RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs✍️ - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs✍️

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs✍️

- - Post a Comment

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs✍️

              Www.bankinhausanovels.com.ng *ALHERI WRITERS ASSO.*           *A.W.A* https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/


https://chat.whatsapp.com/FqpYwmmbahRLaZHssfLpfu


 *_RAYUWAR CAMPUS_* 

 _(rayuwar  'yanci)_ 


 *_Na Fateeyzah mbs✍️_*


Fzahmbs.blogspot.com

 *_Fateezah@watpad_* 

 _*Marubuciyar*_👇

 *_Gidan nagoggo_* 

 *_Doctor zahrah_*

 *_Yakin mata(Aure)_* 

 *_Kuda wurin kwadayi_* 

_____________________________________

* ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ *

*Page 01*

Security light din daya haska wurin ya bani damar ganin

abunda ke wanzuwa , duk girman filin dake bakin girls

hostel din nan cike yake taf da motoci na alfarma, wanda

zakayi tunanin dinner party ake awurin saboda yanda mata

keta fashion parade a wurin, ko wacce ka ganta taci

kwalliya sai kace zata red carpet, kallon agogon wayata

nayi na ga karfe sha daya na dare, wanda a

wannan lokacin

ya kamata ko wacce macen kirki da tasan darajar kanta

tana dakinta, amma sabanin nan da zaka dauka rana ce,

*RAYUWAR CAMPUS* kenan mai cike da 'yanci, babu mai

kwaba maka ko ya maka nasiha, kowa zaman kanshi yake,

sannan kowa karatun gidansu yake biyawa.

Daga can gefen dama, 'yan mata ne kyawawa su biyu suke

tsaye ko wacce fuska tasha smoky make up, sanye suke da

wasu fitunanni kimono wanda suka sha kwalliya da stones,

sannan ga wani uban takalmi high hill da sukasha, bakajin

komai, sun yane kansu da wani siririn gyale da yasha

stones, sai kas kas na taunan cingum da sukeyi cike da

fitsara.

Daya daga cikinsu ce ta kalli agogon hannunta tare da sakin

tsaki, sannan tace " wallahi meena na gaji da jiran sumy,

tun tuni ta tafi taje tayi zaman ta, tana can yana kwakuleta

mu kuma ta barmu a tsaye, wannan ai tana zubar mana da

class ne duk wanda zai wuce sai ya kallemu".

Wadda aka kira da meena tace" haba hibba kiyi hakuri

mana, kinsan in muka tafi muka barta baza taje ba, sannan

itace pass dinmu in mun dawo, kinsan securities din nan

basu da mutunci in ba wani abun kabasu ba, ba za su taba

barinka ka wuceba, kuma kinsan sumy ce kadai bata

kyankyamin su a cikin mu, ga tacan ma ta fito" ta karasa

magana tana nuna bakin wata mota kirar prado.

Kai duba nayi, wata kyakkyawar budurwace da baza ta

wuce shekara sha shidda zuwa sha bakwai ba take tsaye

da wani tsoho wanda akalla zai kai shekara sittin a duniya

yana ta washe mata wawulan bakinshi, hugging dinshi tayi

tare da mai kiss, sannan ta nufo su meena, dogon wando ne

na jeans a jikinta wanda ya matseta sosai ya fito da shape

dinta na figure 8, sai wata armless top data matse ta breast

dinta, hannunta rike da kimonon ta, sannan kafarta sanye

da wani uban high hill wanda yafi nasu meena tsawo.

Karasowa tayi wurinsu, sannna cikin zakakkiyar muryarta

tace" sorry friends, wallahi sugar ne ya tsayar dani kunsan

madam dinshi na on, shine nadan taimaka masa ya rage

ruwa" ta fadi tana mai tura hannunta cikin riga.

Tsaki Hibba ta ja tare da banka mata harara sannan tace" ai

ga alamanan bra dinki tayi kasa, sai ki gyara mu tafi don

dare ya fara yi Allah ma yasa mu samu Napep" ta karasa

magana tana mai duba agogon hannunta.

Marairace fuska tayi tare da cewa" don Allah ku kareni in

gyara, kunga mutane na wuce mu".

Wata uwar shewa meena ta yi tare da fadin" ta baya ta

rago, san da kika je wancan tsohon najadun ya matse miki

kayan cowbell baki ji kunya ba sai yanxu zakice kina jin

kunyar masu wucewa, zo badan dai halinki ba mu kareki,

kuma wallahi kar ki bata mana lokaci don nasan ana can an

fara sakin masu zafi".

Bubbude kimononsu su kayi suka rufa mata, dukkansu

shigan dogon wandon jeans ne a jikinsu da armless top

kamar yanda sumy tayi, cikin kankanin lokaci ta gama

gyarawa, sannan tace musu "muje na gama".

Ba tare da sun tankata ba suka gyaygyara sannan suka dau

hanya, suna tafe ba wacce ta tanka ma 'yar uwarta, sai da

suka kawo dai² building din S.U.G (student union

government), sannan sumy tace" wai naga kuna karawa

gaba, ba zamu kira salma bane".

Yatsina fuska meena tayi tare da cewa" tace baza taje ba,

don yau suna da meeting a S.U.G karfe sha biyu, inaga ma

anan zata kwana in an gama meeting din".

Wata dariya sumy ta kece da ita sannan tace "shegiya

salma, kice yau su presido zasu kwashi gara, don dai nasan

baza su barta haka ba".

Murmushi Hibba tayi tare da cewa" kuma dai kunsan Salma

taxi no garage ne, bata gamsuwa da namiji daya, tafi so taji

kamar uku akanta, shi yasa ni ban sata akaina don ko wani

gaja salma bi take". Ta karasa tana mai yatsina fuska.

"Shi yasa in akayi hutu take shan wuya, kinsan gidansu

kulle ake musu" cewar meena dai² sun karaso bakin gate

din fita daga makarantar.

Daga gefen gate din, wani matashi da zai kai shekara

hamsin da uku,wanda yake sanye da uniform din security

yace" Allah ya tsare kannina, a dawo lafiya".

Hada baki suka yi wurin Amsawa" Allah ya yadda

yayanmu".

Bakin gate din a cike yake da motoci wanda suka sha bakin

tint, kasancewa ba a barin mota mai tint shiga.

"Shegiya Rufy ashe ta dawo" cewar sumy tana nuna wata

'yar duma² da ta fito daga cikin wata camry.

Meena ce ta murmusa tare da fadin" Ai Rufy ta ji dadi

wallahi, saurayin nan nata na ji da ita, tun level one fa suke

tare, amma kinga har yanxu tare suke runs dinsu".

Hibba ce ta yatsina fuska tare da cewa" Don Allah kubar

wannan maganar, in mun dawo kwa dasa, kuzo mu nemi

napep sha biyu fa tayi".

Tare napep sukayi tare da fada masa wurin da zai kaisu, ba

tare da sun tsaya ciniki ba suka shige, mai napep ya ja.

A can bakin hostel kuma, securities ne kebin kowacce mota

da sunan koransu, saboda sha biyu tayi, wanda shine

lokacin da Dean yabada domin kulle hostel tare da koron ko

wanne student dake bakin wurin, sai dai abunda zai baka

mamaki shine yanda maimakon kora sai dai karban kudi da

sukeyi a matsayin cin hanci a wurin masu mota da student,

wanda in ka bada ka zauna, in kuma baka bayar ba, ka kara

gaba.

A bangaren su Sumy kuwa, sabon gari suka nema, inda mai

napep ya saukesu a kofar club din *BUBBLE PLUS* ba kajin

komai sai tashin disco, sallamar mai napep sukayi tare da

bashi dubu daya, haka ko ya wuce yana mai sa musu

albarka tare da neman musu shiriya wurin Allah, don duk

wanda/wacce ka gani a wurin yana/tana bukatar Addu'ar

shiriya.

Tsayawa sukayi a kofar wurin tare da cire kimonon jikinsu

da gyale, Suka ajiye a wani boxes da akayi don ajiye

muhimmin abu, nan danan kamannin su ya sauya zaka

rantse irin karuwan nan ne na kudu, domin bazo da kitson

attach din da suka yi har gadon bayansu, sannan suka

kutsa kai cikin wurin.

Katon hall ne, wanda akayi decoration dinshi da yadi black

and red, sai kujeru leather seat, da taburan roba, sai bulb

din wuta mai kala² wanda sai wal wal yakeyi, daga hannun

dama kuma giya aka jera akan tabur kala kala yayin da

saman gurin aka rubuta *BAR* da manyan baki.

Gaba daya wurin Ya mutse yake da maza da mata, yayin da

wasu ke rawa, wasu na shaye² dangin su giya, codien da

shisha, wasu kuma suna rungume² da shafe² , gashinan

dai abun ba kyan gani, don duk matan wurinnan babu mai

sanye da wata sutura ta kirki.

Suna shiga kowacce ta kama gabanta, yayin da sumy ta

nufi bar, Hibba ta nufi masu rawa, sai meena da ta ke kutsa

kai cikin jama'a, tana tafiya kamar mai sanda.

Sun kwashe kusan awa daya da rabi a wurin sannan naga

Hibba da meena sun nufi wurin sumy wacce ke zaune a

*bar* tana busa shisha, dago kanta tayi ta kallesu yayin da

idonta yake jajawur, kyafta ma juna ido sukayi, take sumy

ta taso ta nufosu tana tangadi, saurin kama ta sukayi suka

nufi waje.

Napep suka kuma tarewa inda Hibba tace mai" Eleganty

zaka kaimu, basu jira cewar shi ba suka shige.

*Don't miss any single page*

 *_Fateeyzah mbs_*✍️

Post a Comment for "RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs✍️"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...