ABU-MALEEK CHAPTER 9 BY Nimcyluv

ABU-MALEEK CHAPTER 9 BY Nimcyluv

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da wani irin sabon tashin hankali Oumuu-Ayman ta shiga girgiza kanta,

Abu Maleek ko a jikinsa ya shirya idan har Mahaifin nasa zai samu lafiya,

Ya rasa uwa mahaifiya dan haka ba zai yi saken da zai rasa mahaifin sa ba,

Oumuu-Ayman ce taka numfashi tare da kallon makamin gaba ɗaya hankalinta yaƙi kwanciya da wannan tafiyar da Jalaluldeen zaiyi,

Cikin damuwa tace.

“Jalaluldeen zai zauna da mahaifinsa, zan sanya ɗaya daga cikin fadawa suje nemu maganin”

Da sauri Makamin ya girgiza kansa yace.

“Hakan bamai yiwuwa bane, jinin King Tunde Muhammad Jalal ake buƙata yaje da kansa, idan ya shirya tafiyar zan faɗa masa ta ƙasashen da zaibi”

Kafin kowa yayi magana Abu Maleek dake zaune ya rungome King Tunde a hankali ya fesar da numfashi tare da sauke ajjiyar zuciya,

Cikin rashin damuwa da haɗarin da tafiyar take dashi yace.

“Gobe zan tafi, ka faɗi da komai na tafiyar”

Gaba ɗaya suka kallesa, sosai Abu Maleek ke ƙaunar iyayensa kamar yadda suke ƙaunar sa, 

Cikin fahimtar maganar ta Abu Maleek Malamin yace.

“Ta kasashe biyu zaka shige ƙasar dake gaban Guinea itace Birnin Bera, zaka tsaya a wata rugar Fulani, wacce ake ce mata Rugar Mahinjo, daga nan zaka samu dukkan bayanan da zai sadaka da Birnin Bera”

Ya faɗa yana zaro wata peper daga cikin aljihunsa,

Kana ya ɗura da faɗin.

“Wannan taswirar wajance koda zaka ɓata a hanya, kana duba taswirar zaka Fahimci inda kake”

Abu Maleek bai ce komai, idanunsa akan fuskar King Tunde Muhammad Jalal wanda kawo yazo ko buɗe ido baya iyawa,

Hannunsa ya ƙanƙame a hannun Abu Maleek,

A cikin ransa ji yake inama zai iya buɗe baki yayi magana ko kuma zai iya rubutu,

Da babu abinda zai sanya yabar Abu Maleek ya yi wannan tafiyar,

Yayi imani abinda suke tunani sam ba haka bane,

Shi kaɗai yasan abinda ya samesa jiya bayan kowa ya tafi wajan bikin ODUN EGUN.

Oumuu-Ayman ce ta amshi taswirar idanunta ya ciccika da ƙwallar tausayin Abu Maleek da kuma halin da zai iya tsintar kansa a cikin tafiyar.

Sallama Malamin yayi masu kana yabar wajan Otun ne ya miƙe tare da mara masa baya saboda rakasa hanya.

A sanyaye Abu Maleek ya kwantar da king Tunde, kana ya gyara masa kwanciya, ba tare daya kula kowa na wajan ba, ya nufi sashinsa fuskarsa a ɗaure kamar hadari.

Yana miƙewa Kubraah ta miƙe tare da mara masa baya, yana tafe dafe da kansa Kubraah na bayansa, sarai yaji footsteps,

Amma bai kawo cewa Kubraah bace, shi harga Allah mantawa yake yana da wasu mata,

To ba dole ya manta ba, aure har biyu without his permission,

Babu wacce yana so daga ciki gwamma Auran Bola ƙaddara ta haɗa Auran,

Amma ko a yanzu da zai san gaskiyar dake ɓoye Tabbas itama da bazai zauna da ita ba,

Shi babu mace a sabgarsa, mantawa yake akwai wani abu dake shiga tsakanin ma’auratan,

To kuma ya sani ba sai yana da lafiyar yi ba, yana shiga Main Parlo nasa ya tsaya cak,

Sabida yana son yajin dalilin daya sanya Oumuu-Ayman take biyosa, idan ma tazo domin ta hanasa wannan tafiyar to tabbatas ta makara,

Yana nan tsaye yana sauke numfashi tare da taune leɓansa wanda sukai jajirr saboda yawan tsotse su da yake,

Bai an kara ba yaji Kubraah ta faɗa jikinsa ta baya tare da rungomesa.

      *Karatun ABU MALEEK yana buƙatar nutsuwa, daman na faɗa maku salonsa nada banne, zazzafar soyayya ce wacce tafi ƙarfin a haɗa ta data Laylerh da Majanun, balle kuma ta ROMOE DA JUILET, zata fi dacewa ka haɗa ta da Film ɗin TAITAINIK??*

Wani irin sarawa kansa yayi ransa ya ɓaci sabida tsabar raini, kamar shi wata zata haɗa jikinta da nasa,

Cikin sabon wani ɓacin ran, ya wani juya da sauri tare dasa hannunsa ya ɓanɓareta a jikinsa,

Kuka Kubraah ta sanya tare da ƙoƙarin ƙara rungomesa,

Da wani sauri yaja baya ya shiga nuna mata hanyar fita daga sashin nasa, cikin kuka tace.

“Why? Mene yasa Abu Maleek? Ni matar kace, tunda akai Aure na dakai babu taɓa magana ba, ban taɓa sanyaka a cikin idanuna ba, balle na zauna muyi magana dakai har naji ɗumin jikinka,

Nifa macace ina da rauni idan zaka iya zama ba tare da mace ba, ni sam ba zan iya zama babu namiji ba, da haƙurin mata dana maza ba iri ɗaya bane,

Ka tausaya min Abu Maleek ka sauke haƙƙin dake kanka kafin ka tafi, babu da tabbacin zaka dawo a raye ko kuma ajalinka zai riskeka a can ne, pls My dear try to understand my feelings”

Tunda ta fara magana ya kafeta da Manyan gajiyayyun idanunsa, so itace second wife ɗin da Salimerh tace King Tunde ya aura masa ita,

Why duk samarin gidan sai shi za’a aurawa mata har biya, matanma da babu wacce ya taɓa cewa yana so,

Ko kuma ɗan taure ya zama suna ganinsa yana bin mata a guje shiyasa sukai decided na aure mace ba tare da izininsa ba,

Shi gaba ɗaya baiga abinsu a jikinsu, ko wacce ƴar banza da nono bai fi tafin hannunsa ba,

Gajeran tsaki yaja tare da juya zai shige part ɗinsa yaji ta ƙara.

   *Yau free pages zasu ƙare hanzarta biya domin ki zama mace ta farko da zata shiga vip, it’s 500 for vip posting biyu kullum, and 300 for nrml grp ba kullum za’a ake posting ba via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616*

 Sanya masa wani gigitaccen kuka, wanda ya ƙara haddasa tsarawar kansa,

Wannan idan bai taka mata birki ba, Tabbas zata mayar da shi mahaukaci,

Cikin ƙosawa da ihun nata yaja jikinsa zuwa jikin wata luntsumammiyar kujera ya zauna,

Idanunsa yaje ya rufe, a jikinsa yaji ana kallonsa ware jajayen idanunsa yay idanunsa ya sauka akan Kubraah wacce ta tsorawa faffaɗan ƙirjinsa idanu,

Da wani irin sauri ya tattare rigarsa tare da rufe ƙirjinsa baki ɗaya, kafin cikin haɗa fuska yace.

“Me kike buƙata?”

Da sauri taja jikinta zata zauna kusa dashi yayi saurin ɗaga mata hannu,

Hakan ya tilasta mata tsayawa tace.

“Sleep with me tonight, ka kwanta dani Abu Maleek koda baka sauke nauyin dake kanka ba, just romance is okay to me”

A fili yace “O’ohhh”

Jin kalmar Romance yasa ya taɓe baki, kada Allah ya kawo masa wannan ranar da zai ƙwaƙume mace kamar maye, shi gaba ɗaya ba’a fahimtar wanene shi, bashi da lafiyar zaiyi wata tarayya da mace, shiyasa ya ƙauracewa duk wata sabga ta mata,

Domin baya son raini da wulaƙanci, mace kowa da zarar ta Fahimci baka da ishasshiyyar lafiyar da zaka kwanta da ita shikenan ka shiga uku,

Miƙewa yayi tsaye ya shiga taka ƙafafuwansa cike da zallar isa nutsuwarsa,

Al’amarin daya ƙara rikita Kubraah kenan taji gaba ɗaya babu wanda take buƙata a yanzu sai mijinta,

Cak ya tsaya ba tare daya juya ba yace.

“You’re dreaming you poor Kubraah Kabal, jikina sai daga nesa”

Cikin ɓacin rai ta kallesa wato yana san full name ɗinta kenan ko?

Kamar zatai masifa sai kuma tace.

“Idan haka ne, kenan ya tabbata cewa kai lusari ne, wanda bashi da cikakkiyar Lafiya, ko dai abar taka ce bata aiki shiyasa kake ɓoyewa now i understand, to bazan iya zama da namiji lusari ba ina da cikakkiyar lafiyar”

Hannayensa ya watsa irin i don’t care ɗin nan kafin yace.

“Ok I’ll  divorce you Kubraah Kabal”

Ba tare da tunanin da gaske zai iya aikata abinda yace ba tace.

“So What? Nasan wallahi u can’t divorce me, na same maka ƙarfan ƙafan Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal”

Taɓe baki yayi domin ta fara cikasa da magana kamar zai gaba ya barta sai kuma yace.

“Saki ɗaya, saki biyu saki uku, no more relationship between us”

Yana faɗin hakan ya ɓace daga gabanta kamar walƙiya,

Tashin hankali wajan Kubraah Kabal ba’a magana, ihu ta fara tare da cire zani ana faɗuwa ƙasa,

Da gudu kuma ta nufi sashin Mai Babban ɗaki, tana zuwa ta sameta ita da Oumuu-Ayman,

Ganin tashin hankali a fuskar Kubraah Kabal ya sanya Mai Babban ɗaki kwallon ta, ba tare kuma da tayi magana ba, taci gaba da duba kayan da Abu Maleek zai tafi dasu.

Zubewa tayi gaban Mai Babban ɗaki ta shiga surutai,

Wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Oumuu-Ayman ta sauke, at least wani mummunan shashi yabar Abu Maleek,

Mai Babban ɗaki ta ja numfashi tare da kallon Kubraah Kabal tace.

“Kinyi kuskure biyewa Zaki, kinsan matsalar sa kin san damuwar sa musamman yanzu da yake cikin damuwa, kamata yayi ki samu ki kwantar masa da hankali, yanzu ba lallai yana cikin hayyacinsa yay maki wannan sakin ba,

King Tunde yana da mata biyu, Queen Ayoola sai kuma Queen Roomana, Queen Ayoola yaranta guda uku ne, Aremo Shakiru, Aremo Sharefddeen, gaba ɗaya kuma sune manya ƙaramar su ce Salimerh, Queen Roomana tana da yara biyu Babban shine Aremo Adams sai kuma Zaki na Jalaluldeen wanda ake ce masa Abu Maleek,

Junaid ɗane wajan Otun (Galadima) Galadima kuma ƙanine wajan King Tunde Muhammad Jalal, mene ya sanya kaf cikin samarin babu wanda yake da mata sai ƙaramin cikin su Abu Maleek? Mene yasa kuma aka haɗa shi da mata har biyu? Baki da Wannan masaniyar ko? Mene yasa sunan Abu Maleek ya bisa? Baki sani ba? Kin san dai cewa MALEEK ɗa ne wajan Jalaluldeen, to Kubraah Kabal bani da abin cewa kin rusa damarki da kanki, saki har guda uku ai ba wasa ba, dan haka ki koma Masarautar ku komai ake ciki zamu tura wasiƙa”

Tunda ta fara magana Kubraah Kabal take Kallonta a haukace, wato yasan ya kwanta da matarsa Bola har ya bata ciki ta Haihu ita ya mayar ƴar iska, anyi auranta dashi baya ƙasar even miss call ko text message babu, and yanzu ya dawo shi ne ya bita da saki,

Miƙewa tayi ba tare da tace komai ba ta nufi hanyar fita, sa sauri Bola dake baƙin ƙofar shigowa ta juya.

A can sashin Queen Ayoola kowa, Aremo Shakiru ne yake ta Safa da marwa,

Wato a kullum dama ƙara zuwar masa take ba tare kuma daya sha wahalar komai ba,

Murmushi yayi tare da kallon mahaifiyarsa wace take tsaye tana gyara zaman Alƙyabbar jikinta,

Cikin farin ciki yace.

“What a great idea Mumy? Wow! Harna fara jiyo ƙamshin nasara”

Murmushi tayi cike da ƙasaita tare dayin baya ta nemi kujera ta zauna tace.

“Haka ne, Amma dai kayi a hankali domin lamarin akwai sarƙaƙiya cikinsa, wanne yake suffar Hadima Zubaida? Wane ya sace Queen Roomana? Sannan jiya an ƙara ɗurawa King Tunde goba, wannan dalilin ya sanya aka hana Abu Maleek ya dubasa a matsayinsa na babban likita, domin ana da tabbacin zai iya bashi kariya, wannan dalilin ya sanya aka shirya tafiyar Abu Maleek zuwa Birnin Bera, duk waye yake shirya hakan? Kaga muma kanmu dole mu sanya idanu, domin duk Mutumin da yake haka akwai abinda yake buƙata wanda zata iya kasancewa abinda muke so shine yake so”

Shiru Aremo Shakiru yayi sai yanzu shima ya fara wannan tunanin da sauri ya juya tare da nufar inda zai samu Iyalode.

Da daddare bayan sun yi sallar Isshā wajan 9 na dare kowa ya kasance a saman dinning area, kowa duk Family ɗin suna wajan hadda Oumuu-Ayman da Mai Babban ɗaki,

Cikin nutsuwa yake taka ƙafafuwansa zuwa wajan dinning ɗin,

Ƙamshin turarensa ya sanya duk suka fahimci shine yazo, basu taɓa tunanin zuwan nasa a dai-dai irin wannan lokacin ba.

Da Murmushi Salimerh ta miƙe tare daja masa wata haɗaɗɗiyar kujera a gefen Oumuu-Ayman,

Lumshe idanunsa yay yana sanye da wasu fitananun Panjams masu santsi da taushi, ƙwantaccen gashin kansa yay luff dashi,

Ya ƙara faɗi sosai da kuma tsayi, gaba ɗaya ya kerewa sauran ƴan uwan nasa.

Zama yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, yana taune bakinsa, Sharefddeen ne yay Murmushi yace.

“Bari na gaisheka ni, how are you Brother? Ya Madrid da kewar ƙwallon ƙafa?”

Ya ƙare maganar cike da zulaya,

Gently ya ɗago da kansa, tare da tsare Sharefddeen da idanu,

Kamar bazai magana ba sai kuma yace.

“Allahamdulillah Bro”

Shakiru shima ya saki Murmushi yace.

“Nine ba za’a kula ba? Sabida kaga bani da ƙaton jiki kamar naka ko? To ya kazo Nigeria ya kuma masoyiya ball?”

Ya ƙare maganar with smile on his face,

Taune baki Abu Maleek yayi kafin ya ɗan sauki Ajjiyar zuciya yana lumshe idanunsa cikin ƙasa da murya yace.

“Na sameku lafiya?”

Suka amsa da “Allahamdulillah” Adams kam ko kallon inda Jalaluldeen yake bai ba, shima Abu Maleek ya lura da hakan sai kawai ya share duk da cewa yake kewar ɗan uwan nasa.

“My son ya zama Basamude Ma sha Allah”

Cewar Queen Ayoola, Bola kam ko abincin kirki ta kasa ci saboda yadda Abu Maleek yayi kamar bai san da ita a wajan ba,

Oumuu-Ayman ce ta shiga haɗa masa dinner kana ta tura masa gabansa,

Girgiza kai yayi idanunsa a lumshe yace.

“Just coffee Oumuu”

Ta san daman ba lallai yaci komai ba, tana haɗa masa Coffee ɗin ya miƙe tsaye sabida kallon da Bola take masa,

Yana ɗaukan mug ɗin Coffee ɗin yayi gaba walking slowly ya nufi Sashin King Tunde bayan ya duba jikinsa ya fito ya nufi nasa sashin Mai kyau da kuma tsari.

Abu Maleek na zuwa sashin sa, ya zauna saman kujera a hankali ya dinga spending coffee ɗin a bakinsa,

Gefensa kuma tankar Inibi ce wacce tayi sanyi sosai,

Yana zaune yaji ana ɗan tafiya a hankali, tsaki yaja saboda zuwa yanzu yana son ya jisa shi ɗaya, 

Yana Buƙatar nutsuwar ƙwaƙwalwa domin ya samu lokacin yin tunani,

Yana ƙoƙarin miƙewa tsaye yaji an faɗa jikinsa tare da rungomesa ana jan sajan fuskarsa, wata irin bugawa zuciyarsa tayi tare dayin wani tsalle ta cikin ƙirjinsa kamar zata faso ƙirjinsa ta fito, da wani irin sauri ya buɗe idanunsa da sauri ya rufe saboda arba da yayi da.

   *Littafin ABU MALEEK na kuɗi ne, biya 500 domin samun posting sau biyu kullum, biya 300 amma posting ba kullum ba via 0116886423 sulaiman Naima s union bank*

Kyakkyawan farin yaro ɗan kimanin shekaru 10 a duniya, fari ne tass kamarsa da Jalaluldeen harya ɓaci, MALEEK kenan yaron da dukkan Alaafin ta sanyawa idanu,

Wangale fararan haƙoran sa yayi yace.

“Bàami Áróyin sómi gidigàn” (Bàami nayi kewarka sosai).

MALEEK ya faɗa yana kwantar da kansa a jikin Abu Maleek ɗin.

A.m runtse idanunsa yayi yana jin gudun zuciyarsa na ƙaruwa sosai,

Gaba ɗaya mantawa yake yana da wani ɗa a duniya, cikin jarumta da kuma dakiya Abu Maleek yasa hannunsa ya shafa sumar kan Maleek ba tare da yace komai,

Miƙewa yayi dashi ya nufi bedroom ɗinsa mai kyau,

Wata ƙatuwar chocolate ya ɗauka tare da bawa Maleek still bai ce komai ba, tun kallon farko da yayi masa bai ƙara ƙoƙarin kallonsa ba.

Bathroom ya shiga tare da sakarwa kansa shower kana ya shirya cikin fararan kayan bacci Panjams..

Yana gama shiryawa ya samu MALEEK yayi bacci kusa da Sweet,

Wani bathroom ɗin ya shige tare da kwanciya bayan ya ƙure gudun a.c ya daɗe kafin bacci yayi gaba da shi.

Rugar Mahinjo.

Julde ce zaune a cikin bukkar ta sai sauke Ajjiyar zuciya take tana jan numfashi da ƙyar,

Hannunta riƙe da ƙirjinta saboda ciwon da yake mata ga wani irin nauyi da ƙirjin yayi mata,

Tana zaune taji an shigo cikin bukkar Ajjiyar zuciya ta sauke tana ɗan lalubar hanya tace.

“Madibbo na, yunwa zata karni bani madarar nasha”

Ta ƙare maganar hawaye na saukar mata, Barkido kowa Murmushin jin daɗi yayi yau ya samu Julde ita kaɗai,

Zai aiwatar da abinda yake ransa, yau ƙwaɗayin sa zai faɗa, jikinsa na mazari yayi kan Julde take ƙoƙarin miƙewa tsaye,

A rikice Julde tace.

“Madibbo!! Madibbo!! Madibbo na?”

Jin Shiru ya sanya ta shiga ƙoƙarin Miƙewa tsaye tana miƙewa Barkido na sanya hannunsa yayi….

 Saura page 1 free pages ya ƙare?

   SHARE FISABILILLAHI SABIDA ALLAH DA ANNABI??

About AIS

Check Also

ABU-MALEEK CHAPTER 6 BY Nimcyluv

ABU-MALEEK CHAPTER 6 BY Nimcyluv                Www.bankinhausanovels.com.ng  Baƙin zanan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *