NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


                  Www.bankinhausanovels.com.ng 


 

MUN TSAYA 

Akwai wata makusanciyarki da aka gano min ita a wani waje da bai kamata ba, lallai ni dan adawa ne da irin wannan lamarin, duk wanda bai san fishina ba zai iya ganinsa a nan bangaren, don haka.nake ba ki shawarar ki bi hanyar da na bi, ita zata bulle da ke, duk duniya ba shegen daya isa siyo maka soyayyar wani kuma ba shegen da ya isa hana abinda ubangiji ya hukunta, in ba ki sani ba ma ki sani, yawancin malamai da bokayen daga ‘yan iska sai yan damfara, sai kuma wadanda suke nesanta mutum da rahmar Ubangiji fau-fau!”. - Bai saurari cewarta ba ya kada kai ya fice ya bar mata dakin. Www.bankinhausanovels.com.ng
-Sai ya barta.da jirin da ta ji yana neman kwada ta da Kasa, da Kyar da jan gindi ta ja kanta ta leka KarKashin gadonsu inda ta gano ludayi.: .dumanta yana nan zaune inda ta bar shi, ba shi Adamu ya gani ya janyo mata wadannan ayoyi ba da gaske Anti Sa’ar aka gano masa? Sun shiga uku sun lalace!.

ZAMU TASHI 

Salmanu bai yi bacci yadda yakamata kamar yadda ya saba a darcn wannan ranar ba, lallai yana zargin faruwar wani abin tsiya a duniyar Adamu da Husna tunda aka ga Sa’a a gidan boka, wanda ba ya tantamar cewa Salma ta jewa Da haKurinsa ya kasa daukar wannan, lissafinsa kuma ya kasa samun mafita safiya na yi ya buga sammako ya tafi gidan wani. shaihinsa a unguwar Malfa, bai yi Kasa a gwiwa ba ya kwance masa dukkan labari tare da neman daukinsa. Malamin ya ba shi shawarwarin da zai kai wa Adamu na rike azkar safiya da yammaci, ya kuma ba shi wani adadi na Hasbunallahu da zai dinga karantawa Www.bankinhausanovels.com.ng kullum, daga karshe kuma ya hada masa — da takardun da aka rubuce ayoyin karya’ sihiri wanda za’a_ je a karanta a ruwa a hada da ganyen — magarya a

dinga sha ana wanka..Har sha biyu su Adamu suna jiran zuwan Salmanu amma bai bullo ba, an kira wayarsa kuma a kashe abinda ya dame su kenan, musamman da yake suka dinga yawan samun baKi, ciki har da Innar_ ' Salmanu wato matar Babansa da kuma Honorble da ya zo da albishir din an soke takarar dan adawarsa an mayar kansa. Suka dinga sallamar mutane da_hanzarin Malam ba ya nan, amma dai sun zaunar da Jummai ta yi jiransa har zuwa lokacin da zai dawo. Karfe daya ya dawo musu jiki a sanyaye, gashi kuma kasancewar juma’a ce babu ishasshen lokacin tuhuma sai kawai suka yi shiri suka tafi masallaci da zummar sai sun dawo ya sha tuhumar. A masallacin ma sai da ya rada wa Adamu, ~
Adamu duk mu biyun nan ni da Tanimu ka fi mu rauni, ka fi buKatar neman tsari a ahalin yanzu, ina tuna maka cewa duk wata dama ta nuna wa Allah buKatunka kar ka yi sakaci da ita”. Sai da Kwalla ta taru a idon Adamu, bai boye abinda ke ransa ba yace,Ka damu da ni Salmanu”.Kai tsaye Salmanu ya amsa,  “Ba ni da wanda ya fi ka Adamu”.
Da suka dawo gida, maimakon tuhumar inda Salmanu ya bace tun safe sai suka fada aikin Hajiya Jummai. Ta kawo cikon kudin aikinta dubu ashirin cas! saboda haka Salmanu ya karkace ya shiga sheKo mata bayani ta sigar tambayoyi, Wannan da kuka zo tare mijinki neko?” Hajiya Jummai ta muskuta cikin Barin jiki ta
“Shine‘ Salmanu ya shiga girgiza kai da fuskar alhini,
“Amma dai na yi mamaki gaskiya,..”, A dan tsorace Jummai ta ce, “Me nene Malam?”, : Salmanu~yayi. dum! Alamar abinda zai fada mai girma ne, “Kodayake ba’a mamaki a cikin lamarin mutane. Wanda ba ka zaci makirci tare da shi ba yawanci shine makirinka”. to Yanzu ba jikin Jummai ba, hatta zuciyarta bugawa take. Ta Kara muskutawa tana Kara Www.bankinhausanovels.com.ng tattara dukkan hankalinta ga Salmanu, _ “Na shiga uku, kuma na shiga duhu Malam”’. _ Kai tsaye Salmanu ya amsa mata, ' “Gaskiya duk wata naKasun rayuwa daga - wajensa kike samu, kina da Kashin arziKi taraiyarki dashi ce take tarwatsa miki albarka” Rangwada kai kawai Jummai take babu bakin magana.“Aji ba ki haihu da shi ba ko?”. : “Haka ne Malam”. Ta amsa da sauri_“Shi kuma yana da da guda daya kacal ko?”. - Nan kuma jikinta a sanyaye ta kada kai. . “Kuma a idonki ya sha nuna miki ba ya - Kaunar wannan dan nasa ko?” Muryarta na rawa ta Ce, , *Tun da na fahimci ya fiye son dan na shiga
na fita na raba su, ko sunan dan ba ya son ji...” . - Salmanu ya tura mata ashar a zuci amma a fili sai ya tare ta da Karamin murmushi, Matsalar kin fada hannun Malaman da ba su gama gane kan aiki ba, mijinki ya dade yana yaudararki ba ki sani ba:“Jikina ya bani tun tuni”. . “Ki bari na dire mana”. ' . Tayi saurin riKe lab6anta tana yi masa alamar ' ban hakuri, shi kuma ya gyara zama ya cigaba da bata bayani. “Maganar gaskiya mijinki yana nan maKare da Kaunar dansa, lamfa yayi miki yana nan da aniyar " tatse ki ya azurta dansa...” Arikice tace, . “Yi haKuri Malam ina katse ka, wallahi ban gane bane”. _
“Niyyar mijinki ita ce, saiya gama azurta kansa da ke sannan zai fita daga rayuwarki ya gayyato dansa su ci tare, yadda zancen yake shi ne akwai sa hannunsa a wajen batan kayanki a hannun jami’an kwastam, daga baya zai koma ya karbe ya adana a asusun da ya bude da sunan dansa”. Ta dafe Kirji ta zaro ido. ‘Salmanu ya sake kicin-kicin ya cigaba,__. “A takaice dai ba taurarinku daya ba-da mijinki, in kina tare da shi ba zaki taba arziki ba, Www.bankinhausanovels.com.ng
sannan shi kuma akwai wata nufaka a zuciyarsa game da ke, wannan ne dalilin dayasa na yi dabarar cewa ki dawo yau don ba zan iya cin fuskarsa in fada miki gaskiya a gabansa ba... amma dai gaskiyar kenan, ina horonki da gaggauta rabuwa da shi sannan ki zo mu zuba sabon aikin da zaki zama Kasurgumar attajira”. Jummai ta rasa abinda zata cafka ta ce shi ya fi girgiza ta, zamowar mijinta da ta mayar sakarai cewa shi je ha’ininta, ko kuma arzikin da ke jiranta nan gaba? Duk ta hada tana ji da su, don haka lokaci - guda ta shiga yi wa Salmanu sambatu,
“Ai yau din nan ba gobe ba Malam na gama auren Salisu, wallahi komai tsiyarsa da nacinsa sai ya sallame ni a yau din nan”. :
“Ki KoKarta ki yi hakan, shine hanyar - gayyato da arzikinki cikin gaggawa’”.Ta mike cikin barin jiki, . .“Bari in tafi a yi ta ta Kare Malam.' Ya dakatar da ita, _ “Ki dakata akwai sharadi”’. . Ta sake zama da sauri, - ; “Zaki Boye dukkan yadda muka yi da ke ga kowa ciki har da shi mijin naki, dalili, rauhanan da suka sa mana hannu a aikin jinsi ne da ba su Kaunar yamadidi da abinda zai kawo koma baya, sun shaida mana mijinki hatsabibi ne yana da nasa malaman na  musamman da suke masa aiki kanki, zasu iya sanya hannu wajen kawowa aikinki tsaiko, don haka akwai bukatar ki dan dakatar da bakinki har zuwa lokacin da zaki fitowa jama’ar gari a attajirarki, lokacin ko matsayin abin kwashe shararki mijinki bai isa ya kai ba”. ‘An gama ranka ya dade, wallahi babu mai ji’Yauwa kije kawai a cikin irin dabarun nan naku na mata ki nemi yayi miki saki uku rus! Kar ki sake ki yarda ya gano lagonki, in an yi sakin da kwana bakwai ki zo ki same ni”Tana ta zura godiya ta fice da rawar Kafa. A guje su Adamu suka fado dakin suka zo suna dariyar da suka saba. Amma dai daga bisani Adamu ya ce,“Salmanu ka yi abinda bai kamata ba, wato kashe aure”.“Wannan shi ne burina na farko a rayuwa, na sami cika shi da izinin Allah”. Salmanu yayi fuska ya amsawa Adamu. Tanimu yayi Www.bankinhausanovels.com.ng saroro yana kallonsa, sannan yace, Burinka shi ne abinda bai kamata ba Salmanu? Komai tashen balaga fa yakamata a dinga rage wasu abubuwan’’Idanun Salmanu suka ciko da hawaye “Kuna son in fada maka Karya kenan? Kune a wajenku raba wancan banzan auren bai kamata‘ba, amma ni a yanzu ban ga abinda ya kai shi kamata ba, duk wani aure mai zalinci ni mai adawa da. shi ne, Jummai ba Zata shiryu ba, don haka dole ne na raba ta da ubana dan na katse-cutar da take masa’ Jikin Adamu a sanyaye yace-“Mu bar maganar, wai. ina ka shiga ne tun safe?” “Asibiti naje bana jindadine tab“Kai ne kake wani. zuwa-asibiti idan ba ka da lafiya?”’_Tanimu ya tambaya. Salmanu ya amsa da cewa,,“Shikenan idan kuna tuhumata da wani ha’inci sai kawai ku dau mataki, akan. me za’a.iskeni ni da tambayar ina naje?"SarKa mai rikicin gangan kenan”inji Tanimu amma-‘Adamu shiru yayi yana jinsu, yana da tabbacin -lallat akwai wani abu. da Salamnu ya boye musu Suka bar maganar suka shiga-kasafin kudade kujerar makka.  Salmanu nada nasa.tanadin akan?’ kujerar -makka don haka shi ya kawo nasa kasafin, Mu na da tsurar kudade har kusan-dubu dari - hudu, me zai hana a kasa su biyu, daya cikinmu ya dau kujerar makka, biyu kuma su raba kudin?”Duk suka yi shiru suna canke-canke suka bar Salmanu da bugun zuciyar Allah ya sa kar Tanimu ya zabi kujerar makkan ya bata masa shiri. Can kuwa ga fargabarsa sai gashi Tanimu ya fara daga hannu, Salmanu ya bishi da kallo cikin dukan zuciya. Ni na fi-son kudin, ina da kudurin siyan mota kafin naje umara na dawo na dinga rigima da dangi akan tsaraba”,Salmanu ya sauke ajiyar zuciya ya zarce da dariyar jindadi, ‘Amma yanzu ka gama yi min maganar komai tashen balaga yakamata mu dinga Www.bankinhausanovels.com.ng rage wasu _ -abubuwan...”. ~ Shi ma Tanimu na dariya ya tare shi, “Kai wai ba ka fahimtar al’amura ne? don fa kar ka Kalubalance ni ya sa na hada maka da hujja”Salmanu ya sake murmushi ya dubi Adamu wanda yayi.zaune yana kallonsu kawai, -Shikenan kawai sai Adamu yaje makkan, ni ma kudin nake so”. Adamu ya zabura, A’a wallahi ni ma kudin nake so...”.
“Kai Adamu, a nan ma kai me son Allah ne sai kuma ya kira ka dakinsa ka Ki zuwa?”. In ji Tanimu. Salmanu ya.ce, “Kyalc soko...”. . Adamu ya shiga girgiza kai, “Duk na fi ku buKatar kudi, ni hidimar aure a gabana, sannan bugu da Kari in zaka je gaban Allah -
ai sai, ka je masa ta tsarkakkaiyar dukiya, ina jin
kunyar Allah na je dakinsa da kudin damfara...”. Salmanu ya tare shi da zafin rai, Menene Kazantar a hanyar da ka bi ta zuwa makka? An haye kane kaje ka yi addu’a don haka in kaje sai ka yi addu’ar, Allah ga Honorable, in yana da Alkahiri Allah ka bashi kujerar da yake nema, in kuma babu alkahiri Allah ka zaba masa . abinda yafi alkhairi ka kuma zabawa jama’ar Kasa_ shugaba nagari, shikenan fa ka ci kudinka, to kokawa aka ce ka je saudiyyar ka yi ko yankan aljihu?” .Nan da nan Tanimu ya shiga hayaniyar goya .baya. Adamu kallonsu kawai yake yana murmushi, sai da suka rage hayanya sannan ya tanka, Kun turbuda buKatar kudina saboda zan yi . Aure a Kasa Tanimu, ita ma muhimmiya ce Salmanu, ai da ba ka da nauyin kowa kai yakamata kaje’Yana rufe baki Salmanu ya masa, “In dai buKatarka ta kudi ne nawa kudin aikin me suke da ba zasu yi maka rana ba’? Lallai ni ba ni da buKatun da suka fice ci da sha da yan suturu, in dai zan sami dan na busa sigari...”Farin cikin na tseren zagaya Adamu ya kai wa Salmanu mangari, Au sigarin da ka sha daukar min alkawarin zaka daina sha ko ma ka daina?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na dai san nace ka ba ni lokaci zan fara da ragewa, da kwali biyu nake sha a rana amma yanzu kara biyar ma na gamsar da ni”.Tanimu tsayawa yayi kawai yana kallonsu, abotarsu da sadaukarwarsu ba Karamin burge shi take ba. Kodayake ya kula an hada masu amana da rashin Kyashi biyu ne shi kansa da yazo musu daga baya suna Kokarin mayar da damuwarsa ta zama tasu, ya koyi darasi a zama da su sosai, kuma ya sha rayawa a ransa duk da sun zai shiga turbar mutanen banza, sun sami abubuwa dayawa wadanda suke na mutanen kirkine.
Sun dan yi caftarsu.kamar yadda suka. saba sannan suka sha wanka suka fice
Akwai shirin zasu je wajen Husna amma sai sun fara kai wa Hajiya da Alhaji ziyara an yi shawarar yadda za’a kai lefen Husna, kudin za’a kai ko kayan? ,
Hajiya na ta ina ka saka ina ka aje da baKinta Adamu da abokansa. Hajiya na matukar son Adamu, shiyasa duk abinda ya dangance shi take jarabar so. yadda take tattalinsa haka ta dinga tattalin salmanu da Tanimu. Shi ma wannan duk tare kuke aikin ginin?”,
Ta tambayi Salmanu da Adamu tana nuna Tanimu. -
Adamu ya so ya manta Karyar aikin gini da yayi don haka yayi saroro yana kallonta kamar ‘yadda Tanimu da bai san kan garin ba yayi saroro _ din, sai Salmanu ne yayi saurin kada kai yana_. amsawa, duk tare muke”,
Adamu yayi ajiyar zuciya bayan ya tuno inda gizo yayi saKar.Allah sarki Hajiya, duk da maganar ba ta  gama ratsa zuciyaria ba haka ta kada kai ta shiga kwararo musu neman albarka wajen ubanguji, don ta san lallai babu abinda suke buKata sai ita, ko wacce  irin jumurda suke murdawa in ana nuna wa Allah su zai iya warware ta ya shiryar da su hanyar da ta kamata. Don wannan ba ta bacci ba ta hutawa, tana cike da sa ran ko a ina Adamu ya salwantar Www.bankinhausanovels.com.ng lokacinsa da biyayyarsa ga Allah, Allah take roKa ya dawo mata da shi hanya madaidaiciya. Salmanu ne ya kwaso zancen kayan lefe ya kawo mata, , “Kayan lefen da za’a kai wa Husna, shin ke zamu bawa kudin ki siyo ko kuma shawartar Alhaji zamu yi? Mun so zuwa mu siyo sai muka ga in mukayi hakan Kila ba zaku ji dadi ba”Hajiya na bayewa tana matsar hawaye na dalilin rashin sanin inda suka samo kudin, ta amsa Masa, gara da kuka yi azancin kawowaba ni banida matsala, amma su Sa,a Kila ransu ba zai so. ba, alhalin Kan harkokinmu, saita ga kamar dalilin _ Salma ake baya da ita”tunda dai ta ambaci Sa’a daga Adamu_ har * Salmanu suka Kule, don haka cikinsu babu wanda ya - ’ sake tankawa kan maganar lefen har suka yi sallama da ita suka tafi gidan Alhaji... . A hanya Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu yake cewa,“Adamu akwai yiwuwar fa mu fasa bayar ‘da_ kudin nan, in dai akwai Sa’a cikin manunar nan to ni kam hankalina bai kwanta ba" Adamu yayi shiru yana nazari, shi ma dai ya _tsani Sa’a Kila fiye da yadda Salmanun ya tsaneta, don dai kawai bai kai Salmanu nuna zara bane. Ai kuwa, suna kawo wa Alhaji maganar ya gyara muryarsa yace - ku bayar da kudin sai a bawa Sa’a ta siyo, na Salma ma ita ta siyo komai

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 4 CHAPTER 1 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...