UMM ADIYYAH CHAPTER 17 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 17 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 17 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 17 BY AZIZA IDRIS GOMBE


                  Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Tunda ya sauketa a gida, ta wuce dakin su Maryam, haka kawai ta ji ba ta cika son ma ta zauna cikin jama'a ba, domin duk inda hirar ta je ta dawo, to kanta da Yaya Zaid yake sauka. Ita kuma kallonsu kawai take yi, yadda suka gama daukar matsayi
na musamman suka damKa masa, koda yake ko don yadda yake kula da su yake nuna masu Kauna yake kyautata masu, dole su yi zaton shi gagarumin mutumin arziki ne. Bata san me yake nufi da Www.bankinhausanovels.com.ng kalamansa na Karshe ba, amma tabbas ta san ta tabo inda yake masa ciwo. Wannan ya sa ta murmushi. Dan kunnayenta ta cire, sannan ta fada bandaki, don ta dan watsa ruwa.
Ko kafin su Maryam su gama abinda suke yi, su shigo ta bi lafiyar gado, kasancewar ya fada mata da safe za su kama hanya, wannan ya sa ta kwanta da wuri, sai dai kan barcin ya dauketa, saKo ya shigo wayarta. "Sweet dreams Twinkle, keep being yourself." Kwarai saKon ya daure mata kai, ba ta san me yake nufi ba, don haka ta rabu da shi, ta san duk a cikin salon sa na tsokanarta ne, don ranta ya Baci a banza. Addu'a ta yi ta shafa abin ta, ta fara KoKarin mance damuwar Zaid a karo na farko, tun
randa ta gan shi a ofis dinsa, wanda wannan rana daya kadai ta juya dukkan al'amuran rayuwarta.
Komai da yadda Allah ya tsarawa bawansa, ba abinda za ta ce game da wannan

ZAMU TASHI 

ranar, illa ta yi fatan Allah sa hakan ne alkhairi a rayuwarta, yadda Maami ta fada,
idan kuwa akwai abinda ya fi hakan alkhairi. Allah ya yi mata canji da wannan.
Ita dai abu guda ya daure mata kai, ta kuma kasa fahimta, ta san Zaid baya sonta, bai taba nuna hakan ba, idan banda lokacin da ya sameta da batun neman aurenta,


bayan ta gan shi a ofis. To me ya sa tunda aka ce anyi aurensu yake nunawa kamar ya damu da ita a wasu lokutan, har ma yake fadin cewa yana sonta a gaban jama’‘a, bayan ta san ba hakan bane har cikin ransa. Ko dai jira yake yi ya ji abin da ke ranta game da shi, sai ya wulaKanta ta? Ko kuwa Www.bankinhausanovels.com.ng
dai wata muguntar ya shirya mata, shi yasa yake yaudararta da sanyin hali, domin yadda ta san Yaya Zaid, idan da ya ga daman gasa mata gyada a hannu da tun tsakanin kwanakin nan da aurensu, ya gwada mata hakan. Duk abinda take masan nan, duk tsiyarta da ba ta isa ta yi masa ba? Sannan kuma idan da yana sonta da gaske, me zai Sa ya amince da batun auren Fatima, tunda an ba shi ita ne a sanadiyar Kin sa da tayi? Wadannan tambayoyin ne suka kulle mata kai. Amma tunda ta Kuduri aniyar cire komai a ranta, ta goge wannan tunanin da ma na komai daga ranta hade da yin ajiyar zuciya ta runtse idanunta, daidai lokacin da barcin ya fi Karfinta.

***************

Tun Karfe bakwai ta gama shirinta cikin wata abaya mai fadi, tana da Kananan duwatsu ruwan goro a jikin saman hannun daga kafada har tsintsinyar Www.bankinhausanovels.com.ng hannun rigar. Kanta ma gyale ta yi amfani da shi ruwan goron, ba ta sa gyalen da abayar ta zo da ita ba. Sansanyar Kamshin turaren Monday da Safaa ne ke tashi a jikinta. Ta kulle jakarta kenan, bayan ta sa cajanta. Ta ji muryarsa a falon cikin gida, wanda ya hada Kofofin ko wane daki da ke cikin sashen.
Bayan tunannukan da suka ziyarceta a jiya, ba ta san me take ji a ranta ba a halin yanzu. Abin dai kawai da ta sani, shi ne ba ta san ko za ta sake farin-ciki na haKiKa a rayuwarta ba.
Shigowar Fadeela da gudu ne, ya fitar da ita daga tunanin da ta fada. Fadi, ke kam dai Allah ya shiryeki, har yaushe za ki bar wannan yarintar taki ne?" "Anty Ummu, kawo jakar a fitar maki, yanzu sai yaushe kuma za ku Kara zuwa?" Umm Adiyya ta yi murmushi tace, "Yanzu kam, ai sai dai nace sai na ganku, idan kun yi hutu, sai ki zo mana mu sha hutun tare."Kasa-Kasa ta yi da muryarta sannan ta ce, "To ki fadawa Yaya Zaid kar ya ce zai hana." Murmushi Umm Adiyya ta yi, a ranta kuwa ta ce ‘Allah dai ya kyauta, ace duk inda mutum yaje banda tsoronsa, ba abinda yake cusawa mutanen wurin? "Kar ki damu, zai ma yarda Inshaa Allah." Jin gyarar murya suka yi cikin wani zurfaffan siga. Ba shiri Umm Adiiyya ta ji gashin Keyarta sun miKe, hadiye yawu ta yi ta juyo ta dube shi cikin fara'a, saboda ganin Fadeela a wurin. "Ina kwana." Ta fada tana kallon inda yake tsaye, ba tare da ta bari sun hada idanu ba, shi kuwa
Zaid idanunsa tsab, a kanta. Yana son ya yi murmushi, amma ya gintse ganin yadda gaba daya ta daburce da ganin shigowarsa. "Lafiya Kalau, kun shirya ne mu kama hanya?" Kai kawai ta gyada masa. Fadeela ko ta soma fita da jakar hannunta. Zaid ya tsayar da ita ya karba. Ganin girman jakar ya juyo ya dubi Umm Adiyya. "Me ku ka kawo a cikin wannan Katuwar jakar kamar masu zaman wata guda?"
Juya idanunta ta yi, ba tare da ta ba shi amsa ba.
Haka suka Karasa cikin gidan suka yi sallama da kowa. Baffa Abdu dai sai da ya
masu nasiha, ya kuma masu addu'o'i hade da fatan Zaid ya cimma nasara kan abin da zai je yi, sannan ne suka dauki hanya. Zaid ya ji mamaki yadda kai tsaye Umm Adiyya ta nufi Kofar gaba ta bude ta shiga.
Yau ‘yan gardaman ba su kusa kenan. Sun yi kusan minti talatin suna tafiya a haka, ba wanda ya ce da dan-uwansa komai, ta gefen idanunsa, ya ga tana goga hannunta a gefen daya hannun nata, wannan yasa ya rage Karfin A.C din da ke motar
"Ke wace irin mutum ce? Ki na jin sanyi ya dameki, amma da ki yi min magana, gwamma kin ci-gaba da zama a hakan ko?" Www.bankinhausanovels.com.ng
"Akan ban iya ragewa da hannuna ba ko me? Da ya dameni, ai da kaina zan kashe, ba sai ka taimaka min ba."Murmushi yayi ya kada kai, "Da kyau, na zaci surutun naki duka ya Kare a jiya ai, ganin cewa cikin kwanakin nan na fahimci cewa ashe ki na magana da c duk ja mana aji ake yi.” To da sai na zauna na yi ta zuba maku surutu, don ba ni da aikin yi ko?" Yanzun me ya canza? Ko na cika a jerin wadanda ake iya yiwa surutu ne?" Kada kai kawai ta yi, ta koma ta jinginu da jikin kujera. Na fara tantamancewa da gaske, ban iya hira mai dadi ba." Ya Kara fada.
Don Allah ka yi shiru, ka na Kara min ciwon kai."
Ba ta gama rufe bakinta ba, ta ga ya fara rage gudu, a hankali ya sauka a kan titi.
Har motar ta tsaya cak! Juyowa ta yi ta dube shi da alamar tambaya. Tunaninta daya Allah dai ya sa ba motar bace ta lalace masu, yau da yaya za ta yi, idan ta Kara awanni tare da Yaya Zaid?
Fita ta ga ya yi a motar, sannan ya bude mata Kofarta. "Ki fito mana ki na kallona kamar kin ga sabon mutum?” "Ina zan je?" Bai kulata ba, sai ma dauke kansa da ya yi yana kallon gefen hanya, kallon fuskar sa take yi, yadda sabon fitowar rana ya haska shi, gashin da ke kwance a fuskarsa
sai sheKi yake yi. Goshinsa a tattare kadan, alamar maida hankali kan abu, ko damuwa ko tunani.
"Tafiya za ka yi ka bar ni a jeji? Me ya yi zafi? Ai da ka bar ni gidan Baffa Abdun ma zan iya bin motar haya, ba sai ka daukoni ba." Www.bankinhausanovels.com.ng
Sa hannu ya yi a cikin motar, ya janyo hannunta ta fita daga motar. Ba ta ankara ba, taji an Kara janta, an bude Kofar baya an cusata ciki. Kafin ta samu damar furta
kalma daya ta ji Kofar ta rufu gam! Sai da ta matsa gefe don tsoro, ta zaci har da Kafarta ya yi niyyar hadawa. Tunda ya koma bangaresa, ya fara jansu kuwa bai sake furta mata kalma guda ba, ko waya Zai yi, sai ya tsaya ya fita yake yi. Tun abin yana ba ta mamaki har ya koma bata dariya, har ta koma ji kamar ta ranKwashe shi. Sa'arta daya, wannan karon Mama ta yi masu tanadin abincin mota, shi ta
yi taci, tana sha da kunun ayarta. Ba su suka isa Abuja ba, sai Karfe hudu na yamma. "Huh! Finally.”
Burinta ta ganta ta fita a motar.

*************

Sauri take yi ta gama shiryawa, domin yau ta yi latti har da na Kin Karawa. Suna isowa, ba ta bi kan komai ba, tana sauke sallah ta yi wanka ta jibgu ta fara barcin gajiya. Sai da aka yi issha ta tashi ta yi sallah, sannan ta tsaya Karasa dan kimtsa wurinta, duk da komai an shirya mata shi a dakin nata yadda ya kamata, sai da ta dan sauya wasu abubuwan.
Gyalen Jilaab dinta ta maKala a saman kanta, sannan ta wurga face tissue, wayarta, chewing gum da biron ta a cikin jakar da ta dauka hannunta riKe da makullin motarta, wanda Fa’iz ya kawo mata da safen, daga gida sai kwanfutarta. A Kasan matakala suka hadu da shi, nan ta kauce masa daga hanyarsa ba tare da ta ce masa komai ba. Ta sa kai za ta wuce ne, ta ji an riKo hannunta riKo kuwa mai Karfi. Ba shiri ta dawo baya hade da kai idanunta kan hannun.
"Yaya Zaid lafiya za ka Dallani da sassafen nan?"
"Ke ba kya daukar darasi ko? Ba ki iya gaida mutane bane kome? Na ga alama har Www.bankinhausanovels.com.ng
yanzu kanki bai gama saituwa ba, tun kidimarki na jin labarin aurenmu. Sannan ina ki ke da shirin zuwa, ba nida labari?"Hannu ta sa tana KoKarin cire riKon da ya yi mata, "Aiki zan tafi, sannan ban jin yi
maka magana yau. Ka sakar min hannu.” "Ban yi tsammanin zan sake ki ba har sai mun assasa waye Mai-gidan tsakaninmu."
Ganin ya daga mata gira cikin saurarenta, ya sa jikinta ya mutu, ko bai girmeta ba
yanzu shi mijinta ne, hakan zai sa ta kasa yi masa yadda take so. Don wannan kadai take ganin Yaya Zaid ya gama da ita.Na ji, Yaya Zaid, ina son na tafi wurin aiki, ka yi min izini?" Wani murmushi ne ya Kawata fuskarsa, kafin ya hade fuskar kuma. Wasu lokutan ji take yi mutum biyu ne a jikin Yaya Zaid, idan ta yi la'akari da yadda yake saurin canza yanayinsa. Na ji, amma ki koma, kin daina aiki daga
yau. Tashin hankali ma kala-kala ne, amma yau ba ta tantamar Yaya Zaid ya tsokano wa kansa babban tashin hankali. "Idan ka yi min haka, ka na ga shi ne za ka cigaba da abin da ka ga dama, ba mai
sanya maka ido? Well, ka san da cewa idanun mai iko da mu duka na kanka ko ina wurin aiki ko ba na nan, don haka idan ka ga dama ka min kulle, wannan ba zai
hana asirinka tonuwa ba. Mr. Zaid Abdur-Rahman.
Maimakon ta ga ya bata rai, ganin ta kira sunansa kai tsaye, sai ma lumshe idanu taga ya yi. "So lovely, ban taba jin wanda ya fadi sunana yadda ki ke fada ba, kina fada cikin natsuwa da kula cike da so da
Kauna. Na gode. Ina so kuma ki sani kar ki yi tunanin barazanarki a koda yaushe zai yi aiki a kaina. Mu je da kaina sai na kai ki, ki fadama koma wanne ne sirrin nawa. Na yi maki shi a sauKaKe."
Juyawa ya yi ya kama hanyar waje, ta saman kafadarsa ya ce. "Ba na tsammanin
wurin aikin naku suna jure masu zuwa a makare. "
Kallonsa ta yi ido a bude, wannan yana nufin ya yi mata izinin ta je wurin aikin kenan. Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta girgiza kanta, ji take yi kamar ta rusa ihu a falon. Ko leKa kicin din gidan dama ba ta yi ba, saboda ba ta san ma me za ta fara yi ba a
wannan Karancin lokacin. A take kuwa ta tuna yau Litinin, suna da morning briefing. Sauri kawai take yi, domin Yaya Zaid ya Kara sawa ta makara. Www.bankinhausanovels.com.ng
A waje ta same shi yana zaune cikin motarsa, ba ta kula shi ba, ta wuce ta bude tata motar ta tayar abin ta, ba abinda ta tsana, irin wannan murmushin da ke Kunshe a kan fuskarsa, tamkar yana jin dadin halin KaKanika yin da take ciki. Daurewa ta yi ta KaKalo fara'a ta sa a fuskarta. Zuwa yanzu ta tabbata ‘yan ofis dinsu sun fara tunanin ana ba ta kulawa ta daban da su, domin Allah kadai ya san
sau nawa ta yi fashi da dalili da babu dalili, idan aka dauke lokutan da ta kwasa bata aikin ma, da su kenan kafin a dawo da ita, da Karfi da yaji. Na tsani Yaya Zaid!" Jamila ce ta dubeta ta ce. "Umm Adiiyya, lafiya ki ke kuwa?" Murmushi ta KaKalo tace. "Lafiya, me ki ka gani?" "Ji na yi kamar ki na magana da kanki, sannan tun dazu Oga Akim yake maki
magana ba ki tanka ba, wai za ku je (Lab). Akwai aiki." Ya-Salam, ta kusa ta rasa aikinta a wannan
wurin, idan ba ta maida hankali ba, a
halin yanzu kuwa aikinta ne kawai zai taimaka mata, ta daina jin kamar ta zama zautacciya.

************

BABI NA SHA BIYAR

Wuraren Karfe uku wayarta ta yi Kara, tana ganin sunan gabanta ya fadi, ta sauke ajiyar zuciya. "Hello, Fatima ina wuni?" "Lafiya Ummu A. Yaya aiki?" “Alhamdulillahi. Sorry na fita ki na barci dazu, ba mu gaisa ba." Ta fada a tsarge. HaKiKanin gaskiya sau daya ta taba Kofar, ba ta san me za tace mata, idan sun hadu ba a hakan ya sa ta yi saurin sauka Www.bankinhausanovels.com.ng Kasa. "Ba komai, ni ma ai na makara ne. Na bar maku abinci idan kun dawo. Baba ya turo driver ni ma zan koma Zariya yau, kin san za mu fara jarabawa." Oh, yaya Za ayi ta manta watan da ya shige, tace mata suna gwaji a makaranta, kasancewar tana yin MSc. Dinta a nan jami'ar Ahmadu Bello. Wayyo, ki jira don Allah, yanzu zan zo muyi sallama, ba dadi tafiya hakan ai." "Ba komai, ki zauna ni sai na biyo tunda kan hanya ne duka." To sai kun zo." Ta fada tana KoKarin saita kanta wurin yin magana daidai yadda
suka saba yi da Fatima. Amma a haKiKanin gaskiya tunani take yi na yadda za su fuskanci juna a
matsayinsu na matan Zaid dukansu, sannan a wurin aikinsa, ta san ba zai so hakan
ba, wannan ne ma Karin Kaimin cewa Fatiman ta zo Ba a dade ba kuwa sai ga wayarta akan sun iso.
Wayarta ta dauka ta ajiye jakarta cikin durowar teburinta, sannan ta ce. "Jamila bari na fita, ina da baKuwa a waje."Okay." Jamila ta amsa mata hade da dan dago kanta kadan. ‘yan Kafafunta take
cillawa a hankali har ta fita waje, wurin adana motocin ma’aikatan kamfanin.
Ba ta san me take tunani ba, da har ta yi zaton ita za ta shayar da Zaid haushi sabanin sa. Yanzun ma shi ta hango tsaye kusa da motar su Fatiman, ta gane motar ne saboda motar Baffa Mai Kano ce ta zo daukarta. Murmushi ta KaKalo, zuciyarta cike da Halli Halli tace. “Sis. Wannan tafiya haka ba sallama, ba tayi ba fa. Maimakon ki bari sai gobe?"
"Ina da paper ai, na san idan na zauna kuma ba karatu zan yi ba, shi ya sa," "To shi kenan. Allah Ya bada sa'‘a, ana dai gamawa a dawo, ba sai mun biyo sawu ba." Ta fada tana kallon bangaren da Zaid yake tsaye, ya yi shiru kamar ruwa yaci shi, Www.bankinhausanovels.com.ng
koda ya zaci fada za su yi ta yi a kansa, kamar kaji, oho masa. A'a Ummu A. Ai ba wata fargaba, bayan ga ki a nan, Za ki wakilce mu, ai sai na gama hutawana, sannan na dawo.” To ka ji me ka yiwa uwargidanka sati kacal da ‘yan duriya, tace sai ta dauki hutu kan
ta zo?" Idan ta dawo ta ba ki labari, hakan inaga zai fi armashi." Juyawa ya yi bangaren
driver din. "Malam Garba, ku je kar dare ya yi maku, ku je a hankali dai banda gudu.”
"To Sis. Sai anjima, ki koma ki ci-gaba da aikinki, sai mun yi waya."
Kafin Umm Adiyya ta ba ta amsa, ta ji hannun Fatima sun zagayeta tamkar a da idan sun hadu yadda ba sa son rabuwa da juna. Tana sakin ta. Umm Adiyya ta
sakar mata murmushi wanda tana tantama idan ba a raunane ya fito ba. "Take care." Ta ji muryar Zaid ya ambata, kafin ta bar wurin, wanda ya haddasa
mata wani irin turniKi a ranta, yau ta ga ta kanta, wai me ke faruwa da ita ne? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba ta ga shigowarsa ba, tana tsammanin ya fita ne, bayan ta shigo, haka ta koma kan Karashen aikinta na ranar.

*********

Daga tafiyar Fatima zuwa yau kwanaki takwas ne cif! Tun wancan rana kuwa ba ta


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 17 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...