AMANAR MU CHAPTER 5

AMANAR MU CHAPTER 5

K’arfe 6 daidai Zee ta isa garin abj already driver na jiranta a tasha hakan yasa tana zuwa ta zarce mota!+

Gidan koda tashugo babu kowa da alamu dukkanin baqi sun koma, fitowa tayi daga cikin motan sannan driver ya jaa mata trolley d’inta zuwa cikin gida.

Harta gifta zata shiga cikin gida sai ta tuno da zancen Humy data sameta in private (cikin sirri) ana gobe d’aurin auranta!

_Zee dan Allah inaso kimin wani alqawari_

Kallonta Zee tayi sannan tace “ok inaji “

_Zee dan Allah ina rok’anki bayan tafiyana kiruqa shiga kina duba su baba koda sau d’ayane a rana kimin alk’awari zaki ruk’a kula dasu saboda sunada tsananin Buk’atan wani a kusa dasu,kinga yanzun zan tafi zuwana abuja zai ruqa d’aukan lokaci!_

_Kinga babu kowa yanzun a cikin gidan sai ke da momy da masu aiki su kuma kinsan ba kwana sukeyi ba momy kuma sai yamma take dawowa aiki,Na rok’eki Zee kiruqa shiga kina d’ebema su mama kad’aici daga ita sai baba kawai suke wuni acikin gidan nan fa! Mama ita kad’ai kema Baba duk wani hidima nasa tayi na baba tazo tayi nata baki ganin k’arfinta yafara k’asa masu aikin nan ko ance suyi ba yi suke sosai ba! Zee awannan lokacin iyayenki nada matuk’ar buk’atanki wlh Zee kinada Zuciya mai kyau wanda bai maki farin sani bane kawai zai d’auka zuciyanki ba fari bane amman ni Humy nice nasan Wacece Zee kuma nasan zaki kula da mama da Baba a wannan lokacin dan kece kawai zaki zama mafi kusa dasu a yanzun! _

Dogon lumfshi Humy tasake dan taga alama tamkar Maganganunta sun fara ratsa Zee d’in dan haka ta kuma sassauta kalamanta had’ida dafa Zee d’in sannan ta cigaba da cewa;

_Dan Allah karki bari shaid’an ya ruk’a ingizaki har yasa kina banzatar da iyayenki ,shaid’an yayi alk’awari kauda halittun ubangiji daga duk wani rahmar Allah.Karki bari yaci galaba akanki ked’in mutum ce mai Sauk’in kai da Sha’ani saidai wanda bai maki farin sani bane zai d’auka kinada zafi plss Zeeta kimun wannan alqawarin dan_”

Tabbas maganganun Humy gaskiane ita kanta wasu lokutan inta zauna ta tuna yadda take hantaran iyayenta da kyamatar su abin na susa ranta saidai ya ta iya haka Allah yayita bata k’aunan talaka kuma bata mafarkin had’a wuri wajen talaka da ace mahaifinta arziqinsa bai karyeba kuma ba nak’asaishe bane ai da babu wanda zai kaita son iyayenta itafa da ace iyayenta kaman iyayen Humy ne ai babu abinda zai hanata yimusu ladabi da biyayya tamkar yadda take ma iyayen Humy!

Kallon Humyn tayi sannan tace

_Shikenan in Sha Allah zan k’ok’arta_

Murmushi Humy ta sakar mata had’ida rungumanta!

Dogon lumfashi Zee tasauke sannan takalla side d’in iyayen nata wani qullutun bak’in ciki ya turnuk’eta dukda side d’imsuma akwai kyau da tsaruwa amman ai in an had’a da side dinsu Humy side nasu bakomai bane face boys qauters!

K’udurtawa tayi a zuciyanta ko ana ha maza ha mata itama sai nata iyayen sunyi kud’i sannan ita kanta sai tayi arziqi tayadda baza ta ta6a sake zama a k’ark’ashin wasu ba bare ata hantaranta ana mata fad’a dan ita aganinta saboda iyayenta ba masu shi bane yasanya Umar tsananta sannan ita Humy dan taga iyayenta da en uwanta da ita kanta duk ak’ark’ashin Dadynta suke shine shansu,Cinsu,suturansu ,kudin makaranta da Islamiya su! Kai har iyau dinnan iyayen Humy ke masu komai shiyasa Humyn ke tunkaranta tana gaya mata maganganu iya son ranta akan iyayenta!

Amman bakomai in sha Allahu daga rana irin tayau zata chanza halinta zata koma ta runguma iyayenta,watarana suma arziqinsu zai dawo su tashi a k’ark’ashin wasu!

STORY CONTINUES BELOW

Suma su shiga duniya asan dasu,amman tawacce hany’a zata bi dan samun wannan ‘yancin?babanta kudinsa bawai kwacewa akai ba arziqin ne dakansa ya karaya ya gudu tamkar baiyi dukiya ba! Dama kwacewa akai zata iya cewa zata shiga tafita dan kwacema mahaifinta hakkkinsa

Ta wacce hany’a ya kamata tabi itako? Dan she is desperate (k’aguwa)  tabar k’ark’ashin wasu suma sudawo masu kudi masu yima kansu komai da komai ba tareda taimakon kowa ba!

Dole tanada buk’atan taimakon wani amman wa zai taimaketa? Karatunta?

“Aa sam karatuna bazai taimakeni ba dan kona sama aikin kafun abiyani sai wata ya qare sannan kudin daza a ruqa batan bawai mai yawa bane!

Toh wazai taimaketa?

Yaah bash?

Kai no yaah bash zaii 6atamun shiri ne nasan sa dabin kwakwafin bala’i zai iya bincikowa yasan dalilinta dakuma sirrinta! Wanda sam bazata ta6a barin wani yasan wannan sirrin nata ba!

Dole kenan ita kad’ai zata yi abinta bata buk’atan taimakon kowa kenan!

Dole indai tana son wannan mission (buri)d’in nata ya cika tana buk’atan ta aiwatarda abinda tajima dashi a ranta takeson aiwatar wa kenan? Shi kad’aine zaisa iyayenta su azurta itama ta azurta kenan?”

Tabbas wannan itace kawai hany’a mafi sauqi dazai iya 6ullar da ita ga cin nasara dolenta ta chanza takun ta dole kuma tayi bincike mai zurfi akan wannan k’udiri nata!

Murmushi tayi kawai sannan afili tace

“Nagode Humy sosai da shawarwarinki ked’in Amintacciyar k’awa kuma er uwa ce! If badan nasihohinki da shawarwarinki ba dabaki gajia dayimunsu da bazan ta6a natsuwa Na rungumi iyaye na nafiddo su cikin k’angin nan ba!thank u in Sha Allah iyayena kuma kuna gab da zama masu enci masu kuma dogaro dakansu ni Zee namaku alqawarin hakan!dukda zuciyata nasan da kyar zata aminta akan kusanci daku ayanzun ba! Amman zanyi iya yina kafun lokacinda zaku azurta nasoku kaman raina kuma mahaifina yawarke “

Murmushi takuma sakewa wanda ita kad’ai tabarma kanta sanin fassaran ma’anoninsa!

Juyawa tayi tawuce side d’in iyayenta!

********************************

10:30pm

Zaune take akan kujeran falan nata hannunta riqeda remote tana kallan Televista!

K’aremata kallo nayi sany’e take cikin riga da Wando wanda yayi matuqar kama jikinta da fidda surarta tayi kyau sosai sai fidda k’amshi take mai dad’i!

Tun d’azun zaman jiran yaah Umar take dan tunda Zee ta tafi suna shugowa falo akayi kiransa wajen aiki badan yasoba yaje dan anshaidamai zuwansa dolene hakan yasa ya lalla6a Humyn yatafi tun tafiyansa har yanzun bai dawoba “

Knocking kawai taji anayi hakan yasata kallan agogon dake manne abangon falanta 10:50pm mik’ewa tayi tanufa bakin k’ofan a hankali ta sany’a idanunta wajen kallan mutum dake waje yaah umar ne hakan yasata saurin bud’ewa k’uramata ido yayi saiyaga yau tachnza mai dan babu wani surarta dabata fito acikin kayan ba sosai yaji wani kalan bak’on yanayi na shigansa a hankali taje ta rungumesa tamai peck a kumatu sannan cikin  sexy muryanta mai rikita duk wanda yaji tace “I missed u so much Sweetheart “

Kuma rungumota yayi sannan ya k’arasa shugowa falan dake ta tashin k’amshin turare mai sany’ay’a rai da zuk’ata!

“Missed u more Humynah “

D’agota yayi yana k’aremata kallo daga sama harqasa shikam inbai godema ubangijinsa da azurtashi da mace kaman Humy ba baisan maizai yiba kuma! Godia ya shiga yima ubangiji Na mallakamasa Humy amatsayin abokiyar rayuwarsa (life partner) matsowa yayi daf da ita harsuna iya jiyo bugun da zuciyoyinsu keyi a hankali yasa hannunsa ya talla6o ha6arta sannan ya matso da fusknsa daidai saitin wuyanta!

STORY CONTINUES BELOW

Wani kalan yaaar Humy takeji daga saman kanta har k’asa ,kwantarda fusknsa yayi a wuyantayana sunsunan k’amshin turarenda yazama jikinta a hankali yacire fuskansa akan wuyanta yamaido dashi saitin fusknta itakam Humy runtsa idanunta kawai tayi dan jima tayi k’afafunta suna gagara daukanta!

Bakinta yasoma laluma a hankali itama ta shiga bud’esu sany’a bakinsa yayi cikin nata yasoma mata wasu kalan hot kisses masu rikitarda kwakwalwa!

Tsayuwan ma gagaransu yasomayi a hankali yazaunarda ita kan kujera ya shiga sarrafa bakinta!

Waiyooo itakam Humy tunda take tana ganin bata ta6a tsintan kanta cikin yanayi mai wuyan fassarawaba irin yanzun kai aure ma rahmane Allah ya k’arama annabi daraja (Amin)

Ganin zata jikata gashi yaah umar yasoma fita hayyacinsa yasata saurin janyewa had’ida wucewa d’aki da gudu!

Shiko yaah umar binta da kallo kawai yayi dan gudun ma kyau yamata yanda mazaunanta keta karkad’awa ?

Da sauri ya shugo d’akin isketa abakin gado yayi tana maida lumfashi jin kaman mutum a tsaye akanta yasata d’agoda kai sukai ido hudu saurin rufe fuskanta da tafukan hannayenta tayi dan kunyarsa takeji!

Murmushi yayi ya qaraso inda take zaune shima yazauna har jikinsu na gugan na juna!

Rungumeta yayi sannan a hankali ya rad’a mata a kunne

“Zan cire wannan kunyan nawa da kikeyine ma ai ayau dinnan “

Ya ida maganar yana murmushi da ya bayyarda fararen haqoransa itama Humy murmushi tayi tad’an bugi k’irjinsa a hankali tana fadin “kai yaah umar!”

Daria yayi sannan yace miqe muje muyi alwala muyi salla mugudema ubangiji daya mallakamana junan mu ayau Humynah!”

Kuma sunnar dakanta qasa tayi tana murmushi k’asa k’asa chak taji ya d’auketa kaman baby yayi hany’an toilet da ita bai direta a ko inaba sai sink nan sukai alolan tare sanan suka fito sukayi nafila raka’a biyu bayan sun sallame Umar yajima yana masu rok’on Allah da basu Zuria d’ayaba da d’aurewan auransu har a aljannah!

Bayan ya kammala yamata tambayoyi kuma tsaf ta amsa masa su daidai harda k’arin sharhi ma sosai Umar yaji dadi dan yasan baima ‘yay’ansa za6en tumun dare ba kobai tura ‘ya’yansa naiman karatuba mahaifiyarsu mai basu ingantacciyar ilimine!

Miqewa yayi yaje ya bud’e fridge din d’akin ya fiddo fresh milk da nama yazo ya diresu agaban Humy wacce duk jinta take kaman a mafarki yau gata ga masoyinta wanda tun bata san mainene so ba tafara sonsa shine first love dinta kuma tana fata yazama last ma! Yau sune zaune a d’aki d’aya a matsayin ma’aurata ba masoyaba ?!

“Heys are u lost?”

Yayi maganar yana huremata fuska da iskan bakinsa

Murmushi tayi sannan ta gyad’a mai kai!

Ajiye komai yayi sanan ya kamo hanna yenta ya kalleta yace:

“Humynah mai yakai yau dad’i a rayuwannan yau gani gaki a matsayin ma aurata Humy ayau in Allah ya amsa raina zan mutu cikin farin ciki dan koba komai ban rasa raina ba harsaida na mallaka abar qaunata wlh Humynah  Ina sonki ,inasonki so na haqiqa banta6a son wata mace a doran duniyannan bayan keba nasoki tun bansan zakizo duniya ba nasoki tun kina cikin Momy wlh Humy bazan iya qiyasta rayuwa babu keba”

Dogon lumfashi yasauke yana kallan Humyn da itama shi take kallo tanajin wani adda6a66iyar soyayyarsa har cikin ranta!

Dafe kanta da hannunsa yayi sannan yace “Ayau ni Umar Khalil maigoro namaki alk’awarin zama dake har abada Na maki alqawarin baki dukkanin wani kulawa da dukkanin farin ciki a rayuwan nan , namaki alk’awari bazan ta6a bari wani abu ya sameki  bare har yasaki cikin damuwa ba. I promise i will always be there!”

“Bazan ta6a daina sonki ba Humynah har abada ko a aljannah kece shugaban matayena a duniya kuma kece kad’ai Matar Faruq! Kuma ke kad’ai zai qauna,zai So, har abada bazai hadaki da kowaba wannan alk’awarine ni Umar Faruq Na daukan maki in Sha Allah rabbi zai dafamun dan cika wannan alqawarin “!

Itakam Humy tuni hawayen dad’i suka gama wanke fuskanta rungume Yaah umar din tayi tana kuka !

D’agota yayi suna kallan juna gyad’a mata kai yayi alaman maganansa hakan yake kuma in Sha Allah ta6batacciya ce!

Nan yashiga bata naman abaki itama tana basa abin gwanin ban shaawa!

Allah kak’arama aure daraja

Allah kabama sauran al’umman annabi mazaje da mataye na gari!

Bayan sungama ya umar yadauketa chak saikan gado ya rungume abarsa ya kashemasu wuta sannan ya tofesu da aduaa sannan a hankula ya shiga naiman hakkinsa……………??‍♀️??‍♀️

Sumsum nafita a d’akin na jany’o masu k’ofan d’akin dan annabi da kansa yace fayyacha sirrin ma’aurata ba kyau!

Tohm Yaah UMAR da Humy asuba tagari a kumaci amarci lafiya!

Bari mu waiwayi Zee kuma!……..✍?

Sad’af sad’af kaman wata minahika haka ta kusa kanta cikin gidansu ba kowa a tsakar gidan,da sallama ta shugo cikin falan ta tarar ba kowa sai tashin k’amshi kawai straight d’akin babanta ta wuce da sallama d’auke abakinta !
“Waalaikumussalam”+
Mama dake sanyama baba kaya ta amsa,shugowa ta yi tana k’arema iyayen nata kallo wani kalan baqin ciki taji yana ziyartan ta amman da sauri ta kawarda abinda zuciyanta ke hasaso mata sosai takeso ta chanza rayuwan ta Amman wlh ita harga Allah ta tsana ta bud’e idanunta taga wannan nak’asaishen talakan ne mahaifinta,ta k’udurta a ranta duk inda ake samo lfy saita sama ma mahaifinta lfy shima yaruk’a takawa da k’afansa ya kuma ruk’a yin komai da kansa ba tareda taimakon kowa ba!
“Ah Zee saukan yaushe?halan momyn kune ta aikoki?ya kika baro Humyn?!”
Tambayoyin mahaifiyartane ya katseta daga tunanin data lula a hankali ta kalla mahaifiyarta sannan ta kawarda kanta ranta na matuqar susa murmushi tayi sannan tazo kusada mahaifiyar nata wacce tabude baki da ido tana bin Zeen da kallan mamaki!
Jikawai tayi Zee ta kwanto kanta a kafad’unta abinda tun shekara 10 dasuka wuce ko hannun Zee mama bata sake rikewa a cikin nata ba! Could it be a du’an datake ma Zee ne Allah yasoma amsa masa?dagaske wai ‘yarta ce yau kwance a kafad’an ta? Dagaske itace ta tako tazo d’akinsu hartana murmushi mai fidda sirrin kyawunta.Any’a kuwa ba mafarki take ba yau Zainab dakanta itace kwance ajikin ta? Tabbas indai mafarki takeyi tohm bata fata wani ya datse mata wannan mafarkin dan in ta tatane ma bataso tafarka a baccin da ana dawwama abacci toh datayi! Jin muryan Zeen tayi tana fad’in:
“Yanzun Mama har sai in Momy ta aikoni ne zanzo wajenku?ko bakiyi farin cikin zuwana bane?!”
Da sauri Mama tashiga girgiza mata kai tamkar k’araman yariny’a murmushin tayafi kuka ciwo Zee tayi sannan ta d’ago kanta daga kafad’un mahaifiyarta ta gyara zamanta sannan ta kalla gefenda mahaifinta ke kwance yana bacci duk ya rame yasama zuciyan sa tsananin tunanuka iri iri!
Saurin kawarda idanunta tayi dan bataso ta kwafsa tanaso ta gyara rayuwanta da iyayenta sosai so dolenta tazamana tana k’arfafama kanta da zuciyanta gwiwa murmushi takuma saki akaro na barkatai sannan ta kalla mama da tun d’azun ta kafeta da kallo tanason gano wani abu akwayar idon d’iyarta babu abinda take gani aciki face tausayi hakan zuciyanta ya raya mata kan Zee tausayinsu tafara ji tasan aduaane dakuma wa’azin da Humy kematane suka soma tasiri akan d’iyar tata albarka zuciyanta ya ruk’a kwararama Humy saboda ta gyaramata d’iyarta kafun ta tafi gidan aurenta!
“Mama inawuni?”!
Karo nafarko bayan shekaru masu yawa da mama taji Zee ta kirata da kalman MAMA ! tasan dai insun hadu tana gaisheta amman bata ta6a cemata mama inawuni saidai inawuni! Ayau Zeenta ta kirata da Mama kenan dagaske Zeenta ta gyaru?Allah ya amsa aduaan ta?
Ita kanta Zee saida abin yamata wani bankwarai dan bata saba ba bakinta baisaba ambaton Mama ba saidai momy danne zuciyanta tayi tana maijin zafin kanta!
“Mama! Bazaki amsamun ba ina gaidaki?”
Ta ida maganar tana narai narai da fuska tamkar zata fashe da kuka!
Jany’ota mama tayi ta rungume tana fidda kwalla,a karo nafarko data sake jin d’umin jikin ‘yarta ajikinta, yau ‘yarta mafi sauyuwa awajenta ne rungume ajikinta bayan shekaru aruaru data gujeta take kyamatarta bata son bud’e idanu taganta bakuma taso ta danganta ta amatsayin mahaifiyarta!
STORY CONTINUES BELOW
Itama Zee garetan hakanne saitajita duk kaman awani duniya nadaban a kullum tana runguman momy amman yau runguman da mahaifiyarta ta mata saitaji yafi runguman da momy kemata saitaji d’umin jikin mahaifiyarta dabanne kuma narkewa tayi ajikin mahaifiyarta tana mai sak’a abubuwa dayawa azuciyanta wanda ita kad’ai da mahaliccinta tabarma sani!
Sundau kusan mituna talatin ahaka kafun Zee ta d’ago ta k’urama mahaifiyarta ido wanda itama kallan Zeen take tsantsan soyayyarta tagani a Kwany’an mahaifiyarta! Ganin hawaye sai bin fuskan mahaifiyarta yake yasata d’aukan lallausan tafun hannayenta tashiga gogema mahaifiyar nata sannan alokaci d’aya tana girgiza mata kai alamun ta daina kukan muryan baba ne ya katsesu:
“Zainàbu!”
Yaaar taji wani kala saboda bata sabaji ana kiranta da hakan ba waigowa tayi da sauri ta kalla mahaifin nata:
“Baba”!
Kallan kallo baba da mama sukama juna saboda totally kasa amincewa zuk’atansu take akan Zeen suce wannan hartake kiransu da sunayen su BABA,MAMA!
Murmushi tasakanma baban sannan tace “Allah baka lfy “
Daganan ta mik’e da sauri tabar d’akin tsaban yadda zuciyanta kemata k’una tasan dolenta sai ta koyama Zuciyanta zama da iyayenta dan hakanne kawai zai kaita ga cika burinta amman ina zuciyanta nason kwafsawa,wlh bataso tabud’e idanunta taga wai mahaifinta nak’asaishe ne mai zama a k’ark’ashin abokinsa wlh bataso tanaso itama yau ace mahaifinta wanine a k’asan nigeria koda baa damawa dashi a gwamnati adaice ana damawa dashi a kasuwanci!
Zuciyanta yanzun ya gama bushewa kota halin mainene wlh itama iyayenta sai sunyi arziqi sai sunfita a k’ark’ashin wasu su dogara dakansu kaman kowa!
Amman wai tayaya zata farane ma?!
Dolenta kafun ta azurta kanta tafara azurta iyayenta dan taji dadin yadda zata kutsa duniya kowa yasan tabbas itadin yar masu hannu da shunine sannan ita kanta mai kudin kantace adai san cewa daga tsatson masu kudi take!
“Alhaji any’a wannan Zee ce kuwa?anya ba aljanu bane suka zo mana a sigar Zee d’in?”
Murmushi Baba yayi sannan yace “kayya Fatina karki fad’a haka mana maisa aljanu za suyi disguising kansu suzo mana a matsayin Zainab?zainabun ce dai kawai Allah ya soma dawo da ita hany’a madaidaici yane!”
“Toh abindai da mamaki Alhaji “
“Kimata fatan d’aurewa ahaka kawai “
Daga wannan ranar Zeee ta chanza kwata kwata tadawo kaman ba ita Zee ba mai saurin fushi da zuciya da gadara yanzun tawani zama shuru shuru magana ma ba kasafai ta cika yiba kullum tana cikin muhawara da zuciyanta ta tafka ta warware shine aikinta kullum,takan je wajen iyayenta sau biyu a rana kuma ta zauna suyi hira har mintuna 10 zuwa 15 kafun tamasu sallama takoma d’aki tahau tufka da warwaranta zuciyanta ayanzun shi yazama abokinta dashi take shawara dakuma shi take qulle wanchan ta warware wanchan!
Sosai Zee tasauya tazamana mai sany’in hali kowa yanzun agidan najin dad’in zama da ita musamman iyayenta dan tana zuwa ta gaidasu su d’an ta6a hira sannan ta dawo gun momy wacce tafi kowa jin dadin sauyin Zee har Humy saida momy takira ta kissa mata chanzawan Zee,ai Humy tamkar tasa ruwa a k’asa shiko Yaah Umar chanza wanta bai damesa ba saboda baiga anfanin damunsa dazai ba ita tasani intanaso har qiyama karta ma iyayenta biyayya ruwanta ba nashiba dan bashi zai bata aljanna ko wuta ba wannan yarage ita da mahaliccinta! Shidai kawai yana nuna farin cikin chanza wanta a gaban matarsa dan taji dadi if not ko akwalan rigarsa!
Satin Humy yanzun 3kenan da aure sunacin amarcinsu itada umar dinta babu kama hannun yaro sosai suke gwadama junansu tsantsan So baza shakka kuma basa kunyan nuna soyayyarsu afili akuma ko inane,sosai kowannensu ke dagewa wajen farantama junansu rai sam basa yadda k’aramin abu dasukasan zasu iya magance shi yayi silan 6atawansu sam a kullum suna kiyayewa shiyasa zamansu yayi dadi kowa na mutunta kowa!
STORY CONTINUES BELOW
Yauma kaman kullumtana kwance akan cinyarsa daga ita sai wani mininin dogon riga wanda iyakarsa gwiwanta!
Shikuma yaah umar yanata faman shaqan k’amshin jikinta yana wasada gashin kanta!
“Yaah Umar yaushe zamu abuja wai?”
Kuma shaqan k’amshinta yayi had’ida mata sunba agoshi sannan yace “next week dama nake cewa zamu “
Dasauri ta d’ago kanta tace “dagske sweeetheart “?
Gyad’amata kai yayi sannan yace “amman a surprise zamuje masu kingane karki gayama kowa “
Gyad’a kai tayi sannan tashige jikinsa tana fadin “I love u so much yayana inasonka “
Shima kuma shigarda kansa yayi cikin qirjinta cikin husky voice dinsa yake cewa “ina maki Sanso Humynah “
Dagana ya d’auketa chak yayi d’aki da ita suka shiga farantama juna rai kafun daga baya suka luliya duniyan ma’aurata da sai inkayi auren kawai zakasan wani irin duniya kake shiga aduk lokacinda kuka fad’a duniyan mauratan!
******************************
ABUJA
Wai dagske Zee kaduna aka posta ki?”
Hararanta Zee tayi sannan tace “kee wlh Humy kinga yadda kika chanza kuwa mai Yaah umar ke baki haka?”
“Myswwwe banda iskanci ga tambayan dana maki amman kina bani amsa daban,banson shaqiyanci faa Zee “
Ta6e baki Zee tayi sannan tace “toh kinga yadda kika chanza ne wai ba dole na tambaya ba,zuwan ma zuwan bazata kukai ma mutane fisabilillahi faa?”
Filo Humy ta cillama Zee sannan tace “Wlh Zee bakida kirki kije ki tambayi yaah umar d’in mana “
Daria Zee tayi sannan tace “afwan madame mekikice nabaka nazuba ,eh kaduna aka postani barewa college ma aka turani achan kd din”
Shewa Humy tayi sannan tace “kice k’afata k’afarki gbe sai kd “
“U ain’t serious angaya makii kona zo kdn zan ruk’a zuwa gidankine “
Harara Humy tasakar ma Zeen sannan tace “karkizo mana mtsiwwww”
**************************
“Mama ya jikin baba?”
“Shatu da sauki sosai kinga nanda 3wks ma dadynku zasu fiddashi waje ance angano wani babban likita daya kware a fannin therapist”
“Ma Sha Allah mama in Sha Allah k’arshen matsalan baba yazo da yardan Allah “
“In sha Allah”
Fad’in Zee
Sosai Humy taji dad’in yadda Zee ke muamula da iyayenta a yanzun sosai abin ya faranta ranta!
Kwanansu 2 a abj suka koma kd wanda sam tun zuwansu abj Zee bata sanya Yaah umar a ido ba hakan bai dameta ba dan kotaji muryansa suna hira da momy ba saukowa takeba itakam Humy tayi magiyar harta gaji amman zee taqi zuwa tagaida Umar!
“Sweetest kaga kd fa akai postn Zee”
Ta6e baki yayi sannan yasaka plantain a bakinsa kuma kallonsa tayi azatonta baiji mai tace bane hakan yasata kuma nanatawa “Sweeetheart Zee kd aka turata NYSC a barewa college “
Shayinshi yayi sinipping sannn ya kalleta yaga shi take kallo tana jiran amsanta!
“Okay “
“Amman nifa nace mata zaman camp bai kamata ba….:.::
Da sauri ya k’atseta yace sai zaman ina ya kamata?”
Murmushi tayi tace “nan mana “
Ajiye cup din hannunsa yayi sannan ya kallota da kyau yace “ina ne nan?”
Ba tareda tadamu da kallon dayake mata ba tace “nan gidan nake nufi zatazo tazauna har ta kammala service din ina barewa college ina malali?”
Kallonta yayi sosai yaga harga Allah iyakan gaskian ta take gayamai “ban amince ba “
“Habadai yaah Umar aiko dady ma dana kira na fadamai ya aminta kuma yayi convincing Zee ma itama tayadda zatazo nan tazauna din amman daa taqi saida Su dady sukai mata magana da fad’amata hatsartsarin zama camp!”
“Nace ban amince Zee ta zo gidana ta tare ba “!
Ta6e baki tayi dan gaskia itafa bazata bar ‘yar uwarta tayi zaman camp ba tana zaune agarin kaduna! Saidai yaah umar gaskia yayi haquri dan wannan karan kam she won’t listen to him!
“Humm yaah umar u have to pls kbarta shekara d’ayane kawai fa dan Allah yazan barta tayi zaman camp bacin gani agarin da take service “
“Humy that my final decision “
Narai narai tayi da idanu tamkar mai shirin kuka sannan tace “ok shikenan indai bazaka barta tazo gidan nan ba nima camp din zan koma sai sadda nagama service dina sannan nadawo “
Kallonta yayi yaga iyakan gaskian ta tafad’amai baice uffanba ya miqe yabar mata gidan gaba d’aya!
Da kyardai da magiya Humy tasamu Yaah umar ya amince Zee tadawo gidansu dazama dad’i ranar kaman tasa ruwa a k’asa tasha murmushi kawai Umar keyi sannan yace “I only did this for u saboda farincikin ki kawai na amince “
Dad’a rungumansa tayi tace”I love u so much mijina “
******************************
Yau saura 3days su mama sutafi k’asan Singapore ?? dan samun lafian baba both dady da momy da mama zasu tafi Zee kuma zata wuce kaduna dan soma service dinta!
Yau duk ta qillace komai nata dazata buqata sosai iyayenta suka mata nasiha qarfe 2 tabi jirgi ta iso kd cikeda kewan iyayenta da fatan Allah bama mahaifinta lfy mai dorewa!
Driver dinsu Humy ne yazo yadauketa a airport dan Humy ita tafara nata service din a CBN na kaduna!
Koda suka iso bakowa agida hakan yasata zaman falo tanajiran dawowan en gidan!
K’arfe 5:30pm Humy da yaah umar suka dawo dasauri ta fito a motan dan ta k’agu taganta gaban Zee girgiza kai kurum Umar yayi dan shi ya rasa wacha kaliyar soyayyah Humy kema Zee tsakaninta da Allah take k’aunan yarinyannan!
“Pls Yaah umar for the sake of my love karka ruk’a nuna tsanan Zee agabanta kaga she will feel uncomfortable dan Allah ka danne zuciyanka kazauna da ita amatsayin ‘yar uwar mu pls kaji”
Gyad’a mata kai yayi sannan yace “ok ma I promise “
Maganan dasukai yau dasafe kenan ya shiga ringing a kwakwalwansa murmushi yayi sannan ya kashe motar yafito!
Da gudunta tashugo falan ji kawai Zee tayi an rungumeta daga sama k’amshin turarenta yasanya ta sanin Humy ce itama cikin jin dadin ganin er uwar tata kuma aminiyarta ta kuma rungumeta suna ihun murna!
Tsaye yayi yana kallonsu kawai dan wani sain insun hadu suna shiriritar su tamkar yara haka sukeyi!
Zee ce ta lura dashi hakan yasata janyewa daga jikin Humy fuskanta bayabo ba fallasa itama Humyn kallanta tayi sannan ta kalla yaah umar murmushi tayi sannan tace “Zee baki gaida yaah umarba “
D’ago kanta tayi ta kalla umar din a karo Na farko dataji yamata kwarjini a fuska hakan yasata takowa har inda yake tsaye yana kallansu miqamai hannu tayi tana murmushi tace “Hy yaah umar “
Kallan hannun nata datake shirin basa suyi handshake ya kalla sannan ya kalla Humy alamu tamai akan ya bata nasa hannun mana miqa mata hannun sa shima yayi sukayi handshake ? sannan yace “Hy barkanki “
Jany’e hannunta tayi tana murmushi tace thank u yaah Umar”
A lallai dagaske Zee ta chanza sosai ta chanza halayyanta tinda har yau ta tsaya sunyi magana da yaah UMAR
Humy ke kissa hakan azuciyanta!
Wucewa yayi ya haura sama yabarsu suna cigaba da murnan ganin junansu….,,,,,………Mintsilin hannunta tayi dan tabbatarda ba mafarki take ba,kai no wlh mafarkine ko kuma imaginary thoughts ne kawai takeyi.Toh in haka ne man ta daina tunanin! Mintsilin kanta tashigayi sosai a lokaci guda kuma tana girgiza kai “no no! It can be wlh wannan ba yaah umar d’inta bane wlh mafarki nake wlh kawai shaid’an ne ke samun wannan tunanin,Auzubillahi minaishaid’anir rajim!”
Tuf tuf tuf tashiga tofi ako ina a falon tamkar wata zararriya,ganin abin nason zarce tunanin ta yasata saurin hayewa stairs din falan dazai sadata,da d’akin umar d’in bud’e k’ofan tayi ta iske shi zaune akan gadon sa ya kishingid’a kansa akan filo ya lumshe idanun sa da alama ba bacci yake yiba da sauri saurinta gudu gudu ta fad’a jikinsa tana sauke lumfashi runtsa idanunta tayi ta kuma kwantarda kanta akan k’irjinsa!+
Kaman daga sama yaji mutum kwance a k’irjinsa bud’e idanun yayi ya sauke akan fuskanta runtsa idanunsa gam gam yayi sannan yasa hannunsa ya tureta da sauri a jikinsa har tana fad’awa a k’asa dan a gefen gado yake kishingid’e,ai a 360 ta bud’e idanunta tana kallonsa gani tayi kwayan idanunsa sun juye sunyi wiki wiki sunyi jazur hankalinta yayi mugun tashi dan koda wasa bata ta6a experiencing yaah umar haka ba “lahaula wala k’uwayta illa billah,”
_toh da shaye shaye akace maki na tsayayi har k’arfe 1_”
Amsan daya gaya mata d’azun tayi ringing a kwakwalwanta “kodai Yaah umar shaye shayen yafara da gaske shiyasa yamata gatse d’azun?inba abu ya sha ya bugu ba tayaya launin idanunsa zasu chanza?”
“Fitanmun a d’aki Aisha!”
Galalo tazuba masa many’an idanunta da kyar ta had’o sauran kuzarinta sannan ta iya had’a kalmomi uku “infitan ma d’aki?”
Ba tareda ya kalleta ba yace “yes haka nace “
Mik’ewa tayi tazo daf dashi sannan tace;
“Haba u most be kidding yaah umar kaga banson wannan wasan wlh , kadaina pls kaima kasan bazan iya resisting kalan wasan nan ba pls kabari ka chanza salon wasan amman ba kalan wannan ba “
Komai ya tuna oho kawai sai ya fashe da daria yasoma nunata da yatsa yana daria,k’arema jikinta kallo tasomayi dan ganin wat funny a jikin nata!
“Matsoraciya kawai “
D’agowa tayi tana kallansa da mamaki dan abin sai take gani tamkar a film ko novel!
“Gaskia kin tsure dayawa dama haka kike da tsoro “
Ballomai harara tayi sannan ta d’au filo ta wurga mai tana chuno bakinta tana fad’in “wlh yaah umar na tsorata mai hakan toh?mai anfanin yinsa?mai yasa kake dawowa so late?ehmn ummm?why?”
Da ido kawai ya bita sannan ya sauko akan gadon ya k’araso daf inda take har yana iya jiyo bugun tsoronda zuciyanta keyi!
Rungumeta yayi itako kaman wacce aka jonama shocking haka ta tsaya takasa runguman sa back!dan abin sai take ganin kaman wasa da kwakwalwanta kawai yake!
“Dear duk tambayoyin nan ni kad’ai?gaskia bazan iya am sasu ba sai gbe da safe am very tired now bacci nake ji “
“Amma……………
Bai bari ta k’arasa maganan dake bakin taba yasa hannunsa akan bakinta yace
“Shhhh not now nace sai gbe da safe good nyt ki kashe wutan d’akin”
Wuf ya fad’a akan gado,sororo tabisa da kallo!
Wlh ita kwakwalwanta ma kasa furta koda kalma d’aya tak yayi barema ace zata iya tambayan shin maike faruwa?brain d’inta tsayawa yayi chak ya kasa koda tunanin abinda ke gabansa!
Tafi k’arfin mintuna 30a tsaye ta kasa koda kwakwaran motsi!
“Bazaki kashe wutan bane kidaina mun tsaye akai ba?”
Muk’ut ta had’iya wani miyau da kyar kuzarinta ya gifto ta d’an ja k’afafunta tamkar wacce kwai ya fashewa aciki har wajen abin kashe wuta! Waigowa tayi ta kallesa yayi kwanciyansa ransa lahia lau tamkar babu abinda yayi! Kashe wutan tayi sannan a hankali tazo ta kwanta chan nesa dashi kowa kwance a edges d’in gado!
STORY CONTINUES BELOW
Tun tana jira taji yaah Umar ya mirgino ya rungomota dan ba haka suke bacci ba infact kullum d’aukanta yake in lokacin baccinsu yayi in bridal style ya kaita har kan gadansu ya shifid’eta shima yazo ya kwanta rungume da ita a jikinsa!
Amman taji shuru har waigowa take amman sai gani tayi baccima yayi awan gaba dashi!
Kai abu kaman almara all of a sudden ace mutum ya chanza tamkar wanda aljanu suka shafa ?”
Shine abinda taketa saqawa a ranta!
Toh waima wani kalan tunani ya kamata tayi dan abin nan tamkar almara ko mafarki wat going on?”
Juyi taruqa yi akan gadon nan ta kasa sanin abinyi jira kawai take gbe da safe yayi wlh sai ya gaya mata y d sudden change mai haka sai kace wani ta6a6e?da kyar da kyar dai ta samu bacci 6arawo yayi gaba da ita!
******************************
@ 7:30Am daidai ta soma bud’e idanunta a hankali a hankali har ta bud’esu tangarau akan k’aton hoton su dake manne a bangon d’akin ,sannun a hankali kuma kwakwalwanta yasoma mata flashing back abinda ya faru a daren jia da sauri kaman wata ta6a6iya ta kalla side din da yayi bacci amman wayam ba mutum akai da sauri ta mik’e akan gadon tana kallon agogo 7:30Am kuma tasandai yaah Umar bai tashi a bacci bayan ya koma daga sallan asuba sai 9 kafun 10 ya gama shiri ya tafi office,tasan tana fashin salla shiyasa bai tasheta sallan asuba ba but amman mai faru ya tashi dawuri,da sauri tawuce toilet d’in d’akin ta d’an kasa kunne kozataji motsin mutum ko motsin ruwa amman shuru hakan yasata murd’a k’ofan bayin tajishi tagarau a bud’e lek’awa tayi ba kowa hakan yasata saurin fitowa ta bud’e k’ofan d’akin ta fito ta lek’a nata d’akin ko yana ciki shima har bayin d’akin bayanan wayam!
Da sauri sauri da sarsarfa ta sauko daga stairs tana d’an kwala kiran sunansa amman shuru kaman an shuka dusa.Babu inda bata shiga acikin gidan ba lungu da saqo amman ba yaah umar ba labarinsa da sauri ta nufa parking lots sai anan ta tarar babu motansa sai nata dana gida kawai da sauri ta k’arasa wajen mai gadi tana kwalamai kira:
“Isa ina yaah umar yaushe ya fita?”
Kallonta yayi yaga kaman bata cikin hayyacinta sannan yayi mamakin tambayan datamai toh d’aki daban suke kwanane dazai fita bata saniba?!
“Isa magana fa nake ina yaah umar “
Yace:”hajia oga ya fita tun wajen 6:30 ai “
“Yafita?”
“Eh kaman ma fitan shirin office yayi ai “
Bata sake mai magana bata ta juya ta wuce ciki mamaki fal ranta,shiko maigadi girgiza kai yayi ya shiga d’aki abinsa dan a tunaninsa fad’an mata da miji sukai shine ya tafi bai sanar mata ba!
Zagaye falan nata takeyi hannunta rik’e da wayanta sai safa da marwa takeyi a karo na 5 data kuma laluban lanbansa amman answern d’aya ce  *line busy*!
Bubbuga forehead d’inta da tafin hannun hagunta take yi tana fidda huci
“Yaah Umar pic d call waidawa kake waya “
Kuma trying tayi d’an tsayawa chak tayi dan wayan yashiga tana ringing gani tayi an sa user busy maana yamata rejecting kira sororo tabi wayan da kallo:”ni yaah umar zai katsema kira?ni Humy ni yaah umar zaima rejecting call?yaa Allah!wai mai ke shirin faruwane?”
Dasauri kaman wacce aka mitsitsina ta shiga laluban lanban Zee bugu d’aya Zee da fitowanta daga toilet kenan taji wayanta na k’ara da sauri ta k’arasa ta d’au wayan ganin Humy ne tayi saurin d’auka daman yanzun take shirin kiranta danjin yadda ta kwana jiyan nan sam takasa runtsawa wlh dataji muryan Humyn nata cikeda damuwa !
“Hello Humy ykk?yaa gida ina yaah umar d’in mai yace makii jia ina yaje?”
Jeromata tambayoyin tayi a tare! Ba tareda Humy taba Zeen duka amsoshin tambayoyinta ba tace “Zee dan Allah kidawo kizo kd yau pls kibi jirgin k’arfe 2pm kizo dan Allah I can’t handle this alone am going emotional “
Jim Zee tayi dan bataso ta koma gidan Humy dan harga Allah gani takeyi kaman tana takuramasu basu sakewa sosai intana wajen sau dayaw in Yaah umar nason ma Humy wani abun ganin idonta baya Mata, itama Humyn haka toh maiyasa zataje ta takura masu!
STORY CONTINUES BELOW
And gashi mahaifinta yanzun kam jiki Alhamdulilah yana takawa kuma yana wasu abubuwan dakansa ba tareda ya naima taimakon kowa ba! Yanzun ne fa ya kamata tasoma cika burinta yanzun ne ya kamata tasa iyayenta su azurta!
So takeyi dama tasan yadda zatayi amata transfer back to Abj ammn Humy ta bijiro da wai tadawo kd !
Amman dole kuma ya kamata taje taga halinda er uwarta ke ciki she have to dan Humy ta mata abubuwa dayawa a rayuwan nan wanda a yanzun tana buk’atan taimakonta amman zuciyanta nason k’in amincewa? Itace kawai fa ‘yar uwarta sauran en uwanta duk mazane fa ba kuma komai that matters btwn ita da mijinta ya kamata ta fad’ama momy ba,she have to go ya kamata taje dolema takoma kd yau d’inan dan ganin mai yaah umar keson yima Humy any’a shine kuwa?!
“Zee baki jina ne ?”
Firgit Zee ta dawo daga tunanin da takeyi dafe goshinta da tafin hannunta tayi snnan tace “okey Zee yau zan dawo ganinan zuwa “
“Sai kinzo amman karki sanarma su Momy abinda ya faru plss “
“Ok trust me bazan fad’i ba “
Kashe wayan sukai a tare Zee ta wuce tasoma had’a kayanta ita kuma Humy ta wuce d’aki zuciyanta tamkar ya faso dan fargaba!
******************************
3pm
Daidai Drivern Humy ya dire Zee a gidan da saurinta ta shugo cikin falan amman bata nan hakan yasata shiga d’akin Humy isketa tayi raku6e a k’arshen gado ta had’a k’afafunta da jikinta ta takuresu a wuri d’aya!
Da sauri ta iso wajenta sannan ta rungumeta Humy naganin Zee ne dama kad’an take jira ta fashe da kuka mai ta6a rai saketa Zee tayi sannan ta had’e ranta tamau ta dawo asalin Zee d’inta na daa mai bone fuska!
Kallanta Humy tayi tanason ganin mai yasata had’arai da bone fuska haka!
“Dukanki yayine?”
Share hawayenta Humy tayi sannan tace “zauna barka da zuwa ya jikin Baba?”
Zama Zee tayi sannan tace “ban amsata dukanki yayi?”
“Aa “
“Toh mai yayi mai yasa kikazo kika takura kanki anan?”
Lumfashi Humy taja sannan ta dafa hannun Zee tace “wlh Zee ban san mai ke going ba I just don’t knw mai yasa yaah umar ya soma chnzawa jia fa bayan mungama waya ya dawo……..:.::
Nan Humy ta fayyacema Zee komai dayafaru ita da Yaah umar a daran jia har yau da safe da yayi tafiyansa ba tareda saninta ba!
“Kaman yaa wasa yake maki?”
“Haka yace kinsan Allah kaman wani wanda yasama ta6in aljanu “
Tsaki Zee tayi sannan tace “iskancin banza kozai yi wasansa sai  yasaki aciki?mai anfanin abinda yake yi d’in toh bari yadawo dole ya mana bayani “
Kwantarma Humy hankali Zee ta shigayi da kyar tasamu Humyn tayi wanka taci abinci!
Har wajen 11:30pm babu umar babu labarinsa takira wayansa yafi sau 30 amman bai d’auka ba ta kira shi ta wayan Zee ma yaqi d’auka sosai hankalinta yakai k’ololuwan tashi!
“Zee anya ba shaye shaye Yah umar ya fara ba kuwa?kiga fa bai daukan calls dinmu ma,Allah Zee nidai nafara tsorata da wannan al’amarin “
Da sauri Zee ta kamata ta zaunar da ita dan Humy kaman tafara fita a hayyacinta dafata Zee tayi:
“HUMY”!
Kallonta Humy tayi ba tace komai ba Zee ta lumfasa sannan tace “Haba kidaina fad’in irin maganganun nan mana kibari yadawo mu tsaresa dolen sa ya gaya mana wani kalan stupid attitude ne ya bijiro dashi “
Humy bata kaiga bama Zee amsa ba sukaji an sa key an bud’e k’ofan falan sororo suka Zuba mai ido suna kallonsa tamkar Tv,idasa shugowa yayi ya rufe k’ofan sannn ya kallo inda suke kallo d’aya yamasu ya cire idanunsa akan su yayi haurawan sa upstairs Zuciyansa na tafarfasa ganin Zee ta dawo mai gida “ko uwar mai tadawo yimasa a gida oho shifa wlh ya tsana ganin yariny’an nan a gidansa alfarman Humy kawai take ci amman zaiyi maganinta sai tabar masa gida “
Tsaki ya kuma ja yayi shigewarsa d’aki !
STORY CONTINUES BELOW
Bin bayansa da kallo kawai sukai dan abin ya girmama zatonsu yaah umar bai ta6a dawowa yayi shigewansa d’aki ba tunda suke a rayuwan nan ko kafun auransu indai Humy na waje kuma yazo to in sha Allahu sai ya tsaya awajen komin saurin da yakeyi kuwa all his time is for Humy!
Zee ce tace “tirk’ashi abinga da mamaki “
Sai asannan Humy tacire idanunta daga kallon inda yabi ta saukesu akan Zee wacce tsananin mamakin abinda Umar ya aikata yaqi barin fuskanta!
“Wlh Zee nafara tsoro,any’a ba aljana bace ta shiga ta aure mun miji ba?”
Kallanta Zee tayi sosai sannan tace “wani kalan aljana kuma kina nufin jinnul ashiqi?”
“Ehamana zee inba haka ba why zai chanza all of a sudden?”
“Kinga Humy mik’e kije d’akin nasa kisan tayadda zaayi ki sauko dashi yazo falo “
“Zee baki ganin ko nuna Allah ya haliccemun a wajen nan baiyiba yayi tafiyansa innaje ya dukeni fa?dan wlh nafara tsorata da yaah Umar wlh kaman da aljanu ajikinsa “
“Wani kalan bugunki zaiyi malama Jeki san yadda zakiyi kice ya sauko wlh inba haka ba gobe goben nan ina mai kiran su dady nakai k’aran sa ai in yafi k’arfin mu baifi k’arfin su Dady ba “!
Mik’ewa Humy tayi jiki ba kwari ta wuce d’akinsa Zee tabita da kallon tausayi,knocking tayi jin anqi bata izinin shugowa ya sata bud’e d’akin kawai ta shiga,kallan d’akin tayi baya ciki amman taji k’aran ruwa da alama wanka yake samun gefen gado tayi ta zauna tana jiran fitowansa amman zuciyanta fal mamaki da tsoro wlh ita ganin komai take kaman a mafarki ko kuma karanta novel take a toh abu kamar juyin agogo a second da basu wuce a k’irga ba ace mutum ya rikid’e yadawo wani daban kaman wanda akama asiri ko shafun aljanu!
Bud’e k’ofan toilet d’in da yayi ne yasata datse tunanin da takeyi,tayi saurin kallansa!
Turus ya tsaya yana kallanta ya tsaida goge jikinsa da yakeyi da towel da sauri ya shiga warware towel d’in yana rufe k’irjinsa sa da ruwa ya jik’e gashin k’irjinsa suka k’onta suluf a qirjin nasa!
Rufe k’irjinsa da Towel d’in yayi a lokaci d’aya kuma yana sakan mata harara tsaban mamakin abinda yayi ta shiga kallan d’akin kozata ga wani ko wata dake zaune a d’akin yasa shii saurin rufe k’irjinsa,amman taga wayam daga ita sai shi a d’akin toh ita yake kullema k’irjinsa ko wa?”
Batakaiga samun amsan magananta ba taji yace:
“Fita “
Da mamaki tace “In fita inje ina?yau nasaba ganinka ba kaya?komai?in fita kasa kaya kake nufi ko mai?”
“Fita zakiyi ki wuce d’akinki bacci zanyi “
Da mamaki ta kuma ce masa “bangane naje d’akina ba,naga anan nake kwana gado d’aya muke kwana rungume da juna “
Maganganunta sunfara isan brain d’insa bazai iya dogon surutu ba hakan yasa shi k’arasowa inda take ya finciko hannunta yayi hany’an k’ofa da ita duk tirjewan da takeyi bai hanasa hankad’a ta ba har tana shirin fad’awa sannan ya nunata da hannu:
“Kee! Kifita agonata Aysha karki bari na damqo ki acikin gidan nan dan wlh hakan bazai maki dad’i ba u should better respect ur self daga yau na raba shimfid’a dake karki sake shugomin d’aki that’s ur room over there karki kuma shugomin nawa d’akin if not wlh zan 6a66allaki nayi gunduwa gunduwa dake “
Bagam taji ya rufe k’ofa d’akin zata iya rantsewa bataga shigansa d’akinba rufo qofan kawai tagani!
Kasa motsi kasa tunani tayi tama rasa wlh mai zatayi kuka?ko mai?mai zatayi wlh bata saniba!
Zee da gudunta ta k’araso Inda take dan akan idonta ya rufe k’ofansa harda dannamaa k’ofan key!
Zee kam mamaki ya isheta tama kasa sanin mai zatayi!
Rungume Humyn kawai tayi atake kaman had’in baki suka fashe da kuka Na ban tausayi!
Janta Zee tayi suka shiga d’akin Humyn!
Zaunar da ita tayi akan gadonta sannan ta wuce ta rufo k’ofan d’akin tadawo wajen Humy dake zaune takasa furta koda kalma d’aya tak a kwakwalwanta bare bakinta ya furta!
“Humy mai yake shirin faruwa waii mai yayah umar ke nufi?mai ribar abinda yayi ayanzun?”
Fashewa da kuka Humy tayi sannan cikin muryan kuka tace:
“Zee any’a kuwa ba jikina kawai yaah umar keso ba?”
Saurin kallon Humyn Zee tayi a mamakince tace “kaman yaa I don’t get u jikinki yake so kaman yaa?a in how?”
Bayan hannunta tasa a fuskanta tana goge hawayenta tana fad’in “jikina ya aura ba gangan jikina ba (soul) jikina yake so ba soul d’ina ba,wlh shine ma yau nagano dalilinsa Na chanzamun “
Ganin sai 6aro zance kawai Humy keyi yasata saurin kamata tace “Humy oya ki natsu kimin bayani yadda zan gane “
Kallan Zee Humy tayi cikin ido tace “I mean he only wish to have sex with me! Yasan taste d’ina kawai shiyasa ya soni kuma ya aureni “
“A haba tayaya zakice haka how on earth zai soki dan yaji taste d’inki tunfa kina ciki yake sonki ya raineki har girmanki ya soki har ya aure ki,kawai dai there is somtn hidden dabamu sani bane!”
“Amman batun wai jikinki yakeso bai tasoba dan tun bakida komai yake sonki “
“Wallahi Zee hakanne ma jikina wlh Yaah Umar keso yanzun tunda ya sanni in and out zaiyi dumping d’ina yau watanmu 3 da aure yagama sanina ya bud’eni yamaidani cikakkiyar mace ai yanzun ban gaban sa am not longer budurwa “
“U are just talking bulshits Humy sam maganganun nan kwakwalwa ma bazata iya d’aukansu ba,pls kidaina tunanin hakan ke kanki kinsa k’aryanshi yace ya aureki dan jikinki bane wlh u deserve to be loved by everyone ko mata duk inda suka ganki sai sun soki kinzama k’awarsu bare maza! Shi ai shaidane uwar samarin da kika kora duk dan ki kare soyayyar sa,sai a yanzun ne zai bijiro maki a haka wlh Sai ansanar masu Dady in ma aljanune suka shigesa toh mu masu cin uwarsu ne “

About AIS

Check Also

AMANAR MU CHAPTER 8

AMANAR MU CHAPTER 8 Www.bankinhausanovels.com.ng  Bud’e idanuwan ta tayi tagan ta cikin wani irin  yanayi. …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *