RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Tabbas na amince AKWAI LOKACI, da komai zai zama labari. Mu dai ci gaba da bin ‘yar mutan Borno na tabbata za ta ci gaba da hada mana zumunci mai Karfi ta yadda mutanen duniya za su yi koyi da mu, wajen hada kai da tallafawa dukkan macen da take da buKatar taimako. Zumuncin mu ya fita daban ba irin nasu bane. Nasreen ki gaya mana damuwarki ko muna da shawarwari, idan kuma abin ya fi Karfin mu sai mu dangana da uwar dakin mu Fatima Dan Borno.”
Gabadaya suka yi na’am da zancen. Muslima ta ce, “Ni ma nasha wahala, har dan fashi na aura. Allah ya saka wa Mahbub da alkhairi ya Kara masa kwarjini a idon duniya. Idan kana yin abu baka tuna MAFARIN LAMARIN, dole abin zai kwabe maka, da muka dogara ga Allah ba ga shi yanzu ya zama labari

ZAMU TASHI 

ba? Mata suna kuka da halin maza amma mu mun fita daban. Mazajen mu sun kasance ‘yan Aljannah masu koyi da fadin Allah da Manzonsa.”
Nasreen ta dago, tana jin damuwa tunda bata iya kallon su, ta ce, “Ina jin damuwa dukka jaruman ‘yar mutan Borno suna iya ji suna iya ganin junan su, amma ni akwai sabanin hakan a tare da ni. Ko da yake na yarda na amince ni
RUBUTACCIYA ce, in ji Abbana da Deedina, haka ma dan uwana Naufal yana yawan gaya ° min hakan. Ku yi min hakuri idan na sami lafiyar idanu yadda zan ganku sosai, sai mu ~

tattauna.”Www.bankinhausanovels.com.ng 
Gabadaya sun yi na’am da _wannan maganar. A ranar a gidan Sultan suka kwana su dukka, washegari abin burgewa, dukkan su suka shiga kitchen kowacce tana baje basirarta wurin girka abinda ta fi Kwarewa. Cikin KanKanin lokaci gidan ya cika da Kamshi. Jidda tana hada lafiyayyan zobonta suka ji muryar Zakiyya a bayan su, “Sannunku da aiki, naso in fito in tayaku wani abun, sai dai ina wurin mijina ina bashi tasa kulawan.”
Jidda ta fara dagowa kasancewar har yanzu ba wai ta daina halin nata gaba daya bane ta ce, “Oh wai a hakanne kike kula da miji? Dube ki fa, ko wanka baki yi ba. Matsalata da wasu matan kenan, sun Kware wajen biyayya akan shimfida, amma sun kasa gane me miji ke so. Ni ki je ki tambayi wacece ni, idan Kazanta kike takama da ita Jidda ta take ki, amma da na fahimci babu amfaninsa ai na watsar. Ko da yake ni girman Kauye ce ba girman mutanen Kaduna ba.”
Mamaki yasa Zakiyya zuba mata idanu, domin dai bata taba ganinta ba, za ta yi mamakin dalilin da zai sa ta dinga danKara mata magana. Kai tsaye zuciyarta ta gaya mata Nasreen ce ta gaya masu komai. Yumnah ta dago tana murmushi, ta so a ce Six lover’s suna kusa da tuni ta yi masu yaren da su kadai suke fahimta, kuma za ta samu amsar da take da buKata. Duk da hakan sai da ta furta. “Oh su Www.bankinhausanovels.com.ng Roro ba a iya samun wuri ba, sai a buge da watsa na doki a tsakiyar ka?” Gaba daya sun fahimce ta, tana nufin Attachment din da ke kanta. Musulima ta yi saurin karbe zancen, “Akwai abin tausayi, musamman yadda Uwale ke manna kashin kaza mai kwanci a dai-dai Kasan na shanu.” Sun fahimceta, kashin kaza mai kwanci wari ne da shi, tana nufin Kasan mamanta ba a wanke wa, musamman yadda suka zube kamar wacce ta shayar, ta tabbata akwai wari a ciki, Dukkansu suka yi murmushi. Za su ci gaba da magana, Nasreen ta shigo tana cewa, “Don Allah duk wacce ta gama ta zuba min, Dee yana ta tambayar ba a gama bane? Nima kuma ina da buKata.”
Zakiyya ta shaKo wuyan rigarta, tana huci, “Ke kika gaya wa ‘yan gidan nan sirrin cikin gidan nan ko? Yau sai na kakkarya ki idan ya so daga can sai a duba lafiyar Kafar.”
Jidda ta juyo a fusace tana dauraye  hannunta, Yumnah ta riqe rigarta. Hakan yasa ta! waiwayo tana duban Yumnah. Dole ta sakar mata hannu.
Tasleem da sauran gaba daya suka isa har gabanta suna dubanta. “Idan kika taba ta, babu shakka sai naki Kafafun sun karye.”
Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Sakar min kwalar riga, bansan me yasa idan baki yi haushi ba, bakya jin dadi. Na fada maki Zakiyya ke karya ce, wacce kullum take haushi a titi ana
korarta da dutse. Kin Kware a dambe da wulakanta dan adam, kin ce miji na bar maki abinki, shi ne yanzu duk bai yi maki ba sai kin tozartani a gaban jama’a? Kin ji kunya Wallahi, kin yi girman banza! Kina nan kina dariya duniya tana can tana zaginki. Yabawar duniya tana taimakawa har zuwa makwancinki. Kin fitar da halinki kin jawowa kanki. Duk yadda miji ke sonki idan kin kasance daga fitinannu kin zama koma baya a wurinsa, wannan ba sai na gaya maki ba, nasan kin san hakan.”
Sau tari idan Zakiyya tana rigima da Nasreen, kaifin kalamanta kawai take tsoro, domin duk ranar da ta gaya mata magana kwana take babu barci. Jidda ta samu ta Karaso ta fizgo Zakiyya daga irin riKon da ta yi wa Nasreen ta waska mata mari mai tsananin zafi. Ta hankada ta baya. “Ki je ki gayawa duk wanda ya daure maki gindi ni Jidda Junaid na mareki.”
Zakiyya ta fita da ihu tana fadin ankasheta. Su kuma suka ci gaba da aikin su. Kowa zuciyarsa babu dadi. Ita kuwa Zakiyya kai tsaye falon ta shiga ta sami Sultan da su. Al-ameen
suna tattaunawa. Zakiyya ta shigo tana kuka ta zayyana masa komai.
Sultan bai ji dadi ba, amma saboda kawaici ya ce, “Ke kika jawo. Kuma babu yadda za ayi Jidda ta mareki haka kawai dole da abinda kika yi
Al-ameen da ransa ya yi matuKar baci ya dubi Zakiyya, “Kiyi hakuri Zakiyya zan dauki mataki akanta.”Www.bankinhausanovels.com.ng 
Zakiyya ta juya tana kuka, Al-ameen ya mike yana huci. Sultan yace’menene haka? Don Allah zauna kada ka bata mata rai, ta ce ta fasa raka mu. Ka san dai halin Jidda.”
Al-ameen ya koma ya zauna bai ce komai ba. Suna nan har su Jidda suka fito da abincin da ( suka girka suna shirya falon. Jidda da kanta ta ~ kaiwa Umma komai sai albarka take sa masu. Tana shigo wa, Zakiyya ta leKo tana son ganin irin hukuncin da zai yanke a kan Jidda. Za ta fice yasa hannu ya fizgota ta fada jikinsa, ta zaro idanu sosai, “Me na yi maka don Allah?”
Ta fada tana me zura idanunta a cikin nasa, sai da ta tabbatar da ta ci nasara sannan ta zame kanta tana dubansa. Da Kyar ya ce, “Wai me Zakiyya ta yi maki kika mare ta? Ba ki jin magana ko?”
Kanta ta dora a kafadarsa tana magana cikin natsuwa. “Ba haka bane shigowa ta yi na ganta duk datti, sai na gaya mata idan Kazanta ce bata kaini ba, nayi mata maganganu, shi ne da shigowar Nasreen ta shake ta, wai sai ta yi mata dukan da idan muka fita waje sai dai ayi aiki biyu. Ni kuma da naga taki sakinta na dora mata tafi.” Ta Karasa maganar da dago kanta ta dan shafi fuskarsa ta ce, “Ka ji abinda ya faru.”
Dukka dakin suka yi ajiyar zuciya. Sultan kuwa jikinsa ne ya yi sanyi ya ce, “Matar da ke dauke da juna biyu menene nata na cewa za ta yi dambe?”
Yumnah ta juyo tana dubansa, “Waye ke da cikin? Ba dai Zakiyya ba?”
Ya gyada kai yana dubanta, “Zakiyya dai.” Ba ta sake magana ba, suka shirya masu komai._—_Jirgin yamma za su bi don. haka kowa ya gama shiryawa, sai a lokacin idanun Nasreen ya fara kawo Kwalla. Naufal ya Karaso kusa da ita yana magana Kasa-Kasa, “Nasreen kada kiyi kuka idanunki za ki taimakawa.”Www.bankinhausanovels.com.ng 
Ta gyada kanta. Motocin masu dauke da sunan dukkan littafan da suka fito a ciki, sune a jere a hanya za su nufi Airport. Da Kyar Umma ta yi masu addu’a ita kuwa Zakiyya dakinta ta shige abinta. Hafsat ce ma ta raka su har wurin mota. Haka su Al-ameen suka wuce da Sultan wanda bai gayawa kowa zai yi rakiya zuwa Lagos ba. Da isowarsu ke da wuya suka nufi masauki domin sai gobe za su wuce London din. Nasreen bata shiga huldan Sultan ba, sai ma ware kanta da ta yi ita da Naufal ta bar Jidda da ke maKale da mijinta. Sultan ya fahimci akwai + wani abu a zuciyar Nasreen tunda ya ga tana gudunsa.
Gajiya ya yi ya Karaso wurin su hannunsa rike da power Horse da shansa ya zame masa jiki. “Hutawa kuke yi, kuka ware Dee dinku?”
Nasreen ta dan yi yaKe, Naufal ya dube shi yana dariya, “Dee mun barka ne kaima ka huta.” Idanun Sultan suna manne akan Nasreen. Dubanta ya sake yi ya ce. “Nasreen babu abinda ke damun ki?”
Bata yi magana ba, sai daga kanta da ta yi. A tsakiyar su ya zauna suna dan taba hira da Naufal. Kiran Abba ya shigo wayarsa ya dauka
yana fadin gata Abba. Ya sawa Nasreen wayar a kunne.
Tana dauka ta gaida Abba cikin natsuwa. Abba ya ce, “‘Nasreen na sanki da Addu’a ki sake dagewa, mu ma nan muna nan muna yi insha Allahu za ayi aikin cikin nasara. Allah ya kaiku lafiya.” Muryarta tana rawa hawaye suna zuba take godiya. Sultan ya karbi wayar ya fice yana magana. Naufal ya dubi Nasreen cikin takaici ya ce, “Na ga Deedinmu yana maki magana kina sharewa ne? Me yake damunki?”Www.bankinhausanovels.com.ng 
Nasreen ta ce, “Naufal ina ta son insami dama in gaya maka. Dee yana KarKashin ikon Zakiyya ne a yanzu, ba ya kula ni baya zuwa in da nake. Umma ta yi min, Zakiyya ta yi min, shima kuma baya tausayina., Ka fada min me zan yi? Na gaji da wannan abin.” Naufal ya dube ta ya ce, ““Haba Nasreen, ke da ya kamata kiyi masa addu’a? Ki daina fushin nan tunda tafiya za ki yi mai nisa, ko me Deedi zai yi ya fi Karfin wulakanci daga garemu, mu zama masu tuna alkhairi ba sharri ba. Ki dauka ya isa ya aikata komai na cin mutunci akanki, ba tare da kin ji kin gundura ba. Idan yana ganinki a
cikin damuwa shi ma zai damu, don dai baki gani ne da kin ga yadda yanzu fuskarsa ta sauya a lokacin da yake kallonki.”
Bata ce komai ba, ta yi shiru kamar marainiya. Zuwa can suka je suka ci abinci kowa ya gabatar da Sallah, sannan suka yanke shawarar zuwa wani park mai kyau domin baiwa idanunsu abinci.
Al-ameen yana kula da yanayin da Sultan da Nasreen suke ciki, don haka ya jawo Naufal da Jidda suka nausa wani wurin. Nasreen ta ji ankamo hannunta, ta gane hannun Sultan ne don haka ta saki ajiyar zuciya ya kamota suka zauna a wani wuri. Kwantar da kanta ta yi a kafadarta ta yi shiru. Bai dubeta ba ya fara magana, “‘Babyna fushi kike yi da ni? Ki yi hakuri babu wanda ya taba yin hakuri a Karshe ya tabe. Mai haKuri shike da nasara.”
Nasreen ta sake narkewa a jikinsa, tana jin nasihar Naufal tana ratsa ta. “Babu abinda kayi min mijina, idan da akwai shi ma na yafe maka duniya da lahira. Ba ka ba ni kudi ba, amma ka gina min rayuwata wanda a yanzu kudi bai isa ya siya ba. Ka bani kulawa. Da gaske nake yi na yafe maka dukkan abinda kay min da ma wanda za ka yi min anan gaba.”Www.bankinhausanovels.com.ng 
Sumba ya yi mata a tsakiyar kanta sannan ya shafa kan. “Na gode Nasreen. Ki dAina kuma cewa nayi maki abubuwa, idan kina fadan hakan sai in yi tunanin kamar ba dolena bane yi maki wadannan abubuwan. Ki dauka ya zama dole in yi maki kin ji?”
Shiru suka dan yi sannan ya ce, “Gobe za ku tafi ku bar ni. Zan yi kewarki sosai.” Murmushi ne manne a fuskarta, “Babu wata damuwa tunda muna kwana mu tashi baka ganni ba, baka j1 muryata ba, don haka wannan tafiyar ba za ta daga maka hankali ba, insha Allahu zamu je lafiya mu dawo lafiya.”
Ya gane abinda take nufi, da yake bai da abin kare kansa sai ya yi shiru. Can ya ce, ; “Nasreen akwai abinda kike’ son ki yi min * magana akai, idan kika bude baki sai ki fasa. Gaya min mene ne?”
“Babu komai, Dama so nake inrokeka ranar da za a bude idanuna idan aikin ya yi kyau ina son ka zama mutum na farko da zan dora idanuna akansa. Kai kadai nake so ka zama
mutum na farko, Naufal zai zama na biyunka insha Allahu. Ka yi min wannan alKawarin.”
Shiru ya yi yana tuna ayyuka ne a gabansa ba na wasa ba, amma yana jin ba zai iya ce mata a’a ba a irin halin da take ciki, don haka ya ce, “Babu damuwa, zanyi iya bakin kokarina inyi hakan ya faru. Na gode da kika zabeni a cikin mutane na farko da zan hada idanu da ke. Wannan karramawar ba zan taba mance ta ba. Ina sonki Nasrcen, soyayyarki tana ilata ni a duk lokacin da ban ganki ba. Nasreen baki gani ne da sai kin tabbatar da raman da na yi. Zakiyya ta zame mani masifa, idan ban yi abinda tace ba, ji nake kamar an zuba min karara.”’Www.bankinhausanovels.com.ng 
Nasreen ta ce, “Kullum sai na yi maka  maganar ibada, amma sai kayi fatali da maganata, ka nesanta kanka da Allah shiyasa wannan abubuwan suke ta faruwa da kai. Kadage da addu’a ka yaki duk mai nufinka da ; sharri.” Ya ce, “Babu komai zan sake dagewa, idan zan je Masallacin sai in ji kamar ansa igtyoyi andaure ni.” Suka sake yin shiru, can yace “Barci nake ji ko za ki raka ni?” Bata karga mayana ba, wayarsa ta dauki kara. Ganin lambar Umma yasa ya dauka, “Gidan uban wa kaje? Ashe da kai za a tafi lagos din shi ne bani da mutuncin da zaka gaya min?” Sultan ya shafi kansa kamar tana ganinsa ya ce, “Umma ki yi hakuri don Allah, gobe insha Allahu zan dawo.” Umma ta ce, “Ya yi maka kyau Sallamammai. Saura ka takura mata tunda kana sane aiki za ayi mata.” Umma ta fada haka cike da damuwa da addu’ar kada Sultan ya aikata wani kuskure da zai hada jininta da shegu. Sultan ya dubi Nasreen yana sauke wayar, yasan ta ji dukkan abubuwan da Umma take gaya masa, sai ya share kawai Www.bankinhausanovels.com.ng 
Da daddare kowannen su suna dakin su, Nasreen tana kwance a Kafafun Sultan yana aika sako ta Email dinsa. Bayan ya gama ne ya daga ta ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito, itamia ta shiga tayi wanka da ruwan da ya tara mata ta nufi ‘yar Jakarta ta shafa man Kamshin da ya karbo mata daga shagon Jafar, ta shafe jikinta. Kamshin yasa ya dago yana dubanta da Katon Hijabi a jikinta. Murmushi ya Kwace masa, gaba daya ya fara mance sakon me yake aikawa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...