HEEDAYA CHAPTER 14 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 14 BY By Khaleesat Haiydar

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

3months later….

Kaka ce tsaye kan Khadijah inda take shiga ba nan take fita ba, Khadijah sai turo baki take tana yatsina fuska, Haka 

Rabi’ah dake tsaye bakin kofar parlon Mumy, Kaka tace “Yar banxa kawai me bakar fuska kazama, mummuna, ni 

dai wllh da ba don ina asibitin aka haife ki ba ma cewa xanyi ke ba ‘yar Amadu bace canje aka masa, dama hutun da 

suka baku a makarantar cewa suka yi ku dawo gida ku dinga yi ma babban ku rashin kunya ban sani ba?” A fusace 

Khadijah tace “To wai ni kaka me nayi maki ne, ni kadai ne kika gani a parlon nan….” Kaka tace “Wllh Sudess xan 

kira yanxun nan ya casa min ke idan kika kara xagina, kawai don yarinya Allah ya yo ta makauniya sai ki juye mata 

shayin da take sha ki dura ruwa a kofin saboda bakin hali ko me? Sannan wannan yarinya Farida ta maki magana 

xaki hau ta da dambe kamar ‘yar da6a? To bari yanxun nan xa a kira min Sudess, Allah ya rufa min asiri ya dawo 

shekaranjiya ai da lalacewa ta sameni” Khadijah ta fashe da kuka tace “To ita faridar Ina ruwanta da ni xata tsoma 

min baki?” Kaka tace “Aa wllh da ruwanta, bayan ni da uwarta Rakiya akwai me son Deedayah ne a gidan nan, to 

sai kilan Amadu duk da bamu san xuciyarsa ba, nan nan nan uwarki ta cakali Rakiya da fitina jiya Rakiya ta ki 

kulata, Farida kuma duk da dai agola ce a gidan bata fiye min ku ba sau dubu, Aa wllh ta fiye min ku, Maryam dai 

jaraba kawai ta haifa matsayin ‘ya ya, idan ma bakin ciki kike faridar ta fi ki kyau ne ai sai ki fito ki fada in sa 

Amadu ya samar maki ko ‘yar man kanti ne ki shafa kiyi hasken” Khadijah ta mike fuuu tayi wucewarta bangaren 

Mumy tana cewa “Gobe ta sake saka baki a harkana wllh wllh sai na mata dukan tsiya na farfasa mata baki” Farida 

dake tsaye bakin kofar Mami tare da Heedayah da ta rike rigar faridan, ta tabe baki tace “Toh ba sai ki dokeni ba, 

wllh karya ki xan yi….” A fusace Khadijah ta nufo Farida gadan gadan, kaka ta shiga kwala ba isiya kira da karfi, dai 

dai shigowar Shuraim parlon, Kaka ta fashe da kuka sosai tace “Shkkn kuma ni don mijina ya mutu ya barni bani da 

gata sai a ajiyeni a gida daga safe har dare ina ra6on katti yara fada, shi Amadu ya fita neman na xuba ma bakin 

salati, ita kuma wnn kinibabbiyar xabiyar ta bi sa ita ma aikin, uwarka kuma gantalalliya suna fita ta tafi gantali ita 

ma, wllh tun fitan iyayen suke dambe kamar raguna har an ji ma TVn Amadu, yanxu da baka dawo daga Zaria ba ya 

xanyi da raina yau, da gangan malam suka basu hutu don su kashe ni….” Shuraim ya kalli Farida da ta wani turo 

baki, ya kalli Khadijah da ta koma kofar parlon Mumy da gudu, ya karaso cikin parlon yace “Ku dawo nan gaba 

dayan ku” ko rufe baki bai yi ba Farida ta ja Heedayah suka shige parlon Mami ta sa makulli, Khadijah ta marairaice 

sanin in har ta shiga ya bi ta to mai kwatar ta sai Allah, Rabi’ah dake makale kofar ita ma tace “Allah ya so ni dai…” 

Kaka tace “Wa??? Ai kece katuwar munafukar ke ke sa Khadijah tayi komai, duk bakin ki daya” Rabi’ah ta fashe da 

kuka sosai tana kallon kaka, Shuraim ya hade rai yace “Baxa ku dawo nan ba nace” Khadijah ta Rabi’ah suka fito 

main parlon suna matsar kwalla, Cikin rawar murya Khadijah tace “To ita Farida fa Yaya” buge bakinta yyi, kaka 

tace “Ai ba kyaleta xa ayi ba, abinda ba tsoron ta yake ba” Da wayar rechargeable ya xane su a tafin hannunsu gaba 

daya, yayi wucewarsa dakinsa, Kaka da tayi tagumi tace “Dama dai neman wanda xai duka yake tun daga Zaria, 

Banda haka ga dai katti sa’anninsa a titi ya baro ya shigo gida ya ci xali, ku dai kuyi hakuri ku bar sa da Allah kawai” 

Rabi’ah da ke kuka sosai ta dinga hararan kaka, Khadijah na Shessheka tace “To mu kadai xai doka, ita faridan fa” 

kaka tace “Waye ubanta da baxa a doketa ba tunda aka doke ku, ai yanda yyi maku haka xai mata ba cuta” Rabi’ah 

tace “To Heedayah fa?” Kaka ta kalleta da sauri tace “Aa ke kuma baki son gaskiya, waye kuma Heedayah? Me tayi 

xa a doketa, to ko ma tayi in dai shi ba wawa bane akan me xai doketa, ko kula ku kinga tana yi a gidan nan, to ai ita 

ba gantalalliya bace kamar ku” Khadijah ta mike tana hararan Kaka ta wuce part din Mumy, Rabi’ah ta ja tsaki ta 

mike ta bi bayan Khadijah, kaka tace “Oho dai an dai sha mazga” Farida ta ja tsaki tace “Haka xa mu yi ta xama 

kenan baxa mu ci abinci ba, ni dai baxan sha cornflakes ba” Heedayah dake shan cornflakes dinta ta ta6e baki tace 

“Ni ina ruwana, wnn da kike ganinsa din nan mugu ne, wllh duka xai maki in kika fita” Farida tace “To a ina ya san 

ni da xai dokeni? And ni fa Ina ce shine Sudais” Heedayah tace “Aa ba Yayana bane, wannan Ya Shuraim kamar naji 

suna ce masa, I never liked him even for once” Farida tace “To da ina yake tun da na xo ban gansa ba” Heedayah 

tace “Ban san Inda yake ba, but yana dawowa every Saturday” Farida ta ta6e baki tace “To kawai bai san ni ba sai ya 

dokeni” Heedayah tayi dariya tace “That’s because he is wicked” mikewa Farida tayi tace “To kinga mu lallaba mu 

je in xubo mana” Heedayah tace “Ni baxan je ba” Farida tace “Plss mana I can’t go alone, da sauri fa xan xuba mana 

mu dawo” Heedayah ta juya manyan idanuwanta tace “To ki jira in gama shan Cornflakes dina” Farida tayi tagumi 

tace “Tohh” Heedayah na gama shan Cornflakes din Farida ta ja ta suka fita main parlor, bbu kowa parlon sai Tv 

dake kunne, Farida na rike da hannunta suka shige kitchen da sauri ta kulle kofar, Sajida da Karime ne suka yi lunch 

a gidan, Farida ta bude warmer da abincin ke ciki ta debi shinkafa knn xata bude na miya aka bude kofar kitchen 

din, Shuraim ne ya shigo da wayar rechargeable a hannunsa, tana ganinsa ta fasa ihu ta saki murfin warmer din 

hannunta, Heedayah ta ja gefe a tsorace, cafkota yyi, ta rikesa tana basa hakuri a tsorace, Bai ko saurareta ba ya rike 

hannunta ya dinga lafta mata wayar hannunsa, Kaka ta shigo kitchen din a guje tana cewa “Wayyoo wllh uwarta 

lauya ce daure ka xata sa ayi shureen, idan ka doke wasu ka kwana lafiya to ita wllh a seff xaka kwana bbu me ceton 

ka, yau fa kwananta hudu da xuwa gidan, ta dawo daga tsadadden makarantar kwanan nan, duk da dai fitinanniya ce 

ai tayi min wanki yau kuma ta wanke min bandaki, ko da yake jika jika tayi amma ai tafi munanan kanninka…” Sai 

da Shuraim ya lafta mata son ransa sannan ya saketa, ta durkusa a wajen ta dinga ihu tana kiran Mami, ya kalli Heedayah da ta rakube gefe daya a tsorace hawaye cike idonta, ya nufeta fuska daure kaka ta dakata da surutan da 

take ta shige gabansa tace “Aa nan kuma ne xan sa ‘yan anguwa su lallasa min kai, uban me xaka mata?? Ai wllh 

idan ka doki gantalallun nan ka kwana lafiya to kana ta6a Deedayah maka ka xanyi a kotu, me makauniyar tayi 

maka, duk da dai ita ma ba kyalle bace” kallon kaka kawai yake fuska daure, ta kama hannun Heedayah ta fice daga 

kitchen din tana cewa “Ni dai ba ruwana” Farida ta wani hararesa ta mike xata bi bayansu, xai cafkota ta fice a guje 

ta shige dakin kaka… Uku saura Mumy ta dawo gidan, su Rabi’ah suka tsara mata abinda ya faru da safe, tayi shiru 

tana sauraron su, can tace “Tafi maxa ki kira min Shuraim din” Khadijah ta kwanta saman gado tace “Tabbbb” 

Rabi’ah tace “Ni dai kar ma kiyi masa magana Mumy, wllh dukan mu kawai xai kara yi” Karime ce ta shigo parlon, 

Mumy tana kallon su Khadijah tace “Ku fita” duk suka mike suka fita, Karime ta xauna kasa tana ta6a baki tace 

“Hajiya ji nayi daxu a waya tana gaya ma wani wai an kusa fita da Heedayan waje ayi mata aikin idon…” Mumy ta 

gwalo ido tace “Haba??” Karime tace “Wllh kuwa haka na ji….” Mumy ta gyara xama tace “Wa kika ji tace xai fita 

da ita?” Karime tace “Wannan ne ban sani ba Hajiya” Mumy tace “Har dai yanxu baki san Inda kaka ke boye 

maganin nata ba ko?” Karime tace “Ai yanxu kaka ta ma daina sa ni gyaran dakinta, Sajida ce ke yi” Mumy tace 

“Toh watan barin gidan Sajida ya tsaya” Karime tace “Wllh daxu da safe kafin Hajiyar ma ta fita aiki ga dai ni a 

xaune amma Sajida ta sa taje dakinta ta dauko mata makullin mota, ni ta ma daina bari in shiga dakinta ynxu….” 

Mumy tace “Akwai wani aikin da xan baki yanxu, kuma in sha Allahu idan kika yi kokari kika cika aikin, dubu 

biyar xan baki kyauta…” Karime ta washe hakora tace “Hajiya ai ko baxa ki ban komai ba….” Bude kofar parlon da 

aka yi yasa duk suka yi tsit, Shuraim ne ya shigo da sallama, fuska daure Mumy tace “Wannan ai walakanci ne, ayi 

shinkafa dafaduka jiya, yau kuma ayi shinkafa da miya, tunda Sajidar tace maki baxata yi ba ke ba sai kiyi ba…” 

Juyawa Shuraim yyi xai fita Mumy tace “Ina kuma xa ka?” Yace “Naga kuna magana ne ai” Mumy tace “Kawai 

masu aikin jaraba suyi ta sa mutum magana, suna ba mutum wahala” Bai ce komai ba shi dai ya fita, Karime ta kalli 

Mumy, Mumy tayi kasa da murya tace “Yaushe ya xo?” Karime tace “Tun safe” Mumy tace “Tashi ki tafi xan neme 

ki anjima” Mikewa tayi ta fita… Kaka nata aikin linke linke a dakinta, Farida na dakin tana taya ta, Kaka tace “Toh 

dama idan ba ke ba waye xai taya ni, ita wancan makauniyar ba wai amfani gareta ba” Heedayah dake kwance tayi 

rub da ciki tana jin kaka bata dai juyo ba, Farida tace “Kaka wai shi ma a nan gidan yake xama?” Kaka tace “Wa?” 

Farida tace “Wannan da ya doke mu mana” juyawa Heedayah tayi daga kwancen da take tana kallon direction din da 

take jin muryarsu, kaka tace “A’a yana can Zaria yana karo karatu, ko massers naji suna kiran karatun, kinsan bbu 

yanda ba ayi da shi ya fita waje kamar yanda Sudess yaje can yake yi ba amma ya ki, uwarsa kuwa kamar tayi hauka 

don ta kwallafa ran fitansa, kin santa da fafa, so tayi ta bi duk kawayenta tace d’an ta na kasar waje yana karatu, to 

da yake shi ma Amadun kila ba wani son kashe kudi yake ba ya goya masa baya kar ya fita, duk sati kya gansa 

salalo salalo wai ya xo gida hutu, duk ya bi ya takure jama’ah….” Bude kofar dakin aka yi sai ga Shuraim, Farida ta 

juya da sauri ta ci gaba da linkin da take, kaka tace “D’an Halak, yanxun nan take tambayata uban me ke dawo da 

kai gida, shine nake bata labari” da sauri Farida tace “Ni fa ba shi nake tambayar ki ba….” Tana fadin haka ta nufi 

kofa ta fita ya bi ta da kallon gefen ido, ya kalli Heedayah dake kwance, kaka tace “Ka ji wai ita kuma yau bata son 

tayi karatun, kuma duk inda malamin yake nasan yanxu yana hanya, dubu ashirin da biyar haka Amadu ke biyansa 

duk wata, to banda Allah wa xai biya mu, bbu fa abinda muka hada da ita…..” Heedayah ta mike xaune tana sauraron 

kaka kamar xata yi kuka, kaka tace “Kasan idan ba mutum ke biya ma kansa ba sai yyi ta iskanci iri iri, sai ka ga 

uban tsaraban da Sudess ya yo mata daga kasar turawa, ni tsoro ma kamani yyi wllh, ni dama ko tsinke shegen bai 

kawo min ba, shi kuma Junaidu daxu ya kirani wai nan da sati xai dawo har yace in bata suka dade kuwa suna waya, 

ko kanwarsa bai ce in ba ma ba, ita kuma Khadijah daxu….” Shuraim ya dakatar da ita yace “Ina tsaraban??” Kaka 

tace “Ae baxa su dauku ba Shureen” yace “Suna ina?” Mikewa Heedayah tayi a hankali tana laluba hanya xata fita 

kaka tace “Ji algunguma, Ina kuma xaki, kinji nace xan dau kayanki ne da xaki wani mike xaki fita??” Shuraim dai 

sae kallon dakin yake yana neman kayan…..

Ta gefen ido Shuraim ya dinga kallon Heedayah dake kokarin fita ya ga ko xata ta6a sa, she was so careful ko kusa 

da shi bata bi ba har ta fita dakin, kaka tace “Ni sae nake ga kamar karyar makanta take yi, ynxu a hka fa sai ta fita 

har tsakar gida” Shuraim yace “Ina kayan?” Kaka tace “Naga jaraba, Ina ruwanka da kaya Shureen? Tun daxu ka 

isheni ina kaya to kai aka kawo ma kayan? Kayan me xaka dameni haka, Komai fa na da sirri, ba ruwana ni ba ‘yar 

cin amana bace, Bai ce in nuna ma kowa ba har Amadun balle kai karan kada miya….” Wani kallo yyi mata ya juya 

ya fice daga dakin…. Turuss Khadijah tayi rike da bucket din ruwan kumfa a hannunta, ya kalli direction din da 

take kokarin xuwa da sauri, Heedayah ce har sannan bata isa bangaren Mami ba tana tafiya a hankali kuma very 

careful, ya kalli Khadijah da tayi wuri wuri da ido, da sauri ta juya xata koma Inda ta fito, ya bi bayanta tana ganin 

haka ta sake bucket din hannunta a rikice, ya ja baya da sauri ganin ruwan kumfan ya malale kasan tiles bai ankara 

ba sai gani yyi tayi sama sannan aka nanota kasa da karfi, wani ihu tayi can kasa makoshi, ya ma rasa ko dariya xai 

yi ko d’aga ta xai je yyi, ta kwalo ma Mumy kira tana cewa Wayyo bayanta, yana jin hka ya kalli Heedayah da har ta 

kai kofar parlon Mami ta tsaya, Farida ma ta fito da sauri don ganin me ya faru, Shuraim na jin Mumy ta bude 

kofarta xata fito tun bata karaso ba tana tambayar lafiya me ya faru, yyi saurin shigewa dakin kaka ya rufe kofar. 

Farida ta ja Heedayah suka shige ciki ta kulle kofa. Bayan isha Farida na parlon Mami da Heedayah, Mami kuma ta 

je kai ma Abba abinci aka bude kofa Sudais ya shigo da sallama, daga kai Heedayah tayi tana kallon ta Inda ta ji 

muryar sa, da farko Farida ta xata Shuraim ne sai kuma ta ga wannan ya fi Shuraim haske, Ta gaishesa ya amsa yana 

murmushi yace “Ya kike?” Tace “Lafiya lau” ya xauna yana facing din su idonsa a kan Heedayah yace “Ba gaisuwa 

Deedayan kaka” Heedayah ta jinginar da kanta da kujera tace “Ni ba Deedayah bace” yace “To ya sunan?” Ta 

langwabar da kai tace “Ina yini” yace “Lafiya lau Cutie, ya karatun kuna ta yi koh? And kina ganewa?” Ta gyada 

masa kai, ya kalli Farida yace “Ya sunan ki ‘yan mata?” tace “Farida” yace “Ban ta6a ganin ki nan ba Farida, though 

Naga kuna kama da Junaid” Farida tayi murmushi tace “Ehh na xo hutu ne kawai” yace “Wani makarantar kike?” 

Tace “Nigerian Turkish….” Yace “Boarding?” Ta gyada masa kai, yace “Maa sha Allah” Heedayah tace “Yayana 

baxa ka sake komawa UK ba koh?” Yace “Idan ma xan koma tare xa mu koma ae” Ta wara ido tace “Da gaske?” 

Yace “Ehh mana sai in gaya ma su Abba da Kaka su bani ke, kowa ya shaida sannan mu wuce” Murmushi tayi tace 

“To kayi masu magana plss” yace “Da gaske dai xa ki bi ni? Xamu dade fa bamu dawo ba” tace “Allah xan bi ka” 

yana murmushi yace “Toh shkkn” Bude kofa aka yi Rabi’ah ta leko fuska daure tace “Ya Sudais kaka na kiran ka” ya 

kalleta kafin yace komai tayi banging kofar ta wuce, Farida tayi kwafa can kasa kasa, mikewa yayi yace “I’m 

coming back….” A hankali Heedayah tace “No chocolates?” Ya kalleta yyi murmushi yace “Sai na dawo” daga haka 

ya fita, Farida tace “Ke da kike cewa xa ki bisa ke matarsa ce?” Heedayah tace “To ba Yayana bane” Sudais na tsaye 

yana sauraron abinda kaka ke cewa, can yace “Toh yanxu me kike nufi?” Tace “Ina nufin in har baka bani nawa 

tsaraban ba wllh baxan bata ba, gwara in kwashi tarkacen da ka kawo in kai kasuwar ‘yan koli in siyar, haka kawai 

daga ganin sarkin pawa sai miya tayi xaki, uwar me ma ka hada da ita bani da labari, duk wahalan da nayi da kai 

kana karami ka dawo daga kasashen turai ko abun sakace hakuri baka kawo min ba sai yar tsintuwa” dai dai nan 

Shuraim ya shigo dakin da ledan fruits da Abba ya sa ya siyo mata, Sudais ya kallesa sannan ya ci gaba da sauraron 

kaka, Shuraim na ajiye ledan tace “Shureen tunda muke da kai ka ta6a fita kasar waje ka dawo baka min tsaraba ba, 

ko nan nan da Zaria idan kaje ai kana siyo min ‘yar lemon nan” Shuraim na kallonta ya ciro wayarsa dake vibrate a 

aljihu, kaka tace “Toh don me Sudess xai fita ya dawo min haka sai wata can wai Deedayah xai kwaso ma kaya iri 

iri kamar kanwar ubansa” Sudais yace “Saboda ta fiye min ke” shiru kaka tayi tana kallonsa a bit shock, yace “Kuma 

ki fito da kayan in kai mata yanxu” Kaka tace “Al-qur’an kasuwan ‘yan koli xan kai su gobe da sassafe, idan na baka 

in tafi a karkace, Deedayar kanwar ubanka ce ko ta uwarka?? Waye kuma Deedayah? Me na hada da ita banda dai 

d’a na ya tsinto mana ita” Sai kuma ta xauna ta fashe da kuka tace “Ehh lallai karshen duniya ta kankama” Juyawa 

Sudais yyi ya fita daga dakin, Kaka ta kalli Shuraim tana matsar kwalla tace “Ka dai ga ko Shureen?? Hakan da 

Sudess ya min ya kyauta” Yace “Ni baxan ce komai ba sai na ga kayan” Babu wata wata Kaka ta dauko makulli da 

sauri ta bude gun ajiye kayanta ta fiddo akwatunan har biyu da karamin jaka, kallonsu kawai Shuraim yake, ta xuge 

jakar ta shiga fiddo abubuwan ciki, cikin lkci kadan ta fiddo komai ta bajesa a gaban Shuraim tana kallonsa, Kallon 

kayan kawai Shuraim yake, beautiful English wears, teddie bears, biscuits, dolls, chocolates, sweets, shoes, har da 

jewelries, Shuraim ya dauke idonsa daga kan kayan, kaka na matsar kwalla tace “Ka dai gani ko, ni fa na haifi 

ubansa Umaru” Mikewa Shuraim yyi bai ce mata komai ba ya fice daga dakin… Ta bi sa da kallo baki bude sai kuma 

tace “Toh Allah ya isa” Sudais na komawa parlon Mami, Mami dake xaune parlor tace “Mutan UK, sai yau muka 

hadu” Ya gaisheta yana murmushi yace “Jiya da na xo kina gun aiki” Mami tace “Ehh ina can, ya karatun kun gama 

kuwa?” Yace “A’a saura kadan” Mami tace “Maa sha Allah, Allah ya sa a gama a sa’a, ya su Hajiyar ku?” Yace “Suna 

lafiya gaba daya” Tace “To maa sha Allah, a xubo abinci?” Yace “A’a na ci” ta mike tace “To yayi kyau” bedroom 

dinta ta shiga ya kalli Heedayah ya koma kusa da ita yace “Ina kawar ki Farida?” Tace “Ta tafi wanke wanke a 

kitchen” Sudais yace “Masu aiki fa?” Heedayah tace “Mami ce tace taje ta yi” Yace “Ohkk” ta matso kusa da shi a 

hankali ta laluba hannunsa tace “Yaya kasan me?” Ya kalli kofar dakin Mami sannan ya hade forehead dinsa da nata 

yace “No…” Tace “Yau ina son in sha ice cream” yace “Ice cream?” Ta gyada masa kai, yace “Ohk bari Farida ta gama wanke wanke sai mu je gaba daya” Tayi murmushi tace “Nagode” Farida na shigowa yace “Farida tell Mami 

xa mu je siyo abu yanxu, with you and Heedayah” tace “Ohkk” daga haka ta shiga bedroom din Mami, ba a dau lkci 

ba ta fito da Hijab dinta da na Heedayah tace “Mami tace alright” sosai Heedayah ta ji dadi, ya amshi Hijab din ya sa 

mata sannan ya daga ta holding her hands suka fita parlon tare da Farida, Shuraim na xaune parlor shi kadai, tun da 

ya kallesu sau daya ya dauke kai har suka fita parlon…. Wani wajen shan ice cream Sudais ya kai su, yyi parking ya 

sauka motar, ya bude ma Heedayah back seat yana rike da hannunta ta sauka, Farida ma ta fito daga front seat da ta 

xauna, Sudais na rike da hannun Heedayah da ta makalesa suka shiga ice cream parlor din, Ya duka dai dai kunnenta 

yace “Wani irin ice cream kike so?” Tace “Vanilla” ya kalli Farida dake kallonsu yace “Ke fa Aunty Farida?” Tayi 

‘yar dariya tace “Irinsa nima” Wani mutumi ne xaune wajen da roban ice cream a gabansa, su uku ne xaune a round 

table din, all wearing glasses, tun da suka shigo yake kallonsu ta bak’in glass din idonsa, Sudais ya biya kudin ice 

cream da ya siya masu yana rike da hannun Heedayah ya nufi kofar fita Farida na biye da shi, mikewa Mutumin yyi 

ya dau makullin motarsa, wanda ke kusa da shi ya kamo hannunsa murya can kasa yace “Hey… ina kuma xaka? 

Ynxu fa xa su gama su fita…” Ba tare da Mutumin ya kallesa ba yace “Ina xuwa ynxu” daya Mutumin yace “Noo 

this is our only chance….” Ya fixge hannunsa ya fita da sauri, Sudais ya kulle motarsa kenan bayan ya sa Heedayah 

ciki ya bude maxaunin driver ya shiga yana kallon Farida dake gaban motar yace “Did you need anything again 

Farida?” Tace “Aa mun gode” tada motar yyi yayi reverse, Mutumin da tuni shi ma ya shiga motarsa ya bi bayansa, 

mota daya ne interval tsakaninsu, Mutumin ya dinga kokarin ganin yyi over taking motar har suka kusa traffic, 

Sudais na tsallaka wajen traffic din ya nuna red, hakan ya sa motar dake bayansa ya tsaya, Mutumin ya jinginar da 

kansa da kujera ganin motar Sudais yyi nisa sosai… Sudais na parking a kofar gida ya bude ma Heedayah back seat 

ya sakko da ita, Farida na rike da ledan ice cream din suka wuce ciki, har sannan Shuraim na xaune main parlor, 

wannan karan kallon gefen ido yyi masu, Sudais ya duka kusa da Heedayah yace “Sai da safe, I am going home 

now” tace “Xaka xo gobe?” Yace “In sha Allah” tace “Haka kace jiya kuma baka xo ba” yace “Ba gashi na xo yau 

ba” tace “Toh byee” ya ja hancinta a hankali yace “Bye” Farida ma tayi masa sai da safe tana rike da hannun 

Heedayah suka wuce bangaren Mami, Sudais na kallon Shuraim yace “Sai da safe bokan turai” Shuraim na danna 

wayarsa yace “Allah ya tashe mu lfya” Sudais ya juya ya fita parlon… Washegari karfe tara saura Hajiya Amina 

mahaifiyar Sudais ta shigo gidan, Khadijah na xaune dinning suna breakfast da Rabi’ah, duk suka gaisheta suna mata 

sannu da xuwa, ta nufi dining din tana kallonsu murya can kasa tace “Abba na nan??” Rabi’ah tace “Aa ya fita” 

Umma tace “Hajiya Maryam fa?” Khadijah tace “tana daki” Umma ya nufi bangaren Mumy ta bude kofar ta shiga, 

bbu kowa parlon haka yasa ta wuce daki, Mumy ta katse wayar da take yi da sauri tana cewa “Waye??” Umma tace 

“Ni ce Maryam” Mumy tace “Aa Amina, daga ina da safe haka?” Umma tace “Daga gida…” Mumy tace “Allah ya sa 

lafiya dai, ko munafukar ta sake hada ki da Dakta?” Umma tace “Ba gwara a hada ni da Dakta ba a kan wnn 

takaicin….” Mumy ta gyara xama tace “Me ke faruwa?” Umma tace “Uban kayan da Sudais ya kawo ma makauniyar 

nan na xo amsa tunda ba ubanta bne ya basa kudin banxa” Da mamaki Mumy tace “Kaya kuma, wllh bani da labari 

Amina, ta Ina aka shigo da kayan gidan ban sani ba?” A fusace Umma tace “ni kai na da na haifesa a jaka daya ya 

kawo min tsaraba, kanninsa kuwa dama tsaraban baya wuce chocolate da biscuits…” Mumy tace “To wai kayan me 

ya kawo mata?” Umma tace “Wllh tsaraba ya yo mata niki niki, iri iri kuwa, bai san xancen xai dawo kunne na ba, 

har manyan akwatuna biyu da jaka fa Maryam, abinda hakan ke nufi shine na kasa ganewa” Mumy ta gwalo ido tace 

“Sudais din?? Jiya na ji ance ya xo dama amma ko shigowa ya gaisheni bai yi ba, kinsan fa har wani xumunci ya 

kulla da kishiya ta” Umma ta mike tace “Ina xuwa, ba dai Barrister baya nan ba, yau xa ayi ta ta kare” bata jira 

cewar Mumy ba ta fita. Bangaren Mami Umma ta nufa ta bude kofar hade da sallama bbu yabo bbu fallasa, Mami na 

tsaye parlonta tana sa wrist watch ta gama shirin fita, su Farida na parlon, a takaice Umma tace “Ina kwanan mu” 

Mami na kallonta tace “Same to you” Umma tace “Kayan da Sudais ya kawo gidan nan na taho a miko min…” Mami 

tace “Kaya? Kayan me kenan?” Umma tace “Ai kin fini sanin ko kayan menene tunda kece kika amshi kayan, to ba 

duniya na haifar ma shi ba, ayi hakuri a fito da kayan a bani in kama gabana” Mumy dake ta leko parlon tana tsaye 

daga bakin kofa tace “Atohhh, gwara dai ki sanar masu ba duniya kika haifar ma shi ba” Mami bata sake kula su ba, 

ta gama saka agogonta ta dau handbag dinta da veil tana kallon Farida da Heedayah tace “Farida bring hijab for the 

both of you sai in ajiye ku gidan Hasinah” Farida ta mike ta wuce daki, Umma tace “Ni fa ba Maryam bace da xaki 

wani dinga sha ma kamshi bbu hadina dake, kayan da d’a na ya kawo maki nace ki fito min da su yanxu, ko alkali ce 

ke ni baxan fasa amsan abinda na xo amsa ba baxan kuma fasa gaya maki abinda ke raina ba…..” Farida ta fito da 

hijab Mami ta amsa ta sa ma Heedayah, Farida ta ajiye mata takalminta ta a gabanta, Mami tace “Ki je ku sallami 

Kaka, sai ku sameni a mota” Umma ta bude baki tana kallon Mami ganin har sannan ta ma ki kallon inda take, 

Mami ta nufi kofar sai a nan ta kalli Umma tace “Malama xan wuce, bani hanya” Umma tace “Hanyar ya ci kaza 

kazan sa, kayan da aka kawo maki nace ki fito min da su yanxu kada abu ya 6aci tsakaninmu, ni fa ba Maryam bace 

wllh” Kaka ce ta taho wajen da sauri tana cewa “Muryar waye nake ji wnn kamar na Amina, me ke faruwa hka?” 

Umma ta juya tana kallon kaka fuska daure tace “Ina kwana kaka” Kaka tace “Lafiya kike hayaniya haka a kofar 

mutane Amina, me ya faru??” Mumy tace “Wllh kaya wai Sudais ya kawo gidan nan ba mu da labari, kaya wai me  yawa…” Kaka tace “Kayan me??” Mumy tace “Ni kaina bansani ba, ance dai kayan na nan bangaren” Kaka tace “Au, 

wai tsaraban da yayo ma Deedayah?” Mumy tace “Toh shi din kenan” Kaka tace “To sai aka yi yaya? Ai kaya basa 

wajen Rakiya suna wajena, waye ya xo amsa?” Umma da ta daure fuska tace “Ni na xo amsa” Kaka ta kalleta daga 

sama har kasa tace “Haba, to sannu da xuwa Amina, bakin cikin ne ya motsa kenan yau, to bari kiji ko Umaru yyi 

kadan ya amshe ma Deedayah kayan da Sudess ya siyo mata balle ke, kuma in sha Allahu yau xata fara saka kayan 

sai in ga ta tsiya, ke kuma Maryam har kin mance hijaran da kika yi na kwana biyar a gidan nan bayan kin sa an sace 

Deedayah kin maido ta, kin manta yanda kika dawo duk a lalace shine xaki sake shiga wani kess din da sassafe koh, 

to wllh Rakiya kiris take jiran ki ko bata fada ba ni na sani, haka kawai duk kun bi kun sa ma makauniya ido, to wllh 

karyan ku, tunda ina sonta Rakiya na sonta Sudess na sonta, Junaidu na sonta shi Amadu ba wai mun gama sanin 

xuciyarsa bane, to kowa ma ya ki ya indai mu muna sonta” Umma ta fiddo wayarta tayi dialing number Sudais yana 

fara ringing ya daga, strictly tace “Kana ji na Aliyu??” Sudais yace “Ina ji Umma” tace “Wannan kayan da ka kawo 

gidan Barrister da sunan kayi ma makauniya tsaraba maxa maxa ka xo ka amshe su ka kawo min dakina, idan kuwa 

ba haka ba wllh wllh ka canxa wata uwar….”

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *