UKU BALA’I CHAPTER 11

UKU BALA’I CHAPTER 11

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sosai Baffa ke kallon yanayin  cikin takaici da tsananin mamaki abin da bai taba zato ko tsammani ko a mafarkinsa bai yi tsammanin zai sake tuna shuɗaɗɗen wannan lamarin ba amma bisa akasi wai yau Bello ne a gabansa shi ya tsinta shine har yayi masa magani kaico mutumin da ya tsana tsana mai ansa suna tsana a filin duniyar nan bai taba tsanar wani bawa kamar Bello ba amma wai yau shi ne a gidan sa yake zaune har yake tattalin sa yake kula masa da rayuwa ya ajje komai nashi ya bata lokacin sa mai tsayi wajan bautawa wanda ya tsana a filin duniyar nan kaico.+

Wani irin maƙaki ne na takaici yake ji yana tunkodo masa zuciya ji yake yi ko wani sashi na zuciyarsa da ruhinsa suna shiga wani halin kunci mai tsanani.

Kai kawo kawai yake yi cikin dakin zuciyarsa na tunzurashi tana tuno masa da abin da ya faru sama da shekaru ashirin wanda ya ɗaɗe da binne wa ransa ba zai taba waiwaye ba amma yau rana daya ciwon da ke cin zuciyarsa ya tashi.

Runtse idanu yayi ji yake yi kamar ya kurma ihu don takaici da bakin ciki bai san ya zai yi ba bai san abin da zai yi wa Bello domin daukar fansa ba zuciyarsa ta shiga tunkodarsa akan ya dauki hukunci mai girma akansa wanda zai warkar masa da ciwon da ya haifarsa ba ma wannan ba ‘yarsa yake tunawa ‘yarsa mai biyayya a gareshi amma AKAN SO ta ajje duk wani girmamawa da biyayya da take masa ta shiga yiwa so biyayya ta rabu dashi ta rabu da kowa nata ta guje su duk akan so ya yafe ta tuni ya yafe ta cikin zuri’arsa ya sallamawa duniya ita amma yau daya yaji zuciyarsa na tuno masa da zaman da yayi da ita da kyautatawa da take masa.

Numfashi yaja mai karfi idanuwansa lokaci guda suka kawo kwalla komai ya faru dashi a filin duniyar nan Bello ne Sanadi ya raba shi da inda ya zauna zaman shekaru masu yawa ya rabashi da farin ciki ya raba shi da ‘yarsa duk wani tashin hankali da kuncin rayuwa da suka shiga shine sila komai ya faru da su shine sila.

Dafe kan sa yayi zuciyarsa na kara rura wutar kiyayyar da yake yi masa ji yake yi kamar ya kashe shi abin da zuciyarsa take sanar dashi kenan amma yana gudun haka tunanin ‘yarsa yake yau daya ya tuna da ita yau daya yana son ganinta bai san a wani hali take a yanzu ba bai sani ba ko tana raye a duniyar nan ko ta mutu duk bai sani ba ansar tana wajan Bello wanda shi kuma a duniyar ba wanda ya tsana ya sake gani kamar shi.

A hankali ya fara jan kafafuwansa da sukayi rauni sosai gabadaya jikinsa ya saki sosai tafiya yake yi yana bin kowa da kallo har lokacin da ya isa in da ya baro Bello zaune bayan ya gama fahimtar wanene shi tun daga nesa yake hangen sa yana jin yarda zuciyarsa ke kara narkewa da bakin ciki da Bello ya zama sila ji yake yi kamar yana isa ya dauke shi da mari.

A wajan Bello abin da yake ta nazari kenan akan Baffa sosai ya shiga tashin hankali sosai ya shiga cikin firgici da razana sosai yake hango yarda Baffa zai dauke shi da irin hukuncin da zai yi masa in ya gane shi wanene lokaci guda zuciyarsa ta karya ba wanda yake tausayi sai matarsa ya sani komai ya faru da ita shine sila AKAN SO komai ya faru a tsakanin su domin tayi wa so biyayya ta rabu da komawa nata tace sai shi sosai kalamanta suke masa yawo kai a can lokacin baya bayan iyayenta sun sallamata gareshi sunyafe ta gareshi…

  “Bello kai kadai nake dashi a duniyar nan kai ne gata na kai ne komai nawa saboda  so na rabu da kowa saboda so na rabu da komai nawa don Allah ka rikeni da amana karka sa nayi kuka A DALILIN ƊA NAMIJI ina tsoro…ina tsoron abin da zai je ya dawo Bello in har ka ci amanata ka tabbata ba zan taba yafe maka ba ni kaina ba zan yafewa kai na ba na roke ka”.

Wani hawaye ne suka gangararo masa lokacin da ya tuno kalamanta tana zubda hawaye cikin tsananin firgici da yanke tsammani komai na rayuwa sai BIYAYYAR SO da take tsammanin tayi kuma take tsammanin zata samu kulawa akan wanda tayi wa so din.

STORY CONTINUES BELOW

Saukar hucin da yaji ne akan sa ya sanya shi saurin dawowa hayyacin sa yana waigawa Baffa ya gani fuskarsa ta haɗe kamar bakin hadari idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir sai faman hirji yake yi kamar wanda zai ci babu shi kan sa Bello ya tsorata da yanayin da ya gan shi a ciki.

Zuciyarsa ce ta shiga bugawa da sauri-sauri kamar zata faso kirjinsa ta fito saboda tsananin firgita ba abin da yake hangowa cikin idanun Baffa sai kiyayya da rashin so kallon da yake yi masa na tsana da takaicin ganin sa sosai yake tuno waye Baffa sosai yake tuno irin DAMBARWAR da suka kwasa a tsakaninsu akan ya rabu masa da ‘ya har fada Baffa ya ja shi suyi ya sha jibgarsa ya sha yi masa rotse da sanda amma duk wannan bai saka ya guje ‘yar sa ba sosai yake hango irin ikirarin da Baffa yayi a ranar da ya sallama Habeeba gareashi a ranar da aka daura mata aure a ranar da suka kwashe komai na su suka bar garin.

“Ba zan taba yafe maka ba Bello ka cuce ni ka dasa min ciwo a zuciya mai girman gaske amma ka sani wallahi wallahi kaji na rantse zan sallama maka Habeeba ka je ka aure ta amma ka tabbata babu ni babu ku har abada bana kaunar na sake haduwa da daya daga cikin ku”.

Runtse Idanu Bello yayi jin zantukan Baffa suna maimaita kan su a cikin kwanyarsa tsoro na kara ziyartarsa sosai a zuciya ya sani Baffa ba zai  taba kyaleshi ba ya sani dole ya dau hukunci akan sa tun da yau ALKALAMIN ƘADDARA ya hada su har suka zauna waje daya a lokaci mai tsayi wanda shi a akaran kansa ba zai iya cewa ga adadin lokacin da ya kwashe a tare da su ba.

Kawai ji yayi tum akasa da sauri ya waigo Baffa ya gani ya fadi yana faman numfarfashi kamar wanda rai ke kokarin fita daga jikinsa zaro idanu yayi sosai cikin tsananin firgici ya isa gareshi yana kokarin tallabo shi amma duk da halin da Baffa yake ciki bai hana shi kokarin janye jiki daga gareshi ba hakan ya kara rikita Bello sakin baki yayi yana kallonsa gabansa na tsananta bugawa.

A daidai lokacin su Iro suka dawo daga kiwo ganin abin da ke faruwa da gudu suka iso suna kiran sunan Baffa Ja’e ya rungumo shi yana mai duban Bello da hawaye suka balle masa suna ta kwarara kamar wani karamin yaro

“Na…ts.a..na she bana…son…ganinsa”.

Cikin sarkewar muryar Bafffa yake fadin haka  da sauri suka shiga duban sa domin ba su gane in da ya dosa ba ba su gane mai yake nufi da kalmar da yake fadi ba sosai suka rikice suka shiga kokarin daukarsa domin kai shi daki amma idanuwansa na kan Bello da yayi kasa ke yana kallon ikon Allah iya tashin hankali ya shiga a wannan lokaci zuciyarsa sai faman zillo take tsoro yake yi kar ya zama ajalin Baffa don ya lura yanayinsa ya tabbatar ya gane ko shi waye da sauri ya mike ya bi bayan su daidai bunkar da suka shigar da Baffa ya tsaya tsoron shiga yake don bai san abin da zai faru ba ya sani Baffa ya tsane shi in da ya san ko shi waye tun farko ba zai dube shi har ya taimaka masa ba.

A cikin Bunkar kuwa kokarin taimakawa Baffa sukayi har ya fara dawowa hayyacin sa sai faman magana yake saki wanda su dukkansu ba su gane abin da yake nufi ba idanuwansa sun kara kaɗewa sosai.

“Bana son na sake hade idanuna dashi bana kaunarsa na tsane shi ku fitar min dashi daga cikin zuri’a annoba ne shi bala’i ne  komai da ya faru dani shine sila shi ne ya dasa min ciwo mai girma a zuciya shi ya raba ni da farinciki na a dalilin sa na rasa matata a ta dalilinsa ne komai nawa ya kasance da kunci a cikinsa”.

Magana yake yi idanuwansa na kawo hawaye suna zuba sosai su Ja’e suka firgita da ganin tsohon na su cikin wannan yanayin abin da ba su taba gani ba kenan tsayin rayuwarsu kukan mahaifin su lokaci guda suma zuciyoyinsu suka karye kwalla ta cika masu idanu Iro ne yayi kokarin duban Baffa a dan firgice.

STORY CONTINUES BELOW

“Baffa wai me ke faruwa ne me ya same ka kuma waye kake cewa ka tsana?”.

Runtse idanu Baffa yayi zuciyarsa na zafi kafun ya buɗe su yana duban su daya bayan daya yana faman ajiyar zuciya.

“Mutumin da na taimakawa mutumin dana bata lokaci na ina jigilar ganin yana dawo mutum mutumin da na shafe tsayin lokaci ina jinya mutumin da duk na wahala akan shi ashe ban sani ba mikiyi nane ashe ban sani ba annoba ne annobar da ta lalata komai nawa ta hanani farinciki tana hanani kwanciyar hankali ta raba ni da masauki dana kwashe shekaru ni da zuri’ata amma a ta dalilinsa na bar komai na dawo nan da zauna”.

Duban junansu sukayi kafun su sake duban Baffa cikin rashin fahimtar maganganunsa murmushi mai ciwo ya saki kafun ya dauke hawayen da suka zubo masa nan ya shiga ba su labarin komai dake faruwa wanda ba su sani ba don lokaci ba su wuce shekara biyu ba.

Mamaki sosai ya cika su lokacin da ya gama ba su labari duban sa suka shiga yi cike da mamaki da al’ajabin lamarin domin duk wannan lamarin ba su san dashi ba Ja’e ya kokarta duban Baffa cikin yanayi na tausayi.

“Amma Baffa kana ganin wannan matakin daka dauka shi ne daidai?”.

Wani irin duba Baffa yayi masa kafun yaja numfashi.

“Me kake nufi Ja’e? Kana nufin hakan da nayi ba daidai bane ko me?”.

Girgiza kai ya shiga yi cikin kunar zuci sosai yake jin takaicin lamarin da kuma haushin Bello.

“Ba wai nace baka kyauta bane amma kana tunanin abin da kayi wa Yayah Habeeba daidai…”.

“Dakata min Ja’e me kake son sanar dani kana nufin ban yi mata adalci ba ko me kasan Allah ko ita ce ‘YA DAYA TAK! dana haife zan iya rabuwa da ita tunda har ta fifita wani a kai na balle kuma ina da wasu ‘ya’ya mahaifiyarku da sunan Habeeba ta mutu a bakinta tun lokacin da muka baro inda muka ta so shikenan ta rasa kwanciyar hankalinta har zuwa lokacin da ta rasu ta yaya kake zaton zan yafe ko zan dauki lamarin da sauki”.

Ya karashe cikin zafin rai da tsananin fushi mikewa yayi cikin hanzari yayi waje Bello na tsaye kikam tun dazu zuciyarsa da kwanyarsa duk sun tsaya cak! da aiki ya rasa mai ke yi masa dadi saukar duka yaji da sanda a tsakar kai hakan yayi matukar firgita shi Baffa ya hango sai faman Hirji yake yi bai ankara ba ji dumin jini na sauko masa zuwa fuska duban Baffa yake yi cikin wani irin yanayi yana hango kiyayyar da yake yi masa a karo na biyu yana daga sandar yana kokarin sauke masa da sauri Ja’e ya rike wanda ya fito a daidai lokacin ya shiga duban Baffa yana duban Bello dake tsaye jini duk ya wanke masa fuska lokaci guda.

Wani irin duba Baffa yayi masa kafun ya fizge sandar yana nuna Bello da ita.

“Tun wuri ka fice mani daga cikin ruga tun kafin nayi ajalinka na fada maka dama duk ranar da muka sake haduwa da juna sai na yi ajalin ka don haka tun kafin na kashe ka na mai da kai in da na tsinto ka ka san in da dare yayi maka”.

Sake duban Baffa yayi zuciyarsa na zafi da raɗaɗi a hankali ya shiga takowa yana iso wa gareshi da sauri Baffa ya daga sandar jira kawai yake ya iso ya dauke masa a jikinsa sai faman ɓari yake yi kamar wanda ya sha dukan ruwa su Iro kam lamarin ya fara shallake tunanin su ba su taba zaton haka Baffa yake ba ba su taba zaton yana da zuciya haka ba tunda suke dashi ba su taba ganin ya aikata makamancin wannan halin ba gani suke yi kamar a mafarki ba gaske ba.

“Na tsane ka karka sake ka iso inda nake wallahi zan yi ajalinka”.

Duk ikirarin da Baffa yake yi bai hana Bello isowa gareshi ba haka shima Baffa yana isowa ya sauke masa sandar a tsakar kansa wanda tayi sanadiyar zubewarsa kasa warwas sumamme da gudu su Ja’e sukayi kansa shi kuwa Baffa jikinsa ɓari kawai yake yi gaɓadaya ya shiga wani yanayi na rashin hayyaci.Duk yanayin da Bello yashiga amma Baffa ko a jikinsa sai ma tsawa da yake dakawa su Iro akan su tashi daga kansa tun kafin ya bata musu rai.+

Yarda suka ga ya zage yana faman kumfar baki da hayaniya akan dole sai sun bar wajan amma sukayi shiru ko ta kansa ba su bi ba yanayin da suke kallon Bello a ciki bai kamata a barshi ba yana bukatar taimako sosai don haka da sauri Ja’e ya mikewa yayi ya nufi sashin matarsa ruwa ya debo a gora yazo ya shekawa Bello da tun dazu yake halin suma bai motsa ba sai da ya sake sheka masa sannan ya saki wahalalliyar ajiyar zuciya

idanuwansa ya damke sosai kafun yaji kwanyarsa ta fara tariyo masa abun da ya faru dashi da sauri ya saki wata kara mai sauti sosai yana kai hannayensa duk biyun yana dafe kansa da yake jin kamar zai  tsage gida biyu ga wani zafi da raɗaɗi da yake ji ta ko ina.

Numfashi ya shiga ajjewa zuciyarsa na karyewa da tashin hankalin da ya tsinci kansa bai san ya rayuwa zata kasance a gareshi ba bai san ya zai kareta ba sosai ya sani sosai yake ji a zuciyarsa ALKALAMIN ƘADDARA ya rubuto masa ƙaddarorinsa masu zafi ya sani yana ciki JARRABI na rayuwa haka Allah ya hukunta daga wannan sai wannan.

Wata razananniyar tsawa da Baffa ya daka ne ya sanya shi saurin katse zancen zucin da yake ya buɗe idanuwansa lokaci guda Baffa ya hanga tsaye sai faman hirji yake yi kamar mayunwacin zaki yana faman hayaniya su Iro da sukayi shiru suna kallon ikon Allah ga sauran matan sashin na su duk sun fito suna mamakin abin da ke faruwa ganin Bello akwance a kasa ga Baffa ya na sababi ya sanya su cikin tsanani mamaki sosai sai faman kallon juna suke musamman yarda suka ga Baffa ya zage ga kuma sanda a hannunsa hakan ya tabbatar musu shine silar faruwar komai ga Bello.

“Amma Baffa bana tunanin hakan da kake yi shi ne mafita a gareka da mu kanmu…”.

Wani irin duba yayi masa ji yake yi kamar ya shako sa ya hadashi da kasa.

“Kasan Allah Iro ka bar min magana akan wannan matsiyacin mutumin in har ba so kake yi na bata maka rai ba”.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”.

Cewar wani tsoho da ya iso wajan ganin abin da ke faruwa ya shiga duban Bello kafun ya dubi Baffa.

“Lafiya Baffa me ke faruwa ne haka mai ya samu bakon naka”.

Kau da fuska Baffa yayi cikin tsananin takaici zuciyarsa take zafi duk lokacin da aka hadashi da Bello a matsayin wani nashi haushin sa daɗa karuwa yake yi ji yake kamar ya daura hannu aka ya kurma ihu don haushi.

Juyawa yayi ba tare da yayi masa magana ba ya nufi bunkarsa zuciyarsa na daɗa tsanar Bello ganin haka da tsohon yayi ya sanya shi duban su Iro cikin alamun son karin bayani amma suma sai suka kau da kan su Bello ya duba dake durkushe jini gabadaya ya gama wanke masa fuska kallon sa yake yi sosai yanayin da ya gansa yayi matukar bashi tausayi ya tabbata abin da ya hadashi da Baffa ba karamin abu bane amma bisa la’akari da yayi da Bello kamar shi ma ba a son ran shi lamarin ya afku ba numfashi yaja a hankali yana gyaɗa kai.

“Kai kam me kayi wa Baffa haka har yayi maka wannan bugun haka?”.

Ya fadi cikin muryar tausayawa da yanayin da ya ganshi a ciki Bello bai tanka masa ba illa hada kai da gwuiwa da yayi zuciyarsa na sake ya mutsewa da tashin hankalin da bai taba tsammani zai tsince shi ba cin kaddarorin rayuwarsa ba amma yau shine a haka a gaban surukin sa

wanda suka rabu dutse hannun riga ko da yake zai yi farin ciki da haka sosai in har Baffa ya dube shi ya yafe masa laifukansa ya san shi mai laifi ne sosai ya sani ba ko wani uba ne zai iya hakurin abin da ya faru a

STORY CONTINUES BELOW

tsakaninsa da Baffa ba sosai yake ganin laifin sa ya sani Habeeba ta guji iyayenta ne saboda shi don kawai tayi wa SO BIYAYYA ya sani halin so wuyar sha’ani gareshi duk ya manta abin da zai je ya dawo so ya rufe masa ido shi da Habeeba gashi yanzu yarda

rayuwa take juya masa ya sani harda hakkin Baffa ke taba masa rayuwa ta fannoni da yawa bai ga laifin Baffa ba ko wani hukunci ya dauka akansa ba zai ce bai kyauta ba.

Numfashi ya sake ja yana dago kansa yana duban Tsohon nan dake tsaye akansa irin kallon da yaga yana yi masa mai cike da tausayi da jin kai a idanuwansa shi yasanya Bello numfasawa kafun yayi magana tsohon ya sake cewa.

“Yarona kayi hakuri da komai ke faruwa a filin duniyar nan haka kaddara ce da jarrabawa daga Allah amma me ya hadaka da Baffa har ya kai ga zubda maka da jini na san komai mene ba mai sauki ba ne?”.

Murmushi Bello yayi mai sanya zuciya ciwo yana mikewa kan kafafuwansa duban tsohon yayi sosai a hankali ya shiga ba shi labarin komai da ya faru har zuwa wannan ranar da suke tare da Baffa.

Sosai tsohon ke duban sa cikin yanayi na mamaki kafun ya ja numfashi hannunsa tallabe da haɓarsa.

“Kayya ɗana gaskiya baka kyauta ba…ko da yake wannan duk ba abin ace an tayar da jijiyoyin wuya bane amma na san dole dama haka ta kasance sosai musamman yanayin da ka raba shi da ‘yarsa sannan ya baro wajan da yake zaune shekara da shekaru duk da dai komai dake faruwa daga Allah amma duk da hakan kai ne mai laifi kai ne silar komai da ya faru”.

“Nasan da haka nasan ban kyauta ba tun a waccan lokacin amma Baffa bai duban haka duk hakurin da nake bashi bai dube ni ba na san komai ya faru dani har da hakkinsa na sanya masa rashin kwanciyar hankali da nayi amma don Allah ina neman wata alfarma gareka kaɓtaya ni ba shi hakuri ya yafe mani ni da ‘yarsa domin muna cikinɓmawiyacin hali a halin da ake ciki yanzu ban san ya rayuwarta take ciki ba domin sosai na barta cikin mawuyacin hali”.

Yanayin da yayi maganar da tsananin rauni ya sanya tsohon kara tausaya masa kafadarsa ya dafa.

“Kayi hakuri bari zan yi masa magana amma ba a halin da yake a yanzu ba don na lura ya dau zafi da yawa abin da za ayi zo muje sashina da nake ka zauna nasan zuwa gobe ya sauko sai na zo na neman maka afuwansa nasan in Allah ya yarda komai zai zama daidai Baffa yana da saukin kai sai dai na lura ka kai shi bango ne”.

Gyaɗa kai Bello yayi ba tare da yayi magana ba kafun ya dubi su Iro da sukayi fakare suna duban sa a hankali ya shiga bin tsohon yana faman jinyar zuciyarsa da yake ji kamar zata faso kirji ta fito waje.

*****

“Bana tunanin hakan da kayi shine mafita a gareka Malam Baffa bai kamata in rai ya bace hankali ya gushe ba…”.

“Kayi Hakuri don Allah da wannan batun na rokeka”.

Baffa ya fadi cikin yanayi na takaici kafun ya sake cewa.

“Baka san abin da wannan yaron yayi mani bane a rayuwa ban taba samun mutumin da ya wulakanta ni ya tozarta ni ba kamar sa ya dasa min ciwon da har na mutu ba zan mance dashi ba”.

“Ka dai na fadin haka don Allah ya kamata ka lura da wani abu guda akan lamarin nan su kan su yaran ai ba haka suka so ba kuma ka sani duk abin da Allah ya kaddara sai ya faru ba wai sune suka so haka ba a,a Allah ya kaddara haka din Bello ya bani bayanin komai akan abin da ya faru a tsakaninku na san bai kyauta ba nima AKARAN KAINA naji haushin haka kuma na nuna masa kuskurensa ya ansa ni dai roko ka yafe masa”.

STORY CONTINUES BELOW

Haushi ne ya turnuke Baffa ji yake yi kamar ya zama tsintsuwa ya sauka in da Bello yake ya murkusheshi don yarda yake ji a zuciyarsa kamar ya bar duniyar nan.

“Ba abin da zai sa na hada zuri’a da mutunan da ba sa son zaman lafiya damu akan me zan dauki ‘yar cikina na ba su ba wai na tsane shi ba ne a,a ni kawai zaman da ‘yata zata yi a cikin su ne na tsana”.

Baffa ya fadi yana tuna yarda suke rigingimu a tsakaninsu fulani da manoma.

“Ba yarda za ayi ina muna zaman doya da manja da mutane sannan na dauki ‘ya ta na basu ban yi a son raina ba ban so ba amma haka Habeeba ta fifita kaɗo akaina ni mahaifinta nayi bakin ciki nayi takaicin wannan lamari da ya daɗe a zuciyata.

“Na san dole kaji rashin jindadi amma na san hakkin ka dake kansu ba zai bar su zaman lafiya ba domin iyaye ba abin wasa bane ya bani labarin rayuwarsu da Habeeba ba wani abun farin ciki a ciki sai na kunci rayuwa sun sha wahalar rayuwa sosai yanzu haƙa shi kan sa yace bai san a wani hali Habeeba take ba domin lokacin da yayi ɓatar dabo wanda shi kan sa bai san yayi shi ba tana cikin mawuyacin hali sosai”.

Da sauri Baffa ya dube shi zuciyarsa na karyewa jin abin da ke faruwa da ‘yarsa sosai yaji tausayinta sosai yake jin wani iri a zuciyarsa game da ita.

“Ka sani duk wata wahalar rayuwa da suka fada a gidan auren su akwai rashin albarkanka a ciki domin albarkar iyaye babban abu ce ga ‘ya’ya haka in mugun abu ka fada akan su haka zai ta bibiyarsu har zuwa karshen rayuwarsu in har baka yafe musu ba to abin da ya ke afkuwa da ‘yar kenan rashin albarka da kuma rabuwar dutse hannun riga da kayi da ita shi zai hana ta kwanciyar hankali da samun natsuwa”.

Ya numfasa yana duban Baffa ya lura sosai jikinsa yayi sanyi hakan ya kara masa kaimi wajan kara masa bayani domin sassauto da zuciyarsa har ya kula Bello din.

“laifin wani baya shafar wani fada da kuke yi a tsakaninku ne ku manya bai kabata ace har hakan ya shafi ‘ya’yanku ba kai yanzu ba abin  ka duba hukuncin Allah bane yarda ya hada zuƙatan ‘ya’yanku suna kaunar junansu Allah na son ku da rahama ne shiyasa zaman gaba da kukayi a tsakaninku ba komai zai zama a gareku ba sai masifa a ranar kiyama Allah yana fushi da mai gaba musamman ku da kuke addini daya a matsayinku na musulmai sam haka bai dace ba”.

Numfashi mai karfi Baffa ya ajje kafun ya dubi Malam Jauro da yayi shiru yana jiran cewarsa.

“Malam Jauro ba wai naki ta taka bane amma tsakani har ga Allah abin da yaron nan yayi mani shi da ‘yata sosai ya sanyani cikin damuwa da ciwon rai”.

“Hakuri zakayi ka dauki komai a matsayin kaddara a rayuwa dama tun fil’azal Allah ya kaddara hakan sai ta faru ai ka godewa Alalh da abin ya kasance a haka har sukayi aure in da guduwa sukayi fa ko wani abu mara dadi ya gifta a tsakaninsu ya kake ganin lamarin zai kasance na tabbata sai ka fi haka shiga tashin hankali ba a fushi da lamarin ubangiji duk abin da kaga ba saba masa ba ne in dai ya halatta ayi sa shine mafita kawai aure kuwa ai sunnar ma’aiki ne kuma matar mutum kabarin sa inda ka nuna cewa dole sai ‘yarka ta rabu dashi Allah kadai ya san abin da zai faru amma yanzu fa duk da kana cikin kunci na san dole kaji kwanciyar hankali ta wani fannin tunda ‘yarka gidan aure take ba wai duniya ta shiga ba don Allah kayi hakuri nasan dukkanninku yanzu kun ga ishara irin ta ubangiji a taimaka Baffa ka dube shi da idon baseera ka kula shi sannan ka yafe masa laifukansa wannan hanyar ce kadai kuma zaka sake haduwa da ‘yarka na sani ka na son ta don ba uban da zai ce ba ya son ɗan sa ko da kuwa abun da yayi masa na laifi ya kai duniya girma ba zai taba gudun sa ba in har ya yarda da kaddara daga Allah take”.

Shiru Baffa yayi yana jin yarda zuciyarsa ke bashi damar yi musu uzuri ya dauki komai a matsayin daga Allah ne.

“Shikenan Malam Jauro”.

Iyakar abin da ya fadi kenan a zuciyarsa yana jin wata irin nadama da tauya hakkin ‘yarsa da yake ji kamar yayi tabbas sai yau ya gane ya kusan yi ganganci gwanda da hakan ta kasance inda bai bar su sunyi aure ba Allah kadai ya san abin da zai afku kuma shi zai fi kowa kuka don shine sila..haka kawai taji zuciyarta na tashi kamar wanda taci abun da ranta bai so ba tunda aka kawo ta cikin gidan Dr.Erena gabadaya ta rasa gane kanta sosai take jin zuciyarta na raɗaɗi da zafi ga wani kunci mai girma da take jin yana ta faman kai kawo a ko ina na zuciyarta da ruhinta.+

Numfashi take faman saukewa kamar wacce tayi gudun fanfalaki a hankali ta sauko daga kan gadon jikinta sanye da wando da riga wanda suka kamata sosai bayan su ga rigar barci da ta sanya a sama sannan ta daura zani akai duk wannan abin da tayi ta yi ne saboda kar Dr.Erena ya shigo mata daki duk da ta kargame da key amma duk hakan bai kwantar mata da

hankali ba barci ma gagararta yayi a hankali ta shiga takawa har ta isa toilat din tayi abin da zata yi ta fito haka kawai take ji wani iri gabadaya ga wani kamshi da take shaka yana tayar mata da zuciya tun ranar da aka kawota gidannan take jin haka amma ta rasa dalili isa kofar dakin tayi ta buɗe da key sannan ta leka ganin ba kowa ya sanyata sakin ajiyar zuciya ta nufi

falon gidan a hankali tana dube dube cikin yanayi na dan tsoro don bazata manta arangamar da tayi da Dr.Erena aa a daren ta na farko inda suka kwashi rigima tun ranar bata haduwa dashi ba sai dai taji shigowarsa da fitarsa amma ko sau daya bata taba gangancin fitowa yana gida ba.

Tunda ta tunkaro falon take jin warin na daɗuwa sosai har sai da ta toshe hancinta sosai ta shiga zare idanu gabanta na tsananta bugawa

yawatawa da idanuwanta ta shiga yi cikin falon amma bata ga kowa ba hakan ya bata mamaki matuka cikin yanayi na tsoro da fargaba ta tsaya tsakiyar falon tana dube dube sam bata lura da mutumin dake kwance saman kujera ba bata san ya taso ba sai dai kawai taji an danko mata kugu wata irin razananniyar kara ta saki tare da toshe hancinta da take jin warin ya dadu nan ta shiga kiciniyar kwatar kanta amma ina rikon da yayi mata ba na wasa bane ji tayi kamar zata mutu numfashinta sai faman fizga yake yi runtse idanu tayi gami da yin wani yinkuri sosai taji karfi ya zo mata wanda bata san tana dashi ba ta fizge kanta ta daka tsalle can gefe guda sai faman numfarfashi take yi.

Kallo ta bishi dashi da idanuwanta da suka gama razana da tsoro sosai ta firgita da yanayinsa gani take kamar ba Dr.Erena da ta sani ba gabadaya ya canza suffarsa take ganin tana riketa mata kamar ba nashi ba da sauri-sauri ta shiga ja da baya kafun lokaci guda ta kwasa da gudu tayi dakinta ta mai da kofa ta rufe zamewa tayi ta zauna jikin kofar ta runtse idanu cikin wani irin yanayi zuciyarta sai zillo take yi kamar zata faso kirjinta ta fito.

Ta dauki lokaci mai tsayi a wajan zuciyarta da kwanyarta sai kai kawo suke yi mamaki take yi yarda take jin warin nan da ya jima tana jinsa bata taba zaton a jikinsa yake ba sai yau Allah kawai ya kwaceta amma ta tabbata in ba don haka ba da tuni ta mutu don sosai take jin warin na ratsa mata hanci yana samun masauki a cikinta.

Wani kuka ta saki mai ciwo ita kam! taga ta kanta ba ta san kaddarar da ta jayota wannan gidan ba bata san mai yasa tayi wannan AUREN ƘADDARA din ba ita kam bata ga amfanin wannan auren gareta ba illa bala’i da zai jaza mata.

*****

Abu kamar wasa Gabadaya Areefa ta rasa gane kanta tun ranar da wannan lamarin ya faru tsakaninta da Dr.Erena sosai ta firgita yau kimanin wataninta biyu kenan a gidansa amma ta rasa kwamciyar hankali da natsuwa.

“Maama don Girman Allah ki zo ki fiddo ni daga cikin wannan gidan zan mutu”.

Cewar Areefa a wani talatin dare da tayi wani mugun mafarki da yayi matukar tsorata ta.

STORY CONTINUES BELOW

“Wai me ke damunki ne Areefa eyee ba na ce miki ina nan zuwa ba amma kin ki kwatar da hankalinki ki natsu mana ina nan zuwa gobe da safe”.

Wani kuka ta sake rushewa dashi matsanancin sai faman zarya take yi a tsakiyar dakin daga ita sai kayan barci kanta duk a hargitse kamar sabuwar mahaukaci.

“Allah Maama mutuwa zanyi ba zan iya jira har gobe da safe ba don Allah ki zo ki fiddo ni daga bakin gidan nan…”.

Bata karasa maganar da take yi ba taji an hau dukar kofar dakin nata kamar za a karyata wani tsalle tayi ta ɗane saman gado idanu a warwaje.

“Maama kina ji ko kin gan shi nan fa ya zo yana dukar min kofa wayyo Allah na zai kashe ni”.

“Innalillahi wa inna ilaihr raji’un”.

Hajiya Layla ta fadi cikin sauti don tana jiyo sautin bugun kofar da ake yi sosai ta firgita ita kanta ta fara tsorata da yanayin da take jin Areefa a ciki sosai take fargarbar abin da zai je ya dawo kai kawo kawai take yi tsakiyar falon tun lokacin da Areefa ta bugo mata waya tana kuka gabadaya ta fice hayyacinta bata son abin da zai cutar da Areefa bata so a kuma yin na biyu bata so ace ta dalilinta Areefa take fadawa cikin kunci da bala’in rayuwa.

Hannayenta ta saka ta dafe kanta tana jin yarda yake juya mata a hankali ta ja kafafuwanta da take jin sun yi mata nauyi sosai ta zauna bakin kujera jikinta sosai yake rawa.

“Areefa kina jina”.

Ta fadi cikin kwantacciyar murya mai cike da rarrashi.

“Ina jinki Maama ni dai don Allah ki zo ki fidda ni daga cikin gidan nan na roke ki”.

Ta fadi tana mai sake rushewa da kuka a daidai lokacin kuma ya balla kofar ya shigo habawa ba ta san lokacin da tayi cilli da wayar ba ta yi hanyar toilet da gudu tana shiga ta mai da kofa ta rufe.

“Areefa!!”.

Taji ya ambaci sunanta cikin wata murya wacce ta tabbatar bata sa bane gabadaya sautin ta ya cika mata kunnuwa yake yi kamar gidan ma rawa yake yi gabadaya lokaci guda ta sake rikicewa sosai.

Kara kankame jikinta tayi sosai idanuwanta a runtse ba abinda take ambata sai sunayen Allah hawaye sai faman sauka suke a kuncita zuciyarta na kara rikicewa.

A kunnuwanta take jin taku wanda yake ansawa a dukkanin bangwayen gidan ko ta ina kasa da sama zubewa tayi ta zauna kasa cikin yanayi na yanke tsammani abin da yake kokarin faruwa da ita.

Bata san mai ya kai ta yarda da auren nan ba, bata san wani tsautsayi bane yasaka ta amincewa dashi, tana cikin bala’i. wanda bata san ya za ta fidda kanta ba tsoro take kar abin yayi yawa ga duka ga mari gami da tsinka jaka.

Wasu hawaye masu zafi suka zubo mata daidai lokacin da taji takun kafafuwansa na takowa zuwa toilet din fargabarta ta dadu da sauri ta shiga ja da baya domin kafafuwanta take jin suna kokarin kasa daukarta handle din kofar da aka rike hakan ne ya sanyata dauke numfashi gabadaya na dan lokaci kafun ta ji an saki a juya kuma an fara tafiya a hankali jin shirun da tayi na ɗan lokaci ya

sanyata sakin gwauron numfashi tana dafe kanta da yake faman sarawa kamar zai rabe gida biyu numfashi take fizga zuciyarta na kara rikicewa da wannan lamarin wanda bata san yarda zata kwatantashi ba.

Haka ta cigaba da zama cikin wannan talatin daren har zuwa wani lokaci wanda ita akaran kanta ba zata iya cewa wani lokaci ta dauka ba domin barci a lokacin bata san ina ya nufa ba idanuwanta sun kekeshe kiran sallar assalatu ne ya fargar da ita daga duniyar tunanin da ta lulaka cikin kasalallan yanayi ta mike tana jan kafafuwanta da take jin su kamar zata zubda ita kasa ta isa wajan famfon Toilet bayan ta yi tsarki ta daura alwala zuciyarta na ta nazarin ta yarda zata fice daga dakin don gabadaya ta gama firgicewa bata san abin da zai faru ba in ta fita daga toilet din nan bata so ta hadu dashi ta tsane shi sosai take jin tsanarsa na kara samun gurbi a zuciyarta sosai take ganin wautar kanta da ta yarda har ta amince akayi wannan auren gashi yanzu tana cizon yatsa.

STORY CONTINUES BELOW

Sai da ta gama tsalle tsalle da zuciyarta kafun ta tunkari kofar jikinta na faman bari ta buɗe kadan ta leka ganin ba kowa a hankali ta shiga takawa ta fito ganin tabbacin ba kowa ta karasa kusa da kofar ta mai da ta kulle gami da sargafa key wani irin numfashi ta ja gami da jingina da kofar ta runtse idanuwanta zuwa wani lokaci kafun ta buɗe ta ja kafafuwanta sallaya ta dauko ta shimfiɗa gami da saka hijab ta shiga bada nafilfili zuwa wani lokaci tana kai kukanta wajan Allah ya rabata da wannan mugun mutumin ya tsare mata rayuwa ya kare ta sosai take zubda hawaye zuciyarta na kara karaya da tashin hankalin rayuwar da take ciki a yanzu faragaba take bata san abin da zai faru ba tana tsoron abun da zai faru ya hada har da ita shiyasa tun farko ta so Maama ta fada mata komai da zai faru da ita a wannan gidan domin ta shirya amma bata yi haka ba ga shi yanzu tana ganin bala’i….

Ringing din wayar tace ya katse mata dogon tunanin da ta zauna tana ta faman yi bayan ta sallame da gudu ta mike don har ta tsoro amma jin wayarta ne ya hakan ya sanyata shiga dubanta in da ta cillar da ita jiya can ta jiyo sautin bayan loka din gadon ta da hanzari ta isa ta rarumo ta ganin Maama ne ya hakan ya sanyata sauri daga kiran muryarta na rawa.

“Maama kin taho ne kina ina yanzu?”.

Ta fadi da ɓarin jiki numfashi Hajiya Layla ta ajje jin muryar Areefa alamu ya nuna ba abin da ya same ta.

“Areefa dafatan dai kina lafiya ba abin da same ki?”.

“Ni dai kawai ki taho Maama don Allah ki zo ki fiddo ni daga cikin gidan nan…”.

Da sauri Hajiya Layla ta tare ta.

“Ba maganar zuwana Areefa in har na zo Dr.Erena zai gane ke wacece kuma zai gane ni kin ga kuwa in ya san waye ke ai da matsala…”.

“A,a Maama ni ba damuwa ta ba ce ya san ko ni wacece in har zan fice daga cikin gidan ba zan iya zama ba ki zo ki cece ni”.

Ta karashe muryarta na kara karyewa da kuka sosai durkushewa tayi a wajan jin Hajiya Layla ta ce ba za ta zo ba kenan duk abin da zai faru da ita sai dai ya faru kenan.

“Areefa”.

Hajiya Layla ta fadi amma Areefa bata ansa ta ba sake kiranta tayi nan ma bata ansa ta ba sai ma kashe wayar da tayi ta cillar da ita kan gado zuciyarta ta shiga hasaso mata wani lamari mai girma wanda take kokwanto akan sa tsakaninta da Hajiya Layla tana

SHAKKA akan kalaman da take furta mata tana shakka anya ba yaudararta tayi ba domin wani kudiri nata anya kuwa ba GADAR ZARE ta saƙa mata ba ta rufta ciki.

Girgiza kai ta shiga yi kamar wata kadangaruwa cikin tsayin lokaci kafun ta mike tana kai kawo cikin falon da matsanancin tashin hankali mai girman gaske sosai take jin zuciyarta na son gasgata abin da take sanar da ita sosai take jin girman lamarin a ko ina na sashin jikinta.

Bata son hasashenta ya tabbata bata son maganar zuciyarta ya zama gaskiya tana tsoro akan abin da zai je ya dawo in har hasashenta ya tabbata to tabbas da matsala wanda bata san ya zata fuske ce ta ba.

Zame jikinta tayi ta zauna bakin gadon hadi da zabga tagumi zuciyarta da kwanyarta sai faman hayaniya suke yi suna kokarin kamawa da wuta domin gabadaya ji takeyi komai ya rikice mata ta kasa samun tunanin da zata yi.

Ihu taji gami da tsayuwar mota a lokaci guda bata san lokacin da ta zabura ba tana kokarin kwasa da gudu tayi hanyar bayi taja tunga ta tsaya tana faman rarraba idanu bata san gari yayi haske haka ba daga kai tayi daidai inda agogon dakin yake karfe bakwai har da minti hamsin 7:50 mamaki hakan tayi domin bata san lokacin ya ja haka ba nan tsaye take tana jiyo sautin ihun nata shi yana kusantowa cikin gidan sosai daidai lokacin da ka buɗe kofar falon aka shigo ta tsinkayo faduwar abu mai karar gaske har sai da ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta gami da runtse idanunta…Cikin hanzari ta fito daga cikin Toilet din jikinta daure da ta shawul  kallo daya zaka yi mata ka hango tsantsan tashin hankalin da take ciki+

idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kamar wacce tayi KUKAN DOLE kai kawo kawai take yi gabadaya kanta ya gama kullewa ta rasa me ya kamata tayi a yanzu wanda ya dace a daidai wannan lokaci amma ta rasa

gaɓadaya gaboɓin jikinta ji take yi kamar an lakaɗa mata duka ta ko ina.

Da hanzari ta isa bakin gadon dakin nata ta zauna tana mai da  numfashi kamar wacce tayi gudun fanfalaki wayarta da ke yashe gefe guda ta janyo tana mai dubanta tana

jujjuyawa har na tsayin dakiku kafun ta shiga latsata tana binciko lamba ta danna mata kira amma ina! Wayar akashe taji ta hakan ba karamin kara rikita mata kai yayi ba mikewa tayi da sauri ta nufi sif din dake dakin

buɗewa tayi ta janyo doguwa riga baƙa ta zurawa jikinta gami da yin rolling da mayafin ta janyo flatshoes ta sanya key din motarta da ke kan Mirrow ta dauka tare da dauko wayarta sai da ta karewa dakin kallo kafun ta fice cikin hanzari zuciyarta na kara tsinkewa da tashin hankali mai girman gaske.

Cikin hanzari ta fice zuwa tsakar gidan motarta kirar 406 mai launi ruwan toka ta shiga tare da yi mata key bayan ta buɗe get din gidan ta fice ziciyarta na kara rikicewa ba abin da take jiyowa sai sautin muryar Areefa da yarda take kuka tana ihu akan ta zo ta taimake ta zata mutu bata san mai za tayi mata ba ba ta san abin da ya kamata tayi a daidai wannan

lokacin ba tana tsoron Dr.Erena ya sake maimaita abin da ya zama shine sanadi a yanzu tana tsoron a sake komawa gidan jiya za tafi kowa bakinciki zata fi kowa takaici a duniyar nan domin komai ya faru da Areefa a yanzu da lokacin baya duk ita ce sila ta hanyarta komai ya ke tabbata.

Wasu hawaye ne ta ji sun sauko mata da sauri ta sanya hannu daya tana dauke su tana mai tuki jikinta a sanyaye zuciyarta ne ta shiga kai kawo tana so ta samo wanda zai taimaka mata da abin yi sosai kwanyarta take hayaki tana kokarin kamawa da wuta.

‘Alhaji Abdulwahaab’

Sunan da ya zo mata kai kenan da sauri ta runtse idanunta kafun ta buɗe su tana jin wani irin yanayi a zuciyarta mai girma gaske da sauri ta gangara bakin titi tayi parking tana mai hada kanta da sitiyarin motar na dakiku sai faman sauke numfashi take kafun ta dago ta dubi wayarta

lambarsa ta binciko jikinta har rawa yake yi ta danna masa kira gami da karawa a kunne cikin kankanin lokaci ta shiga ruri amma ba a daga ba har ta katse sai da tayi haka sau uku a na hudu Allah ya taimaka ya dauka wani irin ajiyar numfashi tayi mai karfi tana mai cewa.

“Don Allah kana ina Alhaji Abdulwahaab akwai matsala fa sosai ina bukatar ka yanzu yanzun nan ko ina kake ina kan hanyar gidan Dr.Erena mu hadu acan”.

Mamaki sosai ya cika shi jin abin da take fadi.

“Ban fahimce ki ba Hajiya Layla meke faruwa ne?”.

Dafe kai tayi kafun ta sake nisawa.

“Ba mu da lokaci don Allah ka zo yanzun nan akwai matsala ce”.

numfashi ya sauke cikin wani yanayi.

“Amma Hajiya Layla kin mata yanayin da muke ciki ne da Dr.Erena kin san za a samu matsala in har ya gane mu din ne muke tare da Areefa…”.

STORY CONTINUES BELOW

“Alhaji Abdulwahaab!”.

Hajiya Layla ta kira shi tana mai katse shi zuciyarta na kara hargitsewa.

“wannan lokacin ya dade da shafewa na manta dashi yarinyata nake bukata Abdulwahaab duk wani boye-boye ya kare tsakani na dashi zan fuskace shi komai zai faru zan tunkare shi sai dai duk abin da zai faru ya faru”.

“Hajiya Layla da kin yi hakuri man…”

.

Katse wayar tayi jin yana kokarin bata mata lokaci wani kuncin taji ya tokare mata wuya mai Alhaji Abdulwahaab yake nufi da nuna halin ko in kula akan wannan lamarin da ta sanar dashi anya kuwa ya san abin da yake yi anya kuwa ya ji abinda ta fada masa sosai dafe kai tayi na dan lokaci kafun tayi wa motar ki ta fizge ta da karfi zuciyarta cike da zullumi.

Tafiya sosai tayi sannan ta isa unguwar da Dr.Erena yake nesa da gidan tayi parking zuciyarta ta na bugawa da sauri sauri bata san mai zata yi ba sosai take fargaba da tsoro a zuciyarta Areefa take so ta gani so take yi ta ga halin da take ciki runtse idanu tayi gami da kashe motar ta fito ta mai da kofar ta rufe a hankali ta shiga takawa zuciyarta na kara sautin bugu har ta isa bakin get din gidan lekawa ta shiga yi ko zata hango cikin gidan amma ba ta hango komai  ba gefe ta ja kadan tana duban layin amma ba kowa sit kake ji kamar

mutuwa ce ta gifta hakan ya dan kara tsorata ta amma cikin karfin hali da nuna rashin tsoro ta shiga kwankwasa Get a hankali idanuwanta na saitin karamar kofar zuciyarta na kara sautin bugun ta.

“Waye a nan?”.

Ta ji an fadi da sauri ta juya don jin muryar tayi kamar daga sama domin gabadaya a firgice take sai da ta saita kanta sannan ta lura ashe Maigadi ne wanda ya buɗe kofar a daidai wannan lokacin.

Yak’e ta shiga yi shikuwa sai faman gaisuwa yake watsa mata ganin Babbar mace ce mai suffar naira.

“Yawwa Alhaji na ciki kuwa?”.

Ta fadi tana mai kokarin saita kanta sai da ya kare mata kallo don ya so gane rikicin da ke idanunta kafun ya gyaɗa kai alamun eh wani rugugin tashin hankali ne ya dirar mata a zuciya amma ta danne tana mai kara faɗaɗa yak’enta kafun ta numfasa.

“Ok ni mahaifiyar matarsa ce Areefa”.

Da sauri ya kara ladab  yana mai bude mata kofar domin ta shiga sai da tayi addu’a kafun ta saka kafafuwanta cikin gidan tana takawa tana bin ko wani sashi da lungu na gidan tana kara tsorata da Dr.Erena irin dukiyar da ta ga an zuba a gidan ta fitar

hankali ba ta lura da motar dake gabanta ba har ta kusan cin karo da ita san nan tayi baya da sauri motar tabi da kallo ganin yanayin da take da sauri ta zaro idanu waje ganin yarda motar tayi gilashin fitilun duk sun fashe mamaki ne ya cika ta da tsoro a zuciyarta tana tambayar mai ke faruwa Allah yasa ba Areefa ba ce tayi accident wani irin bugawa taji

gabanta yayi da sauri ta yi cikin falon tana zuwa ta tadda shi a bude ba tare da fargabar komai ba ta fada ciki baje ta hango mutum tsakiyar falon sai faman murkususu yake yi

idanuwansa a kankafe da sauri ta ja baya tana mai kiran Areefa da karfi gidan gabadaya ya dauka sautin muryarta.

Hancinta ta toshe jin irin warin dake tashi a tsakar falon gabadaya taji zuciyarta tana sama da kasa kamar zata yo waje rarraba idanu ta shiga yi tana faman kiran Areefa ganin ba alamunta hakan ya sanyata nufar cikin falon sosai tana buɗe daku har ta haye saman benan dakunan da ta gani ajere guda uku ta nufa tana kiran Areefa kamar wacce makoshinta zai yo waje.

STORY CONTINUES BELOW

Ita kuwa Areefa da take can kulle cikin daki kamar daga sama ta tsinkayo Muryar Hajiya Layla bata gasgata ba ta dauka kawai halin firgicin da take ciki ne take jiyo sautin kamar na ta amma kuma sai taji

sautin na daduwa da sauri ta mike ta buɗe Toilet din kamar daga sama ta ji ana kwankwasa kofar dakin da take muryar Hajiya Layla na tashi da gudu ta fito har tana tuntuɓe ta nufi kofar ta buɗe da sauri Hajiya Layla ta gani a tsaye da sauri ta isa gareta ta rungume ta tana faman sakin ajiyar zuciya mai karfi idanuwanta sai zubda hawaye suke.

“Areefa me ke faruwa ne haka?”.

Dago kanta tayi daga kafaɗarta ta dube da jajayen idanuwanta.

“Maama Dr.Erena zai kashe ni ba zan iya zaman gidan nan ba wallahi na hakura ba zan iya zaman aure dashi ba don Allah ki fidda ni daga cikin gidan nan ji nake kamar numfashi zai katse”.

Dubanta take yi sosai ta na hango rashin hayyaci a idanuwanta gami da firgice janta tayi cikin dakin gami da mai da kofar ta rufe bakin gado suka zauna Hajiya Layla tana dubanta kafun ta nisa lura da tayi ba abin da ya same ta.

“Amma me ke faruwa dake haka duk na ganki a wannan matakin AREEFA?”.

Runtse idanu tayi hawaye suka zubo.

“Maama baki jin warin da nake ji ne?”.

Ta fadi muryarta da rauni a ciki tana faman girgiza kai.

“Tun ranar da na zo gidan nan nake jin wannan warin har izuwa yau kuma wallahi daga jikinsa ne warin nan ke fitowa da farko nayi zaton wani mushe ne a cikin gidan amma ban gani ba sai jiya  da muka hadu dashi a falo nake jin warin na fitowa daga jikinsa zuciya ta dinga tashi”.

Kure ta tayi da idanu kafun ta saki murmushi wanda ya jefa Areefa a wani mataki na mamaki.

“Mai ya same shi na ganshi baje a falo yana faman murkususu”.

Zaro idanu Areefa tayi gami da mikewa.

“Wallahi ban sani ba ni dai dazu naji faduwar abu gami da ihu to a tsora ce nake ban fita ba”.

Mikewa tayi ita ma ta ja hannunta suƙa fito  ganin sun nufi falon hakan ya sanya Areefa turjewa tana duban Hajiya Layla.

“Maama..”.

Daga mata hannu tayi gami da nuna mata alamun tayi shiru ba ta sake magana ba ta bi bayanta gabanta na bugawa ga warin da take ji yana karuwa sosai hannu ta saka ta rufe hancinta  har suka isa falon zaune suka hango shi ya jingina da kujera sai gumi yake yi kamar wanda aka watsa wa ruwa hannayensa duk

biyun dafe da kai sakin Areefa tayi ta isa gareshi tana mai yi masa wani irin matsayacin kallo kafun ta saki wani murmushi wanda shi kuma a daidai lokacin ya dago kansa ya sauke a saitin ta.

Kallo yake binta dashi na alamun na sanki sosai yake maimaita kallon nasa akanta zuciyarsa da kwanyarsa suna kwaso masa abubuwa da suka shuɗe na shekaru masu yawa runtse idanu yayi ya buɗe su  bakin sa ya shiga motsawa a hankali yana mai runtse idanuwansa shi kadai ya san wahalar da yake ciki.

“Hajiya Lay…”.

“A kul! din ka karka sake kar ka so ma ambatar sunana da wannan bakin naka”.

Ta nuna shi da yatsa kafun cigaba da fadin.

“Ashe ka gane ni ai na dauka ka mance fuskata a duniyar rayuwarka”.

Sosai yake cikin tu’aji da daurewar kai tashi yayi sosai daga jikin kujerar ya juya ya dubi inda Areefa take tsaye kallon ta yayi kafun ya juyo ya dubi Hajiya Layla.

“Me ya kawo ki gidaɓaa me kika zo yi ba na ce miki karki sake na sake haduwa da ko mai kamar ki bane”.

Ya fadi yana mai cizon labbansa idanuwansa na kara kaɗawa sosai kwaɓe baki tayi kafin ta nuna shi da yatsa.

“Dr.Erena kenan kana tunanin zan bar rayuwarka ne ai duk wanda ya dama dani to wallahi tare zamu shanye na san zakayi mamakin ganina a gidan ka ko?”.

Ta fadi tana mai murmusawa.

Mamaki ne ya sake cika shi tare da firgice mai girma domin shi dai ya mance da wata Hajiya Layla a duniyarsa tun da kuwa ya ganta a yanzu akwai wani abu tattare da ita.

“Dr.Erena Attajirar duniya”.

Ta fadi tana barkewa da dariya wanda sosai ta kaɗa cikinsa amma ya ki nunawa ya shiga kokarin tashi amma ya kasa rikewa yaji bayansa yayi ji yake yi kamar ana doka masa guduma.

“kar fa ka damu kan ka ba wani abu bane Malam Nata’ala ne ya bani sako in ba ka ai na san ba zaka mance sunan ba ko?”.

Ta fadi cikin yanayi na izgilanci.

‘Malam Nata’ala’.

Can kasar makoshi yana tunanin inda ya san sunan kwanyarsa ne ta fara shawagi da sunan amma har ta gama bai canko ba illa idanu da ya zubawa Hajiya Layla da take ta faman sakin murmushi.

“nayi mamaki da naga komai naka ya fara sauyawa wai yau kai ne da yin aure da alamun dai komai dake faruwa kwanyarka bata daukar sa da alamun kuma tarihi zai maimaita kan sa”.

Duban Areefa tayi kafun ta dubi Dr.Erena da yaje ta faman cizon laɓbansa kamar zai cizge su daga jikinsa.

“wannan ita ce matar taka?”.

Ta fadi cikin yanayi na rainin hankali a hankali ta taka ta isa wajan da Areefa take tsaye ta dafa mata kafaɗa kafun ta sake ta dawo ta zauna cikin daya daga kujerun falon tana dora kafa daya kan daya gami da duban Dr.Erena da kan sa ya shiga wani mataki na rashin aiki komai yake ji yana cinkoshe masa ya kasa tuna komai a daidai wannan lokacin.Dubanta yake yi cikin wahalallan yanayi zuciyarsa na ta faman kokarin bankado masa abin dake boye amma kwanyarsa sai hayaki take yi masa ji yake yi kamar ya mike ya shaƙo+

Hajiya Layla don ya tabbata akwai wani boyayyan al’amari game da ita zai iya cewa ma halin da yake ciki a halin yanzu ita ce sanadi ba kowa ba runtse idanunsa yayi gami da sakin wani nishi mai karfi kamar macen da ke nakuɗa.

“Hajiya Layla mai ya dawo dake rayuwata a daidai wannan lokacin kuma meye hadinki da MATATA?”.

  Ya fadi cikin yanayi na azaba da raɗaɗi da yake jin ko ina na jikinsa ya dauka numfashin sa sai sama da kasa yake yi.

  “Dr.Erena kenan kana tunanin akwai abin da zai sake dawo dani rayuwarka a wannan karnin kar kayi zaton wani abu amma abu daya nake so ka tuna a rayuwarka shi ne Sharri dan aike ne duk in da aka tura shi zai je ya dawo abu daya nake so ka kuma tunawa shine Malam Nata’ala”.

  Areefa da ke tsaye tun dazu idanuwanta na tsiyayar da hawaye Hajiya Layla ta dube ta sosai kafun tace da ita.

“Zo ki samu waje ki zauna mana kin tsaya a tsaye in har kika ce kallon wannan mutumin za ki din ga yi kina zubda hawaye kina da aiki sosai a gabanki hawaye ya kamata ace ya tsaya miki a wannan matakin da kike”.

  Girgiza kai tayi tana mai sake watsawa Dr.Erena wani matsiyacin kallo ji take yi kamar ta shako shi ta kashe shi don wata tsanarsa take jin na sake buɗe fili a zuciyarta mai girman gaske.

  A hankali ta shiga takowa tana isowa gareshi warin da take ji yana tashi daga jikinsa shi yafi komai tayar mata da hankali idanunta ta runtse gami da rike numfashinta idanuwanta akafe akan sa ba abin da ke cikin su sai

zazzafar kiyayya mai girman gaske shi kansa sai da yayi mamaki kan irin kallon da take masa kau da kai yayi yana tambayar kan sa mai ke shirin faruwa dashi ne tun da ya tashi yau ya rasa gane kansa tun kafin ya isa wajan aiki ya samu tsautsayin

haduwa da yan fashi ko makasa zai ce masu oho suka yi masa dukan shan gishiri gami da kwace jakar makuɗan kudaɗen da zai je da su Company din sa domin zubawa ga wata harkalla da akayi masa tallarta ya amince zai yi ta.

  Bayan sun dake shi sun fasa masa mota sun kwace kudaɗen kuma wanda hakan bai dame shi ba akan yarda yake jin jikin sa a yanzu sosai ya fara fargabar abin da yake kokarin faruwa dashi a yau din fuskar Hajiya Layla da ta bayya a gareshi akanta ya diga ayar tambaya.

   Kofar da aka turo aka shigo ne ya sanya shi tsinke zaren tunanin sa sosai yake bin kofar da kallo a daidai lokacin yayi arba da Alhaji

Abdulwahaab suna kallon junansu ido cikin ido mamaki al’ajabi ya sake narkar dashi kau da kai yayi tare da runtse idanuwa yana mai tambayar kansa mai ya kawo Alhaji

Abdulwahaab gidan sa a daidai wannan lokacin ganin abin yake yi kamar a mafarki ba gaskiya ba sai faman jan numfashi yake wanda yaji yana kokarin kwace masa.

  A hankali ya shiga takowa tsakiyar falon yana dubansu su duka cikin wani irin yanayi musamman yarda ya ga Dr.Erena aciki abin ya bashi mamaki gefe ya koma ya tsaya yana duban Hajiya Layla da ita ma shi take duba.

“Ka zauna mana”.

Ta fadi tana nuna masa kujera, gyaɗa kai yayi tare da zama bakin sa cike da tambayoyi masu yawan gaske amma ya rasa ta ina zai fara ko da yake akwai abin da yake hasashe akan faruwan haka…

STORY CONTINUES BELOW

Muryar Hajiya Layla ce ta katse masa tunanin da yake yi.

“Lokaci yayi sakon Malam Nata’ala zan isar kamar yarda ya bani shi amma bisa mamaki shi ya manta da waye ma Malam Nata’alar”.

  Ta karashe tana sakin wani mugun murmushi kafin ta mike kan kafafuwanta da hanzari ta shiga kai kawo a tsakar falon hannayenta goye a bayanta.

****

   A hankali take jan motar cikin yanayi na fargaba da tsoron yanayin wajan haka kawai take jin zuciyarta na gargaɗin ta akan ta koma kar taje amma wani sashin na kara mata kwarin gwuiwar zuwa din runtse idanu tayi tana kara kurɗawa cikin dajin da tun da take a filin duniyar nan bata taba zaton akwai wannan dajin ba.

  Tafiya tayi sosai har ta fara yanke tsammani da rabon samun abin da ta zo nema ji take yi kamar kwatancen da Areefa tayi mata ba haka bane domin ta fara sarewa da tafiyar nan da ta kwasa kamar wacce zata bar duniya.

  Burki ta taka da sauri ganin uban tafiyar taki karewa gashi wani abun da take shirin gani ta baro surkukin daji amma nan kuma ta fara hango filin Allah kamar an share shi hakan ya fadar mata da gaba ba tare da ta karasa shiga filin ba don zuciyarta sosai ta tsoratar da ita akan ko wani mugun abun ne a shimfiɗe a wajan.

  Shiru tayi tana tunano labarin da Areefa ta bata akan zuwan su gidan Malam Nata’ala sosai ta fara gano komai da sauri ta sakeyi wa motar key ta fizgeta bayan ta nemi tsari wajan Allah da ya kareta daga duk wani abun ƙi da yake tattare da wannan wajan ba ta gama wannan tunanin ba ta fara hango wani farin gida daga can tsakiyar filin wanda ya kasance shi kadai hakan ya tabbatar mata gidan kenan.

  Tsayar da motar tayi gami da kasheta baki daya ta shiga kallon gidan yana yarda Areefa ta kwantata mata ba abin da ya sauya daga cikin sa mamaki ne ya cika ta dama a duniyar nan a irin wannan dajin har za a samu wanda zai iya rayuwa a cikinsa shi kadai ba tare da wani ba girgiza kai tayi gami da buɗe murfin motar ta fito a hankali ta fara takawa cikin yanayi na tsoro bayan ta rufe motar tana tafiya tana waiwaye don gabadaya tsigar jikinta ji take yi tana tashi kanta yayi mata nauyi sosai.

Gidan taga kamar yana sauyawa a idanuwanta tsoro na kara shigarta amma duk da hakan bata daina kusantar gidan ba a haka har ta isa kofar gidan a buɗe yake hakan ya bata damar shiga ba tare da wata fargaba ko tsoron da take ji zuciyarta na kawo mata ba lokaci guda taji duk wata fargaɓar na raguwa sosai.

A tsakar gidan ta tsaya tana mai kallon cikinsa komai tsaf-tsaf kamar gidan sabuwar amarya.

Daki guda ta hango wanda labule ke sake wajan ta nufa tun da ta tunkari wajan take jin wani wari na kawo wa hancinta farmaki da sauri ta buɗe jakartaa ta zaro farin hankicif ta toshe hancinta amma duk da hakan ba ta daina jin warin ba.

Hannunta daya ta saka ta buɗe labulan da sauri ta saki gami da ja da baya idanuwan ta a warwaje abin da ta gani yayi matukar faɗar mata da gaba nan ta shiga ambaton Allah da neman tsari sai da ta kwashe mintina kafun tayi kundunbalar sake buɗewa hango shi tayi kan buzu a takure sai ka rantse ba mutum bane a wajan

fuskar nan tayi kaca-kaca da kasumba zallar fuskar tashi ba ka gane wa kafarsa kuwa guda daya sai faman wari take yi kana hango tsutsuni na yawo a cikinta.

Runtse idanu tayi lokaci guda taji wani tashin hankali ya ziyarce ta zuciyarta ta karye hawaye ya shiga zubo mata lokaci guda a hankali ta jingina da bango tana jin yarda kanta ke juyawa kamar zata zube a kasa numfashinta na sama da kasa.

STORY CONTINUES BELOW

“Baiwar Allah”.

Kamar daga sama ta tsinkayo muryarsa wanda hakan yayi matukar bata mamaki jin muryarsa raɗau kamar ba wanda yake cikin mawuyacin hali ba dubansa ta shiga yi da buɗaɗɗun idanuwanta zuciyarta na tsalle da tsoro.

“Me ya shigo dake wajan nan kin san bala’in da ke cikin nan kuwa kinsan masifar dake tattare da wannan wajan kuwa kiyi wa kanki fada in ma wani abu ki ka zo nema to kiyi maza ki fice tun kafin wani abu ya same ki”.

Kalamansa taji suna yi mata yawo a kwanya da sauri ta durkushe tana dubansa kafun daga bisa tayi kokarin yi masa sannu bai ansa ta ba illa kau da kai da yayi wani hayaki ne ta ga yana fitowa daga bangon dakin na hagu yana shawagi a tsakar dakin

yana murɗewa hakan ba karamin kara rikita Hajiya Layla yayi ba da sauri ta fara ja da baya tana kokarin ficewa daga dakin.

“Na san abin da ke tafe dake kuma nayi murna sosai da kiƙa zo a daidai wannan lokacin Dr.Erena ko na san akan sa kiƙa zo nan ba zan boye miki ba na san na cuce Khairiyya a rayuwarta nayi dana sani domin tun daga kanta na fara fuskartar matsalolin rayuwa har zuwa wannan lokaci da nake wannan halin…”.

Tari ne ya sarke shi wasu abubuwa su ka shiga zubowa daga bakin sa kamar tsutsotsi sai motsi suke yi Hajiya Layla gabadaya ta rikice ji tayi fitsar na kokarin kwace mata.

“Ki tashi ki tafi lokaci na nan zuwa kuma Dr.Erena shima sai ya dandani bala’in da nake ciki banta taba mugun aiki ba kamar yarda nake yi wa Dr.Erena shine mutumin da naƙe yi wa aiki wanda ni akaran kaina ina tsoro da fargaba in ina yin sa sannan ina kara jinjina rashin imani irin na Dr.Erena domin kuwa a duk sahun mutanan da nake yi wa aiki shine yafi kowa kawo mani mugun aiki”.

Shiru yayi yana jan numfashi kafun ya sake fadin.

“yace zai yi aure ko kuma tsarin aikin da nayi masa babu zancen aure har gaban abada to wannan auren shi zai zama SILAR AJALI gareshi duk ranar da aka daura auren to tabbas shima yarda na zama shima haka zai zama yarinya ta shi ki tafi tun kafin wani abu ya same ki sannan karki sake ki hana Khairiyya aurensa ki bari a yi ko da na rana daya ne na tabbata daga wannan ranar salo zai sauya”.

Mamaki ne ya cika ta zuciyarta na kara karyewa da tashin hankali mamaki take yi sosai da maganganun Malam Nata’ala tun da take a rayuwarta yau ne rana ta farko da ta ji ta tsani duniyar nan gabadaya taji ta tsani zama cikin ta…

“Da hannu na nake amfani da ayar Allah tsarkakankiya domin biya masa bukata ina amfani da jinnu a nan Dr.Erena ya sha cin naman jarirai wanda aka dafa su da ayar Allah da wani suddabaru na jinnu ya sha zuwa da mace mai dauke da ciki wanda bai haura wata biyar ba in saka jinnu su barar dashi tare da yi masa magani don kawai yana so ya zama daya daga cikin ATTAJIRAN DUNIYA nayi da nasani nayi kaico da rayuwata  da ta kasance a haka na san ko a lahira bani da wani amfani hukunci na mai girma ne domin tawa ta kare amma ki sani yarda na shiga bala’i shima sai ya shiga nan kusa kadan Sharri dan sako ne ya na nan tafe gareshi”.

Yana gaman fadin haka nan ya shiga tari wannan abubuwan masu kama da tsutsotsi na sake zubowa kamar an buɗe wani matattarar su tana kallo wannan hayakin ya shiga wuce ta cikin hancin sa jikinsa lokaci guda ya shiga canzawa yana baƙi gami da ruwan toka kansa da duk wani gashi dake jinsa yana canzawa zuwa fari

gami da fidda wani hayaki da sauri ta rarrafa ta fice daga daki gabadaya ta gama rikicewa ta fice daga hayyacin ta tashin hankalinta ya kara ninkuwa duniyar gabadaya tana tsoron ta cikin yanayi na ɓarin jiki da rashin hayyaci ta fice daga gidan idanuwanta a rufe kawai jefa kafafuwanta take yi har Allah ya kaita inda motarta take..

****

Hawaye ne ke zuba sosai a idanuwanta zuciyarta na kara karyewa bata so tuna wannan labarin ba amma ba yarda zata yi domin ta gama tsorata da halin da ta tsinci Malam Nata’ala a ciki wani tsoron Allah take ji yana samun gurbi a

zuciyarta duniyar take ji gabadaya ta fice mata daga rai duban sa tayi kafun ta dauke hawayen da suke zuba mata.

“nasan yanzu zaka tuna labarin da ya shuɗe sama da shekaru ashirin da doriya a duniyar ka na san zaka tuna yarinyar da ka lalata mata rayuwa yarinyar da kayi amfani da ita don kawai cikar burin ka Khairiyya da kasani to ita ce wannan Areefa da ka aura da sunan matar aure na san kuma zaka tuna waye Malam Nata’ala”.

Kuka ne ya ci karfin ta da sauri ta toshe bakinta da hannayenta tana duban Areefa wacce gabadaya kukan take yi da shassheka kamar numfashin ta zai dauke.

Wani irin tari ne suka ji ya sarke dashi hannunsa daya a saitin Areefa idanuwansa lokaci guda suka shiga sauyawa fizga yaji numfashin sa nayi kamar ransa zai fita gabadaya ya gama rikicewa da labarin da yaji domin ya manta da wani mutum wai shi Malam Nata’ala..

About AIS

Check Also

UKU BALA’I CHAPTER 12

UKU BALA’I CHAPTER 12                    Www.bankinhausanovels.com.ng  Tsaye …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *