RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 2 BY Fateeyzah mbs✍️ - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 2 BY Fateeyzah mbs✍️

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 2 BY Fateeyzah mbs✍️

- - Post a Comment

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 2 BY Fateeyzah mbs✍️            Www.bankinhausanovels.com.ng 
*ALHERI WRITERS ASSO*        *A.W.A*


https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/


https://chat.whatsapp.com/FqpYwmmbahRLaZHssfLpfu


 *RAYUWAR CAMPUS*

 _(Rayuwar 'yanci)_


 *_Na Fateeyzah mbs_✍️*


http://Fzahmbs.blogspot.com

 *_Fateeyzah@wattpad_*  *_Marubuciyar_*

 *_Gidan nagoggo_* 

 *_Doctor zahrah_*

 *_Yakin Mata (aure)_* 

 *_Kuda wurin kwadayi_*


 _Tukwicine ga daukacin matan jami'a_ _ina  baku hakuri na rashiin  ganin posting dina  na littafin *kuda wurin kwadayi,* insha Allah gobe zaku jini._ 


* ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ *

*Page 02*

*ELEGANTY* ,Babban club ne a garin wanda ya tara

manyan masu kudi da 'yan siyasa, duk wata yarinya da

take jin ita wata shegiya ce, wacce runs ya bi mata jiki,

zaka sameta a wannan club mai cike da Alfasha.

Napep din na tsayawa a kofar wurin, suka kama sumy dake

gyangyadi duka fitar da ita tare da sallamar mai

napep din,

wasu mirtika mirtikan katti ne a bakin kofar sai mazurai

suke, ganin su Hibba yasa suka bude musu kofa suka shine,

wurin ya masifar kayatuwa,ba ka ganin komai sai hayaki

shisha daya turnike wurin, ga uwa uba kida dayake tashi,

manya manyan Alhazai ne sun sha jallabiya, yayin da

wadansu ke rawa da karuwansu, wanda baka ganin komai

sa katon tumbi, wasu kuma suna shan barasa tare da shan

shisha, wasu kuma gasunan dai anata aikata alfasha da

'yan matan, wanda in ka kalli 'yan matan wurin duk

kananan yarane sa'o'in su sumy.

Direct wani daki suka nufa da sumy, suka kulle kofa, after

some seconds suka fito, inda hibba ta karasa wurin chasu,

meena kuma ta nufi bar, ta karfi wine ta fara tittila ma

cikinta, hibba kuwa tana can tsakiyar alhazai biyu suna ta

shafeta da sunan rawa.

Bangaren sumy kuwa, ko dana shiga dakin tana kwance

haihuwar uwarta, yayin da wani shirgegen

Alhaji yake kanta yana aikata masha'a da ita, ba kajin

motsin komai sai gurnaninshi daya cika dakin.

_(Allah ya shirya, su kuma iyayensu suna can suna shan

baccin su hankali kwance, a tunaninsu 'ya'yansu na hostel,

hattara iyaye, wallahi yanxu abunda ake aikata a school,

lamarin ya baci, dakibar 'yarki a hostel, gwara kin barta a

gidan 'yan uwa, ko ki kama mata haya gidan matan aure,

wadanda duk tsiya suke kulle gidansu da wuri, amma fa

karku sake ku kama musu gidan students zallah, don nan

ma sai dai addu'a)._

Duba Agogon hannunta tayi tare da barin wurin chasun da

take, yayin da Alhajin da suke rawa yace" haba cikaa, muna

cikin jin dadinmu zaki tafi"

Wani killer smile ta sakin mai tare da kanne mai ido, sannan

ta waving dinshi da hannu, wurin meena ta nufa ta janyo ta,

sannan suka nufi dakin da sumy take, suna shiga dai²

Alhaji ya fito daga wanka yana goge jiki da towel, ganinsu

yasa ya saki wani irin murmushi tare da cewa " har lokaci

yayine babies".

Karkada ido hibba tayi cikin salo sannan tace" ko kana da

bukatar karine".

Cikin rawar baki yace" da da hali dana kara dake, amma

maganin dana ba Hajiya ya kusa expire, gwara dai in tafi,

don in ta tashi bata ganni ba gobe akwai yaki" ya karashe

magana yana dariya.

Murmushi Hibba ta saki sannan ta kalli meena da idonta ya

rine yayi jawur tace" beb tashi mu kintsa sumy mu wuce,

time is going".

Cikin tangadi meena ta tashi ta kwaso kayan sumy dake

zube a kasa ta mikawa Hibba, ba tare da bata lokaci ba ta

maida ma sumy kayan Jikinta wanda yayi daidai da gama

shiryawar alhaji, sunkutar sumy yayi a kafada ya nufi waje,

yayin da su kuma suka rufa masa baya.

Wata Mercedes Benz da akayi parking a kofar club din ya

nufa, inda ya bude seat din baya ya kwantar da sumy,

sannan hibba ta tura meena ciki, ita kuma ta bude gaba ta

shiga, wanda already Alhaji ya shiga mazaunin driver, jan

motar yayi suka yi gaba.

Sai da sukazo dai² *BUBBLE PLUS* ya dakata, inda Hibba

ta fita ta nufi box din nan ta kwaso musu kimonon su da

veil, sannan suka wuce.

A can *ELEGANTY* kuwa gaba daya Alhazan wurin sun

gama watsewa sai matasa, inda suma kidan ya fara sanyi,

sai dai gaba daya sun zube a wurin kowa yaja tasa.Ee

Karfe uku dai² suka karaso bakin gate din school, inda suna

zuwa security ya bude musu suka shiga, bakin hostel yasa

ijesu, wanda alokacin sumy ta farka,bude kofar motaz suka

yi suka fice yayi da shikuma ya kalli Hibba yace"mu hadu

karfe biyu na rana a school guest house, amma ke kadai

zakizo, kinga daganan an rufe case din carry over" ya

karashe magana yana kashe mata ido.

Murmushi tayi tare da amsawa da "okay Dakta, sai ka

ganni".

Jan motar shi yayi yabar wurin, yayin da Hibba tabi bayansu

sumy dake tsaye da security a bakin gate din shiga hostel.

Karasawa tayi tare da fadin" Baba ya akayi baka barsu sun

shiga ba?"

Yake wani jajayan hakoranshi yayi tare da cewa" haba

yarinya kema kinsan kan batun, ruwa nake so in rage, kinga

abokin aikina can shima da tashi".

Wani banzan kallo ta sakar mai tare da cewa" Gaskiya Baba

sai dai ka bimu bashi don gaba dayan mu nan a gajiye

muke, kaga su a buge ma suke ba abunda zaka samu".

Nan danan ya hade rai tare da cewa" wallahi in kunga kun

wuce kofar nan kun samun natsuwane, in ba haka ba ku jira

har karfe shiddan safiya in an bude sai ku shiga" ya fadi

yana jefa musu banzan kallo.

Kallon agogon hannunta tayi taga lokaci ya ja, don uku da

rabi tayi, sannan ta maida kallonta ga su sumy, wadanda

sukayi zaman dirshan a kasa, don da alama har lokacin

suna cikin maye, wani kayataccen murmushi ta saki tare da

cewa"shikenan Baba, ka bude ma 'yan uwana su shiga, ni

sai in baka".

Saurin wangale baki yayi tare da cewa" yawwa 'yata yanxu

naji magana".

Bude kofar yayi, sannan Hibba ta tadasu tace su shiga,

haka suka tashi suna layi, sannan suka shige, yayin da

baba yayi kokarin rufe kofa, sai dai riko gaban wandon sa

da hibba tayi ya dakatar dashi, wani nishi ya saki,

murmushin keta Hibba ta saki tare da murde wurin ,wani irin

gigitaccen ihu ya saki, dariya ta saki sannan ta ture shi gefe

ta shige ciki tare da banko masa kofa, cire takalminta tayi ta

zuba da gudu.

*Don't miss any single page*
 *Comment* 

 *Share*

 *Like* 


 _*Fateeyzah mbs*_

Post a Comment for "RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 2 BY Fateeyzah mbs✍️"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...