RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 


Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Haka ta kama hannunsa suka shiga daki. A ranar sai da dukkan Karfinsa ya Kare wajen Zakiyya, ya sha wahala fiye da tunaninsa. Haka ya kasa ko da motsawa. Ita dai Nasreen ko da ta ji shiru bata damu ba, saboda ta riga ta san da wahala Umma ta sake barinsa. Duk da zuciyarta tana gaya mata sai ya san yadda zai yi ya shigo. Shiru-shiru babu Sultan babu dalilinsa. Tun tana iya jurewa har hawaye suka fara aikin su. Har bayan Sallar isha’i babu wanda ya sa Sultan a idanunsa. Umma ta gaji ta aika Hafsat ta dubo shi. Hafsat tana shiga sashensa ta tsaya tana Kwankwasa Kofa. A lokacin Nasreen ta fito falo, haka itama Umma tana zaune da Kafarta, tana addu’ar Allah yasa lafiya Sultan bai fito ba, gaba daya ta shiga damuwa. Hafsat ta jima a tsaye, sannan Zakiyya ta bude Kofar ta tokare tana dubanta sama da Kasa. “Lafiya kike Kwankwasawa mutane Kofa?” Mamaki yasa Hafsat Kare mata kallo, sannan ta ja tsaki ta ce, “Malama ba wurinki na zo ba, gun Yaya na zo.”

ZAMU TASHI 

Zakiyya ta saki malalacin murmushi sannan ta ce, “Sai ki koma domin bai tashi barci ba, kuma ke baki isa ki sa in tashe shi ba.” Daga ciki Hafsat ta ji muryar Sultan yana cewa, “Zakiyya wace ce?”

Cikin isa ta ce, “Hafsat ce, na kuma gaya mata kana barci, sai idan ka tashi.” Ba ta sake jin muryarsa ba, hakan yasa Hafsat ta juya tana cike da mamaki, haka Zakiyya ta dinga jifarta da murmushi daga bisani ta rufe Kofar. Yadda Umma ta ga Hafsat abin ya bata tsoro matuka don haka ta ce, “Me ya faru? Yau na shiga uku, Sultan bai da lafiya ko? Zo maza ki daga ni mu je in ganshi, na san haka kawai ba zai ki fitowa gaida Ubangijinsa ba.”

Www.bankinhausanovels.com.ng

Nasreen kusan ta kusa sumewa_ saboda firgici, bata da burin da ya wuce Hafsat ta yi magana, tana gudun maganar Umma ce, da ba haka ba, da ta riga kowa isowa ga Sultan. Hawaye suka cika mata idanu tana fatan jin jikinsa da sauki. Hafsat da ta yi yaraf a zaune kamar wacce aka cirewa laka, ta dubi Umma idanunta cike da hawaye ta mayar mata da duk yadda suka yi. Nasreen ta saki baki, a lokaci guda jikinta ya Karasa mutuwa murus! Ji take

kamar Karya Hafsat take yi ba Dee dinta yake dauke da wannan lamarin ba. Dakin ya dauki shiru na wasu ‘yan dakiKu, Umma ta kasa furta komai, zargin aminiyarta ya darsu a zuciyarta, tana da tabbacin Hajiya Ladidi ta kai sunan danta gidan Malami, kuma burin su ya cika. Haka kowa ya ci gaba da zama jigun-jigun, Umma ta mike domin tana son zuwa ta tabbatar da abinda Hafsat ta gaya mata. Ta jima tana Kwankwasa Kofar amma babu alamun za a bude, sai da ta juya za ta tafi, ta ji alamun bude Kofa. A hanzarce ta juyo tana Karewa Zakiyya kallo, daga ita sai daurin Kirji. Umma ta saki baki galala tana kallonta, daga ciki ta ji Sultan yana Kwala mata kira. Umma ta harareta ta ce, “Ke! Kirawo min Sultan.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Zakiyya ta tabe baki tana dubanta sama da Kasa, “A’a Umma ba zai yuwu yana barci in _tashe shi ba, shi ya bani wannan umarnin.” - Umma ta juya kawai ba tare da ta furta komai ba. Tana fito wa ta dubi Hafsat ta ce, “Shikenan Hajiya Ladidi ta kai sunan dana ankafe shi, sai wani ikon Allah. Yadda ta mayar da mahaifin Zakiyya kafin ya rasu, haka za ta mayar da dana.”

Nasrcen ta mike tana laluben hanya, zuwa dakinta. Har ta kusa fita suka ji muryarta tana cewa, “Akwai sanin Allah.” Ta Karasa shigewa a lokacin da wani irin kuka ya taho mata da Karfi. Ta jima tana zubar da hawayenta masu yawa, daga bisani ta tuna kukan babu abinda zai yi mata, don haka ta dinga Salatin Annabi tana jin natsuwa tana zuwar mata. Agogon bangon ya buga Karfe goma na dare, a dai-dai lokacin da gabanta ya fadi da Karfi. Haka Karar bugun Agogon ya ci nasarar isowa har cikin zuciyarta. Ta kasa barci, ta kasa haKurin rashin Sultan. A daddafe ta mike ta dawo falo. A lokacin su Umma sun gaji da jiran fitowarsu sun shige ciki. Nasreen ta zauna shiru ta rasa abinda yake mata dadi. Ji take kamar ta bi shi dakinsa ta kwantar da kanta a kafadarsa ya lallasheta, kamar yadda ya saba. Muryarsa ta ji, wanda yasa ta yi firgigit, sai dai babu idanun da za ta gan shi. Don haka ta duKar da kai hawaye suna zuba, sai yau ta sake tsanar makanta, domin tana son ganin halin da Sultan yake ciki. Muryar Zakiyya ta ji tana cewa, “Sweetheart ka gama kallon labaran mu koma ciki barci nake ji. Ko kuma bari inkwanta a kafafunka idan ka tashi kawai ka dauke ni ka mayar da ni dakin mu.” Tun bayan dora idanunsa akan Nasreen ya tsinci  kansa da kunyarta, haka ya kasa amsawa Zakiyya dukkan maganganunta. Da tausayawa yake dubanta, tsoron mitan Zakiyya yasa ya kasa yi mata magana. Dukkansu suna nan zaune, tana son ta tashi, amma _ Kafafunta suna_cikin dabaibayi. Shiru-shiru babu wanda ya _ sake magana, Sai surutan Zakiyya da take yi babu kai. Nasreen bata san tana da kishi ba, sai yau dinnan da Kirjinta ke barazanar rabuwa da gangar jikinta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta sha Karyata mata,.tana ganin kawai kishin hauka gare su, haka bata yarda cewa kowacce mace tana da kishi mai zafi haka ba, sai yanzu da ya faru akanta. Ji take da za a mika mata bindiga ace wa za ta harbe babu ko shakka, Zakiyya ita ce mace ta farko da za ta fara rabata da duniyar gaba daya. Sultan ya gama karantar komai a fuskarta, don haka ya sake jin babu dadi. Ko babu soyayya a tsakaninsa da Nasreen akwai Kauna da shakuwa irin wanda ba zai taba gogewa daga zuciyarsa ba. Sai dai da ya yunKura sai yaji kamar ansa Katon dutse andanne shi. Kallon kawai yake yi, amma baya fahimtar komai. Da haka har barci ya yi awon gaba da Zakiyya.
Ita kuwa Nasrcen tana nan zaune kamar andasata. Ta kasa danne hawayen da ke malala har cikin baki daga makafin idanunta. Da Karfin addu’a ta mike tana laluben hanya. Za ta kauce hanya ya yi maza ya cire kan Zakiyya da ke jikinsa ya Karaso ya riKe ta. Ji take kamar ta fizge kanta, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, ta tabbata Sultan ya fi Karfin dukkan wulakancin daga gareta. Ko da kuwa kullum zai dinga dukanta yana watso kayayyakinta waje ne za ta durKusa ta bashi hakuri. Shi kadai ne sauran gatanta a duniya. Tana jin hucin jikinsa a cikin nata, wanda*ya haddasa mata kasala, ta Karasa zubewa a jikinsa, ta yi shiru, kamar babu wata halitta a wurin. Shima Karasa rungumeta ya yi jikinsa yana kyarma Dukkansu zuciyoyinau buyawa suke yi da Karfi, yana jin tamkar yayi shekara ne babu ita.
Tana jin alamun yana lalubon wani wuri daga sassan jikinta, ta rike hannunsa tana girgiza kai, a hankali kuma ta raba jikinta da nasa, hawaye suna ci gabu da gudu a fuskurta, Www.bankinhausanovels.com.ng
“Dukkan abinda zai faru da kai, ko na asiri, ko . na gangar ka sanya Ubangyji a farko, iyayenka su biyo baya. Kana da lafiya, ka kasa zuwa gaida Ubangijinka? Kana da lafiya ka kasa zuwa duba Umman mu da ke cikin halin jinya? Mace tana samun nasarar cutar da mijinta ne, a duk lokacin da take aikata kuskure yake biye mata. Idan Nasreen matarka ce, kana ganin kana da hurumin share lamarinta, Ubangijin mu da rayuwarmu take hannunsa ba abokin wasan mu bane, muna halin rashin lafiya ma bai dauke mana gaida shi ba, sai da aka kawo hanyoyi ma bambanta wajen aiwatar da ibada, idan muna halin rashin lafiya. Idan ni matarka nayi maka uzuri babu wanda zai yi maka hakan. Ba a hanaka soyayya da matarka ba, amma kada ka shiga lokacin bautar Allah, kada ka shiga lokacin iyayenmu. . “Dee wannan tarbiyyar akanta ka dora mu, idan ka sauya mu ma zamu iya sauyawa saboda da kai muke koyi har gobe. Ka daina yin azkar ya kamata ka koma ka ci gaba da yi, domin idan ka bar Allah da kwana daya tak! Zai barka da shekara. Allah ba abokin wasan mu bane, ina sake nanata maka. Ibadanmu shi zai sadamu da Rahamar Ubangiji wanda kowa ke nemanta ido rufe. Sai da safe.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Za ta wuce ya sa hannu ya dawo da ita, jikinsa a matukar sanyaye. A kunne yake mata magana, kasancewar itama dukkan maganar da take yi masa cikin sanyi take yi, kuma a natse. Don haka ya yi mata magana shi ma cikin irin tasa natsuwar, “Baby ban san abinda ke damuna ba, na rasa gane asalin matsalata. Ki daina cire kanki a cikin masu daraja agurina, kina da darajar da ke kanki baki san kina da ita ba. Bansan me yake damuna bane, ban san me ya hana ni amsa kiran mahaifiyata ba, ban san me yasa na kasa zuwa in dubaki ba, ban san dalilin da yasa na kasa zuwa gaida Ubangijina ba. Don Allah ki taya ni addu’a in iya cinye jarabawata. Don Allah Nasreen.”
Muryarta tana rawa, ta cire hannunsa daga kafadarta ta ce, “Allah ya yaye maka.” Yana . kallonta har ta shige, ya kasa binta kamar yadda zuciyarsa ke gaya masa. Dole ya koma ya dauki Zakiyya suka yi cikin daki. Nasreen dai barci ya Kaurace mata, tun tana sa ran ganinsa har ta cire rai, Zuciyarta kuwa babu abinda bata gaya mata akan mijinta yana can yana manne da Zakiyya, Www.bankinhausanovels.com.ng

yana bata irin kulawar da yake ba ta. Da gaggawa ta ce, “Astagfirullah.” Ta furta tana mai jin damuwarta tana sauka a hankali. Ta fahimci babu abinda ke wanzar da bakin kishi, da kuma jawowa kai masifar bin bokaye da malamai, wajen ganin ancutar da kishiya, da mata za su gane su cire dukkan tunanin wani abu a tsakanin su da mazajen su babu shakka da an zauna lafiya, da kishiya ta zama ‘yar uwa ta jini, sai dai yanzu zuciyoyin mata sun cika da bakin kishi da mugun tunani, wanda baka isa ka KwanKwasa zuciyar mace ba, bare ka gane ta Allah, wata za ta nuna duk duniya babu wacce take so sama da ke, amma da za ki leka zuciyarta, sai kin fahimei akwai Katon ramin da take hakawa take KoKarin tura ki ciki, kina zurmawa za ta mayar da Kasa ta rufeki. Don haka dole mata su fi yawa a cikin wuta, idan har aka ci gaba da tafiya irin haka. A hankali take addu’a akan Allah ya hanata zuciyar cutar da wata akan dai da namiji. A hankali ta ji zuciyarta tana sanyi sai dai tunanin mijinta da halin da yake shirin kasancewa a ciki sun taru sun hanata sakat Dole ta lalubi bandaki ta doro alwala, ta hau kan dadduma tana nemawa mijinta sauKin kan jarabawar da ke tunkaro shi.Tana son kasancewa mace ta gari agun mijinta, Zakiyya tana ganin wayo ne yasa ta aikata hakan, ta kasa tuna makomarta a nan gaba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Washegari da sassafe Sultan ya shirya da ‘yan sandansa suka wuce Kaduna, kamar yadda ya yi alkawari. Da isowarsa ya sami Abbansa da Naufal da Mairo suna karyawa, a cikin natsuwa kamar babu abinda ke damun su. Sai dai Abba da ke riKe da kofi yana jujjuya shayin ba tare da ya iya ci gaba da sha ba. Sallamar Sultan yasa duk suka dubi Kofar, sun sha mamakin yadda ba su ji hayaniyar shigowarsa ba, kamar yadda sukan ji dirar motoci idan ya shigo. Kai tsaye bisa shimfidar Abban ya Karaso inda suke zaman karyawa. Naufal ya dube shi cike da farin cik1, yana shirin miKewa. Sultan ya girgiza masa kai,
suka kama hannun juna. Mairo ta dan durkusa tana gaida Sultan, ya sakar mata murmushi ya ce, “Anti Mairo kina son in sami albarka kuwa? Ban taba jin in da uwa take gaida danta ba. Ki bari in natsa zan biyo ki har in da kike in gaidaki.” Mairo da ke tsananin ganin girman Sultan ta dan sunkuyar da kai, tana jin dadin irin girmamawarsa a gareta, duk da tarin matsayinsa. Abba ya dubce shi, suka sakarwa juna murmushi a lokacin da ya kai dankalin turawa bakinsa yana lumshe idanu, ““Abbana ko karyawa ban yi ba, na fito babban burina in yi tozali da Abbana.”” Abba dai bai yi magana ba, sai murmushi da yake yi, wanda kallo daya za ka yi masa ka gane yana cikin damuwa. Sultan ya saki jiki ya _ ci abincinsa, haka yana yi wa Abbansa hirar Office dinsa, hakan yasa shi ma Abban ya saki jiki yana bashi labarin yadda kasuwancinsa ya kasance. Abin mamaki sai ga shi Abba ya ci abinci Www.bankinhausanovels.com.ng sosal. Gaba daya suka yi Hamdala. Duk suka mike domin komawa cikin falon saman kujeru. Sai a lokacin Nautal ya rungume Sultan fuskarsa tana ‘nuna tsantsar farin cikin ganinsa. Sultan ya ce, “Wai! Nasreen tana can tunaninka yasa duk ta rame, bata da zance sai naka, amma kalli yadda kake Kiba abinka baka da wata matsala. Abba me kake bashi ne?”
Abba ya ce, ““Maryama za ka tambaya, da ni da Naufal duk kiwonta ne. Mamanka din dai za ka je ka tambaye ta abinda take bamu.” Sultan ya ce, “Nima na zo kenan sai na yi irin Kibar Naufal zan koma.” Gaba daya suka yi dariya banda Sultan da yake jin kamar wani abu yana damunsa. Ya so Kwarai ya tafi da Naufal Abba yace masa ba zai yuwu ba, shi kadai yake debe masa kewa, ga kuma Karatunsa. Naufal ya mike ya fice gun ‘yan sanda, tunda ya kula akwai maganar da suke son tattaunawa. Sultan da ke zaune a Kasa kusa da Kafafun mahaifinsa ya dube shi da kulawa yace “Abba, Umma ta gaya min dukkan abubuwan da suke faruwa. Abba na shiga tashin Www.bankinhausanovels.com.ng hankali, ko kuma in ce maka ina cikin damuwa. Amma ina son ka kwantar da hankalinka, na fahimtar da Umma  da hafsat kuma ta fahimta sosai, dama kuma bata amince ba. Don haka ka kwantar da hankalinka ina ji a jikina komai ya kusan zuwa Karshe insha Allahu lamarin zai zo kamar ba ayi ba. Idan kana sa damuwa a ranka bana samun natsuwa Abba.” Abba ya saki ajiyar zuciya mai nuni da ya sami natsuwa sosal. “Na gode Sultan. Allah ya yi maka albarka. Bana cikin natsuwata, kalaman mahaifiyarka ya daga min_hankali sosai. Amma yanzu na sami natsuwa, ni dama damuwata kada ta zargeni da abinda tun yarinta ban taba waiwaya ba. Ka je kaci gaba da hakuri watarana sal labari. Sultan ya amsa masa yana ci gaba da cewa, “Abba Zaria zan je akwai shagon da zanje a Zaria din, wai shagon Jafar, zan yi wa Nasreen siyayya.” Abba ya saki fara’a, “Sai ka hada da Zakiyya.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Gabansa ya fadi ras! Jin an ambaci sunan Zakiyya, sosa kansa ya yi ya ce, “Eh amma ba zan karbar masu iri daya ba, ko kuma ita Zakiyya tunda tasan wurare sai inbata kudinta ta siyo nata, itama Nasreen din irin wanda take so zan siyo mata.” Abba ya jijjiga kai alamun ya fahimta. Sultan ya mike ya shiga gun Mairo yana kallon Kofar mahaifiyarsa a rufe, ya girgiza kai. A daki ya sami Mairo ya gaidata sannan ya ciro kudi masu yawa ya mika mata Da Kyar ta Www.bankinhausanovels.com.ng karba, ya fito ya tasa Naufal suka tafi Zaria tare. Www.bankinhausanovels.com.ng
A cikin mota Naufal yake bashi labarin yadda Abba yake kasancewa a cikin damuwa. Sultan ya dafa kafadarsa, ““Kada ka damu insha Allahu komai zai zo Karshe.” Kai tsaye wurin Hauwa’u Dan Borno suka tsaya daga can suka wuce Kasuwan sabon garin. Sai dai bai shiga ba, ya tura Hauwa’u ita ta siya masa komai, ya yi mamakin da ta dawo masa da canji. Kudi ya Kara mata yace itama ta siya

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...