UMM ADIYYAH CHAPTER 9 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 9 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 9 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 9 BY AZIZA IDRIS GOMBE                  Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

falon tsit! Sannan ta koma kwasan kwanuka. Nan ta zauna tana kallon
labarai don T.V din falon Adda Zubaida ya samu matsala. Karar Kararrawar falon ne ya dawo da ita kalinta zuwa ga Kofa, a hankali ta ajiye
Safiyya da ta yi barci a kan Kafafunta, ta yafa mayafinta, sannan ta isa zuwa Kofar.
Kasancewar Kofar ta glass, tun kan ta bude ta ga waye ne, wannan ya sa suka tsaya kallon-kallo.
Za ki bude Kofar ko sai Karfin tabarau dinki ya Kare?" Tura gilas din idanunta ta yi saman hancinta, sannan ta yi saurin bude Kofar. Me yake damunki Ummu A. Yaya za ki bari ya rinKa kamaki ki na masa irin wannan kallon, ai zai dauka ke mayya ce.
Baya ta matsa, bayan ta bude Kofar, tana shirin daga Safiyya ne ya ce, "Saboda kin bar KarKashina a wurin aiki, ki sani ba wannan bane zai sa kiga mutane ki shiga masu raini ba, a garin nan ba a gaida na gaba da mutum ne? Ko kuwa dai wannan ra'ayinki ne? Kamar yadda _ Irresponsibility yake cikin dabi'unki?" Hawaye ne kawai ta ji sun cika mata idanu, kamar za ta yi kuka don ciwon

ZAMU TASHI 


maganganunsa, duk da cewa abin da ya fada gaskiya ne, ba ta gaishe shi ba, amma ta kidime ne da ganin sa, har ga Allah ita kadai ta san me take ji, duk sanda yake kusa da ita. Wani irin rucetuwa take shiga na ban mamaki. "Ka yi hakuri Yaya Zaid, wani abu ne ya dauke min hankali. Ina wuni. Yaya su Abba?" Kallonta ya tsaya yi sama zuwa Kasa, sannan ya kau da kansa, har ta fara tunanin ko ya karanto abin da take tunanin ne ma. Zama ta yi a Kasan kafet, don tun ba yau ba ta san ya tsani ka tsaya masa a kai, kuma a halin yanzu dai kujera ta ga ya samu ya zauna. Me ya sa ki ka yi saurin fara wani aiki? Ko kin ji cewa ana iya aiki wa kamfani Www.bankinhausanovels.com.ng ko ma'aikata biyu a tare, ba tare da yarjejeniya ba? Idan na ga daman cewa ki biyani lokacina, me za ki ce in your defense?" Hala dai komfutar Yaya Zaid ta makantar da shi ne, ya daina ganin abubuwa, ita


kuma tun yaushe rabon ta da aiki da AZ? "Ko dai ka manta ne, Yaya? Na rubuta takardar barin aiki fa, kuma ai kai na bawa." Yatsina fuskarsa ya yi kadan cikin tunani, "Uhm, amma kuma ban samu wannan
labarin ba wurin HR. Don haka ina tsammanin har yanzu ki na aiki da kamfanin mu, idan kuma ba na  ba, yau da safe kin samu albashinki na farko." A tsorace ta dago kai ta dube shi. Sai lokacin ta tuno da wayarta tun safe tana Kasan filo, ta fita ofis ta manta da ita. Wannan ya Sa ba ta ga Alert din ba kenan. Yaya za ayi ku biyani, bayan ba na aiki da ku?" "Da ki ka rubuta takardar barin aikin, wa ki ka bawa?" Kai mana!" Ta fada kai tsaye, don ta ga abin nasa ya zamo rainin hankali. Ina son ki san da cewa, ba ki yi mailing zuwa adireshin kamfani ba, bare kowa ya san da hakan a bisa dokar kamfani. Saboda haka ga shaidar ki ta ma‘aikata." Ya fada hade da miKa mata (J.D Card) dinta. Ita kam mamaki ya hanata motsi, saboda Yaya Zaid dai sha'aninsa sai shi. A halin
yanzu don abin haushi ma, maimakon ta maida hankalinta kan abinda yake miKa mata, ita kallon gefen fuskarsa take yi a sace, inda ya bar gashi sosai, tunaninta daya, idan da ya dan rage gashin, ya fi masa kyau, yanzu sai ya yi kama da wani babban mutum sosai, ba za ka ba shi talatin da biyunsa ba.
"Ki na jin me na fada kuwa?" A firgice ta dube shi, "Na'am?" "Ki yi hakuri, ki koma bakin aikinki. Har yanzu muKaminki na jiranki kuma..." shiru ya yi kadan, sannan ya kau da kansa daga ganinta, ya yi ‘yar gyarar murya "...Kowa yayi kewarki a wurin aikin." Kafin ya bari maganar ta shigeta, ya yi saurin cewa, "Sai dai ina so ki maida kai ki gane aikinki da kyau, ba zan lamunci wasa da lokaci da kudin kamfani ba." Yau tana ganin ikon Allah. Ana roKonta a lokaci guda kuma ana ba ta oda. "Ki shirya ki bi ni mu tafi. Umm Adiyya ina buKatarki a kusa da ni. (A.Z Consultants) na buKatarki." Ya Karasa fadi cikin tsantsar buKatar ta amince ta koma bakin aikinta.
Da farko har ta sauke ajiyar zuciya da jin kalaman sa, a tunaninta da gaske shi din ne ya yi kewarta yake kuma so ta koma, amma tana jin Karshen zancensa, ta kau da kai Www.bankinhausanovels.com.ng 
"Yaya babu abinda ya gagareku a baya, da ba na tare da kamfanin, haka nan babu abin da zai faru yanzu ma..." Kafin ta Karasa magana ya dago kai a fusace ya ce, "Ba za ki amince ki taho ba kenan?"
Share kallon da ya ke zubo mata ta yi abin ta, ta ce, "Ni na fada maka Yaya Zaid iya sanina ni ba ma'aikaciyarku bace. Sannan ba a kan aiki zan Kare rayuwata ba, randa ba na nan fa? Idan na yi aure, yaya za kuyi? Kawai shawarata a nan, shi ne
ku nemi wani Engineer kawai, wanda ya dauki aikinsa da muhimmanci ba irina mai bada ayyuka na ayi min ba.” Ransa ya baci Kwarai, duk da ya san ta fi shi gaskiya. Don dai ta ga ya zage, sai biye mata yake yi yana lallabata, shi ya sa za ta yi masa yanga wato.
Kin san mutane nawa na sani wadanda a guje za su bar abin da suke yi domin su karbi muKamin da na ke son damKa miki kuwa?" Dauke kanta ta yi fuskarta a dake ta ce, "To ka ga ma cikin sauKi kenan, ka basu
aikin kawai. Ni kam Bauchi ta min dai-dai, idan ka ga na koma, sai idan Allah ya sa mijin aurena a can Abuja yake." Kasake ya yi yana kallonta, daga Karshe ya ce, "Umm Adiyya, har miji ma ki ka yi, shi ne bani da labari?" Ita kanta ba ta san inda ta samu baKi yau ba, amma Yaya Zaid baya daina ba ta mamaki, to don za ta yi aure. Sai ta yi shawara da shi, ko kuma haka dokar kamfaninsa yake?
"Kar ka manta, ba komai bane na (A.Z Consultants), bare ka yi tunanin ka mallaki komai, akwai abubuwan da ba ka da iko da su, ciki kuwa har da ni, don haka idan nayi miji ma, ba lallai bane ka sani, tunda bai zama min dole ba.” Cikin kakkaurar murya ya ce, "Umm Adiyya, ni Zaid ki ke fadawa wannan maganar?
Ko kin manta ni wanene? Bari na tunatar da ke, domin ki sani. Koda kin kawo miji, ni nan zan iya zama madaurin aurenki, don haka find your manners, girl. Sannan kuma har yanzu offer din a bude yake na ba ki sati daya ki yanke shawara." Yana fadar haka ya miKe hade da daukar wayarsa da ya dawo dauka a kan kujera, inda ya mance da ita dazu, ya bar falon.
Kuka kawai ta saka a wurin, yaya za ayi ya mata haka? Me ya sa ko kadan ba ta gaban Yaya Zaid? A da ta yi tunanin Adda Asma’ yake so, to amma Adda Asma ta yi aure. To ko dai har yanzu bai daina son Adda Asman bane? Ba abinda ya fi mata ciwo irin yadda ba ta da wuri a rayuwar Yaya Zaid, sai bangaren aikinsa da kamfaninsa. Idan an wuce nan, shi kenan ita ba komai bace. Yayin da a bangarenta kuwa babu abinda yake dawainiya da ita irin tsantsar Www.bankinhausanovels.com.ng 
soyayyarsa, wanda ko zai kasheta ne, ba za ta taba fada masa hakan ba.

************

Bayan kwana biyu, da sassafe kawai sai ga shi ya dawo gidan, wai ta hado kayanta ta fito yana jiranta, tana ji, tana gani kawai ta hada kadan, don ita kam dawowa za tayi, ba abinda zai zaunar da ita a wurin wannan mugun. Koda kuwa kowa yana mata
kirki, ta kula shi. Amma banda mugunta, babu abinda ya iya. Amma Allah kadai ya san me ya fadawa Abba me ya fada, sai Allah, har Abba ya amince ta zauna a nan wurinsu. Ala dole ta ajiye aikin Bauchi.
Tun lokacin kuwa tsakaninta da shi harara ko gaishe shi ta daina yi. Kwata-kwata sai ta ji haushinsa da take ji, ya fi komai yawa a tare da ita. Wani sabon abu ma da ya shiga yi, kullum yana cikin takura mata, ko ya sa a loda mata ayyuka ko kuwa ya rinKa sintiri cikin ofis dinsu, ba don komai bane kuma ta
sani, sai don ya tabbatar ita take ayyukan duk da ya jibga mata. Wani lokacin ji take yi kamar ta samu Fayemi ya hadata da sauran manyan kamfanin ta bar aikin, ba tare da Yaya Zaid ya sani ba.

************

Tana zaune a falon Maami, tana gyaran farcenta. Maamin ta dubeta ta ce, "Anya Umm Adiyya, kin yi wa kanki adalci kenan?" Barin yanke farcen ta yi a tsanake, ta dubi Maami ta ce, "Maami me na miki? Don Allah ki yi haKuri. Allah ban sani ba. Ba na son na ga ranki ya Daci.” Tome ki ke so na ce Ummu? Ki na ganin abin da ki ke yi kin kyauta? Don kin ga
mun sa miki ido? Kin dai san da cewa burin ko wane uba, da uwa ta-gari, shi ne su ga ‘ya’yansu sun samu abokan rayuwa na Kwarai. Nan ne hankulan su yake Www.bankinhausanovels.com.ng 
kwanciya ko? Ki bar ganin na yi shiru, na sa miki ido, na yi hakan ne don kar ki ji an takura ki da
yawa har ya kai ki ga yin zaben tumun dare. Amma shiru na ba wai yana nufin ni ma
ban damu bane. Don haka ki fito ki fada min menene a ranki?" Hawaye ne kawai suka biyo kuncinta, don tausayin iyayenta, don ta san ita ce sila. Har ga Allah ta rasa yadda za ta fara amincewa ta auri koma wanene, domin addu'a kam dai tana kan yi shi kullum. Akan Allah ya yi mata zai mafi alkhairi a rayuwarta, to ga shi har yau dai ita kam jarabar son Zaid bai bar ta ba, duk kuwa da KoKorin da ta yi ta yakice shi a ranta. "Maami don Allah ku yi haKuri, ni kam koma waye ku zaba min, amma ni dai hankali
na bai kwanta da kowa ba. Ko ma wa ku ka hadani da shi na amince." "Me ya kawo zancen hadi? Ba hadin da za a miki, yadda 'yan-uwanki duka suka
kawo abokan zama, haka ke ma za ki fidda naki. Ayi abu cikin natsuwa da kwanciyar
hankali. Kin ga idan aka samu haka, sai a hada bikinki da na su SaadiK." Gabanta ne ya yanke ya fadi, saboda muddin Maami ta ce su Saadik, ta fahimci har
da Yaya Zaid kenan, tunda dai FaruK da Fa’ iz duk babu me shirin aure a cikinsu, asalima yanzu ne ma za su gama jami'a. Tashin hankali ne kawai ya sameta, yanzu tana ji, tana gani. Yaya Zaid zai yi auren
son ransa. Ya yi rayuwa cikin natsuwa, ita kuwa ko yaya za ta fara wannan rayuwar? Allahu a'alam!
"In shaa Allah Maami, zan fada miki me na ke ciki zuwa nan da Asabar." To ya yi kyau. Allah ya hadaki da miji na Kwarai, wanda ya san ya kamata, mai tsoron Allah." Rungumo mahaifiyarta ta yi tana matsar Kwalla, saboda zogin da ke nuKurkusan
zuciyarta. Yau ta ga ta kanta, yaya za ta yi da rayuwarta?

*************

Yau tun tashinta take jinta wani iri, gaba daya babu kuzari, amma haka dai ta daure ta fita, gaba daya maganarsu ta jiya da Maami ya kashe mata jiki, kawai ta yanke shawarar samun Adda Asma’u a waya, ko za su yi shawara. Kasancewar Karshen wata ne, natsuwa ta yi ta kammala rubuta, duk abin da ya
dace ta yi bayani bisa Project cin da suka kammala, sai dai duk saurinta, kafin ta gama. Oga Akim ya riga ya tafi, saboda za su wuce Lagos shi da Hasan. Don haka ba yadda ta iya, miKewa ta yi ta nufi matakalar da zai kai ta ofishin Yaya Zaid. Ta ji mamakin rashin ganin Stella a wurin zamanta Www.bankinhausanovels.com.ng cikin Reception dinsa, don haka ta dan buga Kofar a hankali hade da murda Kofar. Wani irin numfashi ne ya kubce mata daga cikin Kirjinta, a nan ta saki takardun hannunta, wani yunKuri ta yi tamkar za ta amayar da hanjinta, wannan ya janyo hankalin Zaid gareta. Ba Karamin kaduwa ya yi ba, da ya ga ko wacece a tsaye a bakin Kofar. Toshe kukan da ya taso mata ta yi da tafukan hannunta, ta fice daga ofis din a guje. A hanzarce ya ce, "Adiyya!" Ko kadan ba ta tsaya sauraron abin da zai fada ba. Salati kawai take yi a cikin zuciyarta, koda ta koma ofis, janyo Kofar ta yi ta wuce wurin zamanta, tana kuka. Kasancewar yau babu kowa, ta samu daman yin kukanta yadda take so, yau ta ga tashin hankali a rayuwa. Ta yi da na sanin fitarta kai takardun nan, a lokacin da ta kai, domin kuwa yau kadai girman da take bawa Zaid ya zube a idanunta. Tuntuni daman asalinsa kenan, babu wanda ya taba sani, sai yau. Allah ya nufeta da gani? Ta yi Allah wadaran lokacin da ta dauka tana yi masa Kaunar da ta yi masa.
Subhaanallah! Kamar a mafarki ta ji shigowar mutum, zama ya yi a jikin teburin da take. "Adiyya!" Wani zafi ne ya lullubeta da ta ji ya ambaci sunanta.
"Ba sai ka yi bayanin komai ba Sir, ban cancanci ka amsa laifinka a gaba na ba. kuma rayuwarka ce, don haka ka dauka kan cewa ba na wurin, ban ga komai ba." Ga mamakinta, budan bakinsa cewa ya yi, "Good, zai fi dacewa ki yi kamar ba ki ji ba, ba ki gani ba, domin kuwa koda wasa, na ji maganar nan a wani wuri, na tabbata ba za ki so hukuncin da zan yanke a kanki ba.” Murmushi ta yi na takaici, a sanyaye ta ce, "Me ya sa Yaya Zaid? Me ya sa?"
"Wannan ba damuwarki bace, abin da dai ya dace, shi ne ki tuna, kar ki kuskura wani ya ji." "Idan ni ban fada ba. Allah ya sani kuma Yana gani, shin za ka iya boye maSa komai? Akan me ya sa za ka nuna bangaren halayyarka na Karya a idanun duniya,
bayan a badini ga yadda ka ke? Yaa Subhanallah, Www.bankinhausanovels.com.ng yau na yi da na sanin hada jini da kai bare kuma dangantakar da ta fi kowace daraja." Dubanta ya yi cikin kullewar kai, wace dangantaka take nufi? Ya tambayi kansa. "Kuma ko ban fada ba, wataran Allah zai tona asirinka, kamar yadda yau girmanka ya fadi a idanuna." Gaba daya kansa ya daure, ya rasa me yake masa dadi, amma kuma ba zai taba
bari ta ga cewan hakan ya dame shi ba, don haka ya ce, "Na ga alamar har yanzu ba ki ji abinda na fada ba ko? Ki ka kuskura ki ka nemi fadin wani abu, ni kuwa zan miki abin da za ki tsani rayuwarki gabaki daya!" Kwarai ta kadu, jajayen idanunta ta fitar cikin tsantsar mamakin kalamansa. Har a jiya mafarkinta daya, shi ne ya ce mata yana sonta, to da ba wanda zai kai ta farinciki duk duniya, amma banda a yau, da ta san ko wanene ZAID ABDUR-RAHMAN NAFADA.

"Allah ya ba ka sa'a." Ta fada cikin kalamai masu tsantsar daci hade da daukar jakarta za ta yi waje.
Fincikarta ya yi ya hadata da bango, "Don't try my patience." Ya fada haKoransa a datse, idanunsa cike da tsantsar duhu, duk da sun kada mata ‘yan hanji ko kadan bata nuna ta kadu ba. "Kai ma dai ka san yanzu idanunka sun yi kadan su razanani bare su sa na aikata abinda ban yi niyya ba, ko kuwa su hanani aikata abin da na yi niyya. Sai dai yau kar ka koma cikin dangi, amma sai na yaye wannan Mask (Fuskar) da ka saka a idanun duniya. Mayaudari kawai!" Ta fada cikin Karaji. Wata irin zuciya ce ta kawo masa a daidai wannan lokacin, har yake jin zai iya shaKeta, ya murKusheta koma ya yi mata abin da ya fi haka muni. Amma cikin idanunta kawai ya kalla, ya tabbatar da cewa har cikin ranta a tsorace
take da shi, wannan ya sa ya sake ta. Ya fice daga ofis din, ko sekon daya ba ta Kara ba, ta bi bayansa, ta kuma wuce shi cikin sauri. Www.bankinhausanovels.com.ng 

***********

Kwana ta yi kuka cikin takaicin abinda Zaid zai iya aikatawa. Duk tsawon lokacin nan yaya za ayi ta kasa gano asalinsa? A take ta ji ta tsani kanta. Ta tsani Yaya Zaid, soyayyar da ta dauki shekaru tana yi masa, ta rikide farat daya ta koma muguwar
Kiyayya mai zafi. Kwanaki uku rus! Ta yi ba ta fita ko ina, ko abinci sai dai a haura mata da shi sama,
saboda wani irin zazzabi da ya kai mata damKa.
Yana sane da halin da take ciki na ciwo, kuma ba tantama ya san shi ne sila, amma ya rasa yadda za ayi ya ganta, bare ya gaisheta,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 9 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...