UMM ADIYYAH CHAPTER 13 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 13 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 13 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 13 BY AZIZA IDRIS GOMBE           Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Hannu ta sa a kwankwasonta cikin mamaki, "Ina ruwanka da abincina, bare wankana? Tunda ko ba ku da gami, zan yi duk yadda na ke so."
Ni ma zan ci, amma gaskiya ki je ki yi wanka, sannan ki zo ki daura min nawa." Tana sane sarai, abincin da Yaya Zaid ya fi so kenan duk duniya, amma tsabar
tsantseninsa ya sa baya iya cin ko na waje ne, sai na gida. Shi kam an ce yana yaro Www.bankinhausanovels.com.ng
ma idan an je unguwa, haka yake komawa gida da yunwa, saboda kar ya ci abincin waje. Amma yau tsabar haushin da yake ba ta, ji ta yi da tana da halin zama Kudan zuma
a lokacin za ta cicciji Yaya Zaid, da shi ne burinta na Karshe. Juya idanunta ta yi cikin nuna halin ko in kula, ta bude famfo ta saki ruwa, tana

ZAMU TASHI 


wanke kullin ‘Dan waken daga hannunta. Yana ganin yadda take KoKarin daukar robar sabulun wanke hannu, bai yi wata-wata ba, ya isa inda take ya dauka, ya matsa mata kadan, sannan ya ajiye. Juyowa ya yi yana fuskantarta, sai a lokacin ya kula da inda ya shige mata, domin har yana hango busashen hawayen da ke kan jan fuskarta. Sautin muryarsa ya dan rage dace da matsawa baya kadan. "Ban dauka son da kike min ya yi nisa haka ba. Allah, da ban sa ki kuka ba Adiiyya!"Harararsa ta yi, ta juyo da wuKa a hannunta, wanda ta zara daga cikin abin shanya kwanukan wanke-wanke.

Shi kuwa ya yi murmushi ya bi hannunta da kallo. "Allah ya Www.bankinhausanovels.com.ng sawwaKe na so-ka.”" Wani kallo ta yi masa fuska a yatsine, "Kai wani irin mutum ne ma? Satinka daya da aure, amma ka na irin wannan magana. Koda yake
na manta kai (Mask Man) ne, ba a sanin asalin Www.bankinhausanovels.com.ng halinka, sai an ture fuskar. Amma bari na fada maka. Wannan..." Ta yi nuni da kanta da shi da wuKar hannunta, shi dai yana hankalce da ita, don idan ta yi mugun motsi, Za a iya samun akasi. ,.Ba zai taba faruwa ba, don haka idan ka yi gigin Kara min magana, zan fadawa Fatima komai." Yadda ta yi maganar ne, yake ba shi dariya, don haka ya ce, "Sai aka ce miki tsoronta na ke ji kuma ko? And yes, Idan ba so ba, ban ga dalilin da zai sa ana aurena ba, ki kasa min ko murna, ki kulle kanki a daki ki na Karyar ciwo, kiyi ta kuka a aki, ki yi ta masifa da 'yan biki... I bet ko yau da safe ma kin yi kuka ko?" Yana lissafowa, yana Kirga yatsunsa. Muryarsa Kasa-Kasa cikin rada ya ce, "Ina ga wannan ya game komai da komai, idan ba mace mai kishin mijinta ba, ko macen da ke kishin abin sonta ba, ki fada min waye me yin hakan, don ta ji dan-uwanta ya yi aure? Just admit it, ki na sona.” Wannan miskilallen murmushin nan ne, har yanzu a Kunshe a fuskarsa. Zuwa yanzu
Umm Adiyya tafasa take yi, kamar tukunyar dan-wakenta da ke gefe. Domin abinda take ji a Kirjinta a wannan lokacin ya fi Karfin jin haushi. A tsanake tace, "Zaid Abdur-Rahman Nafada, ka fita daga nan kafin a daureni da laifin kisan kai."

************

BABI NA SHA DAYA

Duba daya ta ga ya yi mata ta idanunta da suka rufe da tsantsar baKin-ciki. Ba ta yi
aune ba, ta gan shi a gabanta daf! Kafin ta yi wata KwaKKwarar motsi kuwa ya sa hannu ya zagayeta, ba za ta ce ya rungumeta ba, amma dai jikin sa na taba nata, hannunsa kuma na zagaye da ita. Ga shi turarensa duk ya cika mata hanci, wanda zuwa yanzu ta gama tsanar Kamshin (Boss Orange), kamar ta Kona kamfanin (Hugo Boss). Cizo ta gantsara masa mai rai da lafiya a kafadarsa. Amma ko gezau. Bai motsa ba bare ya nuna ya ji zafi, idan ka dauke motsin ba zata da ya yi, a hankali ya saketa. Kallon hannunsa da za ta yi ne, ta ga wuKar da ke Www.bankinhausanovels.com.ng hannunta ya karba ba tare da ta sani ba. Bakinta yake kallo, wanda ta cije shi yanzu, "Kar ki damu, za mu iso wurin saurin me ki ke yi? Ni dai kawai burina ki so ni yadda na ke sonki, Twinkle." KanKance idanunta ta yi, tana masa duban rashin fahimta. Twinkle, idan ki na fushi ko murmushi, akwai wani yalki da ke bayyana cikin Kwayar idanunki, wanda ke riKe mai kallonki, ya mance kansa, hakan ya sa na kiraki Twinkle ina fatan sunan ya miki dadi? Saboda daga yau sunanki kenan." Umm Adiyya ta gama datse haKoranta har tana jin Kararsu suna Kas-Kas, Kashin kunnenta kamar zai kurme don tauna. Kalma daya ce ta zo bakinta. "Mugu!" Juyawan da za ta yi ne, ‘ya'yan hanjinta suka murda saura Kiris! Ta saki fitsari ganin Maami a tsaye a Kofar kitchen din.
Kafin ta yi motsin kirki. Maami ta juya ta fice a kitchen din. "Oops, someone is in trouble." Ya fada yana wata dariya Kasa-Kasa hadw da lumshe mata idanunsa, daga inda take tsaye, tana jin dirin muryarsa daga Kirjinsa. Cikin tsananin kaduwa Umm Adiyya ta ture hannunsa. "Ka sake ni, mugu kawai,
Allah ya isa, dan is..." Kafin ta Karasa fadi, ya sake janyo ta. Da ta ga da gaske yake, baida niyyar saduda. Kawai sai ta fashe da kuka. Idan ka ga ba ni da Karfin ramawa. Allah zai rama min.” Ba shiri ya sake mata hannaye, fuskarsa ta daure. "Kar ki sake kuskuren ce min Allah ya isa, na fada miki. Gaba idan za ki bude baki kiyi min magana, ki san da wa ki ke magana." Lokaci daya ya canza kamar ba shi bane ya gama yi mata abubuwan da ya yi mata yanzu.
Harararsa ta yi tana daga nesa, "Daman an ce maka mutuwar sonka na ke yi da ba zan rayu idan ban ganka ba, idan ka ga dama ka mutu.” Sai da ta fadi kalamanta, ta yi da na sanin fadarsu, wanda an ce Keya ce. Ko ba komai shi musulmi ne, kuma ba kyau Www.bankinhausanovels.com.ng musulmi ya zalunci dan-uwansa musulmi koda
kuwa da harshensa ne. Wani kasalallen murmushi ne ya ziyarci labban Zaid, "Ummu A, ko baki fada ba kowa mutuwa zai yi saurin me ki ke yi? Za ki tafi ko kuma sai na miki fiye da na dazu?" Tana harararsa ta fice daga kitchen din saura kadan ta ci tuntube ta fadi. Zuciyarta sai bugawa take yi, yau kam ta Kara tabbatar da zarginta. Zaid bai da kirki ko na misKala zarratin. Ya je can ya yi ta zama da matarsa. A take wasu hawaye masu zafi suka zo mata, yau ta yi da-na-sanin son da zuciyarta ta taba yiwa Yaya Zaid. Karar zubar kumfa a wuta ne, ya dawo da ita kicin din, da sauri da ta tuno girkinta da ke kan wuta, amma nan ta tarar da Yaya Zaid ya sa matsami a cikin tukunyar yana gauraya Dan-waken hade da rage wutar murhun, garin yin hakan ruwan zafin ya tsillu kan hannunsa, da sauri ya yarfe hannun hade da kai shi baki, ya hura wurin. Umm Adiyya ko ganinsa a haka bane ya kasheta da mamaki, illa iyaka tunani daya raK! Da ya ziyarci KwaKwalwarta. A take ta toshe wannan tunanin, ta Karasa ciki ta sa hannu ta karbi matsamin, shi kuwa ya sakar mata, ba tare da da yansu ya furta komai ga dayan ba.

*************

A ranar dai Umm Adiyya ta ci kuka har ta godewa Allah, ta canza kaya kala uku, bayan ta yi wanka da sabulanta masu Kamshi daban-daban, amma har lokacin ji take yi kawai kamar Kamshin Yaya Zaid take yi A haka Asma’ ta shigo da plate din cashew nuts a hannunta, ta same ta, "Subhanallah! Sis. Me ke faruwa na ganki haka a birkice? Kin ga yadda ki ka yi ja kamar tumatur kuwa? Tun yaushe ki ke kuka?"
"Adda Asma’ ki yafeni, idan an daureni ko an kasheni, ki yafe min duk abinda na yi miki, ranar ni na yar da chocolates dinki a dustbin, don kar haKoranki su rube, na fitar miki da (Ice Cream) dinki ya narke a sink, saboda kar ki sha, ki yi ciwon suga, ki
fadawa Adda Zubaida kuma ni na dauki littafinta na (The Prophet's Wives), da take ta nema, kin ji ko?"
Zuwa lokacin Asma’ ta gama gwalo idanuwa tana kallon 'yar-uwarta kamar kanta ya tsiro da Kaho. "Me ya faru Ummu A?" "Na kusa kashe Yaya Zaid a gidan nan." Abinda kawai ta ji ya zo bakinta kenan. Www.bankinhausanovels.com.ng
"Inna-Lillahi’ wa-Inna-Ilaihir-Raji'un! Ke kin san me ki ke fada kuwa? Yaya za ki irin wannan maganar, ba kyau fa. Idan ki ka zamo ajalinsa fa? Kin san kin kashe shin kenan ko?" "Sannu ‘yar mai shari'a, inji waye kenan hakan? To me za ki ce akan wulaKancin da ya min yau da safe kuma fa?" Asma’ kam zare idanu ta yi tana kallon ‘yar uwarta. "Me ya miki Ummu A?" "Yaya za a yi ya zo kusa da ni har ya dora hannunsa a jiki na? Akan dalilin me zai min wannan babban wulaKancin? Bayan ya san haramcin hakan a addini?" Kuka take yi da hawaye da majina, har da shessheKa. Ganin Asma’ ta daskare a wuri guda ne, ya sa ta Kara sautin kukanta, shi kenan ai ta sani ko ta fadawa kowa, ba mai yarda da ita kaf, gidan nan Yaya Zaid ya gama saye zuKatansu gaba daya. Ki yi haKuri, na san kuskure ne ba zai Kara faruwa ba, besides ko ya faru ma ai aikin gama ya gama.”
"Kuskure? Ban yi tsammanin abinda ya yi yana taba zama kuskure ba, kuma Allah zai saka min, da ni da matarsa da ya cuta." Sai a lokacin zancen Asma’ ya fado mata. Wani kallo take bin Asma’ da shi, "Me ki ke nufi?" Asma’ ta yi kamar ba ta fahimceta ba. "Da aka yi me fa?" "Me ki ke nufi da cewa da ki ka yi aikin gama ya gama? Take Asma’ ta shiga inda-inda. "Ba komai fa, ke dai kawai ki ci-gaba da addu'a kuma, tunda Abba ya ce bai ba ki damar kula kowa ba, ina ga ki saurara ki gani ko wani abin ya tsara miki?"
Ajiyar zuciya Adiyya ta yi, duk da ba wai ta yarda da abin da ‘yar-uwarta ta fada bane. "Ke kanki fa kin san me ya faru a gidan nan, tunda na ce naKi batun Yaya Zaid kowa ya dauki Kahon zuKa ya dora min. To laifina ne, don ba na son sa?" Kallon da Asma’ take mata ne, ya sa ta yi saurin maida hankalinta kan wasa da ‘yan yatsunta. "Adda Asma’, na san da na ce ina son shi, amma ai yanzu hankali ya sake shigata,
na san abin da yake dai-dai a gareni da wanda ba dai-dai ba. Don haka, ba laifi bane, don na ce ba na sonsa yanzu." Asma’u ta kai cashew nut bakinta ta tauna sannan tace, "Uhm, ban taba sanin mutum yana daina son mutum cikin sati uku ba." "Well, ki Www.bankinhausanovels.com.ng gwada kwana daya." Adiyya ta fada Kasa-Kasa.
"Me ki ka ce?” "Babu, ni dai kawai ki roKar min su Maami su yafe min. Allah zan yi KoKarin na fidda
wani mijin. Tunda kin ga Yaya Zaid din ma da suke fushi. Maami ta yi masa auren gata kamar yadda ta fada, wata Kila ma yana can ya mance da yace ya taba sona." Ta fada cikin datsattsen hakora. Ta san dama Karya yake yi, ba wani sonta da yakeyi, mutum mai sonka, ba zai maka wulaKancin da Zaid ya yi mata yau ba, bayan yana sane ita ba muharramarsa bace. Haka ya fada miki?" Muryar da suka ji daga
bakin Kofa ne ta kadawa Adiyya ‘yan hanji, domin koda wasa, ba ta san Yaya SaadiK yana kusa ba bare har ya jiyo maganarsu. "Yaya fa ba haka bane, kawai dai..." Idanunta sun riga sun cika taf da hawaye.
Ba wanda zai sa ki dole Ummu A. Amma ki tambayi kanki wannan abin har cikin ranki ya yi miki? Ki na ganin yadda iyayenmu suka ji zafin maganar nan." "Yaya Saadik, Abba da kansa ya taba fada mana babu kyau auren dole a musulunci. Annabi ya yi hani ga hakan. Don me ya Sa to ni suke so su min? Na ce ba na sonsa, ya haKura, ba shi kenan ba, tunda ya saduda?” BaKin-ciki ma maganar ta bawa SaadeeK, bai san lokacin da ya ce "Ki ci-gaba dai da rudin kanki, ki na ja da ikon Allah a kanki, domin kuwa Yaya Zaid bai haKura ba, asali ma saboda tafiyar da zai yi ne, da tuni kin tsufa a gidansa tun last week bayan
an gama biki." Ba shiri Umm Adiyya ta zabura tana Www.bankinhausanovels.com.ng karkarwa, bakinta ya kasa furta komai, sai bin ‘yan-uwanta take yi daya bayan daya da kallo. Idanunta na sauka kan na Asma’ ne, ta gyada mata kai game da lumshe mata idanu, alamar tabbatar da zancen Yaya SaadiK. Da gudu ta ruga ta yi falon Abba. Yana kurban shayi, sai ga ta ta fado cikin
falon. "Mamana lafiya kuwa?" Cikin gunjin kuka ta durKushe a gabansa, tana ihu tana birgima. Bai taba ganinta a haka ba, don haka hankalinsa ya tashi. "Ke meye hakan kuma?" Abba wai da gaske an daura aurena da Yaya Zaid?" Shiru ya yi bai ba ta amsa ba. Can dai ya nisa yace, "Ki saurara ki natsu ki daina
wanan kukan tukun, wa ya fada miki hakan?"
"Yanzu Yaya SaadeeK yake fada... Abba don Allah kar ku... kar ku yarda da shi Karya yake yi baya sona, zai kasheni Abba... Don Allah ku taimakeni ku raba ni da shi idan ma da gaske ne. Allah na yarda koma wa kake so na aura. Abba Allah zan aura, amma don Allah ku raba mu." "Ke ungo naki, meye hakan kuma?"
Daidai lokacin Maami ta shigo falon, ta ga yaran a baKin Kofa cirko-cirko ihun Umm Adiyya take ji kawai na tashi tana ta bori. Yau ta ga ikon Allah, wai me Zaid ya yi wa Adiyya ta tsane shi haka? Da ko a
tunaninta suna shiri ba laifi, kuma akwai girmamawa a tsakaninsu, kai yadda Asma’ ta fada kam Umm Adiyya da bakinta ta ce mata tana son Zaid, to yanzu me ya faru? Cire wannan tunanin ta yi, ta isa falon. "Ya isa Adiyya, tashi ki zo." Da Kyar ta kwantar da hankalinta, kadan ta rage kururuwan da take yi."Maami, ki na jin abinda su Abba suka yi min? Maami yaya za ayi na yi kishi da Fatima? Yaya za ayi na auri Yaya Zaid? Yaya zan rayu da wanda ba na so? Kowa yana auren wanda yake so a zuri'armu, daga yara har tsoffi, me ya sa ni za a min na dole?"
Abba ne ya taso ya tsaya kusa da su, ya rage Www.bankinhausanovels.com.ng tsawonsa. "Adiyya,  Wa yace miki auren dole akayi miki? Ba wanda baya sonki, dukkanmu muna sonki. Kuma Inshaa Allah duk abinda ya same ki, zai zamo miki alkhairi. Ni yanzu ki fada min da bakinki ga Maaminki ma, ki fada mana me ya sa ba kya son Zaid? Na zaci shi ki keso, ba haka ki ka fadawa Asma’ ba?"
Juyawa ta yi ta bankawa ‘yar-uwarta harara, wato ita ce mai tonon sililin. Aku mai tsinin bakin da ta bankade sirrinta. Ita ta janyo mata komai. Shi ya sa da safe Yaya Zaid ya yi mata abinda ya yi a kitchen, ya san ita matarsa ce, kuma shi ya sa Maami ba ta dago mata maganar ba, duk da ganinsu da ta yi a hakan. "Abba na daina son shi yanzu, daman ban gane meye bane, kawai shaKuwa ce ta ‘yan-uwantaka. Kuma Maami ba kun masa auren gatan ba, me ya sa za a hadla masa da ni?" "Kin manta auren gata ne? Ke extra aka Kara masa." Maami ta fada hace da wurga mata wata tafasasshen harara. Haushin Umm Adiyya take ji, idan ta ji tana cewa bata son Zaid, bayan kowa ya san halin da take shiga a kansa.
BaKin-ciki take ji kamar ta yi ihu, wato Maami ta nuna Karara ta fi son Zaid a kanta kenan. Har ma extra ake yi masa da ita. "Maami kun tsane ni ashe, ban sani ba? Abba shi ya sa ka turani wurin aikinsu, don ya yi ta cin zalina, duk duniya ba mai sona. Wayyo ni!" Wani ihun ta sake rusawa, har su ‘yan biyu sai da suka fito daga dakinsu da gudu suka samu diramar da ake yi. Hankulansu ne duka ya koma bakin Kofar falon inda Zaid ke tsaye, take hankalin Abba ya tashi, kar dai ya ji kalaman Adiyya? Bai san me yake damun yarinyar ba, ranar a gaban Yaya Abdu tace ba ta amince da

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 13 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...