NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI                Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA

na fahimce ki, so kike ki ga shi ya dakeni tunda dai kin san ai daga baKar magana sai duka ya rage..." Yana dab da ficcwa ta daga murya, “Au ni shi nc ka gasa min baKar maganar?”, Bai sake cc mata komai ba ya fice. Ita kuma bata yi Kasa a gwiwa ba ta janyo waya ta shiga kiran Salma. 

SKECKKEKEKERKER . 

 Tun daga wa’azin tsakar dare da Adamu yayi wa Salma ta zama cikin rashin sukuni da tashin ‘ hankali, ta dai zaro jikakken goronta na fitsari ta ~ shaya a rana, zuciyarta cikin Kila wa Kalancin yin @ maganin ko barinsa, duk da dai son Adamu ya cigaba da ninKaya a doron zuciyarta yana ta shardanta mata abubuwa marasa dadi da zata dinga gamuwa da su. matuKar a zamanta da Adamu ta guji ‘sthirin. bokanta. Ba ta yaudari kanta ba tana da tabbacin wa’azin Adamu ba zai hana shi Ketare dokar Allah shi ya ci zalinta ba. Tun tum ta san Adamu malami ne mai kai kuka ga Allah, amma Karfin imaninsa bai kai matakin hana shi sabo ba, sannan ko yana cikin sabo in ya ga mai irinsa yana iya toshe kunya yayi masa wa’azi. . Tana ta harkokinta a cikin gida cikin sanyin - jiki har lokacin da ta dora girki.sai ga kiran Sa’a a 

 ZAMU TASHI 

“Wai kuwa Salma in tambaye ki, anya kina amfani da sihirin boka yadda ya tsara miki kuwa?”Hantar Salma na kadawa tace, Meya faru Anti?” cikin Kufula Sa’a tace, “Tabarar da Adamu ke miki gaskiya da maganin boka na ratsa shi bai isa yayi ba “Me ya faru ne Anti?” Kai tsaye Sa’a ta amsa, Ni ba zan iya kawo Www.bankinhausanovels.com.ng miki labari duka ba, muhimmi dai a ciki shi ne, jiyan nan ya kai wa matar da zai aura kudi har dubu dari biyu da hamsin a , -matsayi, kudin kayan lefenta, ni kuma yanzu ya gama baibaye ni da bakaken Maganganun sonta da yake... “ ° Salma ta rasa kaimar zaba bayan, “Na shiga uku”. Cikin hanzari Sa’a tace mata,,Ki yi sauri ki aiwatar da maganin nan da boka ya baki, inba haka ba gaskiya kashinki na dab da bushewa...” Salma ta fashe da kuka gabadaya,


Sa’a tace,
“Ba kuka zaki tsaya yi ba, lallai ki ki hada masa wannan maganin, ba ki da wani isasshen lokacin nuna kuka da damuwa™A rude Salma ta shiga bawa Sa‘a labarin yadda suka yi da Adamu na maganar ya ga wata makusanciayarta a gurin da bai kamata ba, har ma da irin wa'azin da yayi mata. . Sa‘a ta yi mugun kaduwa, harshenta har sarkewa yayi tana cewa,
Allah dai ya tsine wa wanda ya ganni ya kai masa labari, kin ga kenan nima komawa gidan bokan ya zame min dole ko don a rufe masa baki, amma da gaskiya na fara tunanin canja malami”Www.bankinhausanovels.com.ng
Salma na kuka tace“Don me Anti?”. Sa’a ta amsa, “Wasu maganganun banza da kallon banza naga yana neman kwaso min Salma ta dage ta dan saki wani nishi, kawai, don ita dama can bokan bai kwanta mata ba, duk take-takensa a idonta yake, don dai tana ganin ba ta da wani zabi bayan wannan. Sa’a ta ajiye waya bayan tace mata,“Sai ki zama cikin hankalinki kafin kwabar taki ta yi ruwa”. Ba ta jira cewarta ba ta kashe wayar. Salma ta tashi cikin azama ta doshi goronta da ke shanye a rana ta fara juya shi, tana jin tamkar zuciyarta ta faso Kirjinta ta fito.

******

Husna yarinya ce amma mai halin manya ta hanyar tattali da hangen nesa, wannan ya sanya ta dauki kudin kayan lefen nan nata cancakat ta saida zinaran da take da su wadanda suka doshi dubu dari biyu, ta tashi dari hudu, ta ware dari uku ta sayi sakan new din adaidaita sahu ta bayar haya,Www.bankinhausanovels.com.ng ragowar dubu darin kuma ta dan sai zannuwa da takalma da mayafai daidai talaka irinta. Dama macace mai zafin nema, don haka ba ta da matsalar sutura, kusan kullum a cikin dinki take, ta san ba zata sami matsalar sutura a gidanta, ko ma akwai matsalar tana ganin tunda zata cigaba da sana’o’inta ai sai ta dinga siye a hankali. Kodayake su kansu zinaran da irin wannan tattalin ta tara su, tunda tana sana’a tana samun kudi maraicinta ke yawan fada mata tanadi don matsalolin rayuwa na bagatatan.
Ga mahaifinta mai zuciyar gaske, wanda ya dade yana tanadin aurenta, hakan ya sanya yayi mata komai iyakar Karfinsa wanda in bata hada da fariya ba lallai abinda yayi mata sun ishe ta rayuwa.
Bata Boye wa Adamu cewa siyayyar da ta yo ba na duka kudinsa ba ne, har cikin gida ta ja shi ya ga kayan sannan ta dora masa bayani da cewa,
Amma fa Adamu ba duka kudin nan na kaso ba, na dan rage na yi wata sabgar da su”. Adariu tsakaninsa da Allah ‘ya ‘amsa mata, Karki damu ni mai son abinda zai faranta miki ne  da inada wasu kudin da saina baki ki cikashe siyan abubuwan da baki kammala ba
Ta gitmrgiza kai da sauri babu bukata, na siya komai daidai misali’ yace mata To haka ake so
Sai tayi tsuri tana'kallonshi lokaci guda kuma tana tuno mugun fatan da matar babanta ta dinga yi mata, wai Zaibi ba’asi kuma_ ransa ‘zai-iya' Baci ya -
dinga zarginta da ‘rashin ‘riKe? amana,’ “harma da Www.bankinhausanovels.com.ng ci mata alwashin wai taga auren da‘ ya fasu‘saboda irin — _ wannan, wai akan zambar kudin ‘’anko ma ya fasa. Duk da taci mata layar dangantakarta da Adamu tafi karfin‘ wannan cikin tsoro°take tana ganin zai iya Zargin nata musamman saboda Kugiya bokanta yasa ya janyo mata shi-bashi'yayi Zuwan "kansa ba, bugu da kari bokan nata’ dai yace mata akwai matsala a kwance, “wanda tun daga'ranar-da ya fada mata bata sake barci ba“kullum tana tsayuwar dare fadawa ubangiji‘tare da nacewa azkar Sai “gashi* kuwa ‘Adamu_. yaba‘ maradanta kunya, yace babu komai harma da fadin ‘idan yana da wani kudin zai kara mata.Waime kike tinawa?”
Ya farko da ita daga tunanin daya lura ta lula.
Da sauri ta kada kai tana dariya, “Ina ta fatan ya zamana uwar gidanka na da sauKin kai yadda zamu zauna lafiya, ina sonka saboda haka bana son duk wani tashin hankali ya biyo ta kusa da kai Sai da yaji dacin rai da ambatar Salma a matsayin uwar gidansa har sai da fuskarsa ta nuna, ya kawar da kai yana dan mazewa, “Nafi son ki dinga tuna ni ni kadai, kowa ma karki tuno shi Husna”tana dan zura masa idon nazari tace, Ina KoKarta hakan Adamu, na fada maka wannan ma na tuno tane don ina son ka zamana cikin farin ciki ko yaushe”Ya dago yana dariya, ‘
“Zan zamana mana, in dai kina kusa da ni tunda ke ce farin cikina, ni idan akwai ki duk wata hayaniya Www.bankinhausanovels.com.ng dazun ce”.
Husna sai tayi shiru ta kasa magana saboda dadi, Adamu ya gama biyanta, ya iya samar mata abinda ta fiso, wato Kaunarsa da kulawarsa. “Zan dan yi wani balaguro na sati biyu, me yiwuwa sai ana gobe auren mu zan dawo ko ma ranar daurin auren”. Husna ta cika da damuwa nan take, “Subhanallahi, ina zaka je haka Adamu?”Ya dan jima yana kallonta saboda yadda ta damu, “Ke kuwa ki kwantar da hankalinki mana, Umara zani”Ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana kokarin shanye damuwarta. ,
Shi ma Adamu ya kasa magana, ya tsaya yana kallonta kawai, har lokacin da don kanta ta bude fuska tana ajiyar zuciya tace, Ina da buKatarka a kusa fa Adamu, me yasa ka tsara tafiyar nan daidai wannan lokacin?.“Kin fi so sai an kai min ke zan bar ki jiran gida na tafi?”. Ya fada cikin zolaya. Dayake har yanzu tana cikin damuwa murmushin yaKe kawai tayi, bata kuma da alamar tankawa.
Ya lura cikin damuwa take sosai, don haka ya tattara mata dukkan kulawarsa,Duk wanan damuwar wai ta meye? In ba kya son tafiyar zan iya fasawa”.Ta kada kai kawai, nan ma ba ta yi magana ba. Ya Kara dagewa da kallonta shi ma nasa ran babu dadi, ya fara jin haushin Salmanu wanda ya aika masa tafiya makkan da bai shirya ba sai ka ce ana Www.bankinhausanovels.com.ng neman kai da shi.

************

Al’amura sun cigaba da tafiya yadda suka samu, ta hanyar wasu kostomomin nasu fasfot din Adamu ya zo musu da sauki, Honorable kuma dama shi ne me biza da kudin guzuri. Saboda haka komai na shirin tafiya ya kammala rana kawai suke jira.
Zuwa wannan lokacin buKatun Honorable sun cigaba da biya, shine dan takara a jam’iyyarsa kuma, yana cigaba da samun magoya baya.
Salmanu .mutum ne mai basira, ya tsarawa Adamu tafiya ne don yana tsammanin lallai kafin bikin su Salma zasu iya wani yunKurin na juyawa Adamu kwanya ya bijirewa auren Husna, da wannam zaton yake kwana yake tashi har kawo lokacin.da mai aukuwa ta auku.Ya rage kwana uku tafiyar Adamu ya tashi da ciwon ciki, wannan ya hana shi doka sammakon da "ya saba na barin gidan, ya zauna yana faman jinya. Da hantsi Husna ta kira shi, ba tare da wata  shakkar ba a gaban Salma ya daga wayar, ’ Cikin damuwa Husna tace, Lafiyarka kuwa na ji muryarka a birkice?”. Ya amsa mata,
Na tashi da ciwon ciki Husna, amma kar ki damu”. —
Kamar Husna zata yi kuka tace, Ayya sannu Adamu, don Allah tashi ka je asibiti, zan zo na samcme ka”.
Yayi matuKar jin dadin kulawar Husna, don Salma dai ba ta ce masa ya tafi asibiti ba sai faman jika masa wani farin abu take, tace sunansa dutse dan libiya. , Dayake Adamu gabo ne ga Salma a gabansa amma bai ji kunyar keta idonta ya amsawa Husna da cewa,
“Kar ki damu: Husna, wannan matar ta jika min, wani farin abu tace min wai maganin ciwon ciki ne zan jira minti goma haka in bai lafa ba zan kira ki mu hadu a asibitin”,Husna ba don ranta ya so ba tace masa,
To don Allah Adamu kar ka yi wasa, in ba hali kawai ka fito kaje asibiti, meye wani jiKe-jike sai ka ce a Kauye”.
Adamu yayi kasa da murywa wadda Salma ba ta kasa jinsa ba yace, _‘Nima ‘abinda na gani kenan, ba dadi kana wani hali mutam ya kawo maka taimako ka gwale shi’, Suka yi sallama da Husna ya sauke waya ya duKa ya cigaba da murKususunsa, ya bar Salma Www.bankinhausanovels.com.ng tana iyakar shaKar haushi da tashin hankalinta.A yau ba ta iya sarrafa fishinta ba sai da taji  babu wata mafita sai wadda ta hana kanta, wato dankarawa Adamu maganin bokanta, don haka ta ‘-shanye haushin da ya bata ta cigaba da bashi kulawa, Karshe dai ta ba shi ruwan shayi mai dauke da maganin da ya sha surkulle iri-iri daga kan goro wanda ya tsumu a fitsarinta zuwa faratanta da gashi wasu sassan jikinta, ban da garin maganin bokan wanda shi kansa ba ta san da me aka hada shi ba. Ta san wannan zunubi ne mai girma, shiyasa tun tuni take gudun aikata shi, to kuma ta fahimci in babu shi din duniyarta ba zata zauna lafiya ba, Kila ma wataran lakace mata hanci Adamu zai sa Amaryarsa ta yi mata. “Adamu dai yaci magani, da alama kuma - wasan zai canja.

*********

Washegari su Salamanu sun zaci yau ma ciwon cikin ne ya tsayar da Adamu ya hana shi zuwa, suka dinga kiransa a waya bai dauka ba. Ba su daga hankalinsu ba sai suka cigaba da sabgoginsu. -Jummai ta zo'da albishir din ta saki mijinta, yana kuka yana komai ya rubuta mata saki uku, yanzu haka tana gidansu.
Boka Salmanu ya shirya mata wata gadar zaren, _
To yanzu kin kamo hanyar zama attajira  sai dai ban sani ba in dai kina da toro da kyar zaki iya”. Da azamarta tace Bani da tsoro Malam, ko cikin kabari aka sa ni zan kwana" Salmanu yace,
“Yauwa Alhamdulillahi, ashe komai ya kwana gidan Www.bankinhausanovels.com.ng sauki".A nan yayi wa Tanimu mai muryar aljanu inkiya. Babu zato babu tsammani Jummai taji dakin ya gure da wata irin Kara bayan Kamshin da ya cika  dakin. Karar na wanzuwa Salmanu ya rage murya ya ce mata, “Sarkin aljanun Darkis ne ya zo da kansa,
Lallai kina da sa’a” Jummai ta gyara zama tana Kara cika da farin ciki.  Aljani Tanimu ya fara magana a Kasaice, “Hajiya Jummai barka da KoKari”Jikinta na Bari ta shiga amsawa, “Barka kadai ranka ya dade, ya naku KoKarin?” Ya sake shan Kamshi sannan ya amsa, Albamdulillahi, yanzu haka ana gudanar da babban taro a fadata, amma muhimmancinki ya—sanya dole ta karkade komai na taho don na shiga lamarinki Cike da jin dadi Jummai ta amsa, “Godiya nake ai tuni Malam ya sha sanar da ni Kaunarku gare ni”. “Wannan gaskiya ne”. .
Inji Sarkin aljanu, ya sha Kamshi sannan ya dora,
“Akwai wani gwamnan aljanu* da taurarinku suka zo daya, gaskiya shine mahadin arzikKinki, zaki zama attajirar da dukkan attajiran duniya sai sun yi daidai da barorinki”Kan Jummai ya Kara kumbura, ta ji kamar ta tashi ta kwarara ihu, ta kasa magana yanzu sai gyada kai kawai take. Aljani Tanimu ya cigaba,_“Amma dai kin sha jin aure tsakanin bil _ Adama da mu jinnu ko?” . Tsakaninta da Allah ta amsa, “Ranka ya dade na sha ji, ko wanda suke ' shiga jikin mace su aure ta ko kuma wasu attajirai da sarakuna da na sha jin ance suna da mata aljanu”.
Aljani Tanimu ya tare ta, Yan yan yan! Ba wancan Razantaccen auren na ‘yan fashin aljanun da ke shiga jikin mace nake nufi ba, su wannan ko a wajenmu mu jinnu masu doka da tsarinmu na Www.bankinhausanovels.com.ng musulunci ai tsinannu gafalallu muke kallansu, ni ina magana ne a kan wannan kashin aure na biyu da kika sha ji tsakanin attajirai da sarakuna..” A sanyaye Jummai ta kada kai, Oh na fahimata”, Aljanin Tanimu yace, “Yauwa! Ai shi wannan auren sai mutum ya Kasaita yake yin sa, kamar dai ke din nan”Jummai ta sake kada kai, murna da dan tsoro na zagaya kanta.
Dakin ya jima shiru, sai can cikin kakkausar murya Aljani Tanimu yace mata, “Zaki auri shi wancan Gwamnan Aljani, nan da sati biyu zai zo ku gana, zai ‘taho miki da kudin « aure milyan hamsin, na bar ki lafiya”. Sai Jummai taji Kit! An datse hayaniyar da ta cika dakin hade da muryar tasa, Kamshin da ya cika dakin kuma ya fara raguwa. Boka Salmanu ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya yana dubanta, Gaskiya ke mutum ce mai sa’a”. Jummai ta kantamo murmushin murna dana yaKe ta gwamutsa, muryarta na rawa tace, “Boka ta yaya wannan lamari zai yiwu?” Salmanu ya kawar da kai yace, “Ai ba dole ba ne, na sani zabi ya baki, in ba kya son kudin ai zaki iya fasa auren”.


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...