UNCLE NE CHAPTER 9 BY NIMCYLUV - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UNCLE NE CHAPTER 9 BY NIMCYLUV

UNCLE NE CHAPTER 9 BY NIMCYLUV

- - Post a Comment

 UNCLE NE CHAPTER 9 BY NIMCYLUV                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Lamo tayi jikinsa tana sauraran daddaɗar murya dake fita a hankali cike da nutsuwa kamala addini haiba, numfashi ya sauke kafin yace "jeki ƙwanta" turo baki tayi tace "to baka daɗi yadda ake tsarkin ba..

Hancinta yaja yace "ni ban iya ba to"duk da baccin dake cinta bai hana tayi dry ba cikin siririyar muryarta tace "Allah Uncle ka iya,ai komai kai ka iya kafi kowa" baice mata komai ba sai lips ɗinta da ya tsorawa idanu yana kallon yadda ta jiƙasu da yawo sai mutsawa suke a hankali, ɗauke kansa yay yace "A taƙaice TSARKI kashi biyu ne,Hadasi da Kabasi amma zan buɗa maki bayanin yadda zaifi, hope zaiki fahimta?" Kanta dake saman ƙirjinsa ta ɗaga alamar "eh" shafa sumar kanta yay shima yace "good" kana yay shuru yana tunanin irin duguwar maganar da zaiyi a wannan daren, ajjiyar zcya ya sauke kafin ya ɗura da faɗin.Ma’anar Tsarki

Ma’anar Tsarki A Larabci.

Tsafta Da Tsarkaka Daga Kazanta


Ma’anar Tsarki A shari’a

Kawar da kari da gusar da Najasa


Kashe ‿ Kashen Tsarki


1- Tsarki Na Voye

Shi ne tsarkake zuciya daga shirka da sabo, da duk wani abin da yake bata zuciya, babu yadda tsarki zai tabbata matukar akwai shirka a cikin zuciya, kamar yadda Allah ya ce, “Yaku wadanda suka yi imani ku sani cewa Mushirikai najasa ne, kada su kusanci masallaci mai alfarma daga wannan shekarar, idan kuna jin tsoron talauci to da sannu Allah zai azurta ku daga falalarsa in ya so. Haqiqa Allah Masani ne Mai hikima.‿ (At-Tauba : 28).


Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mumini ba ya zama najasa‿. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]


2- Tsarki Na Zahiri

Shi ne tsarkake jiki daga abubuwan da suke warware alwala da najasa, ya kasu gida biyu :


1- Tsarkin Kari

Kari shi ne : Abin da yake hana mutum yin ibadar da aka sharxanta tsarki a cikinta, kamar sallah, dawafi da waninsu. Kari ya kasu kashi biyu :Kari yana hana yin sallah.

- Qaramin Kari


Shi ne wanda yake wajabta yin alwala, kamar fitsari da kashi da sauran abubuwan da suke warware alwala. Tsarki daga kari yana samuwa ne ta hanyar alwala.


Allah ya ce, “Yaku waxanda kuka yi imani idan kun tashi za ku yi sallah, to ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwar hannu, ku shafi kawunanku ku wanke kafafunku zuwa idon sawu‿ (Al-ma’ida :6).Alwala tsarki ce daga qaramin kari

- Babban Kari


Shi ne wanda yake wajabta wanka, kamar janaba, haila, da wanin haka, ana tsarkaka daga gare shi ta hanyar wanka.


Allah ya ce, “Idan kuna da janaba to ku yi tsarki‿ (Al-ma’ida : 6).Tsrkin jiki

2- Tsarkaka Daga Najasa

Gusar da najasa wajibi ne, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki “Ka tsarkake tufafinka‿ (Al-Muddassir 4).


Da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Mafi yawancin azabar qabari daga rashin yin tsarki ne idan an yi fitsari‿. [ Ibn Majah ne ya rawaito shi]


Da faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku ya zo masallaci to ya duba takalmansa, idan ya ga qazanta ko najasa to ya goge, sannan ya yi sallah da su‿. [ Abu Dawud ne ya rawaito shi]Tsarkin jiki


Tsarkin wurin sallah


Tsarkin tufafi

Kashe-Kashen Ruwa


Na farko : Ruwa Mai Tsarki

Shi ne ruwan da najasa ba ta canza kamaninsa, ko xanxanonsa ko qanshinsa ba, kamar:


1- Ruwa Tsantsa

Shi ne ruwan da yake akan siffar shi da aka halicce shi da ita, kamar ruwan sama, ko qanqara, ko rava, ko kuma wanda yake gudu ne a bayan qasa, kamar ruwan teku, da qoramu da na sama, da rijiya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Mun saukar da ruwa mai tsarki daga sama‿ (AlFurqan : 48)


Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Yana saukar muku da ruwa daga sama don ya tsarkake ku da shi‿ (Al-anfal : 11)


Hakanan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana addu’a yana cewa: “Ya Allah ka wanke ni daga zunubaina da rava da ruwa da qanqara[ Qanqara: Ita ce qanqarar da take zuba ya yin saurkar ruwan sama.]‿. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]


Manzon Allah ya ce dangane da ruwan teku “Shi ruwa ne mai tsarki, kuma mushensa halal ne‿. [ Ahmad da Abu Dawud ne suka rawaito shi].


Numfashi ya sauke,bayan ya gama dugun bayani akan tsarki,a hankali kuma ya leƙa fuskarta, murmushi ya saki sbd fararan idanunta daya hango suna juyawa alamar dai tana fahimtar zancen sa,gyara kwanciyarsa yay a saman kujerar kafin ya lumshe idanunsa yana sauraran bugun zcyarsa dake fita da sauri da sauri,cikin ƙasa da murya kuma yace "sai kuma bayani akan WANKA en matan Uncle" ɓoye fuskarta tayi a jikinsa tana sakin wani sound "uhm...uhm"cije lips ɗinsa kawai yay kana yace "shima wanka kashi-kashi ne a musulunce,WANKA ya kasu kashi BIYAR sune WANKAN HAIHUWA,WANKAN JANABA,WANKAN JUMA'A,WANKAN SHIGA MAKKAH,WANKAN MUTUWA" 

shuru yay yana nazartar ta ya faɗa mata ko kuma ya rabu da ita,domin baya so ya faɗi abinda zata zo tana masa surutu akai,sai dai kuma maganar addini babu kunya ko ɓoye wani abu,domin shekarunta sunkai tasan komai, pouting lips ɗinsa yayi kafin yace.


Ma’anar kalmar "wanka" a larabci

Game abu da ruwa,

Wanka a Shari’ance

Shi ne gama jiki gabaxayansa da ruwa, a kan wata siffa kevantacciya, da niyyar bautawa Allah Mai tsarki

Abubuwan Da Suke Wajabta Wanka

1- Fitar Maniyyi

Maniyyi wani ruwa ne fari mai kauri, wanda yake fita tare da jin daxi, yana tunkuxar juna yayin fitowa, mutuwar jiki tana biyo bayan fitarsa, yana wari irin warin bara-gurbin qwai.

Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi wanka‿ (Alma’ida : 6)

da faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Aliyyu : “Idan ka fitar da ruwa to ka yi wanka‿ [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Fitar da ruwa ana nufin fitar maniyyi...,"da sauri Jalilerh ta ɗaga ta kallesa,bai kalleta ba ya haɗe rai hakan yasa dole ta maida kanta taci gaba da sauran sa.

Yace "misali shine


1- Idan mutum ya yi mafarki amma bai fitar da maniyyi ba, to babu wanka a kanshi, idan kuwa maniyyin ya fito bayan ya farka daga barcin to wajibi ne ya yi wanka.


2- Idan ya ga maniyyi, amma bai iya tuna yaushe ya yi mafarki ba, to wanka ya wajaba a kanshi saboda fitar maniyyin. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ana tava ruwa ne saboda fitar ruwa‿ [ Muslim ne ya rawaito shi] Ma'ana ana yin wanka ne don fitar maniyyi.


3- Idan ya ji alamar zuwan maniyyi daga gabansa, amma bai fito ba, to babu wanka a kanshi.


4- Idan maniyyi ya fito saboda wani dalili ko rashin lafiya ba tare da sha'awa ba, to babu wanka a kanshi.


5- Idan mutum yana janaba ya yi wanka, sai kuma maniyyi ya fito bayan ya gama wankan, to ba sai ya sake wankan ba, saboda yawanci yakan fito ne ba tare da sha'awa ba, amma abin da ya fi ya yi alwala.


6- Idan mai barci ya farka, ya ji danshi a jikinsa, amma bai san dalilin zuwanta ba, to xayan abu uku ne :


A) Ya tabbatar da wannan danshin maniyyi ne, to wanka ya tabbata a gareshi, ya tuna ya yi mafarki ko bai tuna ba.


B) Ya tabbatar wannan danshin ba maniyyi ba ne, to wanka bai wajaba a kanshi ba, hukuncinsa hukuncin fitsari ne, sai ya wanke)


C) Ya yi shakka, maniyyi ne ko ba shi ba ne? To a nan wajibi ne a kanshi ya yi kirdado, idan ya tuna abin da zai nuna masa cewa wannan danshin maniyyi ne, to ya bar shi a kan maniyyi ne. in kuma ya tuna abin da zai nuna masa cewa maziyyi ne, to maziyyin ne, in kuma ya kasa tuna komai, to sai ya yi wanka don fita daga savani da ruxu.


7- Idan ya ga maniyyi, amma bai tuna yaushe ya yi mafarkinsa ba, to wanka ya wajaba a kanshi, ya kuma sake dukkan sallar da ya yi bayan tashinsa daga barcinsa na qarshe.


2- Saduwa (Jima’i)

Shi ne haɗuwar gaban namiji da na mace, wato shigar kan gaban namiji zaya sanya cikin farjin mace, ko da kuwa bai zubar da maniyyi ba, saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم )“Idan kaciyar (namiji) ta shige kaciyar (Mace) to wanka ya wajaba‿ [Tirmizi ne ya rawaito shi].


3- Musuluntar Kafiri

Saboda “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya umarci Qaisu ɗan Asim ya yi wanka lokacin da ya musulunta‿ [Abu Dawud ne ya rawaito shi]


4- ɗukewar Jinin Haila Da Na Biqi

Saboda hadisin Aisha cewa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya cewa Faɗimatu ‘yar Abi Hubaish “Idan al’adarki ta zo, ki bar sallah, idan ya wuce ki yi wanka ki yi sallah‿ [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].


Hukuncin jinin biqi kamar hukuncin jinin haila ne da ijma’in malamai.


5- Mutuwa

Saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a hadisin wanke ‘yarsa Zainab lokacin da ta rasu ya ce,“Ku wanketa sau uku, ko sau biyar, ko fiye da haka, in kun ga akwai buqatar hakan‿ [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].


Yadda Ake Yin Wanka

Abin da yake wajibi a wajen wanka shi ne gama jiki gaba ɗayansa da ruwa, tare da yin niyya, koma yaya ya yi shi.


Sai dai abin da aka fi so ya yi koyi da siffar wankan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ), kamar yadda uwar muminai Maimunatu ta siffanta shi, ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sanya ruwa don yin wankan janaba, sai ya karkato abin ruwan da hannun damansa a kan hagunsa ya wanke hannayensa sau biyu ko sau uku, sannan ya wanke gabansa, sai ya doki qasa ko bango da hannunsa sau biyu ko sau uku, sannan sai ya yi kurkurar baki ya shaqa ruwa, ya wanke fuskarsa da sangalin hannunsa, sannan ya kwara ruwa a kansa, sai ya wanke jikinsa, sannan ya matsa gefe guda ya wanke qafafunsa. Nana Maimunatu ta ce, “Sai na kawo masa wani qyalle (hankici) amma bai karɓa ba, sai ya riqa share ruwan da hannunsa‿ [Bukhari ne ya rawaito shi].


- Yadda ake wankan a taqaice shi ne :


1- Zai wanke tafukan hannayensa sau biyu ko sau uku.


2- Zai wanke gabansa


3- zai doki qasa ko bango da hannu sau biyu ko sau uku.


4- Sai ya yi alwala irin ta sallah, ba tare da shafar kai da kunne ba.


5- Zai kwara ruwa a kansa


6- Zai wanke jikinsa gaba xaya.


7- Zai koma gefe ya wanke qafafunsa.


Bayan ya kammala ya sauke wata wahalalliyar ajjiyar zcya tare da jan numfashi yace "kinji wanan" shuru yaji sai kuma yaji saukar numfashinta mai zafi a saman ƙirjinsa, leƙawa yay yaga tuni bacci ya ɗauke ta,waro idanunsa yay da mamaki yana addu'ar Allah yasa dai duk taji me yace bai wahalar banza ba, miƙewa yay da ita a jikinsa tare da ficewa daga ɗakin,kai tsaye parlour ya nufa,a zaune ya samu Mama tana cin soyayyan nama da kuma lemo,kallo guda yay mata,ita kam baki ta saki tare da rafka salati tace "me zan gani yau?wai ɓatan nono a ƙirjin budurwa,zabgegiyar budurwa ka ɗauka kamar yarinyar goye,maza maza sauketa na gani"haɗe rai yay kafin yace mata "hannunki ne?" Cikin ƙufula tace "to sallamamme yimin rashin kunya,da matarka ka ɗauka ma da sauƙi" waro idanunsa yayi waje kafin yace "ok bari na ajjiye ta na ɗauke ki" zama tayi saman kujera tare da fasa kuka tace "wlh ba hali na ka ɗauka ba sai dai na dangin ubanka,amma tirrrr da mummunan hali irin wannan yanzu ni zaka ɗauka Jalalu?" Mummy dake saman upstairs ta danne dryar dake cinta kafin tace "Bobo maza jeka ƙwantar da ita kazo ka shige ka bamu waje" baice komai ba ya haura upstairs ɗin,yana zuwa ya nufi part ɗin su,babu wani haske ɗakin sai wani light blue bed ɗin ta ya nufa ya ƙwantar da ita,kana ya zare nata hijab tare da gyara mata kwanciyar, jikinsa yazo zamewa tayi sauri riƙesa tare da turo baki gaba,kai kawai ya girgiza ya ɗauki ƙaramin pillow ya saka mata da sauri ta rungome pillow,sosai yay mamaki yadda tasan daɗin jiki gashi shi duk lokacin da suka ɓata babu abinda yaji a kanta,tsaki yaja kana ya tofa mata addu'a ya rufeta da duvet,wajan Nihila ya ƙarasa tana jin zuwansa tayi saurin rufe idanunta,ba tare da wani tunani ba,itama yay mata addu'a kana ya bata light kiss a saman goshinta ya gyara mata kwanciya, remote ya ɗauka ya ƙaro masu gudun a.c kafin yaja Ƙofar ya rufe,da idanu ta bisa harya fice daga ɗakin kafin ta juya ta kalli Jalilerh wacce take bacci cikin nutsuwa ta rungume pillow,rufe idanunta tayi a haka bacci itama ya ɗauke ta ta.

Washegari,tun safe Jalal yabar gida sbd saura ƙwana guda Election,kusan a office ya ƙare yininsa,daga Wannan mutane suzo sai wannan suzo,haka yayta manyan baƙi wasu kuɗin compaign,wasu kuma abubuwan zaɓe suke karɓa, Jafar kuma yana can shida Prince Hassan suna ta shiga local government da ƙauyika, Abbou ma ba'a barsa a baya ba dukkan abinda yake gani zai taiamy ɗan nasa dashi shi yake, kuɗi kowa ya fitar babu adadi,haka Irfan Imran kowa da nasa ɓangaren, Mummy da Mameey suma a gida sukai taran mata aka cika sosai yadda Hajiya Atine, Aryan kam yana ɗaki abinda yana sharar bacci sabida bashi da matsala da wani zaɓe a cewarsa, Governor Mubarak Yahya cibo hankalinsu ƙwance yake shida masu mara masa baya da kuma Lamir,domin sun tabbatar a wannan karan plan ɗinsu bazai taɓa barin Dr/Muhammad Jalal Kabeer bobo ba,Lamir ya ajjiye juice ɗin dake hannunsa yace "ai wlh da zarar an saki wannan vedio kare bazai iya binsa ba,badai sakarar ɗan uwan nasa na ɗura sa bisa hanya ba,to Tabbas nan da jimawa zance ya turo min da vedio'n ta whatsapp, mu kuma zamu sakesa matsayin breaking news kaga shi kenan mun tashi hankali jama'ar IBADAN,zamu sanya masu shakku da wasi-wasi a zuƙatansu,kasan mene zai faru ƙarshe?"gaba ɗaya suka ajjiye juice ɗin hannunsu suna kallonsa kafin Hon Faisal Lawan yace"wannan kitimurmurar ai naka ne,tayaya zamu sani?"dry Lamir yyi kafin ya tsuke bakinsa yace "daga ƙarshe hukumar inec za tace the election was cancelled"gaba ɗaya suka saka dry hadda riƙe ciki, Wani mutum a cikinsu wanda ake cewa Baba Tunde yace "kai Lamir you're so selfish,kai mugune exactly abinda nake imagine kenan" ya faɗa cikin gurɓtacciyar hausarsa,Hon Faisal Lawan yace "kaga ana haka za'a ƙara tabbatar da Ur excellence a matsayin cikakken Gwamnan jihar Ibadan" gyaran murya Governor Mubarak Yahya cibo irin a dole yama riga daya zama Governor lokacin kawai yake jira,yace "idan harshashenmu ya zama gaskiya kowa ni kaɗai nasan me zan maku,albashin na kune,zan dauwama ina maku hidima,and tuggun farko da Jalal zai fuskanta rabashi da wannan ƙabilar da zanyi kuma saina tabbatar maku da magana ta gsky ce"

Jalal bai dawo gida ba sai wajan 12:30,a hankali drever yayi parking motarsa sai kuma motocin securities ɗinsa,yana parking wani security ya buɗe masa ƙofa,cikin nutsuwa yake tafiya hannunsa riƙe da babbar rigar sa daya cire a hanya,ya ɗan tura hular kansa baya,gaba ɗaya a gajiye yake bama gajiyar ke damunsa ba sai yadda yake yawon faɗuwar gaba wacce bai san menene dalilin afkuwarta ba,murya can ƙasa yay sallama, Mummy na ganinsa ta miƙe da sauri tare da amsar rigar hannunsa sai jera masa sannu take,da idanunsa kawai yake kallonta ya kasa cewa komai, ɓata fuska tai tamkar zatai kuka tace "wanne irin abune wannan wai?ace tun safe daga fita sai yanzu?ina da tabbacin ko abinci baka ci ba" ta faɗa tana ɗura hannunta a cikinsa,zaro idanu waje tayi kafin tace "what ina zuwa zauna a parlour ka jirani" Mama ta amshe zan can da faɗin "ke kuma saiki kama gabanki tunda ya dawo,algugguma ka ganta nan ta hana ranta sakat sbd baka dawo gidan ba,daga ƙarshe ma kuka ta sawa Mutane"ta ƙare maganar tana nuna Jalilerh wacce take tsaye tun shigowar sa,yana da inda Mummy ta ajjiye sa ya ɗaga gajiyayyun idanunsa ya sauke a kanta,cikin Sa'a suka haɗa ido,da sauri ta janye nata idanun kana ta haura upstairs tana goge hawayen idanunta, idanunsa yaja ya rufe ba tare da yace wani abun ba,kallonsa Mama tayi tace "to Mijin yaya ake ciki ne yanzu?" Shuru yay mata dan baya jin zai iya mata amsa,dan ko yawon dazai haɗiya a bakinsa babu,yana nan zaune Mummy ta fito daga kitchen hannunta riƙe da wani babban tray,tana zuwa ta ajjiye saman carpet kana ta kallesa tace "sauko ƙasa" bai mata musu ba ya sakko yana sakkowar ya zame rigar dake jikinsa,ya rage sai farar singlet a jikinsa,dugwayen ƙafafunsa ya miƙe har ƙarar gajiya sukai,duk abinda yake akan idanun Mummy sosai take tausayin ɗan nata musamman yau,tasan dukkan abinda daza ta basa a yanzu ba lalle yaci ba,dambun shinkafa wanda yaji zugale da gyaɗa da kuma manyan albasa,yasha kayan ƙamshi da zallar hanta ta zuba masa a plat,sai kunun gyaɗa mai zafi da zuba masa madara kana ta haɗa masa mug,sai kuma ƙwaɗon zugala data haɗa masa yasha tomato da albasa da kuma ƙwai,da haɗaɗɗan ƙuli,gaba ɗaya ta jere masa a gabansa,kamar yaro haka Jalal ya kwaɓe fuska tare da langwaɓar da kansa gefe, cikin wata muryar sangarta yace "Mummy na gaji bacci" bata kulasa ba taja ƙafarsa ta ɗura saman cinyarta ta fara matsa masa su tare daja masa yatsun ƙafarsa,zuro Mama tayi masu da idanu,domin a wannan lokacin tunanin mahaifiyar Jalal ne fal a Zcyarta,ko tana raye ko babu uhhhu,bayan Mummy ta matsa masa ƙafar ta miƙe tsaye tare da faɗin "bari na kira daughter, ƙilan taci abinci yanzu" harya buɗe baki zai magana sai kuma yay shuru sbd wayarsa da yaji tana ringing,kallon makeken screen ɗin wayar yay yana sunan Jabir na yawo akai yay,rasa waye Jabir yay har wayar ta yanke yana kallon screen ɗin,a haka wani kiran ya shigo, ɗauke kai yay tare da ɗaukan spoon ya fara cin ƙwaɗon zugalan a hankali,yana zaune Aryan ya fito da sauri daga part ɗinsu yay waje,da sauri Aryan ya buɗe wayarsa da tun ɗazo take a rufe,yanzu haka yazo buɗewa wane domin ya tura wasu photona da vedio'n,fuskarsa fal farin ciki ya buɗe wayar sai dai abin mamaki wayar na gama buɗewa yaga ta nuna an mata waifin,ta nuna restore...A tsorace Aryan yake bin wayar da kallo, lokacin daya tabbar komai na kan wayar ya tafi yasa hannu ya dame kansa, zcyarsa cike da ƙunci yana mmkin yadda hakan ta kasance,yasan cewa rabonsa da wayar tun jiya da daddare sabida killace tan da yay,yana jiran lokacin da Baaba Lamir zai masa magana ya turo masa,sai gashi yanzu babu komai akan wayar ya rasa muhimman abubuwa bayan photonan da vedio'n,cikin takaici ya koma cikin gida,yana shiga ya shige part ɗinsa, Jalal na zaune yana cin ƙwaɗon zugalan ko kallon Aryan bai ba, cikin nutsuwa yake komai,ganin yana zaune kuma ya tabbatar Mummy baza ta barsa ya tashi ba,kawai sai data ya shiga network,kai tsaye twitter ya shiga ya fara duba news harya zo tweet ɗin wani mutum daya sanya photon Jalal a ƙasa kuma yasa _Garkuwar al'ummar gari Ibadan,dukkan farin ciki da kwanciyar hankali su tabba a gareka,in sha Allah garin Ibadan naka ne,nasara takace,kai ne jagoran mu ur excellence Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo_ Murmushi ne ya subuce masa lokacin da ya ga Retweet ɗin mutane sama da 5k,bayan ya gama kallon Tweet ɗin daya samu lokaci,ya shiga wajan Tweet shima ya fara typing kamar haka _Allahamdulillah,Dukkan yabo ga godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala daya bamu a ron dai da kuma lafiya kuma yake shirin nuna mana gobe,wacce ta kasance rana mai muhimmanci a gareni ta kuma dukkan masoyina,bana da wani abu dazan birgeku dashi ko zan kyautata maku dashi a halin yanzu,nasan soyayyar ku gareni daga rabbil samawati take, soyayya kuma domin Allah itace soyayya,to jama'a ban taɓa nema ba,kuma ban san yaya daɗinsa ko wahalarsa yake ba,ni nasan ina nema da dukkan lafiya ta,ilimi na,arziƙina,ina fatan kuma zaku nuna min zallar soyayya ta hanyar sanyamin albarka da kuma kaɗamin ƙuri'unku masu albarka kuma wanda zasu zamu Garkuwa gareni, ku/ki/ka tashi maza da mata aje a fita zaɓe domin tabbatar wa kanku kun zaɓe dai-dai da ra'ayinku,Ni Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo nake cewa ƙuri'ata ƴan cina_

Yana gama rubuta yaka ya saki Tweet (posting na twitter shi ake cewa Tweet, comment kuma Retweet) tun kafin ya fita COMMENTS ɗin mutane suka fara rubdugu wasu na kurar wasu, lokacin guda aka haɗa masa COMMENTS sama da 2k screenshot yay na Tweet ɗin ya shiga account ɗinsa na I.G nan yaga flowers ɗinsa sun ƙara yawa fiye da ko yaushe,shiga yayi ya ɗura screenshot ɗin,tun kafin ya fita nan ma aka fara like and COMMENT, comment na farko ya bashi dry ina wata take cewa

_Daman ka iya hausa?ko daman kai bahaushe ne i through kai Balarabe ne, serious ina son ganinka a zahiri ba photo ba,gani nake kamar photon na rage maka ƙyau,all the best_

Murmushi yay lokacin daya gama karanta comment ɗin kana ya kashe datar wayar,yana nan zaune Mummy ta sakko dwonstrais ɗin hannunta riƙe dana Jalilerh, ɗan waro manyan idanunsa yayi sbd lokacin ɗaya tayi amma ace har yanzu batai bacci ba,suna zuwa dai-dai wajansa ya ɗauke kansa,zaunar da ita tayi a kusa dashi tace "maza kici abinci idan ba su kike ranki ya ɓaci ba,shima ba kiga yaci ba saike za kiƙi ci"ta faɗi hakan tana zuba mata dambun shinkafa a plat,da mmki Mummy ta kalli Jalal,shima da sauri ya rufe idanunsa sbd yasan abinda za tace dashi tace "bobo yaushe na zama abokin wasanka?" Juya idanunsa yay ba tare kuma da yace komai ba,zama tayi tsakaninsu tare da haɗe rai,ba tare kuma da tace komai ba ta wanke hannayenta,a nutse tayi bisimillah ta ɗebo abincin ta nufi bakin Jalilerh dashi,yadda Mummy ta haɗe rai babu alamun wasa yasa dole ta buɗe bakinta ta amshi abincin,shikam Jalal yana sane ya rufe idanunsa wai ko zata ƙyalesa,amma tana ɗebo abincin tasa hannu ta ɗaka masa doka a shoulder ɗinsa,da sauri ya buɗe idanunsa yana kwaɓe fuska, Jalilerh tsayawa tayi da cin abincin tana kallonsa sbd bata taɓa ganinsa yana shagwaɓa ba,kodan bata fiya tsayawa a wajansa idan suna tare da Mummy bane ohuuu?sosai yay mata ƙyau a idanunsa gaba ɗaya ya shagwaɓe fuska yana faɗin "Allah Besty I'm full" dake something idan yana buƙatar wani abu haka yake ce mata ba,hararsa Mummy tayi tace "I'm not ur Besty,gaba ɗaya me kaci daza kace ka ƙoshi? nasan kuma haka zakai gobe kai kafin so kaita zama da yunwa kamar ƙaramin yaro?banda ma Ubangiji ya yanka da auki ai baza ka gano ba sbd siranta" ta faɗa tana nufar bakin Jalilerh ta abincin da sauri ya janye hannun Mummy daga bakin Jalilerh ya nufi nasa bakin yana Murmushi doka hannunta ya tura cikin bakinsa kana ya zare hannun yana tauna abincin, kwaɓe fuska Jalilerh tayi tare da turo baki tace "Mummy" kanta Mummy ta shafa tace "rabo dashi daughter,tunda abin hulaƙanci ne saikin ƙoshi zai ci"gwalo Jalilerh tai masa, kallonta yayi tare dajan idanunsa ya lumshe,haka Mummy ta kasance cikin su idan ta bawa Jalilerh saita bawa Jalal,duk da cewar itama yunwar ta keji amma burinta kawai taga yaci abincin,bayan sun gama Jalal ya ware idanunsa kana ya riƙe hannun Mummy yace "wait...."ya faɗi hakan shima yana ɗiban abinci a hannunsa, riƙe haɓa tayi tace "nikam kaka ka maidani ko mene?" bai ce komai ya nufi bakinta da abincin,dole ta tsaya ta amsa,sai da ƙoshi ya rabu da ita, miƙewa tayi ta nufi kitchen tana faɗin "daughter maza jeki ƙwanta kada ki manta da addu'a" idanunta ne ya cicciko da ƙwalla ganin Jalal bai kulata ba, miƙewa tayi zata bar wajan yay sauri kama hannunta juyawa tayi tana zaro idanunta waje,shima nasa idanun ya zaro yana ɗan juyasu kafin ya miƙe tsaye, hanyar kitchen ya kala yaga Mummy bata fito ba,da ɗan sauri ya rungome ta tare da bata light kiss a goshinta kafin ya saketa ya juya ya nufi part ɗinsa,da ido kawai Jalilerh ta bisa,saurin juyawa tayi sbd munsharin da taji, Mama ce ƙwance ta buɗe baki sai sharara munshari take,da ɗan saurin da take tunanin tana dashi ta nufi upstairs,ganin hakan yasa Nihila tayi sauri juyawa ta shige cikin bedroom ɗin tana shiga ta faɗa saman bed ta rufe jikinta da duvet a dole bacci take.

A kasalance Jalal ya ƙarasa part ɗinsa yana zuwa ya zare wandon jikinsa da singlet ɗin,ya rage daga shi sai boxer, bathroom ya shige ya sakarwa kansa shower sosai yaji daɗin ruwan,bayan yay wanka ya ƙarasa wajan sink ya wanke bakinsa tare da ɗaura alwala,sanye da towel ya fito iya waist ɗinsa,yana zuwa ya nufi wajan dressing mirror ya shafa lotion sbd jin da gari yay yana sauyawa,comp yasa ya taje sumar kansa kafin ya fesa parfume,wasu fararan kayan bacci ya ɗauka ya sanya kana yay addu'a ya ƙwanta tare da ƙaro gudun a.c,kana ya rage hasken ɗakin,babu jimawa bacci ya ɗauke sa.

_Election day_

Dukkan abinda aka sawa rana sai yanzu,idan kaga abin baizo ba to tabbas ba'a sanya masa rana ba,abinda ake jira wajan shekaru 2 da rabi yau gashi ubangiji ya nunawa duk wanda ya keson ganin ranar,ranar da mutanan gari sukaci burinta, ranar da magauta suka shirya yin zaluncin da suka daɗe suna shiryawa,ba wata rana bace face ranar Zaɓe,ranar Governor Mubarak Yahya cibo yake jin ya gama cika burinsa na zama Gwamnan jihar Ibadan,ranar da zai mulki dubban jama'ar gari,a Wannan rana kuma Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo yake tunanin zai samu cikar muradin sa,burinsa na shekara da shekaru zai cika,farin muradin sa zai tabbatar yayinda a ranar yake saka ran sauke nauyin al'ƙawari daya ɗauka wa kansa na zama Gwamnan jihar Ibadan (Who win between two of them, Governor Mubarak Yahya cibo or Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo?).

Dukkan local government da ake zaɓe da ita ta gama cika da mutane,maza da mata yara da manya,tsofaffi da samari,kota ina mutane zuwa suke suna kaɗa ruwan ƙuri'u,kowa kuma da mazaɓarsa,haka zaɓe ya fara wakana babu tashin hankali ko kuma wasu hargitsi.

Governor Mubarak Yahya cibo ne shida mayan amintattunsa a wani keɓantaccen waje suna tattaunawa akan plan ɗin da sukayi nisa a cikinsu,gyaran murya yayi yace "ina ganin zuwa yanzu lokaci yay da zamu juya masa tunaninsa,hutunsa ya ƙare farin cikinsa ya ƙare,kwanciyar hankali gidansu ya ƙare,a cikin ƙaramin lokacin zamu ruguza komai nasa" dry Lamir yyi yace "yanzu na samu Labarin zaice ya kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa" Hon Faisal Lawan yace "kaga abin zaifi dai-dai kenan,yana shiga cikin jama'a mu kuma saimu watsa labarai cikin sauƙi jama'a zasu fara la'antarsa"gaba ɗaya suka sanya dry,wayar Lamir ce tayi ƙara hakan tasa ya tsaya dry yay yace "Au,au,au shegen ne,bana gaya maku ba?"ya faɗa yana picking call ɗin kafin daga can ɓangaren Aryan yace "Baaba Lamir na maka magana whatsapp ka duba"Lamir yace "yawwa yaro na,bari na duba yaya zaɓan?" Aryan yace "Allahamdulillah,yanzu na dawo su kuma mutan gidan zasu fita" shuru Lamir yay kafin yace "fatan muka marawa baya?"Aryan yay dare yana mai danne zafi da raɗaɗin da zcyrsa take masa yace "haba Baaba Lamir kasan cewa zuwa yanzu babu wanda nake ganin baƙinsa irin Yaya tayaya kake tunanin zanyi abinda zai ƙara masa masoya?tayaya zanyi abinda zai kawo masa ci gaba never,babu wanda na tsana a yanzu sama dashi dan haka ni naku ne dukkan abinda kuke buƙata daga gareni ni mai biyayya ne indai zan samu cikar muradin a"dry Lamir yyi kafin yace "shikenan ka ɗauka ka samu wannan yarinyar,yanzu muna cikin jama'a dukkan abinda yake ƙasa zan kiraka" daga nan sukai sallama.

A hankali Jalal ya fito daga cikin ɓangaren sa,yana sanya cikin wani Maroon ɗin boyal mai manyan zane kuma shara shara,domin har farar singlet ɗin sa ana gani,sai kuma babbar riga irinta boyal ɗin,kana baƙar hula ta tangaran,sai half covert shoe shima baƙi, hannunsa sanye cikin agogon warist mai ƙirar iphone,ya sanya farin bluetooth a kunansa,sai ƙamshi yake bazawa tamkar ranar aurensa,yana fitowa main parlour ya samu dukkan ƴan gidan suna jiransa, Mummy na sanye cikin wani Orange ɗin lace mai manyan flowers masu ƙyau,ta sanya farin mayafi a kanta,sai Mameey itama cikin milk ɗin lace irin na Mummy,sai kuma Abbou shi kuma ya saka shadda gezner,shima maroon color,gefe ya kalla yaga Nihila tasa wata rantsatsiyyar abaya black mai milk ɗin stones sai sheƙi take hannunta riƙe da waya sai faman dannawa take,tana ƙara yaɗa manufarsa da kuma tayin jama'a na suka zaɓi Yayan nata, idanunsa ne ya sauka akan Jalilerh wacce yaga tai masa ƙyau sosai,ta saka light blue ɗin lace mai Maroon touchs sai siririn mayafinta shima Maroon da kuma flat shoe shima Maroon,hannunta riƙe da hisilin muslum,babu komai fuskarta sai lipstick tayi fresh kamar amarya,sai ya kasance ita dashi kamar sunyi anko,kallo guda yaywa ahalin nasa yaji wani farin ciki ya rufe sa gefe guda kuma na zcyarsa yana buga tare da faɗuwar gaba,haka dai ya wanzu yana azkar a ransa, Abbou ne yace "muje lokaci naja"Mummy tace "Mama mun tafi" kallon Mummy Mama tayi tace "to Allah ya kiyaye" gaba ɗaya suka fita Mummy still tana cikin parlour'n kamar wacce tayi mantuwar wani abun, Jalal ne ya dawo baya yaja hannunta yana amsa addu'ar da Mama keyi masa,Babbar motarsa Jalal ya shiga,ya zauna mazaunin drever, Jalilerh na gefensa baya kuma Mummy ce, ɗaya motar kuma Mameey ce a gaba Abbou mazaunin drever sai Nihila a baya,sai kuma motocin securities wajan guda uku suna mara masu baya,a haka suka fice daga cikin gidan Baba habu nayi masu fatan nasara.

A haka suka ƙarasa mazaɓarsu, kasancewar duk a mazaɓa guda za suyi zaɓen,nan waje ya hargitse kowa yana murna yaga Jalal bobo,da ƙyar securities ɗinsa suka nema masu waje saida kowa yay zaɓen sanna yayi, Nihila na zuwa aka rufeta mutane suna karɓar rabonsu haka dai ta dinga raba masu kuɗin jakarta,wani ne ya hangi Jalilerh yace "laaa ga matarsa can ai kuzo muje wajanta"tana tsaye sai raba idanu take domin bata saba ganin haka ba taji ance "Hajia muna maku fatan nasara Allah ya taimaki mijinki in sha Allah saiya haye" rasa gane maganarsu tayi,sai tunanin waye mijinta take kafin tai magana yaja hannunta zuwa cikin mota yace "baki iya amsa addu'a bane?" Turo baki tayi bata ce komai ba,a haka suka shiga mota suka nufi hanyar gida,cikin nutsuwa yake driving yana kallon Mummy ta madubin motar data zabga tagumi,ana haka wayarsa ta fara ƙara ganin sunan Jafar na yawo yasa ya danna picking kana yace "uhm" Jafar daga can ɓangaren ya share zufar data karyo masa yace "kana ina yanzu haka?" Da rashin fahimta Jalal yace "hanya" Jafar ya ƙara kallon jama'ar gabansa na wajan zaɓe yace "maza kuyi gida,sannan ku baza securities a layin"Jalal na ƙara giyar motar yace "lafiya?" Jafar kamar zai kuka yace "Jalal bazan iya faɗa maka da bakina ba,amma ka kunna redio nima ina wajan zaɓe ake sanar dani wannan tashin hankalin" Jalal baice komai ya katse kiran kai tsaye ya kunna redio'n dake motar lokacin 12:30 an fara labarai,yana kaiwa yaji ana faɗin 

_Kudin labaran kenan yanzu zaku saurari cigaban labaran..,A yanzu ne muka samu cikakken labari daga bakin wani mutum wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa,inda yake faɗin, Munata murna zamu samu shugaba adali kuma mai asali,ashe shima tumun dare ne domin bincike ya tabbatar mana uban Governor Muhammad Jalal Kabeer bobo bashi da asali kawai yayi dirar mikiya a garin namu na Ibadan,abu mara daɗi an ƙara tabbatar mana shi kansa Muhammad Jalal Kabeer bobo ba'a san inda mahaifiyar sa take ba,a taƙaice ma ance mahaukaciya ce ta haifesa..._

Bai ƙarasa jin labaran ba ya kashe redio'n lokacin guda kuma jikinsa ya fara rawa a zafafe ya juya ya kalli Mummy wacce take baya,a zaune ya ganta idanunta sun firfito waje gumi sai yanko mata yake,kana ya juya ya kalli madubin motarsa nan ya hangi motar Abbou tana biye da tasa, Jalal ƙasa magana yay gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya brain ɗin sa ta daina aiki,a hankali kuma lakar jikinsa ta zare ya fara ganin duhu a cikin idanunsa,yadda tunaninsa ya tsaya haka hannunsa ya zare daga kan motar,motar tafiya kawai take Jalilerh tsoro da firgici ya hanata koda mutsawa musamman da taga kan motar yana sauka daga tsari,ganin inda motar tayi tasa ta fasa uwar ƙara tare dayin jikin Jalal wanda ya kifa kasa ƙasa a kuma dai-dai nan motar ta daki jakin baban gida cikin rashin Sa'a motar ta tuntsira tare da mirgina wa sau biyu a tsakiyar titi....

Sau wajan uku motar na mirginawa tsakiyar titi, Abbou na cikin motarsa yay saurin yin baya cikin tashi hankali tsoro firgici dana sani, da suka masa rufdugu lokaci guda, Nihila tuni ta fasa ihu ta fara kiran sunan Mummy, Mameey kam tashin hankalin abinda ke faruwa yasa ta kasa kwakkwaran mutsi sai numfashi take saukewa, Abbou yana parking a gefen titi yama rasa me zai yi gashi dai a zahiri motar yake amma gaba ɗaya tunaninsa baya ga motar,can yay ƙarfin halin ƙarasawa wajan motar domin ba ƙaramin tension yake ciki ba,a lokacin da zaka tsaga jikinsa ba lalle jini ya fita ba, kasancewar ranar zaɓe ne sai ya tashi babu kowa a titin domin ko babura basa hucewa balle motoci,wayarsa ya ɗauka yama rasa wacce number zai kira,kawai yay shahada ya dannawa ambulance kira,tare dayi masu ƙwatance,suna nan tsaye domin ba zasu iya mirgina motar ta dawo dai-dai, ba wajan 20minutes Abbou ya fara jiyo jiniyar ambulance ɗin,kafin cikinar 22minutes ambulance ɗin sun ƙara su wajan,dasu da Abbou aka haɗu waje guda aka tayar da motar,da sauri Abbou ya nufi side ɗin Jalal yana zuwa ta wajan glass ɗin daya fashe ya zura hannunsa tare da buɗe murfin motar, zuciyarsa ce ta bada sauti da ƙarfi dammmm sbd ganin Jalal da yay zaune akan kujera ya kifa kansa akan motar,cikin sauri Abbou ya shiga kukawar ɗaga Jalal wando ko mutsi bayayi,sai daya ɗaga sa sannan yaga Jalilerh ƙwance a jikin Jalal ashe daman Jalal ɗin shiyasa rufeta da jikinsa,gaba ɗayansu babu mai numfashi a jikinsu kuma ko ɗigwan jini babu a jikinsu,gaba ɗaya aka fito dasu daga cikin motar zuwa cikin ambulance ɗin,gaba ɗaya kan Abbou ya kulle yama manta tare da Mummy suke gaba ɗaya tunaninsa tana motarsa,dai da wani police yace "aƙwai wani a back seat ne?" Da sauri Abbou ya dawo wajan motar shida wasu ƴan sanda kasa buɗe ƙofar yayi sbd jinin da yaga yana zuba ta ƙasan murfin motar,suna motar murfin motar suka samu Mummy ƙwance jini na zuba ta gefen kanta a gani glass daya caketa a wuya,da sauri aka ɗura ta a kan bed zuwa cikin ambulance ɗin, Nihila na ganin Mummy ta ƙara fasa wani ihun tana kiran sunanta tare dayin wajanta,da sauri Abbou ya riƙe,gaba ɗaya aka sanyasu a ambulance sai zuwa babban asibitin dake IBADAN,kasa driving Abbou yayi sai wani daga cikin police ɗin ne yaja motar zuwa asibitin.

Lamir suna zaune shida Governor Mubarak Yahya cibo da Hon Faisal Lawan da wasu manyan mutane,suna zaune suna tattaunawa akan yadda zaɓen ke wakana da kuma alamomin masara da suka gani,wayar Hon Faisal Lawan ce ta fara ƙara yana ɗauka yace "hello.."shiru yay kafin yace "what..?ok bari mu kunna"yana faɗin hakan ya kashe wayar yace "kirana akai wai mu kunna redio an saki breaking news" Lamir yace "kai ma dai da wahala,kasan ko labarin mene" Hon Faisal Lawan yace "bari dai muji"ya faɗi hakan yana kunna redio'n ƙaramar wayarsa,babu jimawa aka fara labaran kamar yadda aka gaya masa,da sauri Lamir ya miƙe yace "what..? ubanwa ya faɗi wannan abun?" da mamaki suke kallonsa kafin Governor Mubarak Yahya cibo yace "kai mene naka?koma waya faɗa ai ya ƙara taimakon mune" cikin ɓacin rai Lamir yace "waya fada wannan labarin a cikinku?idan kun san kuna da hannu ko faɗa min wanene?" Hon Faisal Lawan yace "haba Lamir,babu wanda yabar a cikinmu gaba ɗaya muna tare,sannan dukkan abinda ake shiryawa ai dakai ake komai,munsan cewa munyi niyyar watsa photo nan,amma kuma ba'a samu ba,banda haka ai babu abinda muka tsara wanda kai baka sanshi ba" da kallo kawai ya bisu kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ya fice daga cikin gidan.

Mama kam tana zaune ita ɗaya sai mai aiki Laure wacce tace tazo ta zauna wajanta kafin masu gidan su dawo,tana dai zaune amma minti kaɗan zata miƙe ta leƙa waiko sun shigo, ɓangaren Aryan bawai haka nan yaƙi zuwa wajan zaɓe ba, tunda safe ya tashi da kasala da faɗuwar gaba yanzu ma yana ƙwance saman bed sai juyi yake kamar wanda bai da lfy,Imran Irfan da Jafar duk suna waje guda wajan zaɓen,ga dai alamomi nasara suna gani amma fuskokin su gaba ɗaya babu walwala,gudanar da aikin zaɓen suke babu kuzari a tare da su, Ambulance ɗin na parking a harabar asibitin nurses suka ƙarasu wajan da gadon marasa lfy, ɗaya bayan ɗaya aka dinga ɗura su akai, Nihila da Mameey banda kuka babu abinda suke, Abbou kuwa yana baka taɓa gane halin da yake ciki, lokaci zuwa lokaci yake danne saitin zcyarsa, manyan likitoci suka rufo akansu.

Lokaci kaɗan Labarin accident ɗin Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo da iyalansa suka karaɗe Garin Ibadan da kewayanta, cikin tashin hankali Jafar da Imran da Irfan suka ƙarasu wajan,kallo guda zakai masu su baka tausayi,babu jimawa shima Lamir ya ƙarasu wajan,har yanzu babu wani labari gane da halin da suke ciki domin babu likitan daya fito,Wajan 1:40 Alhaji khamal mahaifin Nusaibat shida matarsa Hajia Atine suka ƙarasu wajan domin ko Nusaibat basu faɗawa ba, lokacin guda asibitin ya cika da mutane,sai da securities ɗin Jalal suka fara kurar mutane ya rage family ne kawai a wajan,misalin 3 dai-dai likitocin suka fito daga cikin emergency room ɗin sai share zufa suke,da sauri Abbou dasu Jafar suka miƙe tare da faɗin "Dr wanne hali suke ciki?"goge glass ɗin hannunsa babban likitan yay kafin yace "muje office tukunna" gaba ɗaya suka mara masa baya banda Alhaji khamal da Irfan wanda ya kasa mutsi dan fargaba,kujera Dr yaja ya zauna tare da nunawa Abbou waje ya zauna,amma sam Abbou bai san me Dr yake cewa ba hankalinsa yana wani wajan daban,ga wani sarawa da kansa yake yana runtsa idanunsa sai yaga abubuwa da yawa suna maza gizo a cikin idanunsa, Jafar ne ya kama hannun Abbou ya zaunar da shi a kan kujera kana yace "Dr yaya ake ciki ne Please,ka faɗa mana halin da suke ciki ka riga kasan ko waye shi a wannan garin,so Please ka faɗa mana muma hankali ya kwanta" jinjina kai Dr yay kafin yace "Allhamdulillah,da farko wajan shi Ur excellence ɗin da sauƙi,ya samu tension ne,wanda shine yaja masa ɗaukewar numfashi tun kafin faruwar accident ɗin,sannan ita yarinyar tsoro ne yay mata yawa sai kuma ɗaukewar numfashi data samu wanda yaja mata ta shiga duguwar suma,to duk su biyun nan da wani lokaci zasu farko..,"shuru yyi yana sauke numfashi ba tare da kuma da yace komai ba,Imran ne yaja numfashi yace "Mummy fa?" Kallon Dr Abbou yay abinda yake ta son cewa kenan sai kuma Allah ya taimake sa,baya Dr yayi yana sauke ajjiyar zcya kafin yace "ban san yaya zance maku ba,amma dai ita sai dai mu bita da addu'a" zcyar Abbou ce ta buga da ƙarfi kafin ya tattara nutsuwar yace "kamarya?" Jafar yace "kai mana maganar da zamu fahimta Dr kasa zuƙatanmu cikin zullumi da kuma fargaba" Dr ya fesar da numfashi kafin yace "Ta samu buguwa a kanta, ma'ana kanta ya fashe,sannan ancire mata wani ƙarfe a cikin wata sanadiyar cakarta da ƙarfan yay ya tsinka mata hanjin cikinta,abu mara daɗin kuma glasses ɗin daya caki wuyanta harya taɓa maƙoshinta"Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"kafin Jafar yace "yanzu Dr mene condition ɗin da take ciki?" Fesar da numfashi Dr yayi kafin yace "she's critical condition,amma in sha Allah everything will be fine ok"da ƙyar ya sauke ajjiyar zcya kafin ya saita numfashinsa yace "zamu iya ganinsu yanzu?"miƙewa Dr yay yace "of course"gaba ɗaya suka miƙe tare da bin bayan Dr kowa da abinda yake tunani a ransa,wani ward suka nufa kai tsaye Dr ya shiga wani special side,wajan part biyar ne a side ɗin,room ɗin farko suka tarar da Mummy ƙwance an juna mata Oxcygen ta cikin bakinta gefen kanta an naɗeshi da bandeji haka ma wuyanta, cikinta ba an sanya anduga da filasta,kana an rufe jikinta da wani green ɗin abu, ɗakin sai ƙarar na'urori gefen hannunta an maƙala mata drip yana shiga a hankali, ƙirjinta dake ɗagawa shine kawai yake nuna tana raye,da sauri Abbou ya juya domin bazai jure ganin halin da matar tasa take ciki a halin yanzu ba,cikin zallar tausayin halin da take ciki Jafar yake kallonta yana jin ƙwalla na tarar masa a idanunsa, juyawa yay ya fita a room ɗin, Imran na fita yay ya rufe ƙofar,daga nan wajan Jalilerh suka shiga itama tana ƙwance an saka mata Oxcygen sai drip,hucin numfashin dake fita ta hancinta shike nuna tana raye,amma babu kurjewa ko ɗaya a jikinta,daga nan suka nufi room ɗin da aka saka Jalal a ciki,tun daga nesa suka hango farar fatar jikinsa data ƙarayin jaaa,ga wani haske data ƙara tai fresh,da sauri Abbou ya ƙara wajan Jalal yana zuwa ya zauna tare da kama hannunsa sai a lokacin wata ƙwalla ta sauka daga cikin idanunsa, ƙwance yake flat ko riga babu jikinsa sbd wani gumi da yake haɗawa duk da sanyin a.c dake kaɗawa a ɗakin,cikin nutsuwa yake fidda numfashi,fuskarsa ta faɗa lokaci guda kamar wanda ya shekara yana jinya,ga yadda sumar kansa ta hargitse,babu abinda aka juna masa sai drip da injection da ake masa,cikin ƙasa da Murya Abbou yace "am so sorry Muhammad,nina ja maka laifi nane,dana san wanene ni da tuni na bai yana gsky,bana da ikon faɗin komai akai na sbd sa gske ban san yaya nake ba,ina da asali bana dashi ban san komai a kaina ba Muhammad,ka yafemin kada kalleni da laifin da banawa ba,ban taɓa dana sani irin na yau ba,ban taɓa ƙunci da shiga damuwa irin na yau ba, Tabbas ni me laifi ne,bansan da wanne baki zanyi maka bayani akan wanene kai ko kuma wacece mahaifiyarka,dan Allah ka gafarta min Muhammad" ya faɗa yana ƙara ƙanƙame hannunsa,wasu siraran hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Jalal,cikin rawar jiki kuma ya riƙe hannun Abbou'nsa nasa still hawaye na kwarara a idanunsa, Jafar tuni yabar room ɗin sbd bazai iya kallon abin tausayin nan ba,lura da halin da Jalal ke ciki yasa likitoci suka rufu akan,cikin zafin nama ya miƙe tsaye tare da fisge drip ɗin da yake hannunsa,wasu likitoci ne suka nufu inda yake suna zuwa yasa hannu ya hankaɗesu cikin sauri haɗi da gudu ya fice daga room ɗin.

Wata zabura Abbou yay jikinsa duk rawa yake,cikin ɗaga murya yace "what...kin san mene kike cewa kowa?noo!! Nasan zafin ciwo yake sakin wannan zantukan,komai zaiyi dai-dai Please Oum Jalal ki daina wannan maganar na roƙeƙi kada ki sanya zcyta bugawa"ya ƙare maganar a lokaci na farko da wasu hawaye Masu zafi suke sakkowa daga cikin idanunsa, Jalal kasa da idanu Yake kallon iyayen nasa ba tare daya iya cewa komai kuma, Nihila kam saurin miƙewa tayi tana jin maganar kamar a mafarki, Lamir kam tuni yabar room ɗin yana zcyarsa nata fasa,sbd ganin komai yana shirin ruguje masa ba tare da yakai ƙarshe ba, murmushin takaice  Mummy tayi kafin wasu hawaye ya fara saukowa daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta,cikin rawar murya tace "wannan ranar nake jin tsoran zuwanta, ranar da zan fallasa asirin zcyata,na cuci kaina da nabiye ruɗin shaiɗan,zata iya yiwuwa kuga laifina,amma banyi hakan da son raina ba,nayi haka ne domin ceton rai" Aryan ne yace "Mummy kinata bayani a rufe,yana da ƙyau koma mene kika aikata ace kin faɗa domin ki ciremu daga cikin ruɗu" ɗan yunƙurawa tayi zata miƙe zaune Jalal ya kama ta tare da jinginar da ita a jikinsa,wasu sabbin hawayen ne suka wanke fuskarta kafin tace "tabbas Jalal ni ba haifiyar ka bace kamar yadda kake tunani,dani da mahaifiyarka ƴar wa da ƴar ƙanwa ce, Mama itace ta haifi mahaifiyarka Zulfa,ni kuma Mama Yayar mahafiyata ce dani da yaya Lamir, sanadiyar rasuwar iyayen mu yasa muka dawo wajanta da zama, Allah ya jarabci Lamir da son mahaifiyarka Zulfa so bana wasa ba,kafin ya bai yana abinda yake ransa mahaifinka yaga Zulfa yace yana SO,nan Lamir yace sam bazai taɓa yiwuwa ba,a nan ya faɗa mata cewa yana sonta,ita kuma lokacin soyayyar Alhaji Kabeer tayi nisa a ranta,don haka tace bata son Lamir Alhaji Kabeer takeso,sosai tashin hankali ya gama bai yana akan fuskar Lamir ya rasa wanne mataki zai ɗauka,gashi bashi da tunun dafawa,ana haka aka fara shirye-shiryen aure,ana saura ƙwana guda aure Lamir yazo da labarin mahaifinka Alhaji Kabeer bashi da asali domin babu wanda yasan wanene shi da kuma iyayensa, Mama tace babu komai ita dai ta yarda da shi,sosai Lamir yay baƙin ciki domin a tunaninsa Mama za tace an fasa auran shi kuma a bashi auranta,haka akai aure cikin mutunci da kamala,domin Alhaji Kabeer yana da dukiya da kuma rufin asiri,bayan an kai Zulfa ɗakinta,wata rana ina zaune a cikin uwar ɗaka kamar mai bacci naji Lamir yana faɗin _ya fison data haihuwa aje har gida a kasheta sannan a kashe mijin,idan kuma hakan zai basu wahala kawai su kasheta subar gidan,idan har suka kasheta shi kuma zai nemi auren wata yarinyar sai yace a bashi riƙon abinda ta haifa daga nan duk dukiyar da mahaifin Zulfa ya bari ɗan ta zai kajeta shi kuma zai riƙe ɗan kaga dukiya ta dawo wajansa_ wannan dalili yasa na fahimci manufarsa ta son auran Zulfa da yace zai yi,dalilin guda ɗaya ne akan dukiyar da mahaifinta ya mutu ya bar mata kasan cewarta ƴa ɗaya tilo garesa,sosai na shiga tashin hankali,kullum cikin tunani nake har na rasa wa zan faɗawa abinda yake damuna,kwanci tashi aka wayi gari Zulfa nada ciki sai tashin hankali na ya nunku fiye dako wanne lokaci,wata rana na shirya naje gidanta,a zaune na sameta cikin shigar duguwar riga abaya mai kalar milk sai touchs ɗin yellow,zama nayi ina gaidata kafin tai Murmushi cikin fuskar mai cike da annuri wacce ta rabuwa da fara'a tace "Ina Mama? Taƙi zuwa ta ganni bata sani ba zan haife abin cikina lafiya ko akasin haka" gaba nane ya faɗi sbd jin abinda ta faɗa,sai kuma a wannan lokacin na tuna da maganar Lamir, Murmushi nai mata nace "haba Anuty ki daina faɗin haka,in sha Allah zaki haihu lfy" kallona tayi sannan ta kalli cikin nata tace "ai Ɗan da zan haifa bashi da wata damuwa indai kina raiye kamar ni ce,dan haka tun yanzu abinda na haifa mallakin ki ne"tsayawa kawai nayi ina kallonta sbd abin na keji kamar almara,daga haka mukai sallama na koma,ina zuwa naita tunanin yau shene E.D.D ɗinta zai cika?kawai sai na kirata a waya na tambaya babu musu ni kuma ta gayamin,ana saura ƙwana ɗaya zata haihu na buga sammako zuwa wajan wani malami sbd na aikata abinda nake gani shine kawai hanyar da zanbi na tseratar da rayuwarta,nan najewa malamin da buƙatar ina son ya haukata min Zulfa,amma ba haukan da zai cutar da ita ba,nai masa bayanin komai,zane yay a jikin ƙasa kana ya ɗago kai yace "za'ai maki abinda kikeso,amma tabbas abinda yake cikinta shima haukan zai taɓasa indai ba ta haihu kafin haukan ya risketa ba" shuru nayi ina nazarin maganarsa sai kuma nace "babu damuwa indai ba wani abu bane mai illa"ban baro wajan ba sai da aka tabbatar min da aiki ya kammalo,a ranar bacci ɓarawo ne kawai ya ɗauke ni tunanin abinda na aikatawa ƴar uwar tawa ya dinga damuna,shin nayi dai-dai kowa? Shi ne abinda zcyata ke ta damuna da tambaya kenan,amma idan na tuna abinda Lamir ke shirin yi sai naji abinda na aikata shine dai-dai, washegari da safe kasa breakfast nayi nabi na damu kaina,ina wannan tunanin na tsinkayi Muryar Mama na sallati da sauri na fito ji kina yana rawa,kallonta nayi nace "Mama lfy?" Cikin damuwa ta shaidamin haihuwar Zulfa da kuma neman ta da akai aka rasa, ɗaki na koma naci kuka na ƙoshi domin duk abinda ya faru NICE SILA,lokacin da Lamir ya samu labari kasa cewa komai yay sai zirga-zirga da ya dinga yi a gidan,yafi kowa damuwa akan abin,bayan haka nice na buƙaci auran mahaifinka domin riƙonka ya dawo gareni, Lamir baiso haka ba,amma haka na rufe ido nace dole ya barni, tun daga nan rainonka ya dawo gareni,ni kuma kullum cikin fargaba nake bana iya bacci ga kuma mafarkan da nake marasa daɗi,ashe abinda naiwa Lamir yana nan ƙasan ransa kuma bokansa ya bashi Labarin ina da hannu wajan ɓatan Zulfa,nan ya ɗura min ƙiyayya sannan yaci alwashi akan abinda zan haifa nan gaba,tunda nazo gidan babu taɓa tarayya da Abbou Jalal ba naje an sauke masa sha'awata sbd wani dalili nawa"

Saurin yin shuru tayi sbd yadda numfashinta yake fisga da ƙarfi ga kuma yadda computer take ƙara ihu alamun rai ya kusa halinsa, Muryar Jalal can ƙasa kamar bai son magana yace "bani Oxcygen"da mmki Dr ya kallesa sbd yasan cewa Mummy ita sa rayuwa sai dai wani ikon Allah, Dr yace "Ur excellence Oxcygen kuma?"da ido kawai Jalal ya kalli Dr alamar "eh" bai gardama ba ya miƙa masa, tallafo kan Mummy yay zai sanya mata Oxcygen ɗin tayi saurin riƙe hannunsa tace "mene yay saura kuma?baka son na faɗa maka cikar muradina ne?ko kuma baka son na faɗa maka asalin uban Nihila?zuwa yanzu kaine garkuwanta kai kawai zan iya damƙawa amanar ta,kai kaɗan nake da tabbacin zaka kula da jini na ko bayan babu rai na"sbd ɓacin rai da tashin hankali idanun Jalal har wani ruwa yake,ga fuskar tayi jajir, pouting lips ɗinsa yay cikin dauriya yace "wanna maganar duk babu amfanin ta,abu guda nake nema wajanki wanda nakeso kiyi min alfarmar sa"cikin sauri Mummy tace "babu abinda bazan iya yi maka ba Jalal,sai wanda Ubangiji ya sanya bazan iya yi maka shi ba" ajjiyar zcya ya sauke tare da jan numfashi kana ya lumshe idanunsa yace "yaya kamin Ammina take?"Murmushi Mummy tayi kafin ta kalli Irfan tai masa nuni da madubin data gani a jingine,da sauri ya dauko madubin ya kawo mata, karɓar tayi da hannu ɗaya kana ta sai tashi a fuskarsa tace "buɗe idanunka" a hankali ya buɗe idanunsa tare da sauke ganinsa a kan madubi,cikin sarƙewar numfashi tace "kaga kamannin mahaifiyarka,aduk sanda nake tare dakai inaji kamar da ita nake tare ne,komai nata ka kwashe sa,hatta dimples ɗinka irin nata ne...Ware idanunsa ya ƙara yi yana mai ƙara kallon kyakkyawar fuskarsa ta cikin madubin,wayar Jafar ce tayi ƙara da sauri yay picking ganin sunan Prince Hassan,daga can ɓangaren Prince Hassan yace "an kammala zaɓe gamu yanzu mun ɗauki hanyar zuwa hukumar inec domin tabbatar da wanda ya samu nasara a zaɓan,amma in sha Allah Ur excellence Jalal shine da nasara domin muna ganin alama" jinjina kai kawai Jafar yay kafin yace "on mah way in sha Allah"yana faɗin haka ya kashe wayar kana ya juya yabar cikin room ɗin domin bazai iya ƙarasa jin wannan labarin ba,da idanu kawai Jalal yabi Jafar, Jalal ne ya kalli Mummy wacce take ta fama da jan numfashi kafin yay magana tace "bayan na ɗauki hukunci ɗaukewa Oum Jalal sha'awarsa akai na,saina fara tunanin tayaya zan haifi ƴar wacce zata zama na a gurbina ko bayan babu raina,hakan tasa wata rana naje har office ɗin Alhaji khamal na nemi alfarma a wajansa,kallo na yay yace "haba Oum Jalal wanne abin naki gsky aƙwai hatsari a cikinsa,bazan iya cin amanar amini na ba,wannan ai shi ake kira da CIN AMANR RUHI,tayaya zanyi mu'amala da matar aminina,gsky bazan iya ba"cikin kuka na kalli Alhaji khamal nace "ka taimakin dan Allah, wallahi banyi da wata manufa amma ina dalili na faɗin hakan kuma kasan komai na faɗa maka" cikin wani hali Alhaji khamal yace "yanzu idan na yarda kika samu ciki kika haihu mene sunan yaro ko yarinyar da kika haifa? Shege fa kenan..⁷⁸ ⁷⁹


Post a Comment for "UNCLE NE CHAPTER 9 BY NIMCYLUV"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...