NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Salmanu na gefe yana yi masa jinjina, wannan ne ya sanya shi Kara Bata murya ya ce, “To kar ki je ko ina, na fasa_ barin unguwar’. . Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin fargabar abinda hana ta fitar zai haifar mata ya biyo baya, kar ta fita ta je gidan bokanta? Abinda ba zai yiwu ba kenan. Ita ma ta dan bata rai ta ce, “Gaskiya Yaya Adamu A’a, har fa na yi waya da su gwaggo, suna nan suna ta shirya gangamin hidimar zuwana...”.
Dayake wayar Adamu na da Kara, Salmanu_. yana jiyo abinda Salma ke cewa, don haka yake ta yi wa Adamu inkiyar budewa Salma wuta, Adamu kuwa ya tunzuru, don haka ya iya tare. Salma da baKar magana, In don abincin da zasu shirya miki ne. wanda ba kya cin irinsa a nan gidan, idan na taso daga sabgata na biya gidan gwaggon na taho miki da shi, ai zasu ba ni ko?”. Mamaki da haushi ya Kara turniKe Salma, . bakinta na karkawa ta ce, “Gaskiya sai na je Yaya Adamu”.
Salmanu ya buga tsalle ya dire can gefe yana cewa, . .“Maca ce take fada maka haka Adamu?”.
Maganar Salma ba ta tunzura Adamu ba sai da Salmanu ya zuzuta ta, muryarsa na sarKewa

ZAMU TASHI 

ya cewa Salma. Shikenan, idan kin je can sai ki cigaba da zama a can”. Bai jira cewarta ba ya sauke wayar, bai ankara ba sai jin Salmanu yayi sama da shi yana ihun jinjina masa. a
Salma na tabbatar da Adamu ya kashe
waya bayan fada mata wannan maganar da bata yi mafarkinta a tsawon rayuwarta da Adamu ba, hannu ta dora a ka tana kuka tana bude kofar falonta tana shigewa -cikin falon tare da neman Www.bankinhausanovels.com.ng wayar Anti Sa’a don ta fada mata yadda kwabarta ke cigaba da ruwa. Anti Sa’a na jin maganar ita ma hankalinta ya tashi, ta dinga rusawa Husna zagi tana cewa ita ce ta Kundumo musu asiri. Daga Karshe dai Www.bankinhausanovels.com.ng 
dole suka rungumi Kaddara suka hakura da zuwan da zummar cewa sai an shawo kan Adamu ya yarda da fitar. Salmanu na cikin kakabin murnar jinjinawa Adamu suka hango baki na shigo musu Kofar gida, a guje suka kwasa cikin gidan ta baya don boka Salamanu ya shimfida shigarsa ta badda sawu. Tanimu ne me lura da baki, ya isko su Salamanu a gigice cikin tsanani kaduwa da damuwa, yace“Ku abokai kun san bakin da muka yi yau_—. din nan kuwa?”. Duk suka ba shi

hankalinsu don basu ga alamun wasa tare da shi ba, Adamu ne yace,“Su waye?”. salmanu girgiza kai kawai yayi.Tanimu ya ce, “Wallahi tallahi Baban Salmanu da matarsa ne - . Dukkansu suka mike tsaye cikin tashin  hankali da tuhuma,Salmanu yace,  “Me suka zo yi? Kar dai sun gano mu zasu zama sanadin tona mana asiri, ai ko da na zama-ajalin mace wallahi”. — ” Tanimu ya girgiza kai cikin son fashewa da tsananin dariya,Su ma tasu buKatarcetakawosu” - Mamaki da al’ajabi Adamu kawai yake nunawa, yayin da cikin azama Salmanu ya mike . ya dinga runtuma tsalle yana naushin iska cikin .- tsananin farin ciki, fadi yake Allah ya kawo min . Damomihar gida. . Jikin Adamu a sanyaye ya ce, “Nama dai kawai Salmanu, duk fishin da zaka yi kar ka sa mahaifinka ciki A tunzure Salmanu ya tare Adamu, ° “Oh ba a Www.bankinhausanovels.com.ng gabanka ba ne fa Babana ya je ofishin ‘yan sanda ya saka hannun cewa ba ni bashi ko? Don ban cancanci zama dansa ba kawai don mahaifiyata ta mutu ta bar ni a raye, duk ba ka san haka ba ko Adamu? Ni na sani kuma ba zan manta ba ya tara jama’a da jami’an tsaro ya shaida musu ya yanke diyancina da shi...”. _ Adamu ya sake tare shi cikin sanyin jiki, “Duk na sani Salmanu, hakkin Allah zaka duba da hakKin haihuwa...” Salmanu ya tare, da alama yana cikin fishi, — “Adamu ka yi min shiru kar ka janyo in hada ku kai da mutanen can in kutuntuma muku ashar... kai wanne iri dan iska ne da bai san _ Www.bankinhausanovels.com.ng mutuncina ba? Adamu daga ubana har matarsa ba haka suka so in tsaya ba, so suka yi in lalace fiye da haka, ba in zauna a inuwa masoya zuciya - irinsu su zo in damfare su ba, so suka yi in rike bindiga in tare hanya in kashe mutanen kirki da na tsiya in kwace musu hakkinsu... duk wanda ya so min irin wannan rayuwar kake son tuna min hakKinsa, me yasa lokacin da ya kore ni yace na shiga duniya kai baka je ka tuna masa hakKina da hakKin Allah ba?”, . - Tanimu ma jikinsa a sanyaye yace, “Duk mun sani Salmanu, amma duk da -haka Adamu nada gaskiya...” Adamu ya tare Tanimu da cewa, “Ka bar shi, in ma ya kafe sai ya yi wa babansa ba daidai ba ni ba zan sa hannu ba...” “Ni ma ba zan sa hannu ba” Salmanu bai iya fishi ba ko kadan, mutum ne mai tsananin zuciya da Kullaci, don haka maganganun su Adamu ba su Kara masa komai_ ba sai daukar zafi, ya shiga tura musu ashar yana Karawa, daga Karshe ya KarKare da cewa,Naji kai ba zaka taimake ni ba, ba zaka sa hannu ba” Yana nuna Adamu cikin fishi, sannan ya murza hannu ya cigaba, Amma a taka sabgar ni nake uwa da makarbiya ko? Duk wanda ya nemi shiga hancinka ina fin ka jin ciwo har nake salwantar da dukkan farin cikina saboda kai ko... to wallahi na gane, daga yau ka nemi mai shige maka gaba a auren Husna...Bai jira cewar Adamu ba ya koma ga
Tanimu, .“Kai ma ba zaka sa hannu ba ko? To wallahi sai dai ka bar wajen nan ai ba da kai muka shiryo harKallarmu ba, kai in rusa tafiyar ne ma a rushe, Allah ya tsinewa tafiyar da ba zata rufawa kowa asiri ta Kwato masa hakki ba, kuma Allah ya tsinewa maKiyan abokai...”. . Bai saurari cewarsu Www.bankinhausanovels.com.ng ba ya fice daga wajen. - -- Tanimu ya dubi Adamu jikinsa a raunane, - “Haka Salmanu yake Adamu?”. Shi ma Adamu jikinsa yayi matuKar rauni, da Kyar ya iya bude baki ya ce, “Wallahi haka yake, yana da sauKin kai: wataran amma in ya murde komai ma ya fi shi dadin sha’ani, shiyasa wasu lokutan nake masa banza wallahi,;ka ga yadda ya rufe ido ya Ki _ karBar gaskiya ko? Ni ban hana ya rama akan matar kawai ba, amma kar ya cutar da babansa”. Tanimu ya dan yi shiru yana nazari. Sai can ya nisa ya ce, . , “Gaskiya nima ban yarda da wulakanta Iyaye ba, duk tambadar da mutum zai yi a duniya in dai yayi KoKarin rabuwa da iyaye lafiya yana samun wanyewa da rayuwar lafiya, albarkacin Www.bankinhausanovels.com.ng addu’arsu sai ka ga ya sami shiriya kuma ya sami babban rabo duniya da lahira.  “Maganar kenan wallahi Tanimu”. Suka sake yin shiru suna duban Salmanu da ya Kara shigowa falon, har ya cire manyan . ~ . rigunan bokancin da aka jibga masa-ya mayarda kananan kaya, ya kuma daye manne-mannen. da ‘ aka fara yi masa a fuska, alamar dai da gaske gayyar zata watse ne.Ya dauki kwalin sigarinsa da ke kan. wani....-. ° ’ tebur ya sake ficewa duk suna bin sadakallo. =~ Tanimu ya sake kallon Adamu ya ce, “Idan ya sha sigarin can kana ganin zai iya . hucewa?”. . Adamu ya girgizakai, Tanimu ya ce,“In haka ne me zai hana mu karbi tayinsa? A dabara zamu iya kawo shawarar da ba za’a cuci uban sosai ba, sai dai da yake shi ne bokan”. Adamu yace, ai “Nima tunanin hakan nake”, Da wannan suka _ yanke shawarar zuwa su sami Salmanu. Adamu ne yayi magana, “Salmanu maganar nan fa ba ta zafi ba ce da zaka yanyame mu da gori, dan kyautawa mun
san ba’ a kyauta maka ba, amma ba zai hana mu kawo tunaninmu akan matakin da kake shirin dauka ba”. . Www.bankinhausanovels.com.ng 
Salmanu ya Kura musu ido duka, “Tunaninku shi ne ku ce ba zaku sa hannu ba? Ni yadda ban iya Karanta rashin mutunci ba haka ban iya yi wa mutane halacci ba, in ku aka taba ko uban waye sai inda Karfina ya Kare...” “Eh mun gano hakan, kar ka damu ka zo mu casa su yasin”, Tanimu ya fada cikin zolaya da dariya har Salmanun ma ya dara, ya ce, Don kun ga dai na-biyo ta inda zan dake ku ku ji zafi, kai zaka koma bumburutun siyasarka, shi kuma wannan auren Husna zai masa nisa’. . “Duk mun yarda”.In ji Adamu, suna dariya su duka. Daga nan suka dunguma. suka koma ciki suka fara shirin taron baKinsu na musamman. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Da alama Salmanu ya fahimci shigo shigo babu zurfi suka yi masa, don haka duk shawarar da suka kawo game da salon bokacin da suke ganin za’a yi wa iyayen Salmanu sai ya kauce ya ce su bar shi dasu, shi ya san abinda zai musu. Dole dai suka haKura suka zuba masa ido. Karfe sha daya da kwata daidai aka shiga da mahaifan Salmanu’ gaban Salmanu, a matsayinsa na boka ba a matsayinsa na dansu ba, su kuma a matsayinsu na masu buKata, ba a matsayinsu na iyayensa ba. Da alama yau Boka Salmanu yana cikin tsananin fishi da fusata, huci kawai yake yana Karewa bakinsa_ kallo suna_ gabatar da kawunansu.
“Wannan matata ce ranka ya_ dade, watannin da suka gabata ta fara safara daga nan kano zuwa wasu kasashe, Saudi, Dubai, China da sauransu. Harkar ana samu babu laifi, to saita — gamu da Www.bankinhausanovels.com.ng matsalar sa hannun magauta, yadda _ komai ta samu yake zaurayewa, mun sha yawon _ malamai suna shaida mana hakan, amma an rasa mai magance mana, kari akan haka ma wannan odar tata ta karshe wadda a nan karfinmu ya Kare don nima na tattara nawa Karfin na bata, har filina na siyar na bata ta tafi, kuma wai kwatsam sai gashi kayan da ta auno na neman Bata a hanya”. Baban yayi shiru da bayar da labarin ita kuma matar ta cigaba cikin rauni,
“Kawata ce ta ba ni labarinka ranka ya dade, shi ne muka zo a taimaka mana,kar mahassada su yi mana dariya, kusan duk mutanen duniyar nan bakin cikin zaman lafiyar da muke suke, in suka samu tozarta zasu yi dariya”’. Salmanu cikin ransa ya ce, Ai kuwa dariyar zasu yi’Yayin da a zahiri ya yi fuska iyakar fuska ya dubi mahaifinsa ya ce,Kai mu ga Kwayar idonka”.Jikin baban nasa na bari ya gwale ido, ya . dan fara Kiftawa Salmanu ya hana, “Kar ka sake Kiftawa ka yi min kallon kuda na tsawon mintuna biyar”. Babansa fa ya dage ya Www.bankinhausanovels.com.ng dinga kallon kuda babu ji babu gani, tun yana yi da son nuna jarumta har ya ji abin ya fara faskararsa, amma dai haka nan ya dage ya cigaba da yi, idanun na karkawar suna hawaye, a hankali kuma suna yin ja kamar farar fulawar da aka dora akan garwashin wuta. Ya ji wahala iyakar wahala har sai da idanuwan suka runtse dan kansu bayan sun daina gani kafin su runtse din. Matar sai kallonsu take cikin fargaba,
amma cike da murna, a ganinta aikin bokan nan
zai iya zama sha yanzu magani yanzu tunda nan take yake wannan aikin a gabansu, dubi dai~ yadda ya jirkita kamannin mai’ gidanta ‘cikin * ” kankanin lokaci, Kila wani asirin ya cire masa da‘” haka. Dama abinda Salmanu ya shirya kenan, da dadewa ya san mahaifinsa ba shi da lafiyar ido, ~ Www.bankinhausanovels.com.ng an taba yi masa aikin ido aka cire masa Yana, har ma aka ba shi gilashin ido amma ya ce shi ba zai_dinga kwaba gilashi kamar wani dan .bana bakwai ba, annan ya sanya ciwon nasa kan tashi _ lokaci lokaci. *- Sanin wannan ne ya sanya Salmanu yayi masa wannan ‘salon damfarar, bayan idanuwansa sun galabaita sannan ya sanya shi ya kwanta ya huta kana ya dawo kan matar. Ya sanya ta ta fara yi masa kallon Kudan_ - har na mintuna biyu, ita dayake tana da lafiyar -_ do kuma tana dan fakar idon Salmanu ta kifta sai taga daidai Ita ma Salmanu yayi zaton haka, a nan ya dakatar da ita da cewa, ; “Yauwa dakata haka, na fara samun abinda nake nema, aikinki babba ne”Www.bankinhausanovels.com.ng 
Cikinta ya Kara kadawa da fargaba, sai muskuce muskuce take tana hurwar a taimake ta. Salmanu dai yana jinta har sai da ya fahimci yawun bakinta ya gama bushewa da hurwa sannan ya tanka ta, “Zan rike ku nan, har zuwa yamma, ku tashi ku koma wajen da aka sauke ku zan turo a baku wajen zama, tashi ki kama shi”Yana nuna mata mahaifinsa da ya sharbe yana numfarfashi idanunsa sai zugi suke.Jikinta na bari ta tashi ta kama shi suka fice tana ta faman godiya, shi ma babansa godiyar_ yake.
Suna fita Salmanu ya tashi ya fada ciki ya  lalubo Adamu a duhu. *Adamu ina mukullin dakin nan da muka ce zamu fara karbar mahaukata mu tara su a nan?” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Cikin damuwa Adamu ya ce, Salmanu su zaka mayar mahaukatan?”Salmanu ya bata rai, . - “Haka na fada maka?”. Adamu ya cigaba da kallonsa kawai cikin duhu Hakan ya sa Salmanu Kara bayani, Zan ajiye su zuwa yamma, akwai shirin da nake musu, ni babu dan iskan da zai taba ni sannan ya shigo hannuna in bar shi ya wanye lafiya’Adamu bai damu da manufar maganar Salmanu ba sai zagin da yayi. Cikin nuna jimami ya ce, “Salmanu ka tuba, ka ce zagin da ka yi ban da MAhaifinka a ciki”Kai tsaye Salmanu ya amsa, .  “Ni dama ba shi na zaga ba”Adamu ya san dai fada kawai Salmanu yayi, amma babu yadda ya iya haka ya yarda da shi, kuma ya je ya nemo masa mukullin, suka. fice tare ta Kofar baya ya kai wa Tanimu, Ka je ka bawa wandancan Laila da .Majnun din masauki zasu wuni da mu yau, kuma ina tsammanin daga wannan satin ba zasu sake zama muhalli guda ba
Tanimu da Adamu suka dubi juna, sai dai babu wanda ya tankawa. Suka watse kowa ya kama aikinsa.
Suka cigaba da samun baKi jefi-jefi suna_ . karbe musu kudi su sallame su. Husna ta yo waya tana son zuwa, Salmanu yayi_ iyakar

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...