KALLON KITSE CHAPTER 1

KALLON KITSE CHAPTER 1

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Garin yayi zafi gashi bbu wuta, haj. Fatima wadda akafi sani da inna, tana fita asaboda zafin da garin ya dauka, duk data bude window da kofar falon da iska yake shiga.

Daga bakin kofar falon ta tsinkayi sallama, ta dago kanta ahanka tareda amsawa, wa alaikussalam, a’a maraba daku. Tamike ta zauna yadda zaji dadin magana. Shatu kece a yau? Shatu ta karaso cike da ladabi ta russana ta gaida inna, inna ina wuni? Lafiya lau ya hanya? Amma kam kun dauko zafi, cikin wannan uwar ranan da ai saiki bari har rana ta sauka ko? Tace inna wlh kam akwai ranar, saidai inaso inkoma a yau dinne shiyasa. Toh ya kwana biyu? Nina zata kin manta da alkawarin mu shatu, tun inasa rai har na hakura. Muna nan lfy inna, kinsan yanzu yan aikin akwai wahala, saboda sun daina bada ya’yan su saboda wasu dalilai, yanzu hka ‘yata na kawo miki dan na lura yanda kike son abokiyar zama. Inna tace kefa kika sani, harma

nasa a nemomin cikin ‘yan kannen larai, saidai mahaifinsu ne yaki dole na hakura. Ina yarinyar takene? Shatu tamike ta leka waje yarinyar na labe a kofar falon, ke zo ciki mana. Ts juyota, inna ta dubi yarinyar ke ‘yar fillo shine kika tsaya awaje, zonan ki zauna. Tana rike da ‘yar ledarta a hannunta taje ta zauna inda tagaga an nuna mata. Tunda haj. Fatima tasa ido akan yarinyar taji sonta yakamata, ta dubi shatu amma bazata wuce shekara biyar ba wannan yarinyar? Shatu tace eh ba wuce hakan ba. Toh kince ‘yar kice gashi ko kama bakuyi ba shatu?

Gsky ne inna, sunanta Aisha, amma iyayen na kiranta uwani, saboda sunana akasamata ‘yar kanina ce, kma marainiya ce, saboda mahainta Dalhatu mahaifanmu daya dashi, nine na raine sakamakon muma iyayen mu sun dade da rasuwa, kma mu kenan suka haifa, tunda suka rasu yadawo zama aguna, dan farautane anan kauyen da nake yana shiga daji.

Ranan ina zaune ya shigo min da yarinya ‘yar fulani cewa matarsa ce. Ya bani lbr cewa achan daji ya hadu dasu, mahaifinta ya bashi ita, baima bar garinba saida aka daura musu aure, abun bbu mamaki dan irin hka yasha faruwa, nidai da yake nasan halin Dalhatu yarone mai zuciya da neman na kansa, sannan yana kwatanta gsky a al’amransa, ya nuna minshi kam yana son matarsa, dole na ware musu daki suka fara zama, dayake mijina nada saukin kai da saurin fahimta, bai nuna damuwarsa da hkan ba. Sun sami kamar shekara sannan suka tashi daga gidan, da yake ya gina musu nasu, kuma a lokacin matarsa ta haifi uwani. Ana cikin hka rannan ya shiga daji, sai aka dawo mana dauke da gawarsa, hankalinmu ya tashi sosai hardaini  dashi kadai ne dan uwana, na tayar da hankalina aosai daga baya mukayi tawakkali. Uwani nada shekara uku mahaifiyar ta tasake yin aure, itama cikin data samune ajalinta, dan kwana tayi jini na zuba, gashi dan dake cikinta ya mutu, dan hka batama haifeshi ba, itama tace ga garinku nan. Uwani dama aguna take, saidai bata sakat a gidan, saboda mahaiyar mijina tace bazata zauna gidan danta ba. Dama yaya yake da har zai rike diyan wasu? Talauci ya masa yawa kona shi ‘ya’yan ma ya yake ciyar dasu. Nida naso uwani ta zauna dani amma saboda yanda batada ‘yanci acikin gdan shiyasa nayi niyar kawo miki ita, inna dan Allah gatanan amana! Haj. Fatima harda kwalla dan irin tausayawa uwani datayi, tayi ajiyar zuciya, tareda gyara zamanta, tace gsky ne insha Allah shatu zan rike uwani amana, inaso ki kwantar da hankalinki Allah ya jikan iyayen mu baki daya. A lokacin indo mai aikin inna tashigo, tana gaida shatu. Inna tace dan Allah indo ki kawo musu abinci suci, kada shatu tayi dare tace a yau zata wuce. Sunci sun sha sunyi hamdala, shatu tace toh uwani ga inna nan kiyi zamanki da inna. Sai kuwa nan ta fashe da kuka tana fadin ita bazata zauna ba.

Da shatu zata tafi har saida itama shatun tayi kukan, da kyar aka rabasu sannan shatu ta wuce jega. Inna kuwa sai hkr takeba uwani, amma uwani kuka take har dare. Ta kuma ki shiga daki tayi zaune abakin kofa. Jafar ne ya shigo, sam hamkalinsa na wani wajen bai lura da mutum ba. Tuntube yayi da har zai fadi yayi saurin kiran sunan Allah “subhanallahi! Baidai fadin ba, amma yaja tsaki “mts! Waye anan wurin? Jikinta na raw tamike tsaye, dan tsabar tsoro dan yanda ya daka mata tsawa, batace komaiba, amma taci gaba da kuka. Ya kara maimaita maganarsa wannan lokacin saida tayi fi tsari don tsabar kaduwa, sai a lokanci haj. Fati ta shigo falon tana fadin jafar bakuwace shigo mana.

Toh shine zata zauna a kofa? Nida kadan na fadi wlh.”

yi hakuri ta fada tana kokarin zama tace ” yau shatu ta kawomin ita ‘yar kaninta ce.

Allah sarki shatu shine bata nemeni ba? Gsky ne a yau kam sauri take dan ta koma jega.

Inna ina wuni? Ya nemi wuri ya zauna, ta amsa masa cike da kulawa. Ya kara kallon bakin kofar falon , yace wai inna wannan yarinyan tsoron falonki takeyine? Ta dubi kofar itama, a’a haushi take shatu ta tafi ta barta, nan dai inna ta kwashe lbrn uwani ta zaiyane masa. Tausaya mata shima yayi, yace…………….Yace, ai ko dan kirkin shatu dole arike mata ita, saboda nikam inna yanda shatu ta daukeni tamkar dan data haifa, tunda ta raineni na fahimci haka, ki duba lokacin dakina zuwa aiki, hka zatai ta fama dani, har saikin dawo, sannan zata sami sassauci. Inna tace gaka da rigima kuwa, kai jafar kayi rigima wallahi. Dariya yayi tareda tafa hannu, gaskiyane inna, amma yanzu na bari ko? Ta harare shi, sai dai abunda ya karu.

indoce ta shigo tare da sallama, suka amsa mata baki daya, ta ajewa jafar abincin sa agabansa, yace sannu indo, tadanyi fara’a tace, “ina wuni kato! Yadan sha mur, inna kinganta ko? Har yanzu bata daina cemin kato ba, ni wlh bana son sunan nan. Indo tana dariya tace zan bari amma saika haifo mana wani katon, sannan sai in daina. Ta zauna akan kafet, tace inna kinga yarinyar nan uwani taki hakura abincin ma taki ci, sai ajiyar zuciya takeyi. Inna tamike ta isa bakin kofar falon. Uwani na nan inda take, tana kuka a hankali. Inna ta dauki abincin dake gabanta tare da rike hannun tace taso mu shiga daga ciki, in kinaso in maidake wurin shatu.

Mikewar da zatayi saita ga fitsari, “haba uwani fitsari kuma kikai anan? Indo dan Allah taso ki taimaka mata ts cire kayan nan. Indo dakinta ta kaita ta tubeta, ta bude ‘yar leda data zo dashi bakomai aciki sai ragadadu, ta rasana wanda zata saka mata, har gara ma wnda ta cire matan, tafi sauki. Indo kam dan kwalin wata atamfar ta ta daura mata, don dai ba kayan da zata sa mata, duk ragane, sun dawo falon ta zaunar da ita, ta dauki abinci ta ajiye a gaban ta. Amma uwani ko kallon abincin batayi ba, ta soma wani sabon kuka, inna sai aikin lallashi takeyi, amma fafur taki. Jafar na zaune, yana sauraren su, saida ya gama sannan yazo har inda uwani take. Ya daka mata tsawa, yace ke zki daina kukan nan kosai na mareki? Nan da nan jikinta ya hau rawa, tayi tsit! Yace sa hannu kici ko in bata miki rai, kinaji ko? Inna tace, haba jafar lallashi fa akeyi da iyayen ta fa aka rabata? Yana duban uwani yace inna kyaleni da ita, haka kawai zatasa mu agaba tanayi mana kuka. Uwani kam sai sa loma take, cike da tsoro dan ita a rayuwarta dama bataso ayi mata tsawa, saida yaga tayi nisa da cin abincin, sannan yabar wurin, yayi wa inna saida safe, ta amsa masa, tana gamawa ko ruwa bata shaba. Ta soma yin bacci indo ta dauketa suka shiga daki, can gefen dakin inna,+

*********************

Haj. Fatima, mace ce mai zuciyar maza, irin mazan nan masu halin dattako, ita ‘yar asalin sokoto ce, anan mahaifanta suke tana da yayye da kanne, dan ba mahaiyarta kadaice agun mahaifisuba, mahaifinta dan boko ne sosai, dan hkane baya aurar da yaransa mata har sai sun gama universty dinsu. Haj. Fatima taci sunan inna tun tana gidan mahaifinta saboda sunan mahaifiyarsa taci, marigayi Hon. Alkali bello shine mijinta na farko kuma shine na karshe,

shima tsohon dan boko ne dan lawyer ne anan jihar sokoto. Allah ya albarkesu da ‘ya’ya bakwai amma uku kadai suka rayu. Shima mijin nata baifi shekara bakwai da rasuwa ba kenan. Sunan yaran nata zainab itace babba, tana aure a gusau, tana auren wani attajiri, da yake aikin mai tanada ‘ya’ya shidda maza uku mata uku duk sun girma, saboda ‘yarta ta fari ma tanada aure anan gusau, harda yara biyu.

Sunanta mariya, saita biyu mansura ita tana nan a universty dake cikin zaria wato (A.B.U) ba wani shekaru mariya ta bawa mansura ba, amma saboda ita tana gama secondary school tayi aure, saina uku shine moh’d shima yana S.S.2, sai mukhtar yana J.S 3, sai faruk yana J.S 2, sai muhibbat tana primary 5. Karamar ce sai yanzu za’a sata makaranta.

Saliha itace ta biyu gun Haj. Fatima, duk da ba ita kebima zainab ba, itama tayi aure suna abuja da mijinta, ‘ya’yanta uku , saidai kanana ne, faisal shine babba, yana aji biyu, hafsat itace ta biyu, ita nusery, akwai dan karami hafiz shibai riga ya shiga makaranta ba.

Jafar shi take kira auta, saboda shine na karshe yana karatunsa a dan-fodiyo universty, yana karatun doctor, yanzu haka ya samu shekara na biyar kenan. Rayuwar Haj. Fatima a saukake bata sama kanta kwadayin duniya ba, saboda tunda mijinta ya rasu ta samu gadon wasu gidaje biyar tasa haya, dasu take rayuwar ta, tana karba kowane shekara, inda tayi sa’a duk yawanci ma’aikata suka dauka haya, dan haka tana samu ba laifi,bata tsaya anan ba, tunda mijint ya rasu da yake da tana aiki, sai tayi rising tana zuwa dubai da china ta siyo kaya, tana sayarwa, takan turawa yaranta in sun saida suturo mata kudi ta banki ta koma kuma.

Jafar kuwa yaro ne dan gata gun inna saboda shiya zamto dan autan ta. Ikon Allah shine ta haifa na karshe, dan bata kara samun ciki ba, dan haka shagwaba ba wanda bayayi, musamman ta samo masa ‘yar raino wato shatu, tun yanada watanni take tare da shi, har ya shekara bakwai, sannan tayi aure, takoma can jega dayake ita ‘yar can ce, dan dan uwan mahaifinta take aure. Saboda shakuwar da sukayi wataran haka zai shirya yaje jega ya dawo…..

yace na gode inna, ki tayamu addu’a muma abun na damunmu. Tace toh Allah ya shirye ku da dukkan musilmin (ameen). Su duka suka amsa, maza ka tashi kaje kayi wanka, duk warin mota kakeyi, ya mike yana sosa keyarsa.

Haka rayuwa taci gaba, gashi har yakai shekara biyar a karatunsa.

***** **** ***** ****

washe gari saida inna taje kasuwa tasaiwa uwani sabbin kaya na kanti, kala bakwai, sai silippers. Tasa indo ta tsefe mata kanta. Indo tsab ta kwance kan, ta wanke shi tas, nan danan ta canza, tayi kyau, inna tace toh ko kefa, duba kiga yarinya da sha’awarta, amma sam bata samu kula ba, zo uwani inji inna, ta kalli inna ta tako inda take, ta rike hannunta tace kina zuwa makaranta kuwa? Uwani tace a’a.

Toh islamiya fa? Ta karace a’a muna zuwa na allo.

Ok wace sura kike a makarantar allon?

Kulhuwallahu. Tace toh yayi kyau.

A lokacin jafar ya shigo ya zauna ya dubi inna ya gaidata da kwana, wai yaushe zaka koma makarantar ne? Yace ai sai next weeak.

Ok zamu shiga insha Allahu, toh dama so nake anema wa uwani makaranta nan kusa damu, ya dubi Aisha wanda tun shigowarsa ta nutsu, tun jiya ta gane shiba na wasa bane.

Toh basai asata makarantar nan ta high standard ba, kin san inna tanada kyau.

Eh gaskiya ne, sai kaje ka bincika, dama a yanzu first term ake dauka kafin ayi nisa.

Da yamma likis ya dawo ya shigo, ya iske uwani batada riga, daga iita sai dan wando, yayi mata tsawa ke ina rigar ki? Jikinta na rawa ta shige daki da gudun ta, sai bayan dake kwance, ta mike zaune kedawa uwani? Ta nuna bakin kofa. Inna itama kofar take kallo. Jafar ya shigo ciki yana magana, in nasake ganinki baki da riga saina dokeki, yarinya sai kazanta, saikace wata….., inna ta kaste shi “wai kai dan Allah meya dameka da ita? Sam ka hana yarinya sakat, saboda me? To bara kaji gaskiya kada ka takura mata. Yana zaune yana aikin hararar uwani, ita kuma tayi kamar bata wurin dan inna rungumeta tayi akafarta. Ya batun makarantar ka nemo?

Eh na nema, har na na biya kudin makarantar, gobe zan kaita insha Allahu.

Toh an gode Allah shiyi albarka, uwani maza kira min indo ta kawo masa abinci, ta kama hanya da gudunta, ta fice daga falon.

Tun daga ranar ta fara zuwa makaranta, ansata nusery one, cikin satin da kyar take barin inna saboda kukan, ta ba zataba, saida jafar yayi da gaske, dan ranar saida ya doketa, inna kuma in banda fada ba abunda takeyi, tace ma bazata ba, saida indo tasa baki. Inna ta maida indo abokiyar shawaranta, saboda ta fahimci indo mutum ce mai rike alkawari, kuma ba munafuka bace, sun sami kusan shekaru shidda tare, amma sam basu taba samun sabani ba a tsakanin su, a ko da yaushe indo tana gudun zuciyar inna, shiyasa suke zaman lafiya.

Jafar ya koma makaranta don haka yasa uwani keyin abunda taga dama, musamman inna ta dauki direba yana kai uwani makarantar boko da islamiya. Yadda uwani ta zmz yar gata gun inna yasa yarinyar har shagwaba ba wanda batayi, bazaka taba cewa bata da jini da inna ba, da yake inna ta dauketa tamkar yadda ta dauki jikokinta, harma ta hadasu da sauran ‘ya’yanta, dan in sunyi waya idan tana kusa saita bata su gaisa. Har suma suna tambayarta in suna magana.

Abunka da mai jiki mai saurin girma, nan da nan cikin ‘yan kwanaki uwani ta warware, tayi kibanta gata bul-bul gwanin sha’awa, gata da saurin shiga rai, saboda suffanta irin ta larabawa ce, duk da ita ba fara bace, wakan tarwada ce, amma msi haske, ga gashi irin mai murdewan ga cika, saidai uwani bata son abinda ya taba mata kai, kullum sai sunyi da gaske, za’ayi mata kitso. Inna dole ta rinka sa indo tana lallaba mata kan, shima sama-sama, dan haka ne kullum zaka ga kan a yakuce, sam inna bataso taji kukan uwani ko akan menene, uwani gata da surutu kamar me, inna kam har ta saba dan kullum suna tare bata zuwa ko ina, indai ta dawo gida toh tana manne da inna.

Mal. Mamman sunan direban inna, zai iya kai shekaru hamsin da wani abu, yanada iyali anan cikin garin, saidai matarsa ta dade da rasuwa, tanada ‘ya’ya bakwai, tare dashi. Dukkansu matan sunyi aure, da yake ‘ya’yan sa maza biyu ne, kai su suka rage, shi yana son auren indo, ita kuwa indo sam taki ta amince kuma taki ta fada dalili.

Inna na zaune a daki taji ana sallama daga can falonta, tace uwani, maza jeki fadi waye? Ta fita a guje, kamar ma zata fadi, inna tace, wai uwani bana hanaki guje-gujen nanba, salon kije ki fadi ko? Ina? Uwani kam bata saurara ba, tanufi falon ta iske mal. Mamman, ta fada jikinsa tana fadin baba dama kaine, inna tace in duba wanda ke sallamar?

Eh nine jeki fada mata. A guje dai ta koma sukai karo da inna, toh ‘yar fama nidai kar kije kiji ciwo. Ta karasa falon, ta zauna, uwani ta dare kan cinyarta, tace a’a mal. Mamman kaine ashe, ka wuni lafiya?

Lafiya lau inna”

ina fata ba uwani ta kara yin wani abun a makarantar bako? A’a inna aita daina.

Kasan Allah bata daina ba, don da naje opening day dinsu, saida malamar takara min magana akan uwani, bata………..

About AIS

Check Also

KALLON KITSE CHAPTER 11

KALLON KITSE CHAPTER 11                     Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *