TAWA TA SAMENI CHAPTER 26 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 26 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng Adams,Adams ya dubeni mun zata ba zaka zo dinner

kanwa ba?yace kasan mai iyali saida na lallameta tayi barci Adams yana yayi kyau muma dai Allah ya kaimu ga jarawa ,ni kam kumallon ya motsa don haka duk haushi suka bani Adams ya dubeni yar gidana kina

gaya min kince zakuyi lunchn da mene?nace sai mun

zauna dasu Amira menene na sauri Adams da sauran

lokaci fa,yace ba wani lokaci gara ki fada min don in na tafi sai ana sauran kwana daya biki zanzo in Www.bankinhausanovels.com.ng nasan komi tun yanzu zaizo da sauki,na dubi yaynmu wanda yake ta aikin danne dannan waya tamkar baya jin mu nan ko yana sauraren komai nace to kafin ka tafi zamuyi zancen, gobe fa zan tafi cikin kosawa da

maganar nace to baga waya ba Adams yace to shi

kenan ya canja zancen da hajiyata tana son jin

muryarki bari na kirata ku gaisa,nace haba dai daren

nan?ka bari sai da safe yace to na bari kinsan ni ba dai cikin gimbiya ba nayi dariya nace to Allah yasa ka dore ba sai naje gidan ba a canza min yace haba aini din nan ko bawa kika samu kinsan yanda nake son ki

kuwa?kin san nutson da nayi a kogin kaunarki?

in da ace kinsan yanda jiki da jijiya da bargo da kashi da tsoka…….. kai yaynmu ya daka tsawa ya cigaba haba Adams ka tasa yarinya karama kana wannan
kauyancin?ai wannan soyayyar dace in kana sonta
idonka kadai ya isa sheda ba sai kanata wannan batun
ba ka gane wannan ai yar da girma ne da ga ni har
adams kallonshi muka tsaya yi sai da ya gama sannan
yace Maska kai komai naka daban ne kana da hali irin
na masu girman kai…yaynmu ya daga mishi hannu ya
isa yi tayi,Sai karfe sha biyu muka tashi daga dinner

washe gari muna sallama da Adams yace sam bikin Www.bankinhausanovels.com.ng
nan bai min dadi ba,dan naso muyi hotuna muyi hira
mai isarmu amma haka bai samu ba nace kar ka damu
tun daga waya maganar hoto sai na shiga na miko
maka munyi sallama nabashi hotuna ya diba son ranshi mun rabu akan sai naji shi a waya haka muka
rabu,bayan gama bikin mami yaynmu bai kuma damuna
ba sam gaisuwa ke hada mu sai dai da naje gidan
babana ne yake cewa yayanmu yana zuwa yana
gaisheshi har yazo da mai dakinshi ya yabeni tare da
fadin kirkinshi,ranar ma muna zaune a falon babana
dani da Anty Maijidda sai ga yaynmu sun gaisa da anty maijidda sannan na gaisheshi anty tace kije ki kira babanki na tashi na dauki dan kwalina naje na sanar dashi,yana fitowa naga ya soma fara’a ganin yaynmu suka gaisa sannan yace yazo ne ya mishi sallama dan gobe zasu koma sai kuma nan da wata hudu lokacin bakina da abokinshi babana yayi mishi godiya gami da sa albarka sannan yace ga kanwar ka nan dama ta dameni wai nayi sallar magariba na kaita gida don haka sai ta tashi ku wuce,na ce sai gobe zani,babana yace a’a ni kinga gobe kwatano ma zamu,na soma shagwaba nayi takwa takwa da fuska nace nidai to ai baka sai Www.bankinhausanovels.com.ng
min abinda kace ba yace me nace zan sai maki?
computer yaynmu ya harareni na kauda kai babana
yace to in na dawo ranar sati monday sai na sai maki
shi kenan?nace eh yace to uwata maza tashi yaynki na jiranki na mike ina fadin ko kana korata ne?ba zan sake zuwa ba suka sa dariya shida anty Maijidda yace wane ni na kore ki ban isa ba nayi kadan anty tace naje daki na dauki kayana na dauka tace na gaida mamana,tunda muka dau hanya ni da yayanmu ba wanda yayi magana can yace gobe zamu koma sai kuma bikinki na dubeshi to Allah ya tsare hanya na fada cikin karfin hali,tunda muka zo gida muka samu haj yaya a harabar gidan na soma tsuma,cikin tsoro nace gasu haj,to menene yace yana fakin na fito da ido suka bini shi kuma ya nufi gurin su ni kam gida na wuce,yace haj daga ina?ta daure tace nan makwafta muka shiga barka ta cigaba matarka tana jiranka ashe kai kuma kana nan kana yawon banza daga ina kake?daga tudun wada,gurin wa?gurin baban iman ta kuma dubanshi muje ciki gani nan tana mamakin halinshi shi mutum ne wanda baya shakka ko karya komai zai fada in dai gsky ne zai fada sai dai a mutu
Haj yaya fada take tana karawa tace eh dan shashanci matrka ta na nan tana jiranka kai kuma ka tafi gidan kanin ubanka yace to haj dan naje munyi sallama shine damuwa?to kiyi hakuri ta dan sassauto kai baka da tunani yanzu in kai wanine yaushe zaka bar Adamu abokinka ya nemi yarinyar nan ga kannenka? yace wadanne kannen kuma bayan sunyi aure?ko ba ma haka ba ai matar mutum Www.bankinhausanovels.com.ng kabarinsa….tace nasan haka amma ni na sha alwashin sai na hana auran Iman da Adamu in dai ina numfashi yanda bana son ta rabeni kaima bana son ta rabi na kusa da kai kaf yayana wacce ce ta samu mai kudi dan mai kudi kamar Adamu?babu dan haka itama ba zata aureshi ba,sororo yayi yana dubanta sai da ta gama sannan yace to haj ke me zakiyi akai?dan Allah ki bar maganr nan,tace nasan abinda zanyi kai dai tashi ku tafi Allah ya tsare hanya kana can zakaji lbr,yaso yayi mata nasiha gami da shawara amma sai taki ta hau shi da fada,dan haka sai yace to haj zan wuce ba zan samu dawowa da safe ba saboda sammako zamuyi ta kano zamu tashi sakon ki gobe in Kabir ya kaimu kano ya dawo zaije banki ya amso maki kudin,ta ce zaka kara min dubu talatin akan na da yace ba komai zai kawo maki ina Mimin mu wuce,haj tace tana gidansu, ya dubi haj wa yace taje jiya fa can ta yini haj tace ai ba’a gajiya da gida ka dai
biya ka dauketa yace Allah ba zan biya ba tunda ban
aiketa ba in ta dawo shi kenan in bata dawo ba ta
zauna,Haj ta dubshi gara da ka nuna na gani dama ta
kawo min kara kana wulakantata son ranka yace haj ni kinsan abinda take min ne? bata san kula da miji ba
bata san darajar miji ba bare yanda zatayi biyayya son jiki bata iya girki ba,ni nasan ina da mata amma
sai na fita yawon gidajen cin abinci,tace to ai komai
dan lallashine yace wane lallashi ne ban mata ba amma nasan maganinta zata gane bata da wayo,ya mike mun tafi haj tace Allah ya tsare kar dai ka yarda naji wata magana. Sosai su haj yaya suka hau shiga malamai duk wai dan araba Iman da Adams ko ina ruwansu oho? nikam bansan me suke ciki ba,muna hira da Adams yanzu na sadagar shine mijina kuma na hakura shirye shiryen dasu mama keyi na bikin nan ba dama har dubai su mama sukaje da anty yagana ga wasu jike jike da suke faman dirkamin bansan ko na menene ba sunce ma in saura sati biu bikin zamuje maiduguri a gyarani bansan gyaran da za’a min ba tunda dai nasan nima ba dan laifi baka ce amma ba bakikkirin ba hancina ba dogo bane kuma ba gajere ba bakina mai dan fadi da sirrin Www.bankinhausanovels.com.ng
lebuna idona farare kal kuma ba kanana ba ne gudar
gadar ne musamman ma in na tsorata kamar yanda naji ana cewa,sai muryata ni kaina nasan ina da murya mai shegen dadi game dajiki nasan akwaini dan kasa da sama ba matsala mutane da yawa jikina ke rudarsu ba wai so ba to ban san gyaran da suke nufi ba. Yau ni da Amira gidan mami muka je dan shirye shirye bayan munci munsha sai muka shiga abinda ya kawo mu can nayi tsaki gara mu tsaida magana don sati na sama zamuje maiduguri mami ta ce yin me?na dan tabe baki wai gyarani za’ayi har ma dariya abin yake bani mami tace ba sauki nace dan Allah wai gyaran menene? sukayi dariya Adamu zai baki amsa gabana ya fadi nace kuyi min bayani mana,mami tace kefa mukayi magana dake kwanaki nace ni duk ynxu tsoron Nasir nakeji kikace ke bakya tsoron Adams to zaki ji tsoron ne sai kin shiga hannu,mu dai ynzu mun ketare sai ku, gashi har wani gyara za’ayi mashi Amira ta yi dariya tace nidai hankalina kwance nace zaima tashi ne na dubi mami nace da wuya ko?mami tayi dariya tace bance ba sai ta kuma kwashewa da dariya nace muguwa tace ba komai zan dai ji jiki ne.Tin ana sauran sati uku biki Adams ya aiko min da katuna ban taba ganin kati mai kyau irin wannan ba tunda naga katin sai jikina yayi sanyi na shiga daki sai kuka,babana ya kirani yace duk abinda nakeso na fada nace komai yayi min yayi,yayi yayi muje kasuwa na zabi kayan daki da kaina
naki,yan uwan Adams sun kawo kaya akwatina saiti biyu sai naga ma kamar ba gaske ba,yau juma’a maiduguri ta dauka tun da muka je sai aka shiga gyara ni daki aka ware mani nida mai gyarani nan gidansu anty yagana satinmu daya mun dawo ana saura sati daya bikinmu ni kaina nayi mamakin kaina dana dubi madubi sai kace bani ba yanzu kam na yarda gyaran da mukaje dan nayi Www.bankinhausanovels.com.ng
kyau san da na dawo su Amira sunyi nisa da rabon kati duk wanda ya kamata sunkai mishi batun yan gidan mu su haj yaya sunsha mamaki ganin shirye shiryen da ake ganin gyare gyaran da ake min ya kara firgita su gashi boka ya masu alkawari za’a fasa auren gashi har lefe yazo mai yawa koda mama tace suje suga kaya ba kunya sukaje don gulma ganin kaya da gwala gwalai sai jiki ya kuma sanyi waya haj yaya tama laure akan tazo da magana bayan sun shiga uwar daki haj yaya tace laure zama bai ganmu ba kaya tun ana kirga zannuwa da nazo hamsin sai na daina ganin gwala gwalai sai hawan jini na yaso taso ya tashi ba arziki na fito daga dakin haj laure tace ynxu menene abinyi?yaya tace inaga gurin malamin nan zamu koma….
Sune zaune gaban malami ko nace boka ya dubesu
kin cika gajan hakuri an daura auren ne?suka ce aah
yace to na gaya muku ba shi ne mijinta ba zaa ba wani ne zaku sha mamaki kuje ku nutsu nan da
kwana uku zakuji lbr ya canza_ rauhanai sunanan suna aiki yanda ya kamata nan suka yi godiya suka fita. Yau sauran kwana uku biki zaune nake akan kujera a wani daki gidan anty yagana nan muke nida kawayena yar borno wacce ta gyarani a maiduguri itace ta zo yau danmin lalle na musamman an zana shi hannu da kafa an ratsa jan rani dama kafin a fara sai da aka milkeni da wasu mayuka na gani na fada masu tsananin kamshi
da su launin fata dama tun da muka dawo daga
maiduguri kamshi duk inda na ratsa sai na barsu da
kamshina yar borno na zaune tana kankare min lallan Www.bankinhausanovels.com.ng
ba bose wata mai gyaran gashi ce ma kwaf tun su anty yagana ne ta hadda ai gyaran gashi ita ce tasa man gashi mai tsada tana min shampoo sai tabke min gashi takeyi wai nayi dabara da ban fara sa mai ba sai da na tashi aure ni dai jinsu kawai nakeyi saboda yau haka nake jin jikina,can text din da aka saba yimin ya shigo Amira ce ta miko min waya gashi ango yayo text nace ba ango bane na duba sai naga ina miki murna amma har ynxu bancire rai da samun ki ba har sai na ga an daura miki aure abinda bana fata dan ban san ya zan kasance ba wannan ranar,nace kaini wannan mutumin
ya dameni Amira karanta ki gani wanda nake gaya maki din nan ne ta amsa tana kokarin dubawa tana cewa kila

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 37 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  haka tukunna ina …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *