MAFARI CHAPTER 1 BY UMMU AZAMM - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAFARI CHAPTER 1 BY UMMU AZAMM

MAFARI CHAPTER 1 BY UMMU AZAMM

- - Post a Comment

MAFARI CHAPTER 1 BY UMMU AZAMM
               Www.bankinhausanovels.com.ng 


SHIMFIƊA

Ƙauyen Mairambiri , wani ƙauye ne , ko kuwa "ƙaramar Alƙarya" da yake tsakanin ƙananan hukumomin bama da konduga, wanda suke a karkashin jahar ( BORNO )

Mutanen garin mafi akasarin su barebari ne " kanurai", sai kuma shuwa, da fulani, tsilla-tsilla, babbar sana'ar mutanen garin shine noma, suna da makarantun primary da secondry na gomnati, sai kuma makarantun allo da mafiya yawan yaran garin shi suka fi zuwa ,tsiraru ne suke zuwa bokon da suke kira karatun "Malam nasara", kasancewar garin nasu yana tsakanin manyan-manyan hukumomi biyu ya sanya suke da kasuwar su a bakin babban titin da yake tsakanin garin bama da konduga" wacce take ci duk ranar Alhamis.


**************


Cikin wani ƙwarababben gidan kasa , wasu yara ne su uku mata, suna cin wani zazzafan damalmalallen tuwon hatsi miyar kuka shar cikin wani tsohon kwanon da duk lamba da tsatsa suka gama munana shi , babbar baza ta wuce shekaru 16 ba ,sai ta tsakiyar me kimanin shekaru 14, sai kuma ƙaramar su me kimanin shekaru 8.


Cikin nutsuwa babbar ta ke kai lomar tuwon bakin ta bayan ta sanyawa ƙaramar su ita ma a bakin ta ,saboda zafin tuwon ta kasa sanya hannu taci ,"alama yanzu aka sauke dumamen tuwon daga wuta "duk da yanzun farar safiya ne ko 6:30am bai cika ba.


Wata doguwar mace siririya me ɗauke da wata irin farar fata sol-sol kamar ta so ta zama zabiya " Albinism"dan hasken ta yayi irin nasu, wacce da ganin ramar da take da shi na tsabar wahala da talauci ne ,tana zaune kofar wani taƙwarƙwasashiyar rumfa da alama madafi ne ganin yadda duhun wajen yafi na ko'ina a gidan, hannunta riƙe da wani jariri namiji kansa tanƙwal da aski , ta ciro yamushashen siririn maman ta tana kokarin cusawa yaron a baki shi kuma daga ya kama yayi tsotsa ɗaya-biyu yake sakewa ya cigaba da tsala kukan da yake da alamun yunwa ce ke addabar sa .9


Wani baƙin dogon mutum ne, ya bullo daga bayan durkusassun ɗakunan nasu guda biyu ,hannun sa rike da babbar robar ruwa (table water ), wacce aka yanke daga wuyan ta zuwa sama gefen ta daga kasa yana ɗan ɗigar da ruwan ciki daidai inda ya ɓule aka toshe da bakar leda .


Duƙawa yayi tare da wanke baƙaƙen kafafuwan sa da suke sanye cikin waɗansu ratattakakkun silifa (da guntun ruwan ) ,ya ɗago tare da kallon sashin da ƴaran nan suke zaune ya ɗan ɗauki wasu daƙiƙai yana kallon su cikin nazarin yadda babbar cikin take ta ciyar da kannan nata domin ya zuwa yanzu dai su duka biyun ita take sanya hannu tana zaƙulo tuwon da ya dilmiye cikin tsululun ruwan miyar da ta haura tuwon yawa har ta shaa kansa ,tana zaƙulo shi sannan ta hura iskar bakin ta ta gutsurawa ɗayar a hannu ta sanyawa karamar sauran abakin ta ,

kuma a take ta sake mayar da hannun ta cikin kwanon da hanzari tamkar dai ita bata jin zafin tuwon .


Yakaka "nyidin biri bun" baa ? Duwan "bii lanyen wande kausuzuin (yakaka ke baza ki ci abincin bane ? Kiyi sauri ki ci mu tafi kar rana ta yi ) cewar wannan mutumin ga babbar ɗiyar ta sa da ya kira da suna yakaka cikin yaren su na "KANURI .


Amsa masa tayi da "toh" ,dai-dai lokacin da ta miƙe da hanzari ta zagaya ta bayan matar nan da hasken fatar su yake yanayi ɗaya da nata ,ta ɗauko wani bakikkirin ɗin tiren kwano da yayi fatsa-fatsa da lamba ta nufi fasashiyar randar su da take binne a kasa sai iya fasashen bakin ta ake gani a waje "wanda za'a iya zaton rami ne" ta sunkuya tayi goho ta kwarfi ruwa a chan kasa ta ɗauraye farantin ,


STORY CONTINUES BELOW

Ta sake kwarfo wani ruwan a cikin bulalliyar moɗar da ta sha liki da leda , cikin gudu gudu ta je ta juye tuwon a kan farantin tare da ajiye musu ruwan , har ta yunƙura ta tashi ,sai karamar ta riƙo hannun ta ,a hankali ta ɗago idanun ta ta dubi kanwar tata wacce idan aka dauke kamanni irin na jini , da kuma siraran zane (Shunkurai ) da yake kan fuskokin su guda tara-tara "wanda yake bayyanawa a sarari daga ƙabilar da suke na barebarin usul " bayan hakan kowaccen su kamannin ta daban ne ,

Babbar su tana ɗiban yanayi da uwar su "watau fara ce sol yanayin hasken mutanen da suka so zama Zabiya ( albino ) yayin da ta tsakiyar take da rangwamen hasken fata ,karamar kuwa baka ce sosai kamar mahaifin su , Da alamu dukkanin su dogaye ne samɓala-Samɓala duk da cewa suna kan shekarun kuruciya sosai "yara ne " .

Cikin yaren su karamar ta cewa babbar ta kawo mata gurji daga gona, shafa kan ta tayi cikin nuna kauna tace zata kawo mata daga haka ta juya ta nufi ɗakin su tare da sako wani ɗangalallen hijabi cukurkuɗaɗɗe yagagge bakikkirin da shi ta kuma zagaya bayan ɗakunan nasu ta ɗauko wani buhu da alama abubuwan bukata a gona ne a ciki.


Duk abun da ake mahaifiyar su tana zaune bata umm "bata a ah ,sai faman girgiza jaririn ta take da sigar lallashi "shima fari ne sol irin ta amma ita fuskar ta babu zane irin na ƴaƴan ta ga alamu ita ba babarbari bace , kamar yadda yaran da mahaifin su kana kallon fuskar su zaka shaida yaren su .


Sun zo zasu fita ita da mahaifin su mahaifiyar su ta miƙe ta rako su bakin zubabbiyar katangar da baza'a ce mutane na rayuwa cikin zagayen ta ba , a bakin labulen tsunman da aka kare wawakeken giɓin da ya kasance mashigar gidan ( ƙofa ) , ta tokare sannan ta ɗaga hannu cikin maganar kurame tana musu alamar a dawo lafiya ta hanyar jujjuya tafufukan hannun ta (bye-bye) tare da yin gwalatu cikin maganar bebaye," wanda hakan shi yake bada tabbacin KURMA ce ( kallo ta bisu da shi fuskar ta ɗauke da murmushin da sai ita kadai ta san dalilin yin sa a cikin wannan yanayin da su ke ciki ) .


Sun dauki tsawon lokaci suna girbi cikin ƙatuwar gonar su da take wajen gari ,Suna hirar su da kana ji kasan akwai soyayya da shaƙuwa me karfi tsakanin uban da ƴar sa kafin lokacin da yakaka ta cewa mahaifin su zata je kama ruwa (Ban ɗaki ) , ta juya gami da shiga cikin dogayen shukokin masarar da suka fidda kai suna jiran girbi , tana tsugunne cikin duhun gonar ta fara jiyo kabbara tare da iface-ifacen mutane .


Ta miƙe da sauri tana sanya ɗan kanfai (wondon ta ) , lokacin da taji mahaifin ta yana kwala kiran neman ta da sauri ta nufo wurin da taji muryar sa , ita ma ta buɗe murya tana kiran sa tare da shaida masa ta dai-dai wurin take , wata razananniyar karar da taji tare da sake kusantowar kabbara da hayaniyar mutanen nan shi ya sake sa ta ruɗe .


Duk da bata san bindiga ba a zahiri amma tasan karar nan da take ji na abu me cutarwa ne , har zuwa lokacin da taji muryar mahaifin ta cikin ƙaraji yana cewa ta kwanta kar harbin bindiga ya same ta , ai sai ta sake ruɗewa ta nufo inda ta ji muryar sa cikin gunjin kuka da kiran sunan sa .


Shi kuma jin ta nufo shi ya sanya ya miƙe daga kwanciyar da yayi dan gujewa harsashi ,ya nufi inda yake jin kukan ta cikin tsoron kar harsashi ya same ta ko kuma ƴan tawayen su ganta su harbe ta ko su tafi da ita ( kamar yadda suka samu labarin hakan na faruwa a sauran garuruwa da ƙauyukan borno ƳAN TAWAYEN BOKO HARAM sun addabi mutanen ƴankin arewacin nigeria musamman jahar Borno da kewayenta wanda a nan mafarin abun ya ke. ) yana miƙewa yayi taku ɗaya biyu a na uku yaji kamar wani abu me karfi ya wuce ta jikin sa ya ɗauke shi yayi jifa da shi , yaji jikin sa kamar ba nashi ba .2


Dai-dai lokacin da Yakaka ta ci tintiɓe da shi da sauri ta sunkuya gami da kamo shi ihun da ya ga ta sa tare da daura hannun ta akan kirjin sa yaga ta ɗago hannun na ta face-face da jini, shi ya tabbatar masa cewa harsashi ne ya same shi ,a take ya fara salati da karanto ɗukkanin addu'o'in da suka zo kan sa a lokacin .


STORY CONTINUES BELOW

Ita da kanta baza ta iya kiyasta tsawon lokacin da ta ɗauka a zaune rungume da gawar mahaifin nata , wanda tun bayan da harsashin ya same shi bai sake ko minti goma ba ya rasu . ( Yaa Allah ya jikan dukkanin ƴan uwa musulmai da suka rasa rayukan su a sanadin annobar Boko haram Ameen )21


Tayi kuka har hawayen ta ya ƙafe har tunanin ta ya tsaya , ta gigice iyakar ɗimaucewa ,ta rasa hankalin ta a tsakiyar gonar rungume da gawar mahaifin ta wanda jinin sa ya bata mata jiki face face ,har wani wuri ya fara bushewa a hankali ta ɗaga kanta ta dubi yadda dare ya fara alamun shigowa rana ta tafi zata faɗi ga kuma hadarin da yake haɗowa, cikin shishiƙar kuka ,jiri da tsananin galabaita ta ɗaga kan mahaifin nata da tun kafin rai ya kammala fita daga jikin sa ta ɗora kan sa a kan cinyoyin ta a gaban idanun ta ya rasu ,ita ta ke bashi kalmar shahada duk da karancin shekarun ta , cikin wani irin kuka ta sake mayar da kan nashi ta ajiye bisa cinyoyin nata tare da sake rungume gawar shi ( da ta Riga ta fara ƙanɗarewa ) tana wani irin shishikar kuka , ta ɗau tsawon lokaci a haka sannan ta sake ɗagowa tare da zare hijabin kan ta ,ta shimfiɗa cikin karfin zuciya ta sauke kansa a hankali daga jikin ta ta ɗora akan hijabin nata, kuma ta ɗauki lokaci tana yi masa addu'a.


Sannan ta mike a zabure ta juya cikin hanzari ta nufi hanyar gidan su domin ta sanar tana tafe tana waiwayen duhun ciyawar da ta riga ta kare gawar mahaifin nata , har dai ta zura da gudu tana kuka tana sharar hawayen ta.


Birki ta jaa tare da rage takun tafiyar ta lokacin da ta bullo bakin hanya , hakan yana da nasaba da guje guje gami da iface-iface da ƙarar harbe-harben da take ji yana tashi daga ainahin cikin ƙauyen nasu , kowa ta nufa da gudu domin ta tsaida shi tayi tambayar me ke faruwa sai taga an bangaje ta an wuce da gudu wasu na kuka wasu na salati da addu'o'i wasu kuwa kana ganin su ma kasan gudun ceton rayukan su suke domin dai duk sun kukkuje sun ji munanan raunika ,amma ahaka suke gudu suna barin ainahin cikin ƙauyen nasu zuwa cikin gonaki da daji.2


A hankali ta ɗaga kanta sama tana iya hango yadda sararin samaniyar ƙauyen nasu ya tuniƙe da hayaki har ma tana iya hango harshen wuta da yayi tsiri yake toroƙo a wasu sashi na cikin garin, nan take wani irin tsoro da tashin hankali ya mamaye zuciyar ta tunowa da mahaifiyar da kannen ta da tayi suna cikin ƙauyen nasu ,da yanzu take hango tarwatsewar sa da mummunan bala'in da ya fada musu .


Cikin karfin zuciya ta yunƙura da gudu ta nufi hanyar gidan su , tana ta cin gware da karo da mutanen da suke gudu daga cikin garin( amma ko kula bata yi ba) zuwa lokacin da ta ji carafa an kama hannun ta da karfi an fusgo ta, da sauri ta waiwaya tana fatan ko ɗaya daga cikin ƴan gidan su ne "mamar su ko ƙannen ta.


Amma sai taga modu ne saurayin da unguwar su ɗaya ɗan maƙotan su ne , cikin sauri ta dawo da baya tare da rike hannayen sa biyu tana haki ,fuskar ta ɗauke da matsanancin tashin hankali take tambayar sa ina mamar ta ina kannen ta ? Amma maimakon ya bata amsa sai taga yana jaan ta da gudu su koma hanyar da ta bullo , da karfi ta fisge hannun ta tare da yi ma sa tsawa tana sake maimaita tambayar ta "Modu nda mamanyi nda kiramiyanyi " ?

Yakaka yanzu ba lokacin tambaya bane domin rayukan mu suna cikin haɗari , ban san inda suke ba , ki zo mu gudu yagana, kashe mutane ƴan tawayen BOKO HARAM suke sun yanka babanmu ,da yaa bakura sun tafi da Fannah da yaakori "(kannen sa) " maman mu ban san inda take ba ita da sauran kannen mu ,sun ƙona gidan mu da gidan ku da ....


Tunda ya fara nisa cikin bayanin sa ta daina fahimtar me yake cewa , zuciyar ta ta tafi ga tunanin me yake faruwa da su ne ?, ta yaya zata rasa kowa da kome nata a yini ɗaya ? Baban ta ya mutu , bata san inda mahaifiyar ta da kannen ta suke ba a mace suke ko a raye ? Ina zata je ? Bata da kowa bata san kowa ba bata taba zuwa ko'ina ba babu inda ta sani bayan ƙauyen su , a hankali ta juya tana nufar cikin garin su hanyar unguwar su cikin ran ta tana aiyanawa gwara ita ma a kashe ta gwara ta mutu .


STORY CONTINUES BELOW

Bata da karfin jiki da na zuciyar tunkarar wannan sabuwar rayuwar da take tunkaro ta wacce bata hango kome a cikin ta ba sai tarin tashin hankali wuya da wahala ,maraici da rashin madafa .


Da karfi modu yake kwala mata kira yana so ta dawo su tafi domin shi yaga irin bala'in da bata gani ba da yake cikin garin wanda mutuwa ce murarar ta , mutuwar ma ta walakanci wanda aka harbe da bindiga ya mutu shi ya ji daɗi akan waɗan da aka kwantar aka yi wa yankan rago da waɗan da aka sanya wa wuta suka kone kurmus ,da waɗan da aka jefawa bom yayi kaca-kaca da su .3


Dan haka ya kasa bin ta ya taro ta "duk da cewa akwai boyayyar soyayyar Yakaka cikin ransa wanda bai kai ga bayyana ta ba" amma baya jin matakin son da yake yi mata ya kai wanda yake yiwa ransa da rayuwar sa baya jin zai iya salwantar da ran sa domin taya ta neman iyayen ta, dan haka ya sake juyawa da gudun gaske yayi gaba ba tare da ya sake waiwayar ta ba ,2


Cikin rashin sanin inda take sanya kafafun take tafiya kunnuwan ta sun toshe daga jin hayaniyar da ta cika duniya, tunanin ta ya bar gangar jikin ta ta yadda har bata jin turewa da bangajewar da mutane suke mata , wanda yawancin su daga unguwannin da suke ƙasa da tasu unguwar suke fitowa wanda a halin yanzu ƴan tawayen suke far musu ,.baza ta ce ta yaya aka yi ba kawai taga kanta ne a gaban rugujajjen ƙonannen gidan nasu da har yanzu ta wasu wuraren wutar bata gama mutuwa ba domin tana iya hango hayakin da ya ke turnuke da gidan .

Da gudu ta taka ta shiga gidan tana kwalla kiran "mama "yaana "falmata " shiru taji babu motsin kowa , cikin tashin hankali take kallon tsakar gidan nasu da yake a hargitse kamar sansanin yaƙi , kome baya muhallin sa duk da daman su basu da kome a cikin gidan nasu sai tsumokarai da ƴan tsofaffin kayan aikin su na gida wanda su ma a halin yanzu duk a ƙone suke idan ka dauke randar su da take binne cikin ƙasa da gudu ta nufi ɗakin su duk da hayakin da take hangowa cikin ɗakin ta saman sa wanda rufin zanar ya riga ya cinye ,ya zama saman a buɗe yake wayam, hakan bai hana ta cusa kanta cikin ɗakin ba babu kome cikin ɗaƙin sai burbuɗin tokar wutar da ta gama cinyewa , bakikkirin hayaƙin ma daga kan guntun kayan su ne da ya gama ƙonewa ba jimawa yake tashi .


Durƙushewa tayi ta saki wani irin kuka da yake fita daga karƙashin zuciyar ta ,kukan maraicin da ya same ta a rana daya , kukan rasa komen ta da tayi , kukan sabuwar Rayuwar da take FUSKANTA .


Ta ɗauki tsawon lokaci tana kukan nan har zuwa lokacin da ta fahimci hayaniyar da ta cika garin nasu ta fara raguwa sai tsilla tsilla take jiyo ihu da wucewar mutane a guje , har zuwa lokacin da ta tabbatar dare yayi , ganin duhun da ya mamaye sararin samaniya , da sauri ta miƙe tunowa da tayi bata yi sallar azahar, la'asar, da magarib ba ta kuma tabbatar lokacin isha'i ya yi tana son yin addu'a ta sani bata da kowa bata da kome a yanzu sai Allah dan haka gun shi zata kai kukan ta .


Tana fitowa tsakar gidan ta rasa abun da zata yi alwala da shi ,( sakamakon duhun da ya mamaye tsakar gidan, ) da taimakon hasken walƙiyar da take ta haske sararin samaniya, ta hango wani bakin kwanon da duk wuta ta kone sa wanda ada shine kwanon da suke ji da shi duk gidan kuma shine kwanon cin abincin baban su .


Da gudu ta karasa ta ɗauki kwanon ta rungume tare da fashewa da kukan tuno mahaifin ta da gawar sa take can a cikin gona bai samu ko darajar suturtawa a kai sa makwancin sa ba .


Bayan ta share hawayen ta takarasa tare da buɗe randar su wacce ita ƙadai ce ba'a tarwatsa ba a gidan su ,"dalilin tana binne ne cikin ƙasa" ta sunkuya tare da buɗe randar , hawayen idanun ta da suka ƙi tsayawa suna ɗiga cikin randar , ta yi goho tare da sa kwanon cikin randar da nufin ɗibo ruwan ciki amma sai taji hannun ta ya tokare bai karasa ƙasan ba sannan kwanon ya bigi wani abu a cikin randa a firgice ! Ta mike jikin ta yana rawa tafara jaa da baya ,tana tunanin menene a cikin randar ?


Ji da tayi kamar wata karamar dushashiyar murya tayi magana Daga cikin randar da ya sanya ta sake shiga cikin fargaba !, kuma kamar wacce aka zabura ! Sai ta nufi randa da gudu gami da durƙusawa ta leƙa cikin randar zuciyar ta cike da zumuɗin Allah ya sa tunanin ta ya zama gaskiya .


STORY CONTINUES BELOW

Ai kuwa da sauri ta sa hannu gami da taya ƴar uwar ta ta fitowa daga cikin randar da tayi maboya a ciki wacce bakin ta ya riga ya guntule ya farfashe daga sama , tana gama taya ta fitowa ta rungume ta cikin kuka yakaka take tambayar Falmata ina mamar su ? ina sauran ƙannen su ?


Cikin kuka da dushewar muryar da bata fita sosai tsabar kuka take cewa lokacin da muka fara jin harbi sosai sai mama ta ɗauki bulama da yaana, ni kuma ta saka ni cikin randa "saboda tasan bazan iya gudu da sauri ba dan bana GANI " ta ce min zata kai su yaana gona ta boye su ta dawo nima ta ɗauke ni , shine har yanzu bata dawo ba, Yakaka ina baban mu ? Ki kaini gurin sa ya nemo mana mama da su yaana ,,, ina jin tsoro dazu naji mutane har gida suna neman mu inajin ihu a gidan su modu da gidan su yanziye naji suna ihu da cewa wuta wuta , ana ta kuka da salati ina ji ana harbin mutane , meye yake faruwa yau a garin mu ?1

Jin shiru ya sa falmata ta fara lalube har ta kama hannun yakaka wacce tun da falmata ta fara bayanin take kuka , kukan mutuwar mahaifin su , da batan mahaifiyar su da ƙannen su , kukan tausayin falmata da take MAKAUNIYA , marar gata marar galihu , daman gatan su Allah sai kuma iyayen su to gashi sun rasa su a lokaci ɗaya , ba iyaye kawai suka rasa ba har da dangin su ƴan uwa , makota da abokan arziki , gidan su da garin su baki ɗaya , dan ko ba'a fada musu ba ta san garin su ya tarwatse , hakan yana nufin sun rasa kome nasu .


Wani irin kuka me karfi ne ya kwace mata ta sake rugume kanwar ta tsam-tsam tana jin bata da kowa bata da kome sai Allah sai FALMATA KANWAR TA ,


Kukan su ya tsannanta lokacin da yakaka ta gama sanar da falmata kome game da mutuwar baban su , kuka suke an rasa me rarrashin wani a tsakanin su , ga wani irin mugun tsoro da zukatan su ke ciki na rashin jin motsin kowa a unguwar su kusan ma garin nasu baki daya , ga baƙin hadarin da ya hado bakikkirin wanda ya kara wa sararin samaniyar garin da dare ya riga yayi duhu sai walkiya da cida ,alamun ruwan sama gaf yake da fara zuba .


A hankali yakaka ta ɗago falmata daga jikin ta tana share mata hawayen da suke zubowa daga gurbin idanun ta wanda idan ba an fada maka ba ko kuma ka lura kaga yadda suke tsaye kem alamun basa amfani uwa uba kagan ta tana lalube , baza ka taba cewa bata gani ba domin tar idanun ta biyu suke a buɗe ,ko meye sanadin makantar ta ? Ko haihuwar ta aka yi da shi ?

Ɗaga kai tayi ta sake kallon sama tana tunanin ina zasu samu mafaka daga dukan ruwan saman da yake daf da tsugewa , da sauri wata dabara ta faɗo mata cikin dusashiyar muryar tace falmata muyi sauri muyi sallah kin ga ruwa za'a fara ke kuma kin san kina rashin lafiya idan ruwan sama ya doke ki "zazzabi da mura" dan haka idan mun idar da sallah sai ki koma cikin randar ki bani hijabin ki na haɗa da zani na na rufa a bakin randar sai na daura murfin "wani ƙuzajjen farantin kwano ne" na rufe ki a ciki zuwa lokacin da ruwan zai tsaya sai musan in da zamu yi .


gƴada kai kawai falmata tayi , cikin sauri-sauri suka yi alwala suka duddungura sallolin su wanda kana gani kasan akwai ƙarancin ilmin addini a tare da su, ko kafin su gama an fara yayyafi da karfi da ya sanya yagana yanke doguwar addu'ar da ta fara ta kama hannun ƙanwar ta tare da kama mata ta koma cikin randar .


ko kafin ta gama toshe mata bakin randar ruwan ya riga ya tsinke, cikin hanzari ta gama rufewa ta tsugunna a bakin randar daga ita sai rigar ta da ɗankwali sai kuma siket ɗin ciki, haka ta takure jikinta ruwan nan yana dukan ta , ta ɗaura kanta akan gwaiwar ta hawaye yana sauka a idon ta tare da zubar ruwan saman da yake sauka a fuskar ta yana wanken hawayen da yake sauka, bakin ta ɗauke da addu'o'i iri-iri da take yin su cikin yaren ta.3


Ruwan saman sai yayi kamar zai tsaya sai kuma ya sake tsugewa , a hankali sai da tsakar gidan su ya cika taf da ruwa, " kamar yadda ya saba" cikin karamar muyar falmata ta ankarar da yakaka wacce ta yi nisa cikin tunani har bata jin yawan ruwan da ya haura idon kafar ta ,"ruwa ya fara shigowa cikin randar yakaka,' cikin tashin hankali da sauri ta zame dankwalin kan ta ta matsa ruwan jiki ta sa dankwalin ta toshe hudar jikin randar da ruwan ya ke tsiyaya ciki ta ɓulin,

Ta sake tsugunnawa gami da takure jikin ta cikin jin matsanancin sanyi da wani ciwon kai da suka dirar mata lokaci daya , hakoranta sai karo da junan su suke tsabar karkarwa,

a hankali ruwan ya fara tsagaitawa bayan kwashe kimanin awa daya da kusan rabi ana tsugawa , sai iska me karfi da matsannancin sanyi ne yake busawo tare da sauran feshin ruwan saman .


MARAƊi Niger République


Jihar maraɗi itace cibiyar kasuwanci a kasar Niger wacce Allah ya albarkace ta da masana'antu , masu kudi, da ma'aikata sanan kuma tana daya daga cikin garuruwa na kudancin Niger karkashin manyan garuruwan kasar hausa kuma ta kasance karkasin mulkin katsina shiyasa ma ake mata lakabi da katsinar maradi domin katsina ta mulke ta tun lokacin yakin kasar hausa kuma hasalima yanzu idan za a kira sarautar maraɗi sai ance sarkin katsinar maraɗi.1


Kenan zamu iya cewa maraɗawa katsinawa , tun asali Maraɗi tayi yake yake sosai a kasar hausa inda taci nasarar wasu garuruwa wasu kuma su ka bata kashi amma dai tarihi ya nuna bamaraɗe jarumi ne kuma baya tsoro wanan shi yasa ta bunƙasa har zuwan turawan mulkin malaka a kasar hausa inda suka sha gwagwarmaya da turawa a wancan locakin ,a zamani sarkin katsinar maradi tsakanin shekara ta 1892 zuwa 1894 .


Bayan jihadin sheik usmanu fodio inda ya yaki sarakunan kasar hausa ya kuma jaddada addinin islama a wanan nahiyar ya kuma canza sarakuna da dama musaman wadanda suka bijirewa kaidodin sa maradi ta shiga cikin jerin kasashe da wanan abu ya ritsa da su

Kuma tasamu sarakuna 23 Tun daga kan Sarkin katsinar maradi Dan kassawa 1817, 1830

Har izuwa kan na yanzu .


Wannan kenan

Cikin Tafkeken falon wanda yake ɗauke da kayan ado da alatu , irin wanda ake samun su kaɗai gidan sarakai ,cikin masarautu irin namu na gargajiya ,

Mutane biyu ne cikin falon Mutumin da kallo daya za'a yi masa a hango girman cikar kamalar sa ,kasaitar sa da mulkin da ke gare shi yana zaune kan ɗunɗumemiyar kujerar da take ware daga tsakiyar falon tana fuskantar duk me shigowa cikin falon .

Gefe da gefen kujerar ƴan kananun teɓurin gilas ne dayan teburin saman sa ɗauke yake da ƴaƴan itatuwa nunannu lafiyayyu tun daga kan inabi,ruman ,zaitun,tuffa,tanjari, da sauran manyan ƴaƴan itatuwa masu daraja , ɗayan teburin kuwa ɗauke yake da wata kyakkyawar butar shayi da take kan wani babban farantin da suka zo tare ruwan zaiba tare da kananun kofunan ta da chokulan da daga gani du tare suka zo ,

Daga kasa kuma tsakanin kewayen manya-manyan kujerun da suka yiwa tafkeken falon ado , wani dogon saurayi ne wanda bayan sa kawai za'a kalla a gane tsawo da cikar halittar sa ta ɗa namiji kansa a sunkuye ,kafafun sa a tanƙwashe yayi zaman raƙumma gaban wannan mutumin yana sauraran duk wasu kalamomi da suke fitowa daga bakin sa ɗaya bayan ɗaya , da yake cewa ,


YOUSSOUFA na samu sakon bukatar da Ka zo da shi ,sai dai ina bukatar jin ƙarin bayani daga gare ka ,? Cikin kwantar da murya wanda aka kira da youssoufa ya ce ranka ya dade kamar yadda na fada wa jakadiya , wani aiki ne ya taso daga gwamnatin kasar nan wanda ta zabi sojoji kimanin dubu ɗaya da ɗari biyar, ta kuma wakiltani a matsayin shugaban su da zan jagorance su zuwa kai tallafin gaggawa ga yankin makociyar mu kasar Nigeria akan ƴan tawayen nan na boko haram da suka addabi yankin arewacin kasar wadda idan muka yi wasarere mu ma annobar tana iya shafar kasar mu nan Niger saboda boda da makoftakar da muke da juna ta kurkusa ,ya ɗan tsagaita gami da ɗaga kai ya kai kallon sa ga fuskar mutumin da ya zuba masa ido yake saurarar sa da dukkan hankalin sa.


Sake sunkui da kai yayi gami da cigaba da cewa shine nake neman alfarma akan a ɗaga biki zuwa lokacin da zan dawo wanda nake tunanin ba zai gaza nan da shekara ɗaya ba , do Allah ayi mini alfarma mai Martaba ,"ya karasa furta hakan cikin marairaicewa da kwantar da murya " ?


Ɗan gyaran murya yayi kafin yace ,wagga lamari naka da ban mamaki ike kai youssoufa anya aikin taimakon ƙasa zai wucce raya sunnah ? ɗan jim yayi ɗaga bisani yace tashi kaje du shawarar da muka yanke tana iso maka ta hannun jakadiya ,


Ras-ras yaji zuciyar sa ta tsinke tun da Mai Martaba yace sai yayi shawara yasan bai gamsu ba bai amince da alfarmar da ya nema ba hakan yana nufin bazai amince masa ya tai zuwa nigeria wanda kuma hakan yake dai-dai da rasa aikin sa da tun da yayi wayo a duniya ya san soja ya kasance bashi da wani burin da ya wuce ya zama SOJA , duk da kasancewar sa ɗan sarki kuma BIYAMARADI , haka ya dunga kawar da duk wasu kalubalen da zasu shiga tsakanin sa da cikar burin sa ya shaa gwagwarmayar da ta kawo sa kan matsayin da yake na yanzu me amsa cikakken sunan COLÓNEL YOUSSOUF ABDOUL AZIZOU BASKORE !!!!!!!....

Cikin sanyin jiki tare da rashin kuzari yake takawa yana wuce zauruka da sashi sashi kamar yadda aka San tsarin ginin masarauta yake.

Jerun gwanon bayin sa su rai biyar suna biye da shi tun daga ƙofar fada inda ya amsa kiran Mai martaba , tafe yake cikin kasaitar da ta amshi tsarin zubin sa na ingarman namiji dogo da ya kere dukkanin mutanen da suke tare da shi tsawo a lokacin.

fuskarnan tasa a murtuke kitib ya fito a SOJAN sa sak kuma BIYAMARADI, baya ko amsa gaisuwar bayin da suke ta faman zubewa a ƙasa suna kai gaisuwar su tare da kirarin da suka saba yi masa.

Biyamaradi dan sarki mai jiran kujerar mulkin kassar mu

albarka, kayi gadon mai martaba. Biyamaradi jarumin jarumai, biyamaradi namijin, ayi yau ayi gobe sai gaskiya jibi rago ya kassa.

Dan sarki mai makaman yaki, Dan sarki mai ado.

Biyamaradi kai zaki ne mai watsar da taron maza Dan sarki mai tarin illimi to kayi ga arabi ga boko wallahi ka kure tunanin Masu tunani.

Allah.ya kare ka gwani na hattara biyamaradi. hattara biyamaradi. Hattara biyamaradi HATTARA BIYAMARADI 1
Sai dai ga Biyamaradi yousoufa a yanzu sam basa burge shi basa sanya shi nishaɗi , babu abun da yake sanya shi nishaɗi a yanzu irin karar kafafuwan sojojin da suke jaan tunga su ƙame masa idan sun hango shi , babu muryoyin da suke burge shi irin na amsawar sojojin da ke karkashin ikon sa idan ya basu umarni ,

Dai-dai ya zo shiga sashin sa da yake bangare guda ko kuwa ɗaula guda a cikin gidan nasu ya ga wani hadimin sa ,wanda yana karasowa wajen ya zube ƙasa yana ƙirari tare da kai gaisuwar sa , bayin da suke tsaye a bayan sa su suka amsa da " Biyamaradi ya amsa gaisuwar ka meke tahe da kai ? " yana daga durkushe yake isar da sakon dalilin tsayuwar sa anan "jakadiya" ce tace ya zo ya jira shigowar yarima ya koma ya sanar da ita .

yana jin abin da bawan nan ya faɗi ya sanya kansa gaba gaɗi ya shiga gidan sa tare da yi wa bayin alama na kadda su biyo bayan sa , ( domin shi ya tsani taron bayun nan da suke zuwa du su zagaye shi su hana shi sakat ko wanne motsi yayi idanun su na kai suna yi masa surutun banza"kirari" a cewar sa)
babu wanda ya motsa daga inda yake cikin bayun nan domin idan da sabo yaci ace sun saba da tsarin halayyar BIYAMARADI"
Yousoufa shine ɗa na biyar a wurin mai martaba ɗa na huɗu a wurin mahaifiyar sa , kuma ɗa namiji na farko a gidan baki ɗaya , mahaifiyar sa ɗiya ce ga sarkin birnin gaoure, ita ce ƴa ta biyu cikin jerin ƴaƴan mai martaba Lamiɗo " Bafullatana ce gaba da baya kamar yadda kowa yasan birnin gaoure garin hullanin usul ne ,
Mahaifiyar yousoufa da mai martaba(sarkin maraɗi ) auren so da kauna suka yi , tun lokacin mai martaba bai kai ga hawa kujerar mulkin birnin maraɗi ba suka haɗu a wurin bikin yaye ɗalibai ƴan makarantar gaba da primary ta makarantar "École Bedir" da ke birnin Niamey a wancen zamanin da sai ƴaƴan wane-da-wane ke yin makarantar ,kanwar mai martaba " Zainab tana cikin ɗaliban da aka yaye a wannan shekarar ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da tara 1979, "wanda shi mai martaba Abdoul azizou ya wakilci mahaifin su wajen taron a lokacin shi ɗalibi ne a jami'ar Abdoul Moumouni Diof da ke nan cikin birnin Niamey"

STORY CONTINUES BELOW
Anan yaga safiyya , tana ɗaƴa daga cikin ƴan matan da aka zaɓa domin su gudanar da ƴar kwarya-kwaryar wasan koikoyo da akan yi lokacin bikin yaye ɗalibai , kallo ɗaya yayi wa ƴar fulanin yaji ta kwanta masa ya kuma ji cewar ya samu matar aure ,
Bai yi ƙasa a gwaiwa ba ya sanarwa zainab tare da gwada mata yarinyar daga nesa lokacin da aka kammala taron ana shirin watsewa nan take kuwa zainab ta shaida ta domin ta san safiyyah farin sani hasalima tamkar kanwar ta take domin koh lokacin da aka kawo safiyyah ajin farko a makarantar ita kuma tana aji na uku a lokacin ɗakin kwanan su guda su biyu ne rak a ɗakin kasancewar haka tsarin ɗakunan kwanan ɗalibai na makarantar yake, mutane bibbiyu ne a kowanne ɗaki , sun shekara guda tare cikin aminci har zuwa lokacin da ita zainab ta shiga ajin manyan ƴan secondry "aji huɗu" a lokacin ne aka sauya mata ɗaki ta koma saman bene a hawa na farko ,

Hakan ne yasa koh da yayan ta ya nuna ra'ayin sa akan safiyyah taji dadi sosai kuma ta wuce masa gaba ta gabatar da shi a wurin safiyyah duk da cewa dai ita a lokacin ne ma take aji na huɗu , Amma tayi na'am tare da maraba da bamarɗe Abdoul azezu .

Haka dai tafiya sannu-sannu suna tare cikin aminci da so da ƙaunar junan su har zuwa lokacin da safiyyah ta kammala karatun gaba da primary a shekarar mai martaba sarki Youssoufa Baskore mahaifin "Abdoul azizou ƴa tura da takardar neman aure da kayan nagani ina so ga masarautar sarki lamiɗo na barnin gaoure inda shima bai yi kasa a gwaiwa ba ya amsa cikin tsantsar farin ciki da lamarin "domin a garesu hakan babbar nasara ce kasantuwar kowa ya san sarautar maraɗi ita ce ta biyu a karfin mulki kaf kasar niger "
Aka tsaida ranar auren su sha biyar ga watan satumber na shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da ɗaya "15-sept-19981, rana ta zo aka sha biki amarya ta tare a gidan mijin ta sasahi guda a cikin gidan sarautar maraɗi .

Kwance tashi rayuwar su ta fara miƙawa cikin aminci fahimtar juna da tsantsar ƙaunar junan su , Allah ya Albarkace su da haihuwar ɗiya mace shekara ɗaya da auren su wacce ta ci sunan marigayiya mahaifiyar su Abdoul-azizou wacce ta jima da rasuwa tun su na yara ,"Halimatu'sa'adiyyah" ana kiran ta "Ammi"

Tsakani shekara biyu cif da safiyyah ta sake haihuwar ɗiya mace aka sanya mata sunan mahaifiyar safiyyah "Suwaiba" ana kiran ta "dada "
Bayan watanni tara da haihuwar "dada "
safiyyah ta sake samun ciki ta haifo "zainab" wacce ta ci sunan kanwar Abdoul-azizou sai ake kiran ta "ubbo"
Tun daga nan fa sai mai martaba sarki Youssoufa ya ce Abdoul-azizou sai ya sake aure koh ya samu magaji tun da ga alama matar sa uwar ƴan mata ce , babu yadda Abdoul-azizou bai yi ba akan ya fahimtar da mai martaba haihuwa kyautar Allah ce babu ɗiya mace koh ɗa namiji dukkaninnsu ɗaya ne har kullum masu albarka ake nema .

Sai dai fir mai martaba yaki saurarar sa domin a gefe guda "hajiya uwa " da takasance matar sarki ta biyu "wacce take matsayin babbar matar sarki tun bayan rasuwar mahaifiyar su Abdoul-azizou " a lokacin ta samu wuri sai daɗa hura wutar kiyayyar ɗiyoyi matan da ake haihuwa a gidan abdoul-azezu take " a cewar ta sarauta ta kama hanyar barin hannun Baskore tunda ga alamu Sarautar tana dakatawa ne akan Abdoul-azizou da yake a matsayin yarima a lokacin ,

Ba tare da neman shawarar Abdoul-azizou ba mai martaba ya nema masa Auren ƴar abokin sa kuma yayan matar sa "Hajiya uwa "Babban Limamin Maraɗi "Malam muhammadou" wacce ake kira "Saratu " .

Tare da sa hannun hajiya uwa wacce tayi ɗare-ɗare akan harkar bikin nan tayi uwa tayi makarɓiya , ranta ƙwal ! tana ƙitsimawa "idan sarauta ta kuskure masu ta wani wuri kasancewar ita bata taɓa haihuwa ba toh tabbas ga sarautar nan dawo masu ta wani hannu " tana da tabbacin daga saratu ta zo ta haifi ɗa namji shikenan sarauta ta zamto tasu.

Saratu ita ce ɗiya ta shiddah cikin jerin ƴaƴan Liman muhamdou , mahaifiyar ta tun tana ƴar shekaru biyu suka rabu da mahaifin ta "mahaifiyar ta ƴar Nigeria ce a can wani gari da ake kira zuru a ƙasar kebbi Nigeria , Saratu ta taso tsakanƙanin matan uba , babu irin izaya da wahalar da ba'a gana mata ba , shi ya sa ta tashi a kangare sannan me mummunar zuciyar da take cike da ƙudirin ɗaukar fansa,2

STORY CONTINUES BELOW
Lokacin da ta shekara goma sha biyar ta kasance fanɗararriyar yarinya ce ta kin ƙarawa wacce tun da ta fara girma ta buwayi matan mahaifin nata da fitsara da raini uwa uba saratu ta kasance me matukar fasahar iya shirya zancen ƙarya da tuggu domin ta tada husuma a tsakanin matan mahaifin ta duk a cikin mummunan ƙudirin ta na ɗaukar fansa .
A take -take zata haɗa zantukan ƙarya ta ɗora mutum kome girman sa akai kuma ya hau ya zauna daram , saboda tsabar yadda ta iya shirin ƙarya , wasa-wasa sai da ta maida gidan mahaifin ta sansanin yaki a wurin matan gidan , kullum cikin faɗa ake kamar garken karnuka , ita kuwa ta koma gefe tana wake-waken ta ,bayan idanun su ta shiga ɗaki ta ci dariya son ran ta ta fito tsakar gida tana karya wuya tare da bai wa wacce ta zuga hakuri .(Saratu kenan , ƴar malam wacce taƙi halin malam )

A tsakanin matan mahaifinta su uku babu wacce ta kai ga fahimtar hallayar saratu na karya da munafurci "sakamakon rashin haɗin kan su tare da zazzafan kishin su tun asali " sai shi mahaifin nata ne da kan sa ya fahimci "saratu ita ce matsalar gidan sa " yana tunanin yadda zai iyi ya samu ya kawar da ita daga gidan sa "( ya aurar da ita ) .

Sai ga sakon kira daga mai martaba "Liman bai yi ƙasa a gwaiwa ba "ya amsa kiran da ya sanya shi kwanan farin ciki bibbiyu na farko dai farin cikin zai zama surikin yariman maraɗi a yanzu , kuma surikin sarkin maraɗi a gobe idan da rai , uwa uba zai rabu da annobar da ta ke sanya shi fargabar shigar sa gidan sa a kullum,3
Dan haka cikin rawar jiki da murnar sa da ta kasa boyuwa ya amsawa mai martaba sarki youssoufa , ya bawa yarima Abdoul azizou auren Saratu koh gobe ake so a ɗaura ya shirya ,

cikin farin ciki da karamci da aka nuna masa Sarki youssoufa ya tsayar da ranar ɗaurin auren Abdoul azizou da saratu ranar ishirin da biyar ga watan sha biyu shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da tamanin da biyar 25-Dec-1985 .

A daren ranar ya aika aka kira masa yarima abdoul azizou , in da ya sanar da shi hukuncin da ya yanke tare da bashi umarnin ya shirya gobe da Maraice ya je su ga juna shi da saratu ɗiyar liman domin kwanaki ishirin da ɗaya kachal suka rage a ɗaura musu aure ,
Ba tare da yarima Abdoul azizou yana fahimtar sauran kalaman bakin mai martaba ba ya amsa masa gami da yi masa godiya da sallama ya fito daga turakar mai martaban zuciyar sa cike da zogi da raɗaɗin bacin ran tashin hankalin da yake iya hango samuwar sa tsakanin sa da abar son sa "safiyyah "
Tabbas shi yasan yadda safiyyah take tsananin kaunar sa da kishin sa , yasan duk lokacin da ya je mata da labarin auren da aka riga aka nema masa ya kuma zama dole a gareshi ya amsa hannu bibbiyu , kasantuwar bai taɓa musantawa mahaifin sa ba akan duk wani hukunci da ya yanke a rayuwar sa domin shi mutum ne me ilmin addini sosai , yayi karatu sosai arabi da boko ya san irin haƙoƙin da iyaye suke da shi akan ƴa ƴan su hakan ya sa ya kasance ɗa mai tsananin biyayyah ga iyayen sa .

Dan haka a yanzu ma yayi aniyar karban auren da za'a yi masa da hannun aminci duk da cewa shi ba son auren yake ba asalima bai taba kawowa ransa sake yin aure nan kurkusa ba kamar yadda tun da yake bai taɓa son wata ɗiya mace irin son da yake yi wa safiyar sa ba kuma baya jin zai sake son wata ƴa mace irin son da yake yi mata " ya ajiye auren da za'a yi masa a karo na biyu a mizanin kaddara "
Sai dai babbar matsalar sa a yanzu tunanin hanyar da zai bi ya tunkari saffiyah da batun karin auren sa ,"a daren yau din domin baya son ma lamarin ya kwana ba tare da ya fitar mata da hakkin ta ya sanar mata ba a matsayin ta na matar sa da suke zaman aminci , kaunar juna da fahimtar juna " sai dai ya san mata idan aka zo batun kishiya ba dama ne '
Haka dai ya shiga gidan nasa baya sun natsa ya fuskance ta da maganar auren , sai dai ga mamakin sa ,' bata tayar da hankalin ta irin yadda yake zato ba hakan kuwa yana da nasaba da zancen ya riga shi isowa zuwa kunnuwan ta "

STORY CONTINUES BELOW
Abun nufi ta ji zance a cikin gida " abun ka da gidan sarauta da kuma yadda ya kasance hajiya uwa tana ta yamiɗiɗi da zance tana yada magana tare da fiffikar ta ta zata shigo gidan " da farko bata fahimci zancen ba sai da ta tambayi jakadiyar sarki ta wancen zamanin ita ce ta warware mata zare da abawa ta kuma kwantar mata da hankali tare da bata shawarwarin alkhairi da za su taimaka mata.

Amma duk da haka bayan dawowar ta sashin ta yini tayi tana kuka tare da tunanin ƙalubalen da yake fuskanto ta "abu ɗaya ne ya rage mata jin zafi ji da tayi matar da za'a aurawa mijin nata ba ƴar wani babban sarki bace ko kuwa wani hamshaƙin attajirin da kasa ta san da shi ba "
Ƴar Limamin Maraɗi ce hakan sosai ya rage mata zafi kasancewar safiyyah irin ƴaƴan sarautan nan ce masu ji da kan su da nuna isa sosai jinin sarauta na ƙasaita , da iko suke yawo a jikin ta ta yadda take ganin duk wani wanda ba ɗan sarautar da ya kai ya kawo ba a matsayin kasasshe a wurin ta,
safiyyah tana son sarauta tana alfahari da sarauta tana kuma ƙaunar masu sarauta , bata daukar mutanen da basu da sarauta da wani muhimmanci a rayuwar ta .2

Dan haka koh lokacin da ranar da aka yanke na ɗaurin auren Abdoul-azizou da saratu ya zo , aka kuma ɗaura auren cikin kwanciyar hankali tare da bakukuwa kamar yadda yake a al'adar su , sam safiyyah bata bayyana matsanancin tashin hankalin ta ba duk kuwa da cewar abun yana nuƙurkusar ta a karkashin rai !Saboda yadda take kaunar mijin ta sai ga shi a yanzu ya zama nasu ita da wacce take ganin bata kai matsayin ta haɗa kafaɗa da ita akan abun da take so ba .

Hakan ya sa bayan tarewar Saratu "a sashin ta da aka gina mata daura da sashin Safiyyah ta hannun hagu "Sam safiyyar bata shiga harkar Saratu "A ganin ta saratu bata isa tayi gogayya da ita ba " "iyakaci idan sun haɗu a cikin gida 'idan sun je gaishe da hajiya uwa da sauran matan mai martaba biyu "Hajiya mai karamin ɗaki da umma Amarya " " su gaisa da juna sama-sama, sosai ita saratu take jin zafin yadda safiyyah ta tattara ta tare da shirgin ta ta watsar a gefe take nuna kamar bata san ma da zaman ta a cikin gidan ba , "
Hakan yana kona ran ta , domin ita ta shigo gidan ne da nufin ta dunga bi ta ƙasa-ƙasa irin yadda ta saba ( a gidan mahaifin ta) tana tunzura safiyyah tana tada bala'i a tsakanin ta da Abdoul-azizu har dai tayi nasarar dusashe karfin soyayyar da ta lura Abdoul-azizu na yi wa safiyyah ,ta yadda ya kasance idan suna tare koyaushe bakin sa cikin ambaton Alkhairin safiyyah da kyawawan halayenta tare da yabawa safiyyar yake ,"1
Sai dai bata samu damar hakan ba domin duk wata kafar da zata bata damar aiwatar da mummunan nufin ta safiyyah ta toshe "ta hana ta fuska "
A cikin hakan ta fara laulayin ciki bayan watanni biyu da auren su "wanda kuma kusan tare suka ɗau cikin da safiyyah " domin ita ma tana ɗauke da ɗan tayin cikin ta na wata ɗaya " .

Nan fa Saratu ta samu abun yin lanɓo ,kitifiri da feleƙe , ita a dole ga mai juna biyu " cikin yana wata uku su ka fasa Sanarwar ai Malamar jinya a asibitin da take zuwa awo a wancen zamanin ta tabbatar mata da cewa "Ɗa" namiji zata haifa '1

Sanarwar ta fito ne ta bakin "Ɗan Zagii" a karkashin jagorancin "Hajiya uwa "wacce ita ma saratu ce ta yi mata Albishir tare da tabbatar mata da abun da malamar jinyan ta faɗi gaskiya ne "cikin rashin sanin Hajiya uwa cewa zancen ƙarya ce tsagoronta wacce ita Saratu ita ta haɗa zancen ta sakamakon jin wata matar babban likita da suka haɗu da ita wurin awu tana bada labarin injin awun da yake bayyana jinsin jariri tun yana cikin mahaifiyar sa " ( Asalima a wancen zamanin injin yin awun da ke gano jinsin halitar da yake ciki bai riga ya bazu a kasashen africa ba )2
Nan take zance ya kewaya fada har ya isa kunne mai martaba ta bakin jakadiya " sosai mai martaba yayi farin ciki tare da bada goron Albishir me yawan gaske"1
A bangaren Yarima Abdoul azizu shima yayi matuƙar farin ciki da wannan albishir har ma ya gaza boyewa ya bayyana farin cikin sa a sarari gaban idanun safiyyah tare da nuna ɗokin sa akan samun ɗa namiji da zai yi nan ba da daɗewa ba "wanda hakan ya tashi hankalin safiyyah a karon farko tun bayan auren sa da saratu "Amma sai ta share ta taya shi murna a sarari "duk da cewa cikin ran ta taso a ce ita ta haifo magajin maraɗi saboda kaunar ta da sarauta ",

STORY CONTINUES BELOW
Sai dai kasancewar ta ƴar sarauta ta kasance me iya boye hakiƙanin cikin ta, ya sa ba wanda ya fahimci halin da zuciyar ta ke ciki , hatta Saratu wacce take yin duk wani kilbibin ta da biyu 'dan ta turawa safiyyah haushi " ta gaza ganin bacin ran safiyyar .1
cikin watannin girman cikin kafin zuwan ranar haihuwar sa kaf an gama tanadin kayan jarirai na ɗa namiji wanda wasu ma mai martaba da kan sa ya sayo su a tafiyar sa Umrah , tarairaya da kulawa kuwa babu irin wacce Saratu bata samu tun daga kan surukan ta hajiya uwa da sauran matan mai martaba "da kusan suke karkashin ikon hajiya uwa "har zuwa kan shi kan sa mai martaba, da uban gayya yarima Abdoul-azizu wanda shima zuwa lokacin zuciyar sa sosai ta rinjaya ga son haihuwar ɗa namiji sakamakon "janye hankalin sa ta siyasa da hajiya uwa da saratu suke yi "
Wanda har hakan ya soma taɓa amintaccen zaman su na fahimtar juna da su ke shi da safiyyah.

Ranar biyu ga watan ɗaya na shekarar alif dubu ɗaya da dari tara da tamanin da bakwai ,2-jan-1987 Saratu ta wuni tana naƙuda taci wahala sosai , kafin zuwa maraice ta haifo Santaleliyar ɗiyar ta mai kama da ita sak "9

An ɗauki tsawon mintoci uku a ɗakin haihuwar da yake cikin baban asibitin maraɗi bayan bayyanuwar kukan jaririyar da likitocin da suka karbi haihuwar suka tabbatar wa hajiya uwa wacce take tsaye a dai-dai kan saratu tana ta faman jera mata sannu , cewar Saratu ɗiya mace ta haifa har ma suka ɗago Santaleliyar jaririyar da ba'a ce yanzu aka haife ta ba saboda girman ta suka nuna wa hajiya uwa da saratu, shiru ne ya ratsa tsakani kafin Muryar hajiya uwa ta bayyana Cikin cewa".

Saratu kika ce Malamin jinya ya tabbatar miki Ɗa namiji ne a cikin ki ? watau ashe zancen ba haka bane ? ashe dai zance Altine "yayar saratun da suke uba ɗaya " zancen ta gaskiya ne da take cewa ke Saratu ba ƙaramar maƙaryaciyar yarinya bace " ,1
Amma ban yi zaton karyar taki da yauɗarar ki ta kai har haka ba , da har domin rashin hankali zaki yi irin wannan ƙasurgumar karyar da yaudarar a gidan sarauta, toh Maza sai ki tanadi ruwan wanke kan ki a idanun mai martaba da shi kan sa mijin naki , ki kuma tabbatar kin riga kin gama zubda ƙimar ki a idanun mutanen gidan nan ciki kuwa har da bayun da suke karkashin ki , haba saratu me ake da wannan irin karyar taki "1
Saratu dai babu bakin magana sai sharar ƙwalla take "wanda hakan ya jaa hankalin malaman jinyar da suke gyara ta har ta kai su ga tambayar dalilin kukan ta "hajiya uwa" ta faɗe musu biri har wutsiya akan yaudarar da saratu tayi mata da kunyar da ta jefe ta " Malaman jinyar su da kan su sun ga rashin kyautawa, tare da mamaki irin karyar saratu sai dai sun bada tabbacin akwai irin na'urar a kasashen da suka cigaba ,"sai dai koh na'urar ma ba koyaushe take bada bayanin gaskiya ba"( Sanin gaibu sai Allah ) jin hakan ya sa "Hajiya uwa jin wani farin ciki ko ba kome sun samu hanyar da zasu fidda , kan su "
Haka aka gama gyara ta tare da jariryar aka tura su ɗakin da zasu zauna "a lokacin ba'a sallamar mace daga haihuwar ta har sai ta zauna a asibiti kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatar da karfin jikin ta "
Bayan isar su ɗakin hutun kafin jama'ah su zo "Hajiya uwa ta sanar da Saratu shawarar da ta gama yankewa domin samun rufin asirin su ,nan take yanke "ba tare da jaa ba" Saratu ta amince .

Da zuwan yarima Abdoul-azizu "hajiya uwa ta sanar masa da ɗiya mace aka haifa ba ɗa namiji ba ta kuma ɗora da bayanin da malaman jinyan nan suka yi musu na cewa ana iya samun kuskuren inji wurin bayyanuwar jinsin abun da ke cikin mahaifiyar sa "
Ƙwarai yarima abdoul azizu yayi kokari wurin nuna rashin damuwar sa akan kuskuren na'urar da ya riga ya yadda akan cewa an samu " Amma cikin ran sa sam sam lamarin bai mar daɗi ba sun riga sun ƙwaɗaitar dashi son haihuwar ɗa namijin .1

Bayan isar labarin haihuwar saratu "Fada " tare da sabon sauyin da aka samu daga haihuwar ɗa namiji da ake sa ran haihuwar sa zuwa samun labarin haihuwar ɗiya mace , Fada ta shiga Alhini da har hakan ya gaza boyuwa akan fuskar mai martaba ,

STORY CONTINUES BELOW
Haka aka yi bikin suna cikin rashin Armashi bayan dawowar su daga asibitin "inda yarinya taci sunan "hajiya uwa Asma'u " Sau ɗaya mai martaba ya sa aka kai masa yarinyar turakar sa "a washegarin dawowar su daga asibiti" in da yayi mata huɗuba tare da bata suna " tun daga ranar bai sake waiwayar su ba.7

Ga bangaren safiyyah har ila yau dai bata bayyana wani alama ba ta bangaren ta ,na farin ciki koh saɓanin sa akan sauyin jinsin abun da Saratu ta samu . Ita ma tana fama da nata cikin , da yayi wani irin mugun girma fiye da sauran cikin ta guda uku na baya , hakan ya sa da zainab ta zo bikin sunan ɗiyar Saratu "ta nemi da ta ɗauki Zainab "ubbo"(takwarar ta )

Kasancewar tun da aka mata aure a lokacin shekarun auren ta bakwai bata taɓa samun haihuwa ba "sai bari da take ta faman yi " ganin yadda cikin yayi wa safiyyah nawi ga kuma rigamar zainab wacce ba ta kai ga cika shekaru biyu ba a lokacin "sannan gata da jarabar ƙiuya bata yadda da tarin bayu da suke cike da bangaren nasu da ma gidan baki ɗaya "sai jikin uwar ta , ya sa ta nemi tafiya da ita nan take kuwa safiyyah da Abdoul azizu suka bata zainab ɗin ta tafi da ita "
Ranar goma ga watan biyu na shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da bakwai 10-feb-1987 ita ce Ranar da ta zamto ranar farin ciki ranar da baza'a manta da ita ba a tarihin masarautar maraɗi ranar da ta shiga jeru ranakun tarihi, Ranar da aka wayi gari gimbiyyah safiyyah tana nakuɗa , zuwa hantsi ta haihu lafiya " farin ciki ne ya wanzu akan fuskar gimbiya safiyyah a lokacin da malaman jinƴar da suka karbi haihuwar ta su ke tabbatar mata da ta samun Ɗan ta namiji 'Ƙato da shi jazir ya ɗauko hasken fatar ta irin ta fulanin usul yayin da tun kallon farko da tayi masa bayan da "malaman jinyan suka gama wanke mata shi tare da shirya shi cikin kayan jarirai" tana yi masa kallo guda ta hango tsantsar kamannin sa da kakan sa"mai martaba sarki youssoufa " kamar an tsaga kara , kakaf cikin ƴaƴan da ake haihuwa a gidan babu wanda yayi kama da Mai martaba irin wannan jaririn "Cikin nutsuwa ta dunga kwararo masa addu'ar kariya kamar yadda take jin matsananciyar kaunar sa tana kwarara cikin zuciyar ta da wani al'amari mai girma irin wada bata taɓa jin sa akan sauran ƴaƴan ta ba"cikin nutsuwa ta ɗaga shi dai-dai fuskar ta gami da sumbatar goshin sa , da kuncin sa dama da hagu,1
Dai-Dai lokacin da yarima Abdoul azizu ya karaso ɗakin , farin cikin zuciyar sa ya kasa boyuwa daga zuci har zahiri bakin sa ya gaza daina furta kalmomin godiya ga ubangijin sa , ba tare da lura da wurin da suke ba ya haɗa su baki ɗaya ya rungume su , zuciyar sa tana buɗewa tare da sabuwar ƙaunar uwar da ɗan ta ,
Biki sosai aka dunga yi tare da yanke-yanke ana sadaka domin nuna farin cikin wannan haihuwar , har zuwa ranar da takasance ranar raɗin suna , ɗaruruwan mutane suka hallarci wurin bikin raɗin sunan inda yaro yaci sunan "mai martaba "Youssoufa"

A nan wurin kuma mai martaba ya Sa aka yi shela akan bai amince ba a boyewa yaro sunan sa "laƙani " a kira yaro da sunan sa Yarima Youssoufa Abdoul-Azizou Baskore Sunan sa kenan .'''
Bayyana irin bacin rai da bakin cikin da hajiya uwa da saratu su ka shiga bai kwatantuwa "domin a ranar da labarin haihuwar ya iso musu kwana suka yi basu yi bacci ba suna jimami da taya junan su bakin ciki " Amma da yake dukkanin su sun ƙware a harkar kissa da kilbibi , sai suka shafe , hajiya uwa tayi ruwa tayi tsaki akan harkar mai jego da jaririn ta , tayi ƙabe ƙabe akan harkar kome , "ta nuna jika dai nasu ne "
Haka ita ma saratu take wuni a sashin safiyyah tana taya ta raino "a cewar ta " sosai ta sake a cikin jama'a ana ta hidima da ita "yayin da take nunawa mijin ta da ma ita safiyyar cewa youssoufa ita ma ɗan ta ne " (cikin rashin sanin su saratu da hajiya uwa suna nan ƙudurce da mummunan ƙudirin su da su kadai suka barwa kan su sanin sa , Sai kuma Allah wanda yake masanin kowa da kome )1

kwance tashi youssoufa yana girma har zuwa lokacin da ya cika shekaru biyu a lokacin ne babban rashi ya samu birnin maraɗi , in da mai martaba sarkin youssoufa ya amsa kiran mahaliccin sa bayan ƴar gajeruwar jinya ,
STORY CONTINUES BELOW
haka aka gudanar da zaman makoki cikin alhinin rashin wannan adalin sarki nasu , bayan an share makoki akayi bikin naɗi inda "Yarima Abdoul azizou ya ɗare kujerar mulki "ya zama sarki " a kuma tsukin kwanakin Saratu ta sake haihuwa inda ta sake samun ɗiyar ta mace "wacce taci sunan mahaifiyar ta Maryam" bayan watanni biyu safiyyah ita ma ta ƙara haihuwar ɗan ta namiji ,"da aka sanya masa sunan lamiɗo "1
Lokacin da Biyamaradi youssoufa ya cika shekaru biyar da watanni a lokacin ne wani babban rashin ya sake samuwa , Allah ya yiwa zainab kanwar mai martaba rasuwa a wurin haihuwa , ta mutu ta bar ƴar jaririyar ta da ta haifa wacce koh samun damar ganin fuskar ta bata yi ba mai rabawa ta raba " bayan share zaman makoki An samu saɓanin ra'ayi akan wacce zata yi rikon jaririyar zainab da ta ci sunan kakar ta ta wurin uba "siyama " A karshe an tsaida shawarar "safiyyah ita zata yi rikon siyama tare da jaririn ta da ta haifa kwanaki arba'in da suka wuce "Aminu " a dalilin sanin da kowa yayi cewar akwai aminci tare da ƙauna mai karfi a tsakanim marigayiya zainab da kuma safiyyah " domin tun ranar da akayi rasuwar ma jaririyar take karkashin kulawar safiyyah ita take kula da ita ,"take shayar da ita maɗarar da aka tanada domin jarirai sabuwar haihuwa "

Dan haka aka miƙa rikon siyama ga safiyyah tare da mayar mata da ƴar ta hannun ta zainab karama "ubbo" wacce a lokacin take da shekaru bakwai tana aji biyu na primary amma sosai ta shaƙu da uwar goyon ta , babar ta ,kuma takwarar ta marigayiya zainab a saboda rikon gaskiya soyayyah da amana da tayi mata " hakan ya sa ta ɗauki son duniya ta ɗora akan wannan jaririyar da take yi wa kallon ƙaramar kanwar ta take kuma son ta fiye da kannen ta da suka fito ciki guda "
Cike da ƙauna da tsaftataciyar soƴayyah safiyyah ta karbi riƙon siyama "gefe guda na zuciyar ta kuma ɗauke da wani babban burin da take fatan kasancewar sa , wanda ta riga ta ayyana shi akan jaririyar da aka bata amanar ta "
Bayan maryam ita ma saratu ta sake haihuwar ɗiyar ta mace "da ta amsa sunan hauwa"u " , kuma ita ce aka yi goyon su tare da su siyama da aminu "2

Zuwa lokacin saratu kakaf ta gama bin gidajen bokaye da ƴan bori akan su taimaka mata ta samu haihuwar ɗa namiji "wanda ita ma zata ɗaga tace wannan ɗan ta ne namiji amma shiru ake ji "wai malam ya ci shirwa " akan cikin 'hauwa'u babu irin tsubbace tsubbacen da basu yi ba ita da hajiya uwa wacce har zuwa lokacin bata saduda ba .

A gefe ɗaya suna nan suna shirin kaddamar da mummunan aikinsu ,
kwanci tashi yara suna girma Arzikin iyayen su yana sake bunƙasa ,cigaba da wayewa yana sake yawaita , sauye-sauye suna samuwa , yanayi yana juyawa ,
2005
yanayin ya juya ta inda ya mayar da kananun yaran nan wasu matan aure wasu kuma samari " inda ƴaƴan sarki Abdoul azezou Baskore suka cika su Goma sha biyar cif-cif , siyama da ita ma take amsa sunan ɗiyar gidan ta cikace su suka zama su goma sha shiddah cif cif "safiyyah tana da takwas ,Huɗu maza huɗu mata "Saratu tana da bakwai shiddah mata ɗaya namiji ' , An rufe haihuwar da ɗiya mace kamar yadda aka buɗe ta da diya macen ,"1

Biyamaradi yousoufa tun tasowar sa mutum ne miskilin gaske marar son hayaniya "yana da tsananin tausayi ko ma ace rauni akan mata da yara kanana " , baya shiga harkar kowa a gidan babu me ganin fara'ar sa idan aka ɗauke iyayen sa , sai kuma abokin sa , kuma Aminin sa Tafeedah da ya kasance ɗan uwan sa domin da mai martaba da mahaifin tafeedah da yakasance me riƙe da sarautar ɗan malikin maraɗi , ƴa ƴan wa da kani ne uwa ɗaya uba ɗaya .

Tun tashin su tare suka tashi tamkar ƴan tagwaye ance sai hali ya zo ɗaya ake abota toh abotar Biyamaradi yousoufa da tafeedah ta ƙaryarta hakan domin idan aka ɗauke ra'ayin su da yazo ɗaya akan karatu da aikin da suka yi haɗakar ra'ayi akan sa ,"watau aikin ɗamara " da ya kasance su dukkanin su sojoji ne sai dai shi tafeedah sojan sama ne , saɓanin yarima yousoufa da yake sojan ƙasa .

STORY CONTINUES BELOW
Bayan hakan kowannen su halayen sa saɓani da na ɗan uwan sa ne , inda Tafeedah ya kasance mutum me barkwanci , surutu da saukin kai, saɓanin yarima yousoufa , hakan ya sa suke yawan samun saɓani akan halayyar juna in da kowannen su yake ƙalubalantar ɗan uwan sa , a ganin yousoufa tafeedah ya cika sakarci da sakewa mutane , yayin da shi kuma tafeedah yake ganin yousoufa a matsayin bauɗaɗɗen mutum miskili marar dadin sha'ani ,
A tsakanin su ɗaya ya kasa sauyawa ɗaya halayyar sa kamar yadda saɓanin halayyar su sam-sam bata taɓa karfin aminci da abotar su ba ,tun suna yaran su har yanzu da suke kan shekarun girma ,basu da abokan da su ka wuce junan su , duk wasu shawarwarin su tare suke yi , sun san sirrin junan su daɗi da rashin daɗi basa rabuwa duk inda dare yayi idan har suna cikin gari ɗaya ,"aiki bai tura ɗayan su wata jahar koh wata ƙasar ba "toh dare yana yi ka gansu tare koh dai a sashin biyamaradi yousoufa koh kuwa a sashin tafeedah da shima yake bangare guda a gidan su da yake baya kaɗan daga shiyar gidan sarki " sosai abotar su me tsafta ce irin wacce take wuyar samu a wannan zamani "
Bayan Tafeedah babu wanda Biyamaradi yousoufa yake so da ƙaunar gani irin karamar kanwar su A'isha wacce ake kira "meram" kasancewar ta (meramar sarki) .

ƙwarai Biyamaradi yousoufa yake kaunar meram duk da cewa kanwar sa ce da suke uba ɗaya , domin meram ita ce ƙaramar ɗiya ga hajiya mama ( Saratu ) a cikin ƴaƴan gidan mata ita ce karama , A'isha"meram" yarinya ce ƴar kimanin shekaru sha uku a yanzu tana aji na uku a makarantar gaba da primary .

Aisha irin yaran nan ne da gatan da suke da shi bai sa sun lalace da rashin tarbiyyah ba , ta samu tarbiyya sosai a wurin uwar goyon ta "Safiyyah" uwa ga Biyamaradi yousoufa , hajiya umma "kamar yadda ƴaƴan ta suke kiran ta" ita ta ɗauki Aisha tun daga yaye wanda hakan yana da nasaba da ƙaunar da ta ga ɗan ta mafi soyuwa agare ta yana yi wa kanwar ta sa da tun daga lokacin da aka haife ta ya ƙyalla ido ya ganta ,Allah ya dasa masa kaunar ta ciki ran sa fiye da duk sauran ƴan uwan sa ciki har da waɗan da suke ciki ɗaya da shi da su .

Lokacin yana matakin farko a jami'ah ai kuwa ya mayar da sashin mama wurin yada zangon sa a duk lokacin da ya dawo daga ɗaukar darasi haka zai kwace aisha daga hannun masu rainon ta yayi ta faman hidima da ita, hakan sam baya yi wa hajiya umma daɗi ganin yadda ɗan ta ya tare a sashin da a da kafin haihuwar aisha sai yayi shekara ma bai taka kafar sa bakin sashin ba " hankalin ta ya tashi akan sanin da tayi cewa garin su baya jiƙuwa a ƙoƙo ɗaya tare da saratu"hajiya mama "
Baza ta iya hana yousoufa zuwa sashin hajiya mama kai tsaye ba kasancewar ta san shi kaifi ɗaya ne ,miskilin gaske da ba'a iya sauya masa ra'ayi ta daɗi , hakan ya sa ta bi hanyoyin da take ganin zasu taimaka mata ta dakatar da ɗan ta daga shiga sashin hajiya mama domin tana gudun ta janye mata ɗa tsaf "sanin halayyar saratu "(hajiya mama) " da tayi na tsantsar kissa da siyasa tare da hilatar mutum ya so ta a dole karshe kuma ta cuce sa "macijin sari ka noƙe ce " ( cikin rashin sanin hajiya umma aikin gama ya riga ya jima da gamawa )1
Dan haka tayi mata shigar sauri ta bi duk hanyoyin da take da damar bi ya haɗu kuma da ita ke jaan ragamar gidan ta ɗauke Aisha can-cak daga wurin mahaifiyar ta a lokacin tana shekaru biyu a duniya ta dawo sashin ta baki ɗaya , ai kuwa murna gurin yousoufa ba'a cewa kome " yayin da hakan da tayi ya baƙan ta ran hajiya mama sosai amma sai ta boye bacin ran ta. (sanin da tayi ta riga ta gama rarake ƙasan hajiya mama )3

Cigaban labari .
Yana shiga tamfatsetsen (palourde-parlour )falon nasa ko kafin ya karasa zama akan ɗaya daga cikin kyawawan fararen kujerun da suka sake haskaka falon wayar sa da take cikin aljihun sa ta hau ruri .
Ciro wayar yayi daga cikin aljihunn sa tare da tsira mata ido tamkar me nazarin ta ,har sai da ta kusan tsinkewa tukun ya ɗaga gami da yin sallama ya ɗora da faɗin "Comment vas-tu aujourd'hui princesse"?

STORY CONTINUES BELOW
Daga dayan bangaren aka amsa cikin wata narkakkiyar murya " je vais bien Mon amour comment va le travail"?

Ya amsa da Alhamdulillah daga haka suka ci gaba da hirar da ake yin ta cike taf da kasaita daga dukkanin bangarorin biyu da shi da wacce ga alamu budurwar sa ce .

Idan ɗaya ya furta kalma sai an biyo bayan wasu ƴan ƙananun daƙikai (seconde -seconds) kafin " ɗayan ya bada amsa , inda daga baya ma ya koma budurwar ita ke jaan ragamar hirar, shi daga yayi murmushi sai yace eh ko a ah.

Har dai zuwa lokacin da ya sako mata zancen tafiyar sa akan aikin sa har na tsawon lokacin da yake zaton zai iya kaiwa shekara .

Nan take ta katse shi tun ma kafin ya karasa yi mata bayani cikin tashin hankali take tambayar sa akan ina lamarin bikin auren su ya kwana ? Wanda ake sa ran zuwan ranar da aka yanke nan da ƴan wasu watannin da suke gaza da uku "lokacin da zata kammala karatun ta" ?
Cikin jin haushin tarar numfashin sa da tayi wanda yake ganin kaf duniya yana iya kirga mutanen da suka isa yi masa haka ,yace ke dakata MAIMOUNA lamarin ayki matsayin shi ya wouce douk yadda kike tounani don haka ki ajiye komi a guefe har sai bayan na cimma matsaya bisa aykina.

Ko kafin ya gama bayani budurwar da aka kira da maimouna ta fara shishiƙar kuka gama bayanin sa yazo daidai da fashewa da kukan ta bata ko kuma saurarar sa ba ta kashe wayar ta ,

Ta barshi riƙe da kan waya a kunne , ɗan jim yayi yana son fahimtar abun da ya sanya ta kuka cikin kalmomin da ya furta ,?
Rashin gano dalilin ya sa shi ɗaga kafaɗun sa biyu cikin nuna alamar rashin damuwa ya miƙe tare da nufar daya daga cikin fankama-fankaman ɗakunan da suke cikin falon nasa yana shiga ɗaki ya nufi ƙaton window ɗakin gami da buɗe sa a take ƙamshi damina da wata sassayan iskar maraice da ta fi ta ac da yake ɗakin dadi ,ni'ima da sanya nishaɗi ta buso zuwa cikin dakin .

Rage kayan jikin sa yayi tare da nufar bayi da alamun wanka yake da niyyar yi ,sai dai wayar sa da ya ajiye gefen gado ta ɗan jaa hankalin sa sakamakon hasken da tayi ,ɗan guntun murmushi yayi ganin sunan princesse da alamar sako a fuskar wayar ,ba tare da ya ɗau wayar ba ya faɗa bayi domin yin wanka.

Yana kammala shirin sa ya fito falo jikin sa sanye da uniforme riga da wondo me dabbare-dabbaren kore , ruwan kunkumadi, ruwan madara, da kuma jaa Wanda ko ba'a faɗi ba za'a san kakin soja ne .( Tenue Saharienne ).

Da sallama ɗauke akan harcen sa ya sanya kai cikin katafaren Palourdes (falon) mahaifiyar sa wanda yake kama da ɗakin taro "hall" dakatawa yayi daga gefe ya sunkuya tare da kwance igiyoyin jikin takalman sa da suke ɗaure gam-gam da kafar sa har kusan ƙwarin sa ,
Wucewa yayi niyyar yi (zuwa ciki wurin umma ) bayan ya amsa gaisuwar jakadiya wacce ya tarar tana zaune daga gefe a cikin palourn amma sai jakadiyar ta dakatar shi cikin cewa "Ranka ya dade biyamaradi " yanzu kuwa nake shirin zuwa sashin naka "ta furta hakan tana me satar kallon bayu uku da suke ta faman goge-goge da ƙwal-ƙwale cikin palourn daga can geufe ( umartar su tayi da su kauce su basu wuri ).

Gyara tsayuwar sa yayi bayan ya kammala sauraron bayanin bakin jakadiyar , sannan ba tare da ya nuna wata alama! Akan fuskar sa ba ya ce "madallah da ke jakadiyar sarki zan kuma yi taka tsan-tsan tare da sanya ido sosai domin gano gaskiyar wannan zancen da kika zo min da shi , "bayyanuwar wani abu wanda ya sha banban da wanda kika sanar da ni a yanzu " zai iƴa jawo hukunci me tsanani a gare ki dai-dai da yadda doka da shari'a ta tanadar ga masu yin ƙage da sharri , wanda kin riga kin san haka .

Daga haka ya juya ya fara tattaki domin nufar wurin mahaifiyar sa "cikin zuciyar sa kuwa cike taf da bakin ciki da baci rai ! Akan labarin da jakadiya ta zo masa da shi game da ɗan uwan sa muhamadou .'mamman"

Muhamadou shine ɗa na huɗu a ɗakin hajiya mama "kuma shine ɗan ta ɗaya tal namiji .

******************

Dai-Dai ya sanya kan shi cikin ɗan madaidaicin wurin "da yafi kama da dakin hutawa " ita ma ta kawo kai kiris ya rage su ci gware cikin sauri ta ɗago kai da niyyar buɗe baki amma ganin wanda yake tsaye a gaban ta ya sanya a take ta diririce "tare da yin ƙasa da sauri ta kai gwiwowin ta ƙasa cikin ƴar siririyar murya tace "ina kwana hamma youssouf " , kallon ta yayi na daƙikan da suke gaza da biyar ya ɗauke kansa tare da sake yin kicin-kicin da fuska daga bisani ya wuce yana me amsawa ciki-ciki da lafiya lau " bayan sa ta bi da sassayan kallo daga bisani ta miƙe daga durƙusan da tayi tana me kakkabe gefe da gefen fara sol ɗin rigar da take ɗore bisa kan kayan ta , gyara zaman farin gilashin idanun ta tayi " da saboda firgitar da tayi kiris ya rage ya subuto daga kan siririn karan hancin ta ",
Cikin sassarfar yake taku fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi da yake bayyana ƙatuwar wushiryar da take tsakanin fararen hakoran sa na sama" har ya ƙarasa gefen dardumar da farar dattijuwar take zaune hannun ta riƙe da wani ɗan ƙaramin littafin addini tana dubawa "zama yayi tare da miƙa hannun sa ya kamo nata hannayen da suke ciƙe da awarwarayen zinare da suke ta faman haske idanun me kallon su , ɗaga hannuwan nata yayi dai-dai fuskar sa ya sumbancin bayan hannuwan nata ɗaya-bayan-daya kafin ya sarƙafe dogayen ƴan ƴatsun sa cikin nata yatsun da suke ƙawace da adon jaan ɓakin lalle da yake ta faman sheƙi tare da tashin sassanyan kamshi "
Fuskar ta ɗauke da tattausan murmushi take bin duk wani motsin sa da ƙwarar idanun ta zuciyar ta fal! Cike da ƙaunar gudan jinin zuciyar ta
"ina kwana ummana kin tashi lafiya ? Yaya fama da jama" ? Allah ya ƙara miki nisan kwana da hakuri da mu umma " cikin murmushi take shafar baƙar kwantatciyar sumar kan sa tana me amsa addu'ar sa da Ameen kafin ta ɗora da tambayar lafiyar sa shima sannan ta ƙara da tambayar sa yayi karin kumallo ? Ƴar dariya yayi sannan "yace umma na makara sai naje officie zan sha café " tana shirin yin magana ta sake shigowa palourdes (falo ) " Bakin ta ɗauke da ƴar siririyar sallama "Budurwar da suka kusan yin karo da biyamaradi ce "
Tare da kulawa hajiya umma take kallon ta kafin ta ce yaya kuma kika dawo SIYAMA ? Ke da kike ta mitar kin yi latti , 'cikin inda-inda tare da satar kallon biyamaradi da ya ciro wayar sa yake dannawa "da alama kira yake shirin yi " tace "umm daman umma kamar nayi mantuwa ne , cikin sauri ta juya gami da nufar wata ƴar kofar da take tsakankanin kofofi huɗun da suke cikin wurin "bayan ta hajiya umma tabi da kallo cikin ran ta kuwa tausayi-kauna gami da soyayyar siyama ce taf take kai kawo"

Tana shiga ta tura kofar gami da dafe kirjin ta bayan ta jinginu da jikin ƙyauren kofar " a hankali ta juya tare da zamewa ta durƙusa gami da sanya fuskar ta a dai-dai saitin ramin ɗan mukullin kofar , nan take idon ta ya ƙƴallo mata fuskar sa yana hirar sa da mahaifiyar sa hankalin sa kwance in da yake sanar mata da zancen tafiyar sa a cikin kwanaki uku masu zuwa "idan mai martaba ya amince" ɗan jim hajiya umma tayi sannan ta ɗora da cewa wai kou yarona (bata kiran sunan sa saboda sunan surikin ta ne ) shi tahia bisa aykin ba'a iya yin sa ne tare da amre "abun nuhi bai yuwuwa mutun ya tai tare da iyalin sa " ?6Gyara zama Biyamaradi yayi kafin yace " A zahiri ummana ba wai ba'a tahia akan hidimar aiki tare da iyali bane sam-sam sai dai duba da irin wurin da zan tai ba kasa ta bace ba ,kuma zan tai ne domin kwantar da tarzoma sannan zan jagoranci mutane sama da dubu ɗaya ne ,ni ne shugaba gare su ina bukatar tattara hankalina kachokam na ɗora bisa aykina tare da kula da mutanen da suke karkashi na "+

Numfasawa yayi daga bisani ya ɗora da cewa kuma"ummana ki yi duba da irin ita Maimuna ɗiyan sarki ce wacce du inda zata ta zauna sai tare da bayun ta masu yi mata hidima , shin ya kamata daga amren mu na douke ta zuwa wata ƙasa a bakin ayki na wurin da babu tabbacin zata samu irin gatan da take samu a gidan su da kuma wanda zata iya samu da ace anan ta zauna da auren mu ? Ummana a duba lamarin nan da kyau ,?

Sauke numfashi "hajiya umma" tayi duk zance ɗan nata gaskiya ne aykin sa me tattare da hatsarin rasa rai ne , ayki ne na sadaukarwa ga ƙasar sa ,shi ya sanya tun farko bata so ba youssof ya zaɓi da ya zama soja , so tayi yayi ta karatu me zurfi har ya zama alkali ta yadda du ranar da ya zama shi ne bisa gadon sarauta mulki ba zai taɓa yi masa wahalar gudanarwa ba ,

Sai dai duba da yadda shi youssof ya ɗage ya tsaya kai da fata kan ra'ayin sa , ya sanya daga karshe ita da mai martaba suka tsaya masa wurin ganin cikar burin sa bayan kammala karatun jami'ar da ita ma da rarrashi da ban baki youssof yayi "domin da farko so yayi yana kammala karatun gaba da primary ya fada makarantar horar da sojoji " sai dai mai martaba yayi masa jaan ido sosai sannan ya yadda yayi karatun jami'a inda ya karanci fannin sociologue" yana fitowa kuwa ya miƙa takaddun sa ga neman shiga soja , nan take kuwa aka ɗauke sa "kasancewar sa ɗan manya"


cike da so da kaunar aikin sa gami da nuna tsantsar ƙwazo ya fara aykin wanda hakan ya jawo nan take ya fara taka matakan nasara hawa hawa , sau biyu ana sawa da shi a cikin zaɓaɓɓun sojijin da ake turawa kwantar da tarzoma a kasashen ƙetere "kasar Somalia da Libya " cikin ikon Allah kuwa duk tawagar da yake jagoranta lafiya suke dawowa cike kuma da tarin nasarori " hakan ya bashi ɗaukaka a cikin ƙanƙanin lokaci har ta kawo sa ga matsayin da yake kai a yanzu wanda a karo na uku sai ga shi an sake tura shi ƙasar Nigeria domin yaƙi da ƴan tawayen Boko haram "

Cikin yanayi marar daɗi yake kallon fuskar mahaifiyar sa wacce da alama tayi nisa cikin tunani "shi ya san daga mai martaba har umma basa son aikin sa "kuma da yana da iko tabbas da ya haƙura da aikin amma toh shi yaya zai yi ne shi ya tabbatar haka Allah ya halicci zuciyar sa da ƙaunar aikin soja "domin baya mantawa tun yana shekaru biyar yake ƙwalafaci tare da mararin ganin sa riƙe da bindiga sanye da kakin soja haka ya tashi ya tsinci kansa kullum wayewar gari da mafarkin ya zama soja "abun a jinin sa yake "1

Muryar sa ce ta doki dodon kunnuwan ta tare da dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula "ummana a cigaba da yi mana addu'a kamar yadda aka saba da iznin Allah babu abun da zai faru da mu sai Alkhairi sannan shekara kamar kwana ce tamkar yau zaki ga ɗan ki ya dawo , ya karashe zance yana dariyar tsokana ".


Ƴar dariya itama tayi kafin ta ce addu'a muna kan yin ta yarona kuma insha Allah zamu cigaba fatan mu Allah ya kiyaye tare da shiryar mana ku a duk inda kuke da sauran ƴaƴan musulmai baki ɗaya ,


to yaya ita ɗiyar tawa da fatan ka sanar mata da batun tafiyar duk da cewa ma nasan idan har tafiyar takasance mai martaba da kansa zai tada ɗan aike zuwa Birnin Agades ɗin " ta ɗora da sake tambayar sa, yaya ɗiyar tawa ta aminta dai kou batare da ta tayar da hankalin ta ba ?

Gimtse fuska biyamaradi youssof yayi kafin ya ɗora da mun gama magana kuma ta fahimta , cikin ransa ! Kuwa mamakin yadda wannan lamari zai tafi a haka karfi da yaji yana namiji umman sa ta dunga nunawa da lalle ne ya yi abun da maimouna take so ,


Sau tari hakan ya sha faruwa hatta akan tsarin ginin gidan sa da aka yi duniya guda daga can Babban filin da yake karshe a cikin masarautar maimouna ita ta zaɓi irin ginin da take so kuma irin sa sak aka yi , ya rasa gano dalilin haka ,


STORY CONTINUES BELOW

Shi shine namiji shine shugaba tayaya za'a dunga gwada masa sai abun da matar da zai aura ta zaɓa shi zai yi ?

Miƙewa yayi yana me duba agogon hannun sa cikin sauri yake yi wa umma sallama "Ummana ni zan wuce ina ga yau zan iya kaiwa cikin dare kafin dawowa ta sabadda yau zamu fara zuwa bakin bodar da ta haɗa mu da Nigeria domin duba irin tsaron da za'a fara ajiyewa ta wurin" ,

Bin sa da ido hajiya umma take "tana lure sarai da sauyin da aka samu akan fuskar sa tun da ta ambaci sunan maimouna "cike da so ta fara kwarara masa addu'a tare da sake jaddada masa ya kula da kan sa sosai , har zuwa lokacin da ya karasa ficewa daga wurin da take ",

Sauke ajiyar zuciya tayi a lokacin da ya bacewa ganin ta ,lokaci daya ta ɗauke fuskar ta daga jikin bulin makullin kofar tare da miƙewa tsaye ta juyo fuskar ta wacce take " ɗauke da wani tattausan murmushin da a zahiri yake nuna zuciyar ta na cikin annashuwa " dan tsalle tayi tare da juyi kafin a hankali ta motsa laɓɓan ta cikin cewa " za'a ɗaga bikin auren hamma youssouf har zuwa nan da wata shekarar me zuwa ,' taku ta fara yi a hankali da ya dangana ta da jikin katafaren gadon da yake rufe ruf da kyakyawan labulen da iskar da take busowa daga jikin tagar ɗakin yake ɗan kaɗa shi a hankali " janye labulen tayi tare da zama a bakin gadon " ɗan rangwaɗa kan ta tayi cikin cewa "ɗaga ranar bikin hamma youssouf yana nuni da nasarar da na kan iya samu ,hakan yana iya yiwuwar samun wata sabuwar dama a gareni ".,2

Lokaci ɗaya ta gimtse fuska domin tunowa da tayi da nisan da hamma youssouf ɗin zai yi mata wanda ya sanya ba shiri ta ji hawaye ya cika gurbin idanun ta ","hamma youssof zai tafi Nigeria har na tsawon shekara , zan rabu da ganin sa na adadin kwanaki ɗari uku da sittin " bazan iya ba " zuciyata zata iya samun matsala kafin cikar adadin kwanakin nan ya zama dole na samowa kai na mafita " ., zabura tayi jin ana ƙwanƙwasa mata kofa ,'

Cike da jin haushi ta ce "waye a nan ? Cikin ladabi hadimar da take durkushe ta bakin kofar tace '"Allah ya huci zuciyar uwargijiya ta sako ne daga " Babbar uwa (hajiya umma ) tace a sanar da ke lokaci yana tafiya " ., ɗan jim tayi kafin ta amsa kina iya tafiya gani nan fitowa ., ki fito lafiya ranki ya dade,'

Miƙewa tayi tana me jin duk fitar ta yau ta fice mata daga kai "tana da tabbacin yau bata iya tsinana wani abun kirki a wurin aykin ta "saboda chakuɗuwar farin ciki tare da bakin ciki ! A lokaci guda cikin ran ta ,'

Sake ɗurkusawa tayi har ƙasa tana me daɗa yin sallama da hajiya umma wacce ta kafe ta da ido tana me yin nazarin ta ", har ta miƙe da shirin tafiya ta ji hajiya umma ta sake kiran ta "yaki nan ɗiya ta ', dawowa tayi tare da sake durkusawa ", babu dai wani abun da yake damun ki koh ?

Da murmushi ɗauke akan fuskar ta ta ɗago tana me kallon fuskar mariƙiya gareta matar da a da take mata ganin mahaifiya tun tasowar ta domin bata taɓa cin karo da wani abu wanda zai sanya ta kokonto akan zaman hajiya umma mahaifiyar ta ba ,' har sai da lokacin da ta shekara goma sha bakwai(ta kammala makarantar gaba da primary ) a lokacin ne hajiya umma ta shaida mata hakiƙanin gaskiyar matsayin ta a wurin ta "hakan kuma ya samo asali ne dalilin ƙin amincewa ta bi mahaifin ta na ainahi da tayi ," da ya nemi son tafiya da ita wurin sa tayi hutun kammala karatun gaba da primary da tayi ", yazo da buƙatar tafiya da ita gidan sa domin ta ga sauran ƴan uwan ta da ya haifa tare da matar da ya aura bayan rasuwar zainab ",

Sosai a ranar tayi kuka ,kukan maraicin ta kafin a hankali ta hakura ," ta bi mahaifin ta , ta kuwa ji daɗi sosai da wannan hutun da tayi tare da kannen ta da matar mahaifin ta da ta kasance matar kirki ,'

Sai dai tun bayan dawowar ta daga gida (daga wurin mahaifin ta ) ta tarar da hamma youssof shima ya dawo daga jami'a inda ya kammala karatun sa ,' Rana ɗaya ta tsinci yanayin ƙaunar da take masa a zuciyar ta tana sauya muhalli ,daga so irin na ƴan uwan taka zuwa wata irin zazzafar soyayyah ,' ta aure wanda take jin idan har bata mallaki hamma youssof a matsayin mijin auren ta ba zuciyar ta kan iya samun babban raunin da zai iya dangana ta da kushewar ta ",

STORY CONTINUES BELOW

Gyaran murya hajiya umma tayi bayan ta gama nazarin ta sosai ta ce "siyama ki kasance me tsananta addu'a a koyaushe akan dukkanin lamuran ki kin ji koh ? Gƴaɗa kai siyama tayi ,' to maza tashi ki je ɗiyar Albarka Allah ya tsare min ke ya dawo da ke lafiya ," cike da jin daɗi da wata irin kakkarfar soyayyar mariƙiyar ta siyama take amsawa da Ameen "umman mu" Alherin Allah ya isar miki umman mu" ,

Tsaf hajiya umma ta gama gano abun da yake nuƙurƙusar zuciyar ɗiyar ta siyama ,'domin tun ba yau ba dai take lure da duk wani motsin Siyama akan youssof ɗin ," a kuma bangare guda na zuciyar ta lamarin sosai yayi mata daɗi ganin yadda yayi kicibus da tsohuwar niyyar da ke kulle a cikin zuciyar ta akan siyama da youssof ɗin tana da tabbacin baza ta samu matsala daga bangaren siyama ba".

Damuwar ta akan youssof ɗin ne wanda tun farko ta lura youssof ɗin bai wani cika kula lamarin siyama ba tun suna yara "kusan ma za ta ce jinin sa bai ɗauki siyama ba domin tun suna yara kullum faɗan sa da yayar sa 'ubbo' akan siyama ne ,' yana dukan siyaman kasancewar ta yarinya me tsinannen rawar kai a lokacin kuruciyar ta ,"shi kuwa youssof mutum ne marar son hayaniya hakan yasa garin sa bai jiƙuwa ƙoƙo guda da na siyama 'nan take zai bige ta ' wanda hakan yake haɗa sa faɗa da yar tasa domin duk duniya idan aka ɗauke hajiya umma da mahaifin siyama na ukun su a ƙaunar siyama ubbo ce ,sam bata ƙaunar abun da zai taɓa siyama ,' sosai take gwadawa siyama soyaƴyah da gata fiye da ƴan uwan ta da suke ciki guda ma, ' har dai zuwa lokacin da ubbo tayi aure a birnin Niamey gidan ta shine wurin hutun siyama a duk lokacin da ta samu hutun makaranta ,har kuma yanzu da siyama ta kammala karatun ta a shekaru biyu da suka gabata daga Université médecine- medical school ( makarantar horar da likitoci ) in da ta karanci fannin likitar haƙora ( Dentiste-Dentist ) ta kuma fara aiki a asibitin gwamnatin tarayya ta ƙasa reshen jahar maraɗi watanni sha tara da suka wuce , siyamar bata da zancen da ya wuce wurin da zata rubuta hutu musamman ta je da ya wuce gidan addar ta ta ubbo ,wacce mijin ta a yanzu ɗan majalisar tarayyah ne na ƙasa baki ɗaya ,"

A lokacin da youssof ya zo tare da batun ya samu matar aure a shekarar da ta gabata "dai-dai lokacin da ita kuma take gaf da fiddo manufar ta na son haɗa youssof da siyama aure ta shaida ga mai martaba "wanda ta san zai fi kowa farin ciki da wannan lamarin sanin da tayi lokacin marigayiya zainab tana raye suna da kyakyawar mu'amala ita da mai martaba duk kuwa da cewa shi mai martaba ya girmewa kanwar ta sa da tazara sosai domin mutane uku ke tsakanin sa da marigayiya zainab " , sai dai kuma youssof ɗin ya riga ta tada maganar auren in da yazo da murnar sa yake sanar mata da samar mata da suruka da yayi,' tun a lokacin ta so ta rusa maganar ta kuma fiddo masa da ainahin nata ƙudirin na son haɗa su aure shi da siyama,'

Sai dai jin wacce ɗan nata yake da zummar aurowa a matsayin surukar ta ya sanya ta yin laƙwas "ba wata bace wacce youssof ɗin zai auro illah maimouna ɗiya ga mai martaba sarkin AGAƊES , Maimouna ita ce ɗiyar sarkin agades mace ɗaya tal 'ƴar da ta samu gata da kulawa irin na bada kwatance .' Maimouna kyakyawar yarinya "ƴar buzaye" wacce ake kwatancen kyaun ta har ta kai sunan ta da kyaun ta ya shiga jerin abun kwatance a bakin al'umma " haka za'a ji budurwa idan ta ƙure wanka da gayu za'a ji masoyan ta na kururutata " wance kin kou ga kan ki sai kace gimbiya maimouna '? " ko kuwa idan budurwa ta cika feleƙe da yanga dan ita ɗiyar masu akwai ce nan za'a ji ƴan adawar ta suna faɗin" yo ai mu munga gimbiya maimouna ma karshen gata dai kenan" a taƙaice dai gimbiya maimouna ɗiyar gata ce gaba da baƴa ,3


Sanin duk wani wanda ya kwan ya tashi ne cikin ƙasar Niger ", Sarautar birnin Agades shi ke da suna har karfin mulki fiye da dukkanin sauran manyan masarautun gargajiya da ke ƙasar Niger , sanin hakan da hajiya umma da mai martaba sarkin maraɗi suka yi ya sanya nan take zuciyoyin su suka cika da farin ciki ganin ɗan su zai auro ɗiya mafi soyuwa ga Sarkin agades ", wanda sun san hakan ba ƙaramin babban nasara tare da samun sabuwar ɗaukaka gare su da ma jahar maraɗi baki ɗaya ba ne ,"

STORY CONTINUES BELOW

Nan take hajiya umma ta ajiye zancen auren siyama da youssof a gefe wanda a da take jiran kammaluwar karatun ita siyama sai ta tado maganar kuma a wancen lokacin siyamar ta riga ta kammala karatun tun watanni biyar da sun ka wuce ", jinkirin da aka samu na son ta sake tsananta addu'ar neman zaɓi ne sai kuwa ga shi jinkirin ya zama Alkhairin da ya sa dole ta ture maganar siyama gefe ba kuma domin ta hakura ta janye zancen baki ɗaya bane "sawun giwa ne ya take na rakumi "sannan cikin ranta tana maimaita ai youssof mijin mace huɗu ne ", da wannan ta ajiye batun gefe , tare da bayyana tsantsar farin cikin ta da batun maimouna ,1


Cikin satin mai martaba sarkin Maraɗi Abdoul-azizou Baskore ya tura da takardar neman aure ga sarki Usoumanu Ibrahim tounouss na birnin Agades , koh da sakon ya isa ga Mai martaba sarkin Agades shima ya bayyana farin cikin sa bayan da yaji ta bakin ɗiyan sa , in da ta tabbatar masa da amincewar ta tare da sake jaddada yawan ƙaunar ta ga biyamaradi youssofa, anan take mai martaba sarkin Agades ya bada tukuici mai yawa tare da takaddar jaddada amincewar sa ,"

Bayan dawowar ƴan aike daga birnin Agades a daren mai martaba sarkin Maraɗi ya gana da hajiya umma inda yake sanar da ita tayi magana ga ɗiyar ta siyama cewa a tare za'a haɗa bikin ta da na youssof dan haka ta tsaida guda cikin masoyan ta ," Anan hajiya umma bata yi ƙouron baki ba ta sanar da mai martaba haƙiƙanin shirin zuciyar ta tun daga farko ',

Ɗan jim mai martaba yayi bayan kammala jin dukkanin kalaman uwargidan sa ," sosai yaji daɗin kyakkyawar niyyar ta sai dai yadda ta ture Al'amarin bayan bayyanuwar maimouna ya sanya shi jin wani iri tamkar dai akwai sautin son kai cikin lamarin nata ," sai dai yayi saurin kauda zargin daga ransa akan sanin da yayi a duniya idan ana kirga masoyan siyama hajiya umma tana daga sahun farko ƙwarai yana alfahari da ita akan irin kyakyawan riƙon da tayi wa ƴar kanwar sa , " dan haka yace idan har ita siyama ta amince da shi youssof ɗin ya zama dole ga youssof ya auri siyama a matsayin matar sa ta biyu shekara guda bayan auren sa da maimouna idan Allah ya yadda ",1

Nan take maɗaukakin farin ciki ya bayyana akan fuskar hajiya umma ,' tana mai sake jaddada masa da ƙaunar da ita siyama ta lura tana yi wa youssof ɗin tun shekarun baya ," nan dai mai martaba ya tsaida batun auren siyama da youssof sai dai ya nemi hajiya umma da ta bar batun nan a tsakanin su ,"saboda gujewa ƴan kai-kawo ', .


Mairambiri Borno Nigeria

Hasken ranan da ta ɗago ta fara ɗan zafi ita ta sanya ta fara motsi , kafin ta buɗe dogayen manyan idanun ta da suke farare tas tas , da sauri ta miƙe daga kwanciyar da take a cikin taɓon da ya cakuɗe da ruwan da ya kwanta a cikin ƙonanne ɗakin nasu wanda wuta ta riga ta ƙona azaran saman ɗakin ," da sauri ta fara lalube gefe-da-gefen ta , jin bata ji almun mutum a ɗakin ba ya sa ta miƙe tsaye ta fara laluben hanyar fita tare da kiran sunan ƴar uwar ta "yakaka "yakaka " santsi ne ya kwashe ta suuu ta tafi ta faɗi dabas a bakin kofar ," bayan ta ya bada ƙara ƙaƙas , " wani kuka ne ya taho mata a lokacin da wani mugun tsoro ya ɗarsu a ranta koh dai ƴan tawayen boko haram sun dawo ne jiya ? Sun tafi da yakaka ," tunanin hakan ya sa taji wani karfi ya zo mata ta yunƙura da karfin ta ," ta miƙe ta fara tafiya a cikin ruwan da ya cika tsakar gidan nasu da ƙasa bata kai ga shanye sa ba ',

Cigaba tayi da ƙwalla kiran sunan yakaka ' yakaka ' yakaka , ruwan hawaye yana me cigaba da ambaliya akan fuskar ta da karfi take jefa kafar ta ba tare da tana laluben gaban ta ba burin ta kawai ta tafi neman ƴar uwar ta ɗaya da ta rage mata," ji tayi ta kaiwa bango karo tayi taga-taga ta tafi da baya ta sake faɗuwa," da gudu take jin takun tahowar mutum kafin taji sautin muryar ta itama cikin firgici tana ƙwalla kiran sunan ta 'falmata 'falmata falmata'

Da gudu ta shigo gidan ,"wurgi tayi da ledar da take hannun ta tare da ƙarasawa gurinta zuwa lokacin ita ma kokarin tashi take tana mai sake kiran sunan "yakaka ', ɗago ta tayi tare da rumgume ta cikin jikin ta ,' itama kamkame ta tayi ," kafin su dukkanin su biyu su saki juna suna masu haɗa baki gurin tambayar junan su,'

"Falmata baki ji ciwo ba koh ?

Yakaka ina kika je babu abun da ya same ki koh ?

Banji ciwo ba yakaka ina kika tafi kika barni kin sa hankalina ya tashi kar ki sake tafiya ki barni yakaka ,"falmata ta furta hakan tana me laluben fuskar yakaka ,"

STORY CONTINUES BELOW

Hannun ta kai gami da share mata hawayen da suke gudu har yanzu akan ƙuncin ta ,"kafin cikin ƙarfin zuciya tace kiyi hakuri kanwata lokacin da gari ya waye naji wucewar mutane ɗai ɗaya hakan ya sa na lallaɓa na leƙa anan naga wani mutum shi ɗaya da gudu zai wuce shine na bishi nima ina tambayar sa koh ya ake ciki a gari ," shine yake gaya min shi hanya ce ta biyo da shi ta nan ƙauyen mu ,'daga ƙaramar hukumar Bama yake ," a yau suka wayi gari da afkawar ƴan tawayen boko haram a yanzu haka sun farma ƙaramar hukumar Bama suna ta kisa ,"irin dai yadda suka yi anan jiya ", mutumin ya tabbatar min da gwara na gudu domin ƴan tawayen boko haram zasu iya dawowa su mamaye dukkanin ƙauyukan da suke tsakanin Bama da Konduga tun da sun riga sun mamaye garin bama ", na tambaye shi to ina zamu ? Shine ya ce min ance wai a cikin Birnin Maiduguri gwamnati ta tanadi wurin da mutane irin mu ƴan gudun hijira zamu zauna a kula da mu kafin a yaki ƴan tawayen boko haram ,"

Tashi mu tafi falmata kar mutumin nan ya yi mana nisa kin ga mu ba mu san hanyar Maiduguri ba bamu taɓa zuwa birni ba ," zame hannun ta da yakaka ta kama tayi kafin cikin muryar kuka ta fara cewa "yakaka ni babu in da zan tafi , yakaka ba mu san inda su mama suke ba , idan muka tafi kuma su mama suka dawo neman mu fa ? Mu zauna yakaka mama zata dawo neman mu zata dawo ta tafi da mu inda ta ɓuya ,"

Share ƙwallar idon ta tayi kafin ta ce falmata su mama fa su ma sun tafi Maiduguri suna jiran mu a can ," da zasu dawo ai da tun jiya zasu dawo idan muka zauna anan koh ƴan tawayen boko haram basu kashe mu ba wuya da yunwa da kishirwa zasu kashe mu ," miƙa hannu tayi ta kamo baƙar ledar da ta shigo da ita wacce take yawo akan ruwan da yake tsakar gidan ," kin ga wannan ma tsintowa nayi a hanya wata kaza tana ta so ta fasa ledar ta kasa shine na bita na ƙwace" biredi ne a ciki ki ƙarba ki ci mu tafi falmata," ta karasa zancen da sigar rarrashi ,"1

********************


Hannun su sarƙafe da na juna suke tafiya ," bayan sun fito daga gidan nasu kowaccen su tayi shiru da abun da take saƙawa a cikin ran ta .


A hankali yakaka ta waiwaya tana me kallon kofar gidan su ," sosai ta tsirawa gidan ido tamkar me son kirga adadin yawan bulon da akayi amfani da shi wurin ginin gidan ," gizo idanun ta ya fara yi inda ta hango mahaifin ta ya fito kamar yadda ya saba hannun sa riƙe da hular sa , gefe guda ita ce a tsaye hannun ta riƙe da buhun su na zuwa gona daga bakin kofar kuwa mahaifiyar su ce tana ɗaga musu hannu kamar dai yadda ta saba ," hawayen idanun ta ne suka gangaro gami da ɗiga akan kafar falmata ɗan jijjiga hannun ta da yake cikin na yakaka falmata tayi kafin ta ce mu tafi mana yakaka,"1


Mu tafi falmata cewar yakaka wacce ta ke bin dukkanin ginin unguwar su da kallo hotunan al'amuran da suka gudana tun daga tasowar ta a cikin unguwar suna ta wucewa ta cikin tunanin ta ," wata irin kewar mahaifarta tana mamaƴar ta tana jin tamkar ta tafi kenan ," tana jin tamkar karshen ganin ta da gidan su da garin su kenan ," gefen zuciyar ta tana jin wani sabon karfi tare da karban sabon sauyin da rayuwa ta zo mata da shi ,"yayin da take jin nawin girman da ya hau kan ta na rike kan ta da kanwar ta falmata yana kama ta,' sai dai tana jin kome runtsi da Wahala zata kula da falmata ko da ita zata rasa rayuwar ta," miskin falmata ,"1

Taku Falmata ta fara yi tana me jin yadda duhu yake mamaye zuciyar ta kamar dai yadda duhun yake a zahiri a idon ta ," tana jin duk wani farin cikin da ta san ta samu daga lokacin da tayi wayo zuwa yau yana barin jikin ta ,' wani irin ƙunci yana mamaye cikin ran ta ," tana jin kuncin yana ƙaruwa da dukkanin wani takun ta guda ɗaya da take yi da niyyar barin garin su mahaifar ta , zuciyar ta tana cike da tsoron sabuwar rayuwar da zata fuskan ta alhalin tana makauniya a garin da bata da kowa bata san kowa ba sai ƴar uwar ta ," tsoro sosai ya ɗarsu a ranta " , sai dai wani sashi na ranta yana faɗa mata zata dawo watarana , wataran zata dawo garin su mahaifar ta , zata sadu da mama da sauran kannen ta ," bata san lokacin da wani matsanacin kukan da yake cike da tsoro da kuncin zuciya ya kufce mata ba ,' kuka take bilhaƙ ,"

STORY CONTINUES BELOW

Matsa hannun ta yakaka take yi alamun rarrashi domin a zuwa yanzu ita ma bata da karfin zuciyar rarrashin falmata domin tana da tabbacin tana buɗe baki kukan zuciyar da take yi zai bayyana a zahiri ," ita ma bukatar rarrashi take tana bukatar matallafin da ko da ba zai taimaka mata da kome ba ," zai furta mata kalmar ZAKI IYA YAKAKA,1


Hanyar da mutumin nan ya gwada mata ita su yakaka suka kama," suna tafe basa jin motsin kowa sai kukan tsuntsaye ," ɗan turus yakaka tayi ganin hanyar bakin jeji sosai ta kawo su ," jin sun tsaya ne ya sanya falmata wacce ta fara gajiya tace yakaka har mun kawo Maiduguri ne ? Cikin sanyin murya yakaka tace falmata gani nayi hanyar da muke tafiya a kan ta ta kawo mu bakin jeji ," jin batun jeji ya sanya falmata sake cukumo rigar yakaka tare da cewa mu koma kawai yakaka ," na faɗa miki daman kar mu taho ,"

Jin takun tafiya tare da hayaniya kamar har da kukan yara da suka ji shi ya sa su saurin juyawa " wasu gungun mata (sun fi su goma ) tare da yara da namiji guda ɗaya suka hango ," bisa ga dukkan alamu su ma a jigkace suke daga su sai kayan jikin su ," wucewa suka yi ta gaban su ba tare da sun ko kula da su ba ," cikin sauri yakaka ta saki hannun Falmata tare da cewa ", bari na tambayo su koh su ma maiduguri suka nufa ," da ɗan gudu ta cimma su saboda saurin da suke zabgawa cikin harshen su take tambayar su ," ko maiduguri za su ?" Ba tare da sun waiwaye ta ba ɗaya daga cikin su ta bata amsa da ",Eh ",1

Da gudu ta koma baya gami da kamo hannun ƴar uwar ta tana jaan ta tare da cewa zo mu tafi falmata mun samu abokan tafiya waɗan nan mutanen su ma maiduguri suka nufa ,' ita dai falmata bata ce ƙala ba ta bi yakaka suka faɗa jeji tare da bin bayan mutanen nan da har sun fara yi musu nisa cikin duhun ciyawa ,"1

Doguwar tafiya suka yi sosai cikin ƙungurmin dajin nan da yake cike da itatuwa da ciyayi gami da ƙayoyin da suke ta faman huda musu takalman su suna sukar kafafun su, ba sa cewa ƙala a tsakanin su ," har zuwa lokacin da rana ta ɗan gota tsakiya alamun azahar ta yi ", namijin ciki shine ya basu umarnin tsayawa a dai-dai wani wurin da ruwan sama ya ƙwanta yayi kamar ƙaramin kududdufi " , cewa yayi a huta a sha ruwa sannan ayi sallah a cigaba da tafiya ,"

Yaraf ,'duk suka zazzauna wasu ma kwanciya suka yi warwas a ƙasa ,kallo ɗaya za'a yi musu a fahimci tsabar gajiya da yunwa a tare da su ," yaran ciki kuwa daman tuntuni suke kukan yunwa da kishirwa dan haka ko da su ka ga ruwan nan , nan take suka nufi wurin wasu suka sa tafukan hannayen su biyu suna ɗebo ruwan suna sha wasu kuwa bakin su suka sa a kan ruwan suna sha ",

Yakaka da falmata suna cikin waɗanda su ke shan ruwan da hannayen su ,ɗauro Alwala su ka yi bayan sun sha ruwan ," su ka kuma jira sauran matan su ma su ka zo sha ruwan tare da ɗaura alwala ," namijin ya jaa su jam'i haka a cikin dajin ,"1

Ƙarar wucewar wani abu me tsananin karfi da matsanancin ƙara da yake barazanar kashe musu dodon kunnuwa shi ya sanya a firgice ! Su dukkanin su, su ka ɗaga kai sama ba tare da sun sallame sallar da su ke ba ," yaran ciki kuwa nan take su ka fasa kuka tare da ƙanƙame iyayen su

Shawagi wannan abun da wasu daga cikin su , su ka ce "jirgi ne " ya cigaba da yi ," yayin da su kuma su ke tsaye carko carko , kawukan su a ɗage suna hango jirgin da yayi ƙasa ƙasa da har su ke iya ganin launin sa da yake koren kala , ruwan madara da kuma ruwan hanta "(coffee),"

Falmata lalubo hannun yakaka tayi tare da riƙe ta gamgam cikin karkarwar murya tace yakaka menene shi jirgin ?

Basu yi aune ba kawai su ka ji an saki wani abu kamar bom ," wanda ya faɗo kurkusa da mutumin nan da yake jagorar tafiyar su tare da wasu mata biyu da suke tsaye ,' nan take su ka tarwatse jinin su ya watsu a jikin sauran su ,"4

wani irin kururuwa su ka yi a tare da yake nuna tsantsar firgicin su ," karo suka fara yi da juna cikin gigicewa suna masu neman hanyar gudu jin yadda jirgin nan ya sake sakin wanna abun da basu kai ga fahimtar harsashi ne ko kuwa bom ?,"

STORY CONTINUES BELOW

Fisgar hannun Falmata, yakaka tayi wacce take ta faman waige-waige tare da ihun tambayar yakaka me yake faruwa ? Ba tare da yakaka ta bata amsa ba ta fisge ta cikin ihun kukan da ƙarar jirgin nan ya dusashe ƙarfin sautin take cewa mu gudu Falmata idan ba haka ba zamu mutu ,"

Takawa su ke da matsanancin gudu suna jefa ƙafafun su wanda ko takalma babu "domin basu samu damar sanya takalman su ba " wurin da duk suka tsinci kan su nan suke jefa kafa basa duba gaban su bare su waiwaya baya ,"wasun su kuka da ihu suke yayin da tsiraru daga cikin su suke addu'a ," gudun ceton rai suke cike da tsananin tsoro tare da tashin hankalin jin kamar ƙarar jirgin nan na bin su  ,"2

Cikin tsananin gudun da su ke ne yakaka taji hannun falmata da take riƙe da shi gam-gam suna gudun tare ," hannun ta ya fisge daga cikin nata lokaci guda kuma taga falmata tayi ƙundubala ta tafi gaba ɗaya ta faɗi ta gaba fuskar ta ta bugu da ya sa ba shiri ta saki wani irin ihun azaba tare da ƙwalla kiran sunan Allah ,"


Cikin kaɗuwa yakaka wacce har ta yi gaba saboda matsanancin gudun da suke ," ta dawo da baya da gudu gami da durƙusawa ta tallafo falmata wacce hancin ta da bakin ta ke fidda jini ," sai dai wata ƙarar da falmata ta sake saki a lokacin da yakaka take koƙarin ɗago ta ya sanya babu shiri ita ma yakaka ta fashe da matsanancin kuka ,"

Falmata sannu Dan Allah ki tashi

" ta furta hakan tana me gogewa falmata jinin da ya bata mata fuska da ɗankwalin kan ta da ta zame lokaci guda kuma tana me ɗaga kanta sama tare da yawata idanun ta a sararin samaniya cikin tsammanin ganin jirgin sojojin nan ,"

Ƙafata yakaka ƙafata ta maƙale a rami wayyo Allah na yakaka zan mutu ,"

Falmata ta furta hakan a lokacin da ta ruƙo ɗayar ƙafar ta, take ƙokarin zaro ƙafar daga wani ɗan ramin da yafi kama da na "ƙurege" ko kuwa dai kananun dabbobi dangogin sa ",

Cikin tashin hankali yakaka ta sake fuskar falmata gami da miƙewa ta koma ta wurin ƙafafun ta ,"kokarin zaro ƙafar ta fara yi ,"idanun ta suna zubar hawayen tausayin kanwar ta da ya sa ta kusan mance halin tsaka mai wuyar da suke ciki ,"

A gigice ta ɗago kan ta ganin wani hannun da tayi ya kama kafar falmata "cikin taya ta kokarin zaro kafar ,"

Ɗaya daga cikin abokan tafiyar su ce ," ita ma yarinya ce wacce zata iya girmewa yakaka da kadan ",


Da karfi su ka samu nasarar fusgo kafar falmata wanda hakan ya sa yakaka tayi faɗuwar ƴan bori akan ciyawar farar ƙayar da ta soki bayan ta ya sa ba shiri ta sake zabura ta miƙe gami da rugowa ta ɗaga kafar falmata wacce tayi futu-futu da ƙasa," ta ɗora akan cinyar ta ,"lokaci guda tana tambayar falmata kafar bata ji ciwo ba koh ," ?


Yakaka kamani na tashi mu gudu," Falmata ke furta hakan a lokacin da take laluben hannun yakaka fuskar ta tana bayyana tashin hankalin da take ciki ," da sauri yakaka ta miƙe bayan ta sauke kafar falmata daga jikin ta ,"yunkurawa tayi tare da ɗago ta ," ganin haka ya sa yarinyar da take tsaye a gefe tana kallon duk abun da suke ta matso gami da kai hannu ta kamo ɗayan hannun falmata da nufin taya yakaka ɗaga ta ,"

Wani irin zamiya falmata tayi tare da warce hannun ta daga jikin yarinyar wanda hakan yayi sanadiyar komawar su ƙasa da ita da yakaka ,a lokaci ɗaya ta kanƙame jikin ta wuri guda tare da cewa ,"

Yakaka waye a wurin nan tare da mu ? Aljanu ne koh ?1

Falmata wacce ta taya ni muka zaro kafar ki daga rami ce ɗaya daga cikin abokan tafiyar mu ........,"

******************


Kika ce kin san hanyar Birnin Maiduguri Yagana ? Tambayar da yakaka ta jefawa Yagana (abokiyar tafiyar su ) kenan lokacin da suke cigaba da tafiya ," sai dai saɓanin ɗazu yanzu a nutsen su suke tafiya ,"samun nutsuwar su ya samo asali ne daga fahimtar da suka yi jirgin nan ya tafi ya daina bin su ,"


Sai dai fa a yanzu zuciyoyin su cike take taf da tsoron ganin su uku ne rak a ayarin tafiyar su sauran duk sun watse kuma basu sake cin karo da ko guda daga cikin mata takwas da kananun yara biyar ɗin da suka rage a ayarin nasu a bayan mutuwar namijin cikin su tare da mata biyun ba ",

Eh nasan maiduguri yakaka mun taɓa zuwa tare da yaakura na ( yayar mahaifiyar ta )

Sau goma kuka taɓa zuwa koh sau ashirin ," da a yanzu kika ce zaki mana jagora ? cewar falmata wacce take ɗingisa kafar ta gefe-da-gefen rigunan su ita da yakaka a ƙulle da na juna ,.


Sau ɗaya dai na taɓa zuwa tun lokacin ina shekaru biyar na taɓa yin rashin lafiya wai wasu kuraje suka fito min shine aka ce sai a Babban asibitin cikin Maiduguri za'a ban magani ," ta karasa zancen tana me ɗaga zanin ta zuwa gwaiwa ," kin ga taɓon kurajen nan yakaka wannan tabon da kike gani tun ina shekaru biyar a duniya,"3

Waiwayawa su ka yi jin Falmata ta jaa ta tsaya lokaci guda suka dawo gefe da gefen ta suka tsaya ," yagana tana cewa kin gaji ne falmata ?

Falmata wani wurin yana miki ciwo ne cewar yakaka ?

Fashewa da kuka tayi cikin shishiƙar kuka ta fara cewa yakaka sai da na faɗa miki kar mu taho kar mu taho kika ce sam sai mun taho ," kika nace ," gashi nan yanzu zamu mutu a cikin daji kura ta samu na kalaci ," ta karashe zance tana jaan majina .4


Shiru yakaka da yagana suka yi domin a hakiƙanin gaskiya su dukkanin su biyun karfin hali kawai suke domin kuwa ƙarƙashin rayukan su cike yake taf da tsoron duhun daren da ya riga ya fara shigowa ne,"alhalin suna cikin ƙungurmin dajin da basu san gabas ba bare yamma ,"

Kiyi hakuri Falmata ni bana son yawan kukan nan da kike kin san dai baki da lafiyar idanu ," muyi ta addu'a kawai Allah yana tare da mu ," cewar yakaka


Eh Falmata addu'a ita ce mafita kuma ina jin kamar ma mun kusa isa maidugurin dan ina tunanin lokacin da aka kaini asibitin kamar ance wai bamu kwana a hanya ba wai awanni bi......


Ke ni dallah ki mana shiru ,"ke idan ana zancen waɗan da suka taɓa zuwa birnin maiduguri ma har kya sako baki ?3

Wucewa gaba Falmata tayi a fusace tana lalube a ranta kuwa tana ayyanawa kome ta fanjama .3

Ƙanƙame da juna suke kwance a ƙarƙashin duhuwar bishiyar kukar da duhun ta ya haɗu da duhun dare tare da na damina ya bada matsanancin duhun da ba'a ko iya ganin tafin hannu .+

Falmata ce a tsakiyar su yakaka da yagana suna gefe-da-gefen ta ,ko ƙokkwaran motsi basa iya yi saboda tsabar zullumi da tsoron da ya cika musu rai ! Numfashi ma a sace suke yin sa yayin da kunnuwan su suke tarwai a buɗe daga jin motsin abun da yake nesa da su da kusan rabin kilomita .


Babu motsin kome a dajin da ya wuce kukan jemagu da kuma wasu ƙananun ƙwarin da ba'a iya tantance kukan su ," haɗi da wani kuka da suke ji daga nesa ƙadan da su wanda tsananin tsoron da suke ji ya sa suka kasa tantance kukan koh na menene ,"ya dai fi musa kama da kukan bijiman sa (shanu) sai kuma jifa-jifa kukan manyan namun dawa waɗanda suke nesa sosai daga wurin da suke .


Ƙasa-ƙasa muryoyin su suka fara tashi ,"

Umm Yakaka zan yi fitsari ,"

Fitsari kuma falmata dan Allah kiyi hakuri mu jira safe.

Falmata kawai kiyi fitsarin nan anan kwance a jikin mu ," cewar yagana


Motsin da suka fara ji mai ɗan karfi yana doso inda suke ne ya sanya su sake damuƙar junan su kafin jikin su ya ɗau karkarwa kar-kar-kar .

Shikenan muryoyin su sun jawo mu su .


Wani ɗumi yakaka da yagana suka ji a jikin su wanda yake tabbatar musu yawaitar motsin da suke ji tare da ƙarin gabato su da motsin ke yi shi ya sanya falmata sakin fitsarin da tace tana ji saboda tsabar tsoro3

Haske suka fara hangowa wanda basa raba ɗaya biyu hasken tocila ne ," kafin su fara jin taƙun kafafun mutum ," tare da tashin muryoyin mutanen da baza su wuce biyu ba sai dai magana suke a cikin yaren da su yakaka basa fahimtar sa ,"

Gani suka yi an ɗan kau da hasken tocilan kafin su ji an taho har kurkusa da su ," karar zubar wani abu kamar ruwa ne ya fara sauka kunnuwan su kafin su ji ruwan mai ɗumi ya fara fallatsuwa akan fiskokin su a zaɓure suka miƙe zaune wanda a tunanin su koh ruwan zafi ake watsa musu ,"

Miƙewar da suka yi shi ya mutumin da yake tsaye shima ya zabura tare da yin eho a take kuma ya buɗe murya gami da yin magana da maɗaukakiyar murya cikin yaren sa nan take sai ga hasken tocila ya dallare fuskokin su yakaka ,"1

*****


A tsugunne suke bisa gwaiwowin su tamkar mai laifi a gaban hukuma ," maza ne kimanin goma a zagaye da su dukkanin su hannun su rike da makamai kama tun daga kan ,sanduna , gatari ,takobi,kwari da baka , wuƙake , da ma bindigar harbi ka buya ,1

Fahimta da suka yi su yakaka basa jin yaren su na hullanci ya sanya ɗaya daga cikin su ya juya harce cikin yaren hausa

Yaro ku su waye ? Kuma daga ina kuke cikin daren nan ?

Nan take yagana wacce da alamu ta fi su yakaka fahimtar hausa ta ce mu ƴan gudun hijira ne daga garin Bama nake waɗanan kuma "tana nuna su yakaka " abokan tafiya ta ne daga nan kauyen mairambiri suke ," ƴan tawayen boko haram ne suka tarwatsa mana garuruwan mu ,"

Duk bayanin nan da suke yi yakaka da yagana basu samu damar ganin fuskokin su waye a tsaye zagaye da su ba su dai sun san mutane ne , kuma a ƙalla sun ji saukin tashin hankalin da suke ciki akan sanin da suka yi ashe akwai mutane dayawa haka kurkusa da su ,".


Juya harshe wannan mutumin da ya tambayi su yakaka yayi ,"tare da yi wa abokan tafiyar sa fassarar bayanin da yagana tayi cikin yaren su na hullanci ," nan take hayaniyar su ta ƙaure a wurin da alama Tausayawa yaran suke tare da Allah wadai da ƴan tawayen boko haram wanda sun riga sun san da zaman su ," kuma tsakanin su da su babu kare bin damo "abun nufi ko da sun haɗu cikin daji basa shiga harkar juna ," ( Makiyaya da ƴan tawayen boko haram )2


Bayan doguwar muhawarar da suka yi a tsakanin su nan mutumin ya juya ga su yakaka yace ":

Yaro yanzu ku ina kuka nufa ?

Maiduguri zamu ," ance gwamnati ta tanada mana wurin zama ', za'a kula da mu cin mu da shan mu sutura da wurin kwana har ma ance za'a samu a makarantun gwamnati ," abincin cin mu ma na....1


STORY CONTINUES BELOW

Katse ta mutumin yayi :

Yaro kun san hanyar Maidugurin ne ?

Nan falmata wacce take fahimtar mafi yawan kalmomin nasu ," mayar da magana cikin hausar ne ke yi mata wahala ,


Tayi tsagal tace Baba wallahi bamu san hanya ba", dan Allah ku taimaka ku kai mu Maiduguri dan Allah ta karashe zancen tana matsar ƙwallar wahalar da ta ciko mata ido,"

Yaro zamu taimaka muku amma mu ba Maiduguri muka nufa ba ," mu daga nan ikko muka nufa ,"amma zamu raka ku har inda muke ganin kun wuce hatsari sai mu gwada muku sauran hanyar ," nan wurin da kuke akwai hatsari sosai ,


Juyawa ya sake yi suka yi magana da ƴan uwan sa ," sannan ya juyo tare da cewa ku biyo mu ,"

Lumshe matsakaitan idanun ta tayi lokacin da ɗumin madarar saniyar sabuwar tatsa ya sauka a cikin ta ," dago kan ta tayi daga cikin ƙoƙon da yake cike taf da madarar ta maida kallon ta ga fuskar kanwar ta wacce tayi kasaƙe hannun ta rike da nata ƙoƙon da bata tunanin ma ta kai bakin ta ," idanun ta suna sheƙin ruwan da ya taru a cikin su a tsaye idanun na ta suke ƙem wuri guda ," da alamar tayi zurfi cikin tunani ," a hankali taga ƙwallar da ta taru a gurbin idanun nata sun silalo da gudu sun sauko bisa ƙuncin ta ," da sauri ta ajiye ƙoƙon madarar ta gami da ƙarasawa inda falmata take zaune akan wani ɗan dutse ," dire gwaiwowin ta tayi a ƙasa lokaci ɗaya kuma ta sanya hannu gami da goge mata ƙwallar da suke cigaba da fitowa

Yakaka yau kwanaki biyu kenan muna wayar gari ba tare da iyayen mu da sauran ƴan uwan mu ba ," Allah ya jikan Baba ya gafarta masa ,"insha Allah shi mutuwa hutu ce a gareshi ,"

To amma yakaka mama fa da sauran kannen mu a wane hali suke ciki ? Wataƙila suma ƴan tawayen boko haram sun kashe su irin yadda suka yi wa Baba ," idan kuwa har suna raye tabbas mama tana cikin mawuyacin halin da ya fi wanda muke ciki a yanzu ,"

Yakaka muna shiga birnin Maiduguri abu na farko da zamu fara yi shine neman maman mu ,"

Ƙai hannunta tayi ta lalubo fuskar yakaka jin tayi shiru bata cewa kome duk bayanin da take yi , nan taji ruwan hawayen da suka faca-faca akan fuskar ta ," share mata hawayen tayi kafin a hankali ta kai kanta ta ɗora akan kafaɗun ƴar uwar ta , idan ke kika yi kuka a halin yanzu ni me kike so nayi yakaka ? ,kiyi haƙuri ki daina kuka insha Allah zamu haɗu da maman mu ,"

Nemo yatsun hannun falmatan tayi ta sarƙe su cikin nata hannun "falmata ba ina kuka bane a domin wahala koh raunin zuciya akan halin da muke ciki ba," ina kuka ne akan tunanin halin da mama da ƙannena suke ciki ina kuka akan wahalar rayuwar da kike ciki a halin yanzu alhalin bani da karfin taimakon ki ,"dubi kafar ki falmata ta ɗago kafar falmatan da take ɗaure da ɗankwalin ita yakaka,"


Duk ƙafar ta soke da kayoyi daga idon sawun ƙafar kuma a kumbure yake in da ta faɗa rami a jiya ," Falmata tun tasowar mu ban taɓa ganin ciwo irin wannan a jikin ki ba ,"duk da cewa muna rayuwa cikin talauci amma iyayen mu suna tattalin mu ,da lafiyar mu" amma ki duba daga shekaranjiya zuwa yau da rikon ki ya dawo kaina na gaza wurin baki kulawa gashi duk kin ji rauni ," sai nake ganin laifin kaina da zan iya falmata da goyon ki zan yi nasan da mama ce da ta sauke Bulama ta goye ki amm dubi ni ...1


Ɗago kan ta tayi tare da toshe mata bakin ta da hannun ta ," fuskar ta babu walwala tace yakaka daga yanzu ki daina ganin laifin kan ki akan duk wani abun da kaddara zata ɗoramin ,"

Sannan ki daina ganin kamar ni a dalilin bani da ido bazan iya yi wa kaina kome ba ," wasu abubuwan zan iya yakaka ,"a yanzu rayuwa ta sauya min ta inda nake ganin dukkanin wasu abubuwan da a baya bazan iya su ba a cikin sabuwar rayuwar da zamu fuskanta zan iya su ," abun da nake so kawai kar ki taɓa ɗauke matsayin ki na wacce take gaba da ni a koyaushe kika ga zan faɗa rami ki taro ni kin ji yakaka ?


Naji Falmata sai dai nima ina son ki bar min matsayina na yayar ki a duk lokacin da na nuna cewa nice gaba da ke wurin baki kulawa ,"kin ji koh ?

Ɗan siririn murmushi tayi

" naji yaa yakaka ,"

STORY CONTINUES BELOW

A hankali yagana ta sanya babban ɗan yatsan ta, ta ɗauke ƙwallar da ta gangaro mata daga cikin ido ," tana tausayin kan ta sosai da sosai tun tasowar ta kasancewar ta tashi ne ba tare da mahaifan ta ba mahaifiyar ta rasu tun tana yarinya yayin da mahaifin ta ya tafi ci rani ,"tun tana shekaru goma har yau bai dawo ba "dan haka a hannun kakar ta mahaifiyar Baban ta ta girma" sai dai daga jiya zuwa yau ta sake tausayawa kan ta a sanadin ganin tsaftatatciyar soyayyar ƴan uwan taka da take gudana tsakanin yakaka da falmata , wanda ya sa ta fahimci ba ƙaramin gibi take da shi a cikin rayuwar ta a sakamakon rashin dan uwa koh ƴar uwa da take da shi ba ," sosai soyayyar da ta lura tana gudana a tsakanin ƴan uwan biyu ta birge ta tare da bata sha'awa .3


Ajiye ƙoƙon ta"wanda ta riga ta shanye madarar ciki tas " tayi a gefe tare da miƙewa ta nufi wurin da har yanzu yakaka da falmata suke zaune ,"sai dai saɓanin ɗazu yanzu a jere suke a zaune inda falmata ta matsawa yakaka ta zauna a gefen ta suna fuskantar mahuɗar rana da ta fara ɗagowa tana keto tsakankanin ciyayin , ranar ta bada wani haske mai kyau ,"

Dafa kafaɗun su tayi da hanun ta ɗai ɗaya ," idan an gama tattaunawar sirrin tsakanin ƴan uwa a tashi mu tafi mu mayar musu da ƙoran nasu kafi su gama shiri su fara jiran mu kuma ,"kun san dai sun ce da wuri zamu kama hanya saboda miƙaƙƙiyar tafiyar da ke gaban mu ," murmushi yakaka tayi ," yagana baki da dama ,"

Satar kallon falmata yagana tayi wacce ko alama bata nuna ma taji abun da yaganan ta ce ba ,"

Kamo hannun falmata ," yakaka tayi da sauri yagana ta zagayo tare da kama mata ɗayan hannun ,"amma ga mamakin su sai ji suka yi tace

"zan iya tashi da kaina ,!

Yunƙurawa tayi amma sai suka ga ta kai hannun ta gami da lalubar hannun yakaka ta rike gam gami da miƙewa a hankali ,"hakan da yagana ta gani ya sa ta fahimci falmata bata so ta ita ta taimaka mata sai ƴar uwar ta "ɗan tabe baki tayi cikin nuna ko oho ",2

*****


To kun ga nan shine karshen dajin konduga daga nan ai gashi kuna iya hango gidajen da suke ta cikin yankin unguwannin Birnin Maiduguri ,"wadancen gidajen da kuke iya hangowa daga nan suna cikin unguwar da ake kira dalori ne , kuna ƙarasawa can kun riga kun shiga birnin Maiduguri ," mu daga nan muke sake komawa mu ɗauki hanyar in da muka nufa ," wannan dogon bayanin yana fitowa ne daga bakin bafullatanin mutumin nan ,"bayan sun kawo su yakaka iyakar dajin yankin konduga da cikin garin maiduguri ,"

Nan take su yakaka suka durkusa akan guiwowin su suna masu jero godiya da tarin addu'o'i ", zuciyoyin su kuwa ƙwal kamar an musu bishara da wani babban abun Alkairi,"

Da murmushi ɗauke akan fuskokin fulanin nan su biyar "da alama sun baro sauran a daji tare da dukiyoyin su (shanun su ) suke amsa jerun gwanon addu'o'in su yakaka ," kafin mutumin ya ɗora da cewa toh yaro sai ku kula da kan ku sosai ,maiduguri babban gari ne sosai domin haka sai kun yi taka tsantsan da kome , da mu ƴan gari ne da zamu sanya ku a hannun wasu da muka sani to mu ma bamu san kowa ba cikin maiduguri,"

Sanya hannun sa yayi a aljihu ya zaro wata tsohuwar naira ɗari biyu ya damƙa a hannun falmata wacce ya lura bata gani ," daga haka suka yi musu sallama tare da juyawa suka ɗau hanya abun su ba tare da sun sake waiwayawa ba ,"

Shirun dakikai biyu zuwa uku ne ya gitta tsakanin ƴan matan uku bayan juyawar fulanin zuwa inda suka fito ,"ga su dai ga birnin maiduguri bayan doguwar tafiyar da suka yi na kimanin kilomita 74-76, akan kafafun su daga ainahin garuruwan su , da kuma tarin ƙalubale da hatsarin da suka shiga a yayin tafiyar ," wanda ya kamata ace a yanzu da maɗaukakin farin ciki za su durfafi birnin na maiduguri , to sai dai a halin yanzu da fulanin nan suka juya tare da tafiya suka bar su a faffaɗan fili sararin Allah da ya tafi ɗoɗar daga nesa suna hango gidajen jama'a da fulanin nan suka tabbatar musu gidajen cikin birnin maiduguri suke ," sai duk suka ji zuciyoyin su sun raurawa ,'akan tunanin ina kuma suka dosa ? Ina zasu nufa ?


STORY CONTINUES BELOW

Falmata ce ta katse shirun nasu a yayin da ta tattaro gutun yawun bakin ta da ya gama bushewa a sakamakon ranar damina da aka bude a yau ", Yakaka tsayuwar me muke yi ne kuma ? Kamata yayi mu ƙarasa cikin garin mu fara da neman maman mu a yau ɗin nan kin ga idan Allah ya sa muka ganta kafin dare ,"yau baza ta shiga cikin lissafin ranakun da zamu ƙara kwana ba tare da ita ba ko kuwa ?

Mukut ! Yakaka ta haɗiye guntun yawun da ya saura mata a baki ," Falmata a yadda fa nake hango girma da yawan gidajen da suke cikin Birnin Maiduguri ya sha banbam da irin na garin mu" amma dai bari mu ƙarasa mu gani ,"

Yunkurawa suka yi tare da kama hanyar suna tafe babu me cewa ƙala ," sun yi tafiya me ɗan tsawo zuwa lokacin da suka fara cin karo da gidajen da suke farko-farkon unguwar dalori Qaurters .


Ware ido sosai yakaka tayi tana kallon tsarin gidajen tare da yawan mutanen da ta gani suna ta kai kawon su ," nan take taji zuciyar ta buga da tunanin ina zasu fara bi su nemo mahaifiyar su a cikin wannan faffaɗan birnin ?

Ta bangaren yagana kuwa yawan jama'a da tsarin gine-ginen , bai wani zama baƙon abu ba a saboda babu laifi garin su "Bama" shima babbar Alkarya ce wacce take cike da Al'umma da kuma cigaba dai-dai da zamani ," tunanin ta ya fi karkata ga inda zasu je su samu mafaka kamar yadda kafin su fito daga gida a lokacin da labarin shigowar ƴan tawayen boko haram ya baza garin su aka fara guje guje da ƙokarin barin garin ɗaya daga cikin ƙannen mahaifin ta shi ya basu tabbacin idan suka tafi birnin maiduguri akwai mafaka agaresu da musamman gwamnati ta tanada ,"

Dan haka take taku zuciyar ta cike da son ganin sun isa mafakar ta su ,"

Ga bangaren Falmata kuwa ita ba ganin garin take yi ba amma hayaniyar muryoyin jama'a tare da ƙarar wucewar ababen hawa da suka cika mata kunnuwa sun isa sanar mata cewa ta shigo wani wuri da ya sha bamban da mahaifar ta me rangwamen hayaniyar jama'ah , ƙarar ababen hawa kuwa sai ranar cin kasuwar garin su take iya jiyo su daga nesa-nesa ," nan take taji tsoro ya kamata sakamakon tunowa da tayi da fannah ƴar makotar su wacce mota ta taɓa bigewa ta karya mata kafafu " , nan take ta lalubo jikin rigar yakaka ta haɗa da jikin tata rigar ta sake ƙullewa ," sannan ta sake jefa hannun ta cikin na yakakar wacce ita ma ta rike hannun falmatan gam-gam .


Cikin mutuwar jiki suke tafiya a lokaci guda yunwar da take ƙwaƙular cikin su tana tuno musu da rabon su da sanya wani abu a cikin su tun madarar da suka sha da safe ga shi dai yanzu azahar ta yi domin suna iya jin kiran sallah daga massalatan da suke cikin unguwar,"Yakaka idan muka samu wurin da ake sayar da abinci mu tsaya mu saya kafin mu isa ga masaukin mu ,"


Uhm yagana wane masauki kike zance a yanzu bayan duk alamu sun bayyana a garemu bamu da hanyar da zamu bi ta sada mu da gidan gwamnatin ,"idan kuma kina da hanyar sai ki faɗa ," cewar falmata ,


Yagana Jaan bakin ta tayi ta tsuƙe domin ta lura ba wani birge falmata take yi ba a kome ," a gefe guda kuma na zuciyar ta ,tana me gaskata zancen falmatan tabbas , ganin kitse take yi wa rogo a duk zaton ta suna tako kafafun su cikin garin maiduguri zasu tadda jami'an da aka ce suna bada tsaro ga mutanen maiduguri zasu chafe su ,tare da sada su da masaukin su cikin farin ciki da walwala ,"


Sai dai tabbas a yanzu tana iya hango yiwuwar sauyawar tunanin ta "wanda ya sanya ta hango kanta a matsayin wacce tayi masauki a kan bola " da hakan ya sanya ba shiri ta fara zare idanu tana kallon mutanen da ta lura su ma a halin yanzu kallo suke bin su da shi a duk inda suka gifta .


Duk ba wannan ba yanzu abun da yakamata mu fara yi shine mu samu wuri muyi sallah daga nan sai mu fara tambayar mutane hanyar masaukin da kika ce an tanada ga irin mu ,"koh me kuka ce ,"Yakaka ke furta hakan bayan ƴar gajeruwar muhawar da taji falmata da yagana suna yi ,

Cigaba suka yi da kutsawa cikin unguwar suna neman wurin yin alwala har dai suka yanke shawarar tsayawa a dai-dai wata mahaɗar da ta fi kama da tashar tsayuwar motoci saboda yawan ababen hawan da suka gani a wurin ,"sai dai yawan masu saye da sayar a wurin kama tun daga kan masu ɗanyen kaya ,da masu kayan abinci na awu ,"har ma zuwa masu saida dafaffen abinci da kuma masu toye-toye , ga kuma ƴan tebura nan dangin su masu saida biredi da sauran su ya sanya su hasashen ƙila kasuwa ce," tsayawa suka yi a wurin suna rarraba idon neman wurin da zasu samu damar Alwala ,


STORY CONTINUES BELOW

Daga gefe kaɗan da su , suka hango masallaci wanda rumfar kwano ta kare gaban sa mutane suna ta Alwala wasu kuwa sun kammala alwala suna sallolin su a cikin rumfar ,"

Ɗan yawatawa da idanun ta yakaka tayi tana neman ruwan Alwala ,"sai dai yawan idanun da ta gani akan su ya saka ta cikin firgici ,"kusan illahirin mutanen wurin hankulan su da idanuwan su akan su yake ," kuma idan ba idanun ta suke mata ƙarya ba kusan duk mutanen wuri ɗaya suke kallo a jikin su", daga kan kirjin su zuwa cikin su ,'!

A hankali ta sauke idon ta tabi inda suke kallo a jikin su ta gani koh wani abun ne a jikin nasu ,"

Hannu ta kai tare da gyara wuyan rigar ta da ya ɗan saɓule lokaci ɗaya kuma tana kai hannu ta gyarawa falmata ita ma nata wuyar rigar , duban ta 'ta mayar kan yagana wacce ta fahimci ita ma ta lura da irin kallon rashin yaddar da illahirin mutanen wurin ke bin su da shi ,"

Ƙasa tayi da muryar ta "yagana kin lura da irin kallon da mutanen nan ke bin mu da shi ? Koh daman haka mutanen birni ke yin kallon su ?

Ina lure da su nima ,"amma ina ga haka suke kallon su "dan yaakura na tace a lokacin da ta kawo ni asabitin tsatsareni da ido likitan nan yayi a cewar ta saura kaɗan ta ɗauke ni mu tafi dan tayi zaton ma koh karama ne (maye ) ɗan guntun tsaki ta jaa a lokacin da suka haɗa ido da wani matashi majiyi karfi yana kallon su tsakar ka, lokaci ɗaya kuma yana danna wayar sa tare da kara ta a kunne ","1


Jibe shi dan Allah ya wani tsare mutane da ido toh kurwar mu kur ," Falmata kawo kuɗin nan na ƙarasa can na sayo mana ƙosai da doya nan wurin ma jama'a sun yi yawa mun ƙara gaba kawai muyi sallar ,"

Falmata bata ce ƙala ba ta miƙa mata gudar ɗari biyun da take duƙunƙune a hannun ta "sashi guda na zuciyar ta! Yana gaskata mata zancen su yakaka na cewa da suka yi an zuba musu ido domin kuwa ita ta riga su sanin ana kallon su ,dan tun da suka nufo wurin jikin ta ya bata akwai wani abun cutarwa ko kuwa idanun mutane akan ta ,'duba da yadda taji tsikar jikin ta tana ta faman miƙewa,'hakan shine alamun da ita take fahimtar akwai matsala a wuri "baiwar ta kenan" , a gefe ɗaya cikin ranta kuwa cike fal! Da haushin yagana akan yadda take nuna ita fa ala dole ta fi su sanin maiduguri Alhalin kuwa su da ita duk sammakal tilo ," basu da wani bambanci.7


Taku biyu yagana ta yi suka fara jiyo tsuwwar wani abu wanda basu san ko meye bane ,"yayin da hankalin su ya kasu biyu ɗaya akan mutanen da suka ga sun fara guje guje wasu ma har suna barin kayayyakin sana'o'in su ,gefe guda na hankalin su na ga kan tsuwar nan da suke ji tana sake durfafo inda suke , so suke su fahimta akan wannan tsuwar ne mutanen ke gudu koh kuwa meye dalili ,?


Yakaka ƙarar meye ne wannan ɗin kuma meyasa naji kamar takun gudun mutane ?falmata ta furta hakan a dai-dai lokacin da take lalubar jikin yakaka tana gyara ƙullin da ya haɗa bakin rigunan su 'da alamun shirin gudu take "

Nima ban sani ba Falmta,"

Yunƙurin buɗe baki yagana take cikin cewa wani abu amma sai maganar ta maƙale mata a fatar baki.' sakamakon ganin manyan motocin da suke ɗauke da irin fentin da suka gani a jikin jirgin saman nan da yayi musu ɓarin wuta a daji ," a take suka fahimci ƙarar nan da suke ji daga jikin motocin nan take fitowa .


Ɗurum dum ,"bugun sautin zuciyoyin yakaka da yagana a lokacin da suka yi idanu huɗu da tarin motocin da suke da tabbacin na waɗannan mamallakan jirgin saman ne ,"shikenan mun mutu mun lalace yakaka , shikenan wallahi sun biyo mu ne su kashe mu ,"

Su waye suka biyo mu ? Yagana wai meke faruwa ne ,"cewar falmata da maganganun yagana suka yi mugun ruɗa ta ,"

Sojojin da suka biyo mu da jirgi a daji sune gasu nan a mota ....

Sauran maganar maƙalewa tayi a fatar bakin yagana a lokacin da ta ga gungun sojojin nan suna durƙowa daga bayan manya manyan motocin su hannayen su duk riƙe da bindigogin su da ya sanya cikin yagana ba da wani sautin ƙululu lokacin da tayi arba da su ,"wannan fa shi ake cewa anyi gudun gara an tadda zago ,"1


STORY CONTINUES BELOW

Jeruwa sojojin suka yi daga nesa kaɗan da inda su yakaka ke tsaye a sandare ko numfashi da ƙyar suke jaa ,"

Da gudu wani soja ya fito daga cikin gaban wata mota hannun sa riƙe da wata jibgegiyar bindiga ," ɗaga ta yayi gami da jaan kunamar bindigar ƙaraƙat ,'ya saita ta akan su yakaka da zuwa yanzu suke ta ɗigar gumi kamar an tsamo su daga rafi ,"2

Remove your clothes all, "1


Sasarai su dukkanin su suka yi suna wulwulga idanu cikin rashin sanin takamaimai ɗin abun yi lokaci guda kuma tsoro ya sake cika zuciyoyin su a sakamakon lura da suka yi cewa duk yawan mutanen wurin nan a yanzu basu ga ko mutum guda ba daga su sai sojojin nan ,"ji suka yi zuciyoyin su na barazanar faso kirjin su .,


Fahimta da sojojin nan suka yi su yakaka basa jin turanci ya sa ɗaya daga cikin su ɗaga murya ",

Ku cire kayan jikin ku idan ba haka ba zamu harbe ku mu kashe ku ,"

Cikin tsananin firgita yakaka da yagana suka kalli juna lokaci ɗaya suka ji falmata ta rushe da kuka ,"

Ji suka yi an sake daka musu tsawa

Zamu harbe ku idan kuka sake minti ɗaya ,"1

Ba shiri yagana ta fara cire tun daga ɗangalallen hijabin ta har zuwa rigar ta da yanzu take kan cirewa ,"

Satar kallon yagana ,"yakaka tayi kafin cikin rawar jiki ta miƙa hannu tana warware kullin da yake tsakanin rigunan su ita da falmata lokaci guda tana me cewa falmata ki cire kayan ki idan ba haka ba zasu kashe mu ,:2

Tsaye suke daga su sai siket din ciki hannayen su rumgume da kirjin su ,fuskokin su kuwa shaɓe shaɓe da ruwan hawayen da ya chakuɗa da majina gami da gumi ,"2

Magana sojojin suka yi a tsakanin su bayan sun gama ƙare musu kallo Daga wurin da suke ,"

Sir I think they're not Boko Haram girls , there was no bomb in their bodies,"

( shugaba ina tunanin waɗan nan. ba ƴan matan boko haram bane , babu nakiya a jikin su )


Yes they're not ,


(ƙwarai ba su bane )1


Daga inda sojan nan ya yake tsaye ya sake ɗaga murya tare da basu umarni su sanya suturun su ,"


Koh kafin ya ida rufe bakin sa har sun yi nisa wurin sanya kayan nasu ,"tsayawa suka yi suna jiran su sake jin umarni na gaba ,"idanuwan su kuwa basu bar zubar ruwan hawayen wannan tozarci da tashin hankalin da suke ciki ba ," ba ma dai kamar falmata wacce har karkarwa take tsabar kuka ,"1

Gani suka yi ɗai ɗaya da ɗai ɗaya suna komawar su cikin motocin su ,"yayin da suka ga waɗan nan biyu da suke yi musu magana ɗaya da hausa ɗaya cikin yaren da basa fahimtar sa sun nufo inda suke bindigogin su saɓe akan kafaɗun su ,"

Suna ƙarasowa wannan me jin hausan yace musu ", daga ina kuke kuma ina zaku ?

A wannan karon shiru yagana da ta kasance jaa gaba wurin mayar da amsa tayi tana zazzare idanu tare da satar kallon bindigogin hannun su ,"

Jin yagana tayi shiru ya sanya yakaka ta buɗe bakin ta cikin maƙyarƙyatar murya tare da gurbatatciyar hausar ta tace ",

:Umh daman mu ƴan hijira ne daga garin mu shine-shine muka zo nan neman gwamnati ta taimaka mana da masauki ,"

Inane garin naku ?

Ƙauyen mairambiri

Magana sojojin nan biyu suka yi a tsakanin su cikin harshen turanci ,"

Ku zo mu kai ku camp mu ajiye ku saboda idan kun cigaba da yawo haka a gari mutane baza su yadda da ku ba a karshe ma ana iya yi muku dukan tsiya da tunanin ku irin ƴan matan da boko haram suke ɗaura musu nakiya ne , su shiga cikin kasuwa koh taron jama'a su yi ƙunar baƙin wake ," bayanin da sojojin nan suka yi musu kenan bayan sun gama shawara a tsakanin su


STORY CONTINUES BELOW

Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakanin yakaka da yagana ," camp ina ne camp ?koh dai gidan horar da mutane ne sojojin nan zasu tafi da mu ? Wannan ne zancen da yake ta kai kawo cikin zuciyoyin su dukkanin su uku lokaci guda kuma suka ji wata sabuwar nadama baki daya ta kama su ,"daman haka mutanen cikin birni suke azzalumai haka kawai sai su hau jibgar mutum ?

Tsawar da aka daka musu ita ta sanya ba shiri yakaka ta kama hannun falmata suka bi bayan sojojin nan da su har sun yi juyawar su sun kusa isa ga motocin su tun bayan da suka basu umarni ,"

Wani irin mahaukacin gudu motocin sojojin nan suke akan tsakiyar titin na Maiduguri ," duk inda suka gifta motoci da sauran ababen hawa darewa suke suna basu hanya ,"

Tsugunne su yakaka suke a bayan hilux ɗin, sojoji biyu sun sanya su a tsakiya a zaune a kan ɗan tudun da aka tanada domin zama ," ji suka yi iskar shaƙa ta musu yawa a saboda gudun da motar ke yi ,"nan take maƙoshin su ya bushe ƙemas , idan ban da sharar hawaye babu abun da suke yi ,tun da suka hau motar babu me cewa ƙala ,"

Gware yakaka da falmata suka yi ," a sakamakon wani irin birki da motar da suke ciki ta jaa," wani marayan kuka falmata ta fashe da shi a dalilin zafin da ya ziyarci ƙwaƙwalwar ta a dalilin gwaren da suka yi ",

Dira sojojin da su ke tare da su a bayan motar su ka yi kafin su yi musu umarni akan su sauƙo ,

Tsayawa yakaka-da-yagana suka yi suna ƙarewa wurin da aka kawo su kallo ,"wata babbar kofa ce a gaban su me kama da kofar gari a ganin su, sai da ƴaƴan hanjin cikin su yakaka ya kaɗa sakamakon ganin wasu gungun sojoji da suka yi daga cikin wata rumfa a gefen kofar ,"

Yakaka ina aka kawo mu ,? Inji falmata ,"

Nima ban sani ba falmata ,amma dai kamar wani babban gari ne shima gashi dai har da wata babbar kofar sa ," ta furta hakan tana me satar kallon sojojin da koh kula da su basu yi ba,"


Ku zo mu je nan shine camp (sansanin ƴan gudun hijira ) inda gwamnati ta tanadar ga ire-iren ku ," a cewar wannan sojan da ya wuce gaba ,"

Da sauri su ka bishi ransu yana wani ɗan motsin daɗi-daɗi ! Duk da cewar dai basu gama aminta da zancen sa ba domin basu tabbatar ba ,'


Yakaka da yagana su na sanya kafa cikin wurin suka fahimci ba ƙaramin babban fili bane ta ciki , a yayin da suka fara yawata idanun su zuciyoyin su cike da mamakin ganin mutane birjik fululu iyakar ganin su suna ta harkokin su ,"

Hayaniyar jama'ar da falmata ta fara ji yana tashi cikin yaren su , shi ya sanya ta ji kaso goma na tsoron da yake cike da ranta ya kau ,!

Bayan ƴar gajeruwar tafiyar da suka yi , bakin wani gini sojan nan ya tsayar da su yayin da shi ya taka ya shiga cikin ɗan wurin mai kama da ɗaki ,"(Office)" bai kai minti biyar ba ya fito ba tare da yace da su kome ba yayi wucewar sa cikin rashin kulawa da gaisuwar da wasu mutane maza da suke zaune turmus a cikin ƙasa da suke yi masa ,"

Cigaba da tsayuwa su yakaka suka yi a wurin har dai zuwa lokacin suka fara jin ƙafafuwan su sun fara sagewa a gefe guda yakaka da yagana cikin ransu suna nazarin tsarin wajen ," daga gefe gine ne a jere reras tamkar ɗakuna da barandar su doguwa wanda aka yi ginin da bulok tare da rufin kwanon da suke iya hango rufin sa da duk rana da ruwa suka gama illata sa ya zama jazir ," babu abun da yafi yawa a sararin wurin irin bishiyoyin darbejiya wanda suka lura karkashin kowacce bishiya a cike yake da mutane maza waɗan da suke zazzaune wasu kuma a kwance ,yayin da wasu suke a kishingiɗe turmus a cikin ƙasa ," daga inda suke tsaye suna iya hango matan da suke cike a cikin kowanne ɗaki har zuwa barandar ,' dukkanin su mata ne da ƙananun yara da kallo ɗai-ɗaya su ka yi musu suka fahimci halin tagayyara da wahalar da suke ciki ( makamanciyar ta su ),

Daga farfajiyar wurin da babu wadatar bishiyoyi wasu manyan ɗakuna ne wanda aka yi su da ƙarafuna tare da rufin leda mai nawi ,"tantinan wucin gadi ", nan ma a cike yake da mutane maza da mata ," wata boyayyar ajiyar zuciya yakaka ta sauke lokacin da taga wasu maza sun zo sun wuce ta gaban su ,"hannun su riƙe da buhun-hunan da ta gane na abinci ne ,

Yakaka wai tsayuwar nan kam ba ta ƙare ba ce koh ? Yagana ke furta hakan a lokacin da ta karya gwaiwar ta da nufin tsugunnawa , "sai dai bata kai ga tsugunnon ba taji ɗaya daga cikin mutanen da suke zaune karkashin bishiya daga gefe ya ce ," kai kai ku tashi daga nan chan za ku tafi ku nemi wurin zama," yana yi musu nuni da sashin ɗakunan nan. "


koh kafin yagana ta samu abun faɗi ,"suka ga an fito daga wannan ɗan ɗakin da daman suke dakon jirin fitowar mutum daga cikin sa ," da sauri suka zube ƙasa suna gaishe da ɓakin jibgegen mutumin da yake yi musu kallon sheƙeƙe ,"

Ba tare da ya amsa gaisuwar ta su ba ya fara cewa to menene ,? Menene kuma ? Kai Duba ni fa na fara gajiya da ku da ƙorefe-korefen ku , ku koma can daga wurin ku idan waɗanda Alhakin faɗa musu ƙorefe ƙorefen naku ke wuyan su , sun zo kuna iya zuwa kuyi dafifi ku faɗa musu , amma nikam bazan iya wannan halayyar taku ta rashin godiya ba

," wuce su yayi tinƙis-tinƙis yana tura cikin sa tare da mita ,"haba ace mutane sam baku da godiyar Allah a ɗau nawin ku ci da sha da gurin kwana ba tare da koh sisin kobo ba amma duk da haka kullum ta Allah sai kun zo da sabon tsirfa ,"yau ku ce wance gobe wannan koh da yake ba laifin ku bane ," gwamanati da ta ƴanta ku daga noma da shan ruwan kududdufi ita ke da laifin ",

An ɗauki tsawon mintuna biyu babu wacce tace ƙala tsakanin su ukun , kowacce da abun da take saƙawa cikin ran ta ,"

Yaraf ,"yakaka ta ƙarasa bajewa a ƙasa daga durƙuson da suke ," a sakamakon bangaje ta da wata mata tayi wacce take tafe tana ta zabga sauri har zanen ta na kuncewa bayan ta kuwa wasu mata ne su ma gungu sun doshi wajen su hamsin koh fin haka ," wucewa suka yi tare da nufar sashin da su ka ga ɗazu wasu maza sun bi da buhunhunan abinci .


Cikin sanyin jiki suka miƙe tsaye Falmata tana me sake lalubar jikin yakaka wacce ta ke riƙe da ɗayan hannun ta ,"

Yakaka ya akayi kika faɗi baki ji ciwo ba koh ?

Banji ciwo ba falmata ," ku muƙarasa daga can .


Watau nan shine masaukin da gwamnati ta tanada domin ɓaki ƴan gudun hijira ,"? Yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da suke zama a bakin ɗaya daga cikin fasasshiyar barandar wurin ,"

a toh ga zahiri dai kin gani ,"cewar yakaka wacce gaba ɗaya ta gama tsinkewa da irin rayuwar da ta hango musu a wannan matattarar kazo na zo ɗin ,"

Wai yaya fasalin tsarin wajen yake yakaka ?. Yanzu fa ba zama yakamata muyi ba , dacewa yayi mu fara zuwa mu ƙarbi abinci mu ci sai muyi sallah mu bazama neman mama kamar yadda muka tsara ko kuwa ?

Haɗa ido yagana da yakaka suka yi kafin yagana ta ce hmmm ai falmata bamu kai ga fahimtar tsarin wajen ba tukun ," ga mu nan dai kara zube kamar yadda muka lura kowa ma a zuɓen yake a wurin nan ," amma bari naje na fara da tambayo mana inda banɗaki yake domin ni mara ta ma cike take dam ,"

Lalee ,sannun ku jama"a dan Allah ina ne inda banɗaki yake ? Sannan kuma ina ne wurin cin abinci mu ɓaki ne yanzu muka zo ," yagana ke yin dogon bayanin nan bayan da ta tadda wasu gungun mata da su da ƴaƴan su a zaune cikin ɗaya daga cikin ɗakunan nan ,1


Ga mamakin yagana ba wacce ta ɗago kan ta ta ɗube ta bare ma ta sa ran za'a amsa ma ta ," duk kuwa da cewa cikin yaren su tai maganar kuma zanen da yake ɗauke a fuskokin mafi yawan matan wurin da suka kusan tasamma su arba'in ya isa sanar mata cewar daga ƙabila ɗaya suke ita da su ,"

ɗai ɗaya take kallon su yayin da ta ke jin wani irin ɗan banzan wari da zarnin futsari yana cunƙushe mata kofofin hancin ta ,' ƙudajen da suke yanyame cikin ɗakin da babu koh shimfiɗar tabarma sai ɗaben suminti ," sai kuka suke yuyuyuyu , gami da kukan ƙananun yaran da wasu ma koh ɗan kanfai babu a jikin su , sai tarin layu da zaren jigida a ɗaure a ƙugun su ," shi ya sanya yagana tayi hasashen koh hayaniyar cikin ɗakin ne ya sanya wasu basu ji ta ba ,"


Sake maimaita bayanin da tayi da farko tayi ," Can baya zaki zagaye kiyi abun da zaki yi maganar abinci kuma ba'a kai ga kammalawa ba ," ki adana sauran tambayoyin ki domin mu ma nan duk da kika ganmu riƙe mu ke da tarin tambayoyin da muke son samun amsoshin su ,"1

Tsam yagana tayi a tsaye bayan da ta gama jin bayanin matar nan ,"jan ƙafafun ta ta soma yi da nufin barin wurin alokacin da taji matar nan ta ɗora da cewa kika ce ku ɓaki ne ? Ke da su wa ? Ba tare da ta jira amsar yagana ba ta ɗora da cewa kun kaima barka domin kuwa a yau gwamna ke kawo ziyara ƙaron farko a sansanin nan ," nan da kika gan mu a zazzaune dakon jiran sa muke ," domin ance tafe yake da tarin kyautukan alkhairi .


Ai nan take yagana ta washe baki ji da tayi sun taki sa'a lokaci ɗaya ta ji ta nemi sanyi jiki da taraddadin da ya fara mamaye ta a sakamakon bayanin matar nan na farko ta rasa ," farin cikin albishirin da matar tayi mata na ganin gwamna ra'ayul'ain a yau ya wanke mata bacin ran da take ta shaƙa tun fitowar ta daga garin su ai da gudu ta kwasa har tana murguɗe kafa tayi wurin da ta bar su yakaka .

   

Post a Comment for "MAFARI CHAPTER 1 BY UMMU AZAMM"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...