UMM ADIYYAH CHAPTER 10 BY AZIZA IDRIS GOMBE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UMM ADIYYAH CHAPTER 10 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 10 BY AZIZA IDRIS GOMBE

- - Post a Comment

UMM ADIYYAH CHAPTER 10 BY AZIZA IDRIS GOMBE               WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG MUN TSAYA 

Sai dai yau kar ka koma cikin dangi, amma sai na yaye wannan Mask (Fuskar) da ka saka a idanun duniya. Mayaudari kawai!" Ta fada cikin Karaji. Wata irin zuciya ce ta kawo masa a daidai wannan lokacin, har yake jin zai iya shaKeta, ya murKusheta koma ya yi mata abin da ya fi haka muni. Amma cikin idanunta kawai ya kalla, ya tabbatar da cewa har cikin ranta a tsorace
take da shi, wannan ya sa ya sake ta. Ya fice daga ofis din, ko sekon daya ba ta Kara ba, ta bi bayansa, ta kuma wuce shi cikin sauri. Www.bankinhausanovels.com.ng 

***********

Kwana ta yi kuka cikin takaicin abinda Zaid zai iya aikatawa. Duk tsawon lokacin nan yaya za ayi ta kasa gano asalinsa? A take ta ji ta tsani kanta. Ta tsani Yaya Zaid, soyayyar da ta dauki shekaru tana yi masa, ta rikide farat daya ta koma muguwar
Kiyayya mai zafi. Kwanaki uku rus! Ta yi ba ta fita ko ina, ko abinci sai dai a haura mata da shi sama,
saboda wani irin zazzabi da ya kai mata damKa.
Yana sane da halin da take ciki na ciwo, kuma ba tantama ya san shi ne sila, amma ya rasa yadda za ayi ya ganta, bare ya gaisheta,

ZAMU TASHI 

kuma ya kula Maami tana hankalce da shi, saboda gudun tuhumarsu yace. "Dazu na haura sama Adiiyya tana bacci, yaya jikin nata dai?"
"Alhamdulillahi da sauKi dai, ka san Ummu da rashin son magani, shi ya sa idan ta yi ciwo take shan dan karen wuya." Wani irin abu ne ya yi masa zafi a ransa, don haka ya ce da Maami, "Ina magungunan nata?" Nan ta miKa masa su, kai tsaye ya wuce falon saman, inda take duKunKune kan kujera, fuskar nan ta yi jazur! Don kuka da take ci, idanun kuwa sun WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG fada sun yi luhuluhu, duk ta bi ta jejjeme. Ya rasa me zai sa har rana mai kamar ta yau ba ta saduda ba, wannan na nufin har yau kuka take yi. Me zai daga mata hankali har haka, bayan ta yi masa nuni da rayuwarsa ce, ba abinda ya dameta da shi? "Adiyya!" A firgice ta dago kai ta dube shi, kau da kai tayi, ta juya masa baya. "Yaya jikin naki?" Taji ya fada da alama ko a zaune yake ko ya durKusa, don ta ji muryarsa daf kusa da kunnenta. "Ki daure ki tashi ki sha magani, kin ga yadda hankalin Maami ya tashi kuwa?" "Za ka iya hadiya, don kai ne mai cuta, ni kam lafiyata Kalau." Ta fada cikin dusasshiyar murya, duk da ba ta da niyyar kula shi. Don Allah ki kwantar da hankalinki, idan don dai kan maganar da na fada miki ranar ne, na fasa, ba abin da zan miki, amma na roKeki ki bar batun can a yadda ki ka same shi."

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Sai a lokacin ta juyo ta Kare masa kallo, hannu ta miKa masa, ya zuba mata maganin da ya Halla a hannunsa, ita kuwa ta hadiya ba tare da ta dubi ruwa ba, duk kuwa yadda taki jinin magani. Ga ruwa ki sha, kar ya yi miki illa. Ba zai yi aiki yadda ya dace ba kuma, idan bai wuce..." "Damuwarka dai magani ne na sha kuma, ba don ka zauna ka cikani da surutu ba,
za ka iya tafiya your secret is safe with me." Ta fada hannunta a nade saman Kirjinta, da ganin idanunta a wahalce take, saboda da Kyar maganar ma ke samu ta fita. "Shi kenan na ji, Allah ya Kara sauKi." Harara ta balla masa, shi kuwa ya fice a falon da gani dai jikinsan ya yi wani iri da irin halin da Adiyyan ta nuna masa.

**********

Koda ta warke ta Ki ta koma wurin aiki, ba yadda Abba bai yi da ita ba, daga baya tace, "Abba ka yi haKuri kawai, ni yanzu aiki ya fita a kaina aure zan yi." Shi kansa Abban ya ji mamaki, don dai iya saninsa, duk ta kori masu zuwa wurinta,tun ba yau ba.
A wannan satin Zaid ya yi Kaura zuwa sabon gidan sa da aka gama gyarawa a (Wuse 2). Kowa ya yi san barka da wannan gidan. Musamman ya taho da su Mama da Anty daga Gombe suka zo suka gani, suka sanya albarka. Ita dai Umm Adiyya kallonsu duka WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG take yi da sun san ko waye dansu, da ba su nuna
masa Kaunar da suke nuna masa ba. Kasancewar gidan a cike yake da jama’ar Gombe, ya sa ta koma falon Kasa ta yi kwanciyarta a falo tana _karanta__littafin (RAYUWAR RAYHAANA) na Sumayya Abdulqadir (Takori), hankalinta ya yi nisa, ba ta ji shigowarsa ba, juyawa kawai ta yi,
ta ga mutum a zaune kan kujera ya daura kafa daya kan daya hannunsa kuwa ya miKe daya a bayan kujerar da yake zaune. Kamshin turaren (Boss Orange) ne yake fita a jikinsa, kayan jikin sa kuwa suit ne ya cire vest din da tie din ya yi saura shirt din, ciki da wandon suit din. Kallon ta yake yi kamar an aiko shi. Ko kuwa ta ce kamar wani maye, don ba ta ga dalili ba. Da ta gaji ne, ta miKe da shirin barin falon. "Adiyya, zo nan." Juyowa ta yi tana fuskantarsa, ba tare da ta zauna ba, duk da kuwa ta san ba abin da ya tsana irin mutum ya tsaya masa a kai. Har zai yi mata fada kan hakan, amma ya tare kansa tun wuri, cikin yatsina fuska, ajiyar zuciya ya yi ko zai huce kadan. Uhmm... Ina so ne na fada miki na samu Baffa Abdu na fada masu cewa KE NA KE
SO da aure, so za su iya kiranki su miki magana, ina fada miki ne, saboda ki san abin da za ki fada, idan suka dago miki zancen.” Kallon sa take yi yana magana tamkar mai hirar yanayi (Weather). Ba magana mai girma da muhimmanci irin aure ba.
Sannan ita ta auri Zaid? Ina! Ya yi kadan kuwa, sai dai a da, amma yanzu da ta yi wayo, idanunta suka bude, ta fi Karfin ta aure shi. Ka ce masu yau kan su watse, su Gaura auren Karshen So kenan."
Bai taba tsammanin abin da za ta fada ba kenan, don haka ya san duk wata dabarar da zai kama ta kubce masa. Aurenta kawai shi ne mafita, saboda komin son kanta ba yadda za ayi ta budi baki ta tona sirrinsa, idan har yana matsayin mijinta a yadda
ya san Adiyya da zurfin ciki, domin kuwa girmansa zai fadi a idanun iyayensa, tamkar yadda ya fadi a idanun Adiiyya, muddin ta budii baki ta yi magana. Abu kamar wasa sai murna ake ta yi wai Zaid ya ce Umm Adiyya yake so da aure, zance ya karade dangi kaf! Musamman wa da Kanin, amma duk da haka Baffa Abdu ya kira Umm Adiyya don aji me za ta ce? Ita kam ko a kwalar rigarta, su Zaid din da Yaya Nazeef da Yaya SaadiK duk suna falon, har Abbanta.
Da farko shiru ta yi, saboda yadda ta ga wurin a cike, don haka ta ce da Baffanta, "Baffa Abdu, ni nafi son mu yi magana mu biyu." Wani Kara tukun ‘ya'yan hanjin Zaid suka fitar cikin gigita, me yarinyar nan take shirin yi? Me za ta fada wanda ba za ta fada a gaban kowa ba? Amma idan ta
kuskura ta furta wani abu da hannayensa zai shaKeta. A take ya shiga share gumi. Jin hakan ya sa Baffa Abdu ya yi murmushi ya ce, "Yawwa ‘yata wadannan sun sa miki idanu ko? Fito abinki mu je." Nan ko suka isa zuwa Karamin falo inda Abba ya same su, don tuni ya sha jinin jikinsa. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Ta san dai Zaid dansa ne, amma yadda ta san yunwan cikinta, haka za ta bada shaida. Baffa Abdu ba zai taba yarda da abinda dansa ya zo da shi ba, don haka ko ba ta fada masa dalili ba, za ta fadi abin dake cikin ranta. Ku yi haKuri Baffa Abdu, ba raini ba ko wani abu, amma gaskiyar magana, ni ba zan iya auren Yaya Zaid ba!" Kafin ta gama rufe baki. Abba ya kwadeta da mari, "Ahaff, yaya haka kuma Zubairu?
Ka tsaya ka saurare ta mana, zaka dau wani mataki cikin gaggawa haka?"
Hankalinsa ya mayar kan Umm Adiyya, "Ummu, daina kuka haka, dubeni ki fada min, idan har ba ki son Zaid, ba mai sa ki dole." Ya kaikaici inda Abban yake zaune.
Shiru ta yi tana inda-inda, domin ba za ta taba yiwa iyayenta Karya ba, haka nan ba zata bari zuciyarta ta rinjayi tunaninta ba. Don haka ta ce, "Ina sonsa..." Wasa ta shiga yi da Kasan mayafinta, kafin ta samu Karfin gwiwar Karasawa "...Amma ba da aure ba." Abba ya gyara zama a kujera, sannan ya dubeta, wani iri kafin ya ce, "Yaya, ka ji shirmen banza, wace irin magana ce kuma wannan? Hala wani abu ki ka fara sha? Bokon ne ya hau kanki, ki ke irin wannan zancen?" Don Allah ka Kyaleta ko kuma ka fita, idan mun gama magana ka dawo, amma ka
bar tarar numfashinta." Ya fad, sannan ya cigaba. "Hala dai dan naka bai nemi yardarta bane ko?"
A hankali ta gyada masa kai, murmushi ya yi ya ce, "Je ki abinki ki rabu da shi, ni ma ba zan ba shi aurenki ba, sai ya san yadda ake bi da 'ya mace cikin lallami da kuma iya sanin menene shi kansa auren. Idan kuwa bai koya da wuri ba, sai na zage na zaba miki wanda zai kula min da ke kin ji ko? Daina kuka kije ki ci-gaba da sha'aninki." WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Wani irin dadi ne ya mamaye mata zuciya. Ikon Allah wasu al'amura sai
(AL'AMARIN ZUCCI  idan banda haka, sati guda da ya wuce idan za ace mata iyayensu suna maganar aurenta da Yaya Zaid, sai ta zuba ruwa a Kasa ta sha, don murna. Amma yau ga shi da kanta ta juyar da zancen aurensa a iska. Tana shirin miKewa, ta ji Abba ya ce, "Kuma koma wane dalili ya sa ki ka daina
zuwa wurin aiki, ina so ki ajiye shi a gefe, ki koma wurin aikinki, tunda Zaid bai kai mutum ba da ya isa ki aure shi, na ba ki nan da sati biyu ki fiddo da wanda ke ki ke ganin ya kai ya zama mijinki. Banda shirme, abin da ya yi Zaid dai, shi ya yi ki, kuma
zan yi wa Zaid auren gata na ban mamaki. Wai wani ba ta sonshi da aure, Mtsww!" Tana jin Baffa Abdu ya sa baki, "Kai kuma me ya sa ka faye son Kananan magana kamar mace, ka rabu da zancen nan a nan, koda wasa kuma ban yarda wani ya sake dago mata maganar ba, har sai idan ta gama shawara." Wucewa ta yi abin ta, ba wani shawarar da za ta yanke haka kawai. Wucesu ta yi a babban falo tana goge fuskarta, ganin haka jikinsu duka ya yi sanyi, duk da dai hirar su suke yi, amma idanun Zaid na Kanta har ta haura sama. Wani abu ya ji ya kulle cikin WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG maKoshinsa, duk yadda aka yi, ba a Kare ta dadi ba.
Don haka yana shirye da ya ji me ta yi, shin ta fada masu komai ne, ko kuwa sa ta za ayi dole ta amince da maganar aurensa da ita?

********

BABI NA TARA

Bayan kwana biyu da watsewar jama'ar Gombe. Duniya ta gama yiwa Umm Adiyya zafi, domin kuwa har gwamma zafin da Abba ya dauka akan yadda Maami ta dau zafi, ita da jin magana har ta gama tsara biki a ranta, sai kawai Abba yake ce mata
Umm A. Ta Ki yarda da maganar. Baffa Abdu kuwa ya ce an bar maganar."Yo har ke kin isa ki ce kin Ki Zaid, ai ke ma kin san Zaid ya fi ki nesa ba kusa ba,
idan a kyau ne, ko dukiya duka, ba daga nan ba, mata kuwa har sai ya ture, sai dai ki tabbata ba aure, amma a dakin nan, a gidan nan, ki na zaune zan aurawa Zaid mata ta kece raini."Maami don Allah ku daina min fada, ni fa ban ce na fi Karfin sa ba, kuma ke da kanki ki ka ce ba za ku min auren dole ba. Shi ya sa na fadi ra'ayina, amma da nasan fadin ra'ayina zai bata maku rai haka, da ban soma ba, ku yo masa aurensa, ni ban hana ku ba. Amma ni kam ba zan aure shiba." Maami kam habarta ta riKe kawai cikin tsantsar mamaki, "To Allah ya ba ki sa’a." WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Da dare ma sai ga wayar Adda Asma’, "Umm A. Wani irin labari na ke ji haka? Meya faru na ji Maami sai fada take yi, wai ga ki, kin girma wuyanki ya yi kauri ba su isa su saki ba, bare su hanaki, kin ce Yaya Zaid ba ajin aurenki bane, kin kalli idon Baffa Abdu, kin ce ba ki son dansa." "Haka aka yi Adda Asma’, ni na ce ba zan auri Zaid ba." "Lafiyarki kuwa?" "Me ki ka gani?”
Daga inda take ta zaro idanu tamkar Umm Adiyya na kallonta, "Sunansa ki ka kira kai tsaye, ba ko Yaya?"
"To sai aka ce ya zama wajibi na ce mar Yaya? Haka na ga daman kiransa kuma hakan zan kira shi, auren kuma ba na yi, sun ce za su yi masa auren gata, idan sunga dama ma su haifa masa matar, amma ni kam
ba naso, a kai kasuwa." Asma’ karan kanta ta rasa bakin magana, wato dama duk shiru-shirun Umm Adiyya jira take yi kan bakin ya bude, domin ba za ta taba yarda ba, idan aka ce mata Ummu A. Ce ke bayanin da take yi yanzu.
"Don Allah ki fada min, me ke faruwa ne Ummu A? Iya sanina ba mai yiwa Yaya Zaid Kaunar da ki ke masa, me ya faru da har za ace miki ana nemar masa aurenki kiqi amincewa a gaban mahainfanmu?"
Wasu hawaye masu zafi ta hadiya, sannan ta ce, "Ba komai. Adda Asma’ kawai ki dauka babu shi a cikin Kaddarata ne, shi ya sa duk abin da suke faruwa suka faru." Ni kam ki na tsoratani, ki taimaka ki fada min komai.” Kuka ne ya ci Karfinta da ta tuna abin da ya faru, ba shiri ta kashe wayar, ta lullube kanta cikin mayafi, taci kuka iya isarta. Ba a je ko ina ba, kanta ya hau ciwo. Amma saboda irin yadda kowa yake shasshare ta a gidan, ta ji ta gwammaci fita da
ta zauna. Don haka ta tattara duk wata damuwa ta ajiye a gefe. Kasuwar yanar gizo ta bazama da WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG kudaden cikin akawun dinta, don tun da aka fara biyanta albashi, bata taba kashe Kwandala ba, ga wanda Abba ya kan ba ta na kashewa, kayan fita aiki
ta yi order daga kamfanin Shukr. Domin idan tana so ta cire abin da ya shude daga rayuwarta, ya zamo dole ta canza komai na rayuwarta, daga yanayin shigarta zuwa yanayin mu'amalarta da mutane.
Da koma menene. Ranar Litinin da ta koma aiki, hatta Mai-gadi sai da ya sake mata kallo, a karo na
biyu, domin kullum idan ta zo shigewa kanta a Kasa za ta wuce, tana kokuwa da jakar (Lapton) cinta, wanda ya yi rabin tsawonta, da shi da igiyarsa.
Amma yau ga ta idanunta babu tabarau, ta sha (Maxi skirt) dinta da rigar Tunic da ya shiga da shi da kuma matsakaicin hijabi mahadin kayan, ba inda ka ke gani a jikinta face fuskarta da tafukan hannayenta,
sannan kayan sun mata das! Ba su rinjayeta ba.
Ta yi fes! Cikin shigar mutumci. Jakarta ta komfutar ma ta dauko marar nauyi (Fibre) ta ajiye babbar. Kai tsaye ta gaishe da mutanen da suke babban falon, sannan ta wuce ofishinsu, dukkansu idanu suka zuba mata. Dubansu ta yi ta ce "Lafiya?" Hasan ya ce, "Hajiya, yau dai wani abin ya faru ne hala?" Me ku ka gani?" Ayo ya ce, "Yau kin wuce ba ki goge hannun Kofa ba da Dettol."
Murmushi ta yi ta ce, "Wasu lokutan ya kamata mu rinKa morar Kananan abubuwa a rayuwa, saboda haka wataran muna buKatar germs din rayuwarmu su koya mana darasi." Yau kuma adon magana ake jin yi ne?" Ayo ya fada cikin turanci. Nan dai aka gaisa, yadda ta ji suna ta tambayarta jiki ne, ya ba ta tabbacin Karyar da Ogan nasu ya masu kenan, koda yake ba ta sha mamaki ba, tunda ya yi kos a wannan fagen. Hankali kwance ta rungumi aikinta gadangadan! Sai dai duk inda ta san za su hadu da shi, ba ta bari haduwar ta yi tsawo, ko kuwa ya zama su biyu ne, duk kiyayewa


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "UMM ADIYYAH CHAPTER 10 BY AZIZA IDRIS GOMBE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...