UMM ADIYYAH CHAPTER 19 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 19 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 19 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 19 BY AZIZA IDRIS GOMBE


                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Bai kira ba dai tukun, ba lambarsa ta can, anjima zan sake gwada na gidan, mu ga ko yana amfani da ita a can.”
To ai shi kenan. Allah ya kai mu. Ki gaida su Abban naki." "Za Su ji, a gaida su Fadeela. Ba ta yi hutun ba ko?" Mama ta yi ‘yar dariya ta ce, "Ga su nan dai tukun suna shirin jarabawa, ai ta dage ita tana hutu, sai wurinku za ta tafi."
"Muna jiranta, a gaida su Anty.” Suna ajiye waya ta saki ajiyar zuci. "Whoah,” Yau ta sha da Kyar. Dole yau ta kira shi kenan, ko don Mama, ita fa sam sabgarsa ce bata cika son shiga ba. Tana isa gida, ruwa kawai ta watsa, sannan ta zauna da wayar a hannunta tana kallon fuskar wayar.
Ta yi minti goma da wayar, tana tunanin ta kira ko kar ta kira. Tana kira zai Kara daukar kansa sama da yadda yake ji yanzu, idan bata kira ba, kuma ta yi rashin kirki. Zabura ta yi lokacin da wayarta ta saki kuwwa, kasancewar ta yi nisa a nazari, kallon
wayar ta tsaya yi, har dai ta tsinke, a karo na biyu ne ta daure ta daga. "Assalamu-Alaikum."

********

BABI NA SHA SHIDA "Assalamu-Alaikum."

"Wa’alaikumussalam, kina lafiya?" Abin da al'ajabi, amma ta tabbata da gaske hakan ne, wani abu ne ya girgiza dan cikin Kasan Kirjinta, dakewa ta yi ta amsa. Lafiya Kalau. Alhamdulillahi. Kun _ isa Www.bankinhausanovels.com.ng lafiya?” Ba mu dade da isowa ba, da wannan lambar zan dinga kiranki, ki adanata, zan kiraki can anjima, idan na samu natsuwa." "Uhum, Mama ma ta kira dazu." "Eh, yanzu zan kirasu duka." A huta gajiya.”

Dif! Shiru ya ratsa tsakaninsu, kowane cikin

ZAMU TASHI 

mamakin kalaman dan-uwansa, domin rabon da suyi magana cikakkiya haka, ba tashin hankali har sun manta, da sauri Umm Adiyya ta kashe wayar. A hankali ta runtse idanunta, ta sauke hucin numfashi.
Yau ake yinta, yaya za ta fara kwana a wannan makeken gidan ita kadai? Banda Mai-gadi babu kowa a wannan rusheshen gidan, ita kuwa ba ta saba kwana ita kadai ba. Bata tashi sanin ba ta da wayo ba, sai da dare ya fara yi. Wuraren Karfe tara tayi kallon, ta yi karatun, amma lokaci yaKi tafiya ga shi nan take taji kamar wata mai cuta, tabbas mutum rahama. Duk zamanta da rashin mu'amalar ta da Yaya Zaid, yau ga shi rashinsa a gida ya
dawo da gidan kamar wani kango. "Hello, Maami?" "Na'am Ummu lafiya dai ko?" Na zo gida na zauna?" Tambayar nan take ta kulle mata kai. Hankalin

Maami ya tashi. "Lafiya za ki taho gida?" Www.bankinhausanovels.com.ng
"Maami kin manta yau Yaya Zaid yayi tafiya, kuma ni kadai ce a gidan?" Ke kin faye tsoro, ba wuta ne a gidan?”"Maami da wuta mana, to amma ni kadai fa kamar mayya, ni kam zan shirya na taho ko gobe da safe ne, sai na zo na kwashe kayana a natse." "Yaya ki kayi da mijinki?" "Na'am." Ta fada tana wani soshe-soshe, har yanzu idan an ambaci mijinta, sai taji abin bambarakwai. "Uhmm, bai ce komai ba, na san ma ba abinda zai ce." Tana magana tana sintiri tsakanin akwatinta dake bude kan gado zuwa wardrobe dinta inda take zaban abubuwan da za ta yi amfani da su na kwanaki biyu. Sai lokacin ta
tuna ba ta san kwanakin da Zaid zai yi ba, a tafiyar tasa. "A'a ba a haka ai, ki kira shi ku yi magana, idan ya amince miki tukun, sannan ki zo, amma har yaushe ma don ba ya nan, ba za ki iya zaman gidanki ba? Mu wa ya zauna mana? Ki rufe Kofa kawai ki yi addu'o'inki, ba abinda zai faru Inshaa Allah." A'a Maami akwai ciwo, bari dai na kira shin." Kafin Maami ta hana, har ta kashe wayar, ta danna lambar Zaid, yanzu kam babu ko dar a ranta, ta kira, burinta yace yaji batunta. Sai dai bayan ta gama masa bayani, shiru taji bai ce komai ba. Me ya sa zaki koma gida? ^^^^^^^^;" Daga Karshe ya fada.
"Ni gaskiya ina jin tsoro. Mai-gadi na can gate, ni kuma ina nan, idan wani abu ya zo kafin ya yi shawara da Mai-gadi ya gama abinda zai yi da ni fa. Saura Kasusuwana, ni dai ka bar ni kawai naje gida."
Kansa ya shafa, ya sauke ajiyar zuciya. "Ba a taba samun wannan ba, iya zamana a wurin, wata Kila idan kina wurin ne, kayan tsoron zasu zo ko?" Don Allah." Shi kenan kije, amma ki kash..."Na kashe komai, na kulle ko ina kan na tafi. Na ji amma sai gobe zan dawo na yi wadannan, yanzu dare ya yi, Zan yi iya iyawana."Bai sake cewa komai ba, ya kashe wayar, ita dai Allah ya hadata da gamonta. Oho Www.bankinhausanovels.com.ng
dai yau kwana sai gidan Abba. Har da dan tsallen murnarta, ta shaKe akwatinta tim da kayan sawanta, ta debi kayan amfaninta dangin su mai da kayan kwalliya, shi ma jaka guda, a Karshe dai kan ta gama, ta fara tunanin ba sai ta dawo nan kusa ba
ma, ta kwashi duk ababen buKatarta. Kitchen ta sauko, ta kwashi kayan da ta san za su iya baci, kan ta dawo su mata yi masu leda guda, ta lolloda a mota. Ba ta kai tara da rabi ba a gidan Zaid, ta Kara wuta zuwa gidan Abba. Maami kam tunda suka yi waya take gwada wayar Umm Adiyyan, ba ta samu, ta fada mata dare ya yi, ta haKura. FaruK ko Fa’iz zasu je su taho da ita. Amma ganin bata sameta ba, ya sa ta tura Fa’iz ya je. Sai kuma kan ya isa sun yi sabani da Umm Adiyya. Zare idanu aka bar Maami da
shi, da ta ga kayan da ake ta jidowa cikin gida. Akwatin kayantan ma rushehe da shi. Ummu, Kaura ki kayi?" "Maami zan iya neman wani abu a cikin kayan kuma ya zama babu, shi ya sana kwaso abubuwa da yawa kawai." "Sannu da KoKari, sai ki shiga kuma ki yiwa Abbanku bayani yana falonsa.” Cikin Umm Adiyya sai da ya duri ruwa, ji kake yi Kulululu...! TaBdijan! Ita bata ma kawo wani tunanin bayani wa Abba ba, tunda Zaid ya yarda. Maami ma ta nuna alamar yarda, kawai sai ta yi gaba abin ta. Mamana lafiya da dare daren nan?" Tattare rigarta da ke watsuwa tayi ta samu wuri ta zauna tace, "Abba dama Yaya Zaid ne yace na zo, na dan zauna a nan kafin ya dawo daga tafiyar da ya yi." Abba ya jinjina kansa, sannan yace, "Da kuma ba a gari ki ke ba fa? Ki na gani 'yanuwanki ina suke zuwa su zauna, idan mazajensu suka yi tafiya? Ba na so ki fara da hakan, kin ji ai?” Kai kawai ta gyada masa. Ta ji mamakin saurin amincewarsa, duk da sai da ya kawo
batunsa kafin nan. Kai tsaye dakinta nada ta tura Kofa ta shige. Fadawa ta yi kan luntsumeme gadonta cikin nishadi ji take yi dama a ce ta dawo Www.bankinhausanovels.com.ng
ne har abada, ta huta da rakai. Sai ko ga raKai yana kiranta a waya. Yanzu kam ta tsorata, haka dazu ya kira lokacin da take tunaninsa, ga yanzu ma an maimaita. "Kin isa gidan?” Abinda kawai yace da ita kenan. Tsumewa tayi ta tura baki, "Eh." "To, ya yi kyau, sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." Mu dare bai yi ba.” Hmm, to sai anjima."
Da safe da saKonsa ta tashi a wayarta. "Yaya ki ka ji bambancin? Ki kula da kanki.” Tabbas Zaid Abdur-Rahman mutum ne murdadde, mai ruhi biyu a jikin mutum daya. Banbancin me za ta ji, ita da ta kwana wurin Maamin ta? Hmm! Kansa ake ji.
Tun daga ranar kullum zai kirata da daren Najeriya da safe kuma za ta tashi ta ga saKonsa, haka suka jera kwanaki uku. Ranar na hudun ne bayan sun gama wayarsu ta ce. "Yaushe za ku dawo?" "Me zan zo nayi miki?" "Ni nace maka don ni na ke son ka dawo, kai da Fatima nake nufi, mun yi magana da ita, gobe za tayi paper dinta na Karshe." "Eh, sai na dawo, zan je sai mu taho tare. Ni kuma ba ni da ranar dawowa, tunda ba za a tambayeni yaushe zan dawo ba.”Lalle ma yaushe, suka fara wannan wasan da shi? Taga alama gaisuwar da suke yi, ya Sa yana nema ya mance kansa. “Ni kuma ina ruwana da dawowarka?"
Haka ki kace ko?" Daga ranar da suka yi magana, ta kashe wayar abin ta, kullum Maami idan sun gaisa, sai ya tambayi Umm Adiyya ko kuma ya ce, idan tana kusa zasu gaisa. Ranar ta ukun ne tace, "Ke me ya samu wayarki ne mijinki yana tambayarki kullum
baya samunki, bayan kuma ina waya da ke idan ba ma tare?" "Oh, ai baida dayan layin nawa ne."
Maami kam salati ta saka, "Yaya za ayi ke da mijinki, ba shi da lambar wayarki? Wane irin shiririta ce hakan? Maza dauki wayar ki kira shi, ya ga lambar yanzu." Haka Maami ta sanya ta a gaba, a take sai da ta kira Yaya Zaid tace masa Wannan daya lambata ce." Wasa gaske, dan wayar da suke yi Www.bankinhausanovels.com.ng kullum, ya sa Umm Adiyya ta saki jikinta kadan,
ta daina masa baKin hali a waya. Duk da dai ba wai ta saduda da Kudurinta bane. Randa ya cika sati biyu da tafiya ne, bayan sun gama maganarsu, kamar kullum
wato gaisuwa. Umm Adiyya ta saki abin da ya janyo jangwam! A lokacin da ta tuna
masa da za ta iya budar bakinta, idan ta ga dama ta tona shi. Bata san me ya dauko maganar ba suka koma kan gabar da tafi kowanne nauyi a tare da su.

***************

Wayarta ta kalla a karo na bila adadin, ba ta yi tsammanin maganar da ta fadawa
Zaid, zata bata masa rai har haka ba, ya yi fushi da yawa. Yanzu kwanaki biyu kenan ba ta samu saKonsa a wayarta ba bare ya kirata. Hakan ba Karamin damunta ya yi ba, kuma ga shi ba daman ta kira shi, kar ya yi tunanin ko ta damu da shi ne, ko ta fara saduda. Gaskiyar dai kawai shi ne, idan suna magana hankalinta ya kan yi gaba, ta daina tunanin komai.
Wunin ranar ko a wurin aiki ba ta tabuka abin arziKi ba, haka nan take jinta fayau! Koda ta koma gida, wanka ta yi da alwala, sannan ta zauna tana bitar karatun AlKur'ani. Daya daga cikin abubuwan da suke dauke mata damuwa kenan. Damuwarta daya yanzu, me zai faru randa Fatima ta dawo? Ko kuwa Yaya Zaid ya dawo? Haka za su ci-gaba da rayuwar yaudarar kai, har illa Mashaa Allah? Don gaba, ba duniya suke rudi ba, kansu suke rudi. Duk da Www.bankinhausanovels.com.ng kasancewar ba ta faye son wasu saKonnin Yaya Zaid ba, masu nuna gadara a wasu lokutan su kan dan debe mata zaman shiru, kasancewar ta kan riga Maami dawowa yawancin lokutan. Wannan har ya kai ga ta yi kewar rashin ji daga gare shi cikin kwanaki biyu kacal! Bayan a cikin sati biyu da suka wuce take jin da tana da hanyar Datar da Yaya Zaid
ya daina damunta da za ta aikata, ko za ta huta da yadda ya addabi rayuwarta. Daurewa kawai ta yi ta danna lambar, Kara uku tayi, sannan taji zazzakar muryarsa a daya bangaren. "Hello." "Assalamu-Alaikum Wa-rahmatullah.” Wa’alaikumussalam, wa-rahmatullah, kin wuni lafiya?"Lumshe idanunta ta yi, take ta ji muryarta ta maKale ji ta yi kamar ta ruwan sanyi bayan dogon Kishirwa. Yaya aka yi ta saba da jin muryar Yaya Zaid? Wai shin me yake mata, duk da kasancewar baya kusa? "Twinkle? Ki na kan layin ko kuwa dai?" "Na’am, eh, ina nan, yaya aiki?" Dole ta amsa muryarta, har tana sargafewa, bata
son yadda ya Kakaba mata sunan, amma haka take amsa shi, duk a cikin gudun gardama. "Lafiya Kalau, Yaya aka yi?" Wani abu ne ya taso ya toshe mata maKoshi, ji ta yi kamar ta kashe wayar ta mance
ma ta kira, sai kuma tace, "Kawai dai na kira mu gaisa ne." Hmm, ki fadi gaskiya, kin yi kewata dai."
"Allah sawwaKa, ni? Na ji shiru ne ya sa na Kira, na duba naji ko lafiya, ka san idan wani abin ya faru da dangi da ‘yan sanda, ni za su fara tuntuba, shi ya sa na kira gwamma na zauna a shirye ai, ko ba haka ba?" "Na gode da nuna kulawarki. Ban samu zama ba cikin kwanakin, shi ya sa ki ka jini shiru. Koda yake jiya zuwa yau ba abin da ya riKeni, na barki ne na ga iya gudun ruwanki ko za ki nemeni, tunda tun Www.bankinhausanovels.com.ng tafiyata kullum ni nake nemanki." "Uhmm, abin haka ne, ba laifinka bane, laifina ne da na kira. Sai anjima." Dariya ya yi mai sauti. "Na ji dadin kiran da ki kayi, da na zama abin tausayi kamar marar gata."
Umm Adiyya ta juya idanunta cikin jin haushi da takaici. "Na ga ai ba ni kadai bace matarka, da idan ban kira ba, nayi laifi, atleast ka na da masu kiranka." "Uhm, akwai wannan ma don wannan. Kin ga ke kuma ba ki da kowa da ya wuceni, shi ya sa ba na fashin kiran naki, koda kuwa za ai min gori, a fada min baKar magana."Ka yi zuciya ka daina kiran mana to." Ta fada a kufule, matsalarta da shi kenan, ba
dama a yi batu na girma da arziKi, sai ya kwabo magana. Gani na yi yanzun ma ai, ba ni na kira ba. Ki amince kawai kin yi kewata yarinya." Ji ta yi kamar ta rusa ihu, ta farfasa wayar ma gabaki daya, sai taga kuma ita ce da asara. Wannan ya sa ba ta sake ce masa komai ba, ta kashe wayar, tana jiyo
dariyarsa mai tada tsigar jiki daga daya bangaren.
Mugu kawai, da yana kusa da yana nesa, ya san yadda ake yi, ya Daga min rai".

********

Ranar da Zaid zai dawo. Umm Adiyya ta shiga taraddadi, domin ta san ba tantama ranar Maami za ta kada Keyarta zuwa gida, ai kuwa ba a bari ta ma yi bayani ba, aka hadata da ‘yan shirginta, aka ce su yi gidansu. Hade da fadin, "Na yi magana za a kawo miki wata daga Gombe, sai ku zauna koda irin hakan zai taso nan gaba, ba sai kin yi ta sintirin dawowa gida ba.Ita dai jin Maami kawai take yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tana KunKuni da mita dai haka ta wuce. Ba abinda ta tabuka duk da kasancewar
Asabar ce, ta dai KoKarta ta yi abinci, jollof ta yi da soyayyiyar plantain, sai peppered meat da mixed salad. Tana gama aiki tayi lis! Wanka ta yi ta banjama doguwar riga ko mai ba ta shafa ba, ta samu takarda ta harde a kan kujerar dakinta,
ta shiga aikin karatu, ba ta ma san lokacin da magariba ta kawo kai ba. Daidai lokacin kiran Sallah ta ji shigowar mota harabar gidan nasu, kasancewar get din Kara gare shi idan an tura. Ba ta motsa ba, asalima canza shafi tayi ta Kara luntsumewa cikin takardarta, kasancewar tana fashin salla. Ita daman dai haka Allah ya yi ta, mutane suna
hutawa idan ba sa aiki, amma ita karatu shi ne hutunta, ta karanta littafai fiye da kima.
Hannun Kofar dakin ne da aka murda ya tabbatar mata da cewa, tabbas shi ne ya dawo. Sauke littafin ta yi tana dubansa, daga inda take. Kananan kaya ne yau a jikinsa, T-shirt rawan toka, da shudin wando.
Wani sansanyar Kamshi ne ya shigo tare da shi, bakaken takalman sau ciki ne a
Kafafunsa, fatarsa ta murje har wani Kyalli yake yi, gashin fuskarsa a kwance a Www.bankinhausanovels.com.ng
kuncinsa, daidai lokacin da idanunta suka koma kan nasa ne, suka hada idanu ta kawar da kanta hade da fadin. "Sannu da dawowa.” Shiru ne ya dan gitta na wani lokaci, kafin ya lumshe idanu, yace, "Ba na son
wannan sannun." Umm Adiyya ta ware idanu cikin mamaki. "Me ka ke so nace to? Da turanci zan maka sannun?" Karasowa ya yi cikin dakin sannan yace, "Ban san daga inda ki ka fito ba, amma sam ba haka ake marabtan mutum ba, ba ko dan murmushi ba fara'a?" A gajiye na ke ban jin yin fara’a." Ganin ta juya taci-gaba da karatunta ne, ya sa ransa ya sosu, kai tsaye ya isa inda take kwance, ya sa hannu ya zare littafin a hannunta. "Karatu dai na ke yi."
Na sani, lokacinki ni kuma nake buKata za ki iya ba ni?" Kanta ta saddar, haka kawai ta ji nauyin idanunsa a kanta, ta san ba ta kyauta ba,
dubi dai yadda ya dade baya nan, ba haka ta saba gani ba, ba haka aka koyar da ita
ba, ammai ta yi masa hakan, don ya gaji yace ta koma gun su Maami. Asalima idan banda Yaya Zaid ba, bata taba kallon idanun mutum ta yi masa rashin

HMMM  LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 19 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...