UMM ADIYYAH CHAPTER 20 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 20 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 20 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 20 BY AZIZA IDRIS GOMBE


                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Umm Adiyya ta ware idanu cikin mamaki. "Me ka ke so nace to? Da turanci zan maka sannun?" Karasowa ya yi cikin dakin sannan yace, "Ban san daga inda ki ka fito ba, amma sam ba haka ake marabtan mutum ba, ba ko dan murmushi ba fara'a?" A gajiye na ke ban jin yin fara’a." Ganin ta juya taci-gaba da karatunta ne, ya sa ransa ya sosu, kai tsaye ya isa inda take kwance, ya sa hannu ya zare littafin a hannunta. "Karatu dai na ke yi."
Na sani, lokacinki ni kuma nake buKata za ki iya ba ni?" Kanta ta saddar, haka kawai ta ji nauyin idanunsa a kanta, ta san ba ta kyauta ba,
dubi dai yadda ya dade baya nan, ba haka ta saba gani ba, ba haka aka koyar da ita
ba, ammai ta yi masa hakan, don ya gaji yace ta koma gun su Maami. Asalima idan banda Yaya Zaid ba, bata taba kallon idanun mutum ta yi masa rashinZAMU TASHI mutumci son ranta ba, yanzu haka ta ji kunyar
wasu abubuwan da take masa, amma
ya zamo lallai ne ta tsaga katanga a tsakaninsu.
"Ina jinka."
Ba ta taba tsammanin abinda zai yi ba kenan,
lokacin da ya durKusa gaban kujerar
da take, hannayenta duka biyu ya riko cikin
nasa. Mamaki ya hanata kwakkwarar
motsi.
"Na yi kewarki da yawa. I missed you, Twin-
kle." Tashin hankali, idan zuciya tana
rabarbashewa ta baje, na Umm Adiyya kam ta
baje, ta sake hacewa a lokaci guda,
kan ta sake bajewa. Shin mafarki take yi, ko
kuwa wani ne zai shigo ya ce mata
candid camera ake yi da ita?Www.bankinhausanovels.com.ng 


"Uhm-Uhm..." Zare hannunta ta shiga KoKarin
yi a hankali, idanunta sun gaza kallon
nasa."Yaya Zaid..."
"Ba sai kin ce komai ba, kawai dai na fada
miki ne, ki sani. Ba na bukatar komai
daga gareki. Na same ki lafiya?"

A hankali ta gyada masa kai, duk rashin kirk-
inta, ba ta isa ta yi masa ba yanzu, don
gaba daya ya kashe mata jiki.
"Yau Twinkle, ta rasa abin fadi, na bari ki
karasa karatunki. Zan huta zuwa anjima na
je gidan Abba, za ayi min rakiya?"
Yanzun ma dai kai kawai ta gyaďa masa, ka-
mar kadangaruwa, tsoron motsi take yi,
kar ya zama ta farka a barcin da take yi.
Haka dai ta daure ta tashi bayan ya yi sallar is-
sha ne suka wuce gidan Abba, ana
hira Umm Adiyya ko mamakin canjin Zaid
farat daya ya sakata tunanin abinda ya
janyo hakan. Me yake shiryawa?
************
A bangaren Zaid kuwa tun dawowarsa daga
Cincinnati (Ohio) ne, abubuwa suka
Kara rincabe masa, domin kuwa ya kasa cire
yarinyar a tunaninsa, abu kamar wasa
ya sa ta a ransa da zimmar aurenta, don ya
boye sirrinsa, amma wasa gaske da ya
rufe ido, ita kawai yake gani.

Ko aiki ya sa a gaba, da ya tuna wani abu game
da ita, sai ya rasa ma wani abin
yake yi, duk ya bi ya sukurkuce kamar ba shi
,
bane Zaid ba, wanda babu abin da
yake kawar masa da lissafinsa.
Wani tashin hankalin kuwa, ko zai yi yaya da
ita tun dawowarsa ba ta taba ba shi
kulawa, ko masifar da take masa ma, duk ta
jingine shi a gefe ta saka masa idanu.
Idanunta baya son ya tunosu, domin abinda
suke haddasa masa, duk shi ya janyo Www.bankinhausanovels.com.ng 
wa kansa, idan banda haka, ya san a saukake
zai shawo kanta.
************
"Yawwa Adda Zubaida ga ta nan ki mata mag-
ana. Ni ma na kawo Kara yau kam."
"Yaya Zaid ni ce na dawo Adda yau kuma?"
Adda Zubaida ta faďa tana dariya.
"Ai an ce mai nema yana tare da nasara ko? To
yau na ba ki girman, amma da
gaske ki fađa mata kin ganta nan, ko kwalliya
ba ta yi kullum kenan ita cikin kuka

take, ta ki ta hakura. Na ce mata idan wurin
Maami take so na maidata, ta fada ta yi
shiru. Ko magana ba ta min."
Umm Adiyya kam baki ta bude cikin ma-
makin Zaid, tun jiya da Adda Zubaida ta iso
gari. Saboda Intabiyu na biza da za su yi da
Baban Walid, ta sanar da Umm Adiyya
za ta zo ganin ďakinta, kasancewar ita ba ta
nan aka kawo Umm Adiyyan. A ranar
tun safe yake sintiri. Da azahar sai ga shi da
Adda Zubaida.
Ashe a rashin saninta Kararta aka kai, ita
daman har an damu da ita ne da za a kai
Kararta? Abin ban dariya. Wai yara sun tsinci
hakora.
Ba ta ce masu komai ba, har
ya
Karasa ya bar
ta da Adda Zubaida. Musamman ya
je gidan Abba ya ďaukota wai ta zo ganin gida.
Ashe da walaki, goro cikin miya.
"Haba Ummu A. Ya za ki bari abu ya lalace
har haka? Yadda na san wayonki ya
wuce ace wai yau sai an miki magana, ki san
abinda ya dace. Auren nan fa an riga

da an yi shi, idan ni ce ke, sai ki kwantar da hankalinki ki riqe mijinki. Nawa ki ka sani
suke neman miji a yanzun, ba su samu na-gari ba?"
Wata dariya ce ta Kwacewa Umm Acfiyya, kan ta yi sauri ta gintse shi. "Sorry ban yi Www.bankinhausanovels.com.ng 
niyyar yin dariya ba. Kawai... Ci-gaba." Dole ta yi dariya wai Zaid ne na-gari. Adda
Zubaida ba ta san Zaid shu'umin namiji bane. Kallonsu kawai take yi.
************
"Ki fada min kin san laifin da ki ke kwasa a kanki na haKKin aure kuwa? Kin san da
cewa ba ruwan Allah da wani shiriritarki? Duk abinda ya dace mace ta yi na
kyautatawa da biyayyar aure, idan har ba kya
Yi-
Allah zai kamaki da laifi, ki duba girman ababen alkhairi da suke kai mutum ga
samun aljanna, amma sai aka ce mace ta kiyaye sallolinta, ta azumci ramadana
tayiwa miji biyayya ta samu aljanna, an gama." Idanu ta Kura mata tana sauraronta.

Adda Zubaida shi ma fa yana da hakkin nan, auren nan ai ba mace kadai ke yinsa
ba, maza ma suna cikin ma'auratan."
"Na ji ace shi ma yana da hakkinsa, amma kaso fiye da sittin, an san mu mata muke
yunKurin gyarawa, tunda mu ne a KarKashinsu. Idan ba ki gyara gidanki ba, wa ki ke
tunanin zai zo ya gyara miki, Iyeh? Don haka ki ajiye duk wata shiririta ki rungumi
aurenki, ki kyautatwa mijinki. Tun kan ki rasa shi wa Kadangarun bariki." kwafa Umm
Adiyya to yi.
"Ki na ma jin me na ke fada kuwa?"
"Ina jin ki Adda Zubaida." Ta fada tana wasa da zoben hannunta. To wai ba mutum
sai yana cikin walwala da jin dadi bane har zai samu sukunin farantawa miji rai?
"Ke ganau ce ba jiyau ba, ba sai na kai da nisa ba, ki na sane da irin rayuwar da na
yi a baya, na auri Isa aure na soyayya, amma ki ga yadda abu ya dawo, kar ki yi
tunanin wai aure yana aiki ne, don irin soyayya
mai zafi da ku ka kwasa a waje,
soyayyar cikin gida ita ta fi muhimmanci.
Wanda baya samuwa sam, idan babu girma-mawar mace ga mijinta. Su maza an
halicce su ne da wani abu na son girma a cikin gidajensu, da ma sauran
mu'amalarsu. Yaya ki ke tsammanin namiji zai ji, idan baya samun wannan girman a
cikin gidansa?
Kuma kwanakinku na farkon auren nan, kamar su ne ginshinKin zamanku, ki ka
yarda suka subuce miki, kan ace kin seta gi-danki, kin gyara yadda ki ke so, yana da
matukar wahala. Wai gurguwa da auren nesa. Yanzu kin samu yana riritaki yana
Dokinki da har zai kula ba kya masa magana ko kwalliya ko wasu abubuwan, ba sai Www.bankinhausanovels.com.ng 
ki gyara ba?
Kwata-kwata watanku guda da 'yan kwanaki da yin auren nan. Tunda kin samu ma
kin san abubuwan da yake so, Allah, kar ki yi wasa wannan damar ta subuce miki."
Al'amarinki da Isa fa daban Adda Zubaida, ki bar sha'anin Yaya Zaid da a gabanku
ne yake nuna maku ya damu da ni, wace irin yaudara ce bai min ba."
"A'aha abin da ya wuce fa ya wuce, yau ki jarraba. Keep an open mind, ina so na ga
canji daga yau din nan. Yanzu ma tashi ki shiga ki yi wanka. Na kula da ke da alama
sa kayan ma kawai ki ka yi, don kin ji ina hanya."
Umm Adiyya ta gwalo idanu waje, yau tana ganin ikon Allah. "Adda Zubaida ke ma
kin san ba na kazanta kam, a wanke na ke tas nake, har ma kamshi na ke yi, idan
ba ki yarda ba ki shinshina ni ki ji."
"Ai ba sai na shinshina ba, ke dai ki sake kawai. Tashi ba na son musu." Ta zaci
wasa take yi har sai da ta ga ta miKe, ta bude ma'adanar kayanta ta shiga zaban
kaya tana ajiyewa a kan kujerar gaban gadonta.
"Maman Walid..."
"Da gaske ko ki tashi ko kuma ina komawa Maami ta ji abinda yake faruwa." Ba
yadda ta iya, haka ta wuce ta hau shirin da ba ta yi niyya ba. Har turarata sai da
Adda Zubaida ta yi, wani gyara da ba shiri ya tashi. Umm Adiyya dai ganinta kawai
take yi.
"Ko ke fa, na ga alama sai na kwashe wadan-nan bunjuma-bunjuman jallabiyoyinkin
ai, mutum ya yi ta shiga kamar ta baduku, babu siffar amarya sam a tare da ke."
"Ni ma zan iya cewa wani abu?" "kwarai kuwa, menene?" "Ki tambaye shi a cikin maganganun da ya taba fada min, daga kan ranar can- shi ya san wace rana- zuwa you mece ce gaski-yarasa bil hakki?" "Me ki ke nufi?" Adda Zubaida ta tambayeta hade da KanKance mata idanu. "Ni dai kawai ki tambaye shi." "Au, da gaske ne kenan ma ba kya masa magana." "Ko yanzu ba lallai ne na yi masa ba, illa don na sauke nauyin da yake kaina. Amma
ya kamata ya san tafiyar nan ba ta yiwuwa, sai an hada kai tare, ni kuma ban son
rashin gaskiya, ba zan hada kai da marar ita ba kuma."
"Oh ni Zubaida. Yanzu duk surutan da na gama yi ya tashi a babatu kenan, ba ki
Dauki komai a ciki ba."
"Na dauka, kuma zan gyara Inshaa Allah Adda Zubaida, amma yaya zan yi idan ni
kadai ce?" Ta Karasa fada tana so tayi mata kuka. Amma sam Adda Zubaida ba ta
saurara mata ba.
Tana ji, ta gama mata huduba da wa'azinta har ta kai aya. Ita duk ba wannan bane Www.bankinhausanovels.com.ng 
damuwarta. Ta riga ta Kudurtawa ranta sai Zaid ya san muhimmancinta ya darajata
kamar macen aurensa, sannan ya gane kanta.

*************
Zama ta yi ta saurari dawowarsa gida, saboda you kam ta kufula, ba abinda ta tsana
irin ta ji wai ana tashin hankali, ana shari'ar gi-dan mutane har da kai Kara, wannan ya sa ita ba
ta cika son wani kai Kara ba, ta fi son ayi ta, ta Kare, shi kuma
ya wani kama ya janyo Adda Zubaida. Yau fadan da ta yi mata sai Allah kadai ya
san iyakarsa.
"Akan me ya sa za ka janyo Adda Zubaida cikin maganarmu, ni na ce maka ina son
wasu su san me na ke ciki a gidan nan ne? Kai ne mai boye al'amuran gidan nan
daga idanun duniya, ni ban matsa maka ba, ka yi rayuwarka na yi tawa. Amma ka
daina kawo min mutane, ka na hada ni fada da 'yan-uwana." Yayi shiru yana
kallonta har ta kai aya.
Sai da ta tsargu ganin kallon ya ki karewa, doguwar rigar getzner ce a jikinta, peach
color mai aikin a jiki, daga wuya zuwa Kirji. Yana da gajeren hannu shi ma an dan yi
masa aiki, ya bi jikinta duk inda ya dace ya lafe, sai sheKi yake yi.
Ta tufke gashinta natural a tsakiyar kanta, har jelar ya sauka saboda wadatar gashin
da take da shi, amma akwai siririn mayafi a
kan nata, duk a cikin kwalliyar Adda
Zubaida ne, ta dai kwance daurin da ta kafa mata ne ta yafa mayafin. Ganin kallon
ya ki Karewa ne, ya sa ta dan kauda kanta cikin nuna alamar Kosawa.
"Kin gama?" Ya tambaya hade da daga girarsa daya. Umm Adiyya ta harde
hannayenta, amma ta Ki ta kallo inda yake.
Hannayensa ta ji sun riKe, saman hannunta sun ja ta a hankali zuwa kujerar da ta fi
kusa da su. "Zauna mu yi magana."
Ba ta yi niyyar yin wata magana ba, amma ta san wani abu Buda, tun lokacin da ta
Duke masa wuta ta kula kamar ya rage yi mata wasu abubuwan, wannan ne ya sa
ta amince ta zauna.
"Ina son yau mu warware komai. Gani ga ki, ki fada min meye matsalarki da ni?"
"Uhm?" Ji ta yi kamar an kawo mata wata gagarumar jarabawar da ba ta shirya Www.bankinhausanovels.com.ng 
masa ba.
"Yau ga Zaid a gabanki ki fadi duk abinda ba kya so game da shi. Na san babbar
matsalarmu ta faro ne, randa ki ka shiga office dina ki ka ganni."
A take Adiyya ta kau da kai gefe, wani tashin hankali ne ya Kara turniKe ta, ba ta ko
kaunar ta tuno abinda ta ganewa idanunta.
"Me ya kawo wannan kuma?"
"Na yarda shi ne, abinda ya janyo komai me zai Nana mu faro ta kansa?"
Wani maha'incin hawaye ne ya fito daga ida-nunta, amma ba amfanin ta boyesu, don
da gaske take jin zahirarren ciwo, duk lokacin da ta ga Zaid a jikin matar.
Hawayenta ta dan share, "Meye sunanta?" Ta daure ta tambaya, duk da ba ta son taja maganar.
"Shin yana da muhimmanci?" Ya tambaya muryarsa a tausashe.
"Dole na ba ta suna, tunda ta yi sanadiyyar wargaza min rayuwa har na kasance a
halin da na ke ciki yanzu haka. Ka ga ai ban ga
ta zama ba, saboda ba zan yarda
koma wace ce ba, ta ci-gaba da tasiri a kanka.
Bayan a lokutan da babu ni ta yi nasarar hakan, a yanzu ya kamata ta san da cewa
abubuwa sun canza, rayuwarka ta canza, lokaci ya yi da za ta san akwai mai kai. Ba
lallai bane ya zamo na mallaki zuciyarka ba, amma ba zan tsaya ina ji, ina gani na bar
mata kai ba. Saboda haka na cancanci na san sunanta kafin ka ce wani abu."
Zaid lumshe idanu ya yi a hankali ya sauke hucin numfashi, ya san tana cikin tashin
hankali sosai, kuma shi kadai zai iya magance mata shakkunta.
"Na san bayan halin da ki ka ganni a ciki, zai yi wuya ki Kara yarda da ni, amma ina
son ki sani, Wallahi wancan ne karo na Karshe, ban sake waiwayar abu makamarcin Www.bankinhausanovels.com.ng 
hakan ba. Ko dama ba
"Ba sai ka rantse min ba Yaya Zaid, idan har ka ce hakan, ba ni da ja, tsakaninka da Ubangi-jinka ne wannan, ka nemi gafararsa, shi ne zai yafe mana gabaki daya, duk
da na san abu ne mai wuya na sake amincewa da kai dan bisa
Hannunta ta kalla da yake cikin nasa. Zaid ya yi dan gajeren murmushi mai ciwo.
"Adiyya, me zan miki ki yarda da ni?"
"Me zai hana ka fara yarda da kanka tukuna, sannan ka sa wani ya yarda da kai?"
Yana sane da yadda take tsorace da shi, "Ki kwatantar da hankalinki, ba na cizo."
Wannan murmushin nasa mai sautin ya sake yi, wannan ya sa Umm Adiyya ta
hadiyi wani abu ta kau da kai.
"Kin san wani abu? Ba wanda ya kai ki mutum. Da farko kin ba ni haushi, ki ka
zo ki ka ba ni mamaki, yanzu kuma ciwo ki ke ji min da ko wane motsinki, sannan
yanzu ki na KoKarin ki bar ni cikin kadaici, me ki ke so da ni Adiyya? Yaya za ayi ki
amince da gaske cewa ina sonki fiye da komai da na taba nema a rayuwa?"Www.bankinhausanovels.com.ng 
Ba ta son dagowa ta dube shi, amma sai dai kafin ta hana kanta, ta riga ta yi garajen
kallon idanunsa, kallon da Yaya Zaid ya ke
mata na daban ne, ta san kallon da yake
mata idan yana zolayarta, ko yana son ta fada wasu tarko nasa, amma yau sai take
ganin alamun gaskiya a maganganunsa.
"Ka san an ce idan mutum ya saba yin Karya, duk randa ya fadi gaskiya, zai yi wuya
a yarda da shi kuma, saboda ya riga ya yi wa kansa mummunar shaida."
"Fada min me zan yi miki na nuna miki cewa babu Karya a cikin batuna?"
"Ka rabu da ni."
Kallonta ya yi tamkar me neman ya karanto wani abu a can cikin ruhinta, sannan ya
sa daya hannunsa ya shafo saman kansa cikin damuwa. "Don Allah ki daina fadan
wadannan kalaman, saboda aje-aje za su zamo normal a KwalKwalwata. Ba na son
hakan ya kasance."
*************
Kallonta yake yi cikin sauraren abin da za tace, ganin ta yi shiru ba ta Kara fadin
komai ba, ya sa ya dan murza yatsun hannunta


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 20 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...