UKU BALA’I CHAPTER 10

UKU BALA’I CHAPTER 10

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zuciyarta zafi take sosai kwanyarta sai kokarin kamawa da wuta take yi ta rasa komai nata mai armashi ta rasa duniyar guntun farin cikinta dake rayuwarta sosai take cikin yanayin kunci zuciyarta sai faman yayyagewa take yi da girman tashin hankalin da take ciki kuka ya daina samun gurbi a idanuwanta HAWAYEN ZUCIYA su ma kan su sun dai samun gurbin zuba komai ya kafe komai ya daina samun numfashi mai kwari daga gareta ba ta san ya zata+

kwatanta wannan lamarin ba bata san ya zata dauke shi ba bata san mai yasa duniyarta take kokarin yamutsewa ba koma tace ta ya mutse ALKALAMIN KADDARA yayi rubutu mai tsauri akanta bata yi tsammanin rayuwarta zata kare a haka ba farin ciki babu shima kwanciyar hankali babu komai da komai babu kawai dai…

Wani irin kartawa zuciyarta tayi da hanzari ta mike daga kwancen da take tana sanya hannayenta duk biyu tana dafewa idanuwanta a runtse kamar wacce ake sokawa karfe mai tsanani jar wuta a jikinsa numfashi take da kyar tana jin kirjinta na kara tsananta bugawa mikewa tayi kan kafafuwanta tana faman cizon laɓɓa kamar zata fizge su daga mazauninsu.

Kai kawo ta shiga yi cikin dakin a hankali tana duban su Umma da suke barcinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da matsala ba sosai take tausayin kanta sosai take ganin kamar ita kadai ce a filin duniyar nan take cikin tashin hankali gani take kamar ita kadai ne so yake bugawa yadda ransa ke so kamar wata ball bata san ya zata dauki AL’AMARIN SO ba a filin

rayuwarta bata san ya zata kwatanta bala’in da fada ba A DALILIN SO ba tana shakka akan cewa so yana da dadi gaskiya ba za ta amince da haka ba so guba ne ba komai ba.

Haka tai ta safa da marwa a tsakar dakin har zuwa wani lokaci mai tsayi cikin DUHUN DARE ba tare da ko yaya ne barci ya so kama ta ba in aka ce ma barci zai zo wajan ta zata karya ta domin kuwa ita a karan kanta ta manta yaushe rabonta da yin barci mai ansa suna barci…

“Ke Mariya wai lafiyarki kalau kuwa?”.

Kamar daga sama taji muryar Umma a dan razane ta juya ta dube ta zaune ta hangi Umma ta kafeta da idanu kafun ta cigaba da fadin.

“Ke yanzu fisabilillahi kina ganin haka ya dace miki Mariya kina zaton wannan abin da kike yi shi ne zai zame miki mafita a filin duniyarki bana zaton haka wannan damuwar da kike shiga ba karamar matsala zata jefa ki ba ke ko fada ba zakiyi wa kanki  ba yaushe ki ka farfaɗo daga ciwo wa yayi zaton ma za ki sake WATA RAYUWA a duniyar nan”.

Rausayar da kai tashiga yi cikin rashin abin cewa ta sani duk maganganun da Umma take fadi akanta gaskiya ne amma ita bata san ya zata koyi duk wannan abubuwan ba zuciyarta sosai da sosai take zafi sosai take cikin tashin hankali wanda ba ta san ya zata kwatanta shi ba.

“Zo ki zauna muyi magana”.

Cewar Umma cikin Muryar rarrashi da tausayin ‘yar tata a hankali Mariya ta ja jiki ta isa kusa da ita ta zauna kafun ta dago ido ta dubi Umma jikinta ya shiga rawa kamar wata mai jin sanyi.

“Umma ina cikin bala’i ban san ya zan kwatanta shi ba bana zaton na shigo duniyar nan a nasara bana tunanin akwai wata rayuwa da zan yi har karshen numfashi na bayan wannan…”.

Sosai tausayin ta ya kara rikita zuciyar Umma nan da nan ƙwalla suka tarun mata a ido bata bari Mariya ta gani ba domin kuwa ita ta san halin da take ciki akan duk matsalolinta amma bata nuna mata ba ta son abin da zai kara dagula mata lissafi dakatar da ita tayi.

“ki daina fadin haka Mariya na sha fada miki duk abin da ki ke ganin yana faruwa da baya dama tun fil’azal ALKALAMIN KADDARA ya zana masa haka a KUDINSA don haka Mariya ke daina cewa ke ce kika fi kowa rashin rabo a duniyar nan ke taki matsalar kika sani in da zaki ga na wani zaki sha mamaki zaki ce ke ba komai bane ya same ki godiya zakiyi wa Allah duk wannan abubuwan suna cikin KUDIN JARABAWARKI…”.

STORY CONTINUES BELOW

“Sauki fa kika ce Umma?”.

Mariya ta fadi da wani irin yanayi mai karya zuciyar mai sauraronta kafun ta ja numfashi tana tura laɓɓanta cikin baki.

“bana tunanin haka bana zaton akwai wanda ya kai ni rashin nasara a filin duniyar nan…”.

Da sauri Umma ta rufe mata baki muryarta na karyewa kamar mai son fashewa da kuka.

“A,a Mariya ki daina yawan batun nan zaki iya yin saɓo Allah zai yi fushi dake ki dinga tunanin bayanki ki dinga tuna wanda ya fiki Mariya akwai wanda yafi ki da yawa su zaki duba domin ki tabbatar da cewa ke rayuwarki ma a haka akwai farin ciki shin kina tunani kuwa akan wanda suke faɗowa duniyar ba tare da

komai ba ba uwa ba uba ba dangi shin bakya tunanin irin rayuwar da suke yi shin kina tunanin in suka shiga matsala akwai wanda yake rarrashin su ke ki godewa Allah kina da masu duba ki har su ji ƙan ki Mariya rayuwar nan da kike gani ba wai farin ciki bane a cikinta ba wani nishadi a cikinta duk wanda kika ji yace duniyar nan akwai dadi to ki tabbatar auren sa duniyar tayi ki sani duniyar nan ba wai zama ake yi na dindindin ba komai dake faruwa jarabawa ce akwai ranar da komai zai sauya kuma zai canza…”.

“zuwa yaushe Umma zuwa yaushe kike tunanin rayuwa zata sauya bana tunanin haka bana tunanin rayuwa zata sake buɗe mana wani shafi bacin wannan ki duba tun da na ta so rayuwa take juya mana baya rashin gata rashin Uba rashin kwanciyar hankali komai ma Umma babu a rayuwar mu ta yaya kike zaton zan yi farin ciki?”.

Maganar take yi cikin rashin hayyaci muryarta na kara buɗewa bakinta sai rawa yake yi Umma kallonta kawai take yi tana faman gyaɗa kai hawaye sai bin kumatunta suke yi bata san ya zata kwatanta wannan al’amarin ba ita gabadaya komai ya kwance mata komai ya kara dagule mata numfashi ta ja mai karfe kafun ta hadiye wani yawu mai tauri ta sake duban Mariya bayan ta dauke hawayen da suke faman zubo mata gabanta yana todakawa so take yi tayi magana amma tana tsoron yarda komai zai watse in batayi wasa ba amma ana ta tunanin ita ce kawai hanyar mafita a garesu.

“Mariya mai zai hana ki zabi daya a cikin su tun da abin da ya kasance haka duk wannan kai ruwa ranar da ake yi bana tunanin zaki iya zama matar su su duka mace bata auren namiji sama da daya maza ne suke da wannan damar ta aure mace sama da daya kokari zakiyi ki baiwa zuciyarki juriya da hakuri ki runtse idanu ki zabi daya a cikin su”.

Galala Mariya tayi da baki tana kallon Umma da wani irin yanayi gabanta na tsananta bugawa kafun wata dariya ta kwace mata kamar wata sabuwar kamu sosai take duban Umma wasu hawaye na zubo mata da take jin su kamar garwashin wuta suna saukar mata a fuska laɓɓanta ta ciza sosai har sai da taji zafi ya ziyarce ta kafun ta sake su.

“Zabi kuma Umma? bana tunanin cikin UKU BALA’I zan iya daukarwa kai na daya gaskiya bana tunanin a filin duniyar nan ko zan rasa mai so na zan iya daukar wani a cikin su bana son su su dukan na hakura da su domin kuwa komai ya faru dani a dalilin su ne duk wata bakar rayuwa da wahalar ta da na shiga a dalilin su ne ba su da tausayi ba su da imani sam a zuciyarsu suna son kan su da yawa in da suna jin tausayina wallahi ba za su yi mani haka ba Umma WASU MAZAN san kan su kwai suka sani da burinsu da suke fatan cimmawa akan abinda suke so ba ruwan su da abin da zai faru in dai ba akan su ba ne”.

“A,a Mariya ki daina fadin haka duk ba mafita bane mafitar kenan ki zabi daya a cikin su dolen su ne su kyale ki tun da ba dukan su zaki hada ki aura ba miji daya a ka sani mace na aura a al’adance haka a addinance”.

Wani murmushi mai ciwo ta saki.

“Bana tunanin zan iya daukar daya daga cikin su…nifa Umma na dawo daga rakiyar su a rayuwa ta ba zan sake kokarin faɗawa matsalar rayuwa A DALILIN ƊA NAMIJI ba an yi na farko ba za a sake yin na biyu ba na gwanmace in zauna haka ba aure har na karashe rayuwa ta…”.

“Ya isa haka Mariya nace miki ya isa haka abin naki yana neman zama rashin hankali kuma kina nuna nufin don wannan abin ya faru dake shikenan kuma kin yanke rahama a rayuwarki kenan butulci zaki yi wa Allah to tun wuri ki san abin yi domin ba zan lamunci wannan shirman naki ba”.

Tana gama fadin haka ta koma ta kwanta hakan ba karamin tashin hankali ya saka Mariya ba duban Umma take yi da mamaki zuciyarta sai faman bugawa take yi sosai take jin wani iri maganganun Umma sai tsananta sauti suke yi a cikin kanta runtse idanu tayi tana daura

hannayenta saman kirji tana jin yarda yake bugawa cikin wani irin yanayi sake buɗe idanu tayi ta kalli Umma wacce tayi shiru ta san ba barci take yi  ba sosai ta lura ranta ya dan sosu kin amincewa da tayi da maganar ta gyaɗa kai tayi kafun ta zabga tagumi hannun bibbiyu.

******

Tunda Baseera ta shigo take kallonta da wani irin yanayi na tausayawa ganin yarda Mariya ta fige ta kanjame kamar wata mai amai da gudawa ko da yake irin wannan bala’in da take ciki komai ma zata iya zama

numfashi ta ja tana zama bakin katifar da Mariya take zaune tayi mata kuri da idanu sai faman yake take yi wanda sam bai mata kyau ba.

“Kin gama fushin da ni kenan kin ga dama kin zo”.

Cewar Mariya tana hararar Baseera da jikinta ya gama yin sanyi da Al’amarin Mariya sai faman gyaɗa kai take yi zuciyarta na tsananta bugu kafun tayi kokarin kirkiro yaƙe ita ma ta yi mata.

“Ban san me yasa har yanzu Baseera ki ka kasa daidai ta komai ba dama fa a hannun ki take amma kin kasa amfani da ita duk wannan abun dake faruwa ke ce kike da mafita amma kin ki amfani da ita ban san me yasa ba?”.

Ta karashe tana janyo hannun Mariya ta damke a nata nan da nan sai ga hawaye a idanuwansu su duka

numfashi suke saki a hankali Mariya sosai take jin wani iri a zuciyarta ana cewa tana da mafita a hannu amma ita ta ka sa gane a ina mafitar take a gareta komai ta kasa tunani akan sa kwanyarta a tsaye take cak! tana babbakewa bata da wani kuzari ko jarumtar yin wani tunani.

“ki yi kokari don Allah ki samarwa kanki farin ciki da kwanciyar hankali har da muma mu sa mu don Allah”.

Baki ta shiga motsawa tana kokarin yin magana amma ta kasa sai da ta runtse idanu kafin ta buɗe su da ƙyar ta daga laɓɓanta.

“Ban san me zan yi ba Mariya sosai na kasa yin komai bana so wani abu ya sake hadani da su Umma tace wai zabi na gareni har da mafita kamar yarda ke ma kika ce amma na kasa tuna haka bana tunanin haka zai yuwu”.

“Mariya ke ki da wannan damar sai dai kin kasa amfani da ita ya kama ta ace kin fidda daya daga cikin su ina tunanin haka shi ne kawai mafita a garek…”.

Da sauri ta fizge hannunta tana ja da baya kamar wacce aka doɗanawa garwashin wuta duban Baseera take yi cikin wani irin yanayi idanuwanta sun kara kaɗawa sun yi jajir sai faman hirji take yi tana jan numfashi yana kokarin kwace mata kai ta ke girgizawa a hankali tana mai runtse idanunta kafun ta kai hannunta daidai kirjinta ta dafe da karfin tsiya.

“Ba zan iya ba Baseera bana son su na tsane su”.

“Zaki iya Mariya za ki iya ki na son su baki tsane su ba ni na san haka daurewa zaki yi don Allah”.

Bude idanunta tayi da sauri tana duban Baseera kafun lokaci guda ta kifa kanta kan katifar tana faman nishi dakyar kamar wacce aka shake a makoshi…Abu kamar wasa Mariya zuciyarta da kwanyarta sai kuwwa suke mata mai sauti akan batutuwan Umma da Baseera sosai take jin lamarin ya fara samun karbuwa a gareta zuciyarta na ta kokarin bata dama tayi abin da suke bukata amma ta rasa ta yarda+

zata fara domin kuwa wani bangare na zuciyarta sai safa da marwa yake yi wajan yanke hukunci kan lamarin.

Numfashi ta ja kafun tayi shiru tana mai tallaɓe haɓarta kamar daga sama ta jiyo kuwwa daga waje da ihu shiru tayi tana sauraron kafun daga bisa ni tayi hanyar fita tsakar gidan Umma ta hango tsaye tana kallon ikon Allah

Goggo Marka ce ta turmushe Hafsat sai faman jibga take yi kamar ta samu jaka daga ita sai dan fatari a kugu zanin ya fadi Mariya da take kallon ikon Allah bata san lokacin da dariya ta kusan kufce mata ba duban Umma tayi cikin yanayi na mamaki abin da tunda take a rayuwarta bata taba gani ba shine yau yake faruwa tabbas in da sauran numfashin ka a duniya kana DA SAURAN KALLO.

“Umma me ke faruwa ne hak…?”.

Da sauri Umma ta daga mata hannu ba tare da tayi mata magana ba idanuwanta na kan Goggo Marka da ta zage sai jibgar Hafsat take yi kamar Allah ya aikota sai faman numfashi take ita kuwa Hafsat sai zunduma ihu take yi tana kokarin kwace kanta.

“Umma zata kashe fa bai kama ta ki bar ta tai ta dukan ta b…”.

Sake daga mata hannu tayi a karo na biyu ta juyo ta dube ta fuskar ta da yanayin bacin rai sosai da sosai kafun ta hadiye wani yawu mai tauri mai nuna a wuya take.

“Yo meye na ki a ciki ta kashe ta mana wa tayi wa jikarta ce komai tayi mata wallahi ko a jikina”.

Nan da nan Mariya tayi rau-rau da idanu tana duban Umma jin abin da tace.

“Haba mana Umma mai yasa zaki ce haka? kina kallo fa irin dukan da take yi mata bai kamata ba…”.

“A wajan ki ne kike ganin bai kamata ba Mariya..tun dazu nake jin haniyar su ina zaune a nan daga cikin dakin su ban tanka ba sai da naji Goggo na zunduma mata zagi kamar wata wacce ta kirkiri maguzanci shine fa na tashi domin bata hakuri in laifi Hafsat tayi mata amma sai ta hada dani tana tsine min har da iyayena take anbata har tana cewa in har ni ba shegiya bace na fice na ba su waje”.

Umma ta karashe tana dauke hawayen fuskarta da suke ta faman zuba kafun ta sake nisawa cike da bacin rai.

“ko ni shegiya ce wallahi dole in bar su in dai ina da zuciya balle kuma uwa da uba akwai su ban hanaki ba zaki iya zuwa ki cece ta domin ‘yar uwarki ce ta jini amma ni kam wallahi a,a haram shan giya gidan liman”.

Ta karashe tana karasawa wajan da take wankin kayanta ta cigaba da yi sai faman ajiyar zuciya take da wani irin yanayi na takaici zagin da Goggo tayi mata tun da take a rayuwarta ko kwatankwacinsa ba a taba yi mata ba.

Jikin Mariya yayi sanyi sosai tausayin Hafsat take sannan kuma

maganganun da Umma ta faɗa mata suna ci mata zuciya sosai taji ranta ya baci tun da taga Umma na hawaye ta tabbata yau an kaita bango numfashi ta ja mai tattare da bacin rai kafun ta dubi Umma wacce take faman dirza kayan wankin  kallo daya zakayi mata ka gane sauke haushinta take a jikin kayan da saurin Mariya ta isa gareta ta riko hannunta dago idanuwanta tayi wanda sukayi face-face da

hawaye sun kaɗa sun yi jajir sosai hannu ta saka ta na goge mata su.

“Haba Umma me yasa kike zubda hawayenki akan Goggo ya kamata ki saba ba yau bane ta saba yi miki haka…”.

STORY CONTINUES BELOW

“Na san ba yau bane amma abin da tayi mani yau na tabbata zai ji ma a zuciyata  bai gogu ba duk abin da take yi mani ina hakuri amma yau HAKURINA ya kare ta kai ni bango amma ba komai Allah na nan ai zai yi mani sakayya”.

Ta karashe tana rike hannun Mariya da take goge mata hawaye da su juyawa sukayi su duka suna kallon Goggo Marka wacce ta dago a wannan lokacin tana faman sakin numfashi kamar wacce tayi gudun faffalaki.

“Ni zaki tozarta ni zaki ciwa mutunci ni zaki kwancewa zani a kasuwa to wallahi ba ki isa ba kin yi kadan a yau din nan sai kin koma wajan uwarki ba za ki ja min abin kunya ba a gidan nan haka kawai ina zaman zama na zaki dauko mani ALAƘAƘAI ba garai babu dalili ban san hawa ba kawai sai naji sauka ai da sake wallahi ba a gidan nan ba”.

Abin da Goggo Marka ta shiga fadi kenan tana faman haki kamar wacce Numfashinta ke gardama sai faman nuna Hafsat take yi wacce ke kwance idanuwanta sun kada sunyi jajir sai zubda ruwan hawaye suke yi tana faman nishi domin ta daku iya dakuwa.

Duka ta sake kai mata cikin rashin tsammani ta doke mata baki lokaci guda ya fara zubda jini kafun ta shureta da kafa ta wuce bayan ta tsintsine mata tayi hanyar dakinta sai faman zage-zage take yi.

Su dai su Umma kasake sukayi gabadaya ta rikita su sun rasa mai Hafsat tayi mata har haka ta duke ta duka mai ansa sun duka haka ko barawo akayi wa wannan dukan sai ya san ya daku a hankali Mariya ta kalli Umma tana faman gyada kai kallon ta Umma tayi ta kau da kai don ta san abin da take nufi a  hankali Mariya ta ja jiki zuwa in da Hafsat take bakinta sai zubda jini yake yi idanuwanta na zubda hawaye

kallonta tayi kafun ta kau da kai jin zuciyar na tunano mata da kiyayyar da Hafsat ke mata tana jin wani iri da bacin rai amma haka ta daure kawai ta dago ta tana mai zare mata dankwalin kanta tana goge mata fuska da jinin dake zuba a jikinta.

“Sannu ko Hafsat me kika yi wa Goggo haka har take dukan ki abin da bai taba faruwa ba?”.

Ta tambaye ta tana mikar da ita kan kafafuwanta ita kuma sai faman cizon laɓɓa take yi saboda tsananin ciwo da jikinta ya kama yi lokaci guda.

“Uban ki tayi min hegiya tsohuwar munafuka in baki sake ta kin bar wajan nan ba in na zo wallahi sai na hada dake”.

Kamar daga sama suka tsinkayo muryar Goggo Marka na fadin haka da sauri Mariya ta ja baya tana mazurai.

“Shaggu na kurya masu gansa kuka a idanu ina ruwan ki da ita kinibabba me ya shafe ki da abin da tayi min in ban da kuturun kinibibi irin na ruwarki shine zaki zo kina tambayar ta”.

Da hanzari ta ja jiki ta bar wajan tana kallon yarda Goggo Marka ke faman watsa mata banzan kallo kafun ta juya wajan Hafsat dake tsaye kikam.

“ke kuma zo ki shige tun kafun nazo wajan nan na karya miki shaggun kafafuwan nan naki bakar munafuka kawai”.

Kikam tayi ko motsi ba tayi ba sai faman zunburo baki take yi gaba wanda ya fara tasawa.

“dake fa nake ko ki zo ki shige ko kuma ki fice daga cikin gidan nan”.

A hankali ta fara dingisa kafar da tayi mata tsami sosai ta tunkari dakin tana zuwa Goggo Marka ta dungure mata kai tare da hankaɗa ta cikin daki kafun ta juyo ta dubi su Umma tana jan katon zaki.

“Tsofaffin munafukai kawai ta Allah ba taku ba”.

Murmushin takaici Umma ta saki kafun ta ja hannun Mariya su shiga cikin dakin su rai a matukar bace.

STORY CONTINUES BELOW

*****

Tafe take kanta a kasa kamar wata maras gaskiya Hijab din ma sakko dashi tayi zuwa fuskarta yarda ba kowa yake gane waye ba hannunta rike da ledar kayan cefanar Cake a hankali take tafiya kamar wacce bata son taba kasa.

Kamar daga sama taji yo Horn din mota da sauri ta dago kai kafun ta shiga ja da baya duk a tunanin ta kan hanya take ake mata horn amma sai ta ga akasin haka motar a tsaye take gefe guda amma sai danna horn ake yi haka da ta gani ya sanyata tunanin ba da ita ake ba da saurin ta shiga waige-waige don ganin da wanda ake amma ba kowa a hanyar sai tsirarun mutane kuma kowa harkar gabansa yake yi koman da kanta kasa tayi ta cigaba da tafiya amma gabanta sai dokawa yake yi domin tunaninta ya bata da ita ake yi hakan ya sanyata kara saurin

tafiyar da take yi daidai kwanar da zata shigar da ita kofar gidan su ta ga Motar ta shawo gabanta da gudu cikin tsananin firgici tayi gefe tare da sakin kara mai sautin kayan hannunta duk suka zube kasa don duk a tunanin ta markaɗe ta motar za tayi amma sai taga akasin haka buɗe idanuwanta tayi da suke runtse ta sauke akan motar ganin ana kokarin buɗewa gabanta ne ya yanke ya fadi ganin waye a cikin motar yake kokarin fitowa haɗe fuska ta kare yi ta

durkasa kasa tana hada kayanta gabanta sai dokawa yake yi da wani irin yanayi gabadaya jikinta bari yake yi lokaci guda idanuwanta suka kada sukayi jajir duk ta rikice kayan nata ta kasa hada su hannunta karkarwa yake yi kawai.

Daddaɗar kamshin turare ne ya daki hancinta lokaci guda ta ja numfashi mai tsayi gami da runtse idanuwa sosai taji a jikinta kallonta yake yi a hankali taji ana ansar ledar dake hannunta cikin rashin kuzari ta saki ledar ba tare da wata gardama ba a hankali ya shiga tattare kayan ya ajje su gefe idanuwansa gabadaya ya sauke akanta yana kare mata kallo kafun lokaci guda ya ja numfashi mai tsayi zuciyarsa na mika shi wani mataki na daban mai cike da abubuwa muhimmai akan Mariya.

Mika hannu yayi kamar zai kamo nata hannun da sauri ta mike tana ja da baya idanuwanta cikin nashi suka sarke gabanta ya cigaba da bugawa a wani mataki wanda yake rikita mata tunanin gabadaya ta rikice sai faman rawar jiki take yi zuciyarta taji tana mikata wani sashi na daban mai kokarin canza mata duk wani

tunaninta memorinta taji yana kokarin goge haddar da tayi runtse idanu tayi jin wani abu mai kama da kibiya mai tsanin haske ya kufto daga fuskar Dr.Karami mai tattare da lallausar murmushi ta tunkarota kafun lokaci guda ta buɗe idanun nata haske ya mamaye fuskarta wani numfashi ta ja mai karfi kamar zata shiɗe.

“Ban san me zan ce miki ba Mariya amma ki sani zuciyata tana matakin da take kokarin tarwatsewa da son ki na azabtu na wahalu lokaci mai tsayi wanda nayi tsammanin rayuwata ta kare ke nan duk a kan ki son ki

Mariya sosai zuciyata ta kasa sarrafa kanta a dalilin sonki komai…komai nawa ya canza sosai da sosai duk dalilinki ki dube ni Mariya ni mai son ki ne so na hakika ki daure don Allah karki baiwa zuciyata kunya”.

Wani irin dokawa zuciyarta tayi wanda har sautin ita kanta sai da ta ji ya bayyana idanuwanta a rufe jin ta take yi zuciyarta na mikata wani mataki da bata tajin taje ba sosai taji kamar kan gajimare take yawo

maganganun Dr.Karami suka shiga sauti a cikin kwanyarta mai kara zuciyarta da ruhinta taji suna buɗewa da wani irin yanayi suna ansar sakon Dr.Ƙarami gabadaya taji komai nata kamar sabo komai ya goge sabbin abubuwa taji suna shigarta ta ko ina sake damke idanuwanta tayi kafun ta bude su ta sauke akan sa wani irin kwarjini da haifa take hangowa saman fuskarsa suna kara narkar mata da zuciya cikin wani mataki wanda ba zata iya sarrafa kanta ba.

Durkusawa tayi ta kamo hannayen ledan kayanta ta mike sosai kan kafafuwanta da taji suna lauyewa suna kokarin zubda ita kasa kokarin motsawa tayi tana ɗaga kafar guda daya da taji tayi mata nauyi sosai runtse idanu ta sake yi kafun ta tura laɓɓanta duka cikin baki a hankali ta shiga takawa idanuwanta na kara lumshewa gabadaya garin taga yana juya mata ji take yi kamar ba ita ba gani take yi kamar wata MARIYA ce ba ita ba tana ji yana kiran sunanta muryarsa na dakar mata zuciya da

kwanya suna kara rikitata amma ta kasa katabus tafiya kawai take yi bugun zuciyarta na kara tsananta sosai a cikin wannan yanayin taji ta cikin soron gidan su lokacin guda ta karasa shiga ta zube tana mai jan wani numfashi mai tsayi dumin hawayen da suka zubo mata ya sanyata buɗe idanu a razane duk a tunanin ta ya biyo ta amma sai ta ga akasin haka bata goge hawayen ba illa wani  kuka ta taji ya zo mata tun daga zuciya da ruhi da gangar jiki kukan take yi mara sauti sai faman shassheka take yi kamar wacce numfashin ta zai dauke…Cikin kwana biyun da tayi bayan haduwarta da Dr.Karami gabadaya ta gama rikiciwa ta rasa mai ke yi mata dadi a rayuwarta zuciyarta sai faman zillo take akan lamarin sa ta rasa ma me za tayi.+

A hankali take kokarin saita kanta da samo mafitan da take ganin ya dace da ita sosai take hana idanuwanta barci tana kai kukan ta wajan Allah domin ya zaba mata abin da yafi zama alheri a rayuwarta baki daya.

Sosai zuciyarta ke matsewa sosai take jin nauyin da zuciyarta ke yi yana raguwa a hankali sosai take jin ya kamata ace izuwa wannan lokaci ta sarara wa kanta da rayuwarta sosai take jin lokaci yayi da ya kamata ta kawo karshen komai.

Amma ta yaya hakan zai kasance ta yaya hakan zai yuwu ba ta san ya za tayi ba sosai zuciyarta ta karkata zuwa ga Dr.Karami yawancin barci in tana yin sa duk shi take hangowa amma bata jin za ta iya aurensa.

Amma kuma bata san dalili ba in maganar aure tafi karkata ga Dr.Aqeel tana son Dr.Karami shima Dr.Aqeel tana jin son sa sosai a ranta ba kadan ba sai dai fili mai yawa Dr.Karami ya mamaye mata.

Haka rayuwarta tayi ta tafiya har tsayin wata daya amma har lokacin bata yanke hukunci ba ta rasa wanda zata tunkaro ta fada masa halin da take ciki domin samun mafita tana tsoron sanar da Umma domin yanzu duk ta ja baya ta bata dama ita akaran kanta tayi abin da ya dace Baseera kuma har zuwa wannan lokaci taki yarda su hadu domin bata son ta zo mata da wani lamarin na daban bata so ta zaba mata abin da ba shi zuciyarta take so ba.

Haka dai ta cigaba da dakon wannan lamarin har da karshe ta yanke zuwa gidan su Baseera domin ita kadai ce k’awa shakikiya da take ganin ya dace ta san matsalar kuma ta bata shawarar da take ganin ya dace.

Sanye take cikin daguwar riga mai kalar baki da ratsin ja kadan ta sanya jan gyale tayi rolling din shi a kanta sosai ya fito mata da kyanta duk da ba wata kwalliya ba ce ta a zo agani tayi amma tayi matukar kyau takalmi flat ta saka a kafarta sannan ta fito tsakar gida ta tadda Umma zaune ita da Mu’azzam duban su tayi su duka kafun tayi murmushi wanda iyakarsa fuska tausayin kanta da na Umma hadi da na kaninta kawai take ji tunowa da tayi da mahaifinta ko yana ina a halin yanzu Allah masani.

Numfashi ta ja mai tsayi har sai da Umma ta jiyo sautin sa juyowa tayi ta dube ta sosai.

“Lafiyarki kalau kike wannan doguwar ajiyar zuciyar?”.

Ta fadi tana kara duban jikinta.

Gyaɗa kai tayi tana sake kokarin kakalo murmushi duk da kwallar da ke kawo mata farmaki a idanu.

“Ba komai kawai dai…Uhmm yawwa Umma zani gidan su Baseera”.

Kallon tuhuma Umma ta shiga yi mata na dan lokaci kafun ta gyaɗa kai.

“Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutan gidan amma karki dade fa kin ga yamma ta fara yi”.

Ansawa tayi da ‘to’ sannan ta dubi Mu’azzam da yayi kuri yana dubanta dakune masa fuska tayi cikin tsokana.

“Yah Mariya zan biki”.

Ya fadi cikin sanyin murya zaro idanu tayi waje.

“Ni zaka bi caɓ! gaskiya a,a ba zan iya jigilar zuwa da kai ba ban son kaje gidan mutane kana yi musu rashin ji ka bar ni da jin kunya”.

Ta fadi tana mai kama hanyar ficewa rau-rau yayi da idanu kamar zai yi kuka amma Umma ta hana shi ta shiga rarrashin sa.

STORY CONTINUES BELOW

Hafsat ce ta fito daga cikin daki fuskarta dauke da rashin walwala sai faman ya tsine fuska take yi kallo daya zakayi mata ka gane ramar da tayi ta ɗashe tayi fari sosai ga idanu duk sun zurma tayi firgai-firgai da ita.

Mariya dake koƙari ficewa ganin Hafsat ta fito ya sanyata tsayawa tana dubanta kafun ta dubi Umma cikin yanayi na tausayawa a hankali ta shiga motsa laɓɓanta.

“Uhmm Hafsa ya jikin naki…”.

Wata harara da ta maka mata shi ya sanyata saurin tsuke bakinta tana kau da kai zuciyarta take ji tana wani iri tuni ta fahimta har zuwa wannan lokacin ba abin da ya canza a Hafsat duk rashin lafiyar da take fama da ita kamar zata mutu amma bai sanya komai ya canza ba duban Umma tayi itama Umma ita take kallo mai cike da ‘Allah ya kara’ ta maka mata harara da sauri ta ja jiki zuciyarta na kunci.

“Munafukar banza sau nawa zance miki ki daina shiga lamarina ina ruwanki da rashin lafiya ta”.

Furucin Hafsat kenan ta fadi da kyar kamar wacce akayi wa dole Mariya bata bi ta kanta ba illa karasa fita daga gidan cikin sauri da tayi.

*****

A hankali take tafiya zuciyarta ta mika ta can wani waje na daban kawai tafiya take ba tare da ta kula da inda take jefa kafa ba cikin wannan yanayin har ta isa bakin titi ta tsayar da mai Napep tana kokarin shiga wata bakar mota kirar 406 ta zo gilmawa ta gabanta kamar ance ta dago kai ta dubi motar wani irin faduwar gaba taji ya ziyarce ta da sauri ta runtse ido ta bude lokaci guda.

Shi din ne ba wani ba har ta mance yaushe rabon da ta ganni a idanuwanta tun lokacin da suka kusan kashe ta sai kuma ranar da ya zo wajan Hafsat abin yayi matukar bata mamaki yarda Huzaif ya kasance mai FUSKA BIYU a gareta yana bibiyarta yana ikirarin yana sonta sannan kuma yana son ‘yar uwarta sosai taji lokaci guda ya fice mata a rai wani haushi da takaicin sa ya tsirga mata a rai domin ganin rainin wayo yake musu a tsakaninsu ya mai da su kamar wasu ball ya buga wannan ya buga wannan. ‘Mtss.

Ta ja dogon tsaki dago kai tayi ta dubi mai Napep wanda shima ita yake kallo haushi ya sake turnuke ta ganin irin kallon da yake yi mata kamar ya ga wata bakuwar halitta.

“Tafi abin ka na fasa”.

Ta fadi cikin haushi da takaici a rayuwarta ta ki jinin kallo shi kuwa kamar wani maye gabadaya ya juyo yana dubanta a hankali ta fara takawa tana barin wajan tana ji yana kiranta amma ko ta kansa ba ta sake bi ba.

Da sauri ta tari wani Napep din ta dane tana hango waccan sai faman dubanta yake yi har suka zo suka giftashi suna hada idanu ta galla masa harara gami da jan tsaki.

Tafiya sukayi sosai daidai wajan wani Mall ta hango motar Huzaif anyi Parking dinta daga dan gefe ta hango shi shida wata mace ya rike mata hannu sun tunkari cikin wajan zaro idanu waje tayi zuciyarta na harbawa da sauri-sauri kamar zata fallo daga cikin zuciyarta rintse idanu tayi zuciyarta na matsewa da wani irin bakin ciki tana tattama akan Huzaif anya kuwa son da yace yana yi mata na gaskiya ne an ya son gaske yake yi mata?.

Girgiza kai ta shiga yi da sauri-sauri zuciyarta na mikata can baya lokacin da suka fara haduwa da yanayin da ya nuna mata ta tabbataa akwai alamar tambaya akansa bata san abin da ya shigar mata kai ba har ta yarda dashi bata san me yasa har ta saki da Huzaif ba sosai take ganin wautarta sai yanzu ta hango kuskuren da tayi har ta bashi fili a zuciyarta yake abin da ya ga dama aciki.

bata san sun wuce wajan ba sai da suka kai daidai wata hawa taji anyi sama da ita sannan tayi firgigin ta dawo hayyacinta ta shiga ware idanu gani tayi har sun shigo layin su Baseera wata irin ajiyar zuciya tayi mai karfi kafun ta runtse idanunta da wani irin yanayi a zuciyarta ta sanar da mai Napep daidai in da zai sauke ta.

STORY CONTINUES BELOW

Tana sauka ta bashi kudin sa ta dauki hanya domin karasawa gidan a bakin Get ta tsaya ta kwankwasa mai gadi ne ya leko ganin wacece ya saki murmushi ita ma murmushi tayi masa tana gaishe shi ya buɗe mata ta shiga a hankali take tafiya tana tunkarar kofar da zata shigar da ita cikin babbar falon haka kawai taji zuciyarta na kunci tana kuma bugawa cikin sauri-sauri a haka har ta isa

bakin kofar ta rike Handle din haka kawai ta ji wata kasala da gajiya ta saukar mata sakin Handle din tayi ta dan ja baya tana ajjiyar numfashi tana mai lumshe idanu kamar mai jin barci a hankali ta sake kamawa idanuwarta a rufe ta tura gami da yin sallama muryar Mami da taji ta ansata ya sanya shiga ciki.

Zaune suke ita da Tareeq ya mike sosai kan kujera waya a hannunsa sai faman latsata yake yi Mami da ta ganta ta saki Murmushi kamar ko yaushi da sauri ta isa gareta ta durkusa ta na gaishe ta ansawa tayi kafun ta dube ta sosai.

“Ya jikin naki Mariya da fatan dai komai Normal ba abin da ke damun ki kuma?”.

Gyaɗa kai tayi ganin Tareeq ya juyo da sauri yana dubanta suna hada idanu tayi kasa da kai shi kuwa har zuwa lokacin idanuwansa na kanta ajikinta take jin haka ana kallonta wani tunani ne ya fado mata kar Mami tace bata kyauta mata ba dago kai tayi a hankali ta dube shi.

“Ina yini Yah Tareeq”.

Ta furta murya can kasar makoshi tana rawa bai ansa ta ba illah duban sosai da ya sake yi mata jin da yayi ance bata da lafiya kafun ya numfasa ya ansata ba yabo ba fallasa tare da yi mata ya jiki.

Haka kawai taji wani iri yanayin da ya ansa mata cikin izza da nuna rashin baiwa gaisuwar tata muhimmanci ji tayi zuciyarta wani iri duban Umma tayi tana faman yake.

“Umma Baseera na ciki kuwa?”.

“Eh tana ciki yanzun nan ta tashi daga nan wai barci zata yi”.

Murmushi Mariya tayi tana mikewa kan kafafuwanta duk sai taji wani iri ganin yarda yake kallonta gabadaya taji kafafuwanta suna harɗewa kamar zata zube a kasa sauri ta kara don kar tayi abin kunya agaban wanda bai san ya kula mutane ba in an kula shi  mtss ta ja tsaki ta dane sama abin ta har ta kai matakin sauka sannan ta juyawa da kanta kasa aiko sai idanuwansu suka sarke zaro idanu tayi sosai ganin har zuwa wannan lokacin yana kallon ta wani murmushi taga yayi na gefe kumatu tare da lumshe idanu da sauri ta kau da kai tana jin zuciyarta na bugawa cikin hanzari ta bar wajan.

Tana isa kofar dakin Baseera ta tsaya cak! tana mai da numfashi me Tareeq yake nufi da ita mai yasa yake yi mata haka me hakan ke nufi wannan kallon na meye yake yi mata ta lura dashi in dai ta zo gidan nan ta same shi gaban Umma ya dinga sha mata kamshi kenan amma in bata nan sai ya dinga jifanta da wani kallo dake faɗar mata da gaba ta rasa me yasa haka.

‘me ya shafe ki dashi’

zuciyarta ta fadi mata da sauri ta daga kafunta alamun ‘babu’ ta tura dakin ta shiga ruf! ciki ta same ta waya a hannunta sai faman danne-danne take a waya da sauri ta karasa ba tare da Baseerar ta sani ba ta zaune gefenta  tare da sanya dan yatsar ta daya ta ta sosa mata tsakiyar tafin kafarta  wata irin razana da ihu Baseera tayi tana mai komawa can gefe ta cillar da wayar saman gado idanuwa a warwaje jikinta sai k’yarma yake yi Mariya ta kwashe da dariya kafun ta ce.

“Ke banza ni ce fa matsoraciya kawai”.

Wata uwar harara Baseera ta cilla mata kafun ta ja wani numfashi mai nuna alamun ta firgita sosai.

“Allah ya isa wallahi ke kam an yi muguwa ai wannan sai kiyi ajalin mutum da tsoratarwa wallahi”.

Ta fadi tana mai sankowa daga gadon tana isowa gareta ta zauna kallon sosai tayi mata kafun tayi murmushi.

“Baby din nan fa kyau kike karawa wallahi kamar wata sabuwar amarya meye sirrin ne ko dai…”.

Sai kuma tayi shiru tana kyalkyalar dariya dubanta Mariya tayi cikin muryar mai rauni.

“Magana na zo muyi don Allah Baseera ki bani shawara”.

Sosai Baseera ta shiga dubanta ganin yarda fuskarta ta nuna alamun damuwa gyaɗa kai ta shiga yi tana kokarin yin magana suka ji an turo kofa gabadayan su suka juya suka Fuskanci kofar Mariya ce ta zaro idanu kafun ta kau da kanta gefe.

“Yah Tareeq”.

Cewar Baseera tana duban sa murmushi ya saki yana duban Mariya kafun ya dubi Baseera ya kashe mata ido daya dakune fuska tayi tana mai girgiza kai ba tare da ta bari Mariya ta ganta ba.Sosai taji a jikinta kamar akwai abin da ke faruwa don haka ta dubi Baseera da taji ita ma tayi shiru tunda ta kira sunan Yah Tareeq dubanta tashiga yi ganin abin da take yi da idanu tana dakune fuska kamar wacce aka tursasa sai tayi abu ba tare da ta so ba.+

  Haka kawai taji gabanta yana faɗuwa dago kanta tayi gabadaya ta sauke wajan Tareeq wanda yake ta faman biyawa Baseera karatu ta hanyar idanu da hannu ganin Mariya ta dago kai da sauri ya wayance yana faman cin magani.

“wai shin me ya faru ne naji ihun ki?”.

Ya fadi yana duban Baseera da tayi tsiru-tsiru gabanta na dokawa tsoronta daya kar Mariya ta gano abin da suke yi a tsakanin su akan ta ne susa keya tashiga yi kamar maras gaskiya tana faman yak’e.

  “Bakomai Yah Tareeq”.

Ta fadi tana mai duban Mariya wacce ta komar da kanta kasa tana nazarin yanayinsu tabbas akwai wani abu a boye a tsakaninsu wanda zuciyarta ta tabbatar mata akan ta suke komai haka kawai ta sha jinin jikinta.

“Uhmm Yah Tareeq..”.

Da sauri ya juya har yana kokarin tuntube wajan fita nuni da Baseera tayi masa kamar Mariya ta gano su shi kuma abin da bai kauna kenan sam! Mariya ta gano halin da yake ciki a kanta.

Son ta yake yi amma ya rasa yarda zai yi ya fuskance ta ba yarda bai yi da Baseera tayi masa kamfe ba amma ta kekeshe kasa ta ki yarda ba abin da bata fada masa ba akan halin da Mariya take ciki amma ya ki amincewa giyar soyayya sai kwasar sa take yi amma ya kasa zuwa ya tunkari Mariyar.

  Wani murmushi Baseera ta saki lokacin da ta hango Tareeq na kokarin bugar bango da sauri ta kalle shi shima kallon ta yayi yana dakune fuskarsa sannan ya fice daga cikin dakin..

“Mariya wai shin me ke faru ne naga duk jikin ki yayi sanyi haka”.

Baseera ta katse shirun da yayi wa dakin ado.

A hankali Mariya ta dago da kanta ta dubi Baseera cikin yanayi na tuhuma sai da ta sha jinin jikin ta ganin irin kallon da Mariya take yi mata.

Murmushi Mariya ta saki na yak’e kafun ta nutsu fuskarta na komawa yarda take a shigowarta alamun damuwa.

“Sosai na kasa fahimtar komai, ban san ya zan fuskanci wannan lamarin ba”.

Ta fadi tana mai tura laɓɓanta cikin bakinta fuskarta na kara bayyanar da tsantsanr damuwar da take ciki zuciyarta take ji tana kara matsewa da wani irin yanayi mai girman gaske haka kawai taji tana shakka akan ta fadiwa Baseera halin da take ciki a wannan lokacin.

Numfashi taja mai tsayi kafun ta mike tsaye tana kai kawo cikin dakin na dan lokaci sannan ta tsaya cak! Ta juyo ta dubi Baseera da tayi shiru tana sauraron zuciyarta itama na ta fadan tsalle-tsalle da fargaban abin da take son kawowa Mariya din so take yi kawai fatanta ya tabbata Allah yasa maganar da Mariyar zata yi ya zo daidai da gaɓar da take so zata yi amfani da wannan damar domin samun abin da take bukata duk da zuciyarta na ta faman gargaɗinta ita akaran kanta jin wani iri take yi kan lamarin amma bata san ya za tayi ba.

Mikewa tayi ita ma Baseera tana takawa zuwa inda Mariya take tsaye jikinta na kara karyewa sosai zuciyarta na bugawa cikin wani mataki na rashin tsammani.

Dafa kafadar ta tayi tana mai ajiyar zuciya.

“Ban fahimce ki ba mai ke faruwa ne?”.

STORY CONTINUES BELOW

Cewar Baseera cikin rashin abin cewa domin gabadaya ta shiga RUƊANI kawai jarumta ce take kokarin sanyawa kanta amma zuciyarta kamar zata faso tayo waje don fargaba.

“So nake yi ki bani shawara Baseera na gaji da wannan Bala’in gwanda na san abin yi tun kafin zuciyata ta buga na mace a banza a wofi”.

Zaro idanu tayi sosai jin abin da take cewa da sauri ta kamo hannunta ta saka cikin nata tana dankewa da wani irin yanayi.

“A,a Mariya ki daina fadin haka wannan ba magana bace sam! komai da kika ga ya na faru dake ALKALAMIN ƘADDARAR ki ne a haka ki dauki komai a matsayin JARRABI a rayuwarki kar kiyi gangawar yanke hukunci ki bi komai a sannu karki ji zuciya ta kwashe ki ki zo kina dana sani”.

Runtse idanu Mariya tayi tana jin zuciyarta na kara ya mutsewa da wani irin mataki tana mikata wani waje na daban buɗe idanunta tayi sosai kan Baseera wanda suka fara kaɗawa.

“Hmm Baseera kenan kin fi kowa sanin halin da nake ciki kin fi kowa sanin Bala’o’in da na shiga dole na nemi mafita tun wuri”.

“Nasan da haka Mariya amma ki saurara ki yi tunani kafin ki yanke hukunci”.

Sosai take dubanta karo na ba a dadi kallo ne wanda ya sanya Baseera shan jinin jikinta gani take yi kamar Mariya tuhumarta take bisa yanayin da ta lura yak’e ta shiga yi kafun Mariya ta kau da kai daga kallon da take mata ta ja wani numfashi mai tsayi tana tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa.

“Wa ya dace na zaɓa a cikin su wa kike ganin shine INGANTACCE wanda ya dace da rayuwata?”.

  ‘An zo wajan’.

Zuciyar Baseera ta fadi tana wani irin dogawa sosai zaka gane firgici a fuskarta idanuwanta a warwaje ta shiga motsa baki tana son yin magana amma ta rasa ta ina zata fara a hankali ta ja hannun Mariya suka koma bakin gadon suka zauna dukkaninsu sai faman ajiyar numfashi suke kamar wadanda suka yi aiki mai wahalar gaske suke zaman hutu.

“Kin fasa canza wani saurayin ne daga cikin UKU BALA’In naki?”.

Baseera ta fadi tana faman sakin murmushin yake gabanta sai dokawa yake so take yi ta dauko gaɓar da zata sanar da Mariya komai amma tana fargaba da tsoro akan abin da zai je ya dawo bata san ya Mariya zata dauki lamarin ba bata san ya zata kalle ta ba anya kuwa ba zata ce ta fiye SON ZUCIYA da son kanta ba? Gyaɗa kai tayi.

“Duk mu ajje wannan maganar gefe Baseera na hakura da komai wallahi na mikawa Allah lamarina hukuncin sa kawai naƙe bukata a duk yarda ya zo zan anshe shi”.

Jin abin da tace ya sanya Baseera dubanta sosai cikin sanya wa kai jarumta duk da dokawar da zuciyarta ke yi.

“Nikam nake ganin kamar ki canza zai fi miki lura da yanayin rigimar da kike ciki a yanzu in har kika zabi daya a cikin su kina ganin za a samu maslaha a tsakani kuwa… ko da yake hakan da kike gani shima ya dace tunda ba dukkansu zaki aura ba dole in kika zabi daya dole sauran su yi hakuri tun dake ba  MATAR MUTUM UKU bace matar mutum daya ce namiji ne MIJIN MACE HUDU ba ma daya ba”.

Tunda ta fara maganar take lura da ita sosai kamar akwai wani BOYAYYEN AL’AMARI da take boye mata haka kawai taji ba ta yarda da ita ba sosai take jin haka a jikinta.

“Uhmm shikenan tom…ko daya ke ke ma kin kawo shawara amma kuma yanzu in nace zan nemi wani daban me kike tsammanin zai faru?”.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi tayi sosai wanda iyakarsa laɓɓan bakinta.

“Mazan ne ai ba wuya suke ba sai dai kice nagartarsu ce za ta yi wuya baki san wanda zai zo gareki ba akwai masuyi don Allah akwai kuma masu zuwa da wata manufa ta daban…”.

Tayi shiru alamun maganar da take bata karasa ta ba numfashi ta ja kafun ta dubi Mariya tana kamo hannunta ta danke cikin nata.

“Mariya dama akwai maganar da nake so muyi dake don Allah amma ina so ki dube ni da idon basira kiyi mani kyankyawar fahimta don Allah ba a son raina zaki ji komai ba amma na rasa yarda zan yi ne”.

Gyaɗa kai Mariya ta shiga yi dama taji ajikinta akwai wani abu a boye.

“Yah Tareeq ya jimawa yana kawo min maganarki tun Time din da ya dawo daga School kuka hadu shikenan yake ta faman zarya yana cewa dani wai…”.

Gaban Mariya yankewa yayi ya fadi lokaci guda ta ji jikinta ya dau ƙyarma amma bata bari hakan yayi tasiri wajan bayyana ba illa murmushin da tayi kokarin daurawa a fuskarta tana karawa Baseera kwarin gwuiwar fadin abin da take son fadi din.

“Son ki yake yi Mariya amma ni dai…”.

Wata irin mikewa tayi gami da fizge hannunta idanuwanta a warwaje ta shiga duban Baseera da tayi mutuwar tsaye kallonta take yi cikin wani irin yanayi bata taba tsammanin maganar da zata yi mata ba kenan bata taba kawo hakan akan taba sosai taji wani iri sosai take jin ta wani mataki wanda ba ta san ya zata kwance kanta ba ‘So kuma Yah Tareeq din yake so na?’. ta shiga fadin haka a zuciyarta tana faman girgiza kai idanuwanta na kara rinewa zuwa ja bakin ta na rawa take duban Baseera wacce ita

gabadaya a rikice take dama ta san za ayi haka sosai ta san Mariya ba zata dauki wannan lamarin ba domin kuwa an shata ta warke ita kanta ba zata goyi bayan hakan ba duk da dai dan uwa ne kuma za ta so ace Yah Tareeq ya auri Mariya sosai take ganin dacewar haka amma ina! ba damar hakan.

A hankali ta shiga ja da baya ta girgiza kai cikin tsananin tashin hankali.

“Kiyi Hakuri Baseera don Allah ki yi hakuri ki fahimce ni zuciyata… zuciyata ba zata iya bada wani GURBIN SO ba ta rigaya ta gama so ta rigaya ta gama illatuwa AKAN SO ko nace miki zan sake so to nayi miki karya kiyi hakuri ba zan iya ba”.

Tana gama fadin haka tayi hanyar ficewa da sauri kanta take ji yana wani irin sarawa gabadaya taji duniyar na juya mata a haka har ta sauka Allah ya taimake ta ba kowa a falon cikin hanzari ta fice daga cikin gidan baki daya ta dauki hanya sai faman zancen zuci take yi kamar waya zararriya.

Ita kuwa Baseera hada kai tayi da gwuiwa tana jin yarda zuciyarta take zafi sosai bata so yin wannan maganar ba dama can abin da zai faruwa take guda bata son abin da zai bata kawancensu akan Yah Tareeq ba yarda bata yi dashi ba amma yaki yarda yanzu ya zama dole ta fada masa gaskiya duk da yana dan’uwanta ba za ta so abin da zai cutar da Mariya duk da itama tana kwadayin yayan nata ya auri Mariya amma lokaci ya kure ba damar yin haka din.

*****

Tafiya kawai take tana saka kafarta duk inda ta sauka ba ta tsaya neman abin hawa ba domin bata da wannan natsuwar Allah ya taimaketa har ta isa unguwarta.

Kallo daya zakayi mata ka gane bata cikin natsuwar sam! Cikin wannan yanayin ta iso layin su har zuwa wannan lokacin bata dawo hayyacin ta ba kamar daga sama taji ta bangaji abu mai girma hakan ya sanyata yin baya luuuu tana kokarin faduwa runtse idanu tayi sosai tana jiran jin ta a kasa amma sai akasin haka rikota taji anyi sosai an dagota wani irin Shock taji jikinta ya dauka ya mikawa kwanyarta da zuciyarta lokaci guda suka tsaya cak! da aiki.

A hankali ta shiga kokarin buɗe idanuwanta zuciyarta na dawowa hayyacinta tana bugawa fargabarta daya Allah yasa ba wani ta buge ba zai hukunta ta…

Bata gama tunanin ba ta ji gabanta ya yanke ya fadi lokacin da idanuwanta suka buɗe akan fuskarsa kallon shi ta shiga yi shima kallonta yake yi da tattausar murmushi a fuskarsa gabadaya taji ta a wani irin yanayi jikinta sai ansa wani bakon al’amari yake yi bata yi kokarin kwace kanta ba domin ji tayi gabobin ta gabadaya kamar sun daina aiki motsi ma ta kasa yi.

Runtse idanu tayi sannan ta buɗe izuwa lokacin ta fara gano komai dake faruwa da sauri ta kwace kanta daga gareshi tana ja da baya idanuwanta har zuwa lokacin ba su bar cikin nasa ba sai faman ajiyar numfashi take yi mai girman gaske.

Sosai ya fita shiga cikin yanayi mai girman gaske zuciyarsa yake ji tana dokawa da wani irin yanayi zuciyar na kara buɗewa sosai idanuwansa suna dauko masa wasu abubuwa masu muhimmanci daga idanuwanta suna sauke wa akan sa.

A jiyar zuciya yayi murmushi na kufce masa a fuska kafun ya kau da kai zuciyarsa na kara saurin bugu ita kam gabadaya ta gama tafiya wani mataki da sauri ta fara daga kafafuwanta da take ji suna kokarin lauyewa su zubda ita kasa a haka har ta zo gilma shi.

“MARIYA!”.

Ya fadi da sauti  tsayawa tayi cak! zuciyarta na bugawa kafun ta dubeshi na yan sakanni sannan ta ja jiki ta bar wajan cikin hanzari domin bazata iya tsayuwa ba ta tabbata in tajima a haka sai dai a tsince ta zube a kasa tana jin zuciyarta na kara buɗewa da lamarin Dr.Karami bata san mai yasa haka ba sosai take jin GURBIN SON da ta bashi a zuciyarta yana kara buɗewa yana kara fadi yana saukar da wasu lamuraka masu taushi a cikin zuciyar ta ta.A hankali take duban Hajiya Layla gabanta na sake tsananta faduwa duban mutumin dake zaune gefe guda tayi sannan ta kalli dubun nan kudin da suke ajje cikin leda wani irin kartawa taji zuciyarta tayi da wani irin yanayi mai zafi da raɗaɗi ji take yi kamar ta hadiyi zuciya ta mace.+

Sosai ta ke jin komai na canza mata sosai take jin zuciyarta na sake yayyagewa da tashin hankali wanda bata yi tsammani zata kasa daukarshi ba tayi tunanin zuciyarta zata bata dama har ta ga kullewar wannan lamarin amma ina! ba zata iya ba da sauri ta fara ja da baya idanuwanta na rinewa da tashin hankali kafun ta juya da gudu tayi cikin dakinta.

Hajiya Layla da tun dazu take kallon Areefa zuciyarta na tausayinta ta sani tabbas dole Areefa taji ba dadi amma ba yarda zatayi dole wannan hanyar ta kasance mafita a gareshi su ita ce kawai take hango komai zai zama daidai bata tare da an samu matsala ba nisawa tayi sannan ta dube shi da fuska cikin damuwa.

“Yanzu ya kukayi da su mutanan da suka zo neman Aure?”.

Murmushi ya saki tare da gyara zama sosai yana fuskartarta kafun ya ja numfashi.

“Ai Hajiya ba wata matsala duk yarda kika ce ayi haka akayi sati biyun nan dai masu zuwa za a daura auren kamar yarda kika bukata su ma ba su ja ba”.

Murmushi tayi wanda iyakarsa laɓɓan bakin ta kafun ta janyo jakarta dake gefe ta zuge zip din kudi ta zaro ta mika masa kafun tace.

“Ga wannan sai ku fara saye-saye wanda ka san gidan biki na bukata sannan duk wani abu zan turo muku dashi wanda zai tabbatar da cewa eh bikin na gaske ne”.

Gyaɗa kai yayi yana ansar kudin goɗiya yashiga zabga mata kafun ya mike ya fice daga cikin gidan.

Sai lokacin Hajiya Layla ta samu tayi ajiyar zuciya mai karfi a hankali ta mike ta dauki ledar da kudin suke ciki zuciyarta na mikata wani mataki na tausayin Areefa a haka har ta isa cikin dakin ruf! da ciki ta hangeta ta hade fuskarta da filo a hankali ta taka ta isa gareta bakin gadon ta zauna bayan ta ajje kudin gefe guda.

Duban Areefa ta shiga yi wacce ta tabbatar taji shigowarta a hankali ta kai hannunta saitin bayan ta tana bubbugawa kadan-kadan kafun ta shiga cewa.

“Areefa mai yasa zaki yi mani haka bayan kin min alkawarin ba zaki sake nuna wani damuwa kan lamarin nan ba karki manta ba wai nayi niyyar yin wannan abun bane don cutar dake a,a nayi ne don ƙwatar miki yancin ki wanda na tabbata in komai ya kammala ke akaran kanki zaki yi farin cikin haka”.

A hankali Areefa ta dago tana zama idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir sai faman cizon laɓɓa take tana dakune fuska.

“Farin ciki fa kika ce Maama kina tunanin a duniyar nan zan sake samun farinciki ne kina tunanin farincikin da ya guje mani zai sake dawowa gareni ne a filin rayuwar ta bana tsammanin haka zai kasance na sani rayuwata ba komai bane a duniyar nan bana tunanin a rayuwata farinciki zai wanzu…”.

Numfashi taja da taji yana sarke mata wasu kwalla masu zafin gaske suka zubo mata saman kuncinta hannu ta saka ta dauke su kafun ta shiga girgiza kai.

“Ban san ya zan fuskanci wannan rayuwar ba kawai ina yin ta ne ba wai don farinciki ko kwanciyar hankali ba dama can Allah ya halicce ni a haka zan kare rayuwa ta cikin kunci da takaici da rashin ‘yanci na lura a duniyar nan in har baka da

makusanci to kai ba ka da wata daraja ko kima da za a ganka da ita kai da banza duk daya ne….Maraya shima mutum ne kamar kowa yana da ‘yanci a wajan ubangijinsa ko bai dashi a idon jama’ar duniya bani nayi wa kaina haka ba ba a son raina na zo a wannan yanayin ba amma saboda rashin ‘yanci da sanin daraja ta aka lalata min rayuwata aka kashe mani duk wani hanyar da zan samu

STORY CONTINUES BELOW

kwanciyar hankali da natsuwa Maami kina tunanin ko na auri Dr.Erena na fita akwai wanda zai aure ni a yarda nake ne?”.

Girgiza kai ta shiga yi kukanta na daduwa hawaye sai sintiri suke mata zuciyarta take ji ta matsewa da wani irin ciwo mai girman haske abun da ya faru da ita shekaru masu auki can baya take hangowa kamar yanzu komai yake faruwa runtse idanu tayi tana sanya hannayenta saman kirjinta da take jin yana barazanar tarwatsewa.

Ita kanta Hajiya Layla hawaye take yi ji take yi kamar yanzu ta tsinci Areefa cikin wannan mawuyacin halin janyo Areefa tayi jikinta ta shiga rarrashin ta hakan ya kara tsananta kuka Areefa sai da tayi mai isarta ba tare da Hajiya Layla ta hana ta ba domin ta san dole taji rashin jindadi dole taji kunci da bakinciki  ba ‘ya macen da zata so aci zarafin ta haka ba ‘ya macen da za ta samu kwanciyar hankali a irin wannan halin.

“kiyi hakuri Areefa kiyi hakuri komai zai wuce ba wai zaki yi wannan auren don ke kadai ba ne Areefa duba zaki yi da halin wannan mutumin in har aka barshi a doran duniyar nan Allah kadai ya san iya yarda zai tsaya da cutar da mutane hanyar daya ce shi ne ki aure shi na tabbata ke sai kin yi mamaki abin da zai faru ba dai shi yace yana son ki ba to wallahi tallahi ya janyo wa kansa duk wani kunci duniya da bala’i da yake saka mutane sai ya ji yarda ake jin sa ni dai kawai ki bani lokaci ki ajje komai a gefe sannan ki cigaba da addu’a da izinin Allah sai munyi nasara akan sa”.

Dago jajayen idanuwanta tayi tana mai ajiyar numfashi zuciyarta sai faman kartawa take yi.

“Shikenan Maama komai ya wuce zan yi yarda kike so”.

Murmushin dole Hajiya Layla ta saki tana sake rungume Areefa tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri hakan ya kara mata jin tausayin Areefa dole ta kwatar mata yanci ta dole ta nunawa Dr.Erena a duniyar nan ba komai yake tabbata ba musamman zalunci da cin amana sai ta nuna masa komai da yake yi akwai karshen sa kuma sai ta tabbatar masa MARAYA shima mutum ne kamar kowa yana da daraja da kima.

****

Kallo daya zaka yi mata ka gane irin ramar da ta zabga cikin yan kwanaki gabaya ta kasa kwantar da hankalin kullum cikin tunani da damuwa take akan abin da zai je ya dawo tsakaninta da Dr.Erena sosai take fargaba da tsoro sosai take jin wani irin yanayi a jikinta komai take ji yana sauya mata ji take yi kamar ba ita ba ba ta san ya wannan lamarin zai kasance ba bata san mai yasa Hajiya Layla take son bikin nan ya tabbata ba taki fada mata dalilinta tace ba yanzu ba hakan na kara sanyata cikin damuwa.

A hankali take tuki zuciyarta na ta faman safa da marwa har ta isa kofar gida tayi parking sannan ta fito hannunta rike da manyan ledoji da alamun sayayya tayi haka kawai take ji yau gabanta na faduwa ta rasa dalili ko da yake ba zata ce ta rasa dalili ba in ta danganta da lamarin nan

lamarin dake kokarin faruwa da ita tana cikin wannan tunanin ta ji wayarta ta fara Ring runtse idanu tayi kafun ta dubi fuskar wayar dake hannunta ganin mai kiran ya sanyata jan dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta sai da tayi kamar ba zata dauka ba amma tuno maganar Hajiya Layla da take cewa karta sake ta nuna hanyar daya da zai fuskanci wani abu ta nuna masa kulawa sosai

musamman a daidai irin wannan lokaci da bikin ya gabato saura mako daya.

A hankali ta kai wayar kunnnan bayan yayi kira na biyar bata daga ba numfashi ta ja ba tare da ta ce dashi kala ba shi kuwa acan nashi bangaren jin ta daga wayar ya sanya shi sakin ajiyar zuciya tare da murmushi.

“Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida”.

Abin da ya fadi kenan cike da tsokana yana faman dariya ita kuwa Areefa ji tayi kamar ta kurma ihu don bakin ciki da takaici haka kawai taji wani kululun wani abu mai girman gaske ya tokare mata zuciya numfashi ma na kokarin gagararta ja runtse idanu tayi tana jin yarda kanta ke sarawa kamar zai rabe gida biyu a hankali ta ciji laɓɓanta kamar zata bula su kafun ta sake jan numfashi mai tafe da makakin takaici da bakin ciki.

STORY CONTINUES BELOW

“Uhmm aiko wannan maganar taka ba gaskiya bane domin in har na kashe d’an mai gida ba abin da zai hana ba a hukuntan ni ba wannan falsafar taka sam bata yi ba”.

Ta fadi da nuna kulawa amma a filin zuciyarta da fuskarta wani kunci ne yake kokarin kashe ta.

Wata mahaukaciyar dariya ya saki mai sauti kamar zai tarwatsa mata kunne da sauri ta zare wayar tana mai sakin numfashi kallon wayar take yi a wani irin yanayi ji take yi kamar ta rotsata da kasa ko ta samu natsuwa ko yaya take a zuciyarta.

“Ai ke ta daban ce ko a cikin matayen ko kin kashe ba wanda ya isa ya hukunta ki”.

Ta jiyo sautin muryarsa na fadin haka runtse idanu tayi a zuciyarta tana mai cewa ‘kenan ce masa akayi kowama mara imani ne a duniyar sa kaico’.

Amma a fili mai da wayar tayi kunnnanta tana murmushin da yafi yak’e ciwo.

“Uhmm ka ji ka da wani batu lokacin da zaka kira jami’an tsaro suyi ram dani ai duk wannan batun mantawa zakayi dashi”.

“Wai kina zaton ba zan iya bane Areefa?”.

Ya fadi cikin iyakar gaskiyarsa bata yi mamaki ba don ta san kadan daga aikin sa ne dakune fuska tayi kafun tace dashi.

“Ina zuwa gida zan shiga yanzu kaji sai an jima”.

Tana fadin haka ta kashe wayarta tana jin yana magana amma taki kula shi tsaki ta ja kafun ta rangwadar da kai cikin yanayi na fidda tsammani zuciyarta na kara tsanar halin Dr.Erena tsoro take yi akan abin da zai je ya dawo.

Da wannan tunanin ta karasa cikin gida zuciyar cike da yarda al’amarin nan zai kasance.

Haka rayuwar tayi ta tafiya zuciyarta Areefa na kara rikicewa da al’amarin Dr.Erena don ta ga dai da gaske yake an kawo lefe da komai da komai ranar daurin aure kawai ake ji izuwa lokacin gabadaya ta gama fidda tsammani Hajiya Layla ce take ta faman tausarta tana bata baki amma ina lokuta da yawa zama take yi ta ci kukanta har ta koshi ba abin da ta tsana kamar wai ita ce zata auri

Dr.Erena mutumin da ya bata mata rayuwa yayi mata illa ya hana ta duk wani farin ciki ya wulakanta ta wai shine a matsayinta kaicon wannan rayuwa kaicon wannan rana da ta zo a gareta mutumin da ta tsana tsana mai tsanani a rayuwarta shine za su hada inuwa daya a haka ta cigaba da dakon kiyayyar Dr.Erena har zuwa ranar da Aure ya tabbata akan su

bayan an yi shagulgula wanda hankali ba zai dauka ba an kashe kudi bidi’o’i ba kalar da ba ayi ba Areefa tayi kuka kuka mai ansa suna kuka a ranar ta so Allah ya dauki ranta ta so ta mutu da ganin wannan BAKAR RANA a rayuwarta kunci da bakin ciki a ranar ya kara daduwa a gareta haka ta wuni cur tun da aka ce an daura auren wani zazzafar zazzabi ya saukar mata ta shiga rawar sanyi

kamar wacce aka saka cikin firji aka fiddo ta numfashin ta sai sauri-sauri yake yi ita kanta Hajiya Layla sai da ta firgita da yanayin da ta ga Areefa a ciki a wannan halin haka ta dauke ba tare da sanin kowa ba ta kaita asibiti nan aka ba su gado sai da ta sha ledar ruwa biyu tare da allurai sannan bayan jikin ya lafa suka dawo gida Hajiya Layla ta yi kuka ita kanta

sannan ta shiga bata baki akan cewa tayi hakuri ba abin da zai faru da ita da izinin Allah Dr.Erena ba zai taba nasara akan su ba sosai ta bata baki har zuwa dare lokacin da za a kai amarya motoci kuwa ba a maganar su jerin gwano sukayi da kyar da suɗin goshi sannan Areefa ta yarda aka fiddo da ita daga cikin gidan bayan Hajiya Layla ta bar gidan domin cewa tayi ba zata iya tsayawa ba tana tsoron abin da zai faru tausayin Areefa zai iya hana ta cimma burinta.

Tunda aka saka Areefa cikin motarta da sauran mutane da Hajiya Layla ta dauki hanyar su yan kai Amarya shikenan ta tsagaita da kuka zuciyarta na dauko mata wani tunani tana kawo mata tsanar Dr.Erena da kiyayyarsa na kara hauhauwa a zuciyarta abin da take gudu shi take jin zuciyarta na kokarin bata damar aikatawa sosai ta aminta da wannan shawara lokaci guda duk wani fargaba da tsoro suka fice mata har lokacin da suka isa katafaren

kerarren gidan da za a sakata wanda ya gama haduwa tsayawa fasalta shi ma kauyanci ne babu abin da babu a cikin sa sai babu din sai dai ga Areefa duk wannan bai yi mata ba tana jin yan kai amarya na zuzutawa da koɗawa da cewa tayi goshi ta samu aljanar duniya amma ita a wajanta ko gidan yari yafi mata da wannan bakin gidan…

About AIS

Check Also

UKU BALA’I CHAPTER 12

UKU BALA’I CHAPTER 12                    Www.bankinhausanovels.com.ng  Tsaye …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *