ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shi kenan Abdulhameed, insha Allahu zan taimaka maka a fitar da hakKin Allah akan ka, tunda hakan ya faru, amma kasan dole sai munje kotun tare sun yi maka tambayoy sannan su aiwatar maka”,
Murna ce ta bayyana a fuskar hameed, ya tashi ya rungume Malam Liman yana kuka, nan take tausayin Hameed da Kaunar sa suka cika ransa, nan ya tambaye shi akan ya fada masa cewa ina iyayen sa suke da zama?
Ya kada harshe ya ce, “Baba kamar yadda na fada maka cewa mahaifina baya goyon bayan da a hukuta ni, don haka yasa na na gudo nan har Allah Ya hada mu da kai, don haka ka wakilci

Iyaye na ka zama cewa kai yayan Babanane nazo mala da wannan labarin shine ka kawo ni nan don ayi min bulalar”.
Liman da kansa ya bashi masauki a gidan sa cikin dakin yaransa manya guda uku, ya hada su guri daya shi kuma ya bashi daki daya don ya samu ya sake sosai. Kwanan sa biyu a gidan ranar nan sun dawo daga kotun Musulunci da yamma an gama tabbatar da duk abin da ake bukata na hujja gare shi, kotu ta yanke masa bulala dari gobe. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna zaune suna hira da Malam Liman suna sauraren rediyo, anan ne yaji sanarwar — batan da yayi. Sam bai damu ba domin yasan mahaifinsa ne ya saka ayi

wannan cigiyar, don haka ya Kudura a ransa ba zai koma gida ba har sai ya gama jinyar bulalar da aka yi masa sannan ne zai dawo gida kuma da zummar tonawa kansa asiri Allah Sarki, Allah Ya bayyamawa iyayen yaron nan shi, ace saurayi mai wannan shekarun ya bata har yanzu ba a ganshi ba?”
Kalaman Malam Liman su ne suka doki ‘ kunnen Hameed daga barin dogon tunanin da ya tafi.
“Malam Aminu ban ji ka ce amin ba, ko. baka ji sanarwar batan yaro saurayi mai irin shekarun ka ba?” Sunan da ya fada masa kenan ba don haka ba da yanzu asirin sa ya tonu a yau din nan,don cewa zai yi ya koma gida gurin iyayen sa don. hankalin su ya kwanta. Cikin sauri ya ce, “Amin Baba, naji, to abin ne dai sai addu’a, kowa da irin nashi matsalar”. .
Sun jima suna hira, daga bisani ya tafi ya barshi a gurin yana tunanin halin da zai shiga gobe, amma idan ya tuna cewa a gurin Allah ya yi (free) ba shi da wani tabo sai na Aziza sai ya Www.bankinhausanovels.com.ng
samu yaji wani farin ciki ya kama shi, domin yasan shi din ma zata yafe masa idan ya je ya roKe _ ta ya gabatar da cewa-shi ne ya yi mata haka. MatuKar ta yafe masa to ko kashe shi za ayi to ayi tun da ya tsarkaka. A ranar da ya cika kwana hudu a gidan a ranar ne aka yi masa bulala dari cif, haka aka yi masa a bainar jama’a ana Kirgawa, tana cika aka saka kabbara tare da ce masa Allah Ya yafe masa.
Duk wanda ke gurin sai da ya yaba da Karfin zuciyar Hameed, domin ya nuna jarumta.
Malam Liman sai da ya zubar masa da hawaye ba don komai ba sai don birge shi da ya yi, da tsayawa da Kafarsa ganin yaji kunyar duniya da ta lahira, da kuma dada yaba da ya yi gurin dagewa da sai an fitar da haKin Allah akan sa. Tabbas a wannan zamanin da za a samu samari da suke da Karfin imani da ‘yan mata . wanda za su bayyana laifin da suke yi don ayi musu hukunci da shari’ar Allah lallai da mun samu saukin wannan masifu da suke addabar mu cikin birane da Kauyuka.
Ya Allah Ka kawo mana Karshen wadannan rashin zaman lafiya da ya addabi ‘yan uwa Musulmi a duk inda muke a fadin duniyar nan, Ka tona asirin dukkan azzalumai da suka hana mana zaman lafiya a Kasar mu, ameen. Suna fitowa daga gurin da aka yi masa bulala a gurin ya fadi sumamme, hankalin Mal. Liman ya yi mugun tashi, domin ya yi matuKar kaduwa ganin yadda yanayin sa ya koma, ko ina cikin jikinsa shatin bulala ne rudu-rudu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya jima can sai Allah Yasa ya farfado a haka cikin taimakon Allah suna shirin barin gurin nan ya sake yanke jiki ya fadi, jama’‘a da dama a gurin sun yi zaton ya mutu, can sai ya soma numfashi. so
A na cikin wannan halin sai ga wani babban Alhaji ya zo da motar sa zai fita aka daga masa hannu akan ya zo ya taimaka musu. Yana zuwa gurin sai ya ga kamar ya gane fuskar sa, dubawar nan da zai yi kuwa sai ya ga ya gane fuskar sa, a kidime ya ce.
“”Subhanallahi! Wannan ai Hameed ne, bayin Allah ku taimaka min na shigar da shi motar na kai shi asibiti, ai danmu ne yau kwanan sa hudu ba mu ganshi ba”.
A rude yake maganar yana ta faman cewa
‘ a taimaka masa, hade da cewa. “Hameed me ya faru da kai haka?” Mal. Liman ya ce, “Alhaji naji kanacewa
Hameed, wannan fa sunan sa Aminu”. Bai jira ya saurari abin da yake cewa ba aka taimaka masa suka saka shi cikin motar, Mal. Liman ne ya shiga suka ja suka tafi abinsu. Arewa suka nufa cikin tashin hankali, a hanya ne Mal. Liman yake cewa. “Aminu ne fa sunan sa ba Hameed ba ~ ranka ya dade”. “Malam don Allah ka barni haka, ko ma  dai meye sunan da ya fada maka wannan yaro nane kenan da sunana ya yi maka amfani? Ni ne Aminun shi kuma Hameed. To wai Malam meye ne ya faru da shi har ta kai shi ga zuwa kotu? Kuma naga duk jikin sa da jini, hatsari suka yi
ne?” Duk a gaggauce yake masa wadannan tambayoyin. Alhaji amma dai ba kai ne mahaifinsa ba
ko?” . . Eh ba ni na haife shi ba dan yayana ne da muke uba daya da shi, ni ne nake bin mahaifin sa a gurin uban mu”Yauwa ko da naji, muje ga zuwa asibitin mu yi KoKarin ceto ransa, daga nan sai na sanar da kai halin da ake ciki”. Yana rufe bakin sa sai gasu sun shiga cikin asibitin, a gaggauce aka fito da shi aka shiga ciki da shi, nan likitoci suka fara aiwatar da abin da ya kawo su. Tsananin rudani da tashin hankali ne suka bayyana a fuskar Alh. Aminu lokacin da ya gama sauraron bayanin da Mal. Liman yake yi masa na game da abin da ya faru ga Hameed.
Tsabar takaici sai da hawaye suka zubo masa ba don komai ba sai don jin cewa ashe Hameed ne ya jefa su cikin wannan bakin cikin da gaba daya ZURI’Ar su suke ciki na tsawon kwanakin nan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mikewa ya yi zumbur ya ce, “Hameed ba shi da wani amfani a gurin mu a yanzu, yaje shi ~ da mahaifin sa mun yafe su cikin ZURI’A tun da abin nasu babu tsoron Allah a ciki.
Wato dama yaya Jafar shi ne ya batar da dansa don kada kowa ya gane me ya faru shi ne zai ZO ya tayar mana da hankali, bamu fita daga wannan ba ya Kara jefa mu cikin wani. Tunda ya ci amanarmu mu kuma za mu nuna masa cewa bai isa ba, domin sai mun datse  duk wata igiyar DANGANTAKA. da_ take tsakanin mu da shi, yaje su Karata Dan nasa ya mutu tunda abin na shi haka ne nima na tsame hannuna akan al’amarin sa”.Yana gama fada ya juya zai tafi, da sauri Mal. Liman ya saka hannu bibbiyu ya riKo shi, ya soma cewa. “Haba Alh. Aminu, bai kamata ka yanke wannan hukuncin ba lokaci guda, shi komai na duniya dan hakuri ne, duk abin.da kayi hakuri  akansa to cikin yardar Allah zai zamo tarihi. Ka tausayawa Hamed ka kuma duba – muhimmancin zumuncin Allah, idan kai ma kayi haka kamar ka jagoranci cewa zumuncin ku ya Kare”,Nan ya samu ya gaya masa duk abin da ya faru da Hamecd da mahaifin sa, ya kumatabbatar masa da cewa hakiKa Hameed ya yi laifi ya kuma yi matukar nadamar abin da ya aikata ba don mahaifinsa ya hana shi fadin cewa shine. ya aikata wannan laifin ba da tuni ya bayyana muku kansa kun hukunta shi. Sai da ya gama fada masa komai jikinsa ya yi sanyi, nan take ya ji tausayin hameed ya kama shi, ya daina ganin laifin sa sosai akan na mahaifin sa.
Babu abin da Mal. Liman ya boyewa Ahj. Aminu na game da labarin da Hameed ya fada masa game da abin da ya faru da shi tun daga ranar da abin ya faru har zuwa yau. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kwana biyu Hameed ya yi a gadon asibiti bai san a wane hali yake ciki ba, Alh. Aminu ne yake zaune da Mal. Liman suna jiyyar sa domin babu wandaya fadawa cewa ya samu labarin Hameed.
A rana ta uku ne ya dawo cikin hayyacin sa, nan ne likitoci suke fada musu cewa ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani hade da ciwon (ulcer) domin tsananin damuwar da yake ciki da rashin cin abincin da yake yi.
Lokacin da Hameed ya dawo cikin . hayyacin sa da ya ga kawun sa a tare da shi ya shiga rudani da mamakin ganinsa, nan ya shiga kuka yana fada masa duk abin da ya faru da shi tas, babu abin da bai fada masa ba.
Bai wani mamaki ba domin ya samu duk labarin gurin Mal. Liman, sai dai wani Karin bayanin da ya yi masa a game da mahaifin sa nan ya gaya masa cewa don Allah Ya barshi ya mutu, bai son komawa ya Kara ganin Zuri‘ar su. Tausayin sa yaji sosai, ya ce ya daina kuka Kuma komai zai wuce insha Allah tunda ya yi nadama, sai dai ya yi KoKarin neman yafiyar
abin gurin yarinyar da mahaifinta, idan sun yafe
“masa to ya yi (free) duniya da lahira tun da ya
fitar da hakkin Allah, idan sun yafe masa shi kenan. .
Zaune suke a falon ya gama labarta masa _ halin da dansa Hameed yake ciki da kuma abin da ya faru suka Boye musu. Zufa ce ta zubo masa, nan da nan hankalin sa ya yi matuKar tashi, ya mike tsaye ya yi saurin . dawowa gurinsa ya zauna kusa da shi, cikin _ kidimewa ya ce. .”Aminu ka daure ka rufa mana asiri, matuKar babu wanda ya sani don Allah ka rufe – maganar nan a gurin nan, domin kada mu tozarta ni da iyalina a cikin Zuri‘a”. Ran Alh. Aminu ya yi mugun baci, ya ce. “Haba Yaya, wai kai me yasa ka fiye son kanka ne? Kai komai kanka ka sani, baka son farin cikin kowa sai naka da na iyalinka. Ka tuna cewa uban yarinyar nan ya yi matuKar yarda da kai da danka, amma ace kai da kanka kasan abin nan bayan ya faru amma ka Ki ka je ka fada masa da kanka, ka ce kuma wani ba zai je ya fada masa. Yaron da kansa yana son ya fada masa amma ka hana shi don kada ka tozarta, amma kai danka ya tozarta tasu, to shin wannan a ganinka shi ne Zumunci ko halacci?” Www.bankinhausanovels.com.ng
. “”Aminu wallahi nima ban yi farin ciki da faruwar hakan ba, har yanzu ina jin bakin cikin faruwar wannan al’amarin” Ban yarda ba, idan har abin nan bai yi maka dadi ba to kamata ya yi ka hukunta Hameed a idanun duniya, ka nunawa Zuri’ar ka cewa dan cikin ka ya aikata ta’asa sai ka miKa shi
ayi masa dukkan hukuncin da ya kamata, sannan ka nuna kayi fushi da shi. Amma baka yi ba, don son nuna Kaunar da sai shi ne ya yi abin da ya dace
Don haka yau tun da komai ya zo kunne. na da kaina zan je na sanar da kowa na Zuri’a din nan yasan abin da danka ya yi mana”. Cikin sauri ya riKe shi ganin ya mike zai tafi, ya ce. Aminu ka tsaya ka saurare ni ka kuma fahimce ni, wallahi ba a son raina haka ya faru ba. Ina so don girmen Allah ka rufa min asiri kada kowa yasan mene ya faru, Aminu ka fadi duk abin da kake so a duniyar nan ko mene ne nayi maka alKawarin mallaka maka shi matuKar za ka rufa min asiri”Juyowa ya yi yai masa wani irin kallo na rashin fahimta. ” “Aminu ka daure ka rufa min asiri domin zumuncin da yake tsakanin mu, wallahi ko me kake so zan yi maka shi, ka fada da bakin ka”.Jafar bani da abin da zaka iya bani, ka barni na yi tafiya ta”.Aminu don Allah jira ni na fito”. Yana fadin haka ya yi sauri ya shiga ya je ya fito da tarin wani (files) ya zo ya ajje su gaban Sa, yaCe. . Www.bankinhausanovels.com.ng
“Aminu ka zauna ka duba (company) na ne da tarin manya-manyan filaye na ka zabi duk abin da kake so na baka shi duniya da lahira matukar zaka bar wannan sirrin tsakanin ni da kai, hatta shi Hameed din ba zan so ya san wannan sirrin ba, kai ko babban (company) na kake so mutuKar zaka rufa min asiri to a shirye nake na baka shi yanzun nan zan saka hannu na mallaka maka shi duk domin kada ka tozarta min Hameed a idanun duniya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaro idanu ya yi yana kallon sa cikin mamaki, ya jinjina kalaman da yake masa magana. Tabbas yasan girman wannan Company din da suna da daukaka da ya yi a Kasar nan, domin da wannan komfanin Zuri‘ar nan take ji da shi, kuma nashi ne halak malak, babu kudin~ kowa, amma haka yake KoKarin ganin ya sama kuwa nasa Investment a ciki shi ne yake masa maganar zai mallaka masa a matsayin toshiyar baki. Nan take yaji yana son gasgata kunnen sa, anya kuwa yaji abin da ya fada masa? “Aminu ko baka ji abin da na fada maka bane?” Cikin sauri ya ce, ” Company?”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

 ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE            …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *