ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Muna tsaye a gurin sai ga likitocn nan sun ° dawo, wannan karon har da wasu samari su uku, babu wanda suka yiwa magana, suna zuwa suka tsaya sai suka tura wani daga cikin matasan nan guda uku cikin dakin da Aziza take. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana shiga bai fi minti uku ba sai muka – jiyo Aziza na ihu kamar yadda tayi lokacin da ta ga Hameed, jin haka sai suka sake tura mutum biyun nan, nan ma dai wani ihun ta shiga saki babu KakKautawa. ‘tana cewa.’ Ban son ganin ku, bana son ganin shi, Abba! Abba!!”. Cikin gaggawa likitocin suka bude Kofar sai ga matasannan sun fito, su kuma sai suka shiga ciki, wannan karon har damu domin cewa suka yi muma mu shiga. Sai da muka shiga Aziza na ganin mu ta fito daga inda take buya da sauri ta zo ta. rungume Abbanta tana ccwa. — “Abba me yasa ka bari suka shigo? Tsoron su nake ji, Abba don Allah kada ka tafi ka barni su Kara shigowa”,

Likitocin cikin hikima da dabara suka samu suka yi mata allurar bacci, nan da nan bacci’ya dauke ta, nan suka nemi a basu guri.
Sun jima tare da ita sannan suka fito gaba daya iyayen mazan suka nema su biyo su, haka suka je, Alh. Jafar da Mukhtar, sai Abban ku duka suka dunguma.
“Alh. Mustapha ina me neman afuwar ka dangane da furucin da nayi maka dazu”. Cewar Dr. Said.


Ya ce, “Babu komai Doctor, na fuskanta yanayin aiki ne kuma komai ya wuce”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Madallah na gode, sai magana ta gaba, yadda muka bincika a zahiri da kuma na’ura mai Kwakwalwa ya nuna mana cewa Aziza a yanzu tana tsoron dukkan wani da namiji matashi wanda hakan ya nuna cewa su ne suka yi mata wannan ta’asa. .
‘ Tun da hakan ya faru bata taba razana irin na yau ba, domin ganin matasan da tayi hakan ne ya razana ta har take son tuno wani abu da ya faru da ita a baya. Don haka muddin zata na – ganinsu to zata ci gaba da zarana wanda cikin biyu dole ayi daya, ko dai (memory) dinta ya
dawo ko kuma wata matsala ta faru da kwakwalwar ta, Allah Ya kiyaye don ba ma fatan haka a gare ta”, . Gaba daya suka ce, “Ameen”, Dr. Umar ya Kara da cewa, “Don haka dole a kiyaye sanin su wane za su dinga zuwa dubiya gurinta, domin gudun afkuwar wani tashin hankali. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tabbas tun da muke bamu taba samun (patient) mai irin wnanan lalurar ba, sai dai mun taba samun wata wadda ita kuma maza ne gaba daya bata son gani daga babba har yaro, tana ganin mun zo duba ta zata shiga ihu da razana, dole muka haKura sai ‘yan uwanta mata ne suka shiga duba ta. Sai ita kuma wannan nata daban ne, matasa take jin tsoro, kasan abin na Allah kowa da irin nashi lalurar”.
Alh. Jafar ya ce, “Gaskiya ne likita, mun gode, kuma insha allah zamu kyaye mu saka ido, kuma insha Allah ba zamu sake barin Hameed ya zo nan asibitin ba har sai ta warke sosai”.
“Shi kenan Alhaji, ba ma shi kadai ba duk wani matashi da zai sa idan ta gashi zai razana ta bama fata ya zo gurinta, domin hatsarin da yake
cikin al’amarin , nasara da kuma rashin ta, kaga abin ya zamo (fifly-fifly)”, .
Mukhtar yace “haka ne likita, amma ni ina da magana da Yaya zai yarda da an raba yarinyar nan da cikin da ke jikinta, kaga sai taji da daya, amma ace ga wannan ga wannan abin ai ya yi mata yawa, yarinya Karama da. ita, shakarunta fa sha hudu zuwa sha biyar har yaushe zata ya jure rainon ciki? Mustapha ya dafa’ Mukhtar ya _ ce, “Mukhtar ka saki ranka, ka dauka wannan duk yana cikin jarrabawar rayuwar .Aziza da mu iyayenta baki daya, don haka Allah Yasan abin da bamu.sani ba, don haka bamu san dalilin faruwar hakan ba,.sai dai mu dauki yarda da Kaddarar Sa mu jira muga ikon Allah. Murnar mu daya da ba ita ce taje yawon banza ba ta dauko shi, Karfi aka nuna mata”. . Www.bankinhausanovels.com.ng
Jikin Alh Jafar ya yi matuKar sanyi, ya kasa cewa komai, banda idanu da kunne da ya zuba babu abin da ya iya tofawa, sai faman cewa
Allah Ya kiyaye Ya bata lafiya dai. Nan suka gama abin da ya kaisu, sannan suka fito suka dawo gurinmu, Alh, Jafar bai juma ba a gurin ya ce zai tafi, nan ya tambayi ina Hameed? Nan muka ce tun dazu ya yi nan bai dawo ba. Sallama ya yi damu ya bi bayansa, haka nan Abban ku suka sanar mana duk yadda suka yi da likitocin, mu dai addu’a muka yi akan Allah Ya fitar damu cikin wannan hali da muke. Alh, Jafar zaune yake cikin motar sa shi “kadai yana faman sauke numfashi da ajiyar zuciya, domin dai yana cikin (tention) ba Kin Karawa, Allah Ne ya taimake shi Ya rufa masa asiri, amma ba don haka ba yau daya kwashi borin kunyar sa. Tabbas yau ya so ya shiga cikin tsaka mai wuta, amma sai gashi Allah Ya rufa masa asifi, abin da yake tunanin zai faru Allah Ya kiyaye. Sai da ya dan samu nutsuwa sannan ya fara tunann matar sa da Hameed, ina suka shiga? . ° Nan da nan ya fito cikin motar ya shiga dubedube babu wanda ya gani cikin su, dole ya ° haKura ya dawo ya shiga motar sa ya koma gida. A falo ya iske Haj. Asiya tayi shiru abinta, daga ganin idanunta kasan ta sha kuka na qin Karawa. “Ine Hameed yake?” Ya jefo mata wata tambaya cikin kaushin murya, don a fusace yake. Daga kai tayi ta kallo shi, cikin sanyin jiki tace, Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ban gane wacce irin tambaya kake min ba, awa ta nawa da barin ku tare zaka zo kana yimin Wannan tambaya?”” “Ya baro ni a can nima, nayi tunanin ko ya gamu da kene kun taho gida. Ina zaton tunda motar haya ya biyo yanzu za ki ganshi ya shigo cikin gidan”.
Yana gama fadin haka ya cire babbar rigar sa ya aje gefe, ya samu guri ya zauna. Kallo daya zaka yi masa kasan ba ya cikin nutsuwa.
“Daddy, yanzu-wacce mafita ka aje mana a ckin nan game da wani sabon tashin hankalin da ya same mu? Kasan dai yanzu dole kayi wani abu akan wannan al’amarin, don abin ya zarce dukkan tunanin mu
Cikin kaushin murya ya ce, “Me kike so nayi bayan wanda nayi tun farko? Ai magana ta riga ta wuce, fatan mu Allah Ya yayewa yarinyarnan abin da ba zata iya ba”. “Kai Alhaji ka ji tsororn Allah kuma ka dinga tausayi da sa tsoron Allah a zuciyar ka, ai kuwa duk mai tausayi da imam dole ne ya tausayawa yarinyar nan irin halin da take ciki, daga wannan sai wannan, bata fita daga wannan halin ba sai gashi tana fadawa cikin wani. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ni dai shawara ta dole ne mu sanar da iyayen yarinyar nan cewa ga wanda ya jefa ‘yarsu cikin wannan gararin, tabbas idan muka yi haka zamu samu saukin tsangwamar da zamu fuskanta, amma muddin muka bar wannan al’amarin ran da duk asiri ya tonu to zamu fi kowa jin kunya a cikin ZURI’A, domin wasu sai sunce mu ne muka sa shi yaje ya yi mata hakan. Ina ganin gwara tun wuri mu yiwa tufkar hanci”. Cikin zafin rai da daga murya sama ya ce. Asiya ban san wane irin gaddama da taurin kan da ke gare ki ba, sau nawa zan fada _miki maganar nan da ki rufce ta amma sai kina dawo da abin baya? Don haka ki sani baki isa ki sa ni abin da ban yi niyya ba, ya kamata ki saurara min. Wannan ita ce rana ta Karshe da za ki sake min irin wannan batun, kin dai ji na fada miki’.
Yana gama fadin haka yasa kai ya fice daga falon cikin fushi da Bacin rai.
Binsa tayi da kallon takaici, nan take hawaye ya zubo a cikin idanunta, a bayyane ta ce, .
“Jafar ka cika marar tausayi da son zuciya, _ kuma insha Allah sai Ya bayyana gaskiya komai daren dadewa, kuma matuKar ni ce na haifi Abdulhameed sai na sa shi yin abin da ranka baya so, naga yadda zaka yi dani”. Tana gama fadin haka ta samu guri ta zauna tayi tagumi abin yana matuKar ta da mata
rai, domin har yanzu ta kasa samun dukkan farin ciki a wannan ranar tun da ta samu labarin cewa Aziza na dauke da ciki”. Www.bankinhausanovels.com.ng
A can cikin daki Alj Jafar ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka ya dinga shiga da fice don _ jiran dawowar Hameed amma yaji shiru, gashi har misalin Karfe goma na dare babu shi babu labarin sa. Nan hankalin sa ya Kara tashi, wannan karon har Kofar dakinsa yasa mai gadi yazo ya jijjige, tunanin sa yana ciki zai yi musu irin na rannan, amma da aka cire Kofar sai aka ga dakin wayam, babu kowa a ciki, haka ya Kara jefa shi cikin damuwa.
Har gari ya waye babu hameed babu wanda aka samu ya zo da labarin ya ganshi, kwana daya, kwana biyu babu Hameed babu  labarin sa, nan hankalin ZURI’A ya tashi saboda da kansa ya shiga fada ma ‘yan uwansa bai ga Hameed ya dawo ba, yau kwana uku.
Kowa yaji abin sai kansa ya daure, domin hakan bata taba faruwa da shi ba. Nan hankalin kowaya tashi, haka aka shiga cikiyar sa har gidan (radio) amma babu wani labari da aka samu a wannan lokacin. :
Kallo daya zaka yiwa Alh. Jafar kasan yana cikin tashin hankali mara misaltuwa. Ganin yadda yayi mugun _tashin hankalinsa akan rashin ganin dansa Haj. Asiya  tana kallon sa amma ita abin ko a jikinta don abin da ta fada masa cewa tayi ita bata son ta sake ganin Hameed a gabanta domin tana ganinsa jefa ta cikin tashin hankali da damuwa yake yi, yaje can ya Karata. Tun da ta fada masa haka ya shiga fushi da ita, hade da fada mata cewa duk abin da ya
fari da dansa ba zai taba yafe mata ba tun da baki tayi masa. Hakan yasa ya dauke mata wuta, sam ba ya sauraronta, haka duk ya bi ya dugunzuma , ya hana ma kansa kwanciyar hankali
Tsananin damuwar da yake ciki yasa ko aiki ya Ki fitayana ta yawon neman labarin inda dansa ya shiga, amma shiru babu labarin sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yadda al’amarin yake tun sanda Hameed ya fito daga cikin asibitin hankalin sa ya yi – mugun tashi jin labarin Azizan sa na dauke da cikin sa, hankalin sa ya yi mugun tashi yaji gaba daya duniyar tayi masa zafi, yaji sam baya sha’awar son ci gaba da rayuwar duniyar gaba daya. Haka ya dinga jin kamar bashi da kowa, bashi da komai a duniya, haka ya dinga jin yaje ya yi rayuwar sa shi kadai babu kowa a cikin rayuwar Sa.
Haka ya fito bai san inda zai je ba, sai dai ko kadan bai sa ma ransa cewa zai koma gida ba, domin bai ga wani amfani da zai sake a rayuwar sa ba tunda har ya jefa Azizan sa cikin wannan
bala’in na datse mata dukkan farin cikin rayuwar ta da burinta, ya kuma illata rayuwarta gaba daya don ya kassara ta baki daya.
KUNAR ZUCI da shi ya wuni a wannan ranar, anan ya bar cikin asibitin, haka yana fafiya ‘ ‘ daga nan sai ya tafi can, don haka ya yanke ma zuciyar sa cewa dole ne yaje ya nemi kotun Musulunci ya gabatar da laifin sa don a hukunta shi.
Bai san ina zai je ba domin bai san ina zai samu kotun ba, don haka da yaga dare ya yi bai yi nasarar abin da yake nema ba, wani masallaci ya samu ya kwanta a gurin yayi barci a can Hausawar Sabon titi, sa safe ne ya samu limamin masallacin da bayan sallar asuba.
Bayani ya yi masa sosai, bai boye masa komai ba, ya gaya masa irin halin taskun da yake ciki, da kuma abin da yake so ayi masa na hakkin Allah.
Jikin liman ya yi maKatuKar sanyi, ya yi matukar tausaya masa tare da jinjina irin Karfin imanin da yake da shi, nan ya Kara tabbatarwa da cewa yin hakan ba halinsa bane, iftila’i ne da rudin zuciya da kuma sharrifn shaidan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ya ce, “Yaro lallai kam kana cikin tashin hankali da rudin rayuwa, hakiKa wannan shi ne tsoron Allah na hakika, tabbas da za a dinga samun mutanc masu irin wannan laifin suna bayyana kansu ana fitar musu hakKin Allah akan su to da tuni duniyar tana nan zaune lafiya. To amma ina! kullum abubuwan sai dada tabarbarewa suke yi.
Dama dole ka shiga damuwa da rashin samun nutsuwa cikin ranka, domin abin da kayi
‘ ba Karami bane, sannan duk wanda yaji me ya faru sai ya yi tsinuwa ko la’antar wanda yayi mata wannan al’amarimka ga kuwa nutsuwa a gurinka ba zata taba samuwa ba_tunda baka bayyana cewa kaine ba a yafe maka.
Amma tunda kayi nadama ka dage akan kana so a fitar da hakKin Allah akan ka, idan yaso daga baya zaka koma ka bayyana gaskiya, to zan taimaka maka, kuma na tabbata idan an fitar maka da hakKkin Allah zaka samu nutsuwa har cikin zuciyar ka. Kuma Allah Zai taimaka maka ta sauran hanyoyin da zaka tsira, amma ina son ka Kudura a ranka cewa ba zaka kuma kusantar inda zina take ba. Ka duba ka ganka shekarun ka basu wuce ashirin ba zuwa da daya, amma ka jefa kanka cikin tashin hankali haka”
Hawaye ne ya shiga zubowa a fusKar sa ya ce,
“Baba ina cikin wani irin rudani da damuwar da ban taba tunanin wani kar rayuwar nan ya shiga irinta ba, wallahi Baba ™ nayi maka alKawari ba zan kuma yin zina ba har in koma ga mahalicci na”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shi kenan Abdulhameed, insha Allahu zan taimaka maka a fitar da hakKin Allah akan ka, tunda hakan ya faru, amma kasan dole sai munje kotun tare sun yi maka tambayoy sannan su aiwatar maka”,
Murna ce ta bayyana a fuskar hameed, ya tashi ya rungume Malam Liman yana kuka, nan take tausayin Hameed da Kaunar sa suka cika ransa, nan ya tambaye shi akan ya fada masa cewa ina iyayen sa suke da zama?
Ya kada harshe ya ce, “Baba kamar yadda na fada maka cewa mahaifina baya goyon bayan da a hukuta ni, don haka yasa na na gudo nan har Allah Ya hada mu da kai, don haka ka wakilci

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

 ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE            …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *