MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 7 KARSHE END BY REAL FAUZAH TASIU - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 7 KARSHE END BY REAL FAUZAH TASIU

MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 7 KARSHE END BY REAL FAUZAH TASIU

- - Post a Comment

MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 7 KARSHE END BY REAL FAUZAH TASIU


             Www.bankinhausanovels.com.ng Miqewa shima Jamal yayi cikin sarqewar murya yace “dad da gaske kasanta Yaya a Ina kasanta meye alaqarka da ita don Allah?" Qit Ja'afar ya kashe wayar tsabar kidima da tashin hankali Ina Jamal yasan Rafi'ah dama ashe Bata mutu ba? A Ina ta boyewa ganinsa tsayin wadannan shekarun kusan antafi hudu meyesa ta kasa nemansa a halin tana raye Kuma tasan shima yana raye? Tambayoyin da yaketa jerawa kansa kenan babu amsa dole ya miqe ya fara neman lambar Mai martaba bugu biyu ya daga ya fara zayyane masa abinda ke faruwa Mai martaba yayi hamdala yace “dama da safe nakeson kiranka kome kakeyi ka bari ka taho gida abubuwa fah sun lalace Ina buqatar ganinka da gaggawa"

Saida gabansa ya fadi da Mai martaba yace dole ya taho gobe yasan wannan Kiran bashida mafuta shiyasa ya aje wayarsa ranar bai rintsaba kamar yanda Jamal ma bai rintsa ba itama Rafi'ah da batasan meye yake faruwa ba Bata rintsa din ba saboda wani azababben ciwon Kai da yayi Mata dirar mikiya tun daren take juyi har gari ya waye sannan ya qara ta'azzara har takaita ga ficewa daga hayyacinta da safen kuwa Alh Hashim ya Kira Jamal yake fada masa abinda take faruwa duk da yanda ya kwana da mutuwar jiki bai iya sharewa zuwan ba haka ya nufi gidan suka dauketa sai asibiti suna tafe yana tunanin tashin hankalin da yake tunkaroshi indai ya kasance Rafi'ah ta zama matar yayansa da gaske shi yanzu meye makomar qaunarsa gareta?"+

A asibitin ma kass hassala Mata komai yayi ya hadata da wasu likitocin suka duqufa kanta shikuma ya duqufa tunani lkc zuwa lkc yana share hawaye dole ta tabbata Rafi'ah ba tasa bace kenan?" Haka ya yini a zaune ruwa ya kasa hadiya baiji sanda aka turo qofar ba saiji yayi an janye hannunsa daga tagumin da yayi ya daga Kai tare da miqewa da sauri suka rungume juna yace “duk wani Abu muhimmanci ya gaza kaiwa muhimmancin da zaka taho takanas saboda shi Amma wannan yakai tabbas da kasan hakan da tun farko kazo ka rabani da ita ba Saida zuciyata ta saba da sonta ba duk da ita bata taba Sona ba kullum Kaine abakinta Kaine take ambato Koda yake ta manta da siffarka ta zahiri Amma Bata manta da yanayinka na badini ba Yaya Ja'afar meyesa kabarni na saba da matarka da danka sabo me tsananin da nakejin bazan iya rayuwa babu suba?"Shafa bayansa yayi ya janyesa daga jikinsa ya zaunar dashi yace “kayi hqr Jamal haka Allah ya tsara mana tunda nayi rayuwa me tsayi babu su kaima zaka Saba har Kama manta dasu Kai bakasan wace Rafi'ah ba Ni nasani inasonta da jikina da zuciyata da ruhina bazan taba amfanuwa babu itaba Kai shedane" miqewa yayi zai fice Jamal ya riqoshi yace “suna cikin asibitin nan batada lfy tun safe" daga haka suka fita suka nufi dakin da Rafi'ah take kwance aunty Bari'ah tana zaune a gefenta sukayi sallama ta amsa tare da miqewa ta dubi Ja'afar dubi Mahir daketa wasa mamaki ya kamata ta matsa ta dago Mahir tace “kayi gsky Jamal idan da Mahir bata yayi aka tsinceshi akaga yayanka yazo wuccewa a hanya zaace Masa ga danka ikon Allah kenan" murmushin yaqe Jamal yayi inda tuni Ja'afar ya wucce inda Rafi'ah ke kwance ya zubanta ido cikin tsananin tausayin kansu da gdy ga Allah daya sadasu a duniya batare da daya cikinsu ya mutu ba, hannu yasa ya shafa kanta kawai sai ya fada jikinta ya rushe da kuka me sauti yana cewa “ashe mafarkina gsky ne Rafi'ah kuna raye keda dana kika watsar dani kikaqi nemana kikaqi waiwayena nida iyayenki kika barni cikin zullumi da ciwo Mara magani Rafi'ah meyesa kikaqi nemana don Allah har yaronmu yayi girma haka?"

Ajiyar zuciya yaji taja me qarfi wacce ta sada hancinta da wani ni'imtaccen qamshi da ya fara tariyo Mata wasu abubuwa da suka faru a baya aikuwa saita miqe ta angajeshi da sauri tana fadin “wayyoh innanillahi zasu haukatani Ja'afar zasu rabani dakai Hajiya Barebari da Bestie Ja'afar riqen...." Rufe Mata baki yayi da sauri tare da rungumeta ya fara tofa Mata addu'o'i sun dauki lkc a haka tana maqale a jikinsa kafin ta janye ta bude idanunta tar a cikin nasa shidinma itan yake kallo taja ajiyar zuciya tare da daga hannu tace “Alhmdllh da wannan mummunan al'amari ya kasance mafarki" sai Kuma ta fara bin dakin da kallo kowa ita yake kallo ta shafa cikinta tare da sake kallonsa tace “Ja'afar Ina jaririna? Ina Hajiya Innah ba a dakinta nake ba meye ya dawo dani asibiti banida lfy ne?"


Matsawa yayi gabanta ya riqota daidai lkcn da Mahir ya taso ya taho ya riqe qafafunta yace “mommy Kinga Abban Nan yana kuka" juyawa sukayi ga Jamal da gaske hawayene sosai suke zuba a idanunsa kallon Ja'afar tayi tace “JM Kuna Kama da wannan mutumin wayeshi?" Da sauri aunty Bari'ah da Jamal da Alh Hisham suka kalli juna Alh Hashim yace “alhmdllh a hakan ma wato da tunanin farko ya dawo saiya kore sabon tunani ya akayi hakane wai meye ya faru?"

Nan Jamal ya qwashe komai ya fadawa su Ja'afar abinda yake faruwa da dalilin haukacewar Rafi'ah aikuwa tayi kuka sosai tana Jinjina girman abin batayi tunanin hakan ba tace “kun cuceni Hajiya keda Ni'imah bantaba tunanin rashin imaninku yakai hakaba meye na tsare muku da kuka cutar dani haka Allah kasani wlh bazan taba yafewa ba Allah kabimin haqqina da gaggawa sun rabani da mijina sun rabani da iyayena sun rabani da garina sun rabani da hankalina Allah kayi musu daidai da abinda sukayimin"
Sake kamota Ja'afar yayi ta lafe a jikinsa tana shafa bayansa tanaci gaba da kukanta tace “basu cutarmin dakai ba ko mijina Ina su Abbana da Ammy inna Hajiyata da Karimatu wayyohhhh mijina sun cutar damu nikam ko ka yafewa hajiyanka wlh bazan yafe Mata ba" shima hawayen yakeyi bai qara tabbatar da yayi missing din wani bangare na rayuwarsa ba sai yau Babu Mata Babu da kayy wadannan mutanen sun tagayyara shi ba haka sukaso ganinsa ba shima bazai yafe ba" sun dade suna koke kokensu sauran mutanen dakin suna tayasu kafin daqyar sukayi Shiru daidai lkcn da Jamal da Mai martaba da Abba suka shigo bayansu Kuma Ammi ce da Hajiya Innah tuni Rafi'ah ta saki Ja'afar ta kwasa tayi gurin Abba da gudu ta fada jikinsa ta sake rushewa da kuka Hajiya Innah ce ta kalli Hashim tace “Aa Hashim ya akayi haka dama a gurinka Rafi'ah take ya akayi banganta ba watana uku fah da zuwa gurin Yaya Rakiya nayi sati guda?" Shafa kansa yayi yace “haka Allah ya nufa Mama in zaki tuna lkcn ai nace kizo gdana kikace sai Bari'ah ta haihu sauri kikeyi da kinzo qila da tuni ba wannan zancen akeyi ba"
Nan aka rinqa mayar da magana itadai Rafi'ah tana kwance jikin Ammi tana kallon Ja'afar shima ita yakewa kallon qurillah tayi qiba tayi wani kyau alamun hankalinta a kwance yake sabanin shi da yake a kode sai tsayi da dogon hanci kawai amma duk Wanda yaganshi yasan a fukace yake

Daganan sallama aka rubuta Mata suka dunguma sai family house dinsu Alh Hashim  Nan fa akayi mayar da yanda akayi shidai Ja'afar ji yakeyi kamar yace yanason ganawa da matarsa Mahir kuwa tunda suka taho yake hannunsa yanajin qaunar dannasa tana ratsashi tare da tausayinsa duk Shirin gatan da yayiwa rayuwarsa data dansa an rushe Masa shi dansa baisanshi ba sauqin ma dake yasan qaninsa sun shaqu sosai Mahir da dan banzan surutu idan aka tambayeshi Ina abbansa sai yace da “abba baqine Abbana Amma yanzu Abba farine abbana" dariya Ja'afar yayi yace “yaro kasan gaskiya ni nasha wahalata da wannan uwar taka tun daga neman aurenta har kawo cikinka da laulayinka kawo yanzu ban hutaba qanne nawa kakeso ayi maka?" Sai ya dunqule yatsansa babba ya nuna hudu kowa dariya yakeyi suna yabawa da wayon yaron.A daren Mai martaba yace zasu wucce Bauchi daqyar suka roqi alfarmar su bari Saida safe Bari'ah ta janye Rafi'ah suka koma gidanta shikam Ja'afar baiso hakan ba yaso ya samu kebewa da ita don dai kawai bayaso ya fito da maitarsa a fili ne, suna zuwa gidan kwanciya tayi zuciyarta wasai ita kadai a dakinta kasancewar Mahir yabi ubansa tanata juyi tare da tunanin mijin nata taji wayarta tana ring ta dauki wayar tana duba lambar duk da batada ita yanzu Amma ta fado Mata ranta tayi murmushi ta Kara a kunnenta yace “naso ace yau tare dake zan kwana na hucce gajiyata na bayyana Miki asalin halin dana shiga saboda rashinki Rafi'ah naga rayuwa fah mutanen nan sun cuceni" katseshi tayi da cewa “sa minjaye sun cucemu dai" murmushi sukayi tare yace.

So nake najiki a jikina matata don Allah bari nazo na daukeki wlh tunda naganki na kasa control din kaina na dade Ina azabtuwa saidai tayau zata bambamta da kowacce saboda kece kika harqitsani da kanki" Sarai tasan halinsa nan ta ringayi Masa magiya Amma ko a jikinsa saima ya kashe wayar ya nufi dakin Jamal  yace “bani mukullin motarka zan dan fita kallonsa yayi zaiyi mgn yace “banson tuhuma in kaso ka kulle gdanka wlh bazan iya kwana ni kadai ba yau" dariya Jamal yayi yace “a baya Kuma ya kayi?" Shima murmushi yayi yace “hqr Kuma lkcnsa ya qare"Yana fadin haka ya fice da sauri ya dauki motar Jamal ya nufi gdan Alh Hashim Saida yaje bakin get din sannan ya Kira Alh Hisham yace masa yanason ganin Rafi'ah mamaki ya cika Alh Hashim wannan wanne irin mara kunyar mutum ne a wannan tsohon daren yazo Wai yanason ganin matarsa, to dake ba me zafafawa bane haka ya kalli Rafi'ah yace "kije ki karbo saqo gurin mijinki a waje" Saida gabanta ya fadi tayi qasa da kanta ya sake kallonta yace "jiranki fah yakeyi yace sauri yakeyi"

Miqewa tayi a sanyaye ta fito megadi ya bude Mata get ta nufi motar yana tsaye jikinta ya harde hannunsa a qirjinsa ta iso kanta na qasa yayi murmushi ya bude Mata yace "shiga" kallonsa tayi tace "Alh yace saqo zaka bani" baice Mata komai ba ya Kama hannunta ya jefata a motar ya shiga shima ya zauna ya zubanta ido yanajin wani sanyi a zuciyarsa cikin sarewar zuciya yaji hawaye na zubo masa ya kamo hannunta ya riqe cikin nasa yace "baayi ba bakuma zaayi kamarki ba matata ke kadaice ke Jan ragamar zuciyata dana rasaki saina zabi na rasa kowa da komai don Allah ki mulkeni bisa adalcinki kinji?"

Sanyi jikinta ya qarayi yana qoqarin tada motar tace "naji JM Ina zaka kaini a tsohon darennan don Allah" yana murzu sitiyarin motar yace "kowa zai kwana bargo daya da matarsa gwauro zai rungumi pillow Ni Kuma sai abarni da tufka da warwara kema kinsan bazai yuwu ba dole yau sainaji dumin da na dade Ina maraici"Magiya ta shiga yimasa Amma dake ance Mai hali baya fasawa kuma Koda shekara dari ka rabu da mutum tambayeshi wani abun ba hali ba, hakance ta faru yayi biris da ita Saida sukaje qofar wani hotel ya shiga yayi parking ya fita ya kulleta ya jima sannan ya dawo ya bude ya riqo hannunta Sai matsar hawaye takeyi baiko kulata ba yajata suka shiga ciki ya bude qofar dakin suka shiga ya kulle tare da zare mukullin yayi miqa tare da salati yace "haba yammata ke yanzu bakifi jin dadin yanayin ba?"

Zama tayi ta hade kanta da gwiwarta tanaci gaba da sharar hawayenta batasan me yakeyi ba saida taji ya dagota ta miqe tajita a qirjinsa ta lumshe idonta tare da Jan ajiyar zuciya shima yaja yace "kullum Ina addu'ar sake juyowar wannan lkcn" daga haka ya fara qoqarin zare Mata hijjab dinta ta riqe tare da bude baki zatayi mgn yace "karki hanani wife don Allah kibarni na huta" sake langwabe Masa tayi tace "amma JM kowa fah zai gane ka bari mu koma gida man..." Manna bakinsa yayi a nata yace "haqiqa bazan iyaba jira na mara rabone Rafi'ah nikam inada rabo saboda haka in bakyayi kibarni nayi" daga haka ya fara zare Mata hijjab din bayan ya cire ya dagata cak ya dorata a gadon tare da hade bakinsu Yana aika Mata da wani zazzafan kiss da yake nuna asalin maitarsa gareta duk yanda taso hanashi jin dadin daren nan Saida yaji tayi kuka da magiya har ta gaji ta lura Ja'afar din ya qaro wulaqanci da idan tayi masa magiya yakan saurara Mata Amma yau magiyar tata sai tazama kamar zugi.Haka suka kwana yayi kwanan farin ciki rayuwarsa ta dawo daidai ita Kuma tayi kwanan wahala dakansa ya hada musu ruwa sukayi wanka ya tayata ta shirya yanata rarrashinta ita Kuma sai fushi takeyi haka suka fito suka nufi gdan Alh Hisham a harabar gdan suka tarar da Alh Hisham ya qarasa suka gaisa itakam wuf tayi ta shige ciki ya fada gadonta tana mayar da numfashi Bari'ah ta shigo ta sameta ta rinqa yimata tsiya kunya ta hanata cewa komai, komai batajin dadinsa sai bakin shayi kawai Tasha ta fito suka sake rankayawa gdan si Hajiya Rakiya daganan suka dunguma sai azare, aka taresu cike da murna kowa yana tayasu murna a gidan sarautar bayan komai ya nutsane Mai martaba ya dubi Fiddausi yace "ina babarku Kaltume?" Sunkuyar dakai tayi tana matsar hawaye tace "Allah ya qara maka lfy jiya bayan tafiyarku ta fice itama ita da Jakadiya Indo suka tafi unguwa a hanya sukayi hatsari aka dungumesu sai asibiti itadai Indo ta cika bayan ta tona musu asiri Wai Ashe barin Yarimah Ja'afar masarautar Nan duk shirinsu ne sune sukayi masa kurciya shida matarsa Amma ba sune suka haukata Rafi'ah ba yanzu dai zancen da nake maka innanmu tana asibiti qafarta daya ta fita fit dayar Kuma ta karye an dorata haqoranta kusan goma sun fice bayan mummunan ciwon data samu a fuskarta"STORY CONTINUES BELOW

Sosai kowa ya kadu da jin lbrn Nafeesah ta cafe da cewa "Barebari ma nacan tanata subadadi Ashe wai ba ita ta haifi Prince Ja'afar ba Marigayiya Bilkisu itace ta haifesa ita Kuma ta haifeni shine ita da Jakadiya Indo suka canza Mata daga namiji zuwa mace bayan ta farfado sai suka fahimci tasan namiji ta Haifa zata tona musu asiri shine suka Bata guba taci ta mutu dalilin da yasa ta hadamu ni da Ja'afar ta Raina kenan sannan ita da Hajiya Sahura da Ni'imah sune suka haukata Rafi'ah sannan sukayi asirin da bazaa warke ba har abada shine kaikayi ya dawo kan masheqiya duk malaman garin nan sunce saidai abarta da abinta a haka har lkc yayi"

Kowa ya kadu dajin wannan mummunan lbr duk da dama ansan dasa hannunta a haukacewar Rafi'ah Amma Babu Wanda ya kawo mugun abin Hajiya Fatsum yakai ga kisa a wannan masarauta shikam Ja'afar rungume Mahir yayi yana kuka me taba zuciya wannan Mata sun cutar dashi musamman Hajiya Fatsum daya rayu yanayi Mata biyayyar da da mahaifiya ya jima kafin a samu yayi shiru ya miqe ya shige bangarensa nan zaman ya watse Rafi'ah tabi mijinta ya tarar dashi har yanzu kuka yakeyi tana shigowa ya rungumeta yana kuka yace Mata "me mukayi musu suka cutar damu Rafi'ah Akan sarautar banza suke wannan haukan na rantse da Sarkin dake busamin numfashi bazanyi sarauta ba indai wannan abun shine sarauta nabarta har abada...."Saurin rufe masa baki tayi tace "kada ka ratse JM ba duka aka zama iri daya ba don Allah kada kaci alwashi ka karba ka riqe ka Basu mamaki saka alkhairi ga Wanda ya cuceka ka barshi da kunyarsa insha Allahu da kansa sai yayi nadamar rayuwa sukam sunyi ai sunakan yi mijina uban yayana" sake rungume shi tayi tana shafa bayansa da haka suka zube a gadon suka fara farantawa juna duk da yanda jikinta ke ciwo Saida tayi qoqarin faranta ran mijinta ta gusar Masa da damuwa sannan ta miqe ta fita

Gurin baqinsu ta koma sukaci gaba da tattaunawa har dare sannan suka tafi bangaren baqi ita Kuma ta koma bangarenta washegari suka tashi da gagarumin taro na rashin zato a gidan nasu kowa tunanin wannan taro yake na meyene Saida komai ya nutsane Mai martaba ya bude taro da addu'a ya gabatar da dalilin taron akan cewa shi Alh Muhammad Mahir Wakil yayi murabus sannan majalissar fada ta tashi tunda suka shiga gda Ja'afar ya fara hada nasa ya nasa washegari kuwa ko sallama baiyi da kowa ba ya dauke matarsa da dansa ya calle dasu Canada tare da barin wasiqa kan cewa shi baya ra'ayin sarauta a nada Jamal.

Da saqon ya ishewa Mai martaba murmushi yayi yasan zaayi haka dama shi tun yana qarami bayada raayin sarauta saidai yariga ya makara, washegarin tafiyarsu Canada da yamma saqo ya iso email dinsa daga state government cewa suna tayashi murna zamowa sabon sarkin masarautar Azare da fatan Allah ya tayashi riqawa, Saida ya kusa faduwa saboda tashin hankali daqyar da ayoyi da hadisai Rafi'ah ta shawo kansa ya saduda ya karbi wannan hukunci Amma yaqi yarda su koma 9ja duk da irin Kiran da aketa yimasa anason ayi bikin nadi Mai martaba ne ya fara fahimtar har yanzu Bai gama dawowa daidai ba yasa aka rinqa yimasa dafa'i dagashi har iyalansa sannan bayan shudewar watanni bakwai ya dawo qasar lkcn Rafi'ah cikinta har ya fito sosai, Koda ya dawo Saida akasha daga sannan akayi nadin sarautar ya tabbata sarkin Azare Hajiya Kaltume na raye Hajiya fatsum na raye sun kasa shafe hukuncin Ubangiji har gara ma Hajiya Kaltume da hankalinta nakasa ce dai ta sameta ta ko Ina itakuwa Hajiya Fatsum batasanma meye makomarta ba don Babu abinda takeyi sai qara turuwa a hauka tun ana maganin har angaji an qyaleta.Ni'imah kuwa ananan Babu aure tayi tayi ta samu ta gyara alaqarta da Rafi'ah Amma Mai martaba Ja'afar ya datse qwaqqwaran kashedi yayiwa Rafi'ah akanta dole ta hqr ta zabi mijinta Ni'imah tayi kukan da takasa samun me rarrashinta ta Bata gomanta dayanta Bata gyaru ba ta koma makaranta ma takasa abin arziki da carry over dinta ma yayi yawa sukayo waje da ita ga Hajiya Sahura duniya ta juya Mata baya Babu qawar zuwa gurin bokaye Yaya Mata biyu a gabanta daya bazawara da ta taka rawa wajen lalacewar aurenta daya budurwa ita bazawara ana yamadidin haukata kishiyarta tayi miji ya korota ita Kuma budurwa ance uwarta yan yawon asiri ne daqyar Alh Nuhu mahaifin Rafi'ah ya samu ya lallaba Rashid ya auri Yusrah qanwar Ni'imah dake Yusrah ita bata tsotso mugun halin uwarta ba qalau suke zaune da kishiyarta Jamal ma yayi aure ya auri Maryam qawar Rafi'ah ta makaranta suna zamansu lfy Fulani Rafi'ah nada Yara hudu Ni'imah ta samu ta auri wani Alhajin Birni matarsa daya da yaransa bakwai hakadai dake taji fadan duniya ta hqr ta zauna a gidanta itama har ta fara zuba nata yaran.

Hajiya Bari'ah ma da Alh Hisham haihuwa ta bude yanzu yaranta biyar har tafi Rafi'ah yara zumuncinsu gwanin sha'awa yanzu Rafi'ah batada qawar da tafita komai daya shafi rayuwarsu tare sukeyi kasuwanci da komai asibintinsa na Gombe kuwa kyautarsa yayiwa Rafi'ah Bari'ah ke kula da komai rayuwa sai son barka yanzu ne Rafi'ah take more rayuwa da Aminiya ta har abada tana tuna wata magana ta masu hikima a kullum da ko yaushe da sukace.

_(A rayuwa dayan biyu ne idan kayi aboki ko qawa kodai ka samu amini na har abada ko Kuma ka samu darasi na har abada)_._Alhmdllh alhmdllh alhmdllh sisters nd brothers wadanda kuka kasance dani cikin wannan lbr me dauke da darrusan rayuwa daban daban na gde da kasancewarku masoya a gareni_

Post a Comment for "MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 7 KARSHE END BY REAL FAUZAH TASIU"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...