AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 14 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 14 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 
Mun tsaya 
za ta huce ta sa mana albarka, musamman idan na maida ita. Babban burin ta shine ni da Hafsat mu rayu tare karkashin inuwar aure, Baffa zan yi zama na soyayya da amana da Hafsah har karewar numfashinmu ba don Mammah ba, sai don zuciyata da ke son ta da kaunarta”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Babu wanda cikinsu da jikinsa bai yi sanyi ba. Abin da zai sa Abdul’azeez kuka tabbas ba karami ba ne sun sani. Tun fil’azal shi jarumi ne tun yana karami, wanda bai jingina a jikin kowa don ya rayu. Yau ga shi a gabansu yana kuka don ya rayu da Hafsat. Hannunsa Baffa ya kama, ya dago shi ya ja shi ya zaunar a gefensa.
“Abdul’azeez!” Ya kira sunansa.

Bai amsa ba, amma ya dago da jikakkun idanunsa ya dube shi.
“Abin la’akari shine, idan sakin Raja’iy ne (Talaq Raj’ah) wato (revocable divorce) da turanci, idan kafin a gama iddah miji yayi kome wannan babu ishkali matar tana cikin zummar mijinta tunda saki ( raja’iy ) ne ko ana gobe zata gama iddah zai iya dawo da ita ko ba da amincewarta baidan har saki daya akayi ko saki biyu. Amma idan iddar (Talaq Raj’ah ) wato(revocable divorce)ta kare ba tareda anyi kome ba ya zama (irrevocable divorce) matar bazata komawa mijin ba har sai in ta amince, kuma an sake daura auren da sabon sadaki. Babu sabanin ra’ayin malamai akan wannan fatawa; ma’ana duk sun hadu akan hakan.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Mutum ya yi aure da niyyar bayan wani lokaci zai saki matarsa malamai sun bada fatawa mabanbanta a kai. Manyan malamai_ daga mazhabobi daban daban sun ce haramun ne; saboda ya saba hikimar aure a shari’ah, sannan akwai yaudara a ciki. Wasu bangaren mafi rangwame na masana sun ce; ba haramun ba ne, amma shari’ah ba ta so, wato ya shiga cikin karhanci . To amma duk ba wanda ya bayyana cewa, auren bai yiwuba, ko in an yi sakin bai yiwu ba. Saboda haka; wasu malamai sun karhanta auren (sun ce makaruhi ne), wasu sun haramta shi bakidaya.Idan aka ce abu makaruhi ne ana nufin abinda shari’a ba ta so, amma babu hukunci a kai. A takaice aure a kan yarjejeniya batacce ne babu shi a shari’ah, kuma musulunci bai yarda da shi ba. Don haka in muka dubi mas’alarka ta fuskar addini aurenku yana nan; mu Www.bankinhausanovels.com.ng
muka daura aure, kumamun daura auren bisa dokoki na shari’ah (sadaki, waliyyai, shaidu), kayi saki daga bayadagagurbatacciyar niyyakuma ka gaggauta mayar da aure kafin matarka ta cika idda da kyakkyawar niyya, wanda shi ne abin da shari’ah ke so. Wancan sharadin da ku ka yi na farko babu shi yanzu a zukatanku. Wancan auren dama an gina shi ne a kan doronmutu’a sai aka sake niyya zuwa auren sunnah, shi kenan! Sai a nemi gafarar Ubangiji bisa kuskuren niyya da aka yi da farko”’.
Abdul’azeez ya ja wani gwauron numfashi, sannan ya sauke shi a wahalce. Ya ba su tausayi sosai. Amma ba wanda ya nuna duk don su kara tsoratar da shi bisa kuskurensa. Baffah ya ce, Daddy ya kira Maryama ta hada shi da Hafsat. An yi sa’a suna tare ta dauko ta daga makaranta kan hanyarsu ta komawa gida. Hafsat na russuna murya tana gaishe da Baffa ya ki amsawa, ya bude mata nata rabon a kan don me bata gaya wa uwarta ba lokacin da Abdul’azeez ya ce su yi yarjejeniya? Fada yake mata ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Fadan da bata taba zaton ya iya ba. Kullum shi mai tausasawa ne a gareta. Ya gaya mata hukuncin abin da suka aikata. Hafsat da gari banza ma kuka ta ke yi balle yau? Baffa fa! Mahaifin Daddy gabadaya. Bai bata damar cewa komai ba ya mikawa Abdul’azeez wayar, “Sake maimaita mata a gabana ka mayar da ita dakinta’. Abdul’azeez da ya _ hau maimaitawa sai da ya fada mata ya kai sau goma. Abdulkarim ne ya kwace wayar ya zuba masa rankwashi a tsakar ka. Ya bawa Daddy wayarsa.
Adda Hafsatu ta ce, yau abin da yake so ta girka, amma wallahi ba za ta zuba masa ba. Hakuri ya dinga ba ta, amma ta kafe ba zai ci ba. Ta ce,
“Ai ko don albarkacin sunana da yarinyar nan ta ci ta fi karfin kalmar saki daga bakinka. Tukunna ma wace ce Mu’azatun? Ku hada ku aura masa mana ya san bambancin mai suna HAFSAH da sauran sunaye?”
Uncle Abdulkarim ya kwance musu labarin zuwansa neman auren Mu’azatu da yadda aka sallamo shi, ya ce har gobe ita yarinyar tana sonsa, mahaifinta ne ya ki, bai san dalilinsa ba, kuma ya yi gaggawar yi mata aure. Shi bai taba ganin mahaukacin so irin wannan ba, wanda Abdul’azeez ke wa Mu’azatu, son da zai ja ka ka saba wa Ubangiji don ka faranta wa budurwa, ka gwammace bacin ran iyayenka a kan farin cikinta? Allah ya yi mana katanga da ‘ya’yanmu da irin wannan son, yau da Abdul’azeez ya auri yarinyar nan watakila ko gaida iyayensa sai ta ba shi izni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Baffa ya yi tsai! Da ransa, yana sauraron labarin da Abdulkarim ke baiwa Addah. Bai ce komai ba, amma ya gane wannan yarinyar ita ce mai farautar jikan nasa. Ya kudure a ransa nemawa Abdul’azeez kariya fiye da dukkan jikokinsa don shi ko yanayin aikinsa ma hatsari gare shi. Ba su baro Kano ba sai da ya sa Abdul’azeez ya yi wanka da ganyen magarya har sau uku, ya ba shi rubutu kala-kala, ya ba shi addu’o’i da nafilolin da zai rika yi duk daren juma’a da litinin. Ya ce kuma idan ya ki yi Allah Ya isansa. Dariya ya yi, sannan ya alkawarta masa zai yi. Ya ba shi na
sauran ‘yan uwansa ya tafi musu da shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tunda suka dawo gida Abuja, Mammah ta kara tsananta matakanta na tsaro a kan Hafsat da Abdul’azeez, da kara toshe duk wani communication gap a tsakaninsu. Ba abin da ya dame ta da wani aurensu da aka mayar kamar ma ba ta san an yi ba, bai wani wani damu ba ya ci gaba da ayyukan gabansa cikin kwanciyar hankali. A ganinsa ba shi da damuwa yanzu a rayuwa tunda kuwa koma nisan jifa kasa zai fado,sannan hausawa suka ce wai “karshen alewa kasa!”’.

*******

Yau watan Hafsat guda da komawa makaranta, karatun session din ya kankama sosai. A watan gabadaya wani abu bai kara hada ta da Abdul’azeez ba ko da gaisuwa, Mammah ta bi kowacce hanya ta sadarwa tsakaninsu ta toshe. Haka suka zauna tsayin wata biyu a gidan ba ruwan kowa da zaman dan uwansa. Idan ya taso aiki gidan yake zartowa, amma Sai dai ya tsaya iya falon farko da wajen Daddy don Mammah ta hana ta fitowa ma in dai yana gidan, har sai ya gama cin abinci da hirar da suke yi tsakaninsa da Daddy da su Isma’el ya bar gidan, ko giftawar Hafsat ba ya gani. Sai dai ta shige toilet ta yi kukanta mai isarta, kukan tausayin Abdul’ azeez dinta! Sau biyar ta ji shi a dakin Mammah ya je bata hakuri, amma ba ta tankawa. Azumi ba ta gari ta je ganin gida can Sokoto, ya tabbata da ta taimaka masa wajen tausar Mammah. Ko gaisawa za ta yi da Dr. Bashar da su Dada sai ta wayar Www.bankinhausanovels.com.ng Mammah, kuma a gabanta. Ta gama ta karbe. Time-table ta ke bi wajen kai ta makaranta, ita
kanta ta gaji da wannan zirga-zirgar da ta sanya kanta babu gaira babu dalili don abu ne da bata saba ba (tukin mota), amma tsabar kada Abdul’azeez ya samu damar kebewa da Hafsat ya sa ta hana Salisu kai ta da daukotan.
Ranar yau ta kasance asabar, sai suka wayi gari da bako a gidansu; Abdul’azeez ne da jakunkunansa, ya bude dakinsa na samartaka na gidan ya ce Salisu ya shigar masa da jakunkunan ya shirya masa kayan a wardrove ya share masa dakin ya goge ko’ina ya wanke masa bayi. Isma’el ya shige nasa dakin wanda ke daura dana Abdul’ azeez din banda dariya ba abinda yake yi. Usman ya Zo ya tadda shi yace.
“Kana zaton Mammah za ta barshi ya zauna ne?”
Ya sassauta dariyar ya ce. “To ya zata yi dashi? Za ta kore shi ne shi da gidansu? Ai ni ya kyauta min, Mammah ba ta jin lallashi, an mayar da aure kuma meye na cigaba da rike masa mata? Attimes she behaves like AddaHafsatu; tough and disciplined”’.
Tun tashinta daga barci ta ke jin scent din Abdul’azeez a gidanta. Bata kawo komai ba tunda ta san yana zuwa gidan amma ba irin wannan lokacin ba sai yamma can in ya tashi ofis. Da ta yi wanka ta shiga kitchen don ta ga me za ta dafa, shi ta gani ya jona kettle yana dafa black tea dinsa wanda shi ne abin shan sa duk wayewar garin Allah, daga shi sai threequater da farar singilet. Daga bakin kofa ta tsaya tana kallon ikon Allah. Juyowa ya yi jin alamun mutum, addu’a yake Allah ya sa Hafsat ce ta fito ya samu ya ganta ko daga nesa ne kafin fitowar Mammah, Www.bankinhausanovels.com.ng
amma sai ya ga Mamman da kanta ba sako ba. Russunnawa ya yi ya soma gaishe ta, bata amsa ba ta wuce ciki ta kunna gass ta dora ruwa. Sai ya tuna mata da shekarun yarintarsa, haka yake ba ya son a dafa masa shayi, ya fi so ya yi shi da kansa. Hafsat ta shigo tana mutstsike idonta da alama tashinta kenan daga barci, riga da wando ne na barci farare sol a jikinta marasa kauri sosai amma ba su kama jikinta ba, kanta ba kallabi ta kame tulin gashin kanta a tsakiyar kan da black hair bound . Kwata-kwata ba ta lura da shi ba ta shigo kitchen din. Kai tsaye gefen Gass-cooker ta nufa inda Mammah ke tsaye tana cika tana batsewa, ba ta lura da yanayinta ba saboda idonta ma bai gama washewa ba.
“Mammah ba ni aron waya zan kira Yaya Imamu, mafarkinsa na yi yanzun nan”.
Ba tare da ta dube ta ba, ta ce. “Tana kan bed-side
Juyawar nan da za ta yi da zummar fita sai ta yi arba da Dan Ambassador Hamzah Atiku, tsaye yake jikin ‘kitchen-cabinet’ ya harde hannayensa a kirji. Lumsassun idanun dake dimauta ta ke kallonta admiringly daga can kasan idanun. Zuciyarta ta ji ta harba da karfi. Yaushe rabon duniya da ayyaraye! Yaya Azeez ashe tana da rabon sake ganinsa nan kusa??? Watanni biyu masu kama da two decades. Hajiya Maryam haushi ya ishe ta ganin sun manta da ita a wurin ta tsaya ta ki ficewa, sai kallon juna suke yi da wani irin yanayi cikin kwayan idanunsu. The excessive emotions for seeing each other continue to linger in their eyes (shaukin su na ganin juna ya cigaba datsayuwa na lokaci mai tsaho cikin idanunsu). Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani uban dundu ta zuba mata sauran kadan ta fada kansa. Da sauri ya taro ta, ita kuma sai ta yi maza ta zame saboda kunyar da ta kamata. Mammah ta dube shi ta ce “fitar min daga kitchen , in ji dai nan din ba gidanka ba ne? Me ma ya kawo ka da sassafen nan?”
Sunkuyar da kai ya yi yana shafa_ kansa. ‘“Mammah ai na dawo nan, the house is very wide for me” ( gidan yayimin fadi da yawa).
Hafsat ta dafe bakin ta da hannayenta biyu ganin yadda Mammah ta fusata, cikin damuwa kuma a marairaice ta ce.
“Mammah we didn’t talk, ni ban san ma yana kitchen din ba da ban shigo ba. Ki yi hakuri”.
Shi kuma ya ce. “Ni ruwan zafi nake dafawa. Allah Mammah I didn’t give her a second look, ki yi hakurv’’
Ya juye tea dinsa a mug (kofin tangaran mai zurfi) ya zuba zuma kadan a ciki ya fita. Hafsat ta ja gefe tana jin wani irin radadi a zuciyarta. Mutum da gatanshi ya koma kamar wani maraya a gidan ubansa! Shayin ma ba za’a bashi ba sai ya dafa da kansa. Da kuka wiwi ta bar kitchen din. Hajiya Maryam ta bi ta da kallo bakinta a bude, sai kuma ta girgiza kai ta yi murmushi ta juya ta ci gaba da abin da ta ke yi.
Ta yi rub-da-ciki tsakiyar gadonta tana kuka ta ji an murda kofar dakinta da alamar shigowar mutum, a zatonta Mammah ce ta biyo bayanta don ta lallashe ta tasan bata iya jure ganin ta cikin bacin rai, don haka ko dagowa ta ki yi. A kan bed-side drawer na gadonta ya zauna kafarsa ta
dama na bisa gadon daya na kasa. “Tashi ki sha tea”.
Muryar Abdul’azeez ta ji kamar a cikin mafarki. A firgice ta dago da hawayenta shabe-shabe suka hada ido. Hankalinsa kwance yake, da alama yanzu kam ba shi da damuwa. Waiwayawa ta yi bakin kofa a kidime kuma ta juyo ta dube shi a rikice. “Na shiga uku!” Ta furta a fili muryarta na rawa har ta so ta bashi dariya, mug cup din hannunsa ya mika mata har ya sha rabin shayin. “Karbi, ko sai na baki a baki?”
Harara ta maka masa tamkar idanun zasu fadokasa.
Da kai ka ke ba ni shayi?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Girarsa ya daga mata. “ Just taste it, mine is special….just beyond comment” (ki dandana ki ji, nawa na musamman ne, fiye da yadda zaki iya sharhi’’
Mikewa ta yi tsakiyar gadon ta dirgo da sauri, gara ta fice daga dakin nan in ba haka bata lura bashi da matsala in Mammah ta sanya ta a turmi ta kirba tunda shi yana da Mu’ azatu. Ita kuwa ba ta da mai damuwa da ita ta wannan fannin wanda zai tsaya ya lallasheta in ta sha dukan. Kafin ta kai kofar Abdul’azeez ya riga ta, ya kuma murza ‘key’ din da ke jiki. Hannu ta dora a ka za ta zuba ihuya toshe mata baki da hannun daman sa ya janyo ta tana tirjewa har gefen gadonta. A jikinsa ya zaunar da ita, ya dauko shayin ya kai bakinta. Turewa ta yida karfi tana kokarin mikewa har da zabura,da haka duk suka zubar da ragowar shayin a jikkunansu. Ga shayin da sauran zafin sa sosai amma ba ta wannan take ba. Ta yi wuf ta mike jin Mammah na buga mata kofa, iyakar rikicewa Hafsat ta rikice, iyakar rudewa ta gama rudewa, tashin hankali baro-baro ya bayyana a fuskarta.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE

About AIS

Check Also

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR             …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *