KALLON KITSE CHAPTER 3

KALLON KITSE CHAPTER 3

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

saboda zafi ga tsoro ya kara tureta, maza barmin dakina,.

Ta fice a guje tana kuka, sai dakin inna, ta fada jikinta, “inna ni bazan sake kaiwa yaya jafar abinci ba, kullum naje saiya dakeni, yau ma rankwashina yayi, bakiji ba kamar kaina zai cire, yanzu haka kaina ciwo yake min.

“yi hakuri zai zo ya sameni ai”.

A’a inna don Allah ki kyale shi, wallahi zai karamin wanda yafi wannan, nidai bazan sake kai masa abinci ba.

“toh shikenan je kidauki maganin ciwon kai kisha.

“a’a inna ai naji sauki.

Dama nasani bazaki shaba.

“yauwa dan Allah inna kibari naje gusau mana, kinsan fa kinyi alkawari. Inna ta zuba mata ido. Anya uwani zan iya bari kitafi ki bari dai auren mansura sai muje, tunda lokacin kina hutu

toh shikenan Allah ya nuna mana.

A lokacin jafar ya shigo tsab uwani ta mike ta wuce dakinsu, ya dubi inna wacce ta hada girar sama data kasa, ba alamun wasa a fuskarta, daga sama yaji tana fadin, me uwani tayi ma ka doketa?.

“ni inna? Ta banka mishi harara wanda ke nuna wai wasa nakeyi dakai? Sai yasha jinin jikinsa kansa akasa yace inna ayi hakuri, ai ita taja.

“kar kasake dukanta akai, kanaji nako? Haka kawai cin zali, kasan inka sake saina rama mata wallahi,

kansa akasa dai yace inna ayi hakuri, baza a sakeba.

Tace ni nafada maka ban amince da neman auren nan nakaba, in kuwa kaki toh sai kaje kayi tayi, amma nikam ba ruwana, kuma bazansa albarka ba, don haka kaje kayi tunani. Tashi tayi ta wuce daki.

Shi kuwa idonsa sunyi jajir, kaman garwashi ahaka indo ta shigo, ta same shi, ta gaishe shi acika ya amsa dan batama ji abunda ya fadaba, ya mike ya fita fuuu. Kamar iska. Indo daki ta karasa, ta iske uwani kwance akan cinyar inna suna hira.

“uhm uwani ta inna, zanso inga ranar rabuwanku, lallai ba karamin aiki bane.

Inna tayi dariya, ai nima ina wannan tunanin, ke dai indo uwani tace, kai inna kema kina biyewa babba ( indo kenan, haka take ce mata), nifa ba wanda zai rabamu saidai mutuwa ko inna?

Eh hakane uwani kedai kyale indo.

Toh shikenan Allah ya nuna mana, nikam nasan akwai ranar rabuwa, inna miya samu jafar ne, yadda na ganshi gaskiya akwai abunda ke damunsa.

“ke rabu dashi wai aure zaiyi, amma shine zaije can ya dauko mana ‘yar maiduguri shuwa arab, nikam gaskiya ba dani za ayi wannan abunba,, na taba gani ba labari aka ban ba, akwai wani abokin mahaifinsu daya auro su, duk arzikinsa suka kwashe, shine shi kuma zai dauko min ya kawo, toh badaniba.

“inna ki barshi yayi, kinsan fa ya dade baiyi auren nan ba, kar aje yakiyi kuma.

Saida ya fasa indo amma badai wannan yarinyar ba, kinsan tunda ya fadamin zancen auren wallahi hankalina bai kwanta ba.

Toh inna kiyi addu’a Allah yayi mai yiwuwa.

“inayi indo, saidai gaskiya ba wannan yariyar ba.

Jafar kam fitansa gidan kawunsa kanin mahaifinsu Alhj. Yunusa halidu ya samu, yayi sa’a kadai ne a falonsa, ya zauna suna gaisawa, jafaru yaushe a garin?

Tun jiya baba, ai jiya da yamma na shigo akace min kaje bunza.

“andawo lafiya? Ya bukata.

“lafiya lau ya bashi amsa.

“ya hanya kaima da aiki? Yace “lafiya lau, kawu addu’arku muke so ako da yaushe.

“ana nan anayi jafaru, ya zancen auren ka? Ya kamata ka ajiye iyali haka nan jafaru.

Ya sosa keyarsa, hakane baba, wallahi maganar ita tasa nazo, amma inna taki bani hadin kai, dan Allah baba kasa baki ta amince nasan in bata amince ba, auren nan bazaiyi tasiri a gunaba.

Yace ka kwantar da hankalinka zamje in sameta, ‘yar inace yariyar? Ya amsa masa ‘yar maiduguri ce, amma a warri suke zaune.

“ba komai, ita kake so?

Eh, baba indai inna ta amince, sun mace in tura aje neman aurenta.

“toh shikenan yaushe zaka koma?

Inasa ranan lahadi, yau saura kwana hudu,

bakomai insha Allahu za a shawo kanta, amma inaso kaje ka fadawa kanin nan nata na sokoto, kasan tana shawara dashi,

yace toh zanje gobe nagode baba.

Nan suka ci gaba da hirar su, bai bar gidan ba sai karfe goma da rabi, koda ya shiga cikin gidan inna ta rufe kofarta. Yasan danshi akayi saurin kulle kofar.

Washe gari gaisuwa kawai yakai. Ya wuce sokoto. Da azahar sai gasu kebbi dama shima kawun nasa ya matsu yaga yayi auren, sai bayan la’asar suka isa gun inna. Tana ganinsu tasan maganar daya kawosu, don haka suna gaisawa Alh. Yunusa yace “fatima nasan kisan dalilin zuwan mu? Munzo ne mu nemi alfarma gareki, kiyi hakuri ki bari ya auri wacce yakeso, yaran yanzu ba a yi musu dole don haka nake cewa ki sassauta masa, don son Annabi.

Hashimu yace “yaya kindai san jafaru ba yaro bane, dazaije ya dauko abunda zai cuta masa,

tace nidai gani nayi duk matan da sukenan basuyi masa ba, har sai yaje can maiduguri ya dauko?

“fatima ba inda aure baikai mutum, so nawa anayi, sai kiga wanima daga nan yaje kasar sin (china) yayi aurensa, duk abunda Allah yayi yinsa shine dai-dai, kedai kisa albarka ki kuma yi masa addu’a.

“toh ai shikenan me zance? Yaje yayi tayi nikam ba ruwana, amma Allah yasa albarka.

“haba yaya ya zakive ba ruwanki, baki amince ba kenan don Allah kidaina haka, yaya hakuri fa muka zo baki.

“toh na amince Allah yasa ayi a sa’a.Toh na amince Allah yasa ayi a sa’a.

“Amin, su duka suka amsa, sai a lokancin jafar ya saki fuskarsa don yaga inna sai hira takeyi dasu.

Anan sukai isha’i, dan har saida sukaci abincin dare, sannan baba yunusa yace, jafar yakai shi gida, tare suka fita da Alh. Hashimu, da yake dama ya daba sauka can gidan baba yunusa. Sai wajajen goma da minti sha biyar ya shigo gidan, ya isketa har daki, ya sami wuri ya zauna, inna na gode.

Ya fada kansa a kasa, ta wurga masa harara, “da akayi me? Ya saki murmushinsa na zolaya, “da amincewarki inna,

“toh bari in fada maka, da duk yarinyar nan ta shigo bata kwantar min da hankali ba, dole ka sake aure.

Yace “eh na yarda inna, yarinya ce ‘yar babban gida, zakiyi mamaki inna, bazata bayar daniba. Ta zumburu baki nidai na fada maka, da duk takini nima zan nemi mai kaunata.

Dariya yayi sosai, “inna zan baki mamaki.

“toh Allah yasa.

Amin. Ya amsa. Nan fa suka ci gaba da hirar da tunda ya shigo garin a wannan lokaci nai samuba.

Ranar lahadi ya koma warri, a ranar ya wuce gurin marliya, yana isa ya danna mata kira, baifi minti biyu ba sai gata, sai fara’a takeyi, ta shiga cikin mota data dauki sanyi, ga sauti yana fita a hankali gwanin dadi, ya dube ta sosai yace “i miss you baby”. Ta sunkuyar da kanta kasa, tace ina wuni? Yadan yar da hanunsa yace nifa kunyar nan taki tayi yawa my marliya, inaso ki sake dani, dan naje nayi magana aje nema min aurenki, kinga kuwa na kusa zama “yours” koba hakaba?

Farin ciki ya bayyana a fuskarta, tana yiwa Allah godiya, cikin ranta ta karasa kanta a kasa, “haba my love ki nunamin farin cikin ki mana.

“you are very special to me”. Ta nemi rufe fuskarta, ya rike hanunta da sauri, “a’ah don Allah kar kyi min haka, inaso inga beutiful face dinki.

Ta fisge hanunta tana kokarin fita daga motar, yayi saurin bada hakuri, “don Allah kiyi hakuri na daina.

Ta dube shi, tace nasha gaya maka bana son hakanan, ance fa duk inda mace da namiji suka kasance su biyu toh na ukun su shaidanne,

don haka nakeso ka rinka hakuri da irin wannan abun.

Ya kara jin dadi a zuciyarsa, dan dai yasan yayi sa’ar mata kamila, yasan zai dace da matar kwarai, wanda take kare mutuncinta, dan haka yasan in sunyi aure zata kare masa mutuncinsa, Allah ya nuna masa. (Amin). Ya fada a fili. Ta dube shi tace, da mene?

“sirrina ne marliya”.

“toh ai sirrinka nima nawa ne”

“hakane, in lokaci yayi zaki sani.

Haka sukai hira na masoya, masu ji da junansu, da kuma son junansu.

**** **** **** ****

MARLIYA YA’U

‘yar asalin maiduguri ce karkida, don haka talaici ne ya dawo dasu zama a portcourt, anan warri mahifinsu ya rasu, tuni ba yanzu ba, suna zaune ne da mahaifiyarsu magajiya aka fi saninta anan warri, ba wanda baisan halinta ba, gogagiyar ‘yar duniya ce, hakama ‘ya’yanta ta koya musu, da yake Allah ya azurtasu da kyau, sunyi kyan dan maciji, don ba abunda sukasa ma ransu in banda son duniya. Marliya itace ta hudu gun mahaifiyarta, itace kuma ta gadota sak! Halinsu daya da mahaifiyarta, malamai da bokaye ba inda bata lekawa, tunda mahaifiyarta ce ta koya mata, tunda tasan tafita iya duniyancin.

Ta soma ganin jafar ne ranar daya biya wani babban shoping mall. Suna daga cikin motar wata abokiyarta, shikuma ya fito daga cikin tasa motar, duk da haduwar motarsa (jeep), ita kam mai motar yafi burgeta, dan dama su mota itace take ganar dasu wane irin mutum ne kai, a rayuwarta bata taba son da namiji ba sai yau, tun da take arayuwarta bata taba zaton zatayi aure ba, ballantana tayi soyayyar gaskiya. Tasha jan ra’ayin maza batama san iyakarsu ba, akan zata aure su, saita gama yagar rabonta, saita yadda dasu, amma nayau ba haka bane, da sauri ta fita daga motar taje ta duba number motar ta rubuta a wayarta, tayi saving.

Jamila abokiyarta tace, “wai ya naji kinyi shiru na marly? (yadda suke kiranta kenan), mu wuce ne? Tace, a’ah jamila dan Allah kiyi hakuri akwai wanda ya shiga wurin nan inaso in dan kara kallonsa.

“kinga bachelor din kuwa ya hadu da yawa.

Jamila tace, ya akayi kika san bachalor ne?

“haka kawai naji ajikina baida aure”.

Ko yanada aure jamila zan nemeshi, in aure shi kota halin kaka ne.

Jamila ta zaro ido waje, “aure marly baby?

Haba dai kin manta da “oath” din mune akan bazamu taba aure ba a rayuwar mu?.

Marliya ta dubi jamila na kusan minti uku, “anya bazan karya wannan rantsuwa ba jamila? I thing am in love”.

Jamila mamaki ya kamata sosai itama sai taji tana so taga wannan bawan Allah, da yayi saurin tafiya da zuciyar marliya, dan ita tasan ba tun yau ba sun sha garzayawa da maza masu kyau ga kudi ba juyin da basuyi haka bai taba faruwa ba, sai yau.

Adai-dai lokacin……Adai-dai wannan lokaci kuwa ya fito, marliya ta juyota tace gashi nan ya fito jamila, dubeshi bai hadu ba? Ki kalle shi da kyau.

Jamila ta girgiza kanta, “hakane marliya “he is too much”, kamar daga sama sai suka hada ido dashi, batasan sanda ta saki bakiba, ta kwantar da kanta kujerar da take zaune akai.

Shikam ya shige motar shi ya wuce inda zashi, cewa jamila tayi mu bishi muga inda zai shiga.

Jamila tayi reverse tabi bayansa saida suka shiga cikin gari, basu san sanda ya bace musu ba, da kyar suka gano shi, suka ci gaba da binsa, haka suka gane yana zaune ne inda sojoji ke zama, jamila ta daga kan mota sukayi gida.

Tun daga lokacin da marliya tasa ido kan jafar, bata kara samun kwanciyar hankali ba koda yaushe zaka ganta cikin tunani, tasa aje abincika mata shi, amma yau kwana hudu kenan babu bayani.

Jamila tayi kokarin ta kwatar mata da hankali, amma ina taki, harda ‘yar rama tayi, duk wadanda taba appointment duk taki zuwa, saidai jamila ta wakilceta, ita kam dama jamila abunda takeso kenan, dan bata kai marliya karbuwa ba a wannan sha’anin, duk da haka yawancinsu basu yadda da hakan ba,

ibrahim shine dan masanin marliya ko kai waye awannan garin, inta turashi ya ganoka, to sai yayi bincike koda number mota ne, shikuma aikinsa kenan, indai ta nemi ibrahim tace tana son ya bincika mata waye mutum dan hakane data dawo gida, shita nema, ta bashi number motar jafar, shikuwa ya shiga gari nemansa, an sami kwana shidda ana neman jafar, ranan saiga ibrahim yazo mata da hotunan jafar kuwa, aranar kudin data bashi bata san ma nawa bane dan murna.

Tayi tsalle, tayi rawa, batasan inda zatasa ranta ba, dan murna. Tas aka bata labarinsa. Ibrahim ya fada mata cewar, sunama da wani taro da za ayi na sojoji in zataje, dan shima zaije, ba inda taji jafar ya burgeta yadda taji cewar shi likita ne kuma soja, gaskiya ya hadu da yawa.

Haka kullum take fadi.

Jamila tace, toh ya zamuje taron kenan?

“haba dan Allah jamila dadina dake sauri da garaje, bazan tunkare shiba harsai naje naga mal. Hussaini da shanshani, ya za ayi kinsan fa wannan gayen sonake in aure shi, don haka dole insan yadda zanyi.

“hakane. inji ibrahim, marli baby magananki kinada kashin gaskiya, don haka yaushe zamuje gunsu?

“yau dinnan zamuje gun mal. Hussaini, da yake shi a bauchi yake, sannan in wuce gun shanshani a maiduguri.

Amma da sharadi banaso Ammi (mahaifiyarta), taji wannan labarin, kunsan bason shawarar zatayi ba kun ganeko?

“toh ai muna tare, ba yanda za ayi taji,

“a’ah jamila ke zaki zauna dan nace da Alh. Sani gold yazo yau, kinga saiki wakilceni. Jamila bataso hakan ba dan itama tanaso taje taga malamin marliya, duk lokacin da zataje sam bata yadda tabita tarasa dalili.

A ranar kuwa suka kama hanyar bauchi, da yake shararren malami ne, yada inda yake sauke baki, bata damuwa da neman masauki, cikin kankanin lokaci aka hadata dashi. Bayan sun gaisa, ta gyara zama tace, mallam kasan yanda nake baji ba gani idan inason aiki dan haka nake son aikin gaggawa, akan wani gaye. Ina sonsa mallam, inaso shima ya soni, kota halin kaka, inaso ya soni tamkar uwar data haifeshi.

Mal. Hussaini ya juya wuyarsa dama, tana magana yana ‘yan rubuce-rubuce yace, bake yafi sonki akan yadda yake son uwar tasa? Tayi murmushi mai gamsarwa tace, inaso mana mallam, inaso kada yaga kowa daga shi saini marliya.

Mallam ya buga kasa sau uku, ya kara bugawa yadanyi tsaki, “mts…marliya kina son gayen nan da aure kikace?

“eh mallam inaso in aure shi, in mallake shi kuma.

“toh naga zako aure shi, zai kuma biki, amma fa akwai duhu mai wahalar ganewa.

“mallam ka gani ko menene. Yaci gaba da bincike, yauwa na gano matsalar, saidai fa da wahala in zaki iya yi.

“wace irin wahala ce banyiba abaya mallam, ka manta dani wacece ka manta dani mai naci ce, akan abinda nasa gaba.

Hakane marliya amma gaskiya wannan daban ne, saboda aiki ne sosai.

“gaya mini wane irin aiki ne? “na farko inji mallam hussaini, “ni zanje wani kauye daba asanni ba, in zama mahaukaci cikin kwana tara, ina binne-binnena, sannan inna kwana sha uku in binne kare mace da namiji agu daya, saidai  kuma ke awannan lokaci zaki kasance baki yiwa kowa magana ba sai bayan na fada maki na gama.

Wannan yaro dakike so yanada karfi sosai, jininsa akwai karfi, sannan iyayensa ba wai mahaifansa ba, a’a kakaninsa sunyi musu kafi mai karfin gaske, asiri baya tabasu, dan haka duk abunda nace dake dole kiyi.

Ta girgiza kanta da sauri, “eh zan iya mallam.

“toh sai abu na biyu zan shiga daji in kwana uku, bayan sati biyun nan, ke wasuma basai na fada maki suba, ayanzu amma fa akwai aiki ja a gabanmu, sai a hankali zan gano saura.

“toh Allah ya taimakemu, ya ams da amin”

yaushe zaki wuce? ya tambayeta

sai jibi, domin gobe zan wuce maiduguri.

“dakin kai saiki kirani dan in fara aikin.

“toh ga wannan mallam.

“marliya kenan dubu hamsin me zasuyi? “a’a ai bawai kudin aiki na bada ba, ina zaton saika gama zan baka cikon kudin.

About AIS

Check Also

KALLON KITSE CHAPTER 11

KALLON KITSE CHAPTER 11                     Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *