UMM ADIYYAH CHAPTER 15 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 15 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 15 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 15 BY AZIZA IDRIS GOMBE


                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

To ke meye abin Kin yarda a sha'anin zuciya kuma da mutum? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ko ce maki aka yi lokaci daya Allah ba zai iya sa masa sonki bane a ransa, da ki ke ganin kamar ba sonki yake yi ba a da? Walimar ma da muka yi ta ba daya amaryar ko uwargida ce ma ni ban san maku ba yanzu kam?" Ta Karasa fada cikin zolaya.
Haba Adda Zubaida. Ke dai a bar kaza cikin gashinta sai anjima. Bari na shirya wai da yamma za su kai ni."
Murmushi Adda Zubaidan ta yi, suka yi sallama. Sai lokacin ta kira su TaRiyya take
fada masu batun aurenta, amma an yi shi cikin gaggawa ne, su yi haKuri ba ta yi wani taro da yawa ba. Kai Ummu A. Ba ki dai kyauta ba, ko notice din kwana dayan nan dai da kin ba mu

ZAMU TASHI

ai za mu zo miki."Ke dai bari, ba a cewa komai, kin san last week Yayanmu yana aure, to kawai sai aka yi shawarar a hada da nawa, da yake zai yi tafiya, shi ya sa abin ya zo ba shiri." Ba ta yi Karya ba, idan ta duba bayanin abin kusan hakan ne. Ta dai dauke cewar ita ma ba ta san an mata aure ba, sai a daren jiya. "Ehm, sai dai wani abin tambayar shi ne, da wa Www.bankinhausanovels.com.ng 

aka yi?" "Ke kin faye gulma dadina da ke. Yaya Damaturu da Ahmad?" "Lafiya Kalau, amma wannan ba zai ba ki damar kaucewa tambayata ba.” Wani abu ta hadiya mai daci, ta runtse idanu. Takiyya ce basu boyewa juna komai, idan banda hakan ma, ko fada mata labarin da ba za ta yi ba, amma idan ta yi haka, ba ta kyauta ba, "Hmm! Yaya Zaid." Can Kasa-Kasa ta furta kamar dole. Wani ihun murna TaKiyya ta sa, sannan ta ce, "Ehen, ga magana ta fito. Allah sanya alkhairi, daman mun san wannan batun kam dai, a hakan za a Kare, tun ba yau ba. 

Ana Yaya Zaid ya kira waya, ba wanda ya kai ki farin-ciki, idan an yi magana kuma ki ce abin nan." "Ba ki da kyau Wallahi. Ki gaida gida." "Inshaa Allah zan fadawa Ahmad wataran za ki gan mu." "To Allah ya kai mu na gode." Ajiyar zuciya ta yi, sannan ta ajiye wayarta. Wanka ta shiga, tana ciki, ta jiyo muryar Maami, wai ta bar mata kayan da za ta saka a kan gado. Haka ta tarar da wasu sabbin dinkunan da ko kalarsu ba ta san da shi ba. Ba ta yi mamaki ba, ta san Asma’ ce ta bada gwajin kayanta tunda duk da su aka shirya komai. Ita babban damuwarta ma, bayan an aura mata Yaya Zaid, wai Fatima ce 

kishiyarta, bayan kasancewarta 'yar-uwarta ‘yar Baffanta, Kawarta ce, don kuwa tare suka taso duka. Duk Zaid ne ya jawo masu wannan shirmen. Yanzu ba ta san ma da wane ido za ta fara kallon Fatiman ba. Banda mai da hoda, ba abinda ta sa a fuskarta ko kwalli bata sa ba. Haka suka shigo suka sameta. Maryam ce biye da Asma’, sai 'yar Adda Sadiyya, yarsu Yaya Zaid can Amira.amaryar ba. Maasha Allah. Anty Ummu kin yi kyau sosai." Maryam ta fada lokacin da ta Karaso gaban madubin. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Harara ta samu daga Umm Adiiyyaa, har gaban Asma’ ya fadi, kar taje ta nuna wasu Maryam din ba ta son dan-uwan nasu, a cewarta, sai dai kafin ta ce wani abu, ta ji Umm Adiyyan ta ce, "Ba na son wulaKanci Maryam, yaushe ni kuma na zamo Antinki?" "Kin zama by induction, tunda kuwa ba yadda za ayi Yaya Zaid yaji mu muna kiran sunanki gatsau! Girma ya kamaki yarinya." Murmushi kawai ta yi, wanda bai kai zuci ba, ta kada kanta. Amira ce ta matso kusa ta ce. "Anty Ummu, kawo dan-kwalin na daura maki na ga kin yafa shi.” "Ke da kin bar shi kawai, ciwon kai zai sani wannan abin, ya yi Kato."Kawo ki gani." Nan dai Amira ta dage sai da tai mata dauri. Maryam kuwa ta fesheta da turare sannan ta ce, "Sai dai na ji haushi ba kiyi lalle ba. Idan mun je Gombe zan samo miki mai yi, sai ai miki.” "To kune da abu kamar daukar wuta.” Ta fada Kasa-Kasa, duk da ba mai fahimtar 

yadda maganar tayi ta cikin zafi, amma hakan ne manufarta. Dariya suka yi gaba daya, bayan sun ji abinda ta fada. Gwamma hakan ai, kafin ai mana two-zero,  Ummu A. Kullum ana wa zaki 

aura, wa ke zuwa wurin Ummu A. Zurfin ciki kamar me, ashe ku ku ka san abinku ke da Yaya Zaid. Zo ki ga fuskarsa, bayan an daura auren kamar an mai albishir din aljanna." 

"Ba dole ba, mata biyu rana guda, shi dan gatan dangi, kuka ki ke so ya yi idan bai yi fara'a ba?" 

Dariya suka sa. Maryam ko ta ce. "Asma’ kin ga Kanwarki ta faye kishi. Kar ki damu, Www.bankinhausanovels.com.ng 

in dai Fatima ce taku za ta zo daya Inshaa Allah." Harara ta bankawa Maryam, ji take yi kamar ta nane mata bakinta da gam! Sai da Maami ta zo ta kada Keyarsu, sannan aka samu suka fito daga dakin, 

kasancewar duk 'yan bikin sun watse, ba wasu mutane, haka su ya su suka sa kayanta a mota ko sallama ba a bari ta sake yi da Abban ba, gudun ta sake rikice masu, suka kai ta gidansa da ke (Wuse 2). 

Abin mamaki dai yau baya Karewa Umm Adiyya, domin sai da ta ji kamar abu na yawo a kanta, don tsabar rudani da suka jefata, ita damuwarta daya ko yaushe suke haduwa su yi ta taron hallaka mata rayuwa, amma ba ta sani ba? Oho! Domin kuwa tun shigarsu gidan take cin karo da abubuwan da suka sassaya da Maami, tun ba yau ba, cikin tarin kayan dakinta da suke yi. Ga su duk an jera mata su a gidan Zaid. 

Ko ina sai Kamshin turare yake yi, an kimtsa shi gwanin kyau ga ma'abocin jin dadin zuciya, amma banda Umm Adiyya da take ji kamar numfashinta na daukewa. Ganin komai take yi kamar a fim, abin da yake ba ta mamaki, yadda duhun kai ya yi mata yawa. Tabbas ta ga ababe da dama da ya dace ace sun yi mata nuni da abinda ake shiryawa. Amma ace ta gaza fahimta, na farko yadda suka yi ta mata dinkuna na musamman, suka bi suka damu lallai sai ta sa Su a kowace rana, sannan ga yadda Maami ta taKarKare ta gayyaci kowa nata, ta san za ta iya yin hakan Www.bankinhausanovels.com.ng 

auren Yaya Zaid kadai, amma abin ya zarce kima gaskiya. Sannan ga yadda kowa yake kallonta da kalaman su Maimuna, tabbas da tana zaman gida a dan kwanaki biyu na bikin, ba zaman Ofis ba, da ta dade da gano me suke shiryawa, amma idanunta sun riga sun rufe da matsalolinta, har ya sa bata gane abinda ake shiryawa ba. Kai yanzu da take tunani ma, sai take gani tamkar akwai matar makwabtansu da ta leKo dakinsu tana tambayar inda amaren suke, har take ce mata, "Umma Bilki basu iso ba ai." 

Ta tabbata su Maami sun boyewa baKin akan da ita ake auren, sun bar su akan cewa Zaid ke aure kawai, don da sai an samu irin Umma Bilki 'yan cincirindon ganin amarya. Wuraren issha ne Asma’ ta shigo falon sama da kayan abinci, biye da ita Amira ce da kuma Kannen Fatima su biyu. Sai lokacin ne Umm Adiyya ta tuna da Fatima tana gidan ita ma. A take tausayinsu duka biyu ya kama Adiyya, saboda ganin ba ta san 

me take ciki ba, ba ta san me ta shigo ciki ba. Can bayan sun gama cin abincin ne, sai ga Fatiman ta shigo. Aka gaggaisa a mutumce. Umm Adiyya dai kamar an sa mata gum a baki, da Kyar ta bude bakinta suka gaisa. Sannan ta fita daga falon. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Maryam ce ta daka mata duka a cinya. "Ke wai ce maki aka yi kece uwargida da zaki wani hakimce, ki na bude baki da Kyar. Ita aka fara kawowa gidan, kin ga technically ita ce mai sarautar matan." Umm Adiyya ta ja dogon tsaki ta ce, "Kanki ake ji, ni kuma ina ruwa na da wannan. Idan ta ga dama ta hada duka biyu ta riKe." Da yake kin san kin gama da dan-uwana ba." Ta fada tana murguda mata baki. 

Dariya suka yi, can sai Amira ta ce, "Amma Anty Ummu, me ya sa Yaya Zaid ya hadaku duka biyu, bayan kuma ke yake so?" Lokacin ne falon ya yi tsit! Domin su kansu ba su san bayanin da manyan suka 

bayar ba, wannan irin murdadden auren. 

"Saboda ni dan gata ne, kuma duka sun ce idan ba ni ba, sai rijiya." Muryar sa suka ji daga bakin Kofar falon. Amira ta sa dariyar kunya ta ce, "Uncle Zaid sorry, ban san ka na nan ba Allah." "Ba wanin nan, daman gulma kawai ku ka zauna ku na yi, nema ku ke yi ku zuga min mata ta gudu ko meye? Sweetheart har da ke ko?" Asma’ ta kada kai ta ce, "Yaya Zaid kar ka soma, yanzu a naushe min fuskata, Www.bankinhausanovels.com.ng 

mijina ya kasa gane ni, yanzu kam da sweet da sugar har da honey heart ma ga su a gidanka." Umm Adiyya kam ta kifa kanta kan Kafafunta, banda kuka ba abinda take yi, tun hawaye na kwarara, ba wanda ya san halin da take ciki, har ta fara shesheKa. 

Anty A’isha Kanwar Maami ce, ta leKo falon tana magana, "Ku kun ga ku tashi mu tafi." Ganin Zaid a falon, ya sa ta tsaya da maganar. Cikin murmushin girmamawa tace, "A'a ango ne da kansa?" Ina wuni Aunty A’isha." Kanta a Kasa ta amsa masa gaisuwar. Zaid ne ya ce, "Mun gode fa da dawainiya. 

Allah ya saka da alheri." 

"A’a ba komai. Allah ya taya riKo, ya ba ku zaman lafiya, ya kuma hada kawunanku. 

Mu kam, mun ida aikin mu, za mu wuce kar dare ya yi sosai.""Za mu je na sauke ku ko? Na ga kamar daya motar ba za ta isheku ba?" "A'a kar ka damu, akwai motar Asma’u, sannan Fa’iz ma yana juyowa. Za mu hada da motarsa." 

“Okay to shi kenan, bari na Karasa masallaci, ku huta gajiya. Amira idan na zo gida, zan fada maki amsar tambayarki, kin ji ko?" A'a Uncle Zaid, ni fa ba ruwana." Amira ta fada cike da jin kunyar Kawun nata. Kallon bangaren da Umm Adiyya take ya yi, ba ta ce kanzil ba, ya kuma gane kuka take yi, don haka ya ce, "Ko kuma ki samu Anty Ummun naki ta yi maki bayani." Suna dariyar Amira da kunya duk ya isheta ne, ya fice a falon. Ba su watse a gidan ba, sai da suka Karasa kimtsa mata komai, a inda ya dace, suka kunna turare mai Kamshi sosai. Ko sallamar kirki ba su yi ba, kasancewar Umm Adiyya kam ta gigice da kuka. Da Kyar ta ja jiki zawa dakin da aka kimtsa, a matsayin nata, gidan ne ya yi mata shiru, tana tsammani Kannen Fatima ma duk sun tafi, don ko motsin T.V Ta daina jiyowa. Tana kishingide a kujerar gaban gadonta ne, ta lula a tunanin rayuwar da ta Www.bankinhausanovels.com.ng 

tsinci kanta a ciki, sai ga saKon Zaid ya shigo wayarta. A daure a daina kuka haka nan, ba na son ki tashi da zazzabi. Ki zauna cikin shiri gobe za mu tafi Gombe Inshaa Allah. Love you.” Zaid AbdurRahman. 

Wani irin dariya Umm Adiyya ta kwashe da shi, bayan ta gama karanta saKon. Ta yi minti biyar tana dariyar, kafin ta Kara fashewa da kuka, daga Karshe dai daurewa tayi ta yi wankanta, ta kwanta hade da jan bargo, bayan ta kunna A.C din dakin ta kashe wuta. 

Da Asuba ta tashi ta yi wanka, sannan ta yi sallah ta Kara bin lafiyar gado. Ba ta yi minti biyar da runtse idanunta ba, ta ji ana buga Kofar dakin a hankali. Kafin hannun Kofar ya murdu. Lumshe idanu ta yi ta ci-gaba da barcinta na Karya, saboda ta san koma waye, kuma ba ta shirya masifa da sassafen nan ba. Asalima kanta wani yuuuu! Haka yake mata. 

Lafiya na ganki a kwance har yanzu?" Ba ta motsa ba, tana jinsa ya tako har tsakiyar akin. 

Adiyya, na san ki na jina. Yaya na ga ba ki shirya ba?" Fuskarta ta leKo ta cikin mayafin ta ce, "Na shirya, na yi maka me? Barci na ke ji kuma ka zo ka na min magana a kai." Juya idanunsa ya yi, shi ma ya san da gangan yake yi, idan ya yi tunanin Umm 

Adiyya za ta bar shi ya sha numfashi lafiya. 

"Don Allah kar ki dagawa kowa hankali, ki yi haKuri ki shirya mu je, kin ji?" Daurewa kawai ya yi ya sassautar da muryarsa, ya dage yana rarrashinta. "Kin ga sati na sama zan tafi, yana da kyau na je na yiwa su Mama sallama, ke ma kuma muje ku gaisa da su. Ki min wannan arziKin, kar su fahimci koma menene yake faruwa,kin ji?” 

Bude idanu ta yi tana kallon ikon Allah. Daga bisani ta yi dariya sosai ta ce, "Zaid Abdur-Rahman ba ka taba burgeni ba irin yau, oh, naso na daukeka a recoder na yi ta kunnawa kullum da safe da dare ina sauraro. Kalamanka sun fi komai dadin Www.bankinhausanovels.com.ng 

saurare, daman ka iya marairaicewa ka roKi abinda ka ke so? Ba damuwa ko wannan ya isa na amince zan bika, amma da sharadi." Tsabar danne haKoransa wuri guda yana tunanin wasu haKoran nasa sun kusa su farfashe don haushi. "Anything for you, my love.” Ya fada shi ma cikin gatse. "Kar ka sake kirana Love." Ta fada a tsume. "An yi an gama, Twinkle." 

Kar kuma ka sake cewa ka na sona, saboda da ni da kai duka mun sani Karya ne, 

idan ka ga dama ka yi ta yi a gaban jama‘a, amma ni da na sani, don Allah ka samu decency na kwatanta gaskiya a gaba na." Karasawa ya yi gaban gadon ya durKusa, yana kallon fuskarta. "Ki yi haKuri, ban 

miki wannan alKawarin ba, domin kuwa ba zan iya Boye miki gaskiyar abinda yake raina game da ke ba, idan kin ga dama ki yarda, idan kin ga dama kar ki yarda. Yanzu dai ba wannan bane a gabanmu, ki tashi ki shirya." Idan na ce na fasa fa?" Ta fada tana kallon sa. Lumshe idanu ya yi, ya bude. 

"Idan na ce ki na da zafi kenan. Don na roKe ki, hakan ba yana nufin ki na da zafi bane, don haka ki tashi ki shirya mu tafi, ina jiranki nan da awa daya.” 

Bai jira amsarta ba, ya tashi ya bar dakin, ita kuwa ta bishi da kallon mamaki. Wato 

duk yadda take tunanin gadarar Yaya Zaid, ya shanye gaban can. Kwafa ta yi ta yaye mayafinta, ta sauka a gadon tana gunaguni. 


**************


Tunda suka fara tafiya, ba wanda ya ce uffam a motar. Umm Adiyya kam tana ma dunKule a bayan motar, ta lullebe jikinta duka da mayafinta, bayan ta kurma masa ihu a tsakiyar hanya, akan ya sauketa ko ya tsaya ta koma baya. Ba yadda ya iya, 

dole ya tsaya ta koma baya, sannan suka cigaba da tafiya. Yana kallonta ta madubin baya, ta rufe fuska sai KunKuni take yi. Tun jiya da aka kai ta gidansa, yake cikin fargaba, bai zaci ma za ta kwana ba tare da ta gudu ba. Wannan ya sa koda ya yanke shawarar zuwa yiwa su Mama sallama, ya ji Www.bankinhausanovels.com.ng hankalinsa zai fi kwanciya, idan ya wuce da ita, domin bai yarda da ita ba, ya san Za ta iya aikata koma meye. Tare suka jera da su Maryam a hanyarsu ta Gomben. Kansa ya daure gaba daya. 

Ta dagula masa rayuwa, shi yanzu ba wanda ya fi ji irin Fatima, duk abin nan da ake ciki ta yi haKuri ba ta ce komai ba, sai yadda ya ce, haka take binsa, amma ga wannan ‘yar kucilar, sai wahala take ba shi. 

Tunda suka dauki hanya, ba su tsaya ko ina ba, sai da suka isa Bauchi. Ya biya ta 

(Bauchi Club), ya saya masu nama da ruwa da su Juice. Jin da ta yi anyi Parking ne, ya Sa ta san tsayawa suka yi. Amma taurin kai ya sa ta Ki dagowa ta dubi ma inda suke. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tana ji lokacin da aka kawo masa order din da ya bayar, amma ta Ki motsawa. Har sunanta ya kira akan ta tashi ta karbi nama ta ci, ta Ki kula shi. Haka ya rabu da ita, ya ajiye Kunshin naman. Gabaki daya Kamshi ya cikata a bayan motar, sai hadiye 

yawu take yi cikinta na kiran ciroma. Bai sake waiwayarta ba, har suka isa Kofar Gombe. Ta ga dai da gaske wucewa za su yi. 

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE 

Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 15 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...