AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 16 KARSHE BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 16 KARSHE BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya

magriba za ta wuce ni. Ka san kuma mutum da ya saba komai a yi masa, sannan the house is somehow dirtyalways ”. Ya fada cikin muryar da dole a ji tausayinsa amma banda Hajiya Maryam.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Dr. Hamza ya ce. “Ki barshi ya zauna mana? A kanki yake zaune? Ga mari ga tsinka jaka?”

Cikin mamakin abin da ya fada ta ce, “Haka ma za ka ce? Wace jakar na tsinka masa?”

“To in dai gidana ne na ce ya zauna, ki gode Allah da ya ba ki shiryayyun ‘ya’ ya a wannan za

manin, wasu da yawa irin damar da ya samu suke nema su tambade. Kai kuma na ba ka wata daya ka kawo min matar aure. Attorney ya bada auren ‘yarsa har katin gayyata ya kawo min duk da ban samu na je ba, tunda ita Hafsat din uwarta tace bata yarda ta koma ba ka barta tabi abinda uwarta ke so. Idan watan nan ya wuce ba ka kawo min mata ba zan je Kano in nemo maka duk wadda na ga dama saboda kai din na dade da gane cewa namamajo ne akan mata, in banda haka ta yaya ga wata an halatta maka a cikin gida da igiyoyin aure na halali,amma hankalinka da soyayyar ka

bakidaya suna ga wata a waje, don haka gara in cika maka gida dasu ko ka nutsu dana gidan aure. Ban amince zamanka ya zama zaman shiga sabgar Hafsat a gidannan ba ko ka dinga shigar mata daki, kowa yayi zaman kansa. Is that ok with you two?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mammah kamar ta goya Daddy yadda ya wanke mata shi tas! Ta ji dadin wannan hukunci har fiye da zaton ta, itata fara fita ranta ya yi wasai daga takaicin da ya cusa mata yau. Dama abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya kenan; shiga dakin Hafsat da yake yi. Ban da haka ya yi ta zama a gidan mana ita ina ruwanta?

Bayan fitarta Abdul’azeez ji ya yi kamar an sauke masa wani gingimemen dutse daga kansa maimakon wankin babban bargon da akai masa ya bata masa rai. “Attorney ya ba da auren ‘yarsa!” Whichmeans bai karya alkawari ba! An je Nema masa auren kamar yadda ya alkawarta, dissappointment din daga iyayenta ne. Babu kaffara a kansa, babu tunanin ya ci amanar wata halitta da ta ba shi dukkan yarda da aminci.
Karasawa ya yi gefen kafafun mahaifin nasa, wanda ya maida gilashin idonsa ya ci gaba da abin da yake yi alamar ya gama magana da su.

‘Don Allah Daddy ka taimaka min ta huce, ka taya ni ba ta hakuri, ta yi fushi da ni mai tsanani, na amsa na yi laifi ku dubi girman Allah ku yafe min. Daddy ko gaisuwa ta ba ta amsawa, na janyo mata cuta, Daddy in na mutu yanzu wuta zan tafi babu tantama…
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta yi min alkhairi na saka mata da butulci. Ban san darajar abinda ta ba ni ba sai da lokaci ya kure mini, kuskuren ya riga ya afku. Ni babu wata mata da zan iya kawowa cikin sati hudu daga nan har gaban abada sai HAFSAH! Ko ba za ta mayar min da ita ba atleast ta furta yafiyarta gare ni in Samu sauki a zuciyata…”.

“Na ji. I will talk to her’. Abin da tsohon Ambassador Hamzah Atiku ya ce da shi kawai ke nan a matukar gajarce.

Jiki ba kwari ya baro falon nasa ya koma ‘main parlour’. A can ya yi kyakkyawan gani, Hafsat ce ta yi wanka ta canza kayan jikinta da wasu riga da skirt ‘yan kanti na ‘calvin klien’ jajaye da ratsin baki. Ta gyare gashin kanta ta kalmashe shi cikin ‘bound’ kalar kayan jikinta. Ko ba komai dai anbi umarninsa anyi masa kwalliya. Ta zubo soyayyen chips tubus dashi da sauce din hanta da koda a faranti tana ci da cokali mai yatsu, ga coffee mai zafi a karamin kofi a gefe. Wani abu ya hadiye da ya tokare a makoshinsa ya koma can kujerar karshe ya harde dogayen kafafunsa. Kallonta kawai yake kamar ya samu T.V, ai a cikin sharuddan da aka kafa masa din ba a ce kada ya kalle ta ba.Kuma kallon babu zunubi. Ta
yi kamar ba ta san da shi a falon ba, ta ci gaba da cin abincinta a tsanake.

Usman ya ce, “Shi mijin ba za’a ba shi ba?”

Ta ce, “Na karfi ne!”.

Ya kama baki. “Rashin kunya ne abin?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta yi masa shiru. Mikewa ya yi har inda ta ke ya dauke farantin ya kwace kofin ya kai masa. Karba ya yi da murmushi ya ce. “Na gode Usman, you are the best”. Ya dora a ‘ center -table’ ya soma cin abinsa.

Tashi ta yi cikin fushi ta yi kitchen wajen Mammah. “Mommah kin ga Ya Usman ya kwace min abinci ya bashi?”

“Zuba wani’”. Kawai ta ce don ba ta son surutu.

Usman ya shigo kitchen din yana_fadin, ‘“Mammah yarinyar nan ba ta da imani na lura. Ya Azeez tun safe ba abin da ya ci sai ruwan shayi, amma ta shako faranti ta zauna tana cin abinta a gabansa babu ko tayi”.

Hajiya Maryam ta juyo ta watsa masa harara, ai ba ta san kan zancen ba. Ta nuna shi da yatsa ta ce “Usman, ka kiyaye ni, kada ka shiga hancina don in na tashi fyato ka ba za ka ji dadi ba”.

“Allah ya ba ku hakuri”. Ya ce yana hada hannuwa irin na indiyawa. Hafsat ta yi masa gwalo da ta ga Mammah ta juya. Ya yi mata alamar, ‘za mu gamu ne’ ya bar kitchen din.

Da rana gabadayansu suka ci abincin rana har Daddy da Abdul’azeez a kan tebir. Shi da ita sai satar kallon juna babu ko kwakkwaran motsi daga Hafsat. Daga Mammah har daddy babu mai walwala a fuska. Shi ya fara jin zafin matar tasa
Www.bankinhausanovels.com.ng
ne kan hukuncinta a kan Abdul’azeez, ba karamin karya mishi zuciya ya yi ba dazun daurewa kawai ya yi. An ce so-so ne, amma son kai ya fi. Yana son dansa fa, na Hafsat karah ne. Ita kuwa Maryama na wani shi ne nata kullum nata ba nata ba ne, ba tun yau ba haka ta ke. Ita kuma Mammah dalilin rashin walwalarta shi ne kada Abdul’azeez ya ga fuskarta ya dame ta da wannan nataccen ban hakurin nashi. Har aka gama cin abincin daga shi har Hafsat babu wanda ya ci wani abin kirki.

A yammacin ranar Azumi ta dawo. Kusan Abdul’azeez ya fi kowa farin cikin dawowar Baba Azumi, mai sonsa da jin kansa. Ya tabbata za ta taimaka masa sosai wajen shawo kan Mammansa.

Tun dawowarta ta fahimci yadda ta tafi ta barsu haka ta dawo ta tadda su, ba wani ci gaba daga bangaren uwargijiyarta. Ita ta ci gaba da kula da komai na Abdul’azeez, tsaftar dakinsa da toilet dinsa da cikinsa. Ba tun yau ba ta san ba komai yake ci ba. Su sun yi rayuwa cikin turawa don haka suna amfani da ire-iren abincinsu sosai-sosal musamman kayan gwangwani. Abdul’azeez kuwa na son ‘Nigerian Food’ musamman na Yarbawa su Amala, sakwara, miyar ganye;su Ugu alayyahu, egusi, water leaf, da kifi da ganda saboda zamansa a kudu (Ibadan da Lagos gidansu Mu’ azatu), su ta himmatu wurin yi masa nasa daban, wani lokacin su Hafsat rai na biyawa ta ce kuma ba mai ci har Maman nasu. Mammah kan kyabe baki ta ce,
“Ina ruwan oduduwa dangin Yarbawa. Shi ya sa duk halinsu na naci kun diba. Ban da haka na ce a bar min gidana, a bar min ‘ya ta, a je a auro ‘yar Yarbawa kun ki, har asalin uwarta na jiyo ba ‘yar Jigawa ba ce ‘yar Ogun ce. Uban ne dan Jigawa”’.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Baba Azumi kan rausayar da kai ta ce, “Kin san wani ba ya auren matar wani, jiya mun ga aurenta a obashin (ovasion magazine) Isma’eela ya kawo mana”. Mammah ba ta kara bi ta kansu ba.

Su Hafsat sun fara C.A don haka a dan tsukin ba ta da sukuni, test-test da assignment kawai suke yi. Yau litinin, Mammah za ta je ganin likita kuma ya yi daidai da lokacin shigar Hafsat test . Ba yadda ta iya ta ce Salisu ya kai ta, in ya ajiye ta sai ya dawo ya same ta a Diff Hospital. Ita ya fara ajiyewa a asibitin, sannan ya karya kan motar suka nufi NILE shi da Hafsat.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Danja ce ta tsaida su a wani shatale-tale. Barrister Abdul’azeez Dakata a nashi motar, cikin shirin office yake (fully robed). Ya yi tsakin bata masa lokacin da danja tayi don ya makara, ya dan juya gefen damansa sai ya hango Salisu da motar Mammah, a kujerar baya Hafsat ce ta warware ‘handout’ tana ta karatu. Magana ya yi masa ba ta san suna yi ba, sai ji ta yi Salisu ya gangara ya faka a gefen titi. Ta dago don ta tambaye shi me ya tsaya yi zai makarar da ita, sai ji ta yi an bude kofar side din da ta ke. Mutum na karshe da ba ta zaci gani ba, suna yin kwana uku a gidan ba su hadu da juna ba sabida yanayin aikinsa da lokacin dawowarsa very late gefen maghriba. Lokacin ita ta shiga sallah, sai wajen cin abincin dare kawai suke haduwa, ita kuma ta tsame kanta. Don ko ta
zauna ba iya ci ta ke ba saboda idanun Abdul’azeez da na Mammah, kowanne na kokarin ganin cewa idonsa ya hana abin da ba ya so. Mammah ba ta son wadannan idanun na Abdul’azeez su yi tasiri wajen karya lagonta, tunda ta bi kowacce kafa ta communication ta toshe. Shi kuma nasa idon so suke su fahimtar da ita how miserable and helpless they are saboda rashin ta cikin rayuwarsa yanzu. Don haka ko da ta daina zaman cin abincin Mammah ba ta ce don me ba, ta ma fi son hakan. Amma tana tabbatarwa Azumi ta kai mata nata daki kuma ta ci. Da safe kuma Azumi a basket ta ke sanya masa karin kumallo ya tafi da shi office ba ya son abin da zai makarar da shi, mutum ne mai tsantseni a kan aikinsa da muhimmancin lokaci.

Ajiyar zuciya ta yi sakamakon tunanin da ya tafi da ita kawai saboda arba da Abdul’azeez a inda bata zata ba. Fuskarsa babu wasa ya ce.

“Fito, ni zan karasa da ke”.

Cikin damuwa ta ce, “Ni ba zan fito ba,

“Wallahi kin ji na rantse ko ki fito ko in dauke ki na fiddo ki, a kan me wani gardi zai fita da matata ni me ye amfanina? Kawaicin da nake yi ne ba ki san ina yi ba sai na fito da true colour dina?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga amon muryarsa ta fahimci a matukar fusace yake, Mammah ta gwammace Salisu ya kai Hafsat makaranta a kansa, Salisu ne ‘trusted’ dinta, shi kuma dan ta’adda mai cutar mata da ‘ya. Jikinta har bari yake ta cizgo jakarta ta fito daga motar, ba tun yau ba ta san duk abin da ya fada zai iya aikatawa.
Shi ya bude mata kofar gaba ta zauna ya rufe. Ya zagaya ya shiga bangarensa. Da matsanancin gudu ya fizgi motar. Ban da faduwa ba abin da gabanta ke yi, tunanin Mammah kawai ta ke yi. Me Salisu zai je ya gaya mata? Ta shiga ukunta! A wannan dan tsukin burinta kawai ta ci gaba da yi wa Mammah biyayya a kan duk abin da ta ke so. Ta fahimci duk abin da Mammah ta ke so ta fahimta. Ta kamma kanta, ta bi abin a sannu. Kada tayi garaje, kada tayi gaggawa wajen komawa cikin rayuwarsa. Namiji ba abin yarda ba ne. Sannan ba dan goyo bane. Balle mai wayo da wayewar kai irin Abdul’azeez Dakata, the smartest person she have ever know . Ba ya fadin sirrikansa sai dai reactions dinsa su nuna. Kamar yadda Mammah ta kafe a kai ne, ‘ how sure she is yanzun yana sonta? How sure she is ya daina son Mu’ azatu? Duk da ko yana sonta ko ba ya sonta yanzun doesn’t matter tunda ta yi aure ta barshi.

Amma Mammah a kan gaskiyarta ta ke, shekara daya da watanni da suka kwashe tare karkashin inuwar aure me ya hana ya so ta? Sai bayan ya yanke ta daga cikin rayuwarshi ta dawo gaban wadda take sonta da kauna ta har abada? Wata zuciyar mai tsananin so da kare Abdul’azeez ta ce. “Ke ma me ya hana ki so shi da farko, sai bayan kin zauna da shi? Wanda ke nufin dukkaninku abu daya ku ke bautawa; You didn’t get to know each other well sai bayan zaman. You are not close to each other sai bayan zaman. Soyayya kuma bata faruwa sai da kusanci. Soyayyar bata huda kowannenku ba sai a cikin zaman. Give him a chance Hafsat, reason with him . Zuciyarta ta ji tana yin wani irin laushi wanda ya sa ko da ta ga ya bar hanyar Nile ba ta damu sosai

ba.

Sai dai ta sa a ranta cikin kowanne hali she’ll not betray her mother! She’llstand by her not by him (ba za ta ci amanar Mammansu ba, za ta tsaya a bayanta ba’a bayanshi ba). Ginin da ya nufa da su ya tabbatar mata ofishinsa ya kawo ta, (Federal High Court of Nigeria).
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya yi parking a parking lot ya cire wayoyinsa daga cajin da ya sanya su a motar. Ya dauko ‘suit-case’ da jakar ‘system’ dinsa, ‘wig’ dinshi a hannu ya fita daga motar. Tsayawa ya yi yana jiran ta fito ya rufe motar. Hafsat ta ki ko da motsi. Kyale ta ya yi ya je office din ya ajiye kayan hannunshi ya dawo, da ya shigo cikin motar juya masa keya ta yi tana duban taga. Murmushi ya yi ya ce,

“Me ki ke nufi da ni ne yarinyar nan?”

Ba tare da ta juyo ba ta turo baki, “Laifin me na yi da za ka kawo ni kotu? Test zan yi amma already ka sa ta subuce mini”. Za ka iya jin damuwar hakan sosai a amon muryarta, domin ta shirya wa gwajin sosai ta kwana tana karatu.

Hannunta ya fizgo ta yi juyowar da ba shiri, a fusace ya ce. “ To hell with your test, duniya kawai ki ka sa a ranki ba kya tunanin lahirarki. Da kin san yawan zunubin da Mammah ke sanya ki kina kwasa da kin tausaya wa kanki Hafsat. Tana tare da mijinta kullum tana gyara aljannarta, ta nesanta ki da naki kina ta kusanta kanki da wuta. Shin ni ba mutum ba ne, ba ni da feeling ? Shekaruna talatin da uku har yau ban san ya ya aure yake ba. Hafsat ko ba kya sona dole ne ni ma ki yi min biyayya yadda ki ke mata. Ko kuwa shi kenan saboda na yi laifi ni rayuwata ta kare?”
Kuka ta soma yi a hankali, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta, shi da Mamansa sun sa ta a kwana, kowanne gani yake shi ya kamata ta yi wa biyayya, a wannan lokacin ba ta san me ya kamata ta yi ko ta ce masa ba banda;
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Me ka ke so in yi maka yaya Azeez?” Hannunta da ke cikin nasa ya janyo a hakali ya hade ratar da ke tsakaninsu. Ajiyar zuciya kawai suke yi dukkanninsu cikin motar. Wata irin nutsuwa da suka dade rabonsu da ita ke overwhelming dinsu tun daga kwakwalwa har babban yatsar kafarsu. Tsawon mintuna ba wanda ya iya yin magana a cikinsu. Hafsat ce ta ankara mutane na gilmawa jefi-jefi suna aje motocinsu. A hankali ta zame jikinta daga nashi ta koma cikin kujerarta sosai ta zauna, ta lumshe idanunta, karfin scent dinsa da na air-freshner din motar suka hade da sanyin A.C suka bada wata atmosphere mai dadi a cikin motar. Kansa ya kwantar a kan sitiyarin yana regaining hargitsewar bugun zuciyarshi. Sun jima a haka kafin cikin raunin murya ya ce.

“Gidanmu nake so mu koma Hafsat direct daga wajen nan. Na roke ki kada ki ce min a’ ah…”

Kai ta shiga girgizawa da sauri showing resentment (cikin nuna rashin yarda) “ I cannot do this to Mommah (bazan iya yin haka ga Mammah ba)”.

Dagowa ya yi daga kan sitiyarin ya dube ta sosai cikin tsakiyar idanunta, duk da ta ki yarda su hada idanu ta san idonsa akanta yake. “ Then blame yourself kan duk abin da na zaba mana!”’.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya tada motar ya fita daga harabar kotun kasa, ya hau kan titin da zai kai shi titin Aguiyi Ironsi.
Hafsat dai ikon Allah ta ke kallo, gabanta na tsananta faduwa don bata san me yake nufi ko ina zai kai su ba, sai dai zuciyarta na gaya mata… ko me Abdul’azeez zai zaba musun nan ba alheri ba ne gare su………!!!

Mu karasa a littafi na hudu kuma na Karshe. Kada ku damu, tare suke. Taku har abada Sumayyah Abdulkadir Takori Www.bankinhausanovels.com.ng

About AIS

Check Also

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR             …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *