NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI


                 Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Suna fita Salmanu ya tashi ya fada ciki ya  lalubo Adamu a duhu. *Adamu ina mukullin dakin nan da muka ce zamu fara karbar mahaukata mu tara su a nan?” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Cikin damuwa Adamu ya ce, Salmanu su zaka mayar mahaukatan?”Salmanu ya bata rai, . - “Haka na fada maka?”. Adamu ya cigaba da kallonsa kawai cikin duhu Hakan ya sa Salmanu Kara bayani, Zan ajiye su zuwa yamma, akwai shirin da nake musu, ni babu dan iskan da zai taba ni sannan ya shigo hannuna in bar shi ya wanye lafiya’Adamu bai damu da manufar maganar Salmanu ba sai zagin da yayi. Cikin nuna jimami ya ce, “Salmanu ka tuba, ka ce zagin da ka yi ban da MAhaifinka a ciki”Kai tsaye Salmanu ya amsa, .  “Ni dama ba shi na zaga ba”Adamu ya san dai fada kawai Salmanu yayi, amma babu yadda ya iya haka ya yarda da shi, kuma ya je ya nemo masa mukullin, suka. fice tare ta Kofar baya ya kai wa Tanimu, Ka je ka bawa wandancan Laila da .Majnun din masauki zasu wuni da mu yau, kuma ina tsammanin daga wannan satin ba zasu sake zama muhalli guda ba
Tanimu da Adamu suka dubi juna, sai dai babu wanda ya tankawa. Suka watse kowa ya kama aikinsa.
Suka cigaba da samun baKi jefi-jefi suna_ . karbe musu kudi su sallame su. Husna ta yo waya tana son zuwa, Salmanu yayi_ iyakar

ZAMU TASHI 

hangensa na dalilin da zai kora Adamu ya rasa, musamman dayake yana tsoron ma ya kora shin, in ya tashi ya nufi gida har Salma ta sami damar sauke masa tijarar ya hana ta zuwa unguwa ko kuma ta sami damar lallaba shi ya bar ta ta fita gobe. Shi inso samu ne ma yau ya rike Adamu har Karfe goma sha biyun dare ko sama da haka, yadda duk jarabar Salma sai bacci ya fara cin Karfinta ko Kafin Adamun zai koma mata. Da wannan tunanin ya sake kiran Husna ya . dakatar da ita da cewa,

“Kar ki taho yau akwai-matsala, kamar na - hango ma Adamun yana shirin zuwa wajenki anjima”. ._ Hankalin Husna Www.bankinhausanovels.com.ng kwance tace, . “To babu komai Malam, Allah saka da alkhairi” Suka. yi sallama duk suka kashe waya. _. Salmanu cikin nazarin yadda zai Bullowa Adamu ya tsare shi har sha biyun. so Ita kuma Husna cikin wani irin farin ciki da jin muhimmancin bokanta, tabbas yana daga _~ cikin muhimman mutanen da ba zata taba mantawa da su a rayuwa bisa taimakonta da suka yi ba, taimako irin wanda ba sa buKatar ta rama musu, don ita wannan kamilin bokan nata ba ta ga ribar da yake nema a taimakon da yake mata ba.
Da azahar Adamu ya shigo wajen Salmanu da abinci a coolcr. Yayi fuska ya dube shi yace, “Zan kai wa su Baba abincin nan, na san zasu buKata.  Salmanu ya bata fuska, “Tunda ka matsa sai ka sami ladan mutanen da ba su taba niyyar su taimaki wani ko ° tausayawa wani ba sai ka je ka yi ta yi, amma
mijin kadai zaka bawa abincin, ita salon damfarar da na shirya mata ina buKatar ta ji yar banzar yunwa, ko ruwa kar ka ba ta”. Adamu ya ji dadin yardar da Salmanu yayi a bawa Baba abinci. Baba ga tsufa ga alamun wahala, dazu ya hange shi yana karkarwa za shi. yayi fitsari, sai laluben hanya yake bai san muguntar da salmanu ya shirya masa ba, don dai ras ya shigo gidan da wankansa da turarensa, dama shi mutum ne mai tsabta da son kwalliya. Ita kuwa matarsa ko shi Adamun ya tsane ta, don . ba ya mantawa yadda ta tsani Salmanu haka ta tsane shi.
Yaje ya bawa Tanimu abincin yayi masa  bayanin yadda suka yi da Salmanu. Tanimu ya je ya kai abincin. Baba cikin tsananin bukata yake wurga Www.bankinhausanovels.com.ng lomar abinci, don dama ko karyawa bai yi ba, yana gani Jummai ta dafa indomi'da zummar _ cewa sauri zasu yi, amma kawarta na shigowa sai ta juye musu a farnti shi ta ce in sun dawo ta dafa masa shayi shaf-shaf, ga shi zama ya kama su Shi dayake tsakani da Allah ya fi sonta a kan kansa, sai ya ce mata,
“Anya Jummai ko a boye ne ba zaki ci abincin nan ba? Yunwa fa ba ta da dadi” Jummai tana kallon abinci tana hadiyar yawutace, -Malam ciwo ai shi yake fitar da ciwo, tunda ya ce kar na ci rashin cin yayi amfani, kai ina ji a jikina ma fa aikin bokan nan ya fara aiki, dazun nan Hajiya Hajara ta kira ni ta ce min ta je kai min biyan bashin dubu talatin din nan da nake bin ta, in zaka iya tunawa kusan shekara biyu ina bin kanta kudin su fito, Dasauri ya amsa,“Ai kuwa na tuna anyi haka, nima jikina . ya bani mun zo wajen waraka, Allah zai Kwato
mana hakKinmu a hannun azzalumai”.Jummai ta ce, . “Wallahi tallahi kuwa Malam”, Suka dan yi shiru kowa na saKka abinda yake ransa,Jummai na shawara da ranta kudaden nan suna fitowa zata kashe wannan banzan auren ta samfe Saudiyya, Kawayenta da yawa suna can suna shanawa, har wata daga cikinsu ta aure wani matashin dan safara arziKi na Kara zama mata, ita tana nan tana fama da wani:tarkwashasshen . tsohon da ta gama tatsewa.
Shi kuma Baba idon nan ne ya dame shi, so yake ya koma asibiti a sake yi masa aikin idon, ‘gashi ko abinda zai ciyar da gida babu, duk ya tattara ya bawa jummai don su Karu gabadaya, Allah ya sa ma ba ta da Kyashi ko da kudin suka -dulmiye ita din ce dai take daukar nauyin gidan. . . Yanisa yacemata, “Jummai tunda kudin nan sun fito har dubu talatin, runtse ido zamu yi ki ba ni dubu ashirin din nan na koma asibiti a yi min aikin nan, idon nan kar ya mace mana muna zaune’. Kamar ta tashi ta shake shi don haushi, amma dayake makira ce sai ta gyada kai tana murmushi Malam mu dai dan jira, ka ga kudaden Www.bankinhausanovels.com.ng hannuna sun watse, in muka yi aikin ido: da wannan zamu zauna da yunwa”Dayake ba shi da zabi bayan abinda ta zaba, kawai sai ya kada kai, Kuma fa haka ne, kin fi ni hangen nesa”. Yanzu haka ciwon nawa a ciki yake, ko a asibiti ka ji ana hana mutum cin abinci kafin ayi masa aiki ai ka san ciwon na ciki ne”.
Ta fada maimaikon taya shi fin hangen Nesansa da yace ta yi. Cikin jimami ya ce, Ni ma na yi zaton haka, allah sa makiran “ da suka yi miki sammun ba a ciki suka ajiye miki ba’ Jikinta a sanyaye ta ce,“Amin”. “

**********

Karfe biyar daidai Salmanu ya cewa Adamu, “Adamu ka daure yau ka bulla wajen Husna mana, in ninne fa zan aurar da yata, da zarar na ga saurayin yayi. kwana uku bai zo ba zan fasa bashi ‘yata don na san bai damu da ita ba,ni idan na tashi neman aure a rana sau uku ma. zan dinga zuwa zance”’Tanimu na dariya yana cewa, .‘“‘Wato kai saboda tsabar zamanancewa har tazarar zuwa zancen surukinka zaka dinga Www.bankinhausanovels.com.ng Kirgawa?”.Cikin bata rai Adamu ya ce, “Ka rabu da shi Karya yake fada makawallahi, so yake ya kore mu ya yiwa dattijan can ._. abinda ya ga dama, ni kuma in ka ga na fita sai idan ya gama alayinsa ya sallame su, ba zan sa Kafa in tafi ina shanya baki ni baban soyayya’ya zo ya kashe matar mutane, ya janyo ina ji ina _gani a kama ni a garKame a kurkuku, ko a fasa. . aurena da masoyiyar tawa ko kuma, a daura ina zaman gidan kaso ita tana jira na a gida ba
‘Ba Tanimu ba, shi kansa Salmanu’ sai ‘da a hasashen Adamu ya tunzura shi da dariya, ya kai wa Adamu duka yana daruya, “Kai yanzu na gane in na kashe matar nan” mugun taimakonta na yi, duk zalincin da tayi zata iya wucewa aljanna ta bar ni ana tuhumata . dalilin kisan da na yi mata, abinda ta yi zan mata wallahi, kana iya tafiyarka wajen masoyiyarka Adamu”,
Adamu ya matse kafada, a ~ “Babu inda za ni”. : ‘Salmanu ya ce, “To shikenan, zo ka hau babur din Tanimu ka je ‘Yan danKo ka siyo min mahadin nata aikin”, A Kufule Adamu yace, “Uban me zan siyo?” . - Salmanu ya amsa,“Kunun Zaranya zaka siyo min Adamu yayi fuska yana tuhumarsa da ido, sai Tanimu ne ya dubi Salmanu a nutse ya ce,“Don Allah me zaka yi da. kunun ~ Zaranya?” Ba tare da jan rai ba Salmanu ya amsa, Aljanu zan zuba mata a ciki, in kun lura ta wuni da tsananin yunwa, idan aka bata abu mai ruda ciki sannan mai dan banzan zafi zaaiya tashin mayaka a cikin nata bayan mintuna goma sha biyar, da jimawa na san tana da ulcer, to za a hada mata da kunun aya zasu hadu su tashi mayakanmu...” Yanzu duk sun fahimce shi, dukkansu dariya suke tuntsirawa. Tanimu ya mika masa hannun suka tafa
yana cewa, Salmanu ka isa makiri wallahi...” Salmanu ya tare shi da amsa cikin dariya “Duk mara gata da galihu irina, in dai ka ga bai yi basira da iya makirci Www.bankinhausanovels.com.ng ba, to ka tabbatar in da yana da gata Karamin mahaukaci za’a yi”. - Nan ma dariyar suka yi, _Adamu ya kishingide, “Allah ya sani na gaji sai dai Tanimu ya je , ‘yan danko”. : Kafin ma Adamu ya rufe baki Tanimu ya - mike, . “Bari na je na siyo, da kunun aya ka ce ko?” Salmanu ya amsa, “Eh, kunun zaranyar kimanin kwanon sha guda, sannan a zabgo Sugar, kunun ayar kuma - kar ka siyo mai sanyi, in so samu ne ma mu sami wanda ya fara bashi”. “An gama’. . Tanimu ya fada. Yana dab da ficewa daga Dakin Salmanu yace In ka tarar da kunun ya Kare ka biya mai yi kudi masu kyau kana tsaye ta dama maka, sannan kar ka manta da ruwan rukiyyar da zamu
sauke aljanun idan sun zo”. Tanimu ya juyo ya dube shi cikin kallon rashin fahimta, “Gishirin adrew nake nufi’. Wannan karon murmushi kawai suka yi. Bayan fitar Tanimu Adamu ya lallabo ya fara yi wa Salmanu maganar da ta zaunar da shi, “Yakamata mu ware rana guda mu je hado lefe Salmanu, dazu dadin hira ya sanya na cewa Husna nan da sati zan turo...” Salmanu na dariya, . . “Ba ka da mutunci Adamu, matarka na can _ cikin kuncin zuciya tana fama da fafutukar yadda zata hana ka aure, kai kuma kana naka wajen kana waya da budurwar har da alkawarin kai mata lefe nan kusa”." Adamu ya bata rai, “Ni har ka tuna min ma, ko wanne shegen - munafukin ne ya fada mata”, Salmanu yayi subutar baki,Zai wuce Sa’a mai raka ta gidan bokayen?”. Da sauri Adamu ya dube shi, “Wai gidan bokaye take zuwa?”. - Da sauri Salmanu ya rufe baki, “Au na manta makaranta nake son cewa, ko ba makaranta take zuwa ba?”’.Adamu ya dan yi kasake sannan ya kawar da kai, Kai dai kawai ka waske Salmanu”.Yana rufe baki ya amsa,“Na ji na waske. Yau idan mun je wajen Husna sai mu ji ra’ayinta game da abubuwan da ta fi sha’awar a sa mata a lefen ko? Gobe ko jibi sai mu je kasuwar, akwai mutumina Abdurrashid a kasuwar zannuwa yake sai mu sa shi gaba, in ma kudin take so sai a bata abinta”.“Yauwa hakan yayi Www.bankinhausanovels.com.ng kyau”.suna cikin hira Tanimu ya dawo, komai kuma ya siyo kamar yadda aka bukata, don tsabar daurewa Karya gindi har Jug mai rike zafi Tanimu ya siya ya zubo kunun zaranyar. Suka dan kikkintsa sannan kowa ya hau bakin aikinsa. Adamu dai ba shi da aiki, don yau babu muryar aljanu, illah iyaka ya labe dan ya ji yadda zata kwashe. Tanimu ne ya je ya taho da su.Baba jiki a mace saboda tsabar Koshi, har bacci yayi ya farka ya sake ci, don haka yanzu ma wani baccin yake ji. Jummai ce dai idonta KeKashe saboda yunwa, dayake tana da Ulcer ko iya mikewa tsaye ba ta yi, a haka suka shiga fadar boka Salmanu.Duk suka zube a gabansa ko wannensu kai a Kasa, . Salmanu na ganinsu ya ji fushinsa ya dawo sabo, saboda haka husashinsa na dazu ya dawo sabo shima. . Ya fara magana cikin ginshira, Na zaunar da ku har zuwa wannan lokacin ne don a tattaro min duk wani sammu da aka yi muku, zan tattara su yanzu guri daya sai kuma na shiga bincike daga inda aka aiko su”.
Ya dan yi tari sannan ya dora, “Bai kamata a fara yi muku ko wanne irin  dafa’I ba sai har an kori turen da aka yi muku, to kai malam ba ka da matsala sosai, an fidda taka ' matsalar tun safe’
Ya nuna Jummai,Kece dama mai babban aiki, dauki wannan maganin ki shanye shi Ya nuna mata Katon Kokon da suka shakare da kunun za suke rufe da Karamin faifai, haka ma suka yi wa kunun aya bayan sun barbade da garin lalle kadan. Hannun jimmai na bari ta janyo Koko, da taga yawan kunun gashi da zafi sai da gabanta ya fadi, ba tare da ta iya daga ido ta dubi boka Salmanu ba tace, . “Duka zan shanye MAlman?” Ya amsa mata, Duka zaki shanye”.Nan ta. daga kai ta fara sha ba ji babu gani, da farko Www.bankinhausanovels.com.ng dandanonsa da zaKinsa ya dada ta da Kasa, amma kafin ta gama shanyewa sai da ta ji babu bala’in da ya fi wannan a duniya, ta dinga jin kamar zata amayo da zuciyarta wadda yawan kunun ya danne, amma dai haka ta daure ba ta bayyana komai sai yamutse fuska. Tana ta faman numfarfashi ta ajiye Koko - tana cewa, . . _ “‘Malam na shanye”Salmanu kamar ya fashe da Www.bankinhausanovels.com.ng dariya saboda gaba daya ta fita daga kamanninta, sai uban gumi take hadawa. Ya dube ta ya Kara yin fuska yana nuna mata KoKon kunun aya da aka barbade shi da koren magani, Ki dan huta sai ki sha wannan, yau duk

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...