LABARIN RAYUWATA CHAPTER 8 BY Ayeshay bee - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 8 BY Ayeshay bee

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 8 BY Ayeshay bee

- - Post a Comment

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 8 BY Ayeshay bee
                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

A daddafe na daure na ke rubata jarrabawan da duk rubutawa kawai nake. A ranar papern mun na karshe ne muka hadu da mai Aliyu. Don har cikin school yazo ya same ni, yan makaranta na ta gulman su mu kayi kaman bamu ji su bama muka fita abin mu. Yanda muje yi duk ranar da yazo ya same ni a makaranta, direct wucewa muke ya taka min har zuwa kofan gidan Goggo. Yau in ma hakan ne ya kasance, mostly ma labarin School insu ya ke bani dake ya kwana biyu da fara karatu a  garin bauchi.+

"Bai in dan amso abu a wurin abokina pls" Ban kawo komai a raina ba na ce mishi "muje mana" Haka mu ka cigaba da tfy, yana ara jana da hira ina dan amsa mishi sama sama dake matsalolin da ke gabana sun fara fin karfin kaina.


A haka har mu ka karasa kofan wani gida mai dan girma. Wayan shi ya ciro ya kira abokin nashi ni dai ina tsaye a gefe ina jiran ya amshi abinda zai amsan mu wuce dake ma duk hanya ne sai dai kuma ba hanyan da muka saba bi ba. "Suhaima mu shiga please, yana so wai ku gaisa da matan shi" bude baki nayi idanuwa na kyar akan shi. "Matar shi? Kana da abokin da yayi aure ne daman?" Dariya ya min yace "lallai ma suhaima wlh kin raina ni. Kuma ma fa mu maza ba wai irin ku bane, saboda mu muna abokantaka har da wadanda suka girme mu, ba kaman ku da kuke ganin shi a matsayin ci baya ba." Ban ce mishi komai sabida nasan gsky ya ke fada. "To Amma ya akayi ya sanni da har zai hada ni da matar shi ku gaisa" murmushi yayi yace "Suhaima kenan an gaya miki akwai wanda yake tare dani da bai san ki bane?"  Ina shirin magana sai ga abokin nashi ya leko. "Mai ku shigo mana ku tsaya nan, ko madam in taka ba ta son shigowa ne?" Saurin sadda kaina kasa nayi, ina mamakin sunan daya kira ni dashi. Nasan maganar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi balle har ma a kirani da madam in shi. Fara'an abokin nashi yasa na basar kawai muka gaisa. "Please shigo ku gaisa da madam sai ku tafi mana" wani nauyin shi naji a lokacin, hakan yasa ban iya musu ba na bi bayan su muka shiga har cikin gida.

Sai bayan mun shiga naga girman gidan sosai. Ashe ta waje nema bai nuna wani girma ba.ga kuma space sosai kafin a kara sa cikin main house in. Haka dai na ta bin su har zuwa falon gidan. Iya haduwa wurin nan nayi don har na fara tunanin baban yarinyar wani attajirin mai kudi ne a cikin Damaturu, in ba haka ba irin wannan kaya kan sai dan wane da wane. Muna zaune kusan mintu uku ya shude, sai ga abokin da tray dauke da drinks da cups. "Sorry Suhaima, ta fito wanka ne tana sa kaya bara tazo" ban ce komai ba, banda murmushin da nayi. Motsin da nake ta faman ji ya sa na aminta akwai mutum a cikin. Duk yanda abokin ya matsa ku sha ruwa, kokallon teray in banyi ba. Ina dai zaune a haka dan har na far kosawa. Abokin ya kara fito, wannan karon kala bai ce min ba yayi hanyan kofan waje. "Ni kam mu tfy kawai" na cewa mai Aliyu sai dai banda murmushi ba abinda yayi min. Ina shirin kara magana naji bude kofa, ban juya ba don nasan abokin ne. Sai dai jin karan mutum a kusa dani, ya sani daga kai. Dum! Naji gaba na ya fada a sanadiyan wanda na gani tsaye gabana, Yaya Baba. Har ga Allah ba abinda ya fara zuwa min a kai sai shi inma kila gidan abokin shi ne. Nan take na murtuke fuska saboda na tsanin ganin shi. Dariya yayi ganin reaction ina "an gaya miki zaki taba guje min ne? Lallai baki sanni ba yarinya" ko kafin hankali na ya gama fahimtan abinda ya ke nufi sai jin wani irin nauyi nayi a kaina. Ban san lokacin da na saki wani irin razanannen kara ba saboda bugun wani abu ds ban iya tantance menene ba ya sauka a kaina. Idanu nane su ka fara kokarin lumshewa, yayin da nake iya jiyo sautin muryan maza dayawa a take a kaina sai babbakewa da dariya suke "Yarinya yau kin shigo hannu, irin wannan nama haka?" Ban san wa yayi maganan ba saboda yanda nayi nisa da fara fita daga cikin hayyacina. Da kyar na iya saita idanuna kan Mai Aliyu da naga wanda ya shigo damu gidan yana mika mishi wasu irin makudsn kudi. "Jeka kuma kar in sake inji wani zance kan wannan abun" da kai ya amsa ya mike, sai da yazo fita mu kayi ido huddu dashi. Wani irin kallo naga yana jifa na dashi, ba zan ce kallon menene ba amma dai nasan bana mugubta bane. He looks so helpless a haka ya fita ya barni a wannan wurin daban san me ke shirin faruwa dani ba. Ga wani irin azaban zugi da kaina har ma gabadaya jiki na ya dauka. Kwakwaran motsi na kasa, haka sautin murya na ba abinda ke iya fitowa. Ban kuma fahimtan duk wani abinda suke fada gabadayan su. Kasa fada nayi dasu lokacin da daya ke kokarin yaga kayan jikina, tun ina bige shi da kafana, yana zuba min wata azababbiyar mari na rafke a wurin gashi dama can kaina bai iya motsi. Amma haka na ciga da kokarin hana shi da hannuna, yana jan kaya ina ja. Hauri na yayi a karahe da kafa, a kuma kan cikina dole yasa na kasa komai har ya cin ma burin sa.4

A cikin irin wannan halin mutanen ba tausayi ko wani digon imani su ka fara far min, bansan su nawa bane haka kuma ban san ko har da yaya baban a ciki ba. Tun na farko da ya fara shiga na, na saki wani irin ihun da nasan ba zan kara yin irin shi a rayuwa ta ba. Ba ko alaman tausayi ya cigaba da abinda yake yi, yayyin da nake jin wani irin dimauta, zafi, azaba da tashin hankali na kewaye dukkan ilahirin jiki na. Karan da nake yi yasa su ka kure sautin waka suna cigaba da kwasan dariyan su, daga baya yana sauka wani ya sake hawa kaina. A ranar na san cewa duniyata tazo karshe, amfani na ya gana karewa haka kuma banda sauran utunci a cikin ta. Na sha azaba irin azaban da nake ganin ba wanda ya san ta, a lokacin duniya ta tsaya min. Tun ina kuka da ihu har sautin murya na ya fara gushewa. Sai ya zaman to gani nan ne dai kawai a raye, ba ehmm ba ehk ehm banda hawayen bala'i da ke ta faman bambali daga cikin idanuna. Rounds suka maida abun, sai da suka gama yin yanda za suyi dani sannan su ka kyale ni a jefe a gefe kaman wata tsumma, dai dai lokacin kuma na fara jin kaman abu na shirin gushewa daga jiki na. Don wlh na dauka mutuwa ce tazo min gadan gadan. Tun ina kokarin tsaida numfashi har na gagara, nimfashin kuwa ya tsaye tak.1

Ban san tsawon lokacin da na kai a hakan ba Wai dai saukan ruwan sanyin da naji a jiki na ya sani farkawa a gigice ina kallon mutumin da ya shigo da mu cikin gidan a tsaye a kaina. "Malama kina iya fita? Ina bukatan kulle gidan" sama sama ba ke jin sai dai ko yunkurin mikewa nasan bazan iya ba. Bala'i ya hau yana ta masifa har yana kokarin harbi na da kafa. Dai dai lokacin kuma naji an turo kofan falon da karfin tsiya. Ina iya jin saukan idanuwan mutum a tsaye a kaina. "Meya faru?" Shine abinda na fara jin ya fito saga bakin shi. Dai dai ban iya tantancewa dani yake yi ba koda Wanda ya iske a tsaye a falon yana kokarin harbi na. Haka kuma tsakanin mu ba Wanda ya iya amsa shi.

"Nace me ya faru" cikin tsawa yayi maganan dan ko ni da nake cikin rai ko rashin shi sai da na girgiza. "Wai ka duba mana" dayan ya amsa shi hade da Jan siririn tsaki "Mu za aka ustazancin karya? Da ba a San ungulu ba..." Bai karasa yayi tafiyan shi ya shige hanyan dakin da ya fito.

Rike kai yayi,ya cire glasses in shi ya ajiye gefe. Sai na ga ya sunkuyo ya tsugunna a gabana yana kokarin juyo da fuskana. Ido hudu mu kayi, said lokacin na gane wanene a gabana. "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Adams ya shiga uku, ya tabe kuma ba zai taba gamawa da duniya lafiya ba wlh" nan da nan naga ya rike da, yayin da idanuwan shi kuma suka sauya kala. Jijiyoyin kanshi kam duk sun taso.

Hannun shi ya dora akan goshi na yana sake min kallo, sosai na ke hango tausayi na kwance cikin idanun shi. Tabbas, ba dan waccan karon shi ya kwace ni saga sharrin Yaya baba da wannan karon ma da in amshi taimakon shi gwara in dawwama a cikin halin da nake ciki har mutuwan tazo ta riske ni a wurin. Tun da na Riga na gama Sanin rayuwata ba ta da wani amfani kuma. Bai kara cewa ya mike. Shiga daya data cikin dakunann yayi sai gashi ya fito da dogon Riga da hijabi. Daman kayan da ke jiki na Uniform ne kuma duk sun yayyage ta inda har ana iya hango wani sashi na jiki na. Ni ko duk hakan ma ban jin ya damene. Tun dai mai afkuwa ya afku ai shikenan komai ya zo karshe kuma,don nasan rayuwata ta tsaya cak. Ganin ba yanda zai yi ya sa Mon rigan ya sa ya ajiye kawai ya dauke dogon hijab in nan ya sa ka min. Kaman jaririya haka ya cincibe ni, yayi waje dani. Saukan nan da ya min ya famo min azaban da nake ji ya mamaye a gabadaya ilahirina. Tun ina sakin wahaltaciyyar kara har ban san lokacin da na kara wani suman ba.

Ban kara Sanin komai ba kuma sai tashin da nayi na tsinci kaina kwance a gadon asibiti. Ga drip nan a hannu na, haka kuma azaban da na keji har ya zu bai gama gushewa ba. Gani ma ban yi da kyau, ga dan banzan nauyin da nake ji kaina ya min. Kokarin daga shi kadan, sai inji kaman dutse aka dauko a ka dasa min a kan.

"Sannu me ke miki ciwo?" Sai lokacin na gane akwai mutum a dakin, taso yayi dagabinda yake zaune, idanuwan shi sunyi ja jawur har yanzu. "Dan Allah ka fidda ni da garin nan" shine abinda ya fara fitowa baki na.

Da tausayi fall idanun shi ya ke kallona, ban san abinda yake ji ba amma nasan abun ba karamin zafi ya ke mishi ba.

"Kiyi hakuri Dan Allah Suhaima, let me follow the appropriate way in kwata miki duk wani yancin da kike bukata. It won't go free, wannan alkawari na miki. Dukkan tsanani da rashin hankali sai na kwato miki yancin ki"

Runtse idanuna nayi yayin da hawaye yayi saurin fitowa ta cikin idon. Tabbas na Riga da nasan na shiga tashinnhankalin da nasan bai da karshe. An riga an cuceni iyakan rayuwata na duniya.

"Daga yanayin ki kadai Suhaima nasan kina jin dacin da rayuwa ta yi miki. Nasan kina jin da man baki zo duniya ba. Tabbas, abun nan da ciwo irin Wanda ba zan iya misalta shi ba saboda ban san ya hakan yake ba. Amma let us do the right thing" a hankali na bude idanuna ina kallon shi, yayin da zuciya ta ta fara kitso min shin me ye sa Umae sanda ke taimako na a halin yanzun bayan nasan yana daya daga cikin manyan makiyana a da.

"A yayin da kunci, bakin ciki da kuna suka kasance abokan zaman ka.

A lokacin da jigo majigina ya bace ma.
A sanda mahimmanci, natsuwa da annashuwa ya kau

Rayuwa ta zama tamkar guba a gare ka.

komai ya zama tamkar dafi da daci a wurin ka.

Sanadiyyar gushewar Uwa, Mahaifiya a rayuwar ka." Magana nake ina jin zafin na Dada karuwa a raina haka kuma ina kara jin a raina komai ke faruwana dani mahaifiyar tace ta na min, domin ita ta bada lasisin abinda  ke faruwa. "Tun bayan gushwan ta, banda komai kuma mai ma'ana illa mini da ke ratsa rayuwata a ko wani irin hali. Ni kam na gaji, ina ma haka CeCe ni ba, ka barni da team tsan wahala na, kila da na rasa rayuwan gabadaya, ni na huta wadanda su ke burin ganin gushewa ta su huta suma"

"Subhanallah!" Saurin taron numfashi na yayi, yanzu kam ba shakka kwalla ne ke tsiyaya daga idanuwan sa. "Kar ki fadi haka Dan Allah, ki duba rahaman da Ubangiji ya miki Wanda wasu ma basu samu irin shi ba. Suhaima, nima na rasa mahaifiya ta tun ina dan kankani, na taso cikin rashin gata sai dai ba kaman irin naki ba saboda ba Wanda ya tsunguma min amma kuma bani Wanda ya damj da tawa rayuwan. Hakan ya sani kwace hanya, har na fara rashin ji kala kala duk unguwa ya dauke da irin mugun hali na. Nina fara koya ma Adams shaye shaye, wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa ni din ban iya barin shi ba bayan ya zama abinda kike gani a yanzun. Sai dai ance dalibi ya kan koya ma yafi malamin, hakan kuwa ya kasance tsakanina da Adams. I used to have a messed up life, a lokacin kowa ya guje ni hatta Anty Yana kyarata take yi sai mahaifiyar ki kawai ke kokarin kira na tana min nasiha at the same time tana kyautata min. Rashin hankali na a lokacin sai ya bani cewa dan aiken da taga tana min yasa take kira na da sunan nasiha, sai na dauke ta a matsayin wanda ya takura min shi yasa lokacin da aka ce ta tafi nake farin ciki, ko bakomai ba wanda zai dinga min fada. Recently, da na koma gun mahaifiyata da zama, da addu'a da daura ni kan hanya na gano hanya mai kyau. Hakan yasa na gane kaina sannan na kuma gane na miki babban laifi a wancan lokacin, ina fatan zaki yafe min?" Kasa amsa shi nayi, ina mamakin lbrn da ya bani wanda ba ko shakka nasan hakan ne.

"Su waye ne?" Abinda na fada kawai kenan ya gane me nake nufi. "Kungiya gare su, da nima ina ciki saboda a lokacin ma ba wanda ya kai ni kaurin suna cikin su. Duk wadanda kika gani yaran masu kudi na a garin nan sosai hakan yasa Duke da daman yin iskancin su son ransu. Sun sha kawo mata suna raping, sai dai kuwa in ba a kyallo ki ba. Ke ma ai tunda suka ga kin fara mutunci da Mai Aliyu su ka fara bibiyan shi. Iyayen shi ba wasu masu shi bane, duk kokarin shi bai da hanyan zuwa jami'a ga kuma mahaifiyar shi kwance rai hannun Allah ba kudin asibiti. Da wannan su kayi amfani da, gabadaya ma su su kayi sponsoring karatun shi haka kuma suka biyawa mahaifiyar shi kudin aiki ta warke. All because daya daga cikin su ya ganki da yake wurin Adams kuma kin biya mishi rai. Ba dan nan garin bane ma, shi ma baban shi babban kusa ne a garin kano."

Wani irin rudu na kuma shiga jin labarin da yake bani kama shirin film ko tatsuniya. "Amma me yasa shi da kanshi yayi attempting far min?"

"Its all a plan Suhaima, shi wancan in yana daki yana jiran bayan komai ya kan kama yazo. Baki ban daman da zan iya miki magana ba ni kuma ban san in ta bibiyan ki. And don't think am so innocent, kaman yanda na gaya miki dani aka fara abun nan. I was the first guy da na fara raping daya daga cikin yan matan ba a nan garin ba a kano. Suna hude kungiya ne garin gari suna rabawa matasa kudi dominsu yada manufar su. Sai dai tun abinda ya faru tsakanina da yarinyar nan, naji rayuwata ta dimauce, na natsuwa duk wani tunanin na ya kau. A kullum duniya in na kwanta sai nayi mafarkin yarinyar nan tana min ihu in kyale ta. A haka abun ya fara yawo har ya dawo banda wani tunanin kirki kuma. Dole naje na nemo ta bayan dimbin wahalan da na sha da kyar na same ta. Sam taki ta yafe min duk yanda na nuna mata Dana Sanin sai dai ta sanar min yanzu haka an FASA auren ta saboda abinda na mata. Ta hadani da yan unguwan su, su ka min wani irin duka da zai da na kwana asibiti. Bayan nan aka wuce dani cell, ba karamin wuya na sha duk da haka ji make nayi deserving komai. Ban san ya akayi ba, daga baya yarinyar tazo tace ta yafe min. Ko da na nuna zan aure ta, sai ta sanar min an sa mata rana da cousin inta. It a life changing experience tunda daga lokacin na dawo turban gsky. Sai suka watsar dani duk da haka ban damu ba, haka kuma yanzun ma sun kira ni ne saboda in ga sun ci manufar dana hana su da farko. " wani irin zufa naji yana keto min a lokacin, da kyar na iya tashi daga kan gadon ko kafin ya ankara ma fisge drip in dake hannu na. "Dan Allah ka fidda ni garin nan. Wlh na tsani in bude ido in mini ina shakan numfashi a cikin ta. Duk da gari nane kuwa"

"Ina zamu je Suhaima? Dole mu tsaya ma a nemo miki yancin ki" girgiza kai nayi na dan cike baki "Baban ka na wani bane a garin nan haka kuma kaima nasan haka da abinda za ka iya jayayya da yayan attajirai irin su. Allah ya isa, Allah ya isa, Allah ya isa." Ina gama fadin hakan nace "Kai ni Maiduguri, Goggo na can ba lafiya" bai kara cewa komai ba sai wani irin sanyi da jikin shi yayi.

A motan shi mu ka tafi har garin Maiduguri. Ya kaini har cikin gidan Baffah. Hatta kafa na ma da kyar na ke taka ta, ga magunguna kala kala daya hada ni dasu. "Ki kulla da kanki Dam Allah Suhaima,  da kuma dukkan abinda nurse in nan tace miki. Bakomai, Allah na nan sannan ina so ki cire damun da nake ganin kin sa kanki a ciki"+

"Damuwa dole ne? Duka duka shekaru na nawa ne a duniya? Amma kasan abubuwan da na fuskanta wani tsohin ma har ya gama rayuwan shi ba zai taba ganin irin su ba" Hawaye shara shara ke zuba a idanuna yayin da na ke magana "Ballantana kuma yanzu da gabadaya rayuwan tawa ma bata da amfani?" Da rudu sosai a fuskan shi ya ke kallona "Ba zan ce kiyi hakuri ba suhaima saboda ina jin baki cancanci wannan kalma ba. Ba a wurina kadai ba, har a wurin kowa ma. Abinda zan ce miki kawai kuma shine, Allah na nan kuma ya san dake" yana fadin haka ya shiga mota yana kokarin tayarwa. Da kyar na iya tsaida shi "Ka gaida Goggo Dan Allah" Hakanan ya bini a baya har zuwa dakin da take zaune. Ina ganin ta na ruga da guda na duk da ciwon da kafafu na keyi, na shige jikin ta. Sai da kuma na shige jikin nata na ji alamun ba karamin ramewa tayi ba. Rudewa nayi in tmbyn ta ba'asi, ba ta amsa ni ba sai datijjuwan matan da ke dakin wacce na gane an kawo tane saboda ta kula da Goggon. "Au Goggona zo da bako bara ya shigo ya gaishe ki"

"Siriki kika kawo min?" Abinda ya fara fitowa bakin ta kenan. Sai da na danyi dariya sannan nace "Aa dan layin mu ne a sabon fegi" ba dai tace komai ba, har Ummar sanda ya shigo su ka gaisa. Har kyautan kudi kuwa ya mata sannan ya fita. Goggo ko taji dadi, dan ita ba dai son mutum mai kyuta ba saboda ita ma gwanace wurin kyautan. Tayi ta sa mishi albarka, sai ce min tayi "Ba zaki je ki raka shi ba?" Ban ce komai ba, haka kuma ban fitan ba har naji tashin motan shi ya wuce. Daganan kullum Goggo sai ta tmbyni gane dashi, ni kam share ta nake yi na kauda zancen. Dan nasan ba wani abinda zai iya taba shiga tsakaninmu dashi a wannan lokacin.

Ba laifi duk da ana yawan zuwa asibiti amma jikin nata yana dan sauki, Alhmdlh. nima naji sauki, saboda duk maganin da aka bani sai da na shanye haka na dinga gasa kaina ina kuka ina zuba Allah ya isa, don har duniya ta kare ban jin zan taba iya yafe ma wadanda suka min wannan abun. Musamman Yaya Baba dashi ne silan komai. In sha Allahu nasan sai sin ga karahen su tun a duniya ma.

Sanda aka koma makaranta ba karmin Dramamu kayi da Abbah ba. Duk dagewan shi, na nuna mishi da in koma Nana Aisha na gwammace in mutu banyi makaranta ba. Goggo ne ta tilasta shi, dole aka siyan min foam in El-kanemi Maiduguri.  Haka kuma na fara rayuwa ta a garin Maiduguri, Borno wato birnin Yarwa. Ba laifi rayuwa gidan ya fi na gidan mn sau dubu duk da ko na san saboda Goggo ne abubuwan suka zo min da sauki, to gashi itama fama take. Rayuwa dai gatanan kawai ne, yau dadi gobe akasin ta. Ban wani samun matsala a makaranta saboda ina jin cewa banda matsalan ind dai ta fannin karatu ne. Ga kuwa dalibai masu kwazo ne sosai aka tattara a makarantan. Haka kuwa muke fafatawa son duk da abinda Mai Aliyu yayi sanadi na katse min dukkan wani mahimmancin rayuwa. Ban jin zan iya hakura da karatun likitanci, ko dan ceton mutane dayawa daga cututuka da kuma taimakon Al'umma musulmi.

Wataranar Asabar aka wayi gari da bakin ciki hade da jimamin babban rashin da aka yi na Inna, abokiyar zamn Goggo kuma mahaifiyar mijin Aunty Amarya. To lamarin Ubangiji kenan, duk da tana fama ita ma dajiki wanda tsufa ne ya jawao amma ko kusa ba za a hada ta da abinda Goggo ke ji. Amma da ke lokaci yayi, ko ba ciwon tafoya za ayi. Goggon kuwa ta ji mutuwan sosai. Musamman su mutanen da, duk da ba za ace ba a taba samun sabani ba, amma kuma anyi zaman mutunci. Duk da ciwon kafan ta hakanan ta sa su Abba da Baffah a gaba sai da suka hakura suka kaita Damaturun. Har aka yi zaman gaisuwan kwana uku, sai daida ka ganta kasn abun yana damun ta sosai, karshe dai ciwo ya tashi gadan gadan kuma shi yayi sanadiyyan komawan mu Borno ba shiri. Abinda ake gudu kam hakanan sai da ya faru. Wannan lokacin ma ba karamin jinya tayi a asibiti ba, da ka ganta kasan tan jin jiki. Ni kam duk lokacin da tayi irin wannan ciwonba karamin damuwa nake ba, kai hatta yanayi na bai boye hakan har wani irin rama na daban nake. Na riga na san ita ce gata na a duniyan nan, kuma raahin ta ba karamin girgiza ni zai yi ba. Sai dai alamu na yawan nuna ban da wani zabi a rayuwa kuwa.


Tun bayan tafiya Umar Sanda bai kara waiwayo ni ba sai bayan shekara daya. Lokacin already na riga na shiga SS3. Kawai sai dawowa makaranta nayi na iske shi suna ta hira da Goggo. Da ke jikin kwana biyu ya mata sauki. Ni da farko ma ban gane shi ba sai da na matso kusa sosai. Ya kara fari sosai sai kace wani balarabe ga kuma wani irin kasumba da duk ya cika mishi fuska.


"Baki gane shi ba halan?" Goggo ta fada. Murmushi kawai na mata, daga yanayun muryan shi ne ma ya sa na gane shi da kuma kamannin shi da bai gama bacewa ba. Gaishe shi nayi, ya amsa cikin fara'a. Daga nan na basu wuri da Goggo su ka cigaba da hiran. Sai da yazo tafiya ta sani raka shi. "Ko ki zauna muyi hira" ya fada bayan na taka mishi wurin motan shi. "Ai naga kuna yi da Goggo." Dariya ya dan yi sannan yace min "Da fatan kina lfy dai ko? Kwana dayawa"


"Alhamdulillah" kawai nace mishi, a raina kuwa ban daina mamakin har irin kiban da ya kara ba. Ni dai ganin nan a yar figigiya ta har yanzu.


"Sorry tun da muka rabu dake ban kasan ne shiyasa ban zo na duba ki ba" ya fada yana kokarin bude motan.


"Lah bakomai, karatu kaje hala" bai amsa ba sai ma ce min yayi "Ya makaranta Suhaima, hope dai komai yana tafiya lafiya ko? Baki da wata matsala?" Da kai na amsa mishi, a raina kuwa ina mamakin mai yasa ya damu da rayuwata. In fact ni tun bayan wancan abun ma ban taba tunanin wai zai kara dawowa wuri na ba. Kallo na ya juyo yana yi sosai kaman mai son fahimtan wani abu a fuskana. Ban san me ya gano ba naji dai yace "Dan Allah ki dinga fawwala wa Ubangiji dukkan lamarin ki Suhaima, Allah ya shige mana gaba. Bara naje kinsan garin naku is not zafe, mutum yayi dare sai kiga yaran can su  tare hanyan azo a samu matsala" Yana nufi Boko haram, saboda zuwa lokacin ta'addancin da suka yi a garin Maiduguri har ya baci. Infact har ya ma shiga garin Yobe. Sai dai dake Unguwan su Baffah unguwa manya manya wadanda su ke ji dasu ne. A ta nan wurin gidan yake hakan yasa tarzoman bai ciki ketarowa ta wurin ba. Sai dai kuma zaman kullum ciki  fargaba ake, ba daman fita ko makaranta a rufe a bude haka ake yi.


Shi ga motan yayi, Babban leda ya ciro ya miko min "Ga tsaraban Cairo, zan kira ki na wuce" amsa kawai nayi ina kallon ledan ina kallon shi. Sai dai tun kan na samu daman mishi godiya. Yayi saurin jan motan shi ya bar wurin, Allah kenan, abun godiya.

Ko da na shiga gida kuwa banyi wata wata ba na bude ledan. Kayan da na gani a ciki ya sani daukowa da mamaki ina dubawa. Abaya na har guda biyu da veils insu peach da black. Nayi mintuna ina mamakin wannan irin kaya haka, tunda dai ba wannan sabin a tsakaninmu da zai kawo min irin wannan abu. Bayan kayan kuwa, sai wani perfume na larabawa mai dan banzan kamshi sai kuwa yar karaman waya. Na dade a raina ina tunanin dalilin da zai sa ya kawo min irin wannan kyautan. Rudewa nayi, dile na dauke su naje na nuna ma Goggo.

Dariya ma tayi ita kam. Tace "wannan ba dan gidan Umaru Machina bane?" Da kai na amsa ta, tace "to ina ce makocin ku ne daman, dan ya miki kyauta kuma sai ki dinga wani mamaki?" Shiru nayi, dan dai a raina ban yadda da wannan dalilin zai sa ya kawo min kayan nan ba. Musamman da nasan ba wani jituwa mu keyi dashi ba, duk da yanzu ya min abinda bazan taba iya mantawa a rayuwa ta ba. Hakika shi din ya kasance mai tausayi, ban shakkan wannan.


Bayan kusan sati biyu, Hakanan na hada wayan daya kawo min duk da dai nasan ba wanda zan kira ko kuma wani ya kira ni. Banda yan danne danne da rage ma kai kewa ba abinda nake yi a wayan sai ko game amma ko app daya na social media ban sauke ba. Ranar da naji wayan yana ringing, banbarakwai naji abun don ni ko ringing tune in wayan ban san shi ba. Kallon wayan kawai nake ina mamakin numban da ya fito baro baro. "Ki dauki waya mana ana kiran ki" Tsohuwar da ke zama da goggo ta fada. Hakanan dai na daure na dau wayan ganin tana kallo na. Hae na amsa sallaman da akayi ban gane waye bane. Sai da naji yace "Sai yau aka kunna wayan kenan?" A daburce na gaishe shi sannan nace "Ban zauna bane saboda school, kuma ma ni banda wanda zan kira ko a kira ni."


"Baki da kawaye ne?" Girgiza kai nayi kaman yana kallo na "Ina dasu kawai dai bama magana a waya ne"


"Yakamata ko a dinga gaisawa, Kinga yanzu sai ki amshi numban su. amma dai kar ki kashe wayan, ko su basu kira ki ba ni zan kira ki mu gaisa ai ko?" Shiru nayi, ina neman inda zan ajiye maganar shi.

"Ko baki son in dinga kiran ki?" Ya sake tambaya. 

Da sauri nace mishi "Aa"

"To ya jikin Goggo" Brief gaisawa mu kayi kafin ya ajiye wayan. Tun daga nan ya kan kira ni amma dai ba kullum, wani lokaci har wurin bayan kwana uku ma. Sai dai yana yawan tmbyna ko akwai wani abu da nake bukata. Akwai ranar da yayi min irin wannan tmbyn sai kawai nace mishi "Ina son Dan Allah a samo min numban Adama kawata ta layin mu"


"Amma gsky baki da kirki Suhaima, ashe ba kwa ko waya?" Kokarin fara kare kaina nayi yace "Aa fa baki da gsky, ko ince dukkan mu baku kyauta ba. Amma shikenan tunda yanzu kin nema, In Sha Allahu za a samo miki"

Ranar da dare kuwa sai ga text in numban ta ya shigo. Da azama na, na dana mata kira. Aikuwa sai ta dauka.


"Suhaiiima" abinda ta fara fada kenan da dan ihun ta.


"Ya akayi kika san nine?" Tsaki taja tace "Dazu Fa Ya Sanda yazo da kanshi wai yana nema na. Ni abun mamaki ya bani sosai wlh, kin fa san shi ba cika shiga harkan mutane yayi ba tunda ya bar zama a garin nan sosai. Gaizuwan mutanema ba lallai ya ke amsawa ba. Sai da na fita yake ce min, wai ke kike son numbana. Ke Allah baki na kasa rufuwa yayi Suhaima, me ke tsakanin ku wai?"


Dariya nayi jin yanda ra dage tana ta min bayani "Kawai dai mutunci mu ke, kinsan kwanaki shi ya kaini Maid shknn tun daga nan mu ke dan mutunci dashi amma fa ba ma wani sosai bane." Siririn dariya tayi, tace min "Dadi na dake rainin wayau, dan mutunci ne har zai zo ya amsan miki numbana. Shikenan kar ki fada, in yayi tsami maji ai" Kyale ta nayi, dan nasan halin ta sarai komai na fada mata ba yarda za tayi ba daman.


"Ya labarin Saurayin mu? Ko ansa ranar ne?"

"Ke shirya dai kizo, ana gama makaranta da wata daya aka sa." Tab, wayaga Adama da miji. Lallai zai sha zuciya.


"Zan zo mana ai dole na ma, Kince mun kusa shiga daga ciki muma" dariya tayi sosai tace "ke dai kika sani Allah. Kuma ranar da aka yi graduation inku, washegari ki tabbatar kin kamo hanyan Damaturu daman" Da eh kawai na amsa mata, dan nasan in naki yarda ma yanzu sai muyi fada. Mun dade muna hira da ita, wanda duka duk maganan aurwn nata ne.


To bayan ta kuna sai Ajiddah da ita kam daman tun a wayan Goggo tana kira na, amma da yake tana makarantan kwana sai ta samo waya sannan take iya kira na. Akwai dai amana sosai, saboda har yanzu muna nan da ita yanda mu ka saba.


Rayuwa ta cigaba da tagoya ba tare da wani canji sosai ba. Kullum dai da irin yanda za tq zo ma dan adam. Umar Sanda ya dade da komawa Egypt, tun da ya tafi ko ya kan dade bai kira ni ba. Amma ranar da na fara ganin international number nasan shi ke kira. Har yanzu dai gaisawa kawai muke yi, sai labarai da ya kan kawo min daya biyu.


"Ya Cairo?" Dan jim yayi kafin yace "Gamu nan dai a cikin ta, Ya kamata watarana kizo ki dana kema ai"

"Ni kuma me zai kawo ni Cairo? Ya Sanda" zaro idanu nayi alamun ba zai yiwu ba, duk da ko ba gajina yake yi ba.


"Kika san ikon Allah? Ai ba yanda Allah bai lamarin shi. Ni ba gani nazo ba yanzun. Sannan kuma ki daina kira na da Sanda, shebi na sha gaya miki ban so"

Kiris ya rage ince mishi, ai kai dan gata ne. Duk da baban shi ba wani mugun attajiri bane amma akwai rufin asiri sosai gsky. Amma maman shi na sha jin labarin wanda ta aura a kanon bayan ta fita daga gidan baban shi, ba karamin mai kudi bane domin a garin kano ma duk girman shi sai da aka san dashi. Daman gata shuwa, kyakyawa don har tafi su Ajiddah kyau, sosai. Da yawan mutane sun ce ya dauko tane musamman a fata da kuma yanayin su baki daya.


"In sha Allah ba zan kara ba, kayi hakuri" na fada cikin saukakan murya, ba tun yau ba ya sha sanar min bai son sunan. Daman baban shi ke kiran shi saboda sunan asalin mai sunan shi kenan. Umaru Sanda, kawai sai kowa ya dauka amma tun da can bai cika yarda ya masa ba, musamman ma abokanan shi bai bari su kira shi da hakan. Sai dai kaji ana Umar Faroukh, ko kuma ma UF, using the initials kawai. Da ke baban nashi ma Umar in sunan shi.


"Ai ke ba kya laifi a guri na, you don't have to apologise ma, kawai ban sin sunan ne" Ba abinda ya fadan bane yayi saurin daure min kai sai irin tune in da yayi amfani dashi wurin fadin. Ba wai yau ya fara ba, amma duk randa yayin sai abun ya zo min wani banbarakwai. Ni fa, ko wayan da muke yi da kyar na saba na dan saki jiki don har yanzu ban gama zama comfortable ba ma.


A haka mu kayi Sallama, sai dai abinda na fara lura dashi kwanan nan hiran namu ya fara yawa. Don wataran hakanan zai kirani ya fara ban labarin abinda ya faru dashi a ranar. Ni dai mamaki na nan dan kare a raina.


Ko da muka gama jarrabawan mu na SS3 baki daya, ban yi wani farin ciki ba kaman sauran yan ajin mu. Savodani kam banga miye na murnar ba, ni dai har yanzun rayuwata jiya i zuwa yau ne, ba wani dadin ta na ke ji. Kai rabo na da dandana wani dadi ma, ina ga tun ranar da Ummi na ta tsallake jiki ta barni cikin kangin Wahala. Duk da na rabu dasu amma ban taba iya manta azaban da na sha hanun bayin Allahn nan. Yaya baba kam, har abada ban jin zan iya yafe mai. Ya riga da ya cuce ni, cuta irin wanda zai bini har karahen rayuwata. Sai dai kuma ina tunanin tun yanzu a duniya ya fara ganin sakayyan Ubangiji. Domin dai karatyn da yake yi ma, tuntuni yaki gamu wa. Ya bar Buk tuntuni yayi Bauchi amma duk bai dade ba ya kara dawo wa gida anyi withdrawing in shi. Sai Yayi Yobe state uni shi inma dai hakan ce ta sake faruwa. Yanzu dai yana poly, amma batun natsuwa babu shi. Yana nan yana ta watingiri, sai arziki shaye shaye fa bin gindin yaran masu kudi yana musu fadanci. Sakayyan duniya dai, ita kan ta Anty Yana ta na gurban shukan ta yanzu. Adda Falmata kuwa, Nursing ta jona bayan secondary. Sai da tazo jarabawan karahe sannan aka zubar harda su a ciki. Taga takaici kam, yanzu dole ta koma State University nan cikin Damaturu ta fara daga farko. Batun aure kam shiru kawai kake ji, ban san jo ta na da samarin a yanzu ba hsky. Amma tub da nake gidan kam nasan suna nan buhu buhu, ina mamakin dalilin rashin auren nata kuwa. Al-lawan ne dai yake Karatu lafiya kalau a Gombe, state university. Ya kan dan kira Goggo shi kam, kuma muna gaisawa dashi ba laifi, lafiya kalau zamu yi ta hira in dai ya kira tan kenan.

Ba a dade da gama jarrabawan ba Adama ta fara min maganar zuwa Damaturu bayan bikin sauran kusan wata da kwanaki. Fir naki zancen, duk da fushin da tayi tayi. Daga karahe dai, sai gata a maidugurin ita da Goggon ta. Na ko ji dadin ganin su, ballantana goggo da na dade ban gani ba. Ganin su yasa Goggo cewa ai ko dole na in tafi, sai dai Adama tayi hakuri sai ana sauran two weeks bikin tukunna.Sauka na garin Damaturu, ji nayi kaman an sauke min garwashi a cikin zuciyana. Saboda wani irin azababbiyar tafasan da ya fara. Zafi na keji sosai yayin da fabadaya jiki na ya dau rawa. To avoid complication, na dau jiki sai Ajeyari duk can inma a yanzu ya zame min tamkar kabari ne duk da ko ban taba shiga a ciki ba. Har yau na kasa sanar ma Anty amarya dalilin da yasa ranar da muka gama jarrabawa a Nana Aisha na tafi maiduguri ba tare da na dawo gidan ba.+


Tayi farin cikin ganina sosai. Baiwar Allah, duk girman gidan nan yanzu ita kadai ce a ciki. Sai yayi wani iri, duk ba dadi. Sai dai itan ma ta sanar min kwanan za su koma garin Bauchi. Anyu ma mijin ta transfer. Adama da ke ta faman jira na da taji cewa Ajeyari nayi, tayi ta bala'i tana hawa tana sauko karshe dai ta kule kaman yanda ta saba. Ban biye mata ba saboda nasan ina komawa gidan zamu shirya da ita.

Hakan ko ya faru, kwana na biyu a ajeyari na nufi sabon fegi. Duk da nasan ba gidan mu zanje amma kuma na kasa boye damuwan da ke mamaye a zuciya ta. Hakan nan dai na karasa, ko kallon hanyan gidan mu ban ba na wuce gidan su Adama. Na iske ma bata nan, mijin ya zo ya dauke ta sun tafi asibiti test wai. Goggo tayi farin  ciki ganina sosai, ni ma kuma naji dadin ganin tan. Don duk  mutumin da ya nuna min so, banji  Ina da kaman shi kuma. Tarba na mutunci da karramawa aka min a gidan, ba laifi yan biki yan nesa har sun fara zuwa. Daman kuma nasan wasu  daga  cikin dangin nasu, musamman yan uwan Goggo da suke yan kollere. Duk da ba su da danganta ka, to amma zaman tare ya hada su da su Ummi na. Ballantana wasun ma da aure ya hada. Na dan yi mamakin farin cikin gani na dasu kayi. Ji kake ana "Ai yar gidan Aeeyn Aminaa ne" tuni na sake a cikin su, sai ma na hau taya su dan  aike aiken  da suke. A haka Adama ta dawo ta sameni. Ba ta ma san nazo  gidan ba, sai gani na tayi kawai bakin famfo ina karasa wanke wurin da aka gama wanke wanke. Da farko harara ta bi ni dashi. Can kuma ko kasa basar da ni tayi, sai kuma tazo da gudu ta rungumeni tana dariya tana turo baki.


"To ai sai ki sake ta hakan nan ko, ko sai kin karya ta" Turo baki Adama ta sake yi jin yanda Goggo ta hau sababi. "Ke ko baki da kirki Allah" dariya na danyi, ganin sabon  hararan da take min. "Yanzu dai ai nazo shknn" Hannu ta fara ja tana kokarin nufan kofan gidan. Da sauri na fincike hannun "Baiwar Allah lfy?"


"Dallah can zamu je ku gaisa da shi ne" Sarai na gane abinda ta ke nufi barin ma yanda ta sunkuyar da kai wai ita a dole kunya. "Waye shi?" Na fuske na fada, ai kuwa sai da na sha hara wannan karon ma har da Karin tsaki "Ke fa baki da mutunci ko?" Dariya nayi "Ai kya bari in dauko hijab ko? Ko haka kike so inje ba ko dankwalin arziki" itan ma sai lokacin ta fahimci hakan. Tilas ta sake ni na dauko Hijab sannan muka nufi wajen, Inda ya ke jiran ta a motan shi. Ai ko yana ganin ya fito, yana dan kara fara'an da already yake kwance a fuskan shi. Gaishe shi nayi, bai amsa ba yace "Maraba da babban kawar mu" Dan dukar da kai nayi, Ina mai cike da murmushi.


"Ya makaranta" ya bukata, a daddafe mu ka gaisa har yana tsokana na wai yayi fushi na bar mishi amaryar shi ita kadai. A gsky Adama tayi dacen miji, sai yanzu na fuskanci sanin da na mishi da muna yara ba wani na arziki bane. Ko da yake ma, tunda na gane  Ya baba na cikin su, na tsani duk wata mu'amala dasu.

"Ya abokina kuma?" Da mamaki na dago kaina ina duban shi, don har ga Allah ban wani fuskanci inda zancen nashi ya nufa ba ma. Murmushi yayi fuskantan yanayin da na shiga "Ko baki San fada min? Ke fa yanzu kawar mu ce kuma muna fatan abin ma yafi haka soon, ko kuwa amaryata?" Dariya Adama tayi, hakan yasa na kalle ta cike da tuhuma. Sai dai na fuskanci itan ma kwata kwata ba wai tasan me yake nufi bane.


Karar wayar shi ce tasa na katse tunanin da nake "Mutanen Cairo, yanzu ko nake maganar ka ai" ban ji bai aka fada a wayan ba sai naji Mustaphan ya sake fadin "Dagaske gani ga mutuniyar ka ma ai" Tab! Sai lokacin kwakwalwata ta kawo min me yake nufi, Umar Sanda ne kenan? Tabbas shi dinne ma. Sai yanzu na tuna shi din ma abokin shi ne sosai ma kuwa. Kallon tuhuma Adama ta bini dashi, nayi saurin fahimtar da ita ban San komai a kai ba ma ta idanu. Ba dai ta gamsu ba amma.


Bai dade yana wayan ba ya gama "To ke kinji ance in kula dake fa tunda biki na kika zo dole na dau aikin ya zanyi. Sai dai ke ma fa dole ki kula min da amaryata amana har zuwa sanda za a kawo min ita ko mata ta?" Sadda kai Adama tayi cike da kunya, itan ma ashe tsokanan ta yake saboda ya san ta da shegen kunya.

"Ga Suhaiman nan ai ko? Yanzu za a iya fada mana abinda ake bukata?" Hararan Adama nayi jin abinda ya fada "Ni kam ba muyi maganar da ita ba. Amma zamu tattauna sai mu fada maka"


"Ai da nace kizo ki kika yi ina" ban tanka taba kar mu saida hali a gaban shi. "Ku tattauna in dai zuwa gobe sai a sanar mana. Inma ba a iya fada min a gaya ma abokina kinji kawar mu?" Dariya nayi kasa kasa, Adama ta ja hannu na muka shiga cikin gidan. Muna Shiga kuwa ta Sani gaba sai na fada mata abinda ke faruwa.


"Ba fa wani abu bane Adama, Maganan Ya Sanda yake kawai muna dan gaisawa dashi ne" zaro idanu tayi tana kallo na, sai kuma taja tsaki "Zama kiyi bayani yarinya"


Mun fara shirye shiryen biki Adama gadan gadan, don gabadaya ma bamu da lokacin kanmu. Alhmdlh! Yan gidan mu baki daya basa nan, dake ana hutu wai sunje Maiduguri. Ni lamarin dadi ya min sosai, munyi sabani dasu hankalina kwance.


Ana jibi daurin auren, mu ka tafi can gidan baban ta da ya gini sabo, basu dade da tarewa ba a waziru Ibrahim. Yan uwan mamanta ne zasu yi mata kitso da lalle, tunda already daman an Dade da fara gyaran jiki. Har dare kuwa mu ka kai, sai dai tsaf dani da ita da wasu kawayen ta yan uwansu sai da aka mana kitso da lallen. Duk munyi kyau abun mu.


Sai dai ni da it aka bari a gidan, su sun fara gaba. Sai wurin karfe taran dare har Goggo ta fara kira tana fadan me ya hana mu dawowa. Adama ma nan sai kumbura take, ta kira angon nata yace gashi nan zuwa kuma bai karaso ba. Da alama dai fushi tayi sosai, saboda ko da ya kira daga bayan kin dauka tayi sai nice na fisge wayan na dauka. Sanar min yayi da yana waje, don haka duk fushin ta haka ta hakura ta sauko muka fita, ta San sarai Goggo ba zata bar ta ta kwana a nan ba.


Ko da muka fita yana tsaye jikin motan ya harde hannayen shi yana kallon ta Inda zamu fito. Ai kuwa muna fitowan, idanuwan shi na sauka akan ta. Daga murmushin da yayi ya girgiza kai na gane ya fahimci fushi tayi. Duk ta daure fuska ko kallon sashen shi ba tayi. Tun kafin mu karasa ya bude kofan baya. Adama ta gaya min ba abinda ya tsana iron mace ta zauna a baya shi Kadai a gaba. Sanin haka yasa duk lokacin da ya bata mata rai sai ta zauna a baya taki mishi magana. Ko gane hakan da yayi ne yasa direct ya bude mata bayan? "A min afuwa Gimbiya mana, uzuri ne ya rike ni" ba ta tanka ba ta shiga. Ni dai zagayawa nayi kawai na shiga ta daya gefen har ya shiga ya fara tafiya.


"Ai juya akai gaisuwa ko malam" Naji Mustaphan ya fada. Sai lokacin ma na San akwai mutum ne a gaba. Gyaran murya ya danyi "Amaryan mu ina Gajiya?" A daddafe Adama ke amsawa har su ka gama gaisawa. "Au ba za ka juya ka ganta ta tanka ba kenan?" Dan sauti dariyan shi naji "Musty problem, to ance ma bata sanni bane?" Bansan kuma meya faru ba, sai gani ji nayi Adama na kallona. Hakan ya Sani dagawa dan dole domin inga abinda ke faruwa. Da farko abun kaman gizo ya min sai da na cigaba da kallon shi still naga dai shi dinne ba wani ba.


Mamakin da ke kan fuska na ya gane sai naga ya dan fadada fara'an shi hade da kashe min ido daya. "Ke kuma ba gaisuwa baiwar Allah?" Rasa ma me zance mishi nayi, gabadaya sai na zamo am totally confuse. Ya fahimci hakan kuwa saboda irin dariyan da naga ya cigaba. "To ya hidiman biki? Tunda ni ba za a gaishe nin ba?"


"Ya hanya? Yaushe kazo?" Da kyar nayi dambe da zuciyata kalaman su ka iya fitowa.


Zai amsa kenan mustapha ya katse shi. "Kyale shi kinji Suhaima, bai fada miki zuwan shi ba kuma zai matsa sai kin wani gaishe shi"

"Malam ba ruwan Ku damu" Umar Sanda ya amsa. Dariya Mustapha yayi. Daga nan zancen ya wuce kuma aka koma wani hiran daban.

Gab da zamu shiga kwanan layinmu Umar Sanda ya dan jiyo yana kallo na. Sai Kuma ya dauke idon shi ya maida kan abokin shi. "Tafiyan kafa ya Kama ka fa" duk ba wanda ya gane abinda ya ke nufi, saboda haka mustaphan yace "Kaman ya kenan?"


"I have to used your car" Kaman bashi yayi maganan ba haka ya fuske. Mustaphan ma bai ce mishi komai ba har mu ka isa kofan gidan Goggo. Bai motsa Sai shi angon ne ya bude kofan shi ya zagayo ya bude ma amaryan shi Yana fadin "bismillah wify" da alamun har yanzu da sauran fushin ta, ba tace komai ba fita kawai tayi tana kallon inda nake tsaye, don haka nagane tana nufin mu shiga gida kenan. Sallama na musu ina jin mustaphan na fadin "au dawa za kayi zancen ka kwace min mota Kuma kana gani ta shiga ciki" a saitin shiga naji yar guntuwar amsan Sanda "In ruwanka" ban San ya suka Kare ba. Don ni har na saki jiki a cikin gidan na Kama wata sabgan Sai ga wayan shi ya shigo. "Pls Zaki iya fitowa?" Abinda ya fada kenan directly. Shiru nayi in dan wani nazari, ashe shi ya dauka doubting fitowan nake. "Just for some few minute, I promise kinji"


Da "Toh" kawai na amsa shi ya katse wayan. Ko bakomai ina jin Yana da wani kima da mutunci da nake gani nashi saboda da dilalai na. Ya min abinda ba wanda ya taba kwatanta yi min shi Kuma a cikin lokacin da nake matukar bukatan hakn. Sannan ya San sirri na Wanda duk duniya ba wanda ya sani, Amma hakan bai sa ya tsane ni ba ko yayata ni Sai ma kokarin kusan ta kanshi da yake dani a ko yaushe.

Dan gefe kadan na hango motan mustaphan da bamu dade da dawowa a cikin ta ba. Amma gudun inje bashi bane a ciki yasa na fara waige waige. Yana ganin haka naga ya hasko fitilan motan. Tun kafin na karasa naji Karan bude murfin kujeran zaman banza.

Maido hankalin shi wuri na yayi bayan na zauna. "Hope dai ban takura miki ba ko? Nasan an sha hidima" murmushi kawai nayi nace "Bakomai fah, ban ma gaji ba" ban lura hannuna yake kallo ba Sai da naji yace "Ma Sha Allah, Wacce ta muku abun nan tayi kokari" dan dago hannuna nayi Kaman ni lokacin na fara ganin lallen. Tabbas nima nasan yayi kyau, duk da kuwa ni baka ce ya amshe ni.


"An gama makaranta, da fatan jarrabawa yayi kyau?"

"Muna fatan hakan in Sha Allah" na amsa, ina tunanin abubuwa dayawa a raina. Musamman yanda Umar Sanda ke maida hankali kan abubuwa na sosai.


"Which school Zaki yi" ban ji shi saboda tunanin da nayi tsamo a ciki. "Emhm?" Na tmby. Sai cewa yayi "Ko ba zakiyi School ba aure Zaki yi kema?" Bambarakwai ma naji abun don haka nayi saurin girgiza kaina. "Medicine nake son karanta" na fada Kai tsaye saboda ba ni da wani buri face shi in. Hopefully, ina fatan hakan ya kasance, Kuma ban San meyesa ni jina ina bukatar goyon bayan sa ba.


"Nasan you will make a great doctor but tell me a ina kike planning karatun?"


"Unimaid" na amsa Kai tsaye.

"Why?" For some seconds nayi mamakin tmbyn nashi saboda na San there must be reason behind him. Sai dai in ganin komai is so clear.


"Goggo" kawai na amsa. Nodding yayi in an understanding. Kaman ba zai you magana ba can yace "Na so kiyi a Egypt, zai fi miki sauki da kwanciyar hankali. Beside akwai abinda ya kamata ki sani a can in but everything can wait" ban gane me yake nufi da last statement in shi ba amma kawai na basar. Sai ma tunanin da na fara to yana nufin shi zai yi sponsoring ina a Egypt in da yake magana kenan ko me?

"Baki tmby tsaraban ki ba" ya fada idanuwan shi a kaina ko motsi ba sa yi. Rasa abun cewa nayi, har Sai da sakwanni suka shude Sai yace "Shknn ko baki tmby ba na zo dasu ma" wasu fararen leda guda biyu ya miko min. Ka sa amsa nayi saboda a ganina abun na nema yayi yawa Kuma. "Kar ki damu, ba Sai kin nuna min kin gaji da amsan abun hannun na ba domin dai ba ni na aiko miki wannan ba" Da sauri nace "To waye" tsab ya karanci mamakin da ke kewaye kan fuskata. "Calm down mana, just somebody that likes you. Zaki san waye ne a gaba in Sha Allah" zan kara magana yayi saurin girgiza min Kai. "Kar ki tmby ni pls because I will lie to you. Ni Kuma ko a da can da nasan na aikata abubuwan da basu dace ba Sam banda karya a ciki. Ban iya ta ba. Na fada miki ne saboda kawai kinsan cewa there is somebody out there that loves and care about you. So desperate to see you."


"Saboda shi kake kula da al'amura na" murmushi yayi Sai Kuma ya dan daure fuska "Part of the reason dai. I care about you ko ba dan wannan ba Suhaima. I can't even explain amma dai ki barshi a hakan kawai. Je ki kwanta, nasan hidiman gobe yafi na yau ko?" Da Kai na amsa mishi, yace "to Allah ya tashi mu lfy".


Washegari, gabadaya hidima ya shige mana gaba da har na manta da tunanin Umar Sanda da Kuma abinda ya zo min dashi, Wanda har yanzu ban gama gamsuwa. Amma dake am occupied, Sai ban samu lokacin da zan yi ishshen tunani ba. Throughout ranar ba ban gan shi ba. Sai Ajiddah da tazo wurina duk da rashin Shirin da suke da Adama. Na fahimci abubuwa dayawa game da canjawan ta. Ajiddah ta waye sosai yanzu, idanun ta sun kara budewa fiye da da. Ga Uban samarin da ta tara, manya da ya'yansu. Inda Naira ke goguwa da kanta kawai. Irin labaran da take bani ma a yanzu daban ne. Ba a Damaturu ta tsaya ba ma har Maiduguri duk ta San su. Adama dai bamu wuri tayi, dan na riga na gama sanin nasu ba zata taba zama iri daya ba. Bayan tafiyan ta, Adama tazo tana min korafi ni dai ban tanka ta ba. Bikin ba wani hayaniya, Goggo ce ta hana tace Sam ba a gidan ta za ayi wani bidi'a ba. In dai an daura auren suje can suyi fitsaran su. Nima hakan ya min dadi, saboda ba gwanar hayaniya bace.

Washegari da safe da yaka asabar wurin Sha daya da rabi na safe aka daura auren. Zo ku ga kuka gun Adama. Bari ma tun da aka fara bikin da alamu kiris ta ke jira daman. Dan bayan wannan fushin nata Sai da suka kara samun wani issue in Kuma har aka daura auren fushi take dashi. Duk da hakan dai ba abinda aka fasa, ni dai ko da ya Kira ni a waya yana rokona pls in bata hakuri misunderstanding in shi tayi Allah. Dariya kawai nayi nace mishi "Ai mutuniyar ta akwai saurin fushi, Sai ka shirya da kyau" dariya yayi Yana sanar min shi kam Sai da bikin ya kusa ta fara mishi hakan. Jinjina abun nayi, Dan nasan tayi kokari ma a hakan. But now, is time for him to get ready for the real deal.


Tun around four aka zo daukan Amarya. Nan ma dai Sai da tayi complain inta akan saurin me yake. Ita dai tasan Sai bayan magreeb ake ziwa daukan Amarya. Banza na mata, Sai sauran friends inta da suka hau dariya. A hakan dai aka dau Amarya zuwa gidan ta dake nan, Abba Ibrahim. Ba a dade ba aka hau Shirin Dinner, Wanda plan in gidan Angon ne. Amarya da Angon Sai a can suka hadu, Dan na lura Kaman tsoron ganin ta ma yake.

A wurin Dinner in bamu dade da hallara ba, aka fara sha'ani. Ina zaune na wani ya tunkaro ni yana min magana. The next I know, Umar Sanda na gani a kaina Yana ma mutumin magana. Ban san me yace mai ba naga ya juya ya tafi. "Taso muje" kawai yace, nako bishi.  Ya bude mota mu ka shiga. Tun ina tsammanin zai ce min wani abu har na lura gabadaya hankalin shi na ga wakan da yake saurara ya kwantar da kujera ya runtse ido. Don haka nima na cigaba da dan danna wayata. Har aka tashi muna waje. Shi da kan shi ya kaini gidan Amaryan back, dake kawaye ranar a nan suke kwana.

Ko washegari ma lokacin siyan baki, ya Kira ni a waya na fito lokacin da suka iso. Ina shiga yaja motan, nima bance komai ba har ya sauke ni gidan Goggo.

Bayan bikin da kwana daya ya zo wurin Googo a cewan shi Mustapha suka you dashi zai maida ni maiduguri. Da ke Goggon ta San shi ba tayi wani musu ba illa ma godiya da ta hau mishi. Hakanan ba Shirin na dauki jaka na, na bishi duk da na so zuwa Ajeyari yiwa Anty Amarya bankwana don a watan zasu kaura Bauchi.+
Ko a hanya ba wani magana mu kayi ba illa Nasihan da ya dinga min akan in natsu in maida dukkan hankalin a kan karatu shine kadai zai zame min gata a rayuwa. Godiya kawai na mishi, ya min fatan alkhairi. Ko da muka isa a tsaitsai ya gaida Goggo saboda ya sanar min daga maidugurin straight Abuja zai nufa. Washegari flight in su zuwa Egypt zai tashi. "Me zan fada ma Wanda ya bani sako a Baki?" Hakan da ya fada ne ya kara tabbatar min namiji ne mutumin.

"Allah ya saka da alkhairi" na fada kawai yayi murmushi yace "To zan isar, Sai munyi magana" daga haka ya ja motan shi ya wuce abun shi. Sai lokacin ma na tuna ban bude ledojin nan ba at all. Kayattatun Gift ne irin namu na mata, na Kuma ji dadin su sosai. Tun daman Abban ba mutum bane mai siya ma yaro duk abinda ya ke bukata balle kuma yanzu da nake wurin Goggo. Ni Kuma ban cika son ina tmbyn ta abu ba. Har ma da kudi, Wanda yawan su har Sai da suka girgiza ni Sai dai ko da muka yi magana na tmbyn shi ba'asi. Sai ce min yayi wai Wanda ya bani, na cancanci fiye da hakan ma a wurin shi.

Har na fara gajiya da zaman gida ba abinda nake yi tukunna Admission in Unimaid ya fito. Kuma na samu medicine in da nake nema dake duk wani abinda ake bukata na samu. Abbah shi ya min komai na makarantan, registration da sauran su. Ya ma so ya sama min hostel Goggo ta hana. Baffah kam mutum ne sam da bai da kara ko kadan. In ba rashin kara ba, har na gama secondary ba abinda ke hada ni dashi. Ko kudin break da kudin transport Sai dai in ya ba Goggo da ya zame mishi dole tukunna ta bani. Mutum ne Wanda bayan yayan shi ba wadanda ya damu da su. Su kam duk abinda su ka bukata Sai dai in basu furta ba. Dan ma ni ba irin mai sa abu a rai bane, komai nawa simple ne hakn ya kara sa suke ganin matsayina da nasu ba daya ba. To wadanda ma muke Uba daya basu soni ba balle kuma cousins.

Da muka yi magana da Yaya Sanda ta waya, ya nuna farin cikin shi sosai tare da kara min fatan alkhairi. Sai dai bayan nan Goggo ya Kira, ashe acc no ya bukata a wurin ta ban sani ba har tasa aka tura masa. Nan wasu kudaden ne aka turo har sun fi wancan. Goggo dai ya sanar mata kyautan shine gare ni. Ta ko ta godiya har da ce mishi wai ya dawo Egypt in nan hakanan kawai ayi auren in yaso na karasa karatu na wai a dakina. Ni dai ba mu taba zancen soyayya dashi ba, Amma duk lokacin da Goggo ta mishi irin maganan nan Sai ya bata wani positive reply. Amma ni da muka yi magana dashi cemin yayi wannan da ya aiko min sakon ne ya kara turo min kudaden. Na so takura shi ya fada min waye wannan hakanan, Sai dai fir yaki zancen  wannan karon ma.

Cikin ikon Allah na fara zuwa makaran ta. Sanadiyyan kara haduwa na da Faree'a kenan. Domin tun a ranar na farko na fito lectures karfe daya na nufin wurin alwala domin gabatar da sallan asuba. Na sunkuya ina cikin shafan Kai naji an riko baya na. "Suhaima" da sauri na juya muka hada ido da ita. Yanda naga ta sakan min fuska nasan ba muyi wannan sabon da ita ba. Na dai share mu ka gaisa faran faran. Daga wannan ranar kuwa har aka gama semester a masallaci muke hadu da ita. Tun muna dagawa juna hannu har muka zo muka fara hira sama sama. Har ina tmbyn ta Anty Nainah, tace min tana Abuja. Daganan dai ban bar zancen yayi nisa sosai ba.

Daga Masallaci next inda muka fara haduwa Kuma wurin cin abinci ne. Nan kam da kawaye kala kala na ke ganin ta. Da ke cafteria in hostel nake zuwa Kuma mata ne kadai a nan. Yawanci ni kadai nake zuwa saboda banyi kwashe kwashe wasu kawaye ba Sai dai course mate da muke magana daya biyu a Abuja. Watarana bayan na gama lectures naje wurin ni kadai. Sai ga ta nan ta shigo ita ma. Ban taba ganin ta ita kadai ba ma sai ranar. Tana ganina da fara'an ta ta karaso ta zauna inda nake bayan tayi ordern abincin ta.

"Ni kam wai wani course kike ne?" Nan na fada mata tace "kice manyan Unimaid ne kawai" cikin hiran take tmbyn ko a hostel nake zama. Dan wautana har address in gidan Baffah na bata, tace min zata zo ta gaida Goggo. Ai ko hakan ya faru, wani weekend kawai ina zaune Sai gata da wata kawar ta. Naji dadi har raina har waje na raka su, ban zatan a mota suka zo ba Sai da na ga motan. Hadadden mota ne sosai, ba wani abinda ya zo min rai banda na gidan su ne ko na kawar ta.
Sai da lokacin Exams ya zo, sannan na gane fa'idar zama a hostel. Domin duk yanda na so karatu a gida ba Kaman yanda nake a library ba duk Sanda na samu dama. A gari har yanzu ba lfy bare ince zan bari Sai dare ina dawowa. Yanzu haka zancen da ake ma an fara kawo hari cikin makarantar.
A wani zuwa library da nayi, wuraren karfe biyu na hadu da faree'a. Wanna karon ma ita kadai ne, tace min "Suhaima lfy kike karatu haka da tsakan rana" dariya nayi nace "kefa ba karatun kika zo ba?" Nan ta sanar min tazo amsan abu ne gun wata. Ni Kuma na shaida mata ban samun daman karatu in na koma gida ne. Kai tsaye tace min "To ki dawo hostel mana?"
"Ai banda accommodation" rike baki tayi can tace "Bani numbanki Suhaima" mu kayi exchanging contact ta wuce.
Har na manta munyi magana da ita, ta Kira ni tana shaida min in same ta cafterian da muka saba hadu in na gama lectures. Ban gane me take nufi ba, Sai da na isa na ta kara ce min inzo common room. Nan na iske su, su dayawa suna kallo. Tana ganina ta taso, can wani block mu kaje da ita. Kusa da dakin da take ta kaini, wai free space in friend inta ne Amma yanzu an samu matsala ta bar school in. Saboda haka in ba matsala in dawo in zauna man. Na mata godiya Amma na shaida ta mata dole Sai nayi magana da Goggo. Ta so ta hanani, Amma Abbah yayi kokarin fahimtar da ita dake shi ya amince. Da ke yanzu jikin ta da sauki sosai ta kyale ni. Ko da faree'a ta kirani, na sanar mata ina son yin siyayya ne. Sai tace in zo akwai nata Kuma waccan kawar ma bata kwashe komai ba, ta barshi a wurin ta. Hakanan na tafi ganin yanda ta matsa. Ko Umar Sanda da yaji komawa na hostel Sai da yace hakan na da kyau, Amma in dinga yawan addu'a saboda security reason. Dake yanzu zaman Borno ya fara gagaran mutane dayawa, shi inma kullum yana cikin kirana domin jin halin da muke ciki. Bafferh kuwa yanzu haka yaran shi gabadaya ya kwashe su daga garin ya Kai Kano. Sai matan shi kawai da Goggo, shi inma Yana nan. Abbah kuwa wannan karon aiki garin Jigawa ya Kai shi.
Haka muka fara rayuwan hostel tare da faree'a. Da ke kullum ina wurin karatu, Sai a hankali na fara fuskantan bata cika zama a hostel ba. Hatta kwana kam Amma in dai tana nan to tana wuri na har girki take yi ta kawo min. Hakan yasa na fara bata babban matsayi a wuri na. Tana so na sosai, duk wani matsala na tana kokarin share min. A lokacin ina 200 level kenan.
Ko a 3 inma ita ta neman min hostel, wannan karon ana su dakin ma na yan final year. Da ke room of 2 ne Kuma, daga ni Sai ita a daki. Lokacin Kuma na kara fuskan tan ta da kyau, domin yawancin ni kadai ke kwana a dakin. In na tmby ta ina take zuwa tace wurin friends ita. Tana dasu kala kala Kuma yawanci yan duniya. Lokacin nasan tayi canjin department yafi sau biyu Kuma har yanzu ba karatun bane a gaban ta. Sai dai Kuma akwai tsafta sosai ga sanin ya kamata sannan akwai karrama dan Adam.
Gabadaya shekarun nan Umar Sanda bai zo Nigeria ba. Sai dai Kuma yana nemana akai akai, duk ya San abinda nake ciki kuma. Kudi kuwa har bansan adadin da ya turo min ba, duk dai da sunan wani ke bashi sako. Ni kam na gama sa wa raina ba wani kawai shi inne  kawai. Har Faree'a ma ta San shi sosai duk da ba su taba haduwa ba.

Sai da karatu ya fara zafi sosai sannan kwatsam Sai ciwon Goggo ya tashi gadan gadan. Wannan karon ciwon yaui zafi sosai, mun kwana a asibiti har ba adadi. Gabadaya a tsorace nake, ga wani irin banzayen mafarke mafarken da na fara. Sai ni inma na rame, na zamo sukuku karatun ma Sai Wanda naji kawai a lectures. Lectures inma ba kowanne na ke zuwa ba. Ba wanda ke tausa ta Sai Faree'a Sai Kuma Sanda idan mun yi magana. Ya kan cemin in maida lamurana wurin Allah ina addu'a ba wata mafita bayan hakan. Da tausasawan nan nake samu ina karatu, a shekaran dai da kyar na tsallake ajin lafiya kalau. Dan nikam har na cire Sai na kara maimai ta wani jarrabawan.

Daga hostel asibiti na wuce, Goggo kam jiki Sam ba dadi har dialysis ake mata na kidney. Magana ma da kyar take yi, abinci kam Sai anyi da gaske shi inma ba kowanne ba. Baccin kirki dani da mai kula da ita ba wanda yake yi. Ina kanta kawai ina kallon ta. Sai addu'a kawai da godiyan Ubangiji. Daganan Kuma ba Sai kafa daya baki daya ya daina aiki ba. Nan fa hankali likitocin baki daya ya tashi aiki ba, dole suka hada da kiran wani babban likita yazo mata surgery.
Ranar Faree'a tazo da ke ana hutu ba ta garin. Hankalina a tashe, don haka tana tare dani ta rike hannu na tana bani Baki. She was there for me in my difficult times.  Ranar dai idanuwa na sun yi luhu luhu, maganan ma yaki zuwa haka kuka ba uhm ba uhmm uhmm. Barin ma tunda aka fito da ita awa daya, biyu, uku Kai baki daya wunin ranar ba ta farka ba. A ranar kam da baccin yana Dan zuwa , Amma lokacin gara rau idanuwa na na karaci daren. Sai wurin asuba ta farka, Sai dai kana ganin ta kasan bata cikin wani lafiya ko kadan. Ga oxygen amma numfashin fita kawai yake ba wani alamun shiga duk da nurses In sunyi denying hakan ni dai abinda idanuwa na suke gane min kenan. Barin ma yanzu da karatun mu ya fara nesa, nasan abubuwa dayawa daga cikin medicine in. Ko da na gaya ma Sanda, ce min yayi inyi hakuri ai sun san aikin su. Don haka na kyale zancen. Amma jiki kam baki daya ya rikice, motsin kirki ba tayi. Abinci kam ba ma ama maganan.
Wani ikon Allah, wurin magreeb abun ya dan yi sauki. Har ta sa na mata alwala na kawo mata hijab, duk ta gabatar da sallolin da ake bin ta. Tana ta min murmushi kawai abin ta, tana tasbihi har Sallan isha tayi. Tana idar kuwa bacci ya dauke ta. Ni kam har na fara murna jiki ya fara kyau, Sai dai su Abbah da Baffah duk ban ga alamun farin cikin tattare dasu ba. Anty Yana ma na nan, gaisuwa kawai ya hada ni da ita. Har yanzu dai ban gaban ta domin ko kallon inda na ke ba tai ba.
Goggo ba ta farka daga wannan baccin ba sai wurin goma da rabi. Nan ma dai murmushin kawai take, Sai dai kana ganin ta kasan tana jin jiki. Abun da na lura Kaman ciwon ya kara tasowa ne. Haka dai Kuma aka dinga fama, motsin kirki ba wanda ya ke iya. Ana zaune Sai ta juya ta kalli wannan Sai ta juya taga wancan duk tana ta murmushi kawai. Zuwa can ta yafi to ni ta ido. Ina gane hakan na kara matsowa daf da ita. Hannu na ta fara kokarin kamowa nata na karkarwa. Da sauri na hade hannayen namu, gam ta rike ni tana kallona. Naji wani irin hawaye sun fara zubo min, girgiza min Kai tayi sannan ta lumshe idanun ta ta bude. Na gane tana nufin inyi hakuri ne, saboda ta taba min haka a wancan ciwon nata. Murmushi ta kara min sosai daga nan kuma ta dade idanun ta na kaina. Abbah ne ya zo wurin ta yana kokarin mata magana, dan haka na saki hannun nata da gudu na fita daga dakin ina jin kaman wani sabon tashin hankali na shirin taso min. Ina fita saura yan dakin suka biyo ni, wai ashe jikin ne ya kara tashi gadan gadan. Daga Abbah Sai Baffah aka bari a dakin da likitan da ke kanta.

Sun kusa awa daya a ciki. Tun daga yanayin fuskan shi na riga na sadakar. Sai dai duk da hakan kafafuwa na sun gaza taka zuwa cikin dakin kaman yanda sauran suka shiga. Zama nayi dabas kawai a kasa na zabga tagumi yayin da kunnuwa na ke jiyo min sautin kuka na tashi daga cikin daki. Hakan ya kara tabbatar min da Goggo dai babu ita. Nan take na fara jin kaina na juya da sauri da sauri Kuma Sai jiki na ya dau rawa. Kaina ya min wani irin nauyi Sai Kuma na fara ganin zallan duhu nan take na kasa fahimtan dukkan wani abinda ke faruwa. Daga nan ban kara sanin ina kaina ya ke ba har na kusan awanni sannan na farfado. Drip in da na fara cin karo dashi ya tabbatar min da kilan faduwa nayi a wannan lokacin. Ashe wai har gari ya waye. Faree'a na gani a kaina sai Kuma Adda Falmata da bansan zuwan ta garin ba ma. Faree'a ce ta min sannu, da kyar na amsa. A firgice na tuno abinda ya faru, jiki na rawa nayi kokarin fisge drip in faree'an ta rike min hannu tana bani Baki. "Goggo Goggo" kawai baki na ke fadi. Yanayin fuskan su kawai yasa ni gane ba mafarki nake ba.

"Da gaske Goggo ta rasu kenan?" Ba wanda ya bani amsa Sai dai nan take na fara jin zuciya ta na bugun fat fat fat. Tabbas yau manya sun kwanta kasa, Allah ya sa karshen wahalan kenan. Addu'a na tsinci kaina dayi da sauri na Mike nace "ina son in ganta, ko an tafi da ita?"
"Bara drip in nan ya Kare mu tafi gidan" Faree'a ta amsa. Adda Falmata kam bansan makasudin zuwan ta wurin nawa ba ma. Da alamun Abbah ne ya sata. Ai kuwa Abban ne ya zo ya dauke mu, muka tafi gida. Tun daga taron nagane mai afkuwa dai ya riga da ya afku. Karfi addu'a ne ya karasar dani cikin gidan nan. Dai dai shiganmu, ana fito da ita filin gidan inda za a mata sallah. Da sauri na karasa wurin makaran, zaman dirshan nayi a gaban makaran ina Kare mata kallo. Kaman in na mata magana zata amsa haka nake ji. Tayi haske abun ta, ta kara wani kyau. Tabbas nata kam yayi kyau, Sai dai muyi fatan namu ma ya kasance hakan.

Da karfin hali baki na ya hau mata addu'a, ina kallon ta ina wani irin murmushin karfin hali komai nawa Kuma a cinkushe yake. Ina jin idanuna ya min wani nauyi Sai dai Kuma ko alamun kukan ma ban ji. Na dade ina addu'an, jiki na kam duk ya kasa dagawa. Ban San waya zo ya janye ni ba.

Mu ma a baya muka tsaya aka mata salla tare damu. Dai dai lokacin da aka daga makaran za a fita da ita. Naji wani hawaye mai zafi ya biyo kunci na. Yanzu shikenan ba zan kara ganin Goggo ba? Ban ko shakka tabbas gata na ya kare.
Ina ji ina gani aka tafi da Goggo gidan ta na gsky. Bbu abinda na iya haka Kuma ba abinda na isa in canja. Sai dai jin komai nake tamkar a mugun mafarki da nake bukatan farkawa cikin gwaggwa. Har mintsilin Kai na, na dinga yi ko zan farka amma ina abun yaci tura. Ban tunanin ina gane mutanen da ke ta Kai komo a cikin gidan nan. Ko su Adama da su kazo blurry na gansu ballantana Kuma wayata da bansan inda yake ba kar ma Kuma a zo kan batun abinci. Har mamaki nake yanda mutane su ka saki jiki suna ta faman diban abinci sai Kuma hayaniya kawai ke tashi don ba wai na wani fahimtar abinda su ke fadi bane. Bansan adadin mutanen da su ka sani a gaba inci abinci ba Sai dai hakan bai sa na cin ba. Gabadaya ma da suka gane ba wai na San inda kaina yake bane, a karshe Abbah aka kira, dole aka kara maida ni asibiti.

Kwana ukun da suka shude min a asibiti baki daya bazan iya cewa ga ta yanda nayi su ba. In za a barni cikin bacci yawuce, baccin gaske da Kuma baccin zaune, domin dai duk abinda ke faruwa kusa dani dai bawani fahimta nake sosai ba. Hana rantsuwa dai nasan Ajiddah, Adama da Faree'a suna tare dani. Sai dai bazan ce ga tsawon lokacin da su kayi a tare dani ba.Dole Sai a kwana na ukun ne na iya Kai wani abu baki na, shi inma ruwan shayi ne. A bakin Adama nake jin irin raman da nayi, fada take yi wai ban yarda da kaddara bane da bazan fawwala wa Allah lamari na ba. Sai dai banga laifin ta ba a wannan lokacin saboda Adama bata taba fuskantan daya daga cikin matsalolin da na gani ba. Na dade da sanin rayuwa ta bata da wani mahimmanci, tunda na taso ma fuskanci mahaifiyar da ta haife ni ma ta tafi ta barni cikin gararin rayuwa hannun wadanda basu damu dani ba.+

Bansan Ya akayi Umar Sanda yazo ba, Amma dai naga shigowar shi tare da maigidan Adama. Ban yi wani mamakin zuwan nashi ba, saboda a halin da nake ciki ba wani abun girgizan da zai shudar da mutuwar Goggo a raina ba. Gaisuwa suka min suka tmbyn ya jiki, duk dai a takaice na amsa musu.
Ina ga alluran cin abinci likita yasa aka min saboda shi kadai ne dalilin da zai sa naji ina jin mahaukacin yunwa. Duk da haka ban wani kula yunwan ba, banda uban fruit da abun ruwa dana dinga durawa ciki na. Shi inma a sanadiyyan nasihan da Umar Sanda ya zauna yayi min, Wanda ba shakka ba karamin ratsa ni yayi ba.

Ranar throughout yana asibitin, motsi kadan zaka ganshi ya shigo. Ina jin Adda Falmata na bala'in wai wani munafunci ne ya kawo shi wurina, daman an bata lbr. Kala ban ce mata ba, don na rasa dalilin zuwa wurina asibiti da take yi. Yaya Baba dai banda shi a maidugurin ma, naji dadin hakan saboda ba wanda naki jini a rayuwa irin shi, tabbas shi in wani irin dafi ne da ganin shi kadai zai ma mutum illa.

A daren ranar Umar Sanda yazo min Sallama, akan wani batu ya taso mishi a Abuja, dole gobe ya ke kafin ya koma Egypt. Nasihan dai ya kara min sannan ya wuce tare da sanar min zai turo min sako ta waya.
Hakanan aka sallame ni a asibiti, na koma gidan Baffah cikin da tunanin wani irin rayuwa zan afka a wannan karon. Ganin ni kadai ne a gidan yasa baffan yace in koma side in Uwargidan shi na zauna. Haka ko aka yi, ba wani abinda ke hada ni da ita banda gaisuwa. Daganan ba ta damu da mai naci ba ko ina na kwana. Ko bata ganni ba, ba abinda ya shafe ta. Har ma gwara dayar matan in bata ganni ba zaka ji tana wai Suhaima kwana biyu kaman bata gidan nan. To tun farko basu dauke ni wata tsiya ba balle in wani girmama su sosai. Duk da haka dai nayi Amanna zaman gidan yafi zama gidanmu dadi ta kowani sashe. Tunda su ba aiki suke sani ba ko aika ko wani wahalan ba. Kawai dai kowa na rayuwan shine.
Da aka koma makaranta Abbah ya turo min kudi na biya registration and all. Accommodation Kuma kudin hostel ya bani, Sai dai faree'a ta nemi da mu Kama wuri nan cikin makarantar kawai mu zauna. Tunda wajen ba security, saboda haka nan staff quarters muka samu wuri muna zaman tare. Zuwa yanzu halin ta ya lalace, ban mata wani wa'azi saboda ba dauka take ba. Takan ce kowa rayuwan da ya zaba ma kanshi zai yi, don haka ita nan ta fuskanta. Na dade da sanin tana bin maza, bi ma'ana runs take yi. Takan ce min ni naga ina da hanyan samun kudi ne Amma ita ba ta da wani da ya wuce wannan in. A lokacin kam Sam bata wasa da Sallah, abinda na jinjina mata kawai kenan. Akan ce ka guji aboki batacce, Sai dai ni a wannan lokacin ina ganin soyayyan da take min ya take komai sannan Kuma ban ganin za ta iya canja min ra'ayi. Babban kuskuren da nayi kenan.
Domin dai a hankali a hankali rashin gata na ke kara bayyana yayin da rayuwa take cigaba min. Abbah ba irin mutum bane wanda ya damu da yaran shi sosai, zai dai sauke muku hakkin makaran ta daganan Kuma sauran Sai anyi da kyar. Duk bayan kwanaki dai zai turo min kudi Sai Kuma in ni na Kira in gaishe shi.
Da farko mafitan da na fara gani shine yakama ta in bi aure ne. Sai dai duk yanda mutane ke fada min Umar Sanda na so na, har yau bai taba furta hakan ba. Ban da maganan karatu Sai Kuma makudan kudin da ya kam turo min da sunan wani ke sa shi. A hankali na fara jan hiran mu a waya kaman yanda ya kanyi ko zan samo mafitan a nan Sai dai bai wani nuna komai ba. Zai dai bani lbrn abinda yayi ranar da Kuma irin rayuwan da yake fatan gina wa kanshi a gaba. Kullum dai kara daure min Kai yake. Ban fadawa Faree'ah ba saboda bata nan, Adama Kuma she is not an option to me don haka direct na Kira Ajiddah.
"Suhaima share shi kinji, maza yan iska ne wlh kema yanda kike da kyan nan ki saki jiki nasan maza dayawa na son ki, ki saurare su kila akwai Wanda za a dace" In har an bi lbr na da kyau tun farko, za ku gane cewa ni mutum ce mai saurin daukan shawara ba tare da yin wani dogon tunani ba don haka a yanzun ma hakan ya faru. Lokacin mun riga mun fara zuwa practical asibiti. Saboda haka duk wani Wanda da yake nuna min ra'ayi ina share shi Sai na fara sakan mai fuska. Kaman ko mazan jira su ke, nan da nan na fara tara samari kala kala. Yau wannan ya zo wuri gobe to wancan zai zo. Ban gane ina da kyaun da takama da zan ita jan ra'ayin da namiji ba Sai da na afka wannan rayuwan. Duk da haka ban wasa da karatuna saboda nasan shine zai zame min gata a rayuwa, Kaman dai yanda Ajiddah ke fada min mazan ma yan iska ne.

Lokacin da faree'a ta fuskanci ba Suhaiman da ta sani da bane Sai ta fara hada ni da wasu daga cikin mutanen ta. Tunda bazan ce ina da matsalan kudi ba Sai dai ba ko shakka akwai matsalan yanda zan sarrafa su. Da nakan rasa me zanyi da kudi Amma yanzu har kadan suke min. Rayuwa dai ta fara gargada Sai dai Kuma ba wanda zai daura ni a hanya in dawo hanyar dai dai.
Tuni na dawo bana ko dar dar dan in shiga motan namiji ya Kama min hannu yana wasa dashi da sunan yazo hira wuri na. Kai har da masu sa hannu a wuya na ma yana matso dani kusa dashi ko kugu. Nan da nan na fara fice, suna na ya fara yawo cikin Unimaid. Har yazo da an Kira sunana kowa ya sanni. Duk wani gasan kyau nice a gaba, dake na fahimci ina da kyan duk dani ba fara bace kuwa. Awards kala kala duk na amsa.
Umar Sanda kuwa wayan mu yaja baya sosai dashi tun da ya fahimci interest ina ya fara raguwa. Sai ya koma wani lokacin kawai Sai dai ya turo min text yana tmbyn lfyna da karatu. Text inma ba ko yaushe nake amsa mishi ba dake duniyan ga min dadi. Na dada gogewa, duk nayi realizing dayawa daga cikin mazan ba da aure suke so na ba. Sai dai ba wanda na sakan ma jiki na. Barni dai ta harkan romance ya Kare a nan, don duk duniyancin namiji dai dai na dawo dashi. Kusan daman ance Wanda bai iya abu ba in ya koya, yafi kowa gogewa. Gidan baffa kuwa Sai na shafe watanni banje ba, ba Kuma Wanda ya damu.
A hankali faree'a ta fara gane a yanzu na fita wayewa da sanin duniya abu daya ta fini zuwa lokacin, shine Kuma wayau. Duk saurayin da ke zuwa wurin ta, guna suke dawowa. Lokacin ta gane lamarin ta ya fara ja baya, barin ma da ta gama Unimaid da result da ba wani Wanda zai kalle ta. Ai Sai ta cilla Lagos, daman tun tuni ashe tana da daki a can gidan yancin, don haka taga gwara kawai ta tsunduma karuwancin gadan gadan, don zata fi kasuwa yanzu a nan. Barin ma a garin Lagos.

Mun dade bama tare, har ta na kusa gama karatuna. Kwatsam Sai ga Faree'a tazo nemana. Nayi mamakin ganin ta domin ma dauka Wanda yayi gaba ai bai waiwaye. Ce min tayi wai ta dawo maiduguri, ban wani tsaya dogon magana ba nace mata "sannun ki to Sai ki dawo mu cigaba da zaman mu" Hakan ko akayi. Duk da kullum tana cikin attending to customers, har nemo min take yi, nace mata ni ban kwana da maza Amma ba ta yarda, Sai dai yardan ta bai dame ni ba. Kuma lokacin na maida hankalina kan karatuna, na fara rage samarin duk da ba kowa ya yarda ya tafi ba. Ni inma ma bazan so duk su tafi ba, domin yanda nasan kudi nasan amfani su to dole Sai da mazan a harkan. Lokacin ne Kuma gadan gadan boko haram suka girgiza borno, kuna lectures Sai a ce muku bom ya tashi daga wani bari a cikin makarantar. Kowa dai a tsorace yake, daga karshe tilas aka rufe makaranta. Gamu muna gab da karasawa Amma ba daman hakan. Maiduguri ya fara gagaran zama kowa ta kanshi yake, ba nan inba ba damturun ba, hankalin jama'a kowa ka gani a tashe.

A wannan lokacin Faree'a ta hadu da Umaymah. Ban san taya suka hadu ba Sai dai kawai naji tana yawan maganan ta. Hutun makarantar da aka yi yasa ni zuwa gidan baffa saboda nasan inda nake is not safe Amma can in da guarantee. Sai dai me? Tun daga kofan gidan naci karo da gundumemen kwado ko alamun mai gadi bbu. Da na tmby wasu makota dasu ke Shirin barin garin suma, ce min su kayi ai sun kusa wata uku da barin garin. Ina suka je, ba wani labari. Tilas na Kira Abbah, ya ce min suma ba kowa a Damaturu Amma na hau mota na same su a Jigawa. In akwai abinda na tsana a duniya shine zama tare da yan gidanmu, Adda Falmata ma na nan har yanzu ba tayi aure ba duk da nasan a yanzu ba uban da ta isa ta min Sai dai banji zan iya hada inuwa da ita. Ban tsaya neman su Adama ba saboda nasan suma basa garin don haka nayi dialling Ajiddah, duka duka ba ta dade da aure ba Kuma nan maidugurin aka kawo ta. Wani attajirin mai kudi ta aura bayan ta gama ruwan idon ta, Sai dai babban mutum ne Kuma ana hudu ta shiga. Saboda yaran duk guduwa su kayi ta nemi na aure ta rasa. Sai da na Kira numbanta bai shiga ba ma sannan na tuna tace min zasu honeymoon Dubai yanzu haka nasan suna can.

To duniya fa tayi zafi ga ba wurin nufa. Duk inda na bari sai inji ance bomb ya tashi a wurin ko Kuma an tare mutane an musu yankan rago. Lokacin Umar Sanda ya fado min, Sai dai na dade da wullar da sim in da ya sanni dashi. Tun Yana nemo inda nake kyautata zaton wurin mijin Adama ya ke samu. Don haka last sim ina Adaman ma ba ta sani ba, ina jin fushi tayi ta share ni tunda ni numban ta na kaina. Shi ko har ga Allah ba wai na haddace numban nashi bane Sai dai in na gani zan gane. Duk yanda na so hada numban in same shi bai yiwu ba Kuma.

Daga karshe Jigawan na yanke shawaran zuwa, don har na gama hada kayana faree'a ke tmbyna inda na nufa. Bayan na fada mata ne tace min "yanzu gidan su Falmatan Zaki?" Faree ma taki jinin Adda Falmata, kullum Sai ta zage ta in dai aka yi maganan ta. "To ai banda wani mafita"

"Ni ina dashi" yanda ta fadi zancen ta karfi Sai da naji saukan shi cikin kwanyar kaina. Kalman da ya canja duk wani sauran farin cikin rayuwata.

"Shirya muje " kawai tace. Na ko shiryan na bita muka tafi Sai hausari, gidan Umaymah. Tana ganina ta saki murmushi tana fadin "Faree wannan ce ko? What a perfect lady, gsky kin kyauta min" Anty Umaymah kaman yanda naji suna fada mata nima na dauka. A ranar mu biyar ta siyan mana ticket muka sauka garin Kano a unguwan sharada. Lokacin ba a wani tare sosai a unguwan ba. Wani narkeken gida muka je Wanda bai rasa komai a cikin shi ba. Mun dade ana nan muna zaune lfy kalau, sim ina kam Kai banma da waya a lokacin bare Abbah ya same ni. Karen mu kawai muke ci ba babbaka, ga Anty Umaymah akwai kashe kudi. Mutunci da take min na daban ne, ban gane manufar hakan ba Sai da nasan mata take nema. Yanda take taba ni, tana wasa da gashin kaina sai dai ko kadan ban hana taba duk da ban sakar mata jiki baki daya. Saukin abun ma tana zama a Abuja ne sosai yawanci. Akwai lokuttan da ni kadai take sa wa inzo muje Abujan. A haka muka saba da ita, nan ma Faree kishi take. Saboda haka nema ta hada kayan ta tayi Lagos duk da ba wanda ta fada ma dalilin yin hakan.

Ba zanyi karyan cewa ban taba ba ma Anty Umaymah jiki na ba, duk da ban taba ra'ayin hakan ba. Ta dai karaci kidan ta da rawan ta ita kadai ta kyale ni. Muna Abuja tare da ita aka koma School. Da na fada mata, da kanta muka dauki jiki muka je maiduguri muka binciki komai na karatun. Ba karamin kudi ta kashe min cikin kankanin lokaci ta samar min inda zan zauna in gama makaranta gidan wata friend ita. Wanda kudi yaji kudi, Kai girman gidan ma har ya baci. Akwai securities sosai ta yanda boko haram ba zasu tunkari wurin ba Sai da babban shiri. In kun ga da securities in da ake kaini makaranta, Sai kun dauka yar wani shegen ne. A haka dai da darr darr in har na samu na kammala da kyar da niyyan zan zo Kano inyi housemanship ina.
Bayan na dawo, nayi mamakin ganin Faree a Kano tare da Anty Umaymah. Har yau ina iya tuna yanda suka zauna suna min bayanin abinda ya ke faruwa da abinda su ke son in aikata musu. Naji labarin Anty Umaymah, Kuma ya ratsa ni. Naji ba wanda na tsana kaman zayd domin gani nake tafiyan su day ta Yaya Baba duk daya ne. Nan take na dau alwashin komai zai faru Sai na cika mata burin ta, ko ta halin kaka kuwa. Saboda ta min alkhairin da ba batun mantawa. Ta so in cigaba da housemanship ina nace mata na gaji Sai na gama aikin ta. Abinda yasa nayi saurin amincewa Kuma shine in duba irin hadarin da ke tattare da karasa makaranta na, burina tun ban gama sanin kaina ba. Amma kuma sai gashi tabi hanyoyin ta, ta cika min shi. Don haka komai zan mata ban jin zan fadi.

Da da farko zayd muka yi niyan targeting direct Sai dai sanin Amal budurwar shi na Lagos sannan Kuma Yana yawan zuwa can Sai muka samu perfect opportunity kawai muka hau aiki. Lokacin na bi Faree zuwa gidan yanci, Sai dai ba wai da niyyan zama ba. Aa kawai saboda in samu daman observing komai da kyau. Don har taso ta Kama min apartment naki.
Zuwa na gidan ma wasu irin mahaukatan samari nayi, Sai ya zamto duk Wanda yazo in dai ya hadu, maganar aljihu kenan to dani magajiya le hadawa. Daganan na samo yar baiwa, dayawa suka fara jin haushi na duk ba shiga harkan su nake yi ba.

A club muka fara haduwa da Amal, duk da komai is delibrate. Na ganta a ranar ba inda kanta yake, ta Sha har ta bugu ba ta gane komai tana gab da zubewa kasa na taro ta. Wayan ta ya fado hannuna. Dai dai lokacin Kiran zayd ya shigo na dauka, nan na sanar mishi yanda na same ta. Sai gashi kuwa cikin yan mintuna ya iso. Shi ya tafi da ita gida, ashe ya bata labarina. Ta dinga nemana a club in nan kusan two weeks basu same ni ba. Sai ranar a wani club in daban, Yana gani na ya nuna mata ni Sai kawai naji an zo an rungume ni. So friendly, a ranar ta amshi numbana. Sai yazo tana Kira na in tasan club in da zani ranar Sai mu hadu a can. A haka har muka saba, har gidan ta mun Sha tafoya da ita in Zayd baya nan.

Nan take tmbyn inda nake zaune, na sanar mata wani single room apartment ne. Na bata lbrn na karya akan zancen boko haram sun kona gidanmu and am stranded a garin. Saboda haka taji tausayi na sosai ta tsaya convincing ina in dawo gidan ta da zama. Sanadiyyan fara zaman mu tare kenan, har kowa ya sanni har cikin gidan su."

Barr mustapha na Kai nan ya San ya gama kaiwa wurin inda yake bukatan jin komai da yake bukata, don haka ya rufe manuscript in yana runtse idanun shi da ya tabbatar su gama gajiya. Kan shi ne ke wani irin sarawa daya San duk na gajiya ne
Amma duk da haka ji yake lokacin hutu bai riga da ya zo mai ba har Sai ya ga karshen wannan shari'a tasu. Duk da dai yasan zuwa lokacin tunanin shi ya riga ya a gama cire mishi Suhaima a rai Sai dai Kuma yana jin zuciyan shi na mishi kwadayin kasancewa da ita.
Matsalolin ne kala kala kawai da suka dinga zuwa mata daya bayan daya Wanda in ana shi hukunci ne yana ganin yanda hanya da tabi wurin magance matsalolin nata ne ke da gargada mai dimbin yawa a tattare dashi.

Post a Comment for "LABARIN RAYUWATA CHAPTER 8 BY Ayeshay bee"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...