NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI                  Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

A sanyaye Jummai ta kada kai, Oh na fahimata”, Aljanin Tanimu yace, “Yauwa! Ai shi wannan auren sai mutum ya Kasaita yake yin sa, kamar dai ke din nan”Jummai ta sake kada kai, murna da dan tsoro na zagaya kanta.
Dakin ya jima shiru, sai can cikin kakkausar murya Aljani Tanimu yace mata, “Zaki auri shi wancan Gwamnan Aljani, nan da sati biyu zai zo ku gana, zai ‘taho miki da kudin « aure milyan hamsin, na bar ki lafiya”. Sai Jummai taji Kit! An datse hayaniyar da ta cika dakin hade da muryar tasa, Kamshin da ya cika dakin kuma ya fara raguwa. Boka Salmanu ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya yana dubanta, Gaskiya ke mutum ce mai sa’a”. Jummai ta kantamo murmushin murna dana yaKe ta gwamutsa, muryarta na rawa tace, “Boka ta yaya wannan lamari zai yiwu?” Salmanu ya kawar da kai yace, “Ai ba dole ba ne, na sani zabi ya baki, in ba kya son kudin ai zaki iya fasa auren”.

ZAMU TASHI 

Ta zabura,Yaya fa bana son kudin? Ina so mana, wai so nake kayi min bayani yadda lamarin zai tafi”. Kai tsaye ya amsa mata.
“Ki lje sati daya ki dawo zan bincika miki, na san dai kurar arziKinki tayi kuka, nan gaba sai dai ni kaina na nemi arziki da taimako a wajenki...Ba ta bari ma ya dire ba da azarbabi ta hau cewa , “Allah ya sa Malam, ai zan maka halacci, ni bana manta alkhairi”

.
Hakan ai yana da kyau, kije ki dawo nan da sati guda zamu shirya muki yadda zaki hadu da shi.Ta zube masa dubu biyar ta yi masa sallamata ~ _ fita. Basu samu damar.shewa ba don akwai wasu bakin a waje, tana fita suka shigo.  Sai da suka sallami baki uku sannan Adamu ya iso gidan yanayinsa a birkice Allah ya sa Www.bankinhausanovels.com.ng babu . kowa a gidan, hakan ya basu damar sanya shi a _ kwana suka hau tambayarsa,  Yana dafe da Kirji ya dubi tsakiyar idon . Salmanu yace, . , ' “Kai nifa na fasa auren Husna...Maganar ba ta zowa Salmanu a bazata ba, don haka haushi bai bashi damar shiru har Adamu ya dire ba ya tare shi,
Shine.ka debo wannan jan idon ka zo ka * fada min ka bar min ita ni na aure ta?”, Adamu ya shiga hayaniya yana yarfe hannu, “Eh in ma hadiye ta zaka yi Karewar aure kaje ka aure ta nidai bana son ta Duk suka tsaya suna kallonsa, Tanimu da mamaki amma Salmanu har hawayce sai daya tsiro masa ya dinga tsinewa Salma da Sa’a yana roKon Allah ya turbuda su a wuta tare da maisiyacin bokansu. Adamu ya cigaba da hayaniya yana cewa,‘Ai duk kai kake zuga ni na Kara auren, ni mai . , kamar Salma me zan yi da wata Husna...Tanimu ya kasa shiru, “A haba Adamu ya zaka yi mana sabo?” Adamu ya zaburo kamar zai hadiye Tanimu, Sabon me nayi?”Babu wani Shakku Tanimu ya amsa_ *“Kundubar nan na ji kana neman hadawa da Husna, in kayi haka gaskiya ka cuci kyau, masu shi ba zasu yafe maka ba”. ‘A tunzure Adamu Www.bankinhausanovels.com.ng yayi KoKarin kai wa ’ Tanimu naushi, amma ya goce, Salmanu cikin nasa . fishin ya ce,ai“Yau ba zan hana kace mata kunduba ba_~- Tanimu, fadi sau dubu in ka so, kuma wallahi in ya _ dake ka, dunKule hannunka ‘ka toshe masa fuska, nima nan zan shigar maka, ai ya san karona da shi babu dadi, yanzun nan sai ya kwana a asibiti 'wallahi” Adamu ya juyo kan Salmanu kamar zai hadiye shi don masifa, “Ai na zaci nima cewa zaka yi zaka kashe ni “To kashe ka wata riba ce? Ba-gara kullum in ' dinga yi maka wawan naushi kana kwana a gadon asibiti waccan .kundubar, na sintirin jinya ko zata samu ta sabe..Adamu ya farahawaye, “Allah ya tsine maka in ka Kara ce mata, kunduba” Don tsabar daurewar kai Tanimu kasa cigaba_, ' da tsaiwa yayi, sai bin bango yayi ya samu ya zauna ‘ yana kallon yadda Salmanu da Adamu ke ta faman zagin juna, har daga Karshe Adamu yayi zuciya ya ‘fara tsintar kayansa wai zai bar musu gidan. Tanimu ne ya lallabo kusa da Salmanu yace masa, . : “Yaya kake neman ka biye masa ne Salmanu ' ka san fa ba a hayyacinsa yakeba, in ka bar shi ya tafi zai cutu...”. Salmanu ya kasa’cewa komai, sai sanya hannu yake kawai yana dauke Kwallar dake taruwa a idonsa, yana kuma satar kallon Adamu wanda ke tattara nasa inasa. “ -Sai da yaga Adamu na shirin ‘ficewa daga dakin sannan ya sha gabansa cikin fishi, An ji zaka tafi, kafin ka tafi sai ka fada min . da ni kake fada ko da Husna, Kiyayyar Husna ce ta shafe ni ko kuma taya Salma Kina kake?”. Cikin gadara Adamu yace Ni duk wanda ka zaba daidai ne”Salmanu ya kai yatsansa fuskar Adamu kamar zai lakuce masa hanci, In ka san daidai din ko? Shashasha kawai”.Adamu bai ji fushi ba, don yana jin fushi ne in an Zagi Salma ba wai in an Www.bankinhausanovels.com.ng zageshi ba. Salmanu ya Sassauta murya yace
Salma ta zugo ka ka fasa aure kuma ka fita hanyata ko?”.Shi ma Adamu ya sassauta murya, Da nazo na ce.maka zan fita hanyarka ne? daga maganar na fasa auren Husna kuka yayimo  fuskata kuka hau ci.. Salmanu ya dan bugi kafadarsa yana KoKarin shanye fushinsa, To yi hakuri an gama, na karbi tayinka na auren Husna, don Allah maganar ta wuce, don haka nake neman alfarmar yadda ba ka so a ci fuskar matarka to nima kar kaci ta tawa matar”Ko a jikin Adamu ya kada kafada alamar ko in kula, sannan ya ce, “Bani da matsala da wannan”.“Ka yi magana da Husna ne ka fada mata . cewa ka fasa aurenta?”, Salmanu ya tambaya, . ’ Adamu ya girgiza kai,“Nazo shawartarka ne, na manta kafi kashi doyi”Oh yi hakuri, ai kaine ka zo da jan ido, amma yanzu na fahimce ka. Ka barni ni zan sanar _ da Husna cewa ka fasa aurenta”. Adamu ya ware ido yana kallon Salmanu, -“Kudadena da na bata daga kudin‘ aure zuwa na lefe da kudaden da na bata na hidima kai, zaka - dawo min da su?, Salma ta nuna min tana da buKatar_ - kudin” Salmanu yayi KoKarin ya mallaki kansa ya — kasa,.sai da ya Kundumo wata ashar ya aunawa Salma,  “Dan kaza-kazan Ubanta kai baka fada mata cewa yawanci ba kudinka ba ne nawa ne ba? Cancakat din kudin kayan lefen na waye? Ko Www.bankinhausanovels.com.ng Ubana ne kai zaka tafi makka? Shi ma kudin auren da duk abinda ka bawa Husna ai hatsin bara ne nawa da naka, kaje kai da Salman ku ware naka ka zo min da lissafi in biya ku dan kaza-kazan ubanku”’Jikin Adamu ya dan yi sanyi, musamman ganin Salmanu ya dau zafin da yake yanke danyen hukunci, a raunane yace,
“Ka ga Salmanu, in ka yi niyyar zagin ubana fa ba sai ka sami wannan dalilin ba ka zaga kawai...”Salmanu ya tare shi, “Kai ma in kana son in zagi ubanka to ka
dinga sako min Salma a hanyata”.Tanimu na can gefe ya shanye baki yana kallon wadannan zakunan abokan' nasa masu abin mamaki. Yana kallon Adamu ya kada kai yace, To ai shikennan, kai ka san adadin kudina, sai ka lissafa ka ba ni abina”.Ba tare da hayaniya ba Salmanu yace, “Zan biya amma da sharadi, lallai ba kai zaka sanar da Husna cewa ka fasa aurenta ba nine”Kafin ya dire Adamu ya amsa,
Ni-ko a hanya ba na fatan na sake ganinta bare wata magana ta hada mu”Yauwa to madalla ka tsira, Kundubarka kuma tafi ka tsira wadda har yau ban sa hannun daukar fansata a kanta ba, wadda duk ran da nayi hakan, Kila numfashin daya a cikin ku zai Kare‘In ka san inda ranmu yake kar ka bari ya kai gobe”“Za ku kai.gobe, ai mutuwar tsaye nake shirinku yi”Adamu ya ja wani dogon tsaki kawai ya shiga mayar da kayayyakinsa da ya riga ya tsince yana mayar da su wajen zamansu. Salmanu ya faki idonsa ya dauke masa waya, ya kashe ta ya boye a aljihu Www.bankinhausanovels.com.ng Yana. samun “Yar tazara tsakaninsa da Adamu ya mika wa Tanimu wayar yayi masa magana Kasa-Kasa, “Maza shiga bandaki ka danna. wayar nan a ruwa ka barta tsawon minti goma sannan ka tsame shegiya ka dawo min da ita”Tanimu bai nemi ba’asin Salmanu ba ya karbi wayar ya wuce bandakin, dama shi tuni-ya sarawa makircin Salmanu, wanda da shi suke sana’ar da suke samun wannan maKudan kudaden. “Tanimu ya je ya aikata, waya ta tashi daga aiki, sannan ya dawo wa da Salmanu ita, shi kuma °* ya lallaba ya buya ya busar da ita sannan ya dawo da ita inda ya dauka. Suka share waccan maganar suka cigaba da sabgoginsu, duk da Adamu ya canja, ba shi da walwala sosai, sannan ya cika zama shiru da alamun tunani Hakan ya sa Tanimu ya dinga tausaya masa, amma Salmanu babu komai a tare da shi sai fushi, ji yake da zai ga Salma a wofance ba idon mutane babu abinda zai hana shi shaKe banza ya kashe. Bai Kara jin tsanarta ba sai da yamma likis suna ma shirin tashi Husna ta kira shi hankalinta kamar a tashe, Kamar zata yi kuka ta ce, “Malam ban -sani ba ko gajen hakurina ne, matsalar da kake min magana ta taso, tun safe na kasa samun Adamu a waya, jiya kuma da dare mun rabu lafiya bayan ya koma gida na kira shi, ni dai in ba kunnena ne yayi min gizo ba na ji Adamu yayi min tsaki ya dura zagi ya kashe wayarsa...”. Ba ta iya cigaba da daurewa ba sai da ta fashe da kuka. - . Lokacin suna tare da Adamu, ya zabga masa wata uwar hararar da bai san yana yi ba saboda . hankalinsa ba ya kan Salmanun, Salmanu ya rarumi _wayarsa ya fice can waje inda babu mai in hirarsa a -waya. Ba kiyi gajen haKuri ba, gaskiya wata gagarumar matsala ta taso an kunno muku wata gagarumar wuta wadda ta sa Adamu ya ji ba shi da _ wata mafita sai ta janyewa Aurenki. Cikin kuka Husna tace, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”  Salmanu yayi shiru yana jinta har ta gama kalmomin bayyana damuwarta shi kuma yana ta auna wa Salma da Sa’a ashar da tsinuwa a zuci, har  zuwa lokacin da Husna tace, ‘To yanzu meye mafita Malam, ko na fito nazo yanzu?”’. Salmanu yayi saurin cewa, “A’a kiyi zamanki, shin kina addau’ar da nace ki dinga Www.bankinhausanovels.com.ng yi?...” “Wallahi ina yi Malam, tun daga ranar ban huta ba don na san in ban sami Adamu ba baKin ciki ba zai bar ninahutaba”. . Samanu yace, Yanzu ki bar lamarin a hannuna, zan tafiyar da komai, abu daya zaki taya ni da shi shine, kar ki sanar da kowa halin da ake ciki daga danginki har - Kawayenki, sannan karki sake kiran Adamu a waya’ Wannan babban aiki ne da zai yakushi farin cikin Husna, amma dai ba ta da wani zabin sai shi, dole tana kuka da nuna damuwarta tana komai ta godewa Boka sannan ta sauke waya duniya na Kara kuntata gareta, ‘Da Salmanu ya koma wajen'su Adamu sai yayi fuska ya ce masa, “Wai kuwa jiya da yau ka yi wankan maganin nan na tofi da na kawo maka?”, Adamu ya gintse fuska,“Ai ni ban taba yi bama, ko nima shashasha ne da zaka zama bokana?”.Au ka na zargina da cutar da kai ashe?”.“Ko ban zarge ka ba tunda ni ba yakin duniya na uku za ni ba ai ban ga dalilin da zai sanya_ka ishe ni da magane-magane ba”. Salmanu ya rage murya yace, “Salma ai tafi Hitila sharri...”. Adamu yaso ya ji Salmanu ya kama sunan Salma don haka ya sa masa ido, . “Me kace?”. Salmanu na dariya ya amsa,“Cewa nayi kafi kowa sanin kana da ‘matsala”. ~ . Adamu ya kawar da kai, “Ai ni kai kadai ne matsalata Salmanu”Salmanu ya tari numfashinsa, Don zan aure maka Husna?”. Adamu ya bata rai, “Banason wannan maganar”Salmanu ya dafa kafadarsa, ya fara yi masa magana cikin sanyin murya,“To maganina na wannan matsalar taka.ce lokaci bayan lokaci ana sake maka zuciya da tsarin rayuwa, yau kana son Salma gobe ba ka sonta, yau kana son Husna gobe ba ka sonta, in ba’a nemo maka maganin wannan zuciyar mai tsalle-tsalle ba, - lallai zaka Kare rayuwarka cikin ginawa da cushewa...Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana magana yana wucewa yaje ya dawo masa da rufaffen bokitin robar da aka karanta masa
ayoyin karya sihiri kuma aka zuba garyen magarya, -ya ajiye masa a gaba yana cewa,“Tanimu mu ba shi guri ya sha yayi wanka ko kuma shafe jiki, mummunan zargin da kake min ka bar ni da Allah kawai”. .
Adamu na son lulawa duniyar tunani ya fito da wayarsa yana kokarin kunna ta don yayi kira, sai ya gan ta a mace, yayi KoKarin ta tashi ya fahimci lalacewa tayi, sai ya dubi Salmanu,,.“Tun tuni muke zancen zan sake waya, kaga wannan ta mutu, sai ka sai min wata yanzu”salmanu ya sako wani murmushin mugunta yace, Haba dai baka da imani ne wai, ko radiyo ai  bai kamata ka ce yanzu na sai maka ba, dole ka jira bayan aurena kamar yadda na sadaukar da duk wani. - jin dadina na so jiran naka auren” -
Cikin halin ko in kula Adamu ya ce, . “Allah ya kai mu”.

***********

Salma ta samu Adamu fiye da yadda ta zata, sai yadda ta so take juya shi har lokacin tafiyarsa yayi ya fice ya tafi saudiyyarsa. sO Sai bayan tafiyarsa ta fahimci cewa bai je ya sanar da Alhaji fasa aurensa ba, gashi babu waya a hannunsa bare ta kira shi ta yi masa umarnin ya sanar da Alhajin ta waya.
Da ta yi gangancin kwasar Kafa ta je ta sanar da Alhajin da kanta, wankin babban bargo yayi mata Www.bankinhausanovels.com.ng tas! Babu irin haukan da bai lika mata ba ta taso babu nauyi kuma cikin tashin hankali. Babu waya a hannun Adamu, sannan zai iya shallake kwanakin bikin yadda har za’a iya aura masa Husna baya nan kamar yadda aka aura masa Salma ba ya nan. Hankalin Salma da Sa’a a matuKar tashe yake da wannan, babu irin shan kai da shan cikin da Sa’a ba ta yiwa Alhaji ba don ganin ya soke auren nan amma sai ya ce mata shi fa ba Karamin mutum bane, ba zai yiwu mutane na ganinsa da daraja yaje ya tarbuda ta Kasa saboda jita-jita ba. Har ya Kara da cewa, .
Jiyan nan da safe fa abokinsa ya zo ya same ni dangane da wajen da za’a sa Amaryar, yayi min bayanin ccwa Adamu ya bar Sallahun a umarci Salma ta kwashe shirginta daga wadannan empty din dakunan” Wannan ya sanya Salma da Sa’a suka sake bazama.gidan bokansu wanda nan take ya tabbatar musu lallai za’a daurawa Adamu aure, amma su sha kuruminsu a ranar da ya dawo zai saki matar.
Sannan ya Kara da basu wani magani da zasu saki


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 4 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...