SAIKA AURENI DOLE COMPLETE BY AISHA A BAGUDO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SAIKA AURENI DOLE COMPLETE  BY AISHA A BAGUDO

SAIKA AURENI DOLE COMPLETE BY AISHA A BAGUDO

- - Post a Comment

SAIKA AURENI DOLE COMPLETE  BY AISHA A BAGUDO


              Www.bankinhausanovels.com.ng 


A babban birnin Barcelona dake kasar Spain me dauke da yawan tarin jama'a tare da wayan tarihi ,a can kasar yake zaune.

 alhaji Adam  cikakken bahaushe ne Dan Boko ne, km tsohon ambassador Nigeria .

a can kasar Spain  yana da mata daya tal tmkr rai hjy baraka tare da ya'ya guda biyu abdulkabir da hauwa'u wace ake kira da ( iman) kasancewar Sunan mahaifiyar alhj Adam gareta. 


Iman itace kebin abdulkabir  byn shekaru masu yawa da hjy baraka da alhj Adam suka dauka byn haihuwar abdulkabir sannan suka sake samun haihuwarta.

 " tun byn sanda aka sauke alhj Adam daga kan mukaminsa na ambassador .

sai jami'ar dake kasar Barcelona ta dauke shi amatsayin babban lectura .

sbd kwarewarsa sosai ata fanin rayuwar yau data kullun .

mutun ne shi me tsananin son hutawa da jin dadin arayuwarshi. kwata kwata baya son damuwa da takura, sannan yakasance mutun Mara son hayaniya da rashin son mgn .

 a duk sanda zaga ganshi cikin nazari lamura yau da kullun yake akan aikinsa ko karanta magazine, yana koyar da darasin English language ne a jami'ar Spain . Lokacin da jami'ar Spain ta daukeshi aiki bai haifi daya daga cikin ya'yansa ba kasancewar bai samu haihuwa da wuri ba .

acan kasar ta Spain ya haifi AK da iman. 


Burinsa arayuwa bai wuce 'dan'sa tilo daya daya mallaka abdulkabir ya samu nagartaccen ilimi ME zurfi ba.

 hkn yasa ya samar masa admission anan cikin makarantar dayake koyarwa, domin ya dinga kula da movement dinsa da duk wani motsinsa . sbd yana mugu mugun son  abdulkabir kmr ranshi km yana son yakasance yagajeshi takowani Fanni .

koma ya zartashi akomai  na rayuwar duniya. 

Sai dai kashi hakan bai samu ba domin kuwa abdulkabir (AK) ma'abocin holewa da emmata turawa ne.

 mafiya tarin lokuta yana tare da matan turawa domin jin dadin rayuwarsa.

 sai dai duk da wannan tarin iskancin nashi hkn bai hanashi meida hankali akan karatunsa na yau da kullun ba .

gashi da tsananin tarin  ilimi maramisaltuwa. karatu ko ba'abiya masa ba, da zarar yakaranta litafin shikennan ya dauke tare da gamsuwa .

 km ko sau daya malami yabiya masa darasi ya dauka Kennan acikin brain dinsa baya bukatar kari bayani ,sbd Allah yabashi wankakkiyar kwalkwaluwa me saurin daukar kowani irin abu. Ganin hk yasa alhj adam bai takura masa ba .

domin daman shi dai burinsa bai wuce Dan nasa yasamu wadataccen ilimi me zurfi ta kowani bangare ba km yana kan samu . mgnr holewa km daman yasan ba'a raba baturen mutun daita.

 aganinsa tunda suna cikinsu Sun rigada 'sun zama daya.

 shiyasa ya kyaleshi sai dai wani lokacin ya kan zaunar dashi yayi masa fada sosai. 

sai km ta bangaren iman wacce take ss 1 alokacin alhj Adam bai yardar mata saka kananun kaya    English wears ba kmr yadda matan can ke Yi ,sai dai  tasaka na gida nigeria irinsu atamfa da shadda wanda ake dinko mata daga kasar Nigeria. 

gashi ita km Allah yayita da mugu mugun son kananun kaya .

Iman ta kasance tana son wannan shigar ta English  wears ,

musamman idan suka matseta ajiki Amman 

dole tasa duk lokacin data saka kayan  sai  ta suturta jikinta da afterdress a saman kayan .

sbd gudun bacin ran mahaifinta. 

hkn ke saka dakayi mata kallo daya acikin shigarta zaka dauka ko ta fito daga cikin jinsin larabawa  ne. kasancewarta farace  Sol gwanin sha'awa tmkr uwarta . 


Duk da zaman alhj Adam akasar Turai hkn bai hanashi sada zumunci da yan'uwansa ba domin Duk karshen shekarar duniya agida Lagos yake yinta tare da iyalinsa hjy baraka da danta abdulkabir Da matashiyar diyarsu alokacin  iman Kennan . 


Cikin haka alhj Adam yayi retire, ya ajiye akinsa dayake matsannancin kauna arayuwa ,adadai wannan lokacin ne shima  A K wato abdulkabir ya kammala da karatunsa na digirinsa na farko akan tattalin arziki kasa .. 

Yayinda itama iman ta kammala da Karatunta na gaba da primary school  .Kmr kowace shekara da suka saba zuwa Nigeria hkn ce wannan Karon takasance garesu. 

yanzu ma sauran kwanaki uku kacal su iso kasar iyayensu ta gado kwata kwata batare da komawa kasar ba.

 sai dai bisa wani dalili na daban .

hkn yasa abdulkabir tsaiguntawa manya abokanshi da km yan'uwa da suke Lagos cewar Suna nan zuwa .itama hjy baraka wace suke kira da ammi ta sanarwa ma'aikatan gidansu dawowarsu domin gyara gidan duk ba gidan suke sauka ba inda Sun sauka akasar . 


Kai tsaye kmr yadda yaba gidan yar'uwarsa alhj Adam ya sauka unguwar morocas dake karamar hukumar agege ,Duk yana da katanfarin gidansa dake gra ikeja Amman sbd shi din ME tsananin son zumuncine yasa yake sauka acikin daya daga cikin bangarorin gidanta. 


aiko ana bude get din  gidan ,ahlin gidan suka nufo motar dasu  AK suke ciki gabayansu sai murna ganin juna suke Amman ita zeey sam bata tare dasu domin tuni hankalinta ya karkata ga gogan nata AK dake kokarin fitowa daga gaban mota. 

take ma'aikatan gidan suka fara kwaso kayayyakinsu suna shiga dasu cikin gidan .

AK ya dubi zeey yana bata rai yace wai ke wannan wani irin kallon ne hk? Sai wani cika kike kina batsewa. 

Zeey tayi fari da idanunta tare da yin murmushi me tattare da tsantsar farincikin ganinsa.

 kana tace kallon farinciki da dawowarka nike gabadaya kasar nan batare da sake komawa koina ba.

Sannan abinda kake ci shi nike ci shiyasa kaga nike cika nike batsewa  .

Ak yayi murmushi iya gefen baki yana cizon lip's dinsa na Kasa.

 Hum yaja numfashi da ajiyar zuciya  at the same time  yace Allah na tuba ai abinda nike ci har ki mutu wani ko ganinsa bazakiyi ba yarinya ballantana har kici. 

    zeey tarausayar da idanunta tace sarkin cika baki kawai .kana nan yadda nasanka baka canza ba. 

AK ba dai kuri ba .

yanzu dai muje kashiga ciki ka samu ka  kaci abinci ka huta. 

sannan saika bani labarin turawan yammatanka wayanda kuke soyewa dasu. 

, take AK ya hade rai tmkr bashine yake mgn da murmushi ba yanzu yashiga jifanta da wani irin kallo wanda shi kadai yabarwa kanshi sani,ma'anarsa  sannan km yasan abinda kallon nan nasa yake nufi. 


Abdulkabir matukar Hadadden gaye NE me jini ajika daka ganshi dole ya birgeka sannan yana da matukar daukar hankali ..

domin ko ba komai da akwai tsantsar wayewa atattare dashi .

dogo ne sosai me dagon fuska da hanci kmr Biro chocolate colour me matsakancin jiki wanda hakan yasanya tswon nashi yayi masa das ajikinsa . 

kallo daya zaka masa kasan yagama hadewa ta koina wannan dalilin ne yasa dayawa yammata suke matowa akan sonsa.

 AK Allah ya hada jininsa Dana zeey sosai fiyye da tunanin me karatu wanda har mutane gidan suke tunanin ko akwai wani Abu ne atsakaninsu .yayinda cikin su babu wanda ya taba kuskuren furtawa dan'uwansa wata kalma wacce ta danganci so.... Zeey ma ba Fari bace sai dai kalar fatar coffee colour gareta sai dai itama babu laifi Allah yayi mata diri me kyau daidai jikinta. 

Kanwar mahaifin AK ce mahaifiyarta sai dai tun suna kanana mahaifinsu ya rigamu gidan gsky .

hkn Yasa kulawarsu take karkashin dady km shiyasa Duk sanda alhj Adam yazo kasar yake sauka gidanta tare da iyalinsa. 


Musty Malik akil duk abokan juna ne da AK kowace shekara tare suke kasancewa domin shagulgulan hutun karshen shekara, musty dan abokin dad din AK ne su km suna zauna ne agarin Abuja. sai dai asalinsu mutane wasagu ne dake jahar kebbi dake karamar humumar zuru.


 Akil da Malik makotan AK ne dasuke zaune gra AK yayi waya dasu a inda musty yake sanarwa AK yazo masu da manyan kudi wanda zasu fancama. 

 Kwanansu biyu suka tarkata suka koma gidansu na gra har zeey wanda yasha gyara daga ma'aikatan gidan ta koina ka kalli gidan kasan ya tsaru iya tsaruwa.


 tafakeken gida ne wanda yake dauke da different part guda shida ga Duk mazauna gidan , Part din me gidan zaka soma gani daga hannu dama idan kashigo gida sai dai shima zagaye yake da sauran part din domin daga part dinsa zaka iya shiga kowane part. 

sai part din ukku dake jere da juna na ammi da iman sai na masu aikinta sai part din AK dake ta baya wanda yake da hanya ME bullewa waje kai tsaye, sai part din masu  gadi gidan .


gidan zagaye yake da manyan bishiyoyi can gefe guda km gurin part din AK tafkaken swimming pool ne wanda dominsa alhj Adam yayi kasancewar yaronsa me matukar son swimming ne. 


A wannan dawowar da sukayi ,ya saka dayawa daga cikin yan'uwa  murna .

yayinda gidansu dake gra ya cika makil da dangi da abokan arziki yan sannu da zuwa. 

Ta kowani Fanni murna ake da dawowarsu abinci da abin sha gasu nan birjik baa mgn daga yan'uwa da abokan arxiki alhj Adam yana zaune babban falonsa shida wani causing dinsa   suna tsutaunawa akan lamuran yau da kullun inda yake tmbyrs game da yanayin AK din .

dady ya numafasa kana ya sauke naunauyen ajiyar zuciya yace to alhamdullahi zamu ce yanzu domin komai yana tafiya normal babu wata damuwa. 

OK ga wannan sakon tsawon wata shida Kennan dana amsoshi daga wani kauyen yarbawa ance zai Yi maganin matsalar idan Allah yaso ya yarda.

 alhj garba yakarasa mgnrsa yana kokarin mika masa bakar laidar dake cikin aljihunsa .

dady yasa hannu ya karba yana masa godiya. 

haba haba godiya atsakaninmu km nima fa abdulkabir dana ne halak malak ko babu kai aduniya ni me tsayawa ne tsayin daka akan lamuransa. 

sukayi murmushi tare. dady nacewa ai Godiya dole ce kayiwa wanda ya kyautata maka .

nan dai suka bar zance AK suka sake shiga wata hirar duniya sai gurin la'asar suka rabu da juna har bakin get dady ya rakashi kana ya dawo.  shigewarsa dakisa  kasancewar baya son hayaniya. Gashi km hayaniya ta cike gidan. Tun biyar abokan AK musty da akil da malik suka gama shirinsu na xuwa sheka ayarsu .

AK kawai suke jira a fasa Dare .

shima AK nagama shirinsa ya samesu, tuni suka  bazama cikin gari yawo zuwa Club cikin BMW din AK ..

gurin buduwar akil aka soma zuwa domin shine zaunane gari .suka dauketa zuwa club .

tunda suka shiga cikin club din AK ya nemi akil yarasa Shida  yarinyarsa sai gurin awa uku ta wuce sai gasu sun jero da alamun MA har wanka suka yo.

 AK yayi murmushi yana girgiza yana dubansu sannan yace Amman fa mutumina kana hutawa agurin yarinyar nan.

 ina son dealing da mayan baby's wannan ko aina tayi ,akil ya dube AK sosai yace ko kaima zaka shiga daga ciki ne? AK yayi saurin girgiza kai har yana kwarewa da ruwan wing din da tsiyaye cikin glas cup yana sha. 

OK to kabari asamo maka daidai kai wacce tafita zata baka kulawa sannan zata gamsar dakai sosai .

dan har kuka sai ta saka ka .

yakarasa mgnr yana kwashewa da wata uwar dariya .

uhmmmmm AK yaja numfashi yana daga masa hannu banda muguwar fahimata akil ni duk iskancina da harakata da mata.

 bana yarda na taka budurwa nidai just romancing kawai ya isheni.

 Malik yace AI idan dai ana yin romancing kadai yaisa, sukayi dry gabadayansu daga nan sukayi wani hadadden hotel  .

inda suka dinga cin karo da manya karuwai  different types cikin shiga ta fitsara .

Suna kawowa AK hari,, yana sharesu.

 Daga can nesa AK ya hango wasu empty sit yaje ya zauna tare dayin balance da kafafunsa yana duban yadda matan kasarsa suma suke da wayewa .

DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "SAIKA AURENI DOLE COMPLETE BY AISHA A BAGUDO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...