GOBE NA CHAPTER 9 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 9 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 9 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

GOBE NA CHAPTER 9 BY KHADIJACANDY

                Www.bankinhausanovels.com.ng 
Wani lokacin Allah yana mana talala mu yi ta aikata zunubi har sai idan ya tashi kama mu sannan yai mana damkar da zata saka mana nadama da dana sani, a duniya kenan da Aminu ya fara haduwa da sakamakonsa, to ina kuma a lahira? Sai dai ina kyautata masa zato kasancewarsa musulmi kuma ya gane kuskurensa ya tuba, Allah yana son bayinsa masu tuba.

   Na shiga gida da tunanin Aminu a raina, ba ma ni ba a halin yanzu Aminu be isa ya tunkari wata mace yace yana sonta ba, sai idan mai dauke da irin lalurarsa ce ko kuma idan boyewa zai yi, wata kila ma yayan da yake aibantawa yana cewa na haifa masa yara da yawa zam tsofar da shi sune kadai yaran da Allah zai ba shi. A ranar na kudirta a raina cewar ba zan fada musu cewar mahaifinsu yana dauke da cuta ba, fada musu ba zai haifar musu da komai ba sai tashin hankali duk kuwa da kasancewar akwai kurciya a tare da su, ba lallai ne su fahimci komai ba.

  Har ga Allah na jidadin da cutar ta kama Sadi da Sa'adatu ko ba komai dukansu sun ci amanar aure kuma sun ci amanata, Sa'adatu kawata ce ta zabi tai mu'amala da mijina bayan kuma ita ma din tana da aure da yara, sadi kuma ya ci amanar dan'uwansa yai ma yar dan'uwansa fyade, ko da yake har da sakacina a wasan lokaci na barinsu da nake suna kebewa a tare yawan shige masa da take ban taba hanawa ba, saboda ban kawowa zuciyata komai a kansa ba, ko da yana zina ban tana ayyanawa a raina cewar zai iya lalata yar dan'uwansa ba, ashe duniyar ta dade da canjawa daga sanin da nai mata, a yanzu babu yarda a tsakanin yaranka da kowa, domin bayan Namra na yi ta ganin labarai masu sosa zuciya wasu uncles dinsu zasu lalata su wasu kuma ubansu na ciki ko makota, kai har malaman makarantar boko da islamiya ba a bari ba, hakan yasa na kara saka ido akan duk wani motsi na yayana ba mata kadai ba har mazan domin suma ba a yanzu ana lalata su, mun kai wani zamani da babu aminci a zukatan mutane kowa kokarin cutar da kai yake.

A washe garin ranar sai na tashi kamar wata marar lafiya, ba labarin Aminu kadai daya saka jikina sanyi ba har da tunanin Ahmad abunda ban tana ba, ko da dai rana ban tana kwantawa ko tashi da tunaninsa ba. Sai dai jiya na raba dare da tunanin abunda yai min da wasu alamomi da sai a yanzu nake fahimtar inda ya dosa.+

“Hello Lims fatar kin tashi lafiya Happy birthday”


Shine farkon abunda ya fara shigo min a waya, kamin na bank dina su turo min. Ni kan har na manta da wani zancen birthday sai yanzu.

  Aje wayar nai na fito tsakar gida na debi ruwa na shiga daki na juna a electric kettle, haka na bi yarana na zuba musu ruwa sukai wanka sannan suka karya suka saka uniform. Zuwa nai na gabansu na risina ina kallonsu wani irin farincikin marar misaltuwa ya lullube ni lallai yara rahama ne, no matter how suke rashin ji ko suke cutar da junansu.

“Allah yai muku albarka ya shirya ku da duk yaran musulmi, ya tsare ku.”


Duka suka amsa da amin, daya bayan daya na busu da addu'a ina dafa kansu ina karantawa har na gama sannan school bus dinsu ta iso, da gudu suka fita daga gidan kowa yana kokarin ya riga dan uwansa gwanin sha'awa. Da kallon kauna na bisu zuciyata cike da shauki ina murmushin jindadi da yi ma Allah hamdalla. Ina juyawa sai ga Namra ta dawo tare da Adnan suna rike da wani katon kwali wanda daker ma suke iya daukarsa, an nade kwalin da fata jar leda mai kyale.


“Momy Momy gashi inji direban Bus yace wai a baki”


Jin hakan yasa nai saurin tashi na karasa na karbi kwalin.

“To Momy bude ki sam mana abunda ke ciki”


Namra ta fada jikinta har rawa yake.

“Kin san abunda ke ciki?”


STORY CONTINUES BELOW

“No”


“To kuje makaranta idan kun dawo zan ba ku nima ban san miye a ciki ba”


“Momy to waya baki?”


“Namra... Ba yanzu kika karbo sakon ba? Ni ina zan san wanda ya bani to?”


“Momy ai shi mai bus din mu ba son ki yake ba ko?”


Ta tambaya tana sako min ido, sai a lokacin na daka mata tsawa domin na fara gundira da tambayoyinta.

“Ban sani ba, wuce kuje sarkin gulma”


Dariya tai ta nufa kofar fita da gudu daman tuni mai bus din ya danna musu horn alamar yana jiransu.

“Daddy na yace idan wani ya zo son ki na fada masa, kuma sai na fada masa wannan”


Hafiza wacce ta nufo dakin da nake ta tari numfashinta.


“Tsohuwar munafuka ki ce tace masa i love you”


“Mama Hafiza i hate you”


Ta karasa fada sannan ta fice daman shi Adnan tun da ya aje kwalin ya koma ita ce dai ta tsaya gulma. Aje kwalin nai a tsakiyar falon Mama na gagara budewa, ko ba a fada min ba na san Ahmad ne yai domin shi yasan yau nake birthday gashi kuma direban motar scul dinsu ce. Hafiza ce ta bude kwalin sauran yan'uwana duk suka zagaye kwalin kowa yana son ya ga abunda ke ciki, katuwar kwalbar strawberry guda biyu ta fara fitarwa sai cake dan madaidaici wanda aka rubutawa happy birthday, a kasan cake din wani madaidaicin kwali ne, da kanta ta bude kwalin sai ta ciro wata farar takardar sannan ta ciro turare man shafawa da wata sarka wacce nake kyautata zaton zinari ne.


“Oh my god oh my god see love abeg duk Babban Baby Namra ne ya aiko ko?”


Ta tambaya tana kallona, sai na rasa me zan ce mata idan nace a a na yi karya tun da fa gaskiyar a bayyane, ban gama tunanin irin amsar da zan bata ba na ji ta fara karantawa wasikar dake tare da kayan.

“On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a woman like you is indeed a gift, People tell me that the best years are still to come. I have to agree with that because my upcoming years will be spent with the world’s most amazing woman.

Happy birthday to someone who improves every life she enters. You always know how to make an impact, but none so strong as the one you made on my heart. I will turn your black and white world into full-blown technicolor. Happy birthday to the leading actress of my life,

If anyone is deserving of all the happiness in the world, it’s you, you are a wonderful mom, a loving woman, and a fantastic human being.


Happy birthday Lims❤️”


Kamar sautin waka haka nake jin ko wane kalami da Hafiza take karantawa a bayyane, wani irin shauki da jindadi naji ya kama ni, ba na kalaman da Ahmad yai min kadai ba har na kyautar da yai min a yau da kuma nuna min ranar haihuwata tana da muhimmanci abunda wani be tana min ba, jin ziciyata tana kokarin alakantuwa da wani abu yasa nai saurin kawarda abun a zuciyata, domin idan har na nace zan sake biyewa kalamai ko wasu abubuwan na koma dakin so to lallai ban dauki darasi akan abunda ya faru da ni ba, domin Aminu ma yana nuna son kamar ba gobe a lokacin da yake nemana, Abdulhamid ma mun yi soyayya da shi a boye kamin daga baya ya dawo min, kuma dukansu ban tsammaci haka daga garesu ba sai gashi sun juya min ba, miyasa shi ma Ahmad din ba zai juya min ba, shi ma ai namiji ne kamar su, ba a gane na gari a fuska ko a aiki har sai an zauna da mutum musamman maza.

“Ke me kike tunani? Ni daman na san wannan rawar kafar da yake son ki yake, ya ga ruwan da ke masa wanka.... Oh wayyo ni inama ace Aminu zai ga wasikar nan yau”


STORY CONTINUES BELOW

Dan murmushi nai.

“A cikin wasikar kin ji yace yana so? ku rika fahimtar abu mana”


“Ohhh se dis woman, sai ya fito ya furta miki ne? Ai su manyan mutane basa fada maka suna sonka, ke bari ma na fada miki ko zancen basa zuwa sai dai a kai musu mata, yanzu idan ya fara zance da ke sai dai ya aiko mata a dauke ki akai masa ke”


“Oh really?”


“Yes Lims”


Sai duk suka kwashe da dariya, a gurin suka gutsitsira cake din aka cirewa su Namra na su na debi kadan na ci na sha lemun sannan na tashi na shirya na nufi gurin aikina.

  As usual ina shiga na nufi office dina kai tsaye, ina shiga office din gabana yai mugun faduwa, zuciyata ta soma bugawa da karfi kamar zata fito sakamakon arba da nai da Ahmad tsaye jikin tebur dina yana sanye da farar shadda kansa da hula sai kamshin turare yake, rikewa nai na kasa sake daga ido na kalleshi kuma na kasa juya na fita daga office din kamar yadda na kasa karasa ciki.

“Lims shigo mana”


Kamar mai koyon tafiya haka na fara takawa na karasa cikin office din. Har na kai gurin kujerata na zauna ban iya daga ido na kalleshi ba.

Wani dan karamin abu mai kamar akwati ya aje min yan zagaye shi da wani jan zare.


“Happy birthday, kin san on my birthday kin bani kyautar agogon da me ma?”


Ya tambaya yana yatsina fuska kamar da gaske ya manta. Muna hada ido sai ya kanne min ido daya ya sakar min kyakkyawan murmushi, sannan ya juya ya fice yana kokari saka hannayensa aljihu. Murmushi nai haka nan kawai sai na ji farinciki ya cika min zuciyata ya wanzarda nishadi da cikinta. Zaren na fara budewa sannan na bude box din mai kama da box din agogo, domin shi na fi kyautata zaton gani a ciki.

To my surprise sai nai arba da chewing gum, irin wanda na bashi a ranar birthday sa, ban san lokacin da murmushinsa mai sauti ya subuce min ba.


***         ****         *****


Kana kallon fuskar Abdallah kasan yana cikin tashin hankali kamar yadda Hajiyarsa ma take ciki, kusan na nashi tashin hankalin ne ke saka shi a damuwa ba kamar na Hajiya wacce ta bi ta gigice saboda batan Abdulhamid, wanda yau kwana uku kenan ba san inda yake ba kuma ba a ji duriyarsa ba, idan kuma aka kira wayarsa bata shiga shi kuma be kira ba, yawancin mutane sun fi kyautata zaton an garkuwa ne suka dauke shi duba da halin da ake ciki a kasar.

  Hajiya kuma tana ganin kamar yan yankan kaine suka sace shi, domin idan yan garkuwa ne ba zai kwana har uku a gurinsuba, ba tare da sun kira waya sun fadi abunda suke bukata ba, yayinda dan'uwansa Abdallah kuma yake wani tunanin na dabam.


“Ya dade a nan zaune, yana ta latsa waya can kuma sai ya kalleni yai shiru kamar mai tunani, ashe yana ji a jikinsa”


Hajiya ta fada cikin kuka.


“Yana zaune aka kira sallah isha'i, a gida yai ta be je massallaci ba, har na yi mamaki dan be saba sallah a gida ba ko ta asuba balle isha'i tun tashinsu shi da Husaini ba su saba sallah gida ba saboda Alhaji ya koya musu sallah masallaci, na ce masa ga abinci yace min a a ya koshi na bashi ruwa shayi ya sha, na sa Furera ta hada masa ruwan shayi ya sha, be bar gidan nan ba sai kusan 11pm sannan yai min sai da safe ya tafi, ita ake har yau be dawo ba, kuma ya saba zuwa da safe ya gaishe ni haka da dare kamin ya wuce gida kusan ma nan yake wuni saboda ba shi da mata a yanzu, kuma dan shirye shiryen bikin nan da ake kusan kullum yana nan da shi ake duk wasu shawarwari tun da lokaci ya kusa”


“Allah dai ya bayyana shi a duk inda yake”


Wata dattijiwa dake kusa da Hajiya ta fada fuskarta dauke da damuwa.

“Amin”


Abdallah ya amsa tare da sauran mutanen da suke falon, gaba daya idonsa da hankalinsa yana gurin Mahaifiyarsa.

“An kai report gurin police amman har yanzu shiru”


“Ai wannan abun bana police bane kawai, ya kamata a shiga malamai ayi sadaka Allah ya bayyana shi a duk inda yake, massada babu abunda basa yi gashi ana kusan biki saura wata daya ace babu ango ina lafiya?”


“Amaryar ita ma ai tana can hankalinta tashe ance sai kuka take, ko abinci bata iya ci”


Cewar Hajiya. Hajiya Rukaiya wacce kanwace ga Hajiya ta rausayar da kai cike da tausayawa.


“Wayyo Allah, ai dole Allah dai ya bayyana shi”


A nan ma Abdallah ya sake amsawa da Amin sannan ya mike tsaye.1

“Hajiya bari na leka office na dawo”


“To Allah ya tsare ka kai ma”


“Amin, In-Sha-Allahu za a ganshi ki kwatarda hankalinki dan Allah”


Kai kawai ta gyada masa ta Lumshe idonta dake cike da damuwa. Shi kuma ya fice daga falon jiki ba kwari.Garin daukar cingan din naji na taba wani abu mai kamar karfe, da na ciro cingan din na duba da kyau sai nai arba da makullin mota.

  Ba shiri na mike tsaye ina dubawa duk da bani da motar ina kallon wannan makullin na san cewa na mota ne, wani irin faduwa gabana yai sai an rasa abunda zan yi kuma na kasa yarda cewar makulin motar ne, yana sane ya saka min shi ko? Ko dai ba da gangan yai ba. Maida makullin nai na dauki box din na nufi office dinsa.

  Tsaye na tararda shi jikin fridge ya kafa gorar ruwa a bakinsa yana sha, ganina yasa ya sauke ruwan ya juyo yana kallona.+

“Ina....ina tunanin ka yi mantuwa a box din na ga wannan”


Na fada ina budewa na dauko makullin na nuna masa. Sake cika bakinsa yai da ruwan sannan ya aje ruwan ya rufe fridge din.


“No ina sane na saka, na yi ta tunanin abunda zan ba ki as birthday gift, sai na ga babu abunda ya dace a yanzu nai miki kyauta da shi kamar mota, saboda zuwa aikin da kike sai ki huta da hawan napep”


“No i can't accept this”


Na fada ina nufar teburinsa na aje makullin.

“Lims why”


“A'a Halima dan Allah, ranka ya dade kana min abunda ba a cikin dokikin kamfanin nan yake ba, ko da kana taimako ina tunanin kana taimako na ne saboda Allah, ba zan iya karba kyauta mai girma irin wannan ba, bana son alakar mu da wuce haka”


“Why? Kina tsoron an sake shiga rayuwarki? Saboda Aminu ya cuce ki? Abdulhamid ya juya miki baya? Abraham ya yaga rigar mutuncinki? Dukansu maza ne ko ba haka ba? Kina tsoron ki sake komawa wani hali ko? Kina tsoron kar wani yace yana son ki wata rana ya juya miki ba right? Kina da gaskiya kuma kina da hujja kuma dole ayi miki uzuri....”


Ya matsa kusa da ni sosai yana kallon cikin idona.

“Duk abunda nake miki, ina yi ne saboda na ga na faranta miki rai, ba ke kadai kika cancanci farinciki ba, nima na cancanci farincikin, amman na danne nawa na manta da nawa, na danne duk wani bakin rai da damuwa da suke raina, saboda ke na sama miki farinciki, daga lokacin da samu labarinki sai nai kokarin mantawa danawa kin san saboda me? Saboda tausayinki ya cika min zuciya”


Ya kara matsowa daf da ni.

“Dukan abunda nake miki ina yi ne saboda zan iya kuma saboda na fi karfin abun, ba zan taba yi miki wani abu dan kawai ya tambayi so daga gareki ba, zuciyata bata taba raya min na siye soyayya kowa ba, balle kuma ke, ban taba jin cewar nai miki wata kyauta ko wani abun jidadi dan na tambayi soyayyarki da shi ba, Lims ina son shiga rayuwarki na taimake ki na taimaki yayanki da yan'uwanki”


Na yi saurin kaucewa ina aje numfashi.


“Ni ban shiryawa aure ko soyayya a yanzu ba, duka mazan nan da suka yaudare ni babu wanda be nuna min so na gaskiya ba, amman daga baya komai ya canja, kai mai gidanane be kamata alakar mu da wuce haka ba, indan har da gaske taimako na zaka yi to ka taimake ni saboda Allah kawai”


Dayan hannunsa ya saka aljihu, ya juyo yana kallona.

“Ni ma ba zan bari kiyi yanka akan danye ciwo ba, ai baki gama warkewa daga ciwon ba, ke kike kokarin saka kanki a so ba ni ba, na kai ki a restaurant din da nake cin abinci ne har na zaunar da ke a kujerar da kike zargin wani abu ne saboda na yarda da ke, na daukeki yar'uwa ne shiyasa na tura miki sakon cewa I'm not just your friend, na aika miki da sakon birthday ne a gidanku saboda kina daga cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata, dukan abunda nake miki saboda kawai ina tausayinki ne kuma ina son ki samu farinciki, idan zan siye soyayyarki ba ta wannan sigar zan biyo ba, shim fada min na taba furta cewar ina son ki? Ko na taba zuwa gidanku da sunan zance? Idan zan nemi aureki a gurin iyayenki zan tafi ba a gurinki ba, domin ni kallon budurwa nake miki yar 18, ba zan yi magana da ke ba har sai da izinin iyayenki, amman abubuwan nan da nake yasa kin fara tunanin son ki nake? Ashe son ki yana da arha da yawa”


STORY CONTINUES BELOW

Na kasa cewa komai sai hawaye nake, wani irin abu na rashin jindadi da kunya ya baibaye ni, tabbas be furta yana so na ba, amman ya nuna yana kokarin boyewa a yanzu saboda yana ganin kamar ba zan ba shi hadin kai ba, wata kila kuma na yi kuskuren fahimta taya babban mutum mai rufin asiri kamar Ahmad zai ce yana so na? Taya mutumen da ya san wani ya min fyade zai yarda ya zauna da ni? Taya mutumen da samu komai na jindadin rayuwar duniya zai ce yana so na?

      Matsowa ya sake yi kusa da ni ya mikomin tissue.

“Share hawayenki, babu kalmar da na fada dan na bata miki rai, babu kalmar da na fada dan na muzanta ki, ba zan ga wanda zai fada miki wata magana marar dadi ba na saurara masa, ba zan cilasta karbar abunda ba ki da ra'ayi ba, lokaci yayi da ya kamata ace kin samu jindadi rayuwa kin daina kuka, ko akan yara ko akan komai ma, shi nake kokarin nuna miki, ki kwantar da hankalinki ki sake jikinki”


Ya fada cike da nuna damuwar hawayen da nake zubarwa, da kansa ya janyo min kujera ya aje bayana.1


“Zauna”


A take na zauna daman jikina ya dade da yin sanyi. Sai ya risina gabana yana kallon fuskata, fuskarsa na dauke da murmushi.

“Fada min gaskiya ko dai ke kike so? Dan kin ga ni kyakkyawa ne?”


Yanayin da kuma sigar da yai min maganar na san ya fada ne kawai dan ya saka ni murmushi, kuma na yi murmushi ina share hawayena.

“A yafe min hawayen nan da na saka kika zubar, seriously bana son naga kina kuka, bana son na ganki cikin damuwa, idan har ba zan iya cireki a ciki ba to be kamata na saka ki a ciki ba”


Ya karasa yana kama kunnesa kamar wani karamin yaro. Sannan ya mike tsaye ya nufi gurin kujerar.


“Idan kina son motar zaki iya dauka, idan kuma ba kya ra'ayi”


Na karasa yana daga kafadunsa alamar hakan be dame shi ba.

“A a na gode”


Na fada sannan na tashi na nufi office dina ina jin nauyi, zuciyata kuma babu dadi, kamar be dace nayi masa maganar ba, idan ma zan maida kyauta ba sai na nuna dan wani abu ya ba ni ba, sai a lokacin ne na ji wata kunyar ta kara baibaiyeni.

Cikin rashin kuzari na zauna na fara aikina ina jin jikina sai a hankali, haka ma rai, juyawa nai na kalli windows dakina dake rufe sai na mike tsaye na karasa gurin ya bude windows din, hangoshi nai tsaye yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa, kamar kullum hannayensa na zube aljihu. Juyowa nai na dawo na zauna amman na kasa samun natsuwa lokaci zuwa lokaci sai na waiga na kalli windows a duk lokacin da zan kalli windows sai na ganshi tsaye yana kallona.

Tashi nayi naje na rufe windows din sannan na samu natsuwa, bugun zuciyata ya daidaita har na samu damar fitar da numfashi a natse.

Na cigaba da aikina amman sai na nemi natsuwata na rasa gaba daya na kasa tsayarda hankalina guri daya, kuma na rasa dalilin haka, after every two minutes sai na ji gabana ya fadi, ba faduwar gaba irin na tsoro ko fargabar faruwar wani abu ba, faduwar gaba ne irin wanda ban saba jin irinsa ba.

  Misalin sha biyu saura wayata tai ringing, sai na saka hannu a jakata na dauko wayar. Abun mamaki yau Abdullah ne yake kirana, abun ka da mai nema jiki na rawa na dauka ina doka sallama kamar yana gabana, da fari na yi zaton ko zai min murnar birthday na ne tunda na dora a status kuma na san zai gani, amman bayan mun gaisa sai ya bijiro min da wani batun na dabam.

“Abdulhamid ya bata yau kwana uku”


Da mamaki na ce.

“Abdulhamid ya bata kamar ya? Sai kace karamin yaro?”


“Nima ban sani ba, an nemi an rasa wayarsa kuma bata shiga, so na fada miki ne saboda ki kula saboda ina tunanin batansa baya rasa nasaba da Abraham”


“Abraham kuma?”


“Eh Abokinsa ne, so be careful”


Yana fadar hakan be tsaya komai ba ya kashe wayar, mamaki da al'ajab suka rufe ni, daman Abdulhamid yana da alaka da Abraham ne? Amman a cikin babu wanda ya taba nuna min cewar ya san wani, shi kansa Abdallah be tana nuna min haka ba duk kuwa da kasancewar na fada masa komai a game da Abraham din.

  To idan ma Abraham ya saci Abdulhamid me zai masa? Me zai saka ya sace shi? Hakan na nufi Abraham yana da alaka da Abdulhamid kenan shiyasa yai min fyade ko kuma me? Ko kuma shi Abdulhamid din ya san Abraham din ya min fyade? Amman kuma Abraham din ai shi police ne, sai dai a sigar da suka shigo gidan zuwan farko da kuma na biyu duka ta sigar fashi suka shigo, a zuwansa na farko ma ya bukaci kudi kuma ya tambayi ina Abdulhamid yake, ba kowa na sani a abokaninsa ba, amman be taba min labarinsa ba, ko da yake Abdulhamid ba mutum ne mai yawan magana ba dan baya son hayaniya.

STORY CONTINUES BELOW

Wani tunanin ne ya fado min a rai, ba ni ce kadai a cikin hadari ba har da Ahmad, domin kuwa Abraham yasan da cewar Ahmad ya san sirrinsa, idan har zai iya sace Abdulhamid to ba zai bar Ahmad ba, jiki na rawa na tashi da sauri na nufi office dinsa, domin gaba daya tsoro ya gama kamani, ko da na shiga na tarar yana waya, sai dai ganina yasa yayi saurin yanke wayar ya ta so ya nufo inda nake tsaye.

“Lafiya ya naga hankalinki tashe?”


“Yanzu Abdallah ya kira ni ya fada min wai Abdulhamid ya bata, kuma yana zargin da sa hannun Abraham”


Kansa ya daga kasa ya lumshe ido ya busar da iskar bakinsa sannan ya bude ya kalleni.

“Kin tada min hankali sosai na dauka wani abu ya same ki, to miye naki a batan Abdulhamid din ko Abraham”


“Zai iya cutar da kai, tun da ya san kasan sirrinsa, ko da yana da sanda, a lokacin da suka shigo min ta siffar yan fashi suka shigo min, zai yi maka komai, zai iya kokarin cutar da kai, idan wani abu ya same ka ta dalilina, ba zan jidadi ba, ban san inda zan saka kaina ba, ban yafewa kaina ba”


Na karasa cikin muryar kuka, kara matsowa yai kusa da ni ya kai hannunsa kamar zai taba ni sai kuma ya fasa ya juya bayansa, yana maida numfashi, can kuma ya juyo ya kalleni.

“Za ki iya zuwa gurin motata ki jira ni?”


Na gyada masa kai da sauri daman tuni hawaye sun wanke min fuska jikina rawa kawai yake kamar mazari.

“Good girl je ki yanzu”


Na juya ina share hawayen na fita na koma office dina na dauki jakata da wayata na nufi inda motarsa take. Kamin ya iso duk na matsu, sai dai na lura da mutane sun fara saka mana ido cikin har da blessed wacce idan ta gan ni na fito ba a lokacin tashi ba take ce min wai zan fita da oga ne ko?

Tun kan ya karasa ya matsa remote din motar ta fita key ni kuma na bude na shiga na zauna, yana shigowa ya tashi motar muka bar kamfanin.

Ganin muna ta tafiya ba tare da ya min magana ba yasa na ce.

“Ba ka ce min komai ba”


Kallon idona yai da ke cike da hawaye.


“Lims sarkin kuka, ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ki”


“Ba ni ba kai”


“Ni kuma ke ce damuwata”


“Haba ranka ya dade...”


Ya katseni


“Ahmad”


“Ahmad....”


Na maimaita cikin sautin kuka sannan na cigaba.

“Wannan ba abun wasa ba ne, Wallahi zai iya cutar da kai, duk mutunen da zai iya keta haddin aure ya lalata rayuwar wata to zai iya komai, ban san adadin abunda ya aikata ba, ban san iya abunda yai ma wasu ba, wata kila ya tana kisa, ban sani ba, zai iya cutar da kai, kana tunanin idan wani abun ya same ka ni zan jidadi? Zan iya walwala?”


“Duk wannan hawayen saboda ni? Mi kake nai?”


Ya tambaya yana faka motarsa gefen titi.

“Ka kwarara tsaro a gidan da kamfani, kuma ka fadawa police halin da kake ciki”


“Police ba za su iya ba ni tsaro ba, kuma ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ni”


Ya miko min ruwa.


“How ta yaya zaka ce babu abunda zai same ka bayan Abdulhamid ya bata kuma....”


“Abdulhamid yana hannun DSS”


“What....?”


Na masa wani irin kallo na mamaki.

“Yes su suka kama shi yana Abuja”


STORY CONTINUES BELOW

“Ho.. How.... Do you know kai kasa aka kama shi?”


Na nuna shi da yatsana.

“No bincike yasa aka kama shi, har Abraham din suna can tare”


“Miya faru? Fada min?”


“Nima ban sani ba”


“Then taya ka san an kama su?”


“Mataimakin DSS na jihar nan he's my friend, shi ya fada min”


“Miyasa aka kama su? Kai ka saka aka kamasu?”


“Saboda me? Idan ma zan saka a kama wani ai Abraham zan saka a kama ba Abdulhamid ba, na fada masa matsalar Abraham ne kawai ana cikin bibiyar sa ana bincike ta masa, sai ga wannan ya faru da Abdulhamid din, shi ya fadi Abraham aka kama su”


“Amman miyasa aka kama su din?”


“Kin san sana'ar da Abdulhamid din yake yi?”


“Yana saida mota kuma yana aiki”


“Ya taba baki labarin Abraham, ko kuma shi Abraham din ya taba baki labarin Abdulhamid”


“A'a”


“Shiyasana fada miki, Abraham din ba son gaskiya yake miki ba, ba zai bar abunda yake saboda ke ba, ba kuma zai fallasa miki sirrinsa ba, da dawo gareki ne kawai saboda yana son haihuwa, kamar yadda ya fada miki zai iya mutuwa a ko yaushe idan asirinsa ya tonu, ya taba fada miki cewar yana da mata?”


Na girgiza kai da sauri.

“A a”


“To yana da mata tana can garinsu enugu, dukansu su biyu suna wani business, kuma babu mai sanin alakarsu sai su i think basa yawan ziyarta juna ne saboda gudun kar a zarge su”


Bude motar nai na fita ina shakar iskar waje. Sai shi ma ya bude gefensa ya fito ya zagayo inda nake.

“Hakan na nufi Abdulhamid ya san cewa shi yai min fyade kenan?”


“Be zama lallai ya sani ba, domin ba kowa zai yarda abokinsa ya keta haddin matarsa ba, zai kuma iya yiyuwa ma shi ya saka shi, ko ma dai minene gaskiya zata bayyana”


Dana lumshe idona sai hawaye suka sauko min. Ina jin lokacin da Ahmad yaja dogon numfashi ya sauke.

“Sometimes, Allah yana jarrabar bawanaa ba dan baya son bawan ba, daga baya kuma sai ya kawo masa sauki, a yanzu ne zaki gane ba karamin taimakinki Allah yai ba da ya raba ki da Abdulhamid, shi kan shi uban yayanki da za ki bibiya tahirinsa wata kila za ki samu wani abun ya same shi, ko kuma zai same shi a gaba, shi kansa Abraham din da kin yi kuskuren aminta da shi kin aureshi da kin jefa kanki a cikin wata matsalar, trust me Allah yana son ki, and i think lokacin kukanki ya kare, wani jindadin nesa, wani za ki ga sai ya tsufa ta hanyar yaya zai samu, wani kuma sai ya sha wahala, wani kuma ya jidadin farko daga baya wahalar ta zo, ki gode Allah Allah ya kawo miki sauki tun a yanzu”


Bude idona nai na kalleshi, sai na ji ya kara kwanta min a rai, yana da gaskiya wani jindadin nesa yake, wani kuma ba za a taba jindadin ba har abada.

“Bana son ki saka kanki a damuwa, bana da tashin hankali a yanzu kamar damuwarki, Doc Nura ya fada min cewar idan zuciyarki ta sake bugawa zan a iya rasa ki, so bana tafar haka, kina bukatar ki rayu ko dan saboda yayanki da ni, ina ji a raina cewar ni kadai ne namijin da zan juya duniyarki ki jidadi, na baki abubuwan da kika rasa, na ranta ran mahaifiyarki da yan'uwanki, ba alfahari nake ba, ba kuma ina fada da wata manufa ba, dukan abunda zan yi a yanzu dan na saka ki cikin farinciki ne na mantar da ke damuwarki, a yanzu kam bana jin zan iya bari ko kuda ya cutar da ke lims, wahalarki ta yanke da izinin Allah”


Ji nai kamar ya daure ni, indai jin kalamai ne na sha jinsu daga bakin maza, amman baka gane gaskiyar kowa sai ka zauna da shi, sai dai idan na kalli Ahmad sai na ga kamar be yi kama da mutanen da za su iya wannan ba. Sai dai idan har kalamansa suna nufin soyayya ko aure to ban shirya ba a yanzu, bana jin akwai namijin da ya cancance ni a yanzu sama da Abdallah.

“Zamu iya komawa Gurin Aikin?”


“No na fito da ke nan waje ne saboda ki samu natsuwa and fresh air, yanzu kuma ki zan kai ki gida ki huta just for today daman yau birthday ki ne you're princess”


Na juya na shiga motar, shi ma ya zagaya ya shiga yai mata key.

“Kamin na hadu da ke, idan na tuna babu matata babu Baby Namra babu Mahaifina sai na ji duniya ta ta koma upside down, ammn daga lokacin kaddarar rayuwarki ta same ni sai komai ya canja, na zama jarumi na ji cewar nima zan sake samun farinciki, a duk lokacin da na tuna da yata sai na tuna ki sai na ji bakincikin rashinta ya tafi”


Kallonsa nai sai ya sakar min irin murmushin nan da ake cewa ya fi kuka ciwo.


“Ya isa a nan zan sauka sai na hau napep”


“Ba ki son a gan ki da ni ne ko? Fine”


“No bana son ina shiga motar mutane ne, yanzu sai ka ji ana magana”


“That's why na baki mota ai dan na dauke miki wahalar hawan napep, kuma tsakani da Allah ina jin bakincikin hawan Napep da kike saboda namiji ne zai tuka ki”


“Idan ka bani motar ka bude hanyar da za su kara zargina, a fara magana akai”


“To shikenan zan aje miki har lokacin da za ki bukata”


Har na bude motar da zimmar fita sai kuma na kalleshi.

“Baka fada min wani irin business suke ba?”


“Nima ban sani ba, amman ko minane idan sun gama bincike ai kowa zai ji”


Na fita daga motar sannan na rufe mishi motar sai ganin nai ya sauke gilashin motar.

“Ki kula min da kanki”


Ya fada sannan yai ma motar key ya hau titi, ba ni da abunda ya wuce na bi motarsa da kallo har sai da na daina hangota.ABDALLAH POV.+

Misalin tara da yan mintuna ya shigo gurin Hajiyarsa kana kallonsa kasan yana cikin damuwa. Yayyen Hajiya ya tarar a falon wato Hajiya Altine da Hajiya Rukaiya, sai da ya gaishe su sannan ya wuce dakin mahaifiyarsa, yadda ya same ta zaune saman carpet rike da carbe fuskarta da damuwa sai ya kara jefashi a cikin nasa damuwar. Kusa da ita ya zauna bakin gado yana kallonta da Fuskarsa da ke bayyana damuwarsa karara.

“Hajiya barka da dare”


Ta dago ta kalleshi kana ganin idonta ka san ta sha kuka.


“Barka dai Husaini, ya aikin”


“Alhamdulillah, Hajiya ki rage saka kanki a damuwa, In-Sha-Allah za a ga Abdulhamid”


“To Allah yasa ni abun yanzu har tsoro yake ba ni, jikina yayi sanyi sosai, idan na duba sai na rasa abunda Abdulhamid zai yi wa wani da zai cutar da shi mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, Allah yasa ba yan fillar kai ya hadu da su ba, domin na san masu neman kudi fansa da su suka kama shi da yanzu sun kira sun fadi abunda suke bukata”


Jimmmm Abdallah yai kamin ya kalleta a natse ya ce.

“Hajiya zaki iya tuna lokacin da akai yi Halima fyade?”


“Na sani”


“Mutumen da yai mata fyade wani kirista ne, kuma abokin Abdulhamid ne, ban san miya kai shi gidan ba har yai ma Halima fyade, a yanzu kuma ina kyautata zaton kamar da sa hannunsa gurin dauke Abdulhamid”


Cikin tashin hankali Hajiya ta kalleshi.

“Kamar kai ya akai ka sani?”


“Halima ta fada min mutumen ya dawo yana sonta, saboda cikin da tai shi kuma haihuwa yake nema, bata aminta da shi ba amman ya dage yana son ta aure shi, shiyasa na fada mata gaskiyar cewar shi yai mata fyade, sai dai ita bata san yana da alaka da Abdulhamid ba, ni kai dai na sani nima kuma saboda na taba ganinsu tare har hotuna sun yi tare, shi mutumen police”


“To me zai saka ya dauke Hassan?”


“Saboda ni na fadawa Abdulhamid gaskiyar daya kasa yarda da Halima a lokacin da abun ya same ta, ke da shi kuna ganin kamar ta aikata zina ne, yayi ta bakinciki yana fadar cewar shi Abraham zai ciwa amana, wata kila yai masa magana ko yai masa wata barazana shi kuma Abraham din ya dauke shi”


“Amman miyasa baka fadi wannan ba? Sai yan sanda su bincike shi mutunen?”


“Hajiya idan baka iya kama barawo ba, sai barawo ya kama ka, shi Abraham din police ne kuma da na bincika sai na samu labarin cewar baya cikin garin nan a office dinsa ma har an saka wani, amman mu saurara na kwana biyu tukuna tun da mun kai report din gurin Police kuma ana Addu'a, ko minene zai bayyana In-Sha-Allah”


“Amman irin wannan ai kama shi za ayi a bincike shi ko kuma ita Halimar, waya sani ko ma ita ta saka shi ya sace shi saboda ta dauki fansa balle ta ji zai yi aure, kuma ta ga shi Abraham din yan sonta”3


“Haba Hajiya wane irin Halima kuma?”


“Zata iya yin komai wannan yarinyar da kake gani, ni sam ban yarda da ita ba ma”2


“Babu hannunta a cikin nan, kuma na fada miki ki bari nan da kwana biyu idan ba mu ga wani abun ba, sai mu fada musu wanda muke zargi”


“To ko ma dai minene Allah ya bayyana shi”


“Amin”


Yayi kusan awa daya a dakin sannan yai mata sallama ya fice. Aiko kamar fitarsa take jira ta fito falo ta labartawa yan'uwanta abunda ya faru dukansu sun cika da mamaki.


STORY CONTINUES BELOW

“Wannan maganar ai ba abar a kyale ba ce”


Cewar Hajiya Altine, sai Hajiya ta amsa ta tana ware hannu.

“Ni ma shi na gani ban zafafa abun ba ne saboda a gabansa ne, na san zai iya shiga cikin lamarin tun da uwarsa ta shigo ciki, yadda kika san ta wanke gaba ta zuba masa ya shanye haka yake da ita, ko sunanta baya son a ambata a wani abu”


Hajiya Rukaiyah ta dora da.

“To waya sani, ko wani abun tai masa, amman duk yadda akai ta san inda Abdulhamid yake”


“Nima shi nake tunani, saboda bakinciki zai yi aure gashi ita ba tai ba zai iya sawa tace shi mutunen ya sace shi, ko kashe shi ma zasu iya yi, ko kuma su masa wani illar, kuma Allah kadai yasan gaskiyar lamarin nan wata kila ma daman can ta san abokinsa nw ta aure shi dan su kashe shi su ci dukiya Allah ba basu sa'a ba, Allah ya gani ko da akai auren nan ba zan ce miki yaron nan yana son Halimatu ba, be taba nuna min ba, kuma a lokacin ma ta neman lafiyarsa yake amman sai ya zo min da maganar aure daga sama, ban san yadda akai ta janyo hankalinsa ba ma, kamar abun magani, cikin kankanen lokaci akai komai”


“Kin san abunda za ayi? Ko yanzu ita ya kamata a kama, idan ta ji wuya dole ta fadi inda shi Abraham din yake da Abdulhamid din, wannan ai ba maganar bari ba ce”2


Cewar Hajiya Altine tana tabe baki alamun mamaki ya gama cikata.

“To yanzu a kira Yusuf a fada masa, gobe tun da farar safiya a doka masu sammako a kamo yar iskar, yarinya ta same mana fitina a cikin dangi”


Hajiya ta fada tana kara yamutsa fuska. Hajiya Altine ta ce.

“Haka za ayi, daman Yusuf din ya fada min ai akwai inda suke saka mutum su saka masa wata hula duk iskancinsa sai ya fadi abunda yake gaskiya, bari na kira shi....”3


Ta karasa tana danna number dan nata rai a bace, Hajiya kuma ta zauna saman cushion tana ta rawa da kafa tana kara kashe ido, babu komai a zuciyarta sai tsanar Halimatu.


HALIMATU POV.

Na iso gida cikin wani yanayi da ban taba samu kaina ba, ni dai ba zan ce ina son Ahmad ba, haka kuma bana kin shi, sai dai a yau kalamansa sun kashe min jiki sosai.

Mama ta yi mamakin ganin na dawo gida da wuri bayan a a lokacin na saba dawowa ba sai yamma, karya nai mata na ce mata yau babu aiki da yawa shiyasa aka tashemu. Har na yi kamar na labarta mata abunda ya faru da Abdulhamid sai kuma wata zuciyar ta hana ni, domin na san ita ma din zata zargi Ahmad da saka a ka masu kamar yadda nima zuciyata take zargi, kuma zata iya cewa zatai wa Hajiya jaje gudun kar ace bata ji ba idan taje kuma dole zata bada labarin abunda na fada mata ne, idan kuwa Hajiya ta ji haka zata zarge ni, so rufin asirina kawai nai shiru da bakina na bar abun a cikina, har sai ya bayyana.

Babu irin tunanin da ban yi ba a ranar har cikin daya ina abu daya, dan son gano abunda Abdulhamid da Abraham suke aikata marar kyau, idan na saka wannan na kwance wacan na kulla wannan, sata yake? Tare da Abraham din suke fashi? Ko kuma wata sana'ar ce dabam? Duk wani mugun aiki da zan kwatanta Abdulhamid da shi sai na ga kamar ba zai iya aikatawa ba, wata kila ma dai Abraham din shari yai masa saboda kar ya cutu shi kadai, domin ko a lokacin da na ke aurensa ban ga wata alama da ta nuna rashin gaskiya a tare da shi ba, duk da yake baka iya gane gaskiyar mutum mai boyo, Abdulhamid kuma yana daga ciki irin mutanen nan da suke boye abu, soyayyar da muka da shi ma a lokacin da nake budurwa a boye muka yi saboda baya son kowa ya sani.

Haka dai nai ta sakesake na har dare raba ban yi bachi ba, domin tun ina jin alamar bachi bachin a idona har ya fitar min gaba daya, tashi nai na fito bakin balcony na zauna ima ta kallon taurari kamar mai kidayarsu, babu komai a tare da ni sai tunani kala kala. Can ciki ciki na ji wayata dake kan drawer tana vibration alamar kira yana shigowa wayata. Sai na tashi na koma dakin, hannu na kai na cire carjin sannan na dauki wayar sai nai arba da number Ahmad, gabana ne ya fadi kamin mamaki ya rufe ni, miyasa ya kira ni yanzu? Abunda be tana ba, ko kirana a gida balle a wannan lokacin da agogon wayata ya nuna karfe biyu saura, to ko dai fada min zai yi an sako Abdulhamid? Ko kuma wani abun zai fada min dabam, kiran na daf da tsinkewa nai picking na kara a kunne sai dai ban yi magana ba sai da na fito balcony. Ina ta jiran yai magana be ce min komai ba, idan na duba wayar sai na ga kiran na tafiya har sai da na gaji da kaina na ce


STORY CONTINUES BELOW

“Hello”


“Lims, kema kin kasa bachi kamar ni kenan?”


“Eh”


“Kin san me? Dakina yai min ba dadi sai na fito na zauna harabar gida sai kidayar taurari nake, yanzu kuma haka nan kawai na ji ina bukatar jin muryarki, duk ban yi zaton za ki dauka ba”


Ya fada da murmushin da zan iya jiyowa, kana jin muryarsa ka san ransa kal yake fa farinciki. Na yi shiru ban ce masa komai ba.

“Fada min miya hanaki bachi?”


“Ni ma ban sani ba, na samu kaina da kasa bachin ne”


Murmushinsa mai sauti ne ya daki dodon kunnena.

“To je ki kwanta, so that's ki tashi da wuri i need to see early in the morning”


“Okay”


“Sweet dreams Lims, ki rufe idonki ki tuna duk wani beautiful memories we share together za ki yi bachi, kuma ina rokon ki yi mafarkina take good care of yourself for me pls”


Be jira abunda zan ce ba ya yanke wayar, for the first time na samu kaina da shiga calls list na kurawa number ido for no reason, before murmushi ya biyo fuskata, sai da na sake kallon taurarin sannan na tashi na koma daki na kwanta. Lumshe ido nai thinking all the good memories we share together kamar yadda ya fada, babu abunda na fi tunawa kamar tears din da muka share with one tissue, and location da yai maganar wai ko dai ina son sa ne? Samun kaina nai da murmushi, kamin wani lokacin bachi yai gaba da ni.

  Na farka raina Fresh har wani shauki nake ji, domin ina aiki ina yan wake wake na, ina cikin shiryarwa su Namra su tafi makaranta muka ji muryar wata mace wacce hausa bata isheta sosai ba.

“Dan Allah wacece Halima”


Zumut nai na fito ance son kira kamar bazarawa, na amsa da cewar ga ni ina kallon matan ashe ba daya bace sai dai dukansu su biyun suna sanye ne da uniform din yan sanda. Kamar jira suke na amsa suka nufo inda nake suna fadin.

“Zamu je da ke office din mu ki amsa wasu tambayoyi”


“Me nai?...”


Ban gama rufe baki ba suka rika ni muka fara ja in ja da su, da gudu Hafiza ta zo ta buge hannu police din ta hau ta da masifa.

“Mi tai muku? Haka kawai za ku shigo cikin gida mu kamata? Wace duka ta baku izinin shiga gidan mutane anyhow”


Police din ta nuna ta a fusace.


“Ke mahaukaci ki san abunda kike yi, karki ce zaki taba police zan ci mutuncinki, marar kunya kawai”


“Yes louder pls mu nan gidan sai mu kashe mutum ba komai ba ne a gurin mu, dan haka mun fiki tantiranci”


Cewar Hafiza tana zare mata ido kamar ba da police take fada ba. Sai da Mama ta daka mata tsawa sannan ta umarce da ta dauko min Hijabina.


“Amman Mama...”


Hafiza bata gama fadar abunda zata fada ba Mama ta tari numfashinta.

“Dauko mata Hijabinta na ce, duk inda za a je indai tana da gaskiya gaskiyarta zai fito da ita, Allah yana tare da mai gaskiya”


Ranta be so ba taje ta dauko min Hijabi na karba na saka, sai da muka fara tafiya sannan yarana suka fashe da kuka, ba ma kamar Amal wacce ta biyoni har kofar gida tana kiran sunana.6

“Momy.....”


Ban san lokacin da hawaye ya wanke min fuska ba, ko ba komai sun tozarta ni, sun saka ni a motar police patrol, duk wanda zai gan ni a ciki dole na zargi wani laifin na aikata, duk kuwa da kasancewar ban san abunda nai ba, ga kuma mutane da suka tara mana a kofar gida, domin motar har da maza sai suka tsaya daga waje. Ina jin lokacin da Inna take tambayatar wane station ne za a kai ni sai mai tukin motar ya amsa mata da.

STORY CONTINUES BELOW

“State CID”


Har muka isa gurin ban daina tunanin abunda na aikata wanda zai saka ayi min wannan kamun ba ban san na yi fada da kowa ba, ban san na yi wa wani kazafi ko kage ba, ban san mi na tarewa wani ba. Abun da kamar wulakanci domin muna isa suka saka ni a cell suka rufe, ko minti biyar ban yafe ba ba na hango Inna tare da Aisha da Mama da, like ten minutes wani kanen mahaifin mu ya iso gurin tare da yayansa.

  Na yi minti talatin a ciki sannan aka fiddo ni aka nufi wani office da ni, ina shiga na samu Hajiya a zaune tare da yan'uwanta, kallo daya na yi mata na gane dalilin kamoni da akai. Mutumen da ke zaune a gabamu yana karanta min abunda ake zagina da shi dan Hajiya Altine wato yayar Hajiya, na san shi ya san ni amman a yau sai kamar be taba ganina ba.


“Ni ban san inda Abdulhamid yake ba, kuma ban san inda Abraham yake ba, nan fa cid ce babba kuma kai police ne Yusuf kai baka sani ba ni ya za ayi na sani?”


“Karki fada min maganar banza karki sake kiran sunana ki dauka ba ki taba ganina ba a rayuwarki”2


Shine abunda ya fada min a tsawace, sai na kalli Hajiya na ce.

“Ba kiyayya ta shiga tsakanina da Abdulhamid ba, soyayyah ce kuma shi ya ji ba zai iya zama da ni ba ya rabu da ni, me zai saka ki yi min wannan zargin? Me nai miki Hajiya wannan maganar wace irin kiyayya ce?”2


“Au baki sani ba? Munafuka, ai auren da kika masa ba na Allah bane, kin janyo hankalinsa saboda ki ci dukiyarsa tun da kin ga shi yafi dan'uwansa kudi, to shi aiki yake yana sai da motoci, dan uwansa kuma likita ne kawai, ko cikin nan Allah kadai yasan gaskiyarsa kin dauka ba zai yarda ta magana tun da kin shanye shi kamar yadda kika yi ma Abdallah, duk yadda akai da hadin bakinki aka sace min d'a, tun da kin ga zai yi aure kin ji bakinciki, wai dan har baki da kunya kike soyayya da kanensa? Kin taba ganin inda aka auri yaya kuma yana da rai a auri kane? Wato gaki autar mata ko, ban cin kin raba kansu kuma ki shiga ki mulke mu son ranki ga bayi, kin ma ci uban rainin wayo Wallahi”2


Haka tai ta jera min bakaken maganganu sai abunda ta mance, jikinta har rawa yake kamar zata dake ni. Ban taba jin nadamar aikata wani abu ba kamar auren Abdulhamid a wannan lokacin, sai dai bawa be isa ya wuce kaddararsa ba.

“Za ki fada mana da arziki ko kuma sai cilasta ki?”


“Ban san komai a kai ba”


Na fada ina hawaye, bana son fadar komai saboda kar na jefa Ahmad a matsala, kuma idan Hajiya ta san ta dalilina ne zata kara zargina ne.

Haka aka raya aka kada aka juya aka na tsaya kai da fata ina fadar ni ban san komai akai ba. Daker aka bawa kanen mahaifina damar shigowa cikin office din wanda shi ma kanene ga mahaifinsu Abdallah, babu irin maganar da be yi da Hajiya ba amman ta ki saurarawa ita ala dole sai na fadi inda danta yake.

“Hajiya zumunci kike kokarin lalatawa, abunda kike yi be kamata, da uban yarinyar da mijinki uwarsu daya ubansu daya, akan me za ki yi wannan abu? Idan Alhaji yana da rai ke kin isa ko hararar zuri'arsa ki yi? Wallahi na tabbatar da ace Alhaji yana da rai yau ba za ki kwana a gidansa ba”


“To sai kaje ka taso da shi a yanzu ka saka ya sake ni, ni ba ku ga abunda tai min ba ta raba kan yayana, da gangan ta kulla soyayyah da Husaini yanzu kuma ta zo ta auri Hassan, yaro ya bata ga ayoyi tambaya akanta sai ku ce na kyaleta saboda ni ban san zafin haihuwa ba? Wallahi ko Alhaji ne a raye ba zai yarda a taba masa yayaba”


Kamar wacce take fada a ciki unguwa haka ta rika daga muryarta tana fadi abunda ranta yake so, Baba Buhari sai yai shiru kawai yana mata kallon takaici. Muna office din har la'asar, ganin na ki amsa laifina na ki na fadi komai yasa Yusuf din yace a shiga da ni wani daki, sai ya hada ni da wasu mata police suka tafi da ni wani bangare na gurin, suka shiga da ni cikin wani daki mai hudu, a yadda na fahimta abun kamar hadin baki ko ma nace cuta ce zallarta domin a iya sanina ko maza sai idan an dokesu kuma an kwana biyu ba su fadi kowa ba sannan ake saka a gurin, amman ni kamar daman can suna jira na ne. A rayuwata ban taba ganin inda aure ya zama kiyayya ba kamar nawa da ya zame min haka da Hajiya.


“Ba zaki fada ba?”


STORY CONTINUES BELOW

Dayar ta fada min cikin tsawa.

“Ni ban san komai ba”


Na amsa ta har lokacin zuciyata bata ayyana min na fadi komai ba. Wata hula suka saka min a saman hijabin da ke kaina, sai kuma suka cire min Hijabi suka saka min hular, wani namiji dake gafena na ga ya kunna wani abu sannan na daki hular kan nawa, a maimakon na fara bayani kamar yadda aka ce min mutane suna yi sai na nemi hankalina na rasa.3

AHMAD POV.

Murmushi yake yana kurba tea dake hannunsa, ya nade kafafauwansa yana zaune gaban Hajiya, ita ma murmushin take tana fadin.


“Haka nake son mace tana da tsantsaye da rayuwa, kasan da wata ce kana bata motar nan zata hau murna ta karba jiki na rawa”


“Sosai ma Hajiya, kuma Wallahi wannan abun ya kara min kirmarta sosai a idona, sai na ji ta kara shiga raina sosai Wallahi”


“Amman ka mata magana kuwa?”


“Har ynzu dai, ki taya ni da addu'a, tana da dan taurin kai dan kadan kuma tana da wuyar sha'ani shi ma kadan, saboda tana tsoron rayuwa”


“Allah ya tabbatar da alheri yasa kuma ya karba maka”


“Amin Hajiya Amin”


Ya amsa cike da jindadi addu'ar mahaifiyarsa, sannan na aje mug din ya mike tsaye.

“Bari naje office”


“To Allah ya tsare, ka dai kusa zama babban mutum kamar da”


Murmushi yai ya fice yan shafa kansa. Driving yake zuwa office cikin nishadi da annashuwa, haka nan kawai idan ya tuna yayi waya da Lims da daren nan sai yaji wani dadi ya lullubeshi. He arrived in time just to see her face yana son yadda yake tsawa jikin windows yana hangota musamman idan zata bude windows din office dinta. Haka yai ta tsaye a gurin tun yana duba agogon ya ga nine saura har ya koma ya zauna can kuma ya taso ya tsaya ya koma ya zauna har kusan 11am abunda bata taba ba, domin duk dadewarta bata wuce 9 ko 9:30.

  A take ya ji duk ya damu, wayarsa ya dauka ya kira wayarta sai ya jita kashe, a lokacin ne ya fara tunanin ko dan abunda ya faru jiya yasa yau ta ki zuwa aiki kuma ta kashe wayarta? Sai duk yaji ya shiga damuwa, har kusan 3pm ba wani labari, line ta ya sake gwadawa, sai yai sa'a wannan karon ya shiga, kamin a dauka duk ya matsu.

“Hello Lims”


“Ba Halima ba ce kanwarta ce Hafiza, Halima tana gurin yan sanda”


“What? Miya faru?”


“Dazun suka zo suka kamata da safe, ba irin wulakanci da ba su mana ba nan gurin wai suna zarginta da hannu a batan tsohon mijinta, tana can hannunsu sun kulleta”


“What? Wane station din ne?”


“State cid office”


Kashe wayar yai ya mike tsaye cikin zafin rai da rashin natsuwa na kira lauyansa, sai da yai masa bayanin komai sannan ya fada masa cewar su hadu a can din.

@360 na isa gurin, ko motarsa kadai ka kalla kasan babban mutum ma'ana mai ji da naira balle kuma shigarsa ta suit da yai, yana shiga cikin gurin lauyansa ya iso, duk wani shiga da fita da ake ciki lauyansa ne yake magana bashi ba, suna shiga office din aka kira Hajiya ta iso tare da Hajiya Rukaiya, ba su zauna ba Abdallah ya shigo office din shima.

Ahmad na kallonsa ya watsa masa wani mugun kallo.

“Kai kasa aka kamata kenan?”


Abdallah yai kamar be ganshi ba ko inda yake zaune be kalla ba balle har ya amsa shi. Hajiya ta kalli Ahmad da kyau tace.

“Waye kai? Ko kai ne Abraham din? Ni na saka aka kamata ba shi ba”


“To kina nan zaune za a fito da ita, kuma idan akan Abdulhamid ne ni zaki saka a kama ba ita ba, nine silar kama shi da akai yi ba ita ba”


“Kai Malam karka fada mana maganar banza, idan baka san darajar iyayenka ba ni san nawa, karka ce zaka yi ma mahaifiyara rashin kunya”


Abdallah ya fada a fusace. Sai Ahmad ta tabe baki yana kallonsa.

“Kasan darajarta ka bari ta ci mutuncin wacce bata da laifi?”


“Hey my friend don't tell me rubbish”


“An fada maka who are you?”


“Ai kai za a tambaya, ka so nan kana wani nuna isa wa kake a gurin Halima? Wallahi idan na so ko kallonka Halima ba zata sake yi ba stupid human being”


“Oh really? Ni ko zan nuna maka wani abu ne a gurinta, ka jira nan da one month sai na nuna maka waye ni a gurin Halima, sai ka gane darajata ta fi taka a gurinta”


Yana fadar haka ya mike tsaye da zimmar zai fita sai ga lauyansa ya shigo yana fadin su tafi gata can an saka a mota. Ba shiri Hajiya ta mike tsaye.

“Ina Yusuf din yake? Ya za a saki yarinya bata fadi komai ba? Ni ina dana yake”


Juyowa Ahmad yai ya kalleta.

“Dan ki yana Abuja hannun DSS kije ki yi fada da su idan kin isa, and idan wani abu ya samu Halima dukanku ba zan kyale ku ba har kai”


Ya karasa yana nuna Abdallah. Abdallah ya masa wani mugun kallo.

“Look at you fool sai na nuna maka baka isa da Halima ba trust me.... ”


Ahmad be sake ce masa komai ba ya fice. Abdallah kuma ya hau rarrashin zuciyarsa domin ji yake kamar ya hau Ahmad da duka, Hajiya kan jikinta gaba daya ya gama sanyi jin Abdulhamid yana hannun DSS.


5

______________________


Guess what will happen next....!Yadda kafarsa take taka kasa da karfi ya isa ya isar maka da cewar ransa a mugun bace yake, balle kuma kai arba da kyakkyawar fuskar nan tasa wacce ta koma kamar bakin hadari idanuwansa gaba daya sun gama canja kala daga fari zuwa ja. Wani irin nishi yake irin wanda bacin rai ya dannewa numfashi, gumi kawai ke karyo masa daman can haka yake idan ransa ya bace sai gumi da dannewar numfashi.

Tare da barrister suka isa gurin motar, sai ya kai hannunsa ya bude gidan baya inda aka saka Halima, hannunsa ya kai ya taba fuskarta zuwa hancinta dan tabbatarwa idan tana raye, tabbas yaji tana numfashi sai dai kana kallonta kasan bata cikin hayyacinta.+


“Wai hula suka saka mata”


Barrister Nuhu ya fada yana tsaye bayan Ahmad, dagowa Ahmad yai ya kalleshi da wata irin murya marar dadi saurari yace.

“Barrister ka shigar da karar matar nan da dan sandan da yai mata wannan abun, zan kaita asibiti yau yau nake son ka fara komai, ba zan iya yafewa ba, ba zan iya kyale wannan abun ba”1


Yana fadar hakan ya zagaya zai shiga motarsa sai ga Inna da Husna sun iso.

“Mun gode Allah ya saka da alheri”


Be iya amsa su ba sai kawai yace.

“Asibiti zan kaita yanzu, asibitin Dr Nura za ku iya samun mu a can”


Yana fadar hakan ya bude motar ya shiga, yai mata key, kamin ya isa asibitin ya sake kiran wayar Halima duk da yasan bata hannunta amman yana son magana da Hafiza ne, akai sa'a wayar na hannunta domin ringing daya ta dauka.


“Hello, ke ce kanwar Lims ko?”


“Eh”


“A gabanki abun ya faru?”


“Eh komai a gabana akai, Mama ta hanani binsu ne can station din, baka ga wulakancin da sukai mata ba har waje suka fita da ita ba Hijab sai da na bita na saka mata mutane sai kallonta suke kamar ta yi sata, tun cikin gida ma yar sandar guda ta fara marinta”3


Juyawa yai ya kalleshi Halima wacce idonta ke rufe sannan ya ce.


“Zan tura miki number wani barrister amman ki kira shi da line ki ba line Lims ba ki fada masa duk abunda ya faru zai shigar da kara akan case din”3


“To ina ita Halima take?”


“Gata nan zan kaita asibiti”


Yana fadar hakan ya kashe wayar, ya sake waigawa ya kalli Halima, sai duk yaji tausayinta ya kara kamashi, da wani irin karfi ya daki sitiyarin motar, yana wani irin nishi kamar zai ciro zuciyarsa daga kirjinsa.

Yana kunna kai cikin asibitin wayarsa tai ringing kamar jiran kiran yake yai picking da sauri.

“Barrister”


“Na'am Ranka yadade ina son na san cewar shin abunda ake zarginta da shi, bata aikata ba din gaske? Kuma bata da hannu a batan mutumen?”


“Bata da alaka da shi mutumen yana hannun DSS, bata da hannu a batan sa ko wata mu'amala da shi”


“To ya akalarka take da ita?”


Juyawa yai ya kalli Halima sannan ya amsa ma Barrister.


“Matata ce....!”5


“Za a shigar da karar a madadinta ne ita kanta ko kuma....!”


Shiru yai for a moment, yasan dai kotu ba a mata wasa, kuma shi din be riga ya auri Halima ba, idan aka shigar da sunan shi din mijinta ne kotu ta gano babu auri a tsakaninsu zai iya kawo musu matsala, how he wish ace ya aureta, ya tabbatar da yau Hajiya ko Abdallah basu yarda ko yatsa sun daga sun nuna mata ba balle har su saka a kamata.


“A madadinta zaka shigar, mutanen nan sun wulakanta ta Barrister i want them to regret, su nemi yafiyarta da kansu kuma kotu ta yanke musu hukunci so that's su san ita ma din mai matarba ce, har marinta sai da yar sandar tai kanwarta ta fada min komai, zan tura mata number ka zata kiraka ta maka bayanin komai, an ji hular da suka saka mata ko criminal sai wanda ya kai kololuwa ake yi ma haka, it's just like plan sun tsara kasheta ne kawai Allah be basu sa'a ba”


STORY CONTINUES BELOW

“Karka damu za ayi duk abunda ya dace”


Ya sauke wayar daga kunnensa daidai lokacin da ya isa harabar asibitin, sai da yai parking a emergency sannan ya fito yana kiran wayar Dr Nura, sai kuma yai rashin sa'a Dr baya cikin asibitin a lokacin sai dai ya saka ayi mata duk wani abu daya dace kamin ya iso. Gurin Ahmad ya samu ya zauna ya jimke hannunsa ya dora a saman bakinsa yana wani irin kashe ido zuciyarsa sai tafarfasa take.

“Sokon banza wawa”


Ya furta tunawa da kalaman Abdallah da yai.

“Daga ganin matar nan yayanta duk ba na albarka ba ne”1


Ya mike tsaye yana jin wani irin tsanar Hajiya da Abdallah, daman can ya tsani Abdallah tun abunda ya faru a kamfaninsa wanda matar Abdallah tai yi ma Halima wulakanci.

“Saboda suna ganin bata da gata kowa ya kwaso hararsa sai ya zuba akanta”


Ya fada yana safa da marwa a gurin. Dr nura be dauki dogon lokaci ba ya iso gurin ya shiga bata taimako da kansa.

  Inna na isowa Mama ma ta iso tare da kanen mahaifin Halima, kana ganin fuskarsu kasan hankalinsu a tashe yake. Dukan yadda Ahmad yajin zafin zuciya sai ya dannen shi yana kokarin kwantar musu da hankali.

“Ku kwantar da hankalinku, zata samu sauki likita yana ciki yana dubata”


Mama ta gyada kai hawaye na sauko mata.1

“Dukanta su kai?”


Inna ta tambaya.

“Ban sani ba tukuna sai likitoci sun gama bincike su”


After like 40 minutes Dr Nura ya fito daga dakin ya nufo inda suke. Ahmad sai kallonsa yake ya kasa tambayar komai.

“Ba wata matsala a yanzu nan da awa uku zata farka”


A hankali Ahmad ya cikawa bakinsa iska ya busar, ya Lumshe ido ya bude sannan ya mike tsaye ya bi bayan Doc Nura. Mama da Inna da Husna kuma suka nufi dakin da aka wuce da Halima.

“Ka tabbatar babu wata matsala Doc”


Bayan sun shiga office din Ahmad yake tambayarsa domin gani yake kamar ya boye ne ganin iyayenta. Sai da Doc Nura ya zauna sannan ya amsa masa.

“Babu wata matsala, abunda aka buga mata akan ne ya mata nauyi shiyasa hankalinta gushewa, amman babu wani matsala”


Ba zai iya zuwa dakin ya zauna ba bayan Mama da Inna ya san suna ciki kuma zuciyarsa ta ki aminta ya tafi ya barta cikin asibitin sai kace bata da kowa ko kuma bata san kowa ba, so he decided ya zauna a office din Doc Nura yai jiran awanin da Doc yace zata farka, da kansa ya kira Hajiya sanin cewar zata kirashi idan an yi magariba be dawo gida ba.


“Hajiya yau ba zan dawo gida da wuri ba”

“Why?”


“Lims ta samu matsala ne”1


“Wacece lims?”2


Runtse ido yai ya bude sai a lokacin ya tuna da Hajiya fa yake waya, duk da ba kunyarta yake ba domin ta zama kamar friend dinsa amman duk haka ita bata san yana kiran Halima da Lims ba duk kuwa da irin yadda sunan da yai mata ya bi bakinsa, duk da haka be kamata ya fadi haka a gaban Hajiya ba.

“Halima i mean”


“Subhanallahi matsalar me ta samu?”


“Kanta ya bugu da wani karfe muna asibiti yanzu haka, so ba zan bar asibitin ba sai ta farka”


“Allah sarki, babu matsala Allah ya bata lafiya”


“Amin thank You Mom”


“Se ka dawo”


STORY CONTINUES BELOW

Ya sauke wayar yana murmushin jindadim yadda Hajiyarsa ta amince a take ba kamar yadda take masa ba a da, ko kuma dai dan yana Halima ne oho.HALIMATU POV.

Ba zan iya kiran bachin da nai da suma ba, ba kuma zan iya cewa ban suma ba, sai dai abunda na sani hankalina ya bace na dan lokaci a lokacin da aka saka min abun da, sai dai ina jin hayaniyar da suke kamar cikin mafarki kuma kamar a wata duniyar, har dauko ni da akai aka saka ni a mota zuwa asibiti har shigowa asibiti duk ina ji sai dai ba ji irin na mai rai ba kuma bana iya bude idona balle nai motsi, hakan ne ya tabbatar min da ba suma nai ba domin wanda ya suma baya sanin abunda ke kansa, sai dai daga lokacin aka suka min allura sai hankalin nawa ya tafi ban farka ba sai da aka sauko daga sallah magariba.

Na farka cikin rashin kuzari yawun bakina ma ba dadi kamar wata mai ciki, ba na wahala ne kawai ba wata kila har da yunwa domin ko karin safe ban yi ba.

“Sannu Halimatu”


A hankali na daga kai na kalleta wacce ita kadai ce a dakin, sai ya gyada mata kai alamar gamsuwa, sannan na maida idona gurin kofar da aka turo. Ahmad ne ya shigo hannunsa rike da ledodi tun da muka hada ido yake sakar min murmushi har ya aje ledar yana fadin.

“Ga kayan marmari na gani a gate na riko muku”


“Allah ya saka maka da alheri”


“Amin, ya jikin nata?”


“Al-hamdulillah yanzu ta bude ido”


“Okay, Baba babu ruwan shayi ko?”


“A a babu su yanzu kam, ga dai tuwo nan da aka kawo”


“Shayin dai zai fi, ko zaki kira gida ki ce a kawo mana ruwan zafin in yaso sai na karbo kayan tea nan waje, Doc yace idan ta farka a bata tea”


Da to Inna ta amsa sannan ta tashi ta fita daga dakin, kamar jira yake ta fice sai ya nufo gadon da nake kwance ya kwanto da fuskarsa daf da tawa.

“Na ji tsoron sosai da na ganki a galabaice dazun, na dauka ba za ki yi saurin farkawa haka ba, ya jikin naki”


Kamar mai rada yake min magana sai kallon cikin idona yake kamar zai cinye ni, kai na gyada masa alamar na ji sauki.

“Wani gurin na miki ciwo?”


Na girgiza kai.

“Can you talk?”


Nan ma dai kan na gyada.

“Then say my name”


“Ahmad... ”


Na fada cike da nauyin baki, murmushi ya sakar min.

“That's my girl”


Ya fada yana kara kashe murya sannan ya mike tsaye ya nufi inda nake zaton bandaki ne ya bude ya shiga sai gashi ya fito rike da karamin bokoti ya nufo inda nake, sannan ya dauko daya daga cikin ruwan gorar da suke saman drawer wadanda nake kyautata zaton shi ya siyo su ya bude daya.


“Za ki iya tashi ki wanke bakinki?”


Haka nan na unkura ba dan ina jin karfi ba na tashi na zaune na tara hannuna yana zuba min ruwa ina kaiwa a baki n kuskure na zubar, sannan na soma wanke fuskata.

“Ji yadda suka saka pretty face din nan na ki ya rame”


Ni dai ban ce komai ba, ko ban duba madubi na san na rame domin na ji fuskar tawa ta zurma. Yana aje ruwan ya dauki bokitin ya maida sannan ya nufi kofar fita yana.

“Bari na fara yin magana da Doc kar na baki wani abun ya saba doka”


Da kallo na bishi har ya fice kofar bata rufe ba aka sake turo ta Mama ta shigo tare da Mama Ramatu.


STORY CONTINUES BELOW

“Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode maka”


Shine abunda take fada har ta iso inda nake ta zauna bakin gadon tana kallona fuskarta da murmushi.

“Ya karfin jikin Halimatu?”


Cewar Mama Rahamatu sai na amsa mata da Al-hamdulillah.

“Kina jin wani ciwon a yanzu?”


“A a”


Na fada ina kallonta babu komai a cikin idanuwa sai son mahaifiyata da kaunarta. Likitan nan ne ya shigo tare da Ahmad ya tambaye ni jiki na fada masa bana jin komai sannan yace a bani abinci na ci sannan a bani magani. Ahmad da kansa ya dauko ayaba ya mikawa Mama yace ta ba ni, ita kuma ta rika barewa tana saka min a baki ina taunawa a hankali har na koshi.

“A saka miki tuwo?”


“A a cikina ya cika”


A nan ma shi ya ballo maganin ya mikawa Mama ta bani na sha.

“Mama rumgume ta, idan mutum ba shi da lafiya yana jindadi a rumgume shi”


Ya fada yana kallona, Mama ta amsa da to tana dan kallonsa kamar yadda nima nake mamakin maganarsa sai kace wata karamar yarinya zai ce a rumgume ni, Mama ta kara haurowa kan gadon taja ni jikinta ta rumgume, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba sai na ji natsuwa ta sauko min har na Lumshe ido.2

“Am Baba daman ina son na fada muku wani abu, na yi magana da lauyana zai saka kara akan abunda akai wa Halima so i think ya kamata ku sani”


Ba shiri na bude ido na dago na kalleshi kamar yadda Mama ma take kallonsa.

“A a idan su idonsu ya rufe sun aikata abunda suka aikata, mu be kamata mu yi haka ba, ba a taruwa a zama daya, akwai zumunci mai karfi a tsakani, da mahaifin Abdallah da mahaifin Halimatu”


“Amman su basu san da zumuncin ba ne suka aikata abunda suka aikata?”


“Hankali da tunani ba daya ba, kuma ba a biye son zuciya kamar yadda tai”


“Ba ki ga yadda sukai mata ba? Zata iya rasa ranta fa sanadin haka”


“Tun da Allah yasa ba a rasa ran ba hakuri shi ya fi, amman shiga kotu a yanzu zai kara lalata zumunci ne kuma ka jawa Halimatu bacin suna a cikin dangi”


Wayarsa ce tai ringing kamar yana nema sai kawai yai picking call din ya fice daga dakin, a lokacin ne Mama ta dube ni cikin yanayin damuwa tace.

“Karki ba ri a kai matar yayan mahaifinki kotu, ita ma uwa ce a gareki, na sani da margayi yana da rai wata kila da yanzu kina can gidansa zaune yana kula da ke, inda yana raye da duk abubuwan nan ba su faru ba, idan kika bari aka saka Hajiya kotu saboda abunda tai miki Abdallah ba zai taba ganin farinki ba, ko dan shi kadai be kamata ki bari akai Hajiya kotu ba, domin zai kara lalata zumuncin ne, idan hankali ya gushe hankali ne yake dawo da shi, ki masa magana kar ya kai abun nan kotu dan Allah”1


“In-Sha-Allah zan yi magana da shi Mama”


“To Allah ya miki albarka”


“Amin”


Tun da Ahmad ya fita ban sake saka shi idona ba sai washe gari da safe, misalin bakwai da wani abu. A lokacin ina zaune a dakin ni kadai domin ba sa barin kowa ya shigo da safe sai yamma ta yi. Ya shigo hannunsa rike da kwandon dake dauke da kulolin har kala uku dayan hannunsa kuma rike da filas din ruwan zafi.

“Ina kwana....”


Na mika masa gaisuwa sun kamin ya karaso, be amsa ni ba kuma be min murmushin daya saba ba har ya aje kayan.

STORY CONTINUES BELOW

“Ga breakfast in ji Hajiya”


“Ina kwana?”


Na sake mika masa gaisuwa a nan ma be amsa ni ba.

“Ya jikinkin na ki?”


“Al-hamdulillah”


Daga haka be sake ce min komai ba sai ya ciro wayarsa ya shiga dannawa. Kallonsa nai yanayinsa da yadda yai min sai ya sa na ji babu dadi.

“Kai hakuri na ja maka ba.....”


Kamin na karasa ya tari numfashinta.


“Ba ki ja min komai ba, ni na ja miki duk wannan abun daya same ki, ba ina fushi ne saboda abunda ya faru ba, kawai ina mamakin hali irin ba ku ne, taya za a ci zarafin mutum kuma ya hana a bi masa hakkinsa? Su ba su san da zumunci ba ne suka wulakanta ki? Har marinki fa aka ce yar sanda ta yi aka fito dake waje babu mayafi  babu wulakancin da ba su muku ba, kin san abunda nake ji a zuciyata?”


Kai na girgiza masa.

“Babu wanda ya mare ni, kuma ba mu fito cikin gidan ba sai da mayafi, duk wanda ya fada maka tsabanin haka karya yake”


“Kanwarki ta fada min kuma baza tai karya ba, kina boyewa ne kawai”


Shiru nai ina tunani a cikin duka kanena babu wacce zata iya fadar haka sai Hafiza.1

“A ina ka ganta”


“Na kira wayarki ta dauka, ita ta fada min komai”


Na yi shiru domin bana son karyata kanwata a gabansa, ko ba komai gobe ba zai sake ganin girmanta ba, balle har ya yarda da ita.

“Idan hankali ya gaushe hankaline yake dawo da shi, ita ita ta aikata kuskure mu be kamata mu aikata ba, ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin ni ce silar batar danta”


“Amman miyasa ke kadai zata zarga? Ya akai ta san da maganar ma? After na fada miki wa kika fadawa?”


“Saboda bata so na, kuma ta fada tana tunanin na dauke Abdulhamid ne ko kuma na saka an dauke shi saboda zai yi aure, kuma saboda ya ki zama da ni, tana tunanin ni an saka Abraham ya dauke shi saboda na dauki fansa”


“Amman ba ita kadai ba har wannan Abdallah.... ”


“Abdallah ba zai taba min haka ba, i trust him, ba da sa bakinsa Hajiya tai min haka ba, ba zai taba bari ba, balle har shi yai min, kiyayyar da Hajiya take min a yanzu ta samo asali ne ta dalilin soyayyar da Abdallah yake min”


“Miya hana ki aurenshi?”


Ya aiko min da tambayar kai tsaye, kallonsa nai ina kokarin kawarda da hawayen da suke son zubo min.

“ A wacan lokacin Abdallah ya nuna min soyayya ne ta hanyar da be dace ba, shi yake yawan kawo min labarin abunda Aminu yake, yana son na kashe aure na na aure, wanda a musulunce haramun ne, domin Annabi yace baya tare da wanda ya so matar wani, ko ya zuga matar wani dan ta kashe aure ta ko da kuwa shi din zai aureta, a lokacin da aurena ya mutu, sai Abdulhamid ya fito so na bayan kuma Abdallah yana so na, amman shi Abdulhamid be san Abdallah yana so na ba, Abdallah kuma be taba sanin cewa na yi soyayya da Abdulhamid a lokacin da ina budurwa ba. A lokacin ina jin tsoron abunda ya kashe min aure kar na sake fada mishi, da kuma ganin da nai Abdallah yana so na tun ina a gidan wani sai nake ganin kamar idan na aure shi, aure ba zai dade ba hakan yasa na take aurensa na auri dan'uwansa, daga lokacin sai mahaifiyarsa ta fara kina, ashe Abdallah ya fada mata yana so na, sai take ganin kamar ni na ja hankali Abdulhamid ne na aureshi saboda na batawa Abdallah, saboda babu wanda ya san mun yi soyayya da Abdulhamid saboda a boye mu kai a wacan lokacin ya hana na bayyana soyayyar, wanda ban san dalilin hakan ba wata kila saboda ba shi da lafiya ne yana tsoron soyyayyar mu ta bayyana sirrinsa, a jiya ina jin tana fadar cewar na lalata zumuncin da yake tsakanin Abdallah da Abdulhamid, ban san iya abunda ya shiga tsakaninsu ba, kuma na san saboda ni ne, komai bana yinsa daidai, yanzu ma idan aka kai Hajiya kotu saboda ni Abdallah ba zai jidadi ba”

STORY CONTINUES BELOW

Dan murmushi yai ya tabe baki


“Kamar dai Abdallah nan yana da muhimmanci a gurinki”


“Yes, ya taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon, ya rike yayana kamar nasa a lokacin da ubansu ya guje su, kuma mijin dana aura wato Abdulhamid ya nuna min baya bukatarsu, duk son da Abdulllah yake min be tana neman yin lalata da ni ko sau daya ba, mi zai saka ba zai zama mai muhimmanci a gurina na”


“Duk da haka dai abunda mahaifiyarsa tai miki ba ki cancanci yayanta ba, kuma ya nuna karara bata kaunarki, domin abunda tai miki makiyi ne kadai zai iya yinsa, zai iya zama silar ajalinki da baki farka ba a yanzu yaya kenan? And tell me taya za ki auri yaya uwa daya uba daya twins ya sake ki, yanzu kuma ki yi tunanin auren kane? A addinance ba haramun ba ne, amman a al'adance haramun ne, so pls ki manta da zancen auren Abdallah for now”


Da kanshi ya tashi yaje ya hada min tea ya miko min, har na karba zan kai baki sai yai saurin dakatar da ni.


“Tsaya tsaya muji”


Ya karba ya kurba kadan.

“Yana da zafi ba ri ya sha iska”


Ya fada yana kura min ido.

“Ji nake kamar ace da aurena abunda nan ya faru, zan kyale Hajiyar for now, amman shi dan sanda da yar sandar da ta mareki sai na hukunta su”


Kallonsa nai na dauke kaina.

“Akwai damuwa karara a fuskarki”


“Idan na ce babu damuwa a tare da ni a yanzu na yi karya”


“Don't be afraid i will by your side, you will be safe”


Kallonsa nai sai ya sakar min murmushi.

“I will surprise you idan kika ji sauki kika koma aiki, a gaban kowa da kowa and i hope you won't disappoint me”1


Ya fada sound so serious.

ABDALLAH POV.

A yanzu Abdallah yana jin ba shi da babban makiyi kamar Ahmad, daman can Allah be hada jininsu ba balle kuma yanzu da ya zama sanadin tashin ciwon Hajiya sakamakom fada mata da yai Abdulhamid yana gurin Dss, ya san duk wanda dss ta kama yana aikata wani mugun abun ne, be tana zargin dam'uwansa da aikata wani mugun abu ba, a yanzu ma ba zai iya zarginsa ba domin ba a fadi abunda yai ba, be zama lallai dan yana abota da Abraham ace aikinsu daya ba, sai dai kalamar da Ahmad ya fada cewar shi ne sanadin zuwansa dss din ya fi komai tsaya masa a rai.

 

Lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya yana kallon mahaifiyarsa wacce ke kwance an daura mata mata drip a hannu sai sharar bachi take. Mikewa tai tsaye yana kallon dakin kamar wani bakonsa sai ka ce ba dakin Hajiya ba. Sam be jidadin abunda Hajiya tai ma Halima ba da ya san haka za tai da be fada mata komai ba, a dayan bangaren kuma yana tunanin ko a wane hali yanzu Halima take ciki? Har ya dauko wayarsa kamar ya kirata sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ajiyar zuciya ya sauke a hankali zuciyarsa na sosuwa da kalaman da Ahmad yai masa, yana mamakin wai a yau har wani zai nuna masa isa da Halimatu,shi ko zai nuna masa cewar be isa ga Halimatu ba, dan murmushin takaici yai.

“Mahaukaci, marar tunani, mayaudari”


Ya furta murya kasa kasa, yana jin a ransa ko da shi ba zai auri Halimatu ba tun da Hajiya tai musu shamaki to ko Halimatu bata dace da auren banza mutum kamar Ahmad ba, mutumen daya gama wulakanta ta yai mata kazafin kisa, yanzu kuma ya dawo yace son ta yake dan bashi da kunya. He know shi kadai zai aureta ga rike tsakani da Allah babu wata kyama, babu tunanin komai a ransa, ba dan Hajiya ta shiga tsakaninsu ba wata kila da yanzu ya aureta ta haifa masa da namijin da yake ta mamari, yake ganin kuma zai iya samu idan ya aureta domin ita ta haifi both maza da mata ba kamar matarsa Suwaiba ba da ke haihuwar mata.5


***   ***  ***

Wasa wasa aka kwashe sati daya kullum sai an sakawa Hajiya drip duk da bi ta rame kamar ba ita ba. A ranar hankalin Abdallah ya tashi sosai ganin halin da mahafiyarsu take ciki, kusa kullum a gidan yake wuni domin shi yake kuka da ita, a yau ma sai da ya tabbatar bachin Hajiyarsa yayi nisa sannan ya kama hanyar gidansa da tunani kala kala.

Yana isa harabar gidan su Inteesar suka zo da gudu suka tare shi kamar yadda suka saba, sai ya fito daga motar yana murmushin karfin hali ya rika hannunsu suka nufi cikin falon.

Ko da ya shiga Suwaiba na zauna  a falon, ta kashe dauri sai kamshin turare take.

“Sannu da zuwa”


“Yauwa”


Ya amsa mata cikin yanayin da ke nuna damuwarsa karara.


“Ya jikin Hajiya?”


“Al-hamdulillah”


Ya kalli Plasma da take kallo kamin ya sake kallonta yace.

“I think ya kamata ki koma can gaba daya, saboda kula da Hajiya”


Ta dan wara ido.

“Ah Doctor Idan na koma can to yara fa?”


“Za ku koma can har su in yaso driver ya rika kaisu school daga can, idan ta samu sauki sosai sai ki dawo”


Juyar da Fuska tai gefe ta bata rai alamar ita akam fa baza tai ba.

***      ***      ***

Duk wani shiga da fita babu irin wanda Abdallah ko yan'uwansa ba su yi ba amman shiru labarin Abdulhamid har suka fara zargin ko dai an kashe shi ne.

A week later in the evening aka dawo da su Gusau bayan hukumar ta bada umarnin rufe duk wani guri da Abdulhamid da aikinsa Abraham suke saida motoci, sakamakon kamasu dan akai da safarar makamai, ga kuma fashi da makaminda Abraham ke yi ta karkashin kasa bayan aikin police din da yake, da bakinsa ya fadi mutane da suka yi wa ciki har da makocin su Abdulhamid wanda babban dan siyasa ne, suka kashe a lokacin da suka je unguwar a ranar da ya so ya kashe Abdulhamid, ba a dawo da su gida ba sai da suka fadi komai ciki har da yadda suke shigo da makaman da kuma wandanda suke kaiwa da inda suke karbowa.

Idan na ce zan iya fadar kulawar da na samu a gurin Ahmad da mahaifiyarsa na yi karya, domin a kwanan da nai asibiti kullum sai na yi bachi yake tafiya gida, mahaifinyarsa kuma sai tavaiko mana da abinci safe, rana da na dare, sau uku tana zuwa duba ni asibiti, a duk lokacin da ta zo tana yi min kalaman da suke kara min kimarta a idona kuma su kara kwantar min da hankali. Tana yawan fada min cewar nai hakuri, kuma na cigaba da yarda da kaddara kamar yadda nake, kar nai tsammanin Allah ba zai sake jarabata ba, kuma kar na tsammaci sake samun wata kadarar a gaba, na kyautata zaton kuma nai ta addu'ar, haka zata zauna tai ta fira da Mama ko Inna kamar ba matar babban mutum ba ko kuma na ce uwar babban mutum, da aka salleme mu a asibitin ma sai da ta kira ta ji muryata.
Yau kam na kara yarda da maganar mutane da suke cewa duk abunda ya baka tsoro wata rana zai baka tausayi, duk kuma abunda ya baka tausayi wata rana zai baka mamaki.
Idan nai na hada kalubalen rayuwar da na fuskanta da na Aminu da Abdulhamid, sai na gane cewar ni din ban ga komai ba, domin a halin yanzu Allah ya min mafita kuma ya wanke ni, wani kalubalen a farkon rayuwa yake wani a karshe, wani a tsakiyar rayuwarsa, ba duka arziki ne na halal ba, na kuma ko wane arziki ne na haram ba, ba duka talauci ne kunci ba, ba kuma duka kunci ne takauci ba, saboda ina cikin takauci ba shi yake nufin ba zan jidadi rayuwa ba, idan kuma ina da arziki baya nufin aki jarabbatata.
Ta wani bangaren na kanyi mamakin abunda ya kai Abdulhamid aikata wannan mummunan abu, ko da yake ko wane bawa be isa ya wuce kaddararsa ba. Kamar yadda ban wuce komai ba sai da ya same ni. Ba ni kadai nake cika da mamaki ba har da Mama da Inna, da duk wani wanda ya san waye Abdulhamid, mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, dole kowa yayi mamakin wannan abun, wata kila Abraham ne yaja zuwa ga mummunar rayuwa, wata kila kuma shi yaja Abraham din, gaskiyar abun yana a tsakaninsu sai kuma bincike idan ya tabbatar.+
Dago kaina nai daga kallon wayar Hafiza da nake wacce ke dauke da hotunan su Abdulhamid, da Abraham da wani wanda ban wayance shi ba, an saka musu handcuffs, police na tsaye a bayansu an jarida kuma nata aikinsu. Na mika mata wayar ina fadin.3
"Abdulhamid ya ban tausayi"

"Tausayi? Tausayi fa kika ce Halima? Haba mutumen daya sakeki har wani tausayinsa zaki ji, ke dai Wallahi kina da matsala"1

Na yi shiru domin na san ba zata taba fahimta ba, sai dai abunda ya fi tsaya min a rai shine shin Abdulhamid ya san cewar Abraham ne yai min fyade? Da saninsa akai? I need to know, na fada ina sauke ajiyar zuciya a hankali. Na unkura zan tashi kenan sai ga su Namra sun shigo da gudu kowanensu rike da leda a ko wane hannu, ledan kuma ba karama ba irin babbar ledar nan ta super market.
"Momy Guess what...?"

Aiman ya fada yana wani irin murmushin jindadi.
"What it's?"

Na tambaya da mamaki a fuskarta.

"Wannan Boss din naki, baban su Baby Namra ne ya dauke mu daga school ya je da mu wani katon shago yace mu dauka duk abunda muke so"

Wannan karon Adnan ne yake magana, sai Namra ya kyalkyale da dariya.
"He say we should called him Daddy, wai yana jiranki a waje yana can cikin mota"

Kana kallonsu kasan suna cikin farinciki, jin cewar yana waje yasa na dauki Hijabina na saka na leka kofar gidan, sai ko na ganshi daf fa kofar ya faka motarsa. Ganina yasa ya sauke gilashin motar yana miko min murmushi.

"Lims how far"

Dan murmushi nai nima

"Mun gode Allah ya saka da alheri, kana ta dawainiya da yara"

"Bude back seat din nan akwai na ki"

Ya fada yana dauke fuskarsa kamar baya son nai masa godiyar. Na yi kamar yadda ya umarta na bude gidan baya na dauko katuwar leda na fito da ita.
STORY CONTINUES BELOW
"Na siyo miki turare duk da ban san choice dinki, amman ni nafi son irin wannan wanda na siyo miki, na mata ina son na ji mace ta saka shi"

"Na gode Allah ya saka da alheri"

"Ki dai shirya komawa aiki on Monday, tun da lafiya ta samu sosai"

Na gyada masa kai sannan na ce.
"In-Sha-Allah, amman dan Allah ina neman wata alfarma"

Kashe motar yai gaba daya, ya fito daga ciki ya zagayo inda nake ya saka hannayensa duka biyu aljihu yana min wani irin kallo wanda da ace akwai wani kusa da ni da sai na ji kunya, domin idonsa ya sako min sosai kamar zai cinye ni.
"Name it"

Ya fada kamar mai rada. Kasa nai da kaina ina wasa da ledar da ke hannuna.

"Lims..... "

Ya kira sunana cikin wata irin siga wacce ta saka sigar jikina tashi, da na kalleshi kuma sai na kasa jure irin kallon da yake min.
"Okay Babe mu shiga mota sai ki fada min idan ba zaki iya fadi in public ba...."1

Idan ban yi kuskuren fahimta ba kamar yace Babe right? Mistake yai ko kuma da gangan ne?5
"You know bani da wannan hurumin da zan rumgume ki na kallashe ki na tambaye ki abunda kike so, so please just tell me idan ba so kike ki wahalar da zuciyata ba"1

The way da yai maganar kamar yana rokona ta shigar lallashi akan na fada masa abunda ni nake da bukata.
"Daman ina son na tambaya ne ko ana barin mutum ya ga Abdulhamid"

Na fada cikin tsoro da fargaba, runtse ido yai ya bude ya sake kallona.
"Abdulhamid...."

Ya maimaita sunan.

"Why?"

"Akwai tambayar da nake son masa, ina son naji amsar daga bakinsa ne kawai"

"It's necessary?"

Na yi kasa da kaina, sai yai saurin matsawo kusa da ni.
"Okay Okay Okay... Kin san irin criminals din nan ba kowa ake barin yana shiga ganinsu ba, saboda gudun abunda zai faru, tun da suna tare da miyagun mutane ne, but idan kina son ganinshi i can talk to my friend sai yai mana hanya ki ganshi, idan ya bada date zan fada miki sai ki shirya na kai ki"

"Thank you so much"

"No Lims dadi nake ji idan kika bukaci wani abu nai miki, so thank you so much for the offer"

Ya fada sound so serious, sannan ya zagaya zuwa side dinsa yana kallona tare da fadin.
"But make sure ba wani kalma mai dadi za ki fada masa ba, ba zan jidadi ba idan kika furta wata kalma mai dadi ga wanin Ahmad, saboda Ahmad yana da kishi sosai idan yana da da dama ma, ko a unguwarku ba kowa za ki yi wa magana ba i swear"

Ya bude motar yana min murmushi.

"Take care of yourself"

Sannan ya shige motarsa yai mata key ya bar ni tsaye a gurin ina mamakin kalamansa. Yace Baby at first, and second to the last sentence ya fadi wasu abubuwa da ban gane ma kansa ba, i thought ba soyayya muke ba, but why yake irin wannan behaviors din? Na san ko bw fada min ba abunda yake min da kuma kulawarsa akaina tana nuna damuwarsa ne, kuma akan damune ne da abunda ake so, ko kuma ya zama muhimmin a rayuwa. Sai dai ni din a yanzu ban shirya ba ban kuma san ranar da zan shirya din ba.
Ko da na koma cikin gidan an tarar sun bude abubuwan da ya siyo musu suna ci, sai labarin abubuwan da suka gani suke badawa, ni kuma an zauna saman tabarma na bude ledar, kananan cakes a ciki sai wata kyakyawar sarka mai ruwan zaiba, turare ya fi yawa sai man shafi cream and lotion, da shower gel, kana ganinsu kasan masu tsada ne.
Ina jin yadda kannen suke kamgama shi ni dai bance komai ba, har suka ci suka shude sannan na dauki kayan bayan na basu cake din na nufi daki na aje.
Kamar wasa da dare Ahmad ya kira ni a waya ya fada min crwarna shirya gobe misalin ten zai zo ya dauke ni ya kai ni can abokinsa yace zai bar ni na shiga nai magana da shi, a lokacin kuma dai na ji kamar bana son zuwan wata zuciyar tai ta raya min cewar miyasa na bukaci haka? Ban kwanta ba sai da na fadawa Mama abunda nake da kudiri akai.
STORY CONTINUES BELOW
"Amman dole ne sai kin yi magana da shi? A iya tunani na Halima, ya kamata ki nisanta kanki da yayan Hajiya, ba nuna nufin ki yanke alaka ba, a a ki yi nesa nesa daga duk wani abu da zai iya sakawa a zarge ki, iyakar cin mutuncin da nuna kiyaya Hajiya ta yi miki shi"

"Na sani Mama kawai ina son na masa wata tambaya ce, wacce nake son amsar ta daga bakinsa"

"To Allah ya tsare, tare za ku tafi da Ahmad din?"

"Eh In-Sha-Allah"

"To yayi kyau"

Shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleni tace.
"Ba zan matsa miki ki yi aure ba, kamar yadda ba zan hana ki sauraren kowa ba, sai dai duk wanda kika san ba aurenshi za ki yi ba, to ki sallame shi da wuri ba sai yayi ta wahala a kanki ba"

Ko bata fito fili ta fada min ba, na san Mama tana magana ne akan Ahmad kuma tana da gaskiya, ya kamata na dakatar da shi daga abubuwan da yake min ko ya fara min, kar abun yai nisa ya zame min wata sabuwar matsala.
Kamar yadda ya fada min zai zo da ten ya dauke ni, sai nai gaggawar yin duk wani abu da nake kamin lokacin na sallami yarana suka tafi Islamiyarsu kasacewar yau Sunday suna zuwa makarantar safe ne, sannan ni kuma na shiga nai wanka na shirya cikin bakar abaya, na yafa farin veils karama wanda ya tsaya min iya wuya, ban shafa komai a fuskata ba bayan powder sai dan man baki dana goga, na feshe jikina da turaren da Ahmad ya akwa min jiya, turare ne mai dadin kamshi ina jinsa a gurin manya mata idan na shiga buki ko office.
Sako ya turo a waya cewar yana waje yana jirana.
"Hey Beb ina jiranki a waje idan kin shirya"

Bayan na karanta sakon na samu kaina da faduwar gaba, ina ta jin tsoro zuwa bayan kuma ni na bukaci haka, sai da na sanarwa Mama sannan na fita ina addu'ar fita daga gida. Ina fito daga cikin gidan ya sauke gilashin motarsa yana kallona har na karaso, da kansa ya fito ya bude min motar ni kuma ban shiga ba sai da na fakaici idon mutane, bayan na zauna ya maida motar ya rufe sannan ya zagayo side dinsa ya rufe gilashin motar yana kallon.
"Kin san Allah? Da kika fito daga gida na hango ki ji nai kamar naje na rumgume ki? And the way you're walking wow Ma-sha-Allah"

Na yi murmushi ina kallon yadda black suit din da ke jikinsa yai masa kyau sai mu ka yi anko kamar na fada masa nima bakin kaya zan saka. Ya bata minti goma a gurin baya aikin komai sai kallona can kuma ya shaki kamshin turaren da ke jikina ya lumshe ido, kamin yai ma motar key mu kama hanya. Kamar wacce tai masa maganin kallo haka ya saka min ido yana ta kallona yana murmushi kamar ba driving yake ba, har tsoro na rika ji kar ya mu yi accident. Mun yi tafiya mai nisa sosai sannan muka isa gurin daga ba a bar mun shiga cikin ba sai da abokin nasa ya fito, the way da abokin ya rika min magana sai na fahimci cewar Ahmad ya fada masa cewar ni matarsa ce wata kila, domin a cikin kalamansa har da zancen wai mijina yana so na sosai duk yabi ya dame shi shi dai matarsa matarsa. Kallona kawai Ahmad din yai ya kashe min ido yana murmushi, can kuma muna sake hada idon sai ya sake kanne min ido daya ya leko da halshensa kadan yai min gwalo still yana murmushi.
"Gaskiya Ma-sha-Allah ka yi dace mata, Allah...."

"Na sani, zamu iya shiga ciki?"

Tun kamin mutunen ya karasa Ahmad ya katse shi yana hade rai kamar ba shi ba. Dariya mutumen yai ya juya muka nufi cikin gurin, nesa da ni Ahmad ya tsaya dan bani damar yin sirri, ni kuma na karasa ciki na zauna a gurin da aka tanada, ta ko'ina akwai security amman hakan be hana ni jin tsoro ba, gabana sai faduwa yake, duk bayan minti daya sai ya juya na kalli Ahmad sai ya dago min hannu ya aiko min da sakon murmushi. After like 14 minutes aka fito da Abdulhamid daga shi sai vest da gajeren wando, gaba daya ya canja, daman can ba jikin ne da shi sosai ba sai ya kara ramewa fuskarsa tai kamar wanda ya shekara be ci abinci ba. Har ya zauna a kujerar dake facing dina be kalleni ba.
Yana ta murza wuyan hannunsa, tsakanin ni da shi sai aka rasa wanda zai fara yi ma wani magana, sai da na sake juyawa na kalli Ahmad ya dago min hannu yai min murmushi sannan na ji karfin guiwa fara ambatar sunansa.
STORY CONTINUES BELOW
"Abdulhamid...."

"Miyasa kika zo nan?"

Na tari numfashina ba tare da ya kalleni ba.
"Kin jidadin abunda ya same ni ko?"

A lokacin ne idona ya soma cika da hawaye.

"Mi zai saka na jidadi? Ko da ban san ka ba, ballantana kai din dan'uwana ne jinina"

Sai a lokacin ya dago ya kalleni.
"Ina son nai maka wata tambaya wacce nake son jin amsarta daga bakinka"

Na hade yawun bakina sannan na ce.
"Miya hadinka da Abraham?"

"Abokina ne more than 11 years, na hadu da shi a Lagos, a lokacin da naje gurin hutu, a hotel din da na sauka daki daya muka zauna a lokacin, kasancewar babu dakuna da yawa a hotel din, kasancewar ana bikin nada sabon sarki a garin, and hotel din da muka sauka kusan duka an kama dakunan ciki kasancewar ta babbar hotel, we share the same room and he is the one da ya biya komai, ya sake min sosai we exchange our numbers, lokaci zuwa lokaci mu kan hadu, some time kuma a waya, saboda shi police ne yana yawo gari gari, shakuwarmu tasa muka fahimcin juna sosai duk kuwa da kasancewar ba Addininmu daya ba, shi ya fara dorani akan sana'ar siyar da motoci, shi ya nada min jari duk da a lokacin ba wai bana da kudin ba ne, kawai dai bana ra'ayin abun ne, bayan mun fara sai ya sake nuna min wannan hayar, ban dubi hadarin da ke ciki ba sai na kalli yawan abunda zan samu, sannu sannu na fara tun ina yi ina jin tsoro har na daina, sai duk irin alakar da ke tsakanina da shi, ba kowa ya san muna abota ba, saboda abu ne da ke bukatar sirri idan aka ga alakar ta yi aminci sosai za a fara zarginmu, that's why idan zamu hadu sai dai mu hadu a sirrice, har Allah yasa ya dawo garin nan da aiki"

Yayi shiru tare da kawardar da fuskarsa.
"Amman ka san cewar Abraham ne mutumen da yai min fyade?"

"Na Sani, ko da Abdallah ya fada min na sani"

Ya amsa ba tare da ya kalleni ba.
"After na rabu da ke, na gano cewar shine saboda ya fada min yasan wandanda suka kashe Alhaji Sama'ila na yaddo, and you told me on that very night suka keta miki haddi, and guess what a wannan daren ya shirya kashe ni ne, saboda babu amana a tsakani, wanda ni ba zan iya hakan ba, shi yana ganin kamar na karbe masa jama'a na fishi samun kudi, domin shi wasu mutanen suna tsoron mu'alama da shi ganin cewar Jam'in tsaro ne, kai tsaye na tuhume sa da cewar shi ya keta miki haddi kuma ya amsa min da cewar yes shine, and now yana neman inda zai same ki ne, saboda kin ci ciki bayan shi be taba kwantawa da mace tai ciki ba, and he already know ni bana da lafiya"

"Amman baka taba fada min ka gano shi yai min fyade ba, baka nemi afuwar kazafin da kai min ba, ba ka wanke ni a idon mahaifiyarka ba"

"Komai ya riga ya lalace Haima, a lokacin na gano cewar Abdallah yana son ki, Hajiya tana kin ki, kuma na san ba zaki tana dawowa a gareni ba, saboda ni ba zan iya komai da mace ba, shiyasa na bukaci boye soyayyarmu tun farko bana son wannan sirrin ya bayyana, gano cewar Abdallah yana son ki shi yafi komai bata min rai, kuma lokaci ya kure Haima komai ya lalace, na kasa yarda da ke na rabu da ke, and silata abokina ya keta miki haddi"

Hawaye ya fito daga idonsa.

"A lokacin ne na gano cewar na rabu da matar da ba zan taba samun irinta ba har na mutu, na rasa komai ba ni da mata ba ni da yaya, babu irin neman maganin da ban yi ba amman na kasa samun lafiya saboda Abdallah"

Ya karasa yana murmushin bakinciki wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, sai ya kalleni.
"You got lucky za ki auri mutunen da zai ba ki abunda ni da aminu muka kasa ba ki.... And the way da ya dage da neman tona sirrinmu i know yana son ki sosai"

STORY CONTINUES BELOW
Waiga nai da zimmar na kalli Ahmad amman sai ban ganshi a gurin ba.
"Ba so na yake, abunda kai min kai da Aminu ya tsorata ni daga son wani ko aure a yanzu, murum data na yarda da shi a rayuwata Abdallah shi kadai nake da tabbacin na zai cutar da ni ba...."

"And you can't marry him...."

Ya fada kai tsaye yana kallona da murmushi a fuskarsa hawaye na sauko masa.
"Ba zai yiyu ki aure ni ba, kuma ki auri twina brother dina, bayan kuma ina raye, Hajiya ba zata yarda ba, hakan kuma na zai kara min komai ba sai tsanar Abdallah, and i know duk yadda za ki so shi ba zaki so shi kamar yadda ni kika so ni ba, I'm your first love i know ko yayana wata rana sai kin ji so a zuciyarki kamar yadda ni ma ba zan iya cire soyayyarki a raina ba, so you can't marry my brother kuma ki rayu da so a zuciyarki, no matter what Abdallah zai baki Hajiya ba zata tana son ki ba, saboda tana ganin kin shiga tsakanin yayanta"

Mikewa nai tsaye sai shima ya mike.
"Ban sani ba ko zan sake ganinki ko a a, ban sani ba ko za su yanke kin hukuncin dauri rai da rai ne ko kuma za su halbemu ne i don't know, but i wish you all the best in your entire life, and I'm sorry for what I did"

A lokacin ne hawaye ya fara sauko min kamar ba gobe, tausayinsa ya rufe ni ya sadakar ya san cewar kashe shi za ayi kenan, maganganunsa suka rika min yawo a cikin kai, cewar ba shi da mata ba shi da yafi komai tsaya min a rai, kasa tafiya nai sai kallonsa nake ina hawaye kamar yadda shi ma ya rika waigena yana kuka kamar ba shi ba. Har na nufo inda motar Ahmad take na bude na shiga ban daina hawaye ba, yana kallona hankalinsa ya tashi.
"Me ya faru? Mi yai miki?"

Kasa magana nai sai kokarin saida hawayen nake, hakan yasa shi fusata ya bude motar sai fita nai saurin riko rigarsa ina girgiza masa kai.
"Be min komai ba"

"Then why are you crying?"

Na yi saurin share hawaye.
"Ba komai"

Kallona yai for a moment sannan ya rufe motar muka kama hanya, sai da muka hau titi ya dauko ruwa ya miko min, na karba na bude ya sha ruwan sosai sannan na rufe na aje. Har muka isa gida ban ce masa komai ba shi kuma be fasa kallona ba, bayan yayi farkin na fita cikin motar.
"Thank you"

Na furta ba tare da na jira abunda zai ce ba na shige cikin gidan, a wunin ranar sai na kasa sukuni cikin abunda nake tunani har da zancen samun lafiyarsa wanda yace Abdallah ne, kamar ya? Shi ya masa wata allurar ne ta zame masa haka? Amman Abdallah ya san da da wannan kuwa? Mi zai saka yayi masa haka?
Kamar ya san ina tunaninsa sai akai sara ka gaba, kiransa ya shigo wayata, sai dai wannan karon kasa daukar wayar nai har tai ringing ta katse sai ya sake kira sannan na dauka. After mun gaisa yace min.
"Abdulhamid yace kin je gurinsa yau"

"Eh"

Na amsa masa a takaice duk da na san ya kira ne saboda ya san dalilin zuwana.

"Okay"

Har zai aje wayar na ce.
"Abdallah zan iya tambayarka wani abu?"

Shiru nai na wani lokaci har sai da yace.

"Ina jin ki"

"Da gaske kai ne silar ciwon Abdulhamid?"

Shiru yai daga can cikin wayar sannan kamin ya aiko min da tambaya.
"Kamar ya?"

"Ya fada min kai ne sila, taya?"

"Magana ce mai tsawo Halima zan na same ki gida daman akwai maganar da nake son yi da ke"

"Ka fada min dan Allah, zuciyata ta kasa yarda kuma na kasa natsuwa"

Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace.
"Abun ya dade tun muna samari ne, na tashi da son yara musamman maza, and Abdulhamid ya san da haka, kamar wasa wata rana muna magana nace masa zan riga shi aure, shi kuma yace ko na riga shi aure ba zan haifi namijin da nake da buri ba, ni kuma na ce masa shi kuma ba zai ma taba haihuwar ba har sai na haifi namijin, and na gano haka ne after Suwaiba ta fara haihuwar Mata, and last barin da tai ma macece, yayi min kofi ne and after that Hajiya ta ba mu maganin kare kofi saboda abubuwan da suke faruwa, na shi ya kare nawa kuma ya rage kaifi that's what i know"

***
( Wannan abun ya faru a gaske, Hasana da Husaina, Husaina tai ma Hassana kofi cewar ba zata taba aure ba, ita kuma Husaina tace mata ko tayi auren ba zata taba haihuwa ba, har yau kuma suna nan da rai sun fara manyanta Hassana ba tai aure ba Husaina kuma bata haihu ba)9

***

Ajiyar zuciya na sauke ina mamakin yadda sukai wa junansu illa.

"Zan zo gobe akwai maganar da nake son yi da ke"

Ban sake ce masa komai ba na kashe wayar, a ranar na kwana da mamakin abun a zuciyata. Sai mafarka da safe kamar wata marar lafiya, haka dai na shiryawa su Amal suka tafi makaranta sannan ni kuma na shirya, yau ma abayar na saka sai dai wannan ash color ce tsabanin jiya da na saka black, sai da nai ma Inna da Mama sallama sannan na nufi gurin aikina kamar yadda Ahmad ya bukaci na dawo aiki bayan hutu daya ba ni wai sai na samu lafiya.
Napep na hau bata sauke ni ko'ina ba sai kofar gate din kamfanin, na gaisa da masu gadin kamar yadda na saba sannan na nufi ciki, a reception ma sai da na tsaya na gaisa da Blessed mace mai kirki da son mutane, sai da ta tambayi abunda ya hanani zuwa aiki kwana biyu na fada mata cewar bana jindadi ne, sannan na wuce na nufi office dina. Ina kai hannu na tura kofar office din gaba daya sai naga kamar ba nawa ba, hakan yasa na dawo waje da sauri na sake kallon kofar sannan na sake shiga, gaba daya an kawata office din da abubuwan kawa kamar gurin taron biki, idanuwana sama na shiga cikin ina ta kallon kyale kyalin da ke saman sai wani kamshin rose ke tashi an kuma jera fulawar rose har saman kujerar da nake zama. Ji nai kamar na taka wani abu mai tsantsi hakan yasa na kalli kasa da sauri sai nai arbar da fulawar rose an yi rubutu da ita cikin mayan haruffa.
*WILL YOU MARRY ME...*

Wani irin faduwa gabana yai, da ni ake ko da wata abunda nake gani a fina fine nake karantawa a litattafai yau shi ne a gabana, motsin da na ji a bayana yasa na juyo da sauri kamar a rikice nai arba da mutum duke a gabana......

Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 9 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...