UMM ADIYYAH CHAPTER 14 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 14 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 14 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

 UMM ADIYYAH CHAPTER 14 BY AZIZA IDRIS GOMBE


                  Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Juyawa ta yi ta bankawa ‘yar-uwarta harara, wato ita ce mai tonon sililin. Aku mai tsinin bakin da ta bankade sirrinta. Ita ta janyo mata komai. Shi ya sa da safe Yaya Zaid ya yi mata abinda ya yi a kitchen, ya san ita matarsa ce, kuma shi ya sa Maami ba ta dago mata maganar ba, duk da ganinsu da ta yi a hakan. "Abba na daina son shi yanzu, daman ban gane meye bane, kawai shaKuwa ce ta ‘yan-uwantaka. Kuma Maami ba kun masa auren gatan ba, me ya sa za a hadla masa da ni?" "Kin manta auren gata ne? Ke extra aka Kara masa." Maami ta fada hace da wurga mata wata tafasasshen harara. Haushin Umm Adiyya take ji, idan ta ji tana cewa bata son Zaid, bayan kowa ya san halin da take shiga a kansa.
BaKin-ciki take ji kamar ta yi ihu, wato Maami ta nuna Karara ta fi son Zaid a kanta kenan. Har ma extra ake yi masa da ita. "Maami kun tsane ni ashe, ban sani ba? Abba shi ya sa ka turani wurin aikinsu, don ya yi ta cin zalina, duk duniya ba mai sona. Wayyo ni!" Wani ihun ta sake rusawa, har su ‘yan biyu sai da suka fito daga dakinsu da gudu suka samu diramar da ake yi. Hankulansu ne duka ya koma bakin Kofar falon inda Zaid ke tsaye, take hankalin Abba ya tashi, kar dai ya ji kalaman Adiyya? Bai san me yake damun yarinyar ba, ranar a gaban Yaya Abdu tace ba ta amince da

ZAMU TASHI 

auren ba, sun samu sun shawo kansa da Kyar ta hanyar Asma’ aka daura auren, ba tare da saninta ba, bayan sun samu tabbaci daga bakin Asma’ akan Ummun tana son Zaid, fada suka yi. Sannan ga shi yanzu Karara ta furta a gaban Zaid din bata sonsa. Bai taba tunanin a cikin yaransa, idan akwai mai sa shi ciwon kai, to bai wuce ta zama Adiiyya ce ba. "Zaid...Cikin murmushi ya Karaso falon, ba ko kunya Umm Adiiyya ta zage Karfin idanunta tana banka masa harara, amma ya kawar da kansa yana kallon Kasa yace, "Maami an wuni lafiya?" Murmushi Maami ta KaKalo, "Lafiya Kalau.

Alhamdulillahi. Yaya Www.bankinhausanovels.com.ng ayyuka? Da Fatima?" "Alhamdulillahi, lafiya Kalau."
Abba ne ya yi gyarar murya, yaCe, "Yawwa tunda ka iso ina da magana da kai dama, mu shiga falon ciki.”
Tun shigowar Zaid kuwa, gaban Umm Adiyya yake ta bugun uku-uku. Suna wucewa Maami ta hauta da fada, "Don kin ga Abbanku na biye miki, shi ne ki ke iya shegen da kika dama ko? Ko kin manta su Maryam suna nan ne? To bari na tuna miki, ba ki isa ki sa a zagemu ba. Kai na ma fasa shirin da aka yi. Tunda saura sati biyu yayi tafiyar, shiryawa za ki yi gobe a kai ki gidanki." Gwalo idanu ta yi tamkar za su fado, don firgici. "Maami don Allah ki yi haKuri na tuba, kar ki min haka, ba zan iya fada maku me yayi ba, amma don Allah kar ku hadani da shi, ba zan iya rayuwa da shi ba."Na ga ai kin mutu da ku ka rayu gida daya ai. Wallahi tun kan ki jawo min magana,
ki yi shiru ki daina koke-koken nan. Asma’ zo ki shige da ita, ta kimtsa fuskarta,mijinta ya zo kar ya nemi ganinta a haka." Ta kasa yarda da abinda kunnuwanta suke jiye mata. Maaminta ce yau take mata halin ko in kula akan wannan Yaya Zaid din? Tabdi! An kusa a kwashi ‘yan kallo ashe. Don kawai suna ganinta shiru-shiru, suna tunanin ba za ta iya yin komai bane.

*************

Haka taja jiki sumui-sumui, suka wuce sama da 'yar-uwarta, suna shiga dakinsu ta
maKe hannun Asma’ daga jikinta, "Wallahi da na mayar ki na Kaunata, na mayar duk duniya daga ni da Adda Zubaida ba ki da kowa, sai ga shi kin cuceni, kin sa an kasheni da raina." Asma’u ta razana da abinda Adiyya take yi, "Don Allah Sis. Ki yi Kasa-Kasa da
murya kin ga su Maryam suna nan, za su iya shigowa ko wane lokaci, kin ga kuwa ba za su so su ji ki na fadan haka game da Dan-uwansu ba, ko ba komai wata kusan ta fi wata.” Ba sai su ji ba, ni dai kin cuceni kawai. Ku yanzu a tunaninku da gaske yake yi sona yake yi? Bari na fada maku, duk abin da ya faru da ni, kune sila. Domin kuwa auren ramako zai yi da ni. Na san sirrinsa, domin..” Www.bankinhausanovels.com.ng
Harshenta ta sa ta lashe labbanta na Kasa, gudun kar ta yi wata Barnar. An riga an Data mata rayuwa, yanzu wai ita matar Yaya Zaid ce? Hannu ta sa ta tallafo kanta tana KoKarin toshe abinda ta gani a idanunta. Yaya ma za ayi ta fara fada masu?
"Ummu A. Sirri? Wane sirri ki ka sani?"

**************

BABI NA SHA BIYU

Tana jin tambayar Asma’ gareta, amma ta runtse idanu, "Babu komai, ya shige. Kibar ni na kwanta na gaji." "Dole ki gaji ai, wannan birgima da ki ka sha."
Harara ta samu, don haka ta sa dariya ta ce, "Oh ni 'ya su. Yaya Zaid ya dawo min da 'yar Kanwata masifaffiya." Ku ku ka sani, kuma ki ja min Kofa, ba na son ganinki." Asma’ ba ta kula ta ba, ta kwashi abubuwanta ta ce, "Asha soyayya lafiya, ni na yi
dakin Maami." Filo Adiyya ta ja ta kaiwa Kofar jifa, ba ta samu Asma’ ba, a nan ta sulale ta ci kuka
iya kukanta. Har muryarta ta dishe. Wayarta ce take Kara, amma ta ji kamar ta dauka ta nanata da bango. Ba ta duba ma sunan mai kiran ba, ta amsa wayar. "Hello." Ta fada cikin siririn muryarta da ta dishe, kuma cike da shagwabar kukan da take yi.
"Hello." Wannan muryar ko a mafarki ta ji, za ta farka, don tsanar mai ita, don haka ta kashe wayarta. SaKo ne ta ji ya shigo wayar. "Adiiyya, ki yi haKuri, ina son mu yi magana. Abba ya ba ni saKo. Zan iya shigowa?" Tana gama karanta saKon, ta ruga Kofa da gudu a kidime, ba shiri ta hau murda
makulli. Yana ji ta yi Kat-Kat har uku, har na hudun ma ya ji, sai dai kawai makullin
ya ki juyawa ne. Don haka ya san amsarsa. Adiyya, please. Na san ki na nan ba zan dauki lokacinki ba." Lallai ma mutumin nan Www.bankinhausanovels.com.ng
Dan rainin wayo ne na Karshe, don bai da kunya ma har dakinta zai shigo ya
sameta, su Maami ne duk suka biye masa, har yake abin da ya ga dama.
Tana manne dama a jikin Kofar tana zubar Kwalla, ba shiri ta tashi daga jikin Kofar
ta nufi bandaki ta yi wanka ta sa kayan barcinta, ta kwanta. Tunda ta ji shiru a bakin Kofar ta san ya gaji ne, ya tafi.
Har barci ya fara fizgarta ne, ta ji an Kara knocking. A zabure ta zauna a kan gadon.
Ta ga ta kanta, kar dai Kararta ya kaiwa Maami?
Ba shiri ta miKe, ta nufi Kofar ta yi saurin bude key din, koda Maamin ta taba ma, za
ta ce barci ne ya dauketa, ba ta ji bugun Kofarsa ba. Tana gama murda key ta bude.
Sai dai ba ta ga kowa a tsaye a gun ba. Don haka ta leKo kanta waje. A jikin stair rail
ta gan shi a jingine ya harde Kafa daya jikin daya yana Kare mata kallo. Da sauri ta
koma ciki ta riko Kofar za ta mayar ta rufe. Hannu ya sa ya tare Kofar. "Ki saurareni Umm Adiyya."
A tsaurare ya yi maganar, don baya kiranta Umm Adiiyya duka a cike, sai zai fada mata magana mai muhimmanci, amma haushinsa da tsanarsa da take fama da shi, sun hana mata jin tsoron tsaurin kalaman nasa ma.Ka watsar da wannan damar, idan ba za ka damu ba, barci zan yi." Kallo ya Kare
mata sannan ya ce, "Na ga alama, amma ya zama lalle ne mu yi magana yanzu."
"Me za ka ce min? Bayan ka saceni, ka yaudari iyayenmu sun mana auren da ba na
so, ban san an yi ba, ka cuce ni, ka cuci rayuwata, duk don so da neman rufin asirinka ko? Ka na tunanin don ka aureni, sirrinka ba zai fito ba wata rana?"
Jin ta fadi haka, ya yi sauri rage murya, "Sshh". Yana duban gefe da gefe, cikin tunanin kada wani ya ji abunda take fada. Ba ta ankara ba, ta gan shi a dakin ya tura Kofa ya rufe. Me ka ke nufi? Ka fita min daga daki Yaya Zaid.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Dallara mata wani zazzafan kallo ya yi, sai da ta kadu kadan. Kafin yace, "Idan anKi fa?"
Kallonta yake yi kamar injin na daukar hoton Kashi, "Subhanallah! Ki nemi hijab ko wani abu ki sa don Allah." Kau da kai gefe ya yi, bayan ya fadi hakan.
Zare idanu ta yi tana dubansa cikin tsantsar kidima, Kare mata kallo yake yi ko me?
Ita tsabar rudani ma ya sa ta manta ma riga da wandon PJs ne a jikinta, da sauri ta yayimo hijabin sallarta ta sa. BaKin-ciki kamar ya kasheta.
Ka kalli iya na kudinka, sai ka fita ai Malam.”
A take ta ga wannan sauyin ya ziyarci fuskarsa, a duk lokacin da ta ga wannan, ta
tabbata da za a gwada BP dinta, to zai Kure sikeli.
Murmushi ya yi, yana kallon ‘yar kucilar yarinyar. "Na ji whatever, ke wannan ya
dama." Har ya yi shiru, sai kuma ya Kara kallonta, "Really? Kayan barcin mickey
mouse? It's an eyesore." Girgiza kai ya yi cikin alamar Kin jinin kayan nata.
"Ban yi tsammanin haka ka ke ba, amma idan hirar dandanona akan kayan barcina
ne ya kawo ka, sai na ce mu hadu a shirin How do I look, amma idan ba shi bane, idan ka gama, za ka iya tafiya."
"Anyway, abin da ya kawoni shi ne tafiyata nan da sati biyu ne, mun yi magana kuma da Abba ya yarda ki koma can gida da zama, tunda ga Fatima tana nan, inaga ba za ki samu wata matsalar zaman ba." Gwalo idanunta ta yi waje, da tunani take yi, yana taba shaye-shaye, amma yau kam
ta tabbatar har da shinshine-shinshine yana yi. "Sai naje mu debewa juna kewa dani da matarka ta dole part one. Ka na jin dadi abinka har mata biyu aka sace maka lokaci guda. Ko ita Fatiman sonka take yi, ka aureta?" Idanunsa sun bar kallonta, sun koma kan gadon da ta tashi, domin idan yana kallonta, ji yake yi kamar ya shaKeta, ta faye fitina yarinyar.
Kishi ki ke yine?" Allah ya sawwaKe." Ta fada da dasasshiyar muryarta. Wata harara ta yi masa.
Hankali dai, yanzu ko ki kwashi lada ko zunubi, wanne ki ka zaba?" Www.bankinhausanovels.com.ng
"Ko duka na yi maka ba ni da laifi, bari kuma ka ji, tunda tursasa kanka ka yi a rayuwata kuma ka aureni, babu yawun baki na, don haka aurenka Invalid." Sai da ta fadi haka, ta ga kallon da yake mata, ko ba komai ta san aunata yake yi, da ta ce ko
duka za tayi masa, kafin ta daga hannu, ta san an matseta ta zama tabarma, tunda
a tsaye ma ya yi kusan biyunta. Kullallen yawu ta hadiya. Daga sama ta ji muryarsa mai zurfi, ya ba ta amsar maganarta. "Za mu gani. Ki
zauna cikin shiri. Sai da safe." Ba ta samu damar amsa masa ba, ya juya ya fice daga dakin.
Wayarta ta dauka ta yi masa Text, "I hate you, criminal kawai." Duk da haka ba ta huce ba. Wurgi ta yi da wayar a kan gado. Sannan ta bi bayanta ta hau kuka. Ba tayi tsammanin yau barci nata bane.
Sai da ta sha kukanta, ta daure ta yi alwala tana Azkar, a nan barcin ya Gauketa. Ta
yi mafarkin murmushi da kuka da taron jama'a da idanu masu duhu da haske.

*************

Abin al'ajabi, bai bar ta ba, sai da ta tabbatar da gaske su Maami suke yi. Washegari za su kai ta gidan Zaid. "Maami, yanzu tsakaninku da Allah kun zabi son ransa a kaina?" Kallo daya Maami ta yi mata ta ji tausayinta ya kama ta, don haka ta bar hada kayan da take yi, ta koma kusa da ita ta zauna.
"Ummu, na san wannan abin ya zo miki a bazata. Amma ina son ki sani, dukkanmu muna da manufa ta alkhairi ne a kanku. Tunda ki ka nuna ba kya son abin nan, ni da Abbanku muka yi shawara, aka nemawa Zaid auren Fatima, sai ga shi, shi bai saduda ba, kullum sai ya yi mana maganarki. Har wajensu Mama zancen kenan. Ba mu yi niyyar yin wani abu ba, sai da muka ga damuwarki Karara kan wannan Www.bankinhausanovels.com.ng
zancen da jin zai yi aure, gaba daya ki ka lalace, ki ka shiga wani hali, fara'ar ki da walwalarki suka kau, wannan ya sa Asma’ ta fada mana batun cewa kin dade kina son Zaid ke ma. Duk da ba wai mun fada masa hakan bane, amma mun shaida masa mun ba shi aurenki. Yanzu ina son ki fada min, meye laifinmu don mun nemi mu hada ki da farin-cikinki ba tare da saninki ba? Sai ga shi jiya kin hautsina mana gida da haukar ki, wai ke ba kya son shi. Ba ki ga yadda ki ka karya zuciyar Abbanku ba da wadannan kalaman
naki, da ya san ba kya so, za mu iya bawa Zaid haKuri, duk da hakan zai mana ciwo, don yadda muke sonku, haka muka dauke shi a matsayin dan mu.
Yanzu ki fada min? Yaya ki ke son Abba ya je ya roKar miki rabuwa wurin Zaid? Sannan idan har ba kya son Zaid, ki na da wanda ki ke so ne sama da shi? Na amince wata Kila kun samu sabani, kun yi fada, ko wani abu, amma idan har zai nuna jajircewarsa haka a kanki, ni a ganina ba Karamin sonki yake yi ba, tunda ya yi miki haka." Umm Adiyya kam da jin haka ta KaiKaitar da wuya, hawaye na bin fuskarta. Yaya za ta dubi iyayensu ta fada masu halin Zaid? Yaya za ta fara fada masu dalilinta na tsanarsa lokaci guda? Ko ita kanta ta san da ace ba ta san halinsa ba, ba wanda zai kai ta farin-cikin abin da ya faru, duk da sanin nata ne, ya janyo har ya nemi aurenta a karo na farko, wurin iyayen nata. Sun gama yarda da shi, ya kuma ha'ince su tabbas! Shi kenan Maami, na ji na haKura. Zan kwatanta zama da aurensa a kaina ."
Tana fadar haka ta sa hannu ta goge hawayenta. Maami ta ja ta jikinta ta rungumeta
tana shafa bayanta. "Ki yi haKuri, komai zai wuce, ba a yanke hukunci lokacin da
ake fushi kin ji ko? Ko kuma dai wani abin ne Zaid ya yi, ya sa ki ka ce ba kya son shi?" Maami ta fada lokacin da ta dago daga jikin Umm Adiyya.
Ga dai kalaman a bakin labbanta, amma ta kasa furta su. Sai kawai girgiza kanta ta
yi, tana hawaye, tana murmushi. "Maami bai iya lallaba da nuna kulawa ba, sam baya nuna yana sona.”" Zaro idanu Maami ta yi cikin mamaki, sai kuma ta sa dariya hade da dungure kan Umm Adiyya, "Ba ki da wayo yarinyar nan har yanzu, daman wa ya ce Www.bankinhausanovels.com.ng miki sun iya lallami? Koya masa za ki yi, amma ki na birgima da bore kam, ai zai zaci ke 'yar dambe ce. Shagwaba za ki masa, sai ya lallabe ki. Koda yake idan dai abin dana gani jiya ba lallami bane, ban san meye bane wannan." Maami!" Umm Adiyya ta fada had da rufe idanunta da tafukan hannunta, ita kadai
ta san tafasar da zuciyarta take mata a ciki.

**********

Da azahar ta samu wayar Adda Zubaida, ita ma nasihar take mata, bayan ta ji bayanin komai daga Asma’. "Allah Adda Zubaida duk garin nan ba wanda ya kai Adda Asma’ gulma da mugunta, wato yadani ta je take ta yi." Zubaida ta ce, "Kun fi kusa ai, akwai wasu kayayyakinki a nan, zan bayar a kawo miki, idan na samu mai tafiya." Hawaye ne a cike taf! A idanunta, "Adda Zubaida ke ma wancan satin, kin san an aura min aure da Yaya Zaid? Shi ne ku ke ta hidimarku har da su yin walima bayan kun san ba na so."
Shiru ta ji, daga dayan bangare, wannan ya sa ta daga kanta sama ta hadiye wani abu mai daci, "Ummu A. Ki yi haKuri komai zai wuce Inshaa Allah. Kawai ki bashi dama. Kin ga yadda yake damun su Abba kuwa a kanki? Yaya Zaid na da haKuri kan abubuwa, tunda ya matsa haka, na san lallai da gasken sonki yake yi. To ke meye abin Kin yarda a sha'anin zuciya kuma da mutum? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ko ce maki aka yi lokaci daya Allah ba zai iya sa masa sonki bane a ransa, da ki ke ganin kamar ba sonki yake yi ba a da? Walimar ma da muka yi ta ba daya amaryar ko uwargida ce ma ni ban san maku ba yanzu kam?" Ta Karasa fada cikin zolaya.
Haba Adda Zubaida. Ke dai a bar kaza cikin gashinta sai anjima. Bari na shirya wai da yamma za su kai ni."
Murmushi Adda Zubaidan ta yi, suka yi sallama. Sai lokacin ta kira su TaRiyya take
fada masu batun aurenta, amma an yi shi cikin gaggawa ne, su yi haKuri ba ta yi wani taro da yawa ba. Kai Ummu A. Ba ki dai kyauta ba, ko notice din kwana dayan nan dai da kin ba mu,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 14 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...