yake a Zaria” 

Junaid dai bai ce komai ba sai murmushi da yake yi, ta mike ta tafi dauko masa ruwa tana cewa “Toh ko ‘yar 

mantinan nan dai bbu a gidan ynxu, tunda ka tafi fa rabona da wani mantina, hana rantsuwa dai Amadu da Umaru na 

siya min” Junaid na kallon Heedayah murya can kasa yace “Lolly…” Heedayah ta wara manyan idanuwanta tace 

“Sunana Heedayah” yace “No Lolly dai” dariya tayi tace “Lolly pop?” Yace “No just lolly” ta langwabar da kanta 

bata ce komai ba, yace “Where is Farida?” Tace “Tana gun Mami” kaka ta ajiye lemo da ruwan hannunta tace “To ae 

gaba daya uwar ta hanata shigowa yau, ko ba Farida ba??? Kila don d’an aikin da take min ne ma aka hanata 

shigowa wa ya sani, kasan bata dade da xuwa hutu daga makaranta ba, shine fa muka sa6a sosai da ita, yarinya me 

hankali ga shegen aiki a cikinta, ta iya aiki yarinyar wllh” Bowl din naman da take ta ci a boye ta dauko ta dire masa tace “Daxu na sa masu aikin nan suka soya min kayana, nama ce ka ci iya cin ka ba komai ka ji” Heedayah ta turo 

baki tace “Amma kince min ba nama bane” Kaka ta galla mata wani harara tace “To meye hadina da ke? Ke dai ki 

raba kanki da kwadayi da sa ido mace kike wllh” Junaid na murmushi ya dau ruwan gora daya ya bude ya fara sha… 

A boye ya dinga ba Heedayah naman, da kaka ta shiga ciki kafin ta fito xai yanka ya sa mata a baki, da ta aji alamar 

kaka ta fito sai ta boye fuskarta shoulder dinsa, Daga karshe kaka tace “Ni dai ban ba Deedayah namana ba gaskiya, 

idan ma ci take ban bata ba gaskiya” Dariya Junaid yyi yana kallon kaka, ita kanta Heedayah dariyar take fuskarta a 

kafadarsa, kaka tace “Aa ba batun dariya bane Junaidu, ba fa Amadu ya siyo min ba balle ace tana da rabo a ciki, 

kudin da nake ta tarawa na bada a siyo min daxu, to meye xata wani makale maka tana kwadayi kai kuma kana biye 

mata? Shegen kwadayi fa gareta wllh” Heedayah ta mike tana turo baki tana ma kanta jagora ta nufi hanyar kofa 

xata fita, Kaka tace “Yanxu xuwa xata yi ta hada ni da farar matar can…” Heedayah ta bude kofar ta fita daga 

parlon…. Sai bayan isha Junaid ya shiga bangaren Mami, bayan sun gaisa Mami tace “Me ya hada kaka da 

Heedayah?” Ya kalli Heedayah dake kwance saman kujera yyi murmushi yace “Ai xa su shirya” Heedayah ta mike 

xaune tace “Ai baxan sake xuwa ba” Mami tayi murmushi bata ce komai ba, Farida dake xaune kusa da Junaid ta 

matso kusa da shi a hankali tace “Yaya tell me the truth, sbda birthday din Aunty Shaheedah ka dawo ko???” Ya 

kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Eh” Irin kallon da yake mata ya sa ta matsa kusa da shi da sauri tana 

dariya…. sai wajen karfe tara da wani abu Junaid ya mike xai bar bangaren Mami, don Kaka ta aika Sajida ta kirasa 

sau biyu kenan, Xai fita parlon Farida tace “Yaya to tsaraban mu fa?” Yace “Tomorrow in sha Allah” yana kallon 

Mami yace “Sai da safe, daga can xan wuce” tace “Me yasa idan ka xo gidan nan baka son cin abinci?” Ya girgixa 

kai yana kallon Heedayah dake kwance saman kujera tayi bacci yace “Na ci abinci kafin in taho ne” Mami tace “Toh 

shkkn, sai da safe” Ya dauke idonsa daga kan Heedayah yace “Allah ya tashe mu lfya, daga haka ya fita parlon, 

dakin kaka ya tadda Shuraim tsaye daga bakin kofa Kaka na cewa “Ai shi kansa Umarun ya girgixa da bala’i na jiya 

Shureen, ynxu kuma dama kiransa xanyi ince idan bai mata magana ta janye gantalallen bakinta da ta daura ma 

bawan Allahn ba nima xan yi Allah ya isa idan shi Umarun ya sake shigowa gidan nan gaisheni, kowa sai yyi ta 

takama da d’an sa ba shknn ba, amma kan me xata hanasa xuwa gidan nan bayan ga ni kakarsa” Tana ganin Junaid 

tace “Haba Junaidu har sai furan da nono ya huce, Amadu fa nasa sai ya siyo min, ni ban ga ji abun kunya ba ka xo 

har dakin nan ka fita baka ci komai ba” Ta gefen ido Shuraim ke kallon Junaid, Junaid ya karasa dakin ya mika masa 

hannu, Shuraim ya mika masa nasa sannan Junaid ya xauna yace “Kaka na ci abinci fa kafin na xo” kaka tace “Aa 

kai dai so kawai kke ka tafi kana xagina a ranka ka xo dakina ban baka komai ba” Dariya yyi ya ma rasa abinda xai 

ce mata, Shuraim xai juya kaka tace “Toh kaji abinda dai ake ciki Shureen, kaya kuma rabi xan ba Deedayah, sauran 

rabin gaskiya kasuwar ‘yan koli xan kai ayi gwanjonsu, to fa bai siya min komai ba ni kamar wanda aka yi ma baki, 

ko jiya sai da na sake mafarkin nan wai Sudess bai min tsaraba ba hankalina ya tashi sosai” Shuraim yace “Ae dukka 

ya kamata ki kai ki siyar” Kaka tayi shiru tana kallonsa, can tace “Allah?” Yace “Wllh” kaka tace “Atoh, me xata yi 

da su ma idan an bar mata su ita ba ido ba, iyaka in d’an debar mata biskit din da swee in ajiye mata” Shuraim yace 

“Hakan yayi” Kaka tace “Atoh, ga dai Rakiya kullum sutura take mata, bbu abinda ta ragi yarinyar da” Shuraim ya 

juya xai fita dakin sai ga Farida ta shigo rike da cooler, gefe ya ja ya tsaya, ta wuce ta ajiye ma kaka coolern tace 

“Kaka gashi Mami tace in kawo maki” Kaka tayi kasa da murya tana kallonta tace “Ita ta hanaki shigowa duk yau 

koh?” Murmushi Farida tayi tace “Aa fa kaka” kaka ta ta6e baki tace “To da ta hanaki ai ita Deedayar da take tamu 

ta shigo kuma ta wuni” Farida tace “Wllh Kaka ni ba a hanani shigowa ba kawai karatu nake yi a ciki” Kaka tace 

“Ayyoo, to ban ji kin gaida Shureen ba, ko baki gansa bane” Farida ta d’an turo baki tace “Ehh ban gansa ba” Kaka 

tace “Gashi can rakube gefe, gaishe sa” Ta d’an kalli inda yake kafin tace komai ya juya yyi ficewarsa daga dakin, 

Kaka tace “Au, to yyi ma kansa, Wai haushi yaji nan fa, kema dai in kin gansa ki dinga gaishesa” Mikewa Farida 

tayi tace “Kaka sai da safe” kaka tace “Toh sai da safe” Farida ta kara yi ma yayanta sai da safe sannan ta fita, kaka 

na kallon Junaid tace “Kai ka ji fa Junaidu, tsaraba na fitan hankali Sudess yyi ma Deedayah a kasar waje ni kuma 

ko abun sakace ban gani ba, shine nake tunanin in siyar” Junaid dake saurarenta yace “Aa kaka, ki bar mata su, kar 

ki siyar” Kaka tace “To ai ba duka xan siyar ba, sai kace wata axxaluma macuciya, ‘yan kadan xan deba in siyar in 

bar mata sauran” Furan da ta dama masa ta ajiye gabansa tace “Kaga dai ko Shureen ban yrda na dibar ma wa ba, 

kuma yana tsaye na dama wllh” Washegari da asuba Abba na dawowa daga masallaci ya ga kaka bakin kofar 

parlonsa tana jiransa, yace “Lafiya kaka?” Kaka tace “Ehh to lafiyan kenan, magana nake son yi da kai me 

muhimmanci, idan na jira sai ka shigo gaisheni bayan ka shirya fita ofiss ba saurarata xaka yi ba sai kace sauri kake” 

Bai ce komai ba ya bude mata kofar parlonsa ta shiga, ya bi bayanta, ta xauna saman kujera, tace “Kana ji na 

Amadu?” Xaunawa yyi yana kallonta yace “Ina ji Baaba” tayi kasa da murya tace “Yauwa dama kan maganan 

Shureen na shigo” yace “Lafiya dai koh?” Tace “Aa lafiya lau, na kawo shawara ne kuma kasan ni bana bada 

shawaran banxa” Ya gyada kai yana sauraronta, tace “Ni dai kaga yarinyar nan Farida ba karamin burge ni take ba 

wllh, gata da biyayya iya biyayya, sannan bata da neman fada, uwa uba ga aiki, yini fa take yi dakina tana min share 

share da goge goge, bata fiye min Deedayah ba sau dubu mai makalewa saman gado? To shine naga gaskiya d’an ka 

Shureen xai dace da ita duk da mugun halinsa, Kuma da kyar idan ba aure yake so ba, ko kai baka lura ba, a rabu da mutum me shiru shiru kawai, na ciki na ciki, toh kuma shirun ma ai baxai bari ya nemi matar auren ba, shine nake 

son ayi masa auren, na duba iya dubawa na, na gama hange hangena naga ba kowa xai dace da shi ba gaskiya sai 

Farida” Tun da ta fara magana Abba ke kallonta with surprise, Kaka tace “Aa ni dai ka daina min wnn kallon kamar 

warce tace a kashe Shureen, gata fa nayi masa, sannan Rakiya yau watana hudu da ita ko kallon banxa bata ta6a min 

ba, kwata kwata matar bata da damuwa kaf halinta d’an ta Junaidu ya kwashe, wayayyiyar mata ce sosai, to don me 

baxan yi kwadayin hada iri da ita ba…” Abba yace “Toh yanxu kaka ni da ba wai ina da iko da Farida bane, ya kike 

son…” Kaka ta dakatar da shi tace “Aa wllh kai mijin uwarta ce ai, kuma ai a gidan ka take yanxu” yace “Yaushe ta 

dawo gidan nawa? Ba hutun makarantar kwana da suka yi bane ya sa ta xo? Gidan yayan babanta take fa Baaba” 

Kaka tace “Toh ni ba ruwana sai in saka gyale a rakani gidan yayan uban nata, Kai sai kayi ta yin abu kamar ba 

namiji ba meye kuma don ka nema ma d’an ka auren Farida? Ni fa gata nake son yi ma Shureen din don baya 

magana kuma ni na san aure yake so, kaga kira min Rakiyan yanxun nan ta xo ayita ta kare, Kar ka wani bata min 

rai” Abba yyi kasa da murya yace “Karatu fa yarinyar take kaka, duka duka ss2 nake jin take yanxu” Kaka tace “To 

ko Jami’a take ni ina ruwana, karatu na hana aure ne dama bani da labari, ku dai kun cika wahala wllh, cewa nayi ka 

kira min Rakiyan ta fito, in dai aka ga Shureen bai auri Farida ba to kilan kashe ni ku ka yi kawai” Abba ya kasa 

cewa komai, kaka tace “To ko in kira Rakiyan da kai na ne Amadu?” Daukar wayarsa yyi, yyi dialing number Mami, 

tana dagawa yace “Meet me at my parlor now Rahinah” Bai jira ta ce komai ba ya katse wayar…. Da sallama Mami 

ta shigo parlon, ganin kaka ta xauna kasa tace “Ina kwana kaka?” Kaka ta washe hakora tace “Lafiya lau Rakiya, ya 

kwanan su Deedayah da Farida?” Mami tace “Alhmdllh” Abba dai bai ce komai ba, Mami na kallonsa tace “Ga ni 

barrister” Ya kalli kaka yace “Ga ta kaka” Kaka tace “Kai Amadun nan dai wani solobiyo ne wllh, to kai baxa ka yi 

mata bayanin ba sai ni? To ai duk kai ka cuci Shureen don kaf halinka ya dauka amma banda mugun halin shi wnn 

na uwarsa ne, Rakiya kina ji na, ba wani abu bane dama ni dai Farida ce ta kwanta min can cikin raina, a gaskiya Ina 

son yarinyar wllh, shine na xo na samu Amadu Ina neman alfarman a ba ma jikana Shureen aurenta….” Tana kai wa 

nan ta fara matsar kwalla, Mami da ta bude baki tana kallonta with shock ta kalli Abba tace “I don’t get her barrister, 

as in??” Abba ya sauke ajiyar xuciya bai ce komai ba dai, Mami tayi murmushin karfin hali tace “To kaka ai karatu 

Farida take yi yanxu, Kuma…..” Kaka ta dakatar da ita tace “Kuma me? Ku dai gantalallu ne marasu mafada, karatu 

ance maku yana hana aure ne, kinga idan na biye ta taku kawai mahakuciya xaku mayar da ni, ni naga dacewan 

hakan shi yasa nace ayi, ynxu ni ba ni da wata magana da ku kuma….” Tana fadin haka ta mike ta fita parlon, Abba 

sai kallon Mami da gaba daya mood dinta ya canxa lkci daya yake, can tace “Plss Barrister kayi ma kaka magana, 

try to let her understand cewar ba mai yiwuwa bane ni bani da iko da Farida wajen yayan Mahaifin ta take, let not 

make things complicated pls Barrister” shi dai bai ce mata komai ba, kaka na fita dama wayarta ta dauka ta lallaba ta 

kai ma Farida can bangaren Mami wai ta kira mata Junaid, junaid na daga kiran kaka ta fita da sauri, tayi kasa da 

murya suka gaisa tace “Kana ji na Junaidu, duk Inda kake ka taho yanxun nan xaka kai ni anguwa ko Rakiya kar ka 

sanar ma, kana isowa bakin get ka kirani sai in fito” Junaid dake kwance yace “Toh bari in taho kaka” tace “Yauwa 

Allah maka albarka, Ina jiran ka yanxun nan” daga haka ta katse wayar ta wuce dakinta tana cewa “Gantalallu wa 

enda basa son abun arxiki, ni bana biye ta taku ba” Kaka na komawa bangarenta sai ga Abba ya shigo da sallama, ya 

xauna saman kujera gaba daya he look confused, can yace “Kaka yanxu kinga cikin watan nan xa a fitar da 

Heedayah waje gyaran idonta, so yanxu kinga ai babu wani abu a gabanmu da ya wuce wnn…” Kaka tayi saurin 

cewa “Haba?? Kuma sun ce idon xai gyaru kuwa? Amma dai da ni xa a je koh? Kasan bata da kowa sai Allah sai ni” 

Abba yace “In sha Allah….” Kaka tace “Toh yaushe ne tafiyan in fara hada kayana?” Yace “Nan dai da sati uku” 

Kaka tace “Atoh Allah ya kai mu lafiya, Allah ya dubemu idonta ya bude ni dai” Abba yyi kasa da murya yace “Don 

haka kaka ki bar ko wani xance yanxu mu ji da gyaran idon da xa a fita yi” kaka ta kallesa tace “Atoh shkkn na bar 

xancen har sai idon Deedayata ya bude” Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, ya mike yace “Bari in je kaka, 

a taya mu da addu’a, ana kan processing din fitan ne” kaka tace “To wani kasar xa aje?” Yace “India” kaka ta washe 

baki tace “Xa mu ga su Hamita da muganbo kenan Amadu??” murmushi kawai Abba yyi ya fita daga dakin kaka ta 

mike ta daga hannu sama tace “Allah ka dubi yar marainiyar Allah ka bude mata idanuwanta, ka bude mata ido ya 

Allah ko son jikinta xai ragu” Karfe takwas dot Junaid ya kira kaka yace yana kofar gida, ta dau Hijabinta ta boye ta 

fito parlor tana kalle kalle xata fita, Shuraim dake xaune dinning yana shan tea ya bi ta da ido har ta fice daga parlon 

da sauri, Junaid ya sakko ya bude mata back seat yana gaisheta da ladabi, ta amsa tana washe baki tace “Allah yayi 

maka albarka Junaidu da bani da kai ai da nayi kuka yau, ni dai wllh ka fiye min kowa ma” murmushi kawai yyi ya 

tada motar, sai da suka bar layin suka hau saman titi yace “Ina xa mu kaka?” Tayi kasa da murya tace “Yau xumunci 

kawai nake son yi, kaga ai bai dace ace har yanxu ban san kowa naku ba, to don haka gidan yayan Mahaifin ka xaka 

kai ni mu san juna” Junaid was so surprise ya dinga kallonta ta madubi yace “Gidan Baffanmu?” Kaka tace “Ehh shi, 

ai xa a samesa yanxu da safe koh?” Yace “Ehh na bar sa a gida” Kaka tace “To maxa kai ni kar yyi ficewarsa, gwara 

xumuntakar tamu yyi karfi” murmushi kawai Junaid yyi ya dau hanyar gidan yayan late Abbansa.

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *