UMM ADIYYAH CHAPTER 12 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 12 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 12 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

 UMM ADIYYAH CHAPTER 12 BY AZIZA IDRIS GOMBE


                  Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Mikewa kawai ta ga ya yi, zai tafi, "Uncle TJ."
Idanunsa ya zuba mata, hannayensa suna cikin aljihun wandon jamfarsa, "Idan har na zauna a nan Abba ya shigo, babu zancen ja da baya, zan fada masa abin da yake raina game da ke, idan kuma ba ki shirya zuwa wurin ba, to sai na ce Allah ya zabawa kowa rabonsa." Kwarai ita ta san yadda TJ. Ya so ta, kuma yake kan sonta, don dai bai da rawar kai
ne ma, amma da kowa ya dade da sani, sannan kullum yana biye mata, kuma gaskiyarsa idan har ba ta yanke hukunci cikin shekaru uku ba, har sai yaushe za ta yanke? Bai jira amsarta ba, ya fita daga gidan. Nan falon ta zauna ta sa fuskarta cikin tafukan hannunta gaba daya ta rasa me yake mata dadi Tana jin zaman Maami a gefenta, ba ta ce mata komai ba, ta fada cinyarta ta sa kuka, "Ummu, me ki ke so a rayuwa?" "Maami ban san me na ke so ba, ni dai kawai ki yi ta min addu'a." "Ba komai Boddo am, Inshaa Allah, ba za ki yi kuka ba. Tashi ki je ki kwanta ki huta." Ita kanta yanzu kam Maami lamarin Umm Adiyya yana damunta da gaske, yarinya WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
kamar mai Jinnul AashiK, ace kaf! Manemanta ta rasa wanda za ta so, ba dama ayi mata zancen aure, sai ta sa wa mutane kuka! Wayar Asma’ ce ta katse mata tunani, nan suka gaisa, take shaida mata akan za su taho Abuja washegari. Kwarai Maami ta ji dadi don tunda aka yi bikin ba su zo ba.

************

Tana saukowa daga sama, tana daura agogonta ne ta ci karo da Faruk, "Wallahi ku dai kun yi tsawo, sai ku yi ta tafiya hankali a sama, yanzu ina za ka, ka ke irin wannan saurin, za ka kade mutane?" "Maami ce ta aiken, ke ma ki na tafiya ki na sa agogo kam, ai har hantsilawa sai kin yi wataran.” Girgiza kai kawai ta yi ta wuce, tana zuwa falon, ta tsaya kallon abin da ke gabanta,Maami wannan fa?" Maami cikin fara'a da farin-ciki ta ke shaida WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG mata, "Kayan Zaid ne ake shiryawa." Cak! Ta ji numfashinta ya tsaya, wani irin mummunar bugu ta ji zuciyarta na yi a bangon Kirjinta, suma ne kawai ba ta yi ba daga tsaye, amma tabbas Kafafunta kam tamkar narkekken roba, suka koma kayan auren Yaya Zaid? Wato ma ya samu mata kenan. Ko shi ne auren gatan da suka ce za su yi masa? A shake ta ce, "Maami ya samu matar ne?"

************

BABI NA GOMA

Wani iri ta dubeta ta ce, "To da ke zai tsaya jira? Wancan satin su Abba suka je gidan Baffa Maikano, suka tambaya masa auren Fatima, kin ga ita da ta san darajar sa, da tushensa, ba ta ci masu mutumci ba, ta amince." Abu ta hadiye a wuyanta da Kyar sannan ta ce, "Allah ya tabbatar da alheri.” Ko bi ta kan kayan ba ta yi ba ta wuce mota, a guje ta Karasa zaman, don dai ba ta so su

ZAMU TASHI 

Maami su ga halin da ta shiga ne, shi ya sa sai da ta bar harabar gidan, ta rushe da kuka, yanzu Fatiman Baffa Maikano ce Yaya Zaid zai aura?
Wata zuciyar tace, "Me ye za ki damu kanki? Tunda ai kin daina son shi, to meye


naki don zai yi aure?" Sai dai duk da haka zuciyarta ba ta samu natsuwa ba. Fatima
Kawarta kuma 'yar-uwarta tare suka taso, ko ba komai, ba za ta bari ta hada rayuwa
da Zaid a cikin duhu ba. Sai dai yaya za ayi ta sanar da ita?  Www.bankinhausanovels.com.ng
Kuma abin haushin ma su Maami yadda ka san ba su da wata damuwa, gadan
gadan sai shirye-shirye kawai suke yi. Tun da aka fara maganar kuwa, ba ta sa Yaya
Zaid a ido ba. Yaya SaadiK dai shi aurensa da Sauda ba yanzu ba, sai farkon
shekarar da za a shiga, kafin nan gidansu Saudan sun gama shiri, kamar yadda
suka ce.
Kwatsam! Da safe sai ga shi ya shigo office rannan, ko kadan ba ta tsammaninci
ganin sa ba. Duk da yake sun kwana biyu ba su
yi general briefings ba, su kan yi na
Department dinsu, sai shuwagabannin ko wane Department kuma su hadu su sake
tattaunawa, domin sanin inda kowa yake a kan aikin da suke kai.
Wannan ya sa satin kaf! Ba ta sa shi a idanunta ba. Daga dawowarsa kuwa da
halinsa ya dawo, ashe wai tafiya ya yi tsawon kwanakin baya nan. Sai a bakin Hasan ta ji.
Yana sane da yadda ta kidime, gabaki daya haduwarsu a Reception, bai san dalili
ba, amma Kwarai ya ji dadiin ganinta, tamkar ita yake jira ya gani, tun shirgowarsa Kasar a daren jiya.
Wannan ya sa yana tashi a wurin aiki, gidan Abba ya nufa, duk da yana sane har
yanzu ba wai ta saduda bane. Ba ta kuma mance komai ba, amma ya san me ya Www.bankinhausanovels.com.ng
tanadar mata, don haka yake mata abinda yake SO.

********

Ita kadai sai sintiri take yi a daki, ta rasa abin da yake mata dadi. Akan me ya sa
bayan laifin da ta kama Yaya Zaid da shi har yanzu take jin tashin hankali, idan ta
tuna an ba shi matar aure?"Yaya za ayi ya kasance har yanzu akwai damuwarsa a tare da ni, sai me don zai yi aure? Ai yana da damar yin duk abin da yake
SO. Ta dai fadawa kanta haka ne kawai, amma kwanaki biyu ta jera ba ta iya barci, muddin dare ya yi, wannan abin ne ya tsorata ta. "Babu wanda na tsana irin Yaya Zaid, don haka ya zama dole na daina tunanin sa." Sai lokacin ne ta ji wata Kila yin aurensa zai sa ta mance da shi, yanzun don tana yawan ganinsa ne.

***********

Gidan a cike yake, kai kace nan aka haife shi, baKin-ciki kawai take yi, duk inda ta juya ta ga dangi suna murna, to su ya su ma sun cika gidan. Duk da dai a Abuja suke, amma nan aka tarkado aka taho, kasancewar gidan Baffah Maikanon a
Kaduna yake, wasu can suka yi, wasu ko suna Gomben ma ba su taho ba. Ga shi kuma Zaid nan gidansu ya tashi. Har da su Adda Asma’ da Adda Zubaida a ‘yan zuwa bikin. Ba ta kula kowa, sabgar gabanta take yi kawai, idan ta dawo gida kuwa ta auki littafi ta hau karatu. Maami don jaraba kaf! Kawayenta har da na wajen gari, sai da ta gayyata da duka danginta,
wai auren babban danta. Bandaki ta shiga ta ci kukanta son ranta, sannan ta wanko fuska ta fito. Nan tsakar dakin ta samu Adda Zubaida da wata jaka. "Meye haka, kin shiga kin zauna a bandaki ana ta jiranki. Ga wannan inji Maami ki shirya ki fito, an fara tafiya wurin Walima."” Kallo ta bi Adda Zubaida da shi na tsoro, daga bisani ta dawo hayyacinta ta ce, "Ku je ni kaina ciwo yake yi tun a ofis, shi ya sa ma na dawo da wuri yau." Ta Karasa magana tana goge fuskarta da dan Karamin towel din hannunta mai laushi. "Wallahi taurin kanki sai ke, na kula tun zuwana ki ke wani Kin shiga jama'a. Ki na ga ya dace ace ana sha’ani a gidanku, amma ke ko a jikinki, ba kya ko kula mutane bare ki yi fara'a, ko ki gaishesu, sannan me mutane ki ke zaton za su ce? Idan sun
ga halin da ki ke nunawa a auren Yaya Zaid? Bayan sanin cewa tamkar Yaya SaadiK, haka yake garemu. Sannan Fatima kusan Kawarki ce me za ta yi tunani
idan ba ta ganki a wurin walimar ba?" Wani juyi ta ji hanjinta sun yi a cikinta, nan da nan ta hau hada gumi. Da gaske fa an dura auren Yaya Zaid da Fatima kenan, tunda har an dauko amaryar za aje walima.
Numfashinta ne ta ji yana fita da sauri-sauri, can ta ji Kirjinta ya Kulle. Nan da nan ta hau lalumen abin dafawa, idanunta suna rufewa cikin alamun Www.bankinhausanovels.com.ng KaKKafewa. Adda Zubaida ce ta kula da halin da take ciki tace, "Umm A. Lafiyarki Kalau?" Nafisa ‘yar Goggonsu Amina ce ta Karaso cikin dakin daidai lokacin, ganin halin da Adiyya take ciki ne, ya sa ta Karasa da sauri kansu ta ce, "Adda Zubaida riketa, tana hyperventilating ne.” An yi sa'‘a ta san kan aikin asibiti, nan dai ta sa Umm Adiyya tana fidda numfashi ta baki, tana mayarwa a hankali, har suka samu ta dan lafa. Ta yi mintoci ba ta san inda take ba, kafin can ta soma motsawa. Adda Zubaidan ce ta kalli Nafisa da neman Karin bayani. "Me ya faru? Ba ta taba yin hakan ba." Ban sani ba, ina ga dai numfashinta ne ya toshe mata ko ta shiga shock." Kallon juna suka yi na can lokaci kadan, sannan Adda Zubaida ta ce, "Ki zauna da ita, bari
na kawo mata ruwa ta sha." Haka ta fice cike da mamakin Umm Adiyya, Kwarai kanta ya kulle, ta shiga tunani. Daga baya ta yi murmushi, ta wuce dakin
Maaminsu inda take tare da Kawayenta.

***********

A hankali ta rinKa jin hayaniyar na raguwa, da alama duk an watse zuwa wurin Www.bankinhausanovels.com.ng

Walimar. Tun da ta farka a barcin da ya dauketa, sai ta dan samu sauKin abin da ta ji dazu, wanda ita kanta ba ta san me za ta kira shi ba. Tashi ta yi ta watsa ruwa, tasa atamfarta mai kyau riga da skirt, ta daura dan-kwalinta, ta sa 'yan-kunnen da suka shiga da shi, ba ta sa sarKa ba, ta fesa turare.
Ba komai ya sa ta wannan shirin ba, sai don Kara tunanin da ta yi kan maganar Adda Zubaida, ko ba komai baKin da za su zo, ba za su fahimci halin da take ciki ba, bare su fahimci rashin shiryawarta da kuma shiga cikin hatsaniyar gidan.
Kuma ko ba komai, ba Zaid bane ke aure yau din, dan su Abba da Maami ne ke aure, don haka ko don su, za ta nuna farin-cikinta, shi kuma rayuwarsa ce, ya yi
yadda yake so. Fitowarta daki. Kitchen ta nufa, ta samu wasu ma’aikata da kuma wasu jama'arsu na Gombe tsiraru. Ko ina a kimtse, an jera buffet dishes a kan tebur tebur din kicin din, budewa ta yi ta debi abinci dan kadan. Ta debi Mocktail a kofi, sannan ta sake komawa dakin, don ta san sun kusa tasowa
daga walimar, amma ba ta son ta hadu da jama'a, ayi ta tambayar inda ta shiga, dazun ma tana ji, ana ta cewa ba aga Ummu A. Ba, sai su Adda Asma’ aka bari da aukin cewa ba ta ji dadi bane, tana barci. Ba ta dade da zama a dakin ba kuwa da littafinta a hannu na (Bob Miller), tana karatu ta ji Karar motoci suna shigowa da rufewa da bude Kofofi, nan da nan kuwa
Sai ga ‘yan-uwansu na kusa, ‘yan matan da kuma sa'‘o'in su Adda Zubaida sun fara shigowa.
Ummu A. Kin yi missing yau, mun sha nasiha mun ci dadi." Asma’u ta fadia. "Ko? Kun sha aiki. To sannunku da jin dadi." Cokalinta Asman ta dauka ta kai baki tana cin abincinta. Umm Adiyya ta janye kwanon gabanta, "Yaya dai Malama, ke da ki ka ci dadi, me ya hadaki da jollof dina?" "Ke ma kin sanni da Party jollof rice, don Allah dan ban na Kara."
"Wallahi ba za ku bar mutum ya yi kiba a gidan nan ba, duk ku yi ku koma gidajenku, ku yi yadda ku ke so, ku bar mutum ya wala." Maimuna Kanwar Nafisa ce ta ce, "Na ga dai mutum ba tabbata zai yi a gaban
Maamin ba." Ta fada hade da yi mata gwalo. Www.bankinhausanovels.com.ng
Arghh! Me ya sa ku ka dawo ne ma? Ki bar min abinci na, wannan ma ba isata zai yi ba.” Ji suka yi an KwanKwasa Kofar, duk da kuwa a bude take, wannan ya sa Adiyya ta san cewa namiji ne zai shigo, don dabi'arsu ce su KwanKwasa Kofa, sannan su yi
sallama a kowane Kofar daki a gidan kan su shiga.
Zaid ne a tsaye a bakin Kofar, yana fara’a cikin farar shaddar da aka yiwa aiki da
zare ruwan toka, haka hularsa launin ruwan toka. Ya sha rantsatsen agogon silver, bai cire babbar rigar ba, kuma sai ta yi masa kyau. Suna hada idanu ta ga murmushin fuskarsa, ta kawar da kai. Nan da nan sauran ‘ya’yan baffaninsu da goggoninsu da su Asma’ suka fara masa,Ango! Ango!! Ba takalma a Kafafunsa ya Karaso cikin akin, "Ba wanin nan, kun zo kun bar min amarya a baya, sai da na sa Maami ta taho da ita, za ku bi ku wani isheni da Ango, Ango."
A to, mun san ko ba mu yi ba, za ka yi yadda ka ke ji da wannan amaryar. Besides mun tafi mun bar 'yar-uwa ba lafiya, shi ya sa muka dawo, mai motar wai za ta tafi ta bar mu, idan ba mu biyota ba. Ayi haKuri kar ayi mana rowar abincin amarya, idan mun je." Yana murmushi har yanzu ya ce, "Kar ku damu, amaryata ba ta rowa, ko ta wane fanni."
"Tunda ka na neman fada, ai dole ka ce haka." Muryar Umm Adiyya suka ji ta yi magana, bai kula ta ba, sai ma Karewa plate cinta kallo da ya yi ya ce.
"In dai haka ake rashin lafiya, ashe ba za a samu matsalar rama a ciwo ba." Ya fada, yana nuni da plate din gaban Umm Adiyya, dago idanunta ta yi ta watsa masa harara, ba ta ko ji nauyin idanun jama‘ar dakin ba. Ta ci-gaba da cin abincinta, tana
kallonsa. "Zubaida na ke nema, ba na samun wayarta." Ya fada hade da kaucewa kallon da suke sakarwa juna, shi da Umm Adiyyan. "Ai kuwa ina ga bata da caji ne, bari na dubo maka ita.” Nafisa ta fada. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kallo daya ya sake yiwa Umm Adiyya, sannan ya fice daga dakin. Asma’u da Maimuna suka tafa suna kallon juna. Umm Adiyya ko gaba ki daya haushin kowa take ji, kamar ta tashi, ta gudu daga gidan. Haka dai aka Karasa hidimar. Washegari lahadi kowa ya kama hanyar gidansa, sai Asma’u da ta rage, wani sati za ta koma Kaduna.

*********

Bayan sallar Asuba, yau ma ta shiga dakin Maami gaisheta, kamar kullum, don idan
ta yi wannan gaisuwar, tunda aka fara bikin, to sai ta shirya ta gudu office, kafin
baKin su tashi ko su fara zuwa. Haka ta yi ta yi har aka gama bikin. Sau biyu Maami
ta tursasata aka hadu a falon Abba jiya da dare aka yi Family Picture. Wanda aka tursasa mata saka sabon dinkin da Adda Zubaida ke ta bin ta da shi.
Ba dai ofis dai yau ma za ki je ba da asuba?" Dariya ta dan yi hade da sunkuyar da kai, "Maami ai yau ma Lahadi ba aikin, kawai dai na saba tashi da wurin ne."
Shiru ta dan yi kafin ta daure, muryarta na dan rawa tace, "Maami, a ina Fatiman take ne, ba mu gaisa ba?" Murmushi ta yi ta ce, "Ummu kenan, ke da kowa ya yi ta tambayarki, kamar an miki layar bata bat! Ki ka bace a bikin nan, ba wanda ya ganki ko wurin walima? Na zaci ko kishin Zaid ki ka soma yi ai."
A zabure Umm Adiyya ta kalli mahaifiyarta, ga-rin yin hakan har ta Kware da yawun bakinta, bayan ta samu tarin ya lafa ne, inda Maami ta miKa mata robar ruwan da ke gefen sallayarta a ajiye. Umm Adiyya ta zaro idanu hade da fadin "Maami..." Koda yake na manta, ba a son dan nawa ma bare ayi kishinsa. An kai masa Fatima tun jiya da dare." Wani abu gululu ta hadiya da Kyar, sannan ta ce, "Allah ba su zaman lafiya." Da sauri ta tashi ta juya ta bar dakin. Maami ta bita da murmushi a fuskarta. Wai Www.bankinhausanovels.com.ng wani bata sonshi da aure. To an masa aurensa, kya ji da shi.

***********

Tunda ta bar dakinsu domin shiga gaida su Maami a safiyar yau ma, ta ji ba za ta ma iya komawa daki ba, bare ta sake yin wani abu wai barci, domin da zarar ta kwanta wasu maha'intan hawaye suke zubo mata, ba ta tantama na yaudarar da ta yiwa Fatima ne, da ba ta sanar da ita gaskiya ba, da kuma na tausayin... Ina, ba ta tausayin kowa, yaya ma Za ayi ta ji tausayin kanta? Tunane-tunane ne suka yiwa kanta cunkus! Har ta kai ta fara ganin jiri. Kafin ta
zauce ta zabi abu mafi sauKi gareta, kicin ta wuce ta hau kwabe-Kwaben abinci. A hakan ne ta kwaba garin dan wake himili guda ta dora makekiyar tukunya a kan murhu. Hannunta cikin Kullu, bayan ta gama kwabawa. Ta juya wurin kwarmin wanke-wanke don ta dauraye hannayen nata ne kawai tayi turus!
Agogon bango na kicin din ta kalla, Karfe takwas saura na safe. Me ya kawo ka gidan mutane da sassafe, za ka haddasa masu bugun zuciya?
Akwai abin da ake kira sallama, idan za a shiga kan jama‘a." Murmushi ya yi yana Kare mata kallo, daga saman kanta har Kasa a rufe yake ruf! Da doguwar rigar sallar da ke hade da hijabi a jiki, wanda ba ta cire ba, tunda ta yi sallar asuba, saboda ta fi so sai ta gama komai, sai ta hau sama ta shirya. Ba dai jama'a ki ke da shirin bawa wannan abincin ba?" Ya fada hade da yatsine fuska, ta gane me yake nufi Www.bankinhausanovels.com.ng sarai. Domin kuwa saran mutan gidan ne. Musamman
samarin, wai su ba za su ci Kazantaccen abinci ba, a tashi ba wanka kawai a shiga a hau girki. Idan ma jama’ar ne ai, ba a gayyaceka ba, idan kuma ka manta ne, to bari na yi maka tuni, an kai maka mai ba ka tuwo tun wancan satin, wacce ba tantama ka
sulalo ka bar ta ita kadai ka taho kwadayi gidan mutane. Za ka iya zuwa ka uzzura mata, ita ce a ka sanka da ita." "Yaya za ayi ki shiga kicin ba ki yi wanka ba?" Yadda ya yi maganar a Kyamace, sannan a tsaurare ya so ya ba ta dariya, tamkar ta aikata wani zunubi. Hannu ta sa a kwankwasonta cikin mamaki, "Ina ruwanka da abincina, bare wankana? Tunda ko ba ku da gami, zan yi duk yadda na ke so."
Ni ma zan ci, amma gaskiya ki je ki yi wanka, sannan ki zo ki daura min nawa." Tana sane sarai, abincin da Yaya Zaid ya fi so kenan duk duniya, amma tsabar
tsantseninsa ya sa baya iya cin ko na waje ne, sai na gida. Shi kam an ce yana yaro Www.bankinhausanovels.com.ng
ma idan an je unguwa, haka yake komawa gida da yunwa, saboda kar ya ci abincin waje. Amma yau tsabar haushin da yake ba ta, ji ta yi da tana da halin zama Kudan zuma
a lokacin za ta cicciji Yaya Zaid, da shi ne burinta na Karshe. Juya idanunta ta yi cikin nuna halin ko in kula, ta bude famfo ta saki ruwa, tana

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 12 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...