UMM ADIYYAH CHAPTER 11 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 11 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 11 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 11 BY AZIZA IDRIS GOMBE             WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

MUN TSAYA 

sannan kayan sun mata das! Ba su rinjayeta ba.
Ta yi fes! Cikin shigar mutumci. Jakarta ta komfutar ma ta dauko marar nauyi (Fibre) ta ajiye babbar. Kai tsaye ta gaishe da mutanen da suke babban falon, sannan ta wuce ofishinsu, dukkansu idanu suka zuba mata. Dubansu ta yi ta ce "Lafiya?" Hasan ya ce, "Hajiya, yau dai wani abin ya faru ne hala?" Me ku ka gani?" Ayo ya ce, "Yau kin wuce ba ki goge hannun Kofa ba da Dettol."
Murmushi ta yi ta ce, "Wasu lokutan ya kamata mu rinKa morar Kananan abubuwa a rayuwa, saboda haka wataran muna buKatar germs din rayuwarmu su koya mana darasi." Yau kuma adon magana ake jin yi ne?" Ayo ya fada cikin turanci. Nan dai aka gaisa, yadda ta ji suna ta tambayarta jiki ne, ya ba ta tabbacin Karyar da Ogan nasu ya masu kenan, koda yake ba ta sha mamaki ba, tunda ya yi kos a wannan fagen. Hankali kwance ta rungumi aikinta gadangadan! Sai dai duk inda ta san za su hadu da shi, ba ta bari haduwar ta yi tsawo, ko kuwa ya zama su biyu ne, duk kiyayewa

ZAMU TASHI 

take yi. Da haka ne har sati biyun Abba ya cika, don haka ta ce ita Yaya Nazeef take so.
Ita kanta ba ta san ina wannan tunanin ya zo mata ba, koda ta fadawa Maami ma
kallon mahaukaciya ta yi mata ta ce, "Ke kam shashashar ina ce? Kin maida mu
mahaukata ne ko kuwa inda ki ka ga dama nan za ki gara mu. Ai duk wanda rai zai yiwa dadi, baran mai shi ne.” "To Maami na ga dai shi ne babba, kuma shi ma bai yi auren ba, tunda zumunci ai duk zumunci ne." Maami kam yau Umm Adiyya ta Kureta, don haka gwabe bakinta ta yi, ta WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG rarranKwansheta har da dundu lafiyayyu guda biyu. Wane irin hauka ne, bayan ki na gani Zaid ya ce ke yake so, za ki ce za ki auri wansa? Ai sai dai duka ki haKura da su, idan dai ba Zaid za ki aura ba, to ki tabbata a haka, amma kar ma ki fada Abbanku ya ji. Kuma shi Nazeef din, shi yace miki ke yake so?" Tsumewa kawai ta yi tana KunKuni. Niyyarta idan aka bari ta auri Yaya Nazeef, shi ne za ta yiwa Zaid yadda take so, tunda ko ba komai, dole ya ba ta girmanta.

************

Kullum aikinta daban ne, koda kuwa ya dace ya raba shi gida biyu, ba don komai ba saboda ta yi complain, amma ya ga ko a jikinta, yanzu ko ya rage sintiri a ofis din, don baya son ma’aikatan su fara tunanin yana ba ta kula na musamman. Sun fito daga (Meeting) ne ya hango wannnan Dan Ibiran da jakarta a hannu suna sauka, za su wuce cin abinci.
Oh, Umm Adiyya! Me ya sa ba kya jin magana yarinyar nan?" Ya fada Kasa-Kasa.
Sa kai ya yi ya fasa shiga ofis dinsa, ba ta san hawa ba bare sauka, kawai ta ji mutum a gefenta.
Sorry, if you don't mind." Ya fada hade da karbar jakar a hannun Musa, ya rataya suka ci-gaba da tafiya. Umm Adiyya, kam ji tayi kamar ta nitse cikin Kasa don kunyan da ya ba ta, suna fita, ya dauki jakar ya rataya mata, "Kin faye son jiki, kullum yana nan biye da ke, kamar wani dan koren ki, idan ku ka yi auren ma, haka za ki maida shi mijin ta ce?"WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
A tsume ta juyo tana duban sa, duk da har yanzu wasu lokutan yana da tasiri a tare da ita, amma tsanar da ta yi masa ya rinjayi komai, don haka ba ta shakkar fada masa duk abin da ya zo mata rai.
"Ka fiye shiga sha'anin da bai shafe ka ba, idan na yi aure kuma abin da na yi da mijina da abin da zan maida shi, ai bai shafe ka ba, don haka ka yi abin da ya shafe ka." Ta fada Kasa-Kasa kamar yadda shi ma ya fada, kasancewar hausar Musan sai a hankali, ba lalle bane ya ji duk abinda suka fad ba. Jin haka ya sa Zaid ya yi masa murmushi ya ce, "Kar ka damu zan kai ta Lunch. Na huttashe ka yau." Musa dai jikin sa ya yi wani iri, ko ba komai ya san gulmarsa suka yi
Ita mamakin Karfin halinsa ya hanata magana, kuma tana ji, tana gani, ya karbi makullin a hannunta ya bude motar, sannan ya umarceta da ta zauna.
Girgiza kanta ta yi, domin da ta zauna, su tafi tare gwamma ta wuni da yunwa. Juyawa kawai ya ga ta yi ta koma ciki. Daga kafadarsa ya yi cikin rashin damuwa, ya tada motar ya yi tafiyarsa. Sai wajen Karfe biyu da rabi ya dawo. Kai tsaye ya shiga, don ya ba ta makullinta, ya samu tana ta aiki. Tsayawa ya yi a bakin Kofar yana Kare mata kallo, har Kasan
idanunta sun yi duhu, saboda yadda take aikatuwa a ofis din, take ya ji wani abu ya motsa a Kirjinsa, nan da nan ya yi gyaran murya, sannan ya ajiye mata makullan kan tebur hadda ledar abinci da ya mata take away. Kallonsa kawai ta yi ta ci-gaba da aikin da ke gabanta. Tana duba wani Prototype (Samfur) ne, ta ji ya ce, "Meye tsakaninki da Www.bankinhausanovels.com.ng wannan Musan ne?" Shiru ta yi ba ta amsa masa ba, wannan ya sa ya ci-gaba, "Na ga sai wani shisshige miki yake yi, sonki yake yi ko? Ina ga sai na raba maku wurin aikin ma, sannan ku rinKa maida hankali dukkanku."
"To sai ya yi laifi, don yana sona? Ban ga dokar kamfaninku a rubuce cewa babu
daman wani ya auri wata ma’aikaciya ba, idan kuma yau za ka KirKiro dokar, ina ga sai ta fara aiki a kanka." Ransa ya yi wani iri da kalamanta, "Ki na ma son shi kenan?" Ban tsammanin wannan yana cikin aikin kamfanin nan ba, don haka bai shafe kaba."
Rankwafowa ya yi saman teburin da take aiki a kai, sannan ya rage muryarsa kadan. "Na san ba za ki iya son shi ba, saboda har yanzu NI KI KE SO."
Kwarai ta razana da jin furucinsa, yaya aka yi ya gane tana sonsa? Koda yake yaya aka yi ya san ta taba son shi a da? Anya ba canka ya yi ba kuwa? Ko zai mutu ba zai taba sani ba daga gareta, ita kuma.
Wani irin kallo ta watso masa mai zafi, "Ka san meye matsalarka? Koda yaushe kana dauka cewa komai a duniya da ke gefenka, dole ne ya kasance da kai. Guess what? Amfaninka bai kai hakan ba, (You're not that important)." Kallon idanunta kawai yake yi har ta yi shiru. "Idan ba za ka damu ba, ka hana ni aiki WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
kuma Ogana ya ba ni umarnin yau yake so, na gama abin da ya sani. Wasunmu aiki ne ke kawo mu wurin aiki." Yana sane da gatsen da ke cikin zancenta, murmushi yayi mai zafi, sannan ya rage muryarsa ya yi Kasa-Kasa, "Adiyya... Why? Me ya sa kike Complicating abubuwa?" Ta tabbata yanzu kam wani abu ya kwance a kan Yaya Zaid. MiKewa ta yi ta isa
inda Printer yake, domin ta dauki takardar da ta tura domin Printing. Shigowar abokin aikinta Ayo ne, ya sa dole ya bar ofis din, ko bai tafi ba, ba ta da
niyyar mutunta maganarsa da ba shi amsa, don haka shi ya jiyo. Da ta tashi tafiya, ta tada motarta ba ta ji mamaki ba, ganin ya yi mata full tank. Oho, ka yi a banza." Kwanaki uku ya dauka yana biye mata. Amma bai ga alamar tana da niyyar sauraren sa ba, shi kuma babu abin da ya sa a gaba, illa yau ya ga ya mallaketa, domin nan ne kawai zai samu natsuwarsa da kwanciyar hankali, har ma ya tabbatar da cewa ba za ta taba budar bakinta ba. Don yanzu sam ba wai garanti yake da shi akan shirunta ba, duk sanda ta bushi iska ta yi niyyar magana, to tabbas nasa ya same shi. Don haka ya daina shiga sha‘aninta kwata-kwata, ya koma ya rike girmansa da ya cancanta kowa ya gan shi da shi, a matsayinsa na babba a kamfanin. Ta ji mamakin yadda aka yi lokaci guda kawai ya daina shiga sabgarta, duk da ba ta
yi tsammanin hakan ba. Sai ta ji ta damu da rashin ganinsa a kai-kai. "Umm Adiyya, ki daina tunaninsa, akan dalilin meye rashinsa zai daga miki hankali WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
ke da ki ka wuce shafinsa a rayuwarki?" Ita kadai sai magana take yiwa kanta, saboda ta Kara jaddadawa kanta abin da kenan.

**********

Tana fitowa ta hango kamar shi ne yake fita a harabar ma’aikatar, daga Kafa ta yi, ta same shi. Ai kuwa tabbas shi ne, "Uncle TJ.!" Juyowa ya yi cikin fara'arsa ta kullum, fararen haKoransa suka bayyana, yana kallonta, "Ummu A? Ki na duniya ashe?" "Ina nan, kai ne ka share mu ai, ba ka neme mu ba."Murmushi ya yi, yace, "Ki bari kawai, ina ta Kokarin settling ne, yaya su Maami?" Lafiyarsu Kalau. Me ka zo yi a nan?" "Wani aiki na zo yi, ke fa?" "Ai nan na ke aiki." "Haba dai! That's nice." Kallonta ya tsaya yi yana murmushi, ita kuma ta rasa abin da za ta ce masa. Ganin shirun ya yi tsawo, ta ce masa. "Bari na wuce gida, ya kamata ka zo dai kaci abincin Maami." Ita kanta ba ta san me ya Sa ta gayyace shi ba, amma zancen gaskiya, ta rasa abin fadi ne. Har yanzu fuska a sake ya ce, "Kar ki damu, ina da niyyar zuwa, har naki ma , amma ina fata banda mi yar kuka?" Kunya ta ji ta dan kau da kanta, ganin kamar tana takure ya ce, "Anyways, zan kiraki kafin na zo, may be zuwa Juma'a da yamma, a daren idan Allah ya kai mu" Yana fadar haka, ta yi murmushi ta ce, "Daren dai ko? Tunda Adda Zubaida ta riga ta yi maka shaida." Fadada fara'arsa ya yi ya ce, "Right, sai na zo kenan."
To Allah ya kai mu.” Nan suka yi sallama, ta wuce sai da suka rabu, ta shiga tunanin idan TJ. Ya je gida me za ta ce wa su Abba? Meye dangartakarsu? Kawai
Kanin Baban Walid, shi kenan abu mai sauKi.
Ganin ta samu mafita, ya sa ta yi murmushi ta fada mota abin ta. (Sahad Stores) ta wuce daga nan.

************

Corn-flakes ta jiKo ta zauna tana aikin kwadayi, shaf! Ta manta sun yi da TJ. Zai zo ran Juma'a, sai wayarsa kawai ta samu yana tambayar adireshinsu. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Da sauri ta zabura, cikin sauri-sauri ta fara fada masa, sai ta kula baya ganewa "Ina sauri ko?"
Murmushi ya yi a hankali cikin KoKarin danne dariyar da ta taso masa, "Uhm-uhm Wuse ki ke kwatanta min, amma na zaci gidanku na Maitama, me zai hana ki yi min tes din adireshin?" Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce, "Ka yi haKuri bari na bawa Fa’iz ya kwatanta maka. Ban iya kwatance bane." Ta san Karya take yi duk rudewa ta yi. Kafin ya ce wani abu, ta kashe wayar ta make goshinta, "Umm Adiyya, idan su Abba
ba su gane waye TJ. Ba, ke za ki fallasa da kanki, ki natsu da kyau!" Ta yi wa kanta fada, sannan ta wuce neman Fa’ iz. Gaba daya sai take jin ta a tsarge, duk da kusan kullum lokacin wankanta kenan, amma da ta zo shiryawa, sai take tunanin idan ta shafa hoda, zai gane har ya yi tunanin ko don shi ta yi kwalliyar.
Don haka ta bar fuskarta sumul! Haka nan, a darare ta isa dakin Maami tace mata, "Maami Uncle TJ. Ne ya zo wai za ku gaisa."
Kallon tsaf! Maami ta yi mata, sannan ta ce, "Ina saukowa." Ajiyar zuciya ta yi ta juya idanunta a hankali, yayin da take jan Kofar, don ta zaci
Maami za ta tambayeta ko waye shi? Kai ita ma dai da garaje take. Sosai ta shirya masa abubuwa, duk da wasu abubuwan Maamin ce ta yi, amma ba ta ce mata komai ba. Kwarai TJ. Ya ji dadin yadda ya samu karbuwa wurin Umm Adiyya. Musamman yadda Maami ta fito suka gaisa a mutumce, suna gaisawa ya ce, "Maami na gaisheku, ni zan wuce. Daman na ce bari dai na ga wurin." Ai ka kyauta kuwa sosai. Yaya wurinsu Hajiya?" "Duk lafiyarsu Kalau."WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
"Madallah, amma ka tsaya mana ka sha ruwa, ina ga yanzu Abba ma zai shigo, sai ku gaisa." Ba daman ya ce mata a’a, don haka ya yi mata godiya, tana fita a falon Umm Adiyya ta miKe za ta tafi ya ce, "Ina zuawa kuma?" Zaro idanu ta yi ta ce, "Ba ka ji me Maami ta ce ba? Yanzu Abba zai dawo, so ka ke yi ya Zo ya ganmu tare?" Kwarai ya ji wani iri a ransa ya ce, "Ummu A. Zauna mu yi magana." Ganin ya sha mur! Ya sa ta samu wuri, "Yanzu kam fa da ni da ke duka ba yaro a cikinmu, kuma ba zan tsaya wani kwanekwane da ke ba, na dawo rayuwarki ba da
wata manufa ba, sai kan batun dai na da, don haka ki fada min kai tsaye tafiyar mu za ta yiwu, ko kuwa ki na da wani a ranki? Don yanzu ba zan iya jira ba kuma." Shiru ta yi kawai tana rarraba idanu, don gaskiya ba ta san me za ta ce masa ba, "Ke na ke saurare? "Ni dai gaskiya yanzu ba kowa a raina, don haka ba zan iya ce maka komai ba, ina bukatar time."
Kallonta ya yi cikin rashin yarda da abin da ta fada, ya dan girgiza kansa yana murmushi, "Shekaru uku idan ba su isheki tunani ba, ban san wane lokaci za ki diba ba. Don haka ina ga bazaki taba shiryawa ba.”
Mikewa kawai ta ga ya yi, zai tafi, "Uncle TJ."
Idanunsa ya zuba mata, hannayensa suna cikin aljihun wandon jamfarsa, "Idan har na zauna a nan Abba ya shigo, babu zancen ja da baya, zan fada masa abin da yake raina game da ke, idan kuma ba ki shirya zuwa wurin ba, to sai na ce Allah ya zabawa kowa rabonsa." Kwarai ita ta san yadda TJ. Ya so ta, kuma yake kan sonta, don dai bai da rawar kai
ne ma, amma da kowa ya dade da sani, sannan kullum yana biye mata, kuma gaskiyarsa idan har ba ta yanke hukunci cikin shekaru uku ba, har sai yaushe za ta yanke? Bai jira amsarta ba, ya fita daga gidan. Nan falon ta zauna ta sa fuskarta cikin tafukan hannunta gaba daya ta rasa me yake mata dadi Tana jin zaman Maami a gefenta, ba ta ce mata komai ba, ta fada cinyarta ta sa kuka, "Ummu, me ki ke so a rayuwa?" "Maami ban san me na ke so ba, ni dai kawai ki yi ta min addu'a." "Ba komai Boddo am, Inshaa Allah, ba za ki yi kuka ba. Tashi ki je ki kwanta ki huta." Ita kanta yanzu kam Maami lamarin Umm Adiyya yana damunta da gaske, yarinya WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
kamar mai Jinnul AashiK, ace kaf! Manemanta ta rasa wanda za ta so, ba dama ayi mata zancen aure, sai ta sa wa mutane kuka! Wayar Asma’ ce ta katse mata tunani, nan suka gaisa, take shaida mata akan za su taho Abuja washegari. Kwarai Maami ta ji dadi don tunda aka yi bikin ba su zo ba.

************

Tana saukowa daga sama, tana daura agogonta ne ta ci karo da Faruk, "Wallahi ku dai kun yi tsawo, sai ku yi ta tafiya hankali a sama, yanzu ina za ka, ka ke irin wannan saurin, za ka kade mutane?" "Maami ce ta aiken, ke ma ki na tafiya ki na sa agogo kam, ai har hantsilawa sai kin yi wataran.” Girgiza kai kawai ta yi ta wuce, tana zuwa falon, ta tsaya kallon abin da ke gabanta,Maami wannan fa?" Maami cikin fara'a da farin-ciki ta ke shaida WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG mata, "Kayan Zaid ne ake shiryawa." Cak! Ta ji numfashinta ya tsaya, wani irin mummunar bugu ta ji zuciyarta na yi a bangon Kirjinta, suma ne kawai ba ta yi ba daga tsaye, amma tabbas Kafafunta kam tamkar narkekken roba, suka koma kayan auren Yaya Zaid? Wato ma ya samu mata kenan. Ko shi ne auren gatan da suka ce za su yi masa? A shake ta ce, "Maami ya samu matar ne?"

************

BABI NA GOMA

Wani iri ta dubeta ta ce, "To da ke zai tsaya jira? Wancan satin su Abba suka je gidan Baffa Maikano, suka tambaya masa auren Fatima, kin ga ita da ta san darajar sa, da tushensa, ba ta ci masu mutumci ba, ta amince." Abu ta hadiye a wuyanta da Kyar sannan ta ce, "Allah ya tabbatar da alheri.” Ko bi ta kan kayan ba ta yi ba ta wuce mota, a guje ta Karasa zaman, don dai ba ta so su

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 11 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...