GOBE NA CHAPTER 7 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 7 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 7 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

GOBE NA CHAPTER 7 BY KHADIJACANDY
               Www.bankinhausanovels.com.ng 
HALIMATU POV.

Ba laifi sai na ji kamar inda aka dawo da ni a yanzu ya fi na farkon dadin zama, domin a can rubuce rubuce ne, a nan kuwa kula da masu shigowa ne kawai gashi sai fira muke tare da sauran ma'aikatan, daya mace ce wacce ta kasance kabila ce sai ni ta biyi sai maza uku, ni kadai ce ba ni da uniform a cikinsu, domin ni tufafin gida ne a jikina.

   Ban yi awa daya a gurin ba aka kawo min wando da riga na kamfanin, irin na sauran ma'aikatan da suke gurin mai dauke da sunan kamfanin, tare da wani dan abu da ake sakawa a wuya wanda ke dauke da sunana sai kuma gurin saka hoto, har ga Allah bana son saka kananan kaya abu ga mai dan jiki balle ni da Allah ya horewa abun duk yadda zan so boyewaba boyuwa zai yi ba, na saka skirt ma suka bayyana balle kuma wando, na dade rike da tufafin ina da tunaninsa sakawa ko akasin hakan, sai dai na san idan har na ce ba zan saka ba zasu iya korata. Ba ni da wani zabi da ya wuce na saka din ai idan ina a reception din babu mai

ganina tunda katon tebur din ya tare ni sai dai idan zan tashi kuma idan zan tashi zan iya canja tufafi ko kuma na saka mayafi. Bandakin kamfani na nufa na canja tufafi sannan na saka hijab dina na fito reception din a lokacin da na tsaya a inda ba a ganina sai na cire Hijab din na cigaba da aikina hankalina a kwance. Wani abun burgewa ashe na wadanda suke reception din har da abincin ake kawo musu da ruwa tsabanin da da sai dai yunwa da kashe ni.

   Mu uku muka je cin abincin tare da blessed da Walid, muna cikin cin abincin yake dauko mana labarin sabon kamfanin da za ake tunanin budewa a wata jihar sai dai suna tantamar garin da za a bude, mun dade muna tattaunawar har nake bayarda shawarar da ace za su yarda da sun bude a Kano domin can ne cijiyar Kasuwanci, ko kuma Jos duba da yanayin garin Walid kuma yace Abuja, a haka dai muka gama cin abincin muka tashi muka koma gurin aikinmu su biyun da basu ci ba suka koma ciki dan cin abincin.

  Ina tsaye a gurin sai ga wasu fararen mutune sun shigo, da fari dai na dauka turawa ne, a take hankalina ya koma gurinsu tun kan su karaso nake ta kallonsu cike da burge domin kusan sai nace ban taba ganin turawa a zahiri ba sai yau, sai dai na lura sauran abokan aikina ba kamar ni suke ba, wata kila sun saba ganin turawa ba kamar ni ba da na zama bakwaya har murmushi nake musu kamin su karaso.

  Ko miye abun burge a farar fatar ma oho sai kace ni din ba fara bace ko da yke nawa farin mai kyau ne, domin na su ba shi da kyau kallo farin yayi yawa har wani kashe ido yake.

  Suna isowa sa abokin aikinki ya tarebe su da yaren turanci su kuma suka masa magana da faransanci hakan yasa na fahimci cewar faransawa ne ba turawa ba kamar yadda nake zato. Hakan yasa na yi kaudin yin musu harbun da tambayar abunda suke bukata a dan abunda na iya na yaren faransanci. A take suka mayarda min da amsa, aiko nan dade ya kusa kashe ni wai ni na magana da wanda ba yare ba kuma ba yan kasa ta ba. Da suka fada min wanda suke bukatar gani wato shugaban kamfanin sai na fadawa Walid shi kuma ya nuna min yadda zan yi na kira na sanar idan bukatar irin haka ta taso, kamin na danna number wanda yace min shi ake fara kira a sanarwa, sai ga Yunus din ya fito daga cikin kamfanin ya tare su da far'arsa har ya basu hannu suka gaisa, sai dai shima na lura be iya faransanci ba kamar dai sauran abokan aikina. Godiya suka min da yarensu na mayar musu da godiyar nima sannan suka bi Yunus zuwa ciki. After like 15 minutes ya fito yana tambayar wai na iya faransanci ne sosai.+

“Gaskiya ba sosai ba gaisuwa kawai na iya sai dan abunda ba a rasa ba, ban iya sosai ba”


“Amman za ki iya kula da su kamin mai fassara mana ya iso?”


“Yes”


“Good zo muje”


Sai da na dauki gyalena na yafa sannan na bi bayanshi, sai dai a yanayin yadda yake tafiya ne yasa nai saurin cin masa duk kuwa da kasancewar ina tafe ina dingishi ne sai muka jera a tare muna tafiya a tare, ba laifi yana da sakin fuska da son magana ba kamar mugun gogan ba, a nan yake tambayar inda na iya yaren faransanci, na fada masa tun a secondary school na yaren yaren sosai lokacin da muna can sai dai shiga FUG yasa na manta da wani abu, ga kuma abubuwa na rayuwa sai na watsar da abun. Sai a lokacin da zamu shiga cikin office din ya bukaci na cire mayafin nawa, hakan yasa ni jin babu dadi wanda har ya bayyana a fuskata.


STORY CONTINUES BELOW

“No ba wani dadewa za ki yi ba, za ki yi tambaye abunda suke bukata ne kawai sai kuma fara gabatar musu da abunda zan nuna miki kamin mai aikinmu ya iso”


“Ba fa komai na iya a faransanci ba, ba zan iya wani dogon bayani sosai ba”


“I know saboda kar mu barsu shiru ne, tun mun zama kurame mu da su”


Ban musa ba na cire Hijab din kamar yadda ya bukata, daman can dankwalin atamfa ne a kai, ga farar riga da bakin wando na kamfani sai ya bada wani kala na dabam, na yi zaton su kadai ne a dakin taron, sai na tarar har da Angry Bird din ya wani shakimce a saman kujera yana ganina ya wani hade rai. Ni kuma na tsaya bakin kofa har sai da Yunus din yai min iso.

  Na shiga ciki na tambaye su abunda suke bukata na sha suka bukaci ruwa kawai, shi ma kuma da aka kawo ba su sha ba, abunka da marar yarda, haka nan dai cikin rashin iyawa na rika dan nuna musu abubuwan da Yunus ya nuna min, wanda suke a katon wani abu mai kamar tv kuma shi ba tv ba, da removed din hannuna na rika nuna musu kalolin zinarin da suke a ciki, domin ya fada min abun nan ja na jikin remote din kawai zan taba su za su rika canjawa da kansu.


  Muna haka sai ga mai fassarar ya shigo, na yi zaton idan ya shigo umarni za a bani na fice sai gashi ya saka ni cigaba da danna remote din shi kuma yana musu bayani da halshen faransancin, ina jin wani abu wani abun kuma bana gane komai, wani abun zai fada ma Ahmad da Yunus abunda suka ce ne sannan ya cigaba da yi musu bayanin,  har akai aka gama Ahmad be ce komai ba, sai aikin tsutsar minti yake, ni kuma ban ma sake kallon inda yake ba. Sai da suka gaisa da shi sannan suka fice tare da mai fassarar, hakan yasa na aje remote din ina jiran a bani umarnin ficewa, amman Yunus din sai karin bayani yake ma Ahmad din. Ni kuwa hankali gaba daya yana gida ga garin ya hada bakin hadari kamar yadda nake hange ta cikin gilashin da ke gafenmu.

“Ranka ya dade zan iya tafiya”


Na fada ina kallon Yunus din a tare suka kalleni daga Ahmad din har Yunus ne.

“Sorry yau mun baki aiki da ba naki ba”


“Babu komai”


Har na aje remote din ina kokarin juyawa sai yace.


“Ta ina za ki bi? Na sauke ki”


Kamin na bashi amsa Ahmad din ya tari numfashinsa sound so serious fuskarsa babu alamun wasa.

“Shi kuma wacan aikin wa zai yi?”


Nikam daman ba shiga motar zan yi ba, hakan yasa kamin ma Yunus din ya bashi amsa na ce wa Yunus din.

“Na gode ranka ya dade zan fi sakewa idan na hau napep”


Daga haka na juyo na fito daga office din ina mamakin irin kiyayyar da Ahmad ke min akan abunda har a gurin Allah bana da laifi domin ban aikata ba, wato yaji haushin da Yunus din yace zai rage min hanya ko waya fada masa ma shiga zan yi oho.

  Da tunanin hadarin na fito hakan yasa ban wani tsaya canja tufafi ba yafa mayafina na dauki kayan na saka riga a handbag dina domin ita kadai zata iya shiga sauran kuma na rike a hannu na bi hanya domin tuni abokan aikina sun wuce har wasu sun karbi duty.

  Ina tafiya aka fara yayyafi ban yi zaton zai yi karfi ba, hakan yasa na kara harama da zimmar kamin ruwan yai karfi na samu abun hawa, da ganin hadarin ba irin wanda idan an fara ruwan nan ba ne a daina, wata kila za a dade a na ruwan.

   Ko da na fita gate babu masu Napep sai achaba su ma kuma kowa da goyonsa, sai gudu suke ni kuma na maida himma sai tafiya nake ina waige waige ko zan samu abun hawan, ban nisa sosai da kamfanin ba aka sako da wani ruwa mai mugun karfi, hakan yasa ni cira kafa har da dan guduna na nufi inda wata yar rufar kwano wacce ke kusa da inda Kabir yake. Babu kowa a gurin hakan yasa na shige rumfar da sauri na fake, domin tuni ruwan ya fara jikani. Sai dai wani abun mamaki duk ruwan nan da ake Kabir na zaune a inda ya saba zama ruwan na duka kansa, ban san lokacin da tausayinsa ya rufe ni, da sauri na aje kayana da jakar hannu a gurin na fita a ciki a rumfar na nufi inda yake cike da karfin hali domin a yanzu kafar ta fi min zafi fiye da dazun. Da fari magana na fara masa akan ya taso ya bar gurin sai na ga yana ta kallona kamar be gane ni ba, hakan yasa na kai hannnu zan riko shi, aiko kamar jira yake sai ya hayayyako min yayi cikina yana zare ido abun be taba, ina baya baya yana cikina har samu sa'ar riko mayafina ya fisge shi gani a gafen titi hakan yasa nai unkurin gudu sai yai nasarar kai mun duka mai shegen zafi, ya kuma rikoni yana kokarin makureni.

STORY CONTINUES BELOW

“Ni ce ni ce Kabir.....”


Shine kawai abunda nake iya fada cikin ihu da daga muryar, tare da kokarin kwatar kaina amman ina karfin mace da namiji ba daya ba tuni ya samu sa'ar fara makurata, ga ruwan sama ana yi balle a kawo min agaji, ko ma ba a ruwan ba kowa ke shiga lamarin mahaukaci ba ballantana ma gurin babu jama'a sosai.

  Kamar daga sama na ji ana kokarin taimaka, sai duka ake kaiwa Kabir ta ko'ina ban san ko waye ba har sai da na samu sa'ar kubucewa daga hannunsa, ruwan dake sauka da kuma makurar da na sha bata hanani gane cewar Ahmad bane, abunda ban tana zato ba, ban tana tunani ba balle har nai mafarki yau yake faruwa a zahiri. Nikam ban tsaya komai ba ganin fadan ya koma tsakaninsu yasa na dauki mayafina da sauri na nufi inda jakata take na dauka tare da kayana na fara tafiya kamar an koroni ko waige inda suke ban sake ba.

  Sai da nai tafiya mai nisa sannan na soma tafiya a hankali ina cigaba ta taron Napep, cikin sa'a motar Abdallah ta wuce ni sai kuma ta dawo baya daidai ta tsaya daga can cikin motar ya bude min front seat. Da sauri na shiga jikina har rawa yake.3


“Ina kika fito?”


Ni dai ban iya bashi amsa ba domin har yanzu ban gama dawowa daidai ba.


“Ina kika fito...?”


“Aiki”


“Aiki da wadannan kayan? Wando ne fa a jikinki da riga..”


Na dan kalli jikin nawa, ruwan da ya jikani yasa tufafin sun dan kama jikina.


“Karki sake saka su daga yau, idan ba barki ki saka tufafinki na hausawa ba, ki daina aikin”


“Am.... ”


“Ba shawara nake ba ki ba, umarni ne”


Ya fada yana daga min hannu fuskar nan tasa a hade kamar dai ba shi ba.


AHMAD POV.


Hannunsa ya kai ya ciro chewing gum din daga bakinsa sannan ya mike tsaye ya nufi window ya jefar da cingan din yana cigaba da yatsinar fuska.

  Ai tun farko be kamata ya ci cingan din ba ko da ba ita ta aje masa ba balle kuma a hannunta ya fito macen da babu ta biyunta a gurinsa gurin tsana. Yawun bakinsa ya tofar a window Yunus dai be ce masa komai ba bayan kallon da ya bishi da shi sannan ya fice.

  Haka ya wuni yana tofar da yawu kamar wani mai sabon ciki, yaba ta jin haushin tauna cingan din da yai, daga bisani ya koma jin haushin Siyama wacce ta bukaci ayi masa abun, kamin jin haushin ya koma gurin Yunus wanda yake ganin shi ya biye mata.

  After sallah azahar Yunus ya shigo office din yana sanar masa cewar bakinsu sun iso.2

“Amman Dahir ya zo”


“No yana kan hanya dai”


“To ya za'ayi communication da su”


“Karka damu da wannan, yanzu dai kaje ka gaisa da su”


After haka ya fice, Ahmad ya bata minti biyar a zaune sannan ya nufi freezer dake office din ya bude ya dauko sweet ya bude ya saka a bakinsa, dan yasan ba zai je can yana tofe tofen yawu ba sai kace mai sabon ciki, idan ma be sha sweet din ba tashin zuciyar da yake ji ba ba zai bar shi ba. Sai da ya dauki rigarsa ya saka sannan ya nufi dakin taro, yana shigowa suka mike tsaye tare da bashi hannu ya gaisa da su da halshen nasara ya fara yi musu barka da zuwa duk kuwa da yasan ba lallai ace suna jin wani abu bayan welcome da kuma gaisuwa ba.

  A gurin daya saba zama ya nufa ya zauna, yana kokarin ciro wayarsa daga aljihu aka turo kofar dakin Yunus ne ya shigo, Halimatu na bayanshi ta tsaya daga jikin kofar har sai dai Yunus din yai mata iso, wani irin bugawa zuciyarsa tai, duk sai yaji ransa ya bace  sai dai ba damar ya nuna a gaban mutanen a dole ta sa ya shanye, sai dai yana mamakin abunda ya kawo ta dakin taron. Takawa ta fara yi tana juya yai arba da mazaunanta sai yai saurin runtse idonsa duka biyu, can kuma ya bude dayar yayinda dayar take a makkale ya rufeta, sai kuma yai saurin rufewa yana jan tsaki a ransa. Be bude ba har sai da yaji ta fara magana da su alamar ta juyo kenan sannan ya bude ido, kallo daya yai mata yaga yadda kayan suka karbe ta sai kuma ya dauke kai. Har akai meeting din aka gama be bari ta san yana kallonta ba, ba ma ita ba ko Yunus da ke kusa da shi ba zai iya gano ya kalleta ba ko a'a domin ta kasa kasa yake kallonsa irin na munafukai.

  After sun gama ta bukaci fita sa Yunus ya nemi rage mata hanya a take Ahmad yai karaf ya hana shi, yana ta mamakin shisshigi irin nasa, after ta fice ya tabe baki ya tashi tsaye ya face daga kamfanin, office dinsa ya nufa yana kara jin bachin rai na kama shi, zaunawa yai saman kujerarsa ya rufe laptop dinsa sannan ya fito daga office din ya nufi gurin motarsa da sauri, so yake ko da za a sako da ruwan yana gida ko banza yau ai ranar birthday sa ne.

A hankali yake tukinsa, sai dai kamar yadda ya kusan zame masa ibada kallon gurin da mahaukacin nan yake zama a kullum saboda abincin da Halimatu take ba shi yasa shi kallo a yau, yana tunani a yau kam ba zata tsaya ba tun da ta fita tana sauri kuma gashi garin har ruwa ya fara sauka, to his surprise sai ya hangota a gurin tare da shi, at first ya dauka ko wani abu ne mai kama da wasa daga baya ya fahimci kokuwa ce suke wanda be san dalilinta ba.2

“Ashe dai itama bata da hankali, daman can ba tai kama da masu hankalin ba”


Ya furta sannan dan karawa motarsa wuta, kamin ya sake kallonsu da kyau ya fahimci dai fada suke, sai kawai ya faka yana ta kallon yadda mahaukacin ya kai mata duka kamin ya hango mahaukacin ya makureta har tana neman taimako. Cigaba yai da kallonsu, har sai da ya fahimci da gaske mahaukacin kasheta zai yi sannan yai unkurin bude motar, a take wata zuciyar ta hana shi, then ya fara tunani ai shi human being ne not like her, ba zai iya kallo ayi kissan kai ba. Cikin sauri ya fita daga motar ya nufi i da suke ya fara dukan mahaukacin ta baya har Halimatu ta samu sa'ar kubuce a hannunsa ta ranta a na kare sai fadan ya dawo tsakaninsu da mahaukacin shi da mahaukacin aka rasa mai hankali kowane kai wa wani duka yake, a cikin rashin sa'a mahaukacin ya naushi idon Ahmad ai take ya ji kalar garin ta canja, be san lokacin da wani karfin ya zo masa ba ya saka kafafuwansa ya buge Kafafuwan mahaukacin ya fadi kasa, a take Ahmad ya ranta a ciki na kare yana dafe da ido daya ya nufi motarsa a rikice ya bude motarsa ya shiga saboda wani azababben zugi da idon ke masa, @360 ya fisgi motar da ido daya da yake gani da shi.6Da hannu daya yake tuka motar yayinda dayan hannunsa yake dafe da idonsa, wani zafin bala'i idon yake masa ga ruwan da ake kama da bakin kwarya, har baya iya gani da kyau saboda karfinsu.

A dole ya faka motarsa gafen titi, slowly ya dauke hannunsa daga idon da ke masa wani mugun zugi, ji yai idaniyar ta cika da abu mai kauri shi ba hawaye ba kuma ba ya san jini ne har sai da ya duba hannunsa. Jini a ciki kuma shine yake cika masa idon har baya gani da idon daya.

  Lumshe idanuwan yai duka biyu yana sauraren yadda zugin yake shigar masa har cikin kansa, a rufe da idon ya saka hannun aljihu ya dauko wayarsa sai a lokacin yai kokarin bude idon daya yana duba iPhone dinsa wacce ta gama daukewa dip, sakamakon ruwan da ta sha, ba wayar kadai ba tufafin jikinsa ma sun gama jika seat dinsa balle kuma wayarsa.

Iskar bakinsa ya bushar yanzu be san yadda zai yi ya kira Doc Nura ba balle yaji idan ma yana gari ko yana asibitin ko gida, daman can a tsarinsa be yarda wani likitan ya duba shi ba sai family doc su, domin ya yarda da aikinsa hundred percent.

“Ba ma ita ce mahaukaciyar ba ni ne mahaukacin, taya zan shigar mata fada? Fadan ma da mahaukaci dan'uwanta? Matar da ta kashe min yarinyar? What's is wrong with me?”+


Ya fada yana jin haushin abunda ya aika..


“Bata ma tsaya ta dubani ba fa sai kawai ta gudu, idan ma kashe ni zai yi ita dai ta tsira, mahaukaciyar banza i hate her”2


Ya sake fada cikin fusata yana cizon bakinsa. A gurin ya tsaya har sai da ruwan suka dauke gaba daya sannan ya karasa tukin zuwa gida kamin ya isa har wani jiri yake ji cikin kansa.


“Ai I'm human being be kamata ina gani ayi kisan kai ba, shiyasa na taimake ta, amman yanzu na gano matar nan bakincikina take so take ta illatani bayan ta kashe min ya, be m kamata na barta tana aiki a kamfani na ba ai”


Shi kadai yake ta magana da kansa har ya faka motarsa a harabar gidan, yana kokarin bude motar ya fita ya tambayi kansa.

“Ko ma miya kai ni fada da mahaukaci? Da mahaukaci da mahaukaciya suna fada ni mai hankali miya kai ni ciki?”


After ya fito daga motar ya bawa kansa amsa.


“Kaddara.... ”


Part dinsa ya wuce, yana shiga ya fara ziyartar bandakin ya wanke fuskarsa, ya saka tissue yana tare jinin a hankali sannan ya dawo dakinsa ya dauko dayar wayarsa da ke gida yana kokarin kiran Doc Nura.

“Hasara nawa ga saka ni a yau? Ta saka na jika tufafina ga idona daya ga phone dina.....”


Wani irin haushinta ne ya kara cika msa zuciya. Sai da ya tabbatar Doc Nura na aibitin sannan ya canj tufafin jikinsa ya dauko key din wata motar ya fice ba tare da ya leka part din Hajiya ba, domin baya son ya tashi hankalinta.

A asibiti babu kalar dariyar da Doc Nura be msa ba.


“To kai yanzu miya kaika raba fada da mahaukaci? Ai gashi an bak tukuici”


“You make me hate her more”


“Wai wacece wannan?”


“Wata mahaukaciya ce mai ruwan masu hankali”


Ya hada fuska babu annuri can kuma yai murmushi.

“Ita ma fa taji wuya, ba da wasa ya moreta ba”


Dadi yaji tun da ita ma ta ji wuya, but maganar Allah shi yafi kowa shan wuya tunda shi be shi yaja mahaukacin ba.

Bayan Doc ya duba idon ya bashi maganin na sha da shafawa a idon ya kuma fada msa yadda zai kula da ido. After ya dawo gida ya kira shiga part dinsa ya kiran Yunus.

“Yu akwai wani mahaukaci da ke kusa da kamfanin mu, daga hannun dama gurin wani shagon kwano, za ka iya gane shi?”


Sai da Yunus yai tunani sosai sannan ya amsa masa da.


STORY CONTINUES BELOW

“Yes na gane shi kullum nn yke zama”


“Ka sa a dauke shi a kai shi gidan mahaukata”


“Why?”


“Why? Ya zan baka umarni ka tambayeni why?”


Ya amsa a fusace, kamar Yunus din ba abokinsa ba ne, saboda yau yana cikin zafin kai. Bayan ya kashe wayar yaje gaban madubi yan duba idon, idonsa daya yayi kwancin jini a ciki gaba daya gefen idon ya kumbura, abunka da farin mutun har wani ja gurin yai.

  “Ina zaman zamana ta ja min masifa.....”


Ya karasa maganar ta tari sai jini ya biyo baya, daman haka yake yanzu da ransa ya bace sai ya fada tarin jinin sai ciwon kirji.

  Toilet ya nufa aman jini yai ba kadan ba, shi kanshi sai da abun ya dan tsorata shi, har yana zargin wata kila saboda ya sha ruwan sama ne abun ya kara hade masa, wanka yai sannan ya dawo dakinsa ya sha maganinsa ha kwanta.

Sai 4:21 ya farka, sallah ce abunda ya fara gabatarwa sannan ya duba idon nasa kamin ya nufi part din Hajiya. Tana ganinsa hankalinta yai mugun tashin musamman idon nasa wanda ta hango jan jini a ciki.

“Miya same ka Gwarzo?”


“Hadarin nan ne da ya taso ina kokarin shiga, mota sai kasa ya shigar min ido”


“Wannan ba kasa ba ne, hannu ne ga kwancin shi nan a idonka, kaga ni ko shiyasa bana son kana zuwa kana dadewa a waje, na sha fada maka da kun gama aiki ka rika dawowa gida, na san halinka da zuciya wata kila kaje ka bugu wani ya rama”


Hannu ya kama yana kokarin zaunawa da murmushi a fuskarsa.

“Haba Hajiya ai na girmi wannan, Wallahi kaddara ce kawai amman In-Sha-Allah ba zai sake faruwa ba”


“Bari na kira Doc Nura”


“Naje gurinsa ya bani magani ya duba idon”


Sam bata yarda ba har sai da ta kira shi da kanta tai magana da shi ya tabbtar mata da cewar ya dubashi sannan hankalinta ya kwanta.

“And daga yau ba zaka je aiki ba sai nan da one week”


Da sauri ya kalli Hajiyarsa yana sakin baki.

“Amman Hajiya kin san idan ba da ni ba wani abun ba zai yiyu ba”


“Doka ta ce wannan”


Ta fada fuskarta babu alamun wasa.


“Yaro ba san ciwon kansa ba, sai idan ana nuna maka abu kace kai ba yaro ba ne”


Rasa yai abunda zai ce mata, ba zai iya karya dokarta ba, kuma ba zai so fashin zuwa aiki ba, zai iya amfani da bakin gilashi ya rufe idonsa.

“Idan an yi magariba ka kwanta karka tashi sai an yi isha'i, zan dafa maka carrot da allayau da wake yanzu suma suna gyara ido”


A dolen dolensa ya amsa mata da okay, ta tashi ta shiga kitchen da zimmar dora masa girkin, shi kuma ya bita da kallo yana ta tunanin randa Hajiya zata yarda da cewar ya girma san ciwon kanshi.


HALIMATU POV.


A hankali na kalleshi, fuskarsa a hade take sam babu alamar wasa a umarninsa. Na sani ba lallai ne su yarda su canja min aiki ba, balle kuma har su yarda na rika saka wasu tufafin na dabam, Ahmad ba zai min wannan lamanin ba, ko a da balle a yanzu da ba san yadda na baro shi da karfi ba, ba laifi ya nuna kulawarsa tun da har ya taimaka min ba dan shi ba wata kila da yanzu na zama gawa, domin ba kadan Kabir ya makure ni ba.

Tunanin nake ta yi ni kadai ina shafa wuyana da har yanzu ciwon yake min.

“Amman za su iya cewa ba za su yarda na daina saka kayan ba”


“Sai ki daina aikin”


“Idan na daina aikin da me zan kula da kaina? Kamin na samu wani aikin abu mai wahala, kuma ka san bana da mai taimakona a yanzu sai Allah”


STORY CONTINUES BELOW

“To sai ki samu miji ki yi aure, ki rike Namra da Amal Aiman da Adnan kuma ki maidasu gurin Babansu.....”


Kai tsaye ya fada min maganar nan ba tare da ya kalleni ba. Wani irin kallon mamaki nai masa, ban yarda daga bakinsa kalaman nan suke fitowa ba, sam ban yarda Abdallah na ne ba, taya zai min wannan maganar me yake nufi da ni? To sai ki fitar da miji ki yi aure...... Kalmarsa na ta maimaita min kanta a cikin kaina.


“Kalmar ka ta min nauyi Abdallah, tana kokarin rikecewa, ban gane komai ba”


Ajiyar zuciya ya sauke ba tareda ya kalleni ba ya ce.

“Har gobe ina sonki, har gobe ina kishinki, har gobe ina tausayinki ki saka wannan a zuciyarki, kuma wannan kaddara ta ce zan mutu da sonki.... Na sani kuskure ne na so matar yayana bayan ya rabu da ita, sai dai sonki ya dade a zuciyata tun kamin ki auri dan uwana, kin riga kin lalata komai Halima, Hajiya ta min katanga tsakanina da ke....”


“Har da aurena....?”


Na tambaya murya na rawa, idanuwana kuma suka soma aikinsu.

“Taya kike tunanin samun farinciki a auren da uwa bata so? Dan'uwa baya so? Da wane irin ido za mu kalli al'ummarmu? Zan mutu da kaunarki Halimatu wannan ita ce kaddarata.....”


Ban taba jin abu marar dadi irin na yau ba, Abdallah be taba fada min wata bakar magana ba irin yau, gaba daya sai na nemi farincikina da kuzarina na rasa, wani irin bakinciki ya cika min zuciya.

“Sauke ni a nan”


Na fada ina kawarda fuskata, ba musu ya faka motarsa gefen titi ni kuma na bude na fita, ina jikin babu kwari kamar na fadi. Key yai ma motarsa ya kara gaba ya bar ni a gurin tsaye ina hawaye.

“Shiyasa ya daina kula ni? Miyasa na auri Abdulhamid tun farko? Miyasa tunani be bani Abdallah ba sai a yanzu? Miyasa kaddara take min haka? A lokacin da ya kamata ba jidadi sai wata matsalar ta saka ni a gaban? Gaba daya ban san jindadi a rayuwata ba....”


Na fada ina fashewa da kuka, ruwa na ta dukan kaina. Kasa na fara tafiya daman tazarar dake tsakanin inda ya sauke ni da gidanmu babu nisa sosai, tun ina tafiya ruwan na sauka da karfi har suka rage, ban daina tunani da kuka ba. Ruwan da ke saukowa ya taimaka min da ya hana a gane ina hawaye saboda yana dukan kaina. A lokacin da na shiga gida kowa yana daki ya fake, kai tsaye na nufi dakin Mama, ban saba shiga ba sallama ba amma a yau haka na shiga babu sallama mana ma iya kallon wake falon waye baya ciki.

Dakin Mama na shiga na cire tufafin jikina na dauki zanenta na daura, tana ta kallona da yadda nake motsa jiki babu kuzari.


“Lafiya kike yau kuwa?”


“Nima ban sani ba, ko lafiya nake ko ba lafiya nake ba”


Na amsa mata ina hawaye.


“Miya faru”


Juyowa nai na kalleta.

“Mama ni ce babba a cikin yayanki, ya kamata na zama mai hankali da tunani ko? Da hangen nesa amman duk ban zama ba”


Zaunawa nai kusa da ita na kai jikina a cinyarta na kwanta ina kuka.

“Fada min matsalarki miya faru”


“Mama Abdallah..... Ya fada min a yau ba zai aureni ba”


Murmushi tai.


“Halimatu kenan, daman taya za'ayi Abdallah ya aure ki? Bayan dan'uwansa ya aure ki? Kuma dan'uwan nasa yana nan a raye? Mu ma ai ba zamu bari ki aikata wannan kuskuren ba, domin na san kiyayya da gaba ce zata shiga tsakaninsu wanda mahaifiyarsu ba zata so hakan ba”


“Amman.... Ba.... Haramun...ba ne... ”


“Ke kika san wannan, abubuwa da yawa yanxu al'adarmu ta mayarda su haram saboda kunya da gudun samun tsabani, kin yi kuskure Halimatu da dai tun farko ne kina da damar zabar Abdallah ki bar Abdulhamid amman ba ki yi ba, tun farko Abdallah ya kamata ki aura na ta nuna miki amman kika kasa ganewa, mutum da be taba kyamar yayanki ba, be taba nuna gajiyawa a taimakonki ba, shine mutumen da ya kamata ya zama abokin rayuwarki tun farko”


STORY CONTINUES BELOW

Dagowa nai na kalleta.


“Amman wani abu be taba shiga tsakanina da Abdulhamid ba....”


“Mutane ba su san da wannan ba”

 

Tashi nai daga dakin gaba daya, na nufi dakina, na zauna saman katifata ban ji ina bukatar komai ba sai kuka da nadama. A ranar ban rumtsa ba har sai da na rubuce labarin kaddarar rayuwata tas a jikin takardar da Abraham ya karbo min.

  Da akam ban yi niyar zuwa ba, amman yanzu zanje saboda yara wadanda ke ta daukin zuwan.

  Misalin takwas da rabi na dare aka aiko ana kirana, na san be wuce Abraham ba, wannan karon ban musa ba na saka Hijabina na fita, a inda ya saba tsayuwa na nufa yana tsaye a gurin jimgine da motarsa yana kallona har na karaso.

“Ya kike?”


“Ina lafiya”


Na amsa ba tare da na kalleshi ba. Sai kuma yai shiru yana kallona.

“Kamar kina cikin damuwa”


Sai a lokacin na kalleshi.

“Kaine karin damuwata, da zaka daina bibiyata da na samu salama, ka tafi na yafe maka, kaima kana cikin kaddara ta ne”


“Za ki aureni kenan?”


“Ba zan aureka ba”


Na amsa masa ina kuka.

“Ko da zan musulunta?”


“Ko da zaka aikata abunda ya fi musulunta, idan zaka musulunta ka musulunta saboda Allah kawai, saboda gudun azabarsa, saboda tsoronsa saboda kaunar Annbinsa, karka musulunta dan ni domin ni bana tabbata amman Allah tabbatacce ne, wanzanje wadatacce, tsarkaken, tsabtatacen, ka musulunta saboda tsoron wuta da kwadayin aljanna, zaka iya musulunta a yau saboda ni gobe Allah ya karbi rayuwata, shi zaka ci gaba da musuluncin ne ko zaka daina? Amman idan ka yi saboda Allah shi Allah tabbatacce ne, imaninka zai tabbata har Aljanna, kada kai komai saboda ni a yanzu ba aurene a gaba na ba, bana jin zan sake soyayya ma balle aure”


“Saboda me....?”


“Saboda mutumen da nke so, ba zai taba aurena ba, ya fada min zai mutu da so na a ransa, ni kuma zan rayu da kaunarsa har izuwa ranar da ajalina zai riske ni... ”


Na karasa cikin kuka.

“Wane mai sa'a ne wannan?”


“Wani ne wanda ya so ni a lokacin da duniya ta guje ni, ya taimaka a lokacin da bana da mai tsaya min, ya so yayana a lokacin da ubansu ya guje su”


“Then miyasa yanzu ba zai aureki ba?”


“Saboda na auri dan'uwansa, mutumen da ka keta min haddi a gidansa, dan Allah wannan zuwan ya zama na karshe a gurina, ka barni na ji da damuwata”


Na karasa ina hade hannayena ina rokonsa.

“Ke ba ki yarda haduwar mu kaddara ba ce? Taya za ka yi mace fyade a dare a lokacin da kake boyon kanka, sai kuma ka dawo da rana ka kawo kanka ba tare da fargabar komai ba? Da zaki buda zuciya babu abunda za ki gani sai kaunarki, son ki yasa na ke sha'awar barin addinina na dawo na ki, zan iya hakurin zama da ke a haka da soyayyar wani a ranki, da sannu zan koya miki so na har ki aminta....”2


“Babu namijin da zai koya min so a yanzu, sai da safe.... ”


Ina fadar hakan na juyo na nufo gida ina jinsa yana kirana na kina amsa har na shigo gida.

Tun daga ranar babu ranar da bana bachi da bakinciki, sai a yanzu na gane cewar na yi kuskure a lokacin da babu hanyar gyara kuskuren.

Daga lokacin ban sake zuwa aiki ba, umarnin Abdallah ya hau kaina na cewar na bar aikin idan ba za su canja min tufafi ba, ban tafi na fada musu ba sai dai na san mawuyacin abu ne su yarda su canja min, balle kuma na jawa mai kamfanin fada da mahaukaci ko ya ma suka kare oho.

 

A ana gobe children day, Aminu ya sallamo min, ban fita ba hakan yasa ya nemi izinin shigowa cikin gidan ya shigo ya same a falo ina gyara tufafin su Aiman. Da sallama ya shigo na amsa masa kaina babu dankwalina ga gashin kaina ya sha tsiro kanana gwanin sha'awa.

  Tashi nai naje na dauko Hijabina na saka sannan na dawo na zauna.

STORY CONTINUES BELOW

“Yanzu Halima kin fi son rayuwar yaran nan ta tagayyara? Ba sa nan basa can? Haba Halima ko ba dan ni ba ko dan yara ai kamata ki duba...”


“Kamin ka sake ni ya kamata kai wannan tunanin ba a yanxu ba, a iya tunani baka shaye shaye Aminu sai neman mata miyasa kwakwalwarka take ta nuna maka cewar zan dawo gareka?”


“Shi ma Wallahi na daina, na riga na gane kuskurena Halima, kuma na yarda abunda ka aikatawa yar wani za a aikatawa, kuma zaka dandani dacin abunda ka aikatawa matar wani a gurin matarka”


“Shiyasa ka rabu da ita kenan? A lokacin ne ka gane cewar ina da matsayi a rayuwarka, shiyasa na dawo gareni, na jidadi idan har ka shiryu da gaske, domin har gobe kai ubansu Namra ne”


“Ban taba ganin mace mai hakuri da kawaici ba irinki Halimatu, wata mace bata taba so na kamar yadda kika so ni ba, ban gane hakan ba sai byan na rabu da ke, da farko arzikina ya fara karaya, sai aka fada min saboda na rabu da ke ne, arzikin yana tare da ke, amman kin san me? A yanzu na gane mutanen nan karya suke fada, ba saboda na rabu da ke na sara wasu abubuwan ba, saboda na ci amanarki ne kuma a maimakon na zauna da ke a haka sai na sake ki, na kuma kyale ki da hidimar yara, wanda hakkina ne, shiyasa Allah ya nuna min sakamakona tun a nan duniya”


“Hakan yana da kyau ko ba komai ai yasa ka shiryu, ina maka murna”


“Ba murna kadai nake son ki taya ni ba, ina son ki dubeni da idon rahama ki tausaya min dan Allah”


“Idan ma ka zo nn ne saboda ka fada min ka shiryu to ka yi kuskure, ka daina dogon mafarki a kaina, ni a yanzu na maka nesa, tun daga lokacin da na baro gidanka ban sake sha'awar zama da kai ba”


“Yaran mu hudu fa Halima, kin fison ki auri wani ki bar uban diyanki? Wa zai kula da su kamar yadda ke za ki yi?”


“Ka auro musu wata uwar mana, idan baka da wacce kake so ni zan iya nemo maka”


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Ya fada yana dafe kansa, ni kuma na dauke kayan na fice daga falon na bar shi ciki. A ranar da zamu je gurin da ake bikin na ranar yara da duniya, na shiryawa yarana cikin kananan kaya sannan ni kuma na saka bakar abaya, tun takwas da rabi mu ka bar gidan gudun kar mu yi latti kuwa da kasancewar akwai mintuna talatin kamin a fara.

Ba a bar mu mun shiga ba sai da na nuna musu dan karamin katin hannuna, sannan suka bude mana kofa, wani irin katon filine mai kamar stadium an jera kujera sai kuma wata yar rumfa da akai daga sama wacce na kyautata zaton ta manyan bakine, ko da muka shiga har an fara gabartawa ana yi wa mutane maraba, a inda aka nuna min na zauna gurin na musamman inda yaran manya da iyayensu suke zama, tsabanin dayan bangaren da yake na talakawa irina, akwai taron mutane sosai ba Lalla ne ka iya ganewa kowa ba.

  Bayan na zauna na kalli wata macen yar sanda dake tsaye kusa da ni na tambaya gurin da ake aje takadar ta nuna min wani dan karamin daki da zan shiga, a gurin na bar su Namra na shiga ni kaina sai na samu wani kwando na gefe ta tarin wasiku a ciki, a gefen kusuwar kwandon na jefa wasikar sannan na fito. Bayan na dawo na zauna ina rabon ido na hango Ahmad zaune gaban teburin manyan baki, wani irin faduwa gabana yai sai nai kokarin kawardar fuskarta ima satar kallonsa, sanye yake da shadda ash color sai da hula kalar shaddarsa, idonsa kuma anye da bakin gilashi wanda ya kara masa kyau da kwarjini.

  Fuskarnan a hade sai sham kamshi yake, yana kallon mutane one after the other. Sai a lokacin kunya ta kamani ya kamata naje nai masa godiya abunda yai min, ban je ba ban ma sake komawa kamfanin ba, ko ya suka kwashe da Kabir din ma oho, sai dai ina da tabbacin a ranar Kabir be gane ni bane saboda ina sanye da tufafin da ban taba sakawa ba, kuma gashi ana ruwa.

  Duk wani abunda ake idonsa na kai, kamar yadda nawa ma yake kai, garin kalle kalle na na hango Abraham zaune a daya daga kujerun da aka tanadarwa yan kallo, muna hada ido ya dago min hannu yana min murmushi ni kuma nai saurin kawar da fuskata. Muna zaune a gurin har akai abubuwan da za ayi sannan aka fara gabatar da wasar numbobi jikin katin aka fara kira har aka kira number mu 17.

  Fita muka yi tare da yarana muka shiga filin da aka tanadar mana, sai a lokacin na lura da cewa ba ni kadai ce uwa bahaushiya ba a gurin, akwai wasu uwayen hausawa biyu bayan ni.

  An raba an sawa gida uku uku ne, wanda hakan yasa hankalin kowa ya dawo kanmu ciki kuwa har da Ahmad.

  Da farko daukar kwai ne akan spoon daga gurin wani dogon tebur zuwa inda ko wace uwar take, yaranta za su dauko da gudu su kawo mata sai ta karba ta saka a gidansa, idan aka girga ko daya be fashe ba to ka ci wannan gasar, na biyu kuma debo ruwa ne murfi bottle zuwa inda anke har a cika wani karamin bokiti, na ukun kuma ko wane yaro sai saka safa a kafarsa ta dama sai yai tafiya da ta hagun har ya isa gurin mahaifiyarsa idan be taka kasa da safar ba su ma sun cinye.

   A hudu kuma wanda shi ne na karshe za abawa ko wane yaro damar rubuta dalilinsa na son cin wasar da kuma wanda zai sadaukarwa.  

Yara uku kawai suka bari na shiga da su duk kuwa da kasancewar dukansu Abraham ya siya musu tickets din, sai dai sun yi hakan duba da wanda za a hada ni da su, daga mai yara biyu sai uku. Sai da suka fara bawa ko wane yaro takardar da biro suka ware kowa dabam yai rubutunsa sannan suka karba,sannan aka soma wasan.

  Ba zan yabi yarana kadai ba, domin a na ga wasu yaran da suma suka maida himma suna ta kokarin ganin sun ci kamar yadda nawa yaran ma suke har abun ya soma bani tsoro, na sani idan ban ci ba yarana ba za su ci dadi ba, kamar yadda nima ba zan jidadin ba ko dan kwallafa rai a kudin ba, akwai ciwo ace ka shiga gasa kuma baka ci ba.

STORY CONTINUES BELOW

Sai da muka fara karawa da mutane farko mu kai nasara a na biyun ma muka yi nasara haka a hana hudu har na karshe ma Allah ya ba mu nasara duk kuwa da kasancewar a lokacin jikinsu Namra da Adnan da Aiman yayi sanyi domin sun gaji sosai.

After mun gama aka saka muka koma saman muka tsaya tare da magabatarwa, sannan suka karbi account number kowa, a lokacin da muka shiga garsar mun fi mu ashirin da daya amman da aka gama mu shi kawai aka tsayar a gaban gurin.

  Sai da aka fara karanta abunda yan ko wane team suka rubuta a takadar, idan an gama sai a fadi number team din sannan a fadi sunan wanda ya rubuta, sai kuma yan team din su daga hannu.

  A lokacin da aka kawo gurin na mu, abunda Aiman ya rubuta shi Adnan ya rubuta haka ma Namra.

‘Momy ta mana alkawari idan mun ci zata biya maka kudin makaranta da su, kuma zata siya mana kayan wasa’


A gaskiya na ji kunya na ji kunya sosai a lokacin da aka karanta cewar wai idan na ci zan biya musu kudin makaranta, duk sai na ji kamar na muzanta, a gurin fadin abun wasan ne ya sha babban ita Namra ta ce teddy, Aiman yace keke, Adman kuma yace mashin din nan na yara. A gurin sadaukarwa kuma kowa yace idan ya ci zai sadaukarwa Momy wato ni kenan, ban da Namra wacce tace idan ta ci zata sadaukar wa kawarta wace ta rasu wato Baby Namra. Ba kadan abun ya taba min zuciya ba, wato har yanzu Namra bata manta da kawarta ba.

  3rd position aka fara sanarwa, wato team 13, a take gurin ya garwaye da ihu ana ta taba musu a lokacin ne bugun gabana ya soma karuwa, ina cikin masu tabawa ammn hakan be hana ni tsorata ba, ni da sauran masu jiran sakamakonsu.

  A na biyun ma an yi ihu, an taba musu wato team 6. Mai sanarwarwa wacce yar jarida ce a gidan redio sai da ta dauki lokaci tana jan rai har sai da tsoro ya kama duk wani wanda ke cikin wasan hakan tasa na runtse ido ina ta addu'a, Namra kuma ta rike min rike da duka karfinta ta rumtse ido.


“The winner is....... Is..... Is....... ”


Haka tai ta jan abun kamin ta fadi.

“Team 17........”


Wani irin mahaukacin tsalle Namra ta daka ta dire tana ihu tare ta rumgume Aiman suka fashe da kuka. ba ita kadai ba, ni kaina hawaye na ke abu ga mai shawaye kusa, Adnan ma rawa ya fara har su jujuyawa, kowa taba mana yake ciki har da Ahmad da ke kallonmu da Murmushi a fuskarsa.

    Sauran ba su ci ba suka sauka daga stairs din sai muka rage team uku kawai, sam ban lura da mahaifiyar Ahmad ba har sai aka kirata ta bada award ga mutanen na uku, a lokacin ne nake jin suna kiranta da tsohuwar shugabar ma'aikata, a na biyun aka kira wani kwamishina ya ba su award.

A lokacin da aka zo gun mu sai aka gayyato Ahmad Muhammad Gwarzo, sai da ya fara ba ni cak din kudin sannan sannan ya gaisa da Adnan da Aiman, kana ya risina ya shafa kan Namra ya sumbanci goshinta.

“How are you my dear”


“I'm fine”


“Congratulations”


“Thank you Sir”


Ita ta mikawa Award din sannan ya tsaya aka dauke mu hoto kamar yadda akewa kowa. Idanuwa ba su sauka a gurin kowa ba sai Abraham wanda ke a tsaye yana taba mana tare da yin well done da hannunsa yana murmushi. Sai da aka gama komai sannan muka koma gurin mu muka zauna tare da sauran mutane na kusa da mu suna ta tayamu murya, kasa hakura nai har sai da na kira waya na sanar a gida sannan na maida hankali gurin shiri na gaba wato karanta wasikun uwa.

  Duk wacce aka karanta wasikarta akan ce daga uwar wane da wane matar wace, sai ta taba mata mai gabatarwa ta yi maganganu akanta sannan a cigaba.AHMAD POV.

Ba kasafai ya cika son irin wadanna taron ba, saboda dadewar da ake ga kuma tahaniyar mutane da speakers wandanda suke takura masa. Amman a haka ya daure tun da kusan shine babban bako a gurin kuma abunda aka saba yi a ko wace shekara ya zame masa dole a bana ma ya tsaya ayi da shi. Babu abunda ya burge shi kamar kalaman Namra na cewar idan ta ci zata sadaukarwa yarsa Baby Namra abunda be yi tunani ba, ko ba komai hakan da tai ya saka masa sonta kuma ya saka ransa yayi fes a taron, duk kuwa da kasancewar a farkon ganinsu be yi murna ba, babu abunda be ayyana aransa ba na ganin har da ita a gasar.

Yana kallon agogon hannunsa ake karanta wasiku wanda yake sa ran ba za a gama karantasu da shi ba, be natsu sosai ba har sai yaji mai gabatarwar tana maranta labarin wata kalar murdaddiyar rayuwa, wata kalar rayuwa ce mai wuyar fassarawa, mai wahalar gaske, ga tarin tausayi da taba zuciya duk wanda labarin ya samu masauki a kunnensa, ga shi kadai ba kusan duk wanda ke gurin sai da zuciyarsa ta sosu da labarin msu saurin kuka a take suka fara hawaye.

“Daga wata uwa mai kaunar yayanta.... ”


Mai gabatarwar ta karasa cikin muryar kuka tana daga takadar sama.

“Wace uwa ce wannan dan Allah? Wacece ita? Dan Allah ko wacece ke ina son ganinki ina son na ganki kawai, hakika ke jaruma ce jajirtacciya, kuma tsayayyiya mai karfi zuciya you deserve an award....”


Taja mashina sannan ta cigaba.

“and... Dan fashin da yake bibiyarki zai iya cutar da rayuwarki ki san da wannan, ni ko ba zan iya ba ki kariya ba na san jami'an tsaro za su ba ki, kuma In-Sha-Allah zan tsaya miki har ki samu salama, ba bayyana ki zan yi ba, ba nunawa kowa fuskarki zan yi ba balle har na fadi sunanki, taimakonki zan yi, and i promise you a cikin albashi na na wannan watan kina da 20,000 dan Allah ki same ni ko a ina ina son ganinki, ko wace irin uwa ce ke ina son ganinki dan Allah....”


Cikin kuka Ummulkhar take fadin hakan hannunta rike da loudspeaker dayan kuma rike da takardar yayinda idanuwanta suke zubar da hawaye.

  Babu wanda zuciyarsa ta raya masa sai matar nan, sosai ya maida hankali yana kallon gurin da take zaune tare da yaranta, the way ta take sharar hawaye ya kara karafafa zatonsa a kanta, labarin yarsa ya shigo ciki duk kuwa da bata fadi sunansa ba ko sunan yarsa sai dai ta fadi cewar mahaifin yarta ya zargeta da kisan yarsa saboda kaddarar mutuwarta ya fada mata, kamar yadda kadarar gushewar hankalin abokin aikinta ya fada a kanta, an keta mata haddi an ketawa yarta, mijinta ya ci zarafinta, a kokarin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa, ga labarin samun aikin kamfanin da tai ya shigo ciki sai dai shi ma bata fadi sunan kamfanin ba.....

  Wani irin kallonta yake, har ya ji kamar gilashin dake idon sa ya tare ganinsa sai ta ya cireshi yana cigaba da kallonta, ita kuma ta soke kai kasa yana ta latsa waya tana sharar kwalla, wa akai wa fyade? Wacen karamar ko babbar? No wait mutunen da take bawa abincin a kusa da kamfaninsu abokin aikinta ne? Is that why take kokarin kula da shi? Waye mijin na ta? Waya ke bibiyarta?

A lokaci daya ya jerowa kansa wadannan tambayoyin, da bashi da amsar su, and he can't take his eyes on her kamar his life defend on her, tun bata lura da kallon da yake mata ba har ta lura ta soma rasa natsuwarta, sai a sannan ya saka gilashin idonsa ya cigaba da kallonta ta yadda ba zata fahimta ba, zuciyarsa cike take da tambayoyin da ita kadai zata iya amsa mashi su, ita kadai duk wannan abun akanta? Be tana jin labarin da ya shiga zuciyarsa ta tsuma zuciyarsa ba irin na yau, bw tana jin labari mai tausayi da tashin hankali ba irin yau, kuma a haka she's still alive tana ta farincikinta ita da yaranta, har akai abunda za ayi a gurin aka tashi be kawarda hankalinsa daga kanta ba.....ABDALLAH POV.

He's walking slowly tun daga inda ya aje motarsa har zuwa cikin falon Hajiya, gidan sai kamshin sabon fenti da aka yi jiya yake. A gajiye ya shigo falon sai ya tarar babu kowa sai sanyin ac. Zaunawa yai a saman sabin kujeru da Hajiya ta sake ya ciro wayarsa yana latsawa, ya kusan minti talatin a haka sannan Hajiya ta fito rike da wuka da katon mangoro a plate.


“Husani kai ne ka shigo”


Ya dago a hankali ya kalleta.

“Eh Hajiya barka da yamma”


“Yauwa sannu dai, ya aikin? Yau baka shigo da safe ba”


“Na fita aikin ne da wuri saboda tiyati za ayi, shiyasa”


“Okay abincin fa akawo?”


“A a gida zanje yanzu”


Daga haka bata sake ce masa komai ba, shi ma kuma be ce mata ba, daman kusan kullum idan ya shigo gidan shiru yake ko wata maganar ake sai daiya bisu da ido.

“Ana ta shirye shiryen biki har yanzu baka ce komai ba”


“Allah ya sanya alheri”


Ya fada a takaice, sai kuma yai shiru kamin ya sake kallonta.


“Hajiya na yi wani laifi”


A take ta dago kai ta kalleshi da sauri.

“Mi kai?”


“Kin min tsakani da Halima, tun daga lokacin ban sake kula ta ba, sai kwana goma sa suka wuce, na ganta a hanya tana tafiya da tufafin da be dace ba, hakan yasa na tsaya na dauke a motata saboda kare mutuncinta, ki yafe min dan Allah”+


“In ban da kai da abun ka, miye amfanin kare mutuncin macen da bata san mutuncin kanta ba, da wata ce ai ba zata yi shigar banza ta fita ba, talla take yi kenan Allah ya kyauta”


Yawu ya hade da karfi da ba Hajiya ba ce da be lamuncin jin wani kalami marar dadi daga bakin kowa ba akan Halimatu idan ba zai iya cewa komai ba to ba zai saurara ba.

“Wato dai na gane ba zaka iya fita daga tsafgar yarinyar nan ba, saboda ka samu salama kuma ku samu fahimta da dan'uwanka yasa na yi muku tsakani amman hakan be wadatar ba, tun da ga shi nan har yanzu ba ku jutuwa da juna, kuma ka kasa daina kulata, har yanzu dai tana nan cikin ranka, yarinyar da ta haifarda rashin jituwa tsakaninku? Yanzu shirye shiyen auren dan'uwanka ake amman babu ruwanka komai sai dai ka bishi da ido haka ake? Ku uku kawai Allah ya bani idan ba ku hada kai ba ya kuke son zama?”

“Ba daga ni ba ne Hajiya, Abdulhamid yana ta ganin laifina ne har yanzu, ko magana nai masa sai idan yaga dama zai amsa ni”


“To ai dole ya rika maka haka, taya zaka rika bibiyar matar da ya saka? Wacce ta zama makiyiyarmu? Ta ruguza rayuwarku?”


Kallon mahaifiyar tasa yai ya dauke kai, wani lokacin idan tana yin abu kamar wacce bata taba karatu ba, ne san abunda yasa son zuciya yake rinjiyarta ba. Be ce sake ce mata uffan ba har tai fadan ta gama, sannan yai mata sallama ya fice zuwa gidansa. Da dan kuzarinsa ya shiga gidan yaransa na harabar gidan suna wasa kasancewar yau Thursday after school babu islamiya a yau. Da gudu suka zo suka masa oyoyo ya daga su sama yana dariya ya sauke sannan ya rika hannunsu suka shiga cikin falon, a falon ya sake musu hannu ya nufi kitchen gurin da yake jiyo motsin Suwaiba. Daga baya ya rumgumeta yana sumbatar gefen kumatunta.

“Madam me kike girka mana”


“Me nake girkawa dai ni da yarana kai da bazawarar ka ta dauke maka nauyin cin abincin gidana”


Ta fada tana yatsina fuska. Sai yai murmushi rabon da Halima ta aiko masa da abinci tun ranar da ya dauko ta a mota, ya juyo da ita tare da saita idanuwansa cikin nata.


STORY CONTINUES BELOW

“Kin ga abunda ke hada ni da ke mita, da rashin yarda, wanda ya baki labarin tana aiko min abincin be baki labarin ta daina ba?”


“Kana kareta ne kawai, amman yq za ayi ta daima bayan ta fara kuma silar hakan ka daina cin abincin rana a gidanka? Daman can ai irin yan barikin zaurawan nan sun fi kowa iya karuwanci”


“Abunda take min kyautatawa ce kawai a matsayina na dan'uwanta kuma kin fi kowa sani Halima na tsattsiya ce”


Yana fadar hakan ya sake ya juya ya fice daga kitchen din fuskarsa na nuna rashin jindadin kalaman Suwaiba, tabe baki tai ta bishi da kallo haushi, ita kadai ta san abunda take ji ta rasa gane wani irin so yake ma Halima? Ko da yake ba laifinsa ba ne laifin Halimar ne daman shi namiji ai kamar yaro ne, duk inda aka bi da shi can yake, ta dade tana masa maganar abincin da Halima take aika masa a office duk kuwa da kasancewar ya sha nuna mata cewar baya son maganar, ta hanyar Yayanta da ke aiki Asibiti a matsayin nurse ta samu labarin.


“Sai na ci miki mutunci Wlh, sai na bayyana halinki a gaban kowa, daga lokacin zan gani idan za ki sake bibiyar Abdallah banza ballagaza kawai, in banda jahilci taya zaka auri yaya kuma ka koma bibiyar kane, kaji iskanci, sai an tozarta ki Wallahi”


Ta fada tana kwafa sannan ta juya ta cigaba da aikinta...
AHMAD POV.

tukin motar kawai yake amman hankalinsa yana can ya tafi gurin labarin da ya ji, sai a yanzu ya fahimci a kashi 100 na kaddarar rayuwa shi ko kashi daya be dauka ba, domin shi ya da mata sai mahaifi kawai ya rasa, amman ita ta rasa abubuwa da yawa a ciki akwai farinciki akwai gata akwai mutunci, a haka kuma har tana filin sake daukar wani kalar bacin rai a zuciyarta, tunawa yai da yadda take yawan masifa wata kila saboda tana cikin damuwa ne, ta yi kokari ta jajirce da har bata haukace ba ko kuma wani ciwon ya hana ta tashi kamar yadda shi a yanzu ciwon zuciya yake neman kai shi kasa. Tunawa da yai da irin abunda yai mata a wacan lokacin da kuma kadeta da yai yasa jin wani iri, anya mai irin wannan rayuwar ya cancanci a sake shimfida masa wata bakar magana ma balle har a aikata masa wani abu marar dadi? An keta mata an keta haddin yarta shi ya fi komai tsaya masa a rai, see yadda yake kyamar auren matar da ta auri wani auren sunna ma, to ita faya zata ji an yi mata da karfi? And ayi wayarta yar da bata san komai ba? And a lokacin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa bayan kuma kanensa ne ya ketawa yar haddi, wani irin mugun miji ne wannan? Baya son ta aureta ne? Ko dole akai mata? Aunata yake a matsayin Siyama, ya zai ji idan wani ya taba masa kanwa kamar haka? And the most saddest thing bata da mai tsaya mata tun a wacan lokacin, she's the first born ya tuna a cikin wasikarta ta fadi hakan, and the other sad part is ya kara mata damuwa da zarginta da mutuwar Namra, sai a yanzu yake gode Allah da Hajiya ta hana shi daukar mataki a kai da ya cutar da innocent soul.

“Gwarzo... Ba gida za mu je ba?”


Sai a lokacin ya tuna ba shi kadai yake a motar ba, Hajiya tana baya tare da shi.

“Gida za mu je”


“Na ga ka dauki wata hanyar ne”


Sai a lokacin ya lura, bakinsa ya cikawa iska ya busar sannan yace.

“Zagoyo zan yi”


“Okay, bikin nan ya kayatar sosai fiye da yadda aka saba yinsa a shekara, wai ka gane wacce ta ci gasar nan kuwa?”


Hajiya na yin maganar zancen yaranta ya fado masa, na cewar idan ta ci zata biya musu kudin makaranta.

“Wow....”


Ya furta a fili yana jinjina irin jarumtarta da karfi zuciya. Hajiya kuma sai ta dauka da ita yake sai kawai ta cigaba da shimfida masa labarin.

“Wannan ce fa mahaifinyar su Namra yarimyar da ke tare da Baby Namra, ashe har yanzu bata manta da ita ba, tace idan ta ci sadaukarwar ta Baby Namra ce”


STORY CONTINUES BELOW

Be ce komai ba sai tukin yake a hankali yana jin wani abu na masa yawo a zuciya na rashin jindadi har suka isa gida.


“Labarin ma da aka karanta ina kyautata zaton na mahaifiyar yarinyar nan ne Halima.... ”


“Halima...... ”


Ya maimaita sunan yana kokarin juyowa ya kalli Hajiya, be taba sanin sunanta ba sai yau, duk kuwa da aikin da take a kamfaninsa, sunan da ya fi ko wane suna yi masa dadi a duniya, har yanzu yana ganin yadda ya wulakanta a kamfaninsa a lokacin da ya bukaci a canja mata position sai a yanzu yake ganin hawayen da take da irin rokon da ta soma masa tana kuka tana fadar dan Allah kar ya koreta tana bukatar aikin nan, and in the restaurant a vip 1 a lokacin da ta zauna a saman kujerar sa matarsa take zama, he remember wadansu kalamai da ta fada, wacce take nan ta yi sa'ar ba kamar ita ba, daman duk wannan take nufi?

“Oh ya rabb”


Ya furta a fili gaba daya zuciyarsa ta daure ta yi nauyi da tausayin Halima. Can ya tsinkayo Hajiya na kokarin fita motar tana fadin.


“Domin labarin da mahaifiyarta ta ba ni, yayi daidai da abunda aka fada a gurin nan kuma ga shi taje tare da yaran, ina jin labarin na gane ita ce, cikin ma uwar bata fada min duka ba, tun da wani abun sai a yanzu na ji, amman matar nan ta ga rayuwa Wallahi ban san lokacin da nai kuka ba”


Fitowa yai daga motar yana kallo mahaifiyarsa wacce ke sanye da tsadadden lace.

“Amman Hajiya ba ki taba fada min ba”


Hajiya ya kalleshi da kyau.

“Ina zan fada maka labarin makiyiyarka? Matar da kace baka son jin komai nata”


“Da kin fada min ko da a tsawace ne, ko kuma ki cilasta min saurare ai dole zan ji, wani mai imani ne zai ji labarin matar nan be ji tausayinta ba?”


Ya fada yana hade yatsunsa fuskarsa dauke ta tausayi.


“Duk lokacin da nai unkurin fada maka sai kace ba zaka saurara ba, tausayinta ne yasa na hana ka kaita kotu ai, ko lokacin da aka fada maka bata cikin hayyacinta ba cewa kai karya ne ba, saboda kawai ta kashe maka ya ne? Ni ko na san mai imani ba zai kashe rai ba sai idan wata kaddara ta fada masa, sai a yanzu da Allah ya kaddara ya bude maka zuciya ka ji komai”


Yes he remember an fada masa she's unconscious ya ki yarda, and he remember how her father beg him akan case din amman be saurareshi ba, and the slap a lokacin da ta kawo Baby Namra asibiti ya mareta har sai da ta fadi..... Ji yai wani irin abu na rashin jindadi da kyautatawa ya mamaye shi, be taba jin tausayin wani abu mai rai kamar a yadda ya ji tausayin Halima ba a yau, a waje daya kuma yana ta jinjina karfin hali da dakiyar zuciya.

  Part dinsa ya nufa yana ta tunani kala kala yes hak rayuwa take zaka ga mutum kawai sometimes a cikin farinciki amman ba san abunda yake zuciyarsa ba, ba zaka iya fassara damuwarsa ko nasararsa ba, da ace be ji labarin Halimatu ba da har yanzu be daina mata kallon makiyiyarsa ba, wata kila da Allah kadai ya san irin abubuwan da zai mata....

  A dare kwana yai da tunanin abun a ransa, duk kuwa da yasan condition dinsa rage yawan tunani yana ciki.


HALIMATU POV.

Labarina ya taba zuciyar mutane da yawa a guri kuma nima ya taba ni a karan kaina, domin sai rayuwar da tunanin gobena ya dawo min sabo. Iyakar kokarin da nai kar nai kuka a bainar jama'a ne, sai dai na zubar da hawayen da ban san adadinsu ba, an rayuwata ta lalace kuma an bata ta yata, amman na yarda da wani abu daya, ko dan yayana zan rayu, zan kara jajircewa zan tsaya tsayin daka na amsa sunan da Ummulkhar ta kira ni da shi wato Jaruma.

Rai na ya kwadaitu da zancen kudin da ta ware min a cikin albashin kamar yadda ta fada, sai dai ina tunanin karbarsu abu ne mai wahala a gurina domin zai iya zama silar da zata saka a gane ko wacece ni wanda hakan zai hanani sakewa cikin mutane.

  Ba mu tashi daga taron ba na ji alert a wayata, na naira miliyan daya, aiko a take na nemi damuwata na rasa farincikin ganin kudin ya maye gurbinta.

   Cikin murna muka fita daga taron wani abun burgewa sai muka zama abun kallo har da masu dauka hoto a tare da mu da award din da aka ba mu, ina yin gaba kadan na hadu da blessing abokiyar aikina, sam ban san ta zo taron ba sai da tai min magana mun gaisa da ita ta tayani murna sannan ta gaisa da su Namra tana fadin ashe ina da yara. Sai nai murmushi.


STORY CONTINUES BELOW

“Ke ma ai kin san ina da yaya”


“Eh amman ban dauka har hudu ba, kuma kyawawa da su har sun fiki kyau”


Dariya nai sai ta soma tambayar dalilin rashin zuwana aiki kwana biyu. Ban boye mata komai ba na fada mata cewar wani dan'uwana ya hana ni aikin ne saboda uniform din be dace da ni ba. Dariya ta fara min tana ta mamakin wautata, wai ya zan daina aikin ban je ma fada musu dalilina ba idan ba su aminta su canja min kayan ba ko kuma gurin aikin ba sai na daina amman a haka ai ba ni da hujja kuma na bar damata ne. Ta yi tamin magiyar na je gobe na fada musu haka idan basu yarda ba sai n aje aikin, ni kuma na amsa mata da to duk da nasan ba za su yarda su canja min ba, amman yanzu na samu kudina zan iya yin sana'a ta kamin na samu wani aiki, tare muka jera muka fita tana fada min wata mata da ke yawan zuwa nemana tun da na daina zuwa aikin har number wayarta ta bari tace idan na zo a kirata. Ni kam mamaki ya cika kuma tsoro ya kama ni wacece kuma? Allah yasa ba wani karin damuwar ba ne, can kuma matar Kabir ta fado min a rai wata kila ita ce, dan nasan wannan mugun Ahmad din ba zai kyale shi ba, domin ko a yanzu na lura da kallon bakincikin da yake min, na ja masa fada da mahaukaci kuma ga shi na ci gasa na san hakan ba karamin zafi yai masa ba.

  Idan na naje aikin Yunus din zan yi ma magana ko Tahir wanda shi ne shugaban sashen mu, shi kam na san ko kallo ban ishe shi ba kuma ba zai saurare ni sai dai ma ya fada min wata bakar maganar.

  A ranar gidanmu ya cika da murna ba mu kadai ba har da makotan da suka samu barin sai da suka zo taya mu murna, Inna da Mama duk tsoro ya kama su wai kar a biyo dare ace sai an bada miliyan din, har ta hana a fadawa. Ba su kadai ba ni kaina na kwana da tsoro a ranar saboda halin tsoro da kasar nan take ciki abu kadan zai tsonewa wani ido.

   Washe garin na tashi raina fes zuciyata kal babu damuwa ko kadan sai farinciki da annushuwa rabon da na samu kaina a haka har namanta, domin a yanzu bayan damuwata har da ta Abdallah tana damuna, tun daga wacan lokacin da yai min magana ban sake sakewa ba, su namra ma baki har kunne suna ta far'a, ban barsu sun je makaranta ba sai da nai kusu kashedi akan kar suje suna fadin abunda muka samo a school din, kuma su fadi gaskiya cewar kudin yana cikin account ba a hannu ba.

  Bayan sun tafi nima na shirya cikin riga da zane na atamfa na saka hijabina, sannan na shiga dakin Mama na fada mata cewar zan tafi kamfanin na nemi alfamar canjin tufafi ko gurin aiki kamar yadda blessed ta bani shawara, daman tun da dare na labartawa Mama abunda ya faru da kuma matar da ke nema, har ta farara min kuiwa yin haka daman tana da complain cewar na daina aiki ba tare da na yi magana ba ban san ko za su aminta su canja min aikin ba.

A yau ban fita ba komai ba a hannuna da sunan kawai Kabir ba duk kuwa da kasancewar zuciyata na raya min na rika masa wani abu kamar yadda na saba, domin tun a lokacin da na daina zuwa aiki na daina kai masa abincin, haka ma take away da nake sakawa a kaiwa Abdallah na daina kasacewar hanya daya ce da gurin aikina a ko yaushe ina bada kudi na ce a kai masa idan 1pm ta yi ko 12,30pm.

  Napep din da na tara akwai mutane biyu a ciki ni ce ta uku, a dole sai da ak saukesu inda za su je sannan aka kai no kamfanin wannan karon har bakin gate din kamfanin aka sauke ni, tsabanin da da ake sauke ni kusa da Kabir sai na bashi abincin sannan na wuce, babu irin dubawan da ban yi ba amman ban ga Kabir ba hakan kuma ba karamin haifar min da tsoro da zullumi yai ba, ina ta rokon Allah yasa ba mugun can yai masa wani abun ba.

  As usual sai da na gaisa da masu gadin sannan na shiga ciki, kai tsaye reception na nufa fuskarta dauke da murmushi da sauri blessed ta zo ta rumgume ni.

“Oyoyo we miss you”


Ta fada sai kace wani dade muka yi muna aikin tare, ko da yake komai gamon jini ne. A nan fira ta kaure tsakanin na da su suna ta tambayar dalilin rashin zuwana aiki na fada musu sannan suka rika taya ni murna wai blessed ta basu labarin na ci gasa, a lokacin ne nake tambayarsu macen da take zuwa nema sai Rilwal ya ce

“Ai zata zo kullum sai ta zo nemanki a nan”


Na bukaci number wayar da suka ce ta bari tace a kirata idan na zo, sai Rilwal ya nuna min ita a wayarsa, na yi ta karanta number ban gane mai ita ba, sai kawai na zuba numbobin a wayata, ga mamaki sai sunan Suwaiba ya fito, miyasa take nema anan? Ba tasan gidan mu? Kuma tana number wayata idan har son ganina take? Wata matsalar ce? Ko wani abu ya faru da Abdallah? Haka zuciyata tai ra raya min abubuwa kamin na basu amsar cewar na gane mi number, nan suke fada min cewar babu wanda ya shigo a cikinsu daga sarkin girman kan har Yunus din da Tahir, hakan yasa na nemi guri na zauna dan na jirasu, ni kaina na san na yi sammako sai dai na zo da wuri ne saboda gudun na na zo suna tsaka da aiki a hana ni ganinsu tun da komai an kamfanin a tsare yake.

  Ban yi minti goma da zama ba naji ana nuna domin sam ban lura da mutane da suke shigowa ba hankalina yana ka ce wayata, ina dago kaina nai yi arba da Suwaiba ta nufo inda nake rai a bace tana tafiya kamar ta fadi abun ka da siririyar mace.

“Kashedi na zo nai miki, ki fita hanyar mijina”


Ta fada cike da masifa tana daga murya iya karfinta, hakan yasa hankalin kowa ya dawo kaina.

“Ki fita hanyar mijina, yafi karfinki”


“Ba ki isa da mijin na ki ba ne shiyasa har kika zo baina jama'a kike min ihu, da ni nake auren Abdallah Wallahi idan na hana shi kallon wata macen ya hanu.... ”


“Ina zan isa da shi kin masa magani kin malleke shi bakar bazawara.... Yar duniya mai bibiyar mazan mutane, aure biyu kika kashe kina bibiyar mijina, marar mutunci kin zubar da yara hudu kin bar ubansu kina bibiyar nawa mijin, dan kawai ba ki san darajarsu ba...... Wani irin karuwanci ne da zaki rika aika masa abinci kullum..... Mijinki ne ko danki?”


Kalmar bazawara bata taba min zafi ba irin yau, ashe akwai ciwo idan aka maka gorin zawarci, a take na ji muzanci ya kamani tace na kashe aure ina bibiyar mijinta ko da karya ta fada wasu zasu gasgatata, na ci mutunci na a bainar jama'a ta gama da ni. Duk yadda na so na ki yin kuka sai na kasa hawaye suka fara min zuba bakina ya kulle gam na rasa me zan ce mata jikina sai rawa yake ina jin kamar na dake ta.

“Securities arrest her...”


Kamar saukar aradu haka muryar Ahmad ta dira a kunnena, da juyo idonw da hawaye na kalleshi yana tafe cikin kamfanin tare da Yunus, a lokacin da Security kamfanin suka nufo inda muke tsaye na yi zaton ni za su rike, sai na ga su kama Suwaiba macen cikinsu ta fisgeta da karfi.

“Ku rufe min ita a kamfanin nan sai ga uban waye mijin naki da za ki zo cikin kamfanin mu kina mana hankali how dare you”


Ya sake fada, a rikice na kalleshi ina hawaye. Sai ya karaso cikin kamfanin yana kallon amsu kallon fadan mu fuska a hade.


“Ku kuma me kuka tsaya yi kuna kallo ana insulting dinta instead of ku yi wani abu kowa ya saki ido fools”


Yana fadar hakan sai kowa yai saurin kama gabansa, shi kuma ya wuce ta gabana ba tare da ya kalleni ba ya bi hanyar da zata sada shi da office dinsa.10Rasa nai abunda zan yi, na bishi nai masa magana ko kuma na zauna ko na tafi gida? Ya Abdallah zai ji idan aka ce wani ya tsare masa mata saboda kuma a kamfaninmu, no ba saboda ni ba ne saboda ta yi hayaniya ne dan haka babu ruwana a ciki.

   Akai akai mutane suke ta kallona, har na soma tsarguwa, tashi nai koma can wani gefe da ba a ganina sosai na zauna, wata zuciyar na fada min cewar naje nai maganar aikina sai dai kuma idan na yi maganar aikin aka koreni ba tare da an gama maganar Suwaiba fa?

  Na kusan awa daya a gurin ina ta tunanin abun ne naje nai masa maganar Suwaiba ko ta aikina, amman ina ruwana da matar da ta ci min mutunci a bainar jama'a, ai kara a kira Abdallah din domin na san ba da saninsa ta zo nan ba.

Ban raba daya biyu ba, aka aiko wata mai sanye da suit kirana, haka ta saka ni a gaba ina baya har muka isa office din Ahmad. A one of visitors chair na tarar da Abdallah zaune, ni kuma sai na tsaya daga bayansa tun da ba a bani izinin zama ba, juyowa Abdallah yai ya kalleni sai kuma ya kawardar fuskarsa ba tare da yace komai ba.+

“Look man aiki bake fa zaka tsayar da ni anan for more than 20 minutes, ba kallo office dinka na zo yi ba”


Abdallah ya fada a fusace, hakan yana nuna alamar Abdallah ya dade da zuwa kenan. Da hannu Ahmad yai min alama dana zauna ba tare da ya kalleni ba. Ba musu na zauna a kujerar da ke kusa da Abdallah ina ta kallonsa shi kuma sai yai kamar be san da ni a gurin. After like 5 minutes Ahmad ya kalleshi yace.

“Aiki nake yi ko baka gani ba? So kake na aje aikin na kula ka? Kai da ka zo ganina ba appointment? And you got lucky na barka ka shigo har office dina ka zauna tare da ni, ban barka visitors room ba?”


“Ba kai na zo gani ba, Matata na zo na ji dalilin riketa da kuka a nan”


“Bata fada maka abunda tai ba? Ko a hanya kawai za mu ga mace a hanya mu dauko ta?”


Babu wasa a fuskar Ahmad a yayinda yake wannan maganar, kamar yadda Abdallah ma nake ganin abun ya masa zafi.

“Matarka ta zo nan tana mana ihu na rashin tarbiya tana fada akanka, tana fada da ma'aikaciyarmu ba za mu dauki wannan ba”


“Kai kuma ka rufe ta, saboda gaka hukuma”


Ahmad ya kwanta jikin kujerar yana masawa Abdallah cikin zafin rai.

“Yes ko akwai abunda za ka yi? Kana ta son nuna isa, bayan you are nothing wanda be isa da iyalinsa ba har ya isa yace zai fito waje yai yi takama? It's a shame”


“Family issues ne wannan babu ruwanka a ciki”


Abdallah ya fada yana kokarin danne fushinsa.

“Family in my company? Public place?....”


Ganin abun kamar zai zame musu fada yasa nai hanzarin cewa.

“Na yafe ni tai wa cin mutunci na yafe mata, dan Allah ka barta ta tafi”


Ina fadar hakan Abdallah ya daga min yatsansa alamar babu ruwana a ciki, Ahmad kuma ya tari numfashina


“To ni ban yafe ba...”


Ya fada kai tsaye yana kallona. A lokacin ne Abdallah ya mike tsaye cikin bacin rai ya daka masa tsawa.

“And who are you? Mi kake takama da shi”


Wani shegen kallo Ahmad yai ma Abdallah, mamaki ya kama shi wato a maimakon ya bada hakuri ya karbi laifin matarsa amman sai neman kareta yake, hakan ya kara tabbatar masa da cewar Halima bata da gata domin da tana fa shi da yau ba shi zai yi fadan nan ba wani wanda ya tsaya mata ne zai yi shi.


“Kudi Alhaji......... ko baka gani ba, na isa ne isar ta isa ma matuka, kawai dan kun ga mace bata da gata sai ku yi ta taka ta any how, idan yar wani mai kudi ce ko kuma tana da wanda ya tsaya mata shashanshar matarka bata isa ta taka kofar gidansu ta fada mata bakar maganar magana ba balle har ta shigo gurin aikinta tana kiranta da suna kala kala tana cin mutuncin, so warn your wife for the last time, bilahil'azee idan ta one bad word daga bakin matarka zuwa ga Halima sai a rufeta a cell ba acikin kamfanin nan ba”


STORY CONTINUES BELOW

Abdallah yayi murmushi yana duba agogon hannunsa, sannan ya kalleni ya sake kallonsa.

“Ba kai ne mutumen da yace idan yarsa ta mutu zaka rufe Halima ba? Ba kai ne mutunen da baka yarda da kaddara ba? Ba kai ka mareta har sai da ta suma ba? Kai duk abunda kai mata ai saboda kana ganin bata da gata ne, yanzu har kana da bakin da zaka fadi haka? Mi ka sani a akan Halima? Baka san komai ba akan rayuwarta fadi tashin da tai ba ka sani ba, sai a yanzu? Tsohon dan iska shiyasa ka bata wando da riga ta saka so that ka rika kallon siraicinta? So kake ka burgeta a yanzu? Shiyasa zaka fara acting kamar wani mutumen arziki... ”


Su suke fadan ni nake kuka, Ahmad be sake cewa komai ba, ya danna dan wani maballi da ke gefen teburinsa, ba a dauki lokaci ba sai ga security kamfanin sun shigo.

“Ku fitar min da shi bana son hayaniya.... ”


Da sauri suka nufi gurin da Abdallah yake saye sai kuma suka saka rika shi sai kokarin masa magana suke.


“Karku taba shi zai fita da kanshi.... Abdallah dan Allah”


Ya fada ina masa magiya, kallo yai ya dauke kai ya juya ya fice daga office din rai a bace, sai security din suka bishi a baya. Karasa matsawa nai kusa da teburin na hade hannayena ina kuka.

“Ka saka a saki matarsa dan Allah, na san ka tsaneni, duk abunda zaka yi Saboda ka musguna min ne  ko kuma wani na kusa da ni, idan har ya zama dole sai ka dauki mataki akan abun dan Allah ka hukunta ni ba matarsa, saboda ni komai ya faru...”


Ba tare da ya kalleni ba ya nuna min wata kujera dake can kusa da kofa.

“Je can ki zauna”


Abun ka da mai jiran umarni sai na nufi kujerar na zauna ina kuka a hankali domin har ga Allah ban jidadin da ran Abdallah ya bace ba, kuma ban jidadin abunda Ahmad yai masa ba.

“Idan kin gama kuka ga tissue box kusa da ke ki goge fuskarki, akwai ruwa a fridge”


Yana fadar hakan ya dauki laptop din da yake aiki da ita ya fice ya bar ni a katon office din, ni ko ban fasa aikin kuka ba har sai da nai wanda ya ishe ni na dauki tissue na goge hancina da idona sannan na bude fridge din na dauko gorar ruwa na sha, domin makoshina ya gama bushewa. Bayan na sha ruwa na koma a inda na tashi na zauna. Kalamansa na dazun ne wuka rika dawo min a rai kamar yadda na Abdallah ma suka tsaya min, na rasa ganewa Ahmad ya fara saukowa daga fushin da yake da ni ne? Da har zai ce idan Suwaiba ta sake fada min bakar magana sai ya rufe? Ya bar ni na shigo har office dinsa ya fada min idan na gama kuka na goge fuskata na sha ruwa... Ina tsaka da tunanin sai gashi ya shigo tare da Yunus yana ta murza wani karamin turare a hannunsa, kallona kawai Yunus din yai be ce komai ba ya cigaba da maganar da yake da Ahmad bayan ya gama ya fice wata matar ta shigo da kofin tea guda biyu ta aje a saman teburinsa sannan ta fice.

  Daukar dayan kofin yai ya nufo inda nake zaune ya miko min, mamaki ne ya hana ni karbar cup din har sai da ya kalleni. Sai nai saurin girgiza masa kai na mike tsaye.


“A a na gode”


Kallo yai for few seconds sannan ya furta.

“I'm sorry....”


Ya juya yana kurba tea ya nufi teburinsa.

“Be kamata ka bani hakuri ba, duk abunda ya faru laifina ne, ni na ja komai sanadina komai ya faru kuma kamfaninka ne kana damar ka yi duk irin hukuncin da kake so....”


“Akan dora miki laifin kisan Baby Namra da na yi”


Ta tari numfashina, wannan karon mutuwar tsaye nai, da gaske hakuri yake ba ni? Ahmad din ne ko wani dai dabam, na dan juya na kalli bayana na sake kallona.

“Ki yi hakuri dan Allah”


Ya maimaita min da yaren da na fi ji. Har lokacin kallonsa na ke gaba daya kaina ya gama kwancewa, mi ke faruwa ne? haka na tsura masa ido ina ta masa kallon da ban san na minene ba, mamaki kadai ko kuma har da tuannin maganar Abdallah? Da gaske hakuri yake bani ko kuma wani abun yake shirya min saboda na kashe masa ya? Kamar yadda yake zargina?

STORY CONTINUES BELOW

“I say sorry”


Na hade yawun bakina.

“Ba komai ba, wannan ma yana cikin kaddarata ne”


Ina fadar hakan na juya zan fice daga office din.


“Ina za ki je?”


“Gida”


Na fada ba tare da na juyo ba, idona na cika da hawaye.


“Aikin fa?”


“Na aje”


“Saboda me?”


“Tufafin da nake sakawa be dace da ni ba”


Na amsa cikin muryar kuka, har yanzu na kasa yadda Ahmad ya bani hakuri akan yarsa, har zuciyarsa yake bani hakurin? Miyasa? Taya yanzu ya yarda ba ni na kasheta ba? A take wasikar da na rubuta a jiya ta fado min a rai, ya fahimci ni ce kenan, kuma zuciyarsa ta bude har ya iya yarda a yanzu ban aikata ba, Al-hamdulillah akalla wani abun ya ragu daga bakincikin da yake raina, a yanzu yana kallona a matsayin marar laifi tun da har ya iya ba ni hakurin. Shigowar Yunus ne yasa nai saurin share hawayena sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka nake ba.

“Lafiya?”


Ya tambaya yana kallo da mamaki a fuskarsa. Ban saurari abunda Ahmad ya fadawa Yunus din ba domin har lokacin kokarin tsayarda kukan farincikina nake.

“Biyo ni muje”


Yunus din ta fada ni kuma na juya ina rokon Ahmad amman ko kallona be yi ba.

“Dan Allah ka saki matar can dan Allah”


Ganin Yunus din ya fice yasa nima na bi bayansa, yana gaba ina bayansa har muka isa wani guri, hannunsa ya kai ya tura kofar sai ya bude ya shiga ni kuma na tsaya a waje har sai da ya yi min izinin shiga.

  Dan madaidaicin office ne mai dauke da desktops har biyu a teburi daya, sai dan karamin fridge da ac makale a dakin daga gefen ac window ne mai kofa biyu wanda yake bawa mutum damar hango windows din office din Ahmad kamar yadda shi ma zai iya hango na cikin office din idan an bude.


“Kin iya typing ai ko?”

Na gyada kai.

“Yauwa to duk emails din da za a turowa kamfanin nan anan zai shigo wanda kika ga ya dace oga ya gani sai ki masa forward kai tsaye zuwa email dinsa, idan kuma za a aika wani abu to all ma'aikatan mu ke za a bawa ki yi typing sai ki tura, sai dai daga yanzu lokacin tashi aikinki ya canja daga 3 zuwa 5pm, amman ba kamar wacan ba ne nan ana bada abinci saboda zaman da kike”


“Ban gane ba....”


Na fada a hankali cikin sanyayyiyar murya.

“Yanzu nan ne office dinki congratulations”


“Da gaske?”


“Ga zahiri kina gani”


A take idanuwa suka kara cika da kwalla.


“Na gode”


“Oga ya kamata ki yiwa godiya”


“Dan Allah ina rokon alfarma”


“Na san kai ma oganka ne, amman kuna da kyakkyawar fahimta wata kila za ka iya yi masa magana ya ji, dan Allah ka saka ba ki ya saki matar da ya saka a ka kulle”


“Ya sake ta ai, tun dazun mijinta ya tafi da ita”


“Da gaske? Amman cewa yai ba zai barta ta tafi ba”


“Gaskiya tun dazun aka wuce da ita”


Dan murmushi nai na juya ina kallon office din. Shi kuma ya juya fice ya bar a gurin tsaye n rasa abunda zan yi murna ko kuka ko mamaki?

  Kasa komai nai a cikin office din sai kawai nai zaune ina ta kallon office din, misalin daya da mintuna wata ta shigo da abinci ta ba aje min, takeway ne na jalof da naman kaza a ciki. Nikam ban ci ba duk kuwa da kasancewar ni kadai ce a dakin sai na saka abina a jaka.

  Biyu na yi na shiga bandakin da ke office din nai alwala na fito nai sallah sannan na dauki wayata na kira gida na fadawa Hafiza ta fadawa Mama an canja min aiki dan haka yau sai 5pm zan dawo.

  Har karfe uku ban duba email din ba ban kuma tura komai ba, har sai da Yunus din ya sake dawowa ya nuna min yadda ake da kuma wandanda ya kamata a turawa Ahmad din.


STORY CONTINUES BELOW

Karfe biyar na yi na dauki jakata na fito daga office din, ko da na fito Rilwal da Blessed basa gurin sun gama aikinsu sun tafi.

  A lokacin da na isa gida na labartawa Mama da dukan yan gidan abunda ya faru tsakanina da Ahmd da kuma abunda Suwaiba tai, a nan Hafiza take fadar wai Suwaiba ta kirata kwanan baya tana tambayar inda nake aiki ita kuma ta fada mata ba ta yi tunanin wani abun ba ashe dan ta samu zuwa ta ci min mutunci ne.

   Su namra na bawa abincin office din, suna ta murna sun ga har da nama a cikin gurin rabon abun har ya so zame musu fada sai da Husna ta shiga tsakani.

Bayan na huta na ci abincin da aka girka gida, na watsa ruwa na sake shiryawa cikin wasu tufafin na nufi bankin da ke kusa da mu, kudin gasar da na ci nake son cirowa na samma kowa wani abu a ciki sannan nai sauran lalurorin da suke gabana. 200,000 na ciro na saka a jaka ta cikin tsoro domin a lokacin an fara kiran sallah sai nake ganin kamar akwai wasu a biye da ni duk kuwa da ba ni kadai na ciri kudi a atm din ba.

  Ina yin gaba kadan sai wata farar mota mai bakin gilashi ta faka a gabana, na san ba zai wuce Abraham ba amman hakan be saka ni jin tsoro ba har sai da ya bude motar ya fito.

“Ki daina cirar kudi a atm idan yamma yayi, wani zai iya sa miki ido wasu ma ba diban kudin suka je yi ba kallon masu cire kudin suka je yi”


Ban ce masa komai ba nai gaba kamar zan wuce sai ya saka ya cin min.

“Kin gani jin labarin ki ya kara min kaunarki, kuma ya kara kafafa min guiwar aurenki, ni kadai zan rayu dake ba wata kyama ba wani tunani, ina da kudi zan sakar miki su ki jidadin rayuwarki”


“Ba kudi ne jindadin rayuwa ba, da su ne da masu kudin ba su shiga kunci ba, ni farinciki nake nema da kwanciyar hankali”


“Na sani shiyasa zan baki ai”


“Baka isa ka bani farinciki ba, baka isa ka keta min haddi da aurena ba har nai ciki yanzu kuma ka biyo ni kace zaka aureni, addininmu dabam al'adarmu dabam, baka san zafin da nake ji a raina ba, baka san yadda mace take ji idan an keta haddinta ba, saboda kai namiji ne, mace tana jin matukar bakinciki ko hannunta a rike balle a keta haddinta, kasan saboda me? Saboda martabarta kimarta mutuncinta jindadinta farincikinta yana a nan ne, to kai ka zubar min da duka wannan ka saka uwar mijina da mijin da ya sake ni suna min kallon karuwa wacce ta zubar da mutuncinta tai fasikanci da wani namijin har ta samu ciki, wannan tabon ba zai taba gogewa ba, idan kuma ka zo ne saboda ka kashe ni da bakincikin kallonka da nake kana da dama”


Na karasa cikin kuka.

“Idan nisanta kaina da ke zai saka ki farinciki, i will do that, amman bana da niyar saka ki bakinciki, sai dai sama miki farinciki ada bakincikin fyaden da nai miki kawai yake damuna, amman a yanzu har da rayuwar kuncin da kike ciki, kina da zuciya mai kyau kuma kina da hakuri”


Bayan ya fadi haka ya bude motarsa ya shiga yai mata key ya bar ni a gurin tsaye. Sai da na daina hango motarsa sannan tari napep na shiga. Ko da na isa gida har an gama magariba, bayan na sallame mai napep na lura da motar Abdallah, na yi zaton yana cikin gidan ne sai ji nai ya kirani, ina juyowa na hango shi ya fito hanyar masallacin unguwar sai ya nufi gurin motarsa ya tsaya, hakan yasa nima na karasa kusa da shi na tsaya.

“Ki yi hakuri da abunda Suwaiba tai miki, ban san yadda akai taje gurin ba kuma ban fada mata cewar kina kawo min abinci ba, kin san zuciya kowa da irin tasa ba tai tunani ba a lokacin da ta aikata abunda ta aikata dazun kuma ban jidadi ba”


“Tana da gaskiya Abdallah, tana tsoron wata ta karbe nata miji mai karamci da sanin ya kamata, mai kula, mai tausayi, mai taka tsantsan akan komai, kai kadai ka yarda da ni Abdallah baka taba yarda cewar na aikata laifi ba, kai kadai ka yarda cewar ban aikata zina, kai ne kadai ka yarda fyade ka min har na samu ciki, amman Hajiyarka da Abdulhamid ba su yarda da ni ba, kai na zarga a lokacin da aka min fyaden kuma na fada maka, amman gujeni ba baka kyamace ni ba, baka fasa so na ba, baka kasa taimaka min ba, so na be taba sa ka nemi aikata alfasha da ni ba, baka taba kyamar yayana ba, Wallahi ina son ka Abdallah ina son ka har kasan raina”


Na karasa cikin kuka mai tsanani. Har ga Allah ban taba jin son wani da namijin a raina kamar yadda nake jin Abdallah a raina ba, sai bayan komai ya lalace na gano shine mutumen da ya dace da ni.

“Ke dai ba kya gajiya da kuka, shiga ciki Suwaiba tana jiranki”


“Ina son na fada maka wani abu, mutumen da yai min fyade, ya dawo yan so na”


“Wooo What....!”


Ya furta da karfi muryarsa na amayar da mamakin da ke cikinsa.

“Waye? A ina ya ganki?”


“Labari mai tsawo ba zai yiyu a yanzu ba”


“Waye shi kin san shi ne?”


Na girgiza kai.

“Ban san shi ba, sunansa Abraham, dan sanda ne, yana aiki a unguwar gwaza, kuma shi ba musulmi ba ne”


Na daga kaina sama ina shanye kuka.


“Abraham.....”


Ya maimaita sunan sannan ya jinjina kansa.

“Shiga ciki za ku yi magana da Suwaiba”


Na gyada kai alamar gamsuwa sannan na saka hannuna na share hawayena sannan na juya na nufi gidanmu. Ko da na shiga na samu Suwaiba zaune falon mama tana ta rutsar kuka kamar ba ita ba, tana ganina ta soma bani hakuri tana fadin na yafe mata, a iya sanina Abdallah baya duka balle nace dukanta yai ya cilasta mata zuwa ta ba ni hakuri sai dai idan wani abun ya fada mata ko kuma cilastata yai.ABDALLAH POV.

Zuciyarsa cike take da tunanin abunda Halima ta fada masa, ba sau daya ba ya sha jin sunan Abraham a gurin Abdulhamid, sai dai da kamar wuya ya iya fada mta kai tsaye idan har shi din ne? Mi zai saka ya tonawa kansa asiri? Mi mai zai saka yayi mata fyaden tun farko? Miyasa yai shigar yan fashi? Sai dai ya yarda Halima ba zata masa karya ba, tun da ita din bata san Abraham ba, kuma bata san cewa shi din ba musulmi ne ba, idan har ba shi ya fada mata ba.

Yana tsaye jikin motar Suwaiba ta fito daga cikin gidansu Halimatu ta nufo i da yake da hijabinta har kasa, be tsaya jiran ta karaso ba ya bude side dinsa ya zauna yai ma motar key tana shiga ya tashi motar.

  Ta yi zaton hanyar gida zai nufa sai ta ga ya dauki hanyar family house dinsu.2

“Doc baka hakura ba?”


Ta tambaya cikin kuka, ko kallon inda take be yi ba har ya shiga titin unguwarsu.

“Na ba ka hakuri kace ita zan bawa hakuri ita ma na bata, amman be isa ya saka ka yafe min dan abunda nai ba”


Sai a lokacin ya kalleta.

“Dan abunda kika yi? Da ne ma? Kin san irin kuncin da Halima take fuskata kike neman kara mata wani? Ko ba u so a tsakanina da ita ai ita din yar'uwata ce kuma kin sani, ko dan yan'uwantakan da ke tsakaninmu be isa ya saka ki raga mata ba ko da ma ace ita ce ta nemi fada da ke? Ko karuwata ce ai ya cancanci ki kyaleta saboda mutuncina, amman wai dan shashanci da aurena akanki ki shiga public place kamar nn kina magana any how, idan auren zan yi kin isa ki hana ni ne ko fadan ki sai ya saka na fasa?”


Tun da ya fara fadan take kuka har ya faka bakin kofar gidansu.

“Da gaske sakina din za ka yi?”


“Ko dai ban sake ki ba, dole na samawa su Inteesar wata uwar mai tarbiya da sanin ya kamata”


Da sauri ta hade hannayenta.

“Dan Allah kai hakuri, ka sake ni idan sakin zai saka ka huce haushi daga baya sai ka maida ni amman karka kara aure dan Allah, wallahi na bari ba zan sake ba”


“Yanzu kuma na gano har da hankali baki da shi, idan aure zan yi kin isa ki hana ne? Ba a aure na aureki? fitar min a mota”


Ya fada a tsawace fuskarsa babu alamar wasa.

“Dan Allah ka yi hakuri...”


“Nace ki fita....”


“To yaushe zaka dawo ka dauke ni?”


“Ban sani ba”


Yadda ya daka mata tsawa ne yasa ta saurin bude motar ta fita. Sam bata taba ganin Abdallah a cikin irin wannan yanayin ba, su kan samu sabani wani lokacin ko da shine da gaskiya sai tai fushi da shi a haka kuma zai bita ya bata hakuri su shirya, amman be tana yunkurin fada mata bakar magana ba, yau kam ta kai ya saka hannunsa ya mari fuskata hakan be masa ba sai da ya cilastata ta je ta bawa Halimatu hakuri abunda yafi kona mata rai kenan, bayan yai mata baraza da saki yanzu kuma ya cilasta mata zama gidansu har yana zancen kara aure.

Lallai sai yanzu ta tabbatar ba kadan yake son Halimatu ba, saboda kawai ta taba yau duk yai mata wannan har yana fadar wai ta taba mutuncinsa, bata kara jin ta tsani Halimatu ba sai da yai reverse da motarsa ya barta bakin gate din tsaye tana kallonsa.

  Kai tsaye gidan Hajiyarsa ya nufa, har lokacin tunanin abunda Halima ta fada masa yake, yana ta neman dalilin da zai saka mutumen yi mata fyade, yana bukatar fadada bincike, kamar yadda yake bukatar jin komai daga bakinta.

  Sai da yai parking sannan fita daga motarsa ya nufa kofar falon Hajiya wacce ke bude, hango ana mopping yasa shi tsaya bakin kofar yana kallon Hajiyar wacce ta nufo inda yake rike da filo. Fitowa tai waje harabar kofar da aje fillon saman wani center carpet da aka shinfida mata gafen kofar ta zauna, tana tsastsagar hakora hakoranta biyu na makka suna bayyana.

  A gabanta yaje ya zauna, yana mika mata gaisuwa.

STORY CONTINUES BELOW

“Lafiya Kalau, Husaini ya gida? Wani gurin ka fito ne hala?”


“Eh Suwaiba na kai gidansu”


“To wani abu suke a gidan ne?”


“Kai ta nai ta kwana biyu dai”


Hajiya ta tashi daga kishingiden da take tana kallonsa abunda bata taba ji ba.

“Ban gane ta kwana biyu ba? Miya faru? Tsabani kuka samu ne”


Be boye mata komai ba daga abunda ya faru har hakurin da ya saka ta bawa Halimatu, a maimakon Hajiya ta bata laifin sai ta koma ganin laifin Abdallah.


“Wato sai yanzu na gano ba karamin so kake ma matar nan ba, nima dan ina mahaifiyarka ne na hana ka kuma ka hanu, miyasa za ka ga laifin Suwaiba? abunda Halima take ni kaina ina jin haushi balle kuma ita da take matarka”


“Matata Hajiya na sani, amman ba zan lamunci matata ta ci mutuncin yan'uwana ba, ko akwai so ko babu Halima jinina ce, yadda mahaifinmu be yarda mu raina yan'uwansa ba haka ba zan yarda ni matata wacce na auro take karkashin kulawata ta raina min yan'uwa ba, ta tsaya a matsayinta na matata, Halima kuma tana nan a yar'uwata”


“Uhm Allah dai ya kyauta idan baka mutu ba komai gani kake, ita ma dai ban da iskanci ya zata rika aika maka da abinci guri aiki neman suna? Bayan tasan kai kanen mijinta ne? Wallahi yarinyar nan bata da kunya sam na raina tarbiyarta”


“Hajiya kin dai tsani Halima kuma bata miki komai ba, matsalarta daya ta auri Abdulhamid kuma Abdulhamid din nan danki ne, ina laifi ta taimaka masa ta aure a halin da yake ciki? Amman kin dauki tsana kin dora mata bata miki komai ba Hajiya, yanzu ai zaki ga ranar ta, zaki gane ta yi jihadin auren danki, ba aure zai yi ba? Yanzu ba budurwa zai auro ba? Duk wanda be san ba shi da lafiya ba yanzu zai sani, ke da shi yanzu za ku gane idan Halima tana da hakuri ko babu”


Tun da ya fara maganar ta zuba mishi ido, ta rasa gane wani irin so yake ma Halima nan, da baya ganin laifinta kuma baya son a ga laifinta.


“Ta dai rubuce ka ta shanye Huisani ina tunanin ko ni da nake mahaifiyarka ba ka so na kamar yadda kake son matar nan, bata samu kan dan'uwanta ba kai ta samu kanka shiyasa kullum ciki mata bauta kake ita da yayanta”


Murmushi yai.

“Hajiya miye laifin Halima dan ta auri Abdulhamid kuma bata aureni ba? Kuma ba cewa tai dole sai ta aureni ba”


“A lokacin da ka ce min kana son ka aureta, wallahi na yi murna sosai, kuma na jidadi domin na fi kowa son hada zumunci da iyala Malam Usman saboda alakarsa da mahaifinku, kuma ita wannan Suwaibar ba kiba take ba zaka auro mai dan kubakuba Wallahi naji dadi tunda ita Halima jikinta luwailuwai yake, aa wai kawai sai na ji zance ya canja ban san yadda akai ta ja hankalin Hassana ba ko dan tana ganin kamar ya fika arziki oho, shi da ba ruwansa da zancen aure ma taja hankalinsa har ya zo da maganarta, kuma bayan tasan kana sonta, yanzu da auren ya dora da sai ka rika kallonta a gidan dan'uwanka kuma kana sonta? Wani abun haushi ma har da aurenta take neman maza waje ko shiyasa ta aureshi dan ta samu damar hakan Allah masani, yanxu kuma aure ya mutu kana nuna alamar sonta taya zamu shirya da dan'uwanka? Kuma jama'a ku ce musu me? A family ayi ta mana kallon tumakai”


Kamar yace wani abu sai wata zuciyar ta hana, ya san dai duk yadda zai yi ma Hajiya bayani ba fahimta za tai ba, ba kuma zata daina ganin laifin Halima ba, shi kanshi be jidadin abunda tai ba a wacan lokacin sai dai ya dauki abunda ta aikata da rashin tunani da kuma kaddarar da ke binta.

Agogon wayarsa ya kalla.


“Hajiya zan wuce gida sai da safe”


“Allah ba mu alheri, na manta ban fada maka ba, surukan Hassan sun kira sun roki alfarmar a daga auren har nan da December”


STORY CONTINUES BELOW

“Sun kara wata hudu kenan”


“Allah ya kaimu ya sanya alheri”


“Amin”


Daga haka ya juya ya fice daga gidan.HALIMATU POV.

A daren na rabawa kowa abunda zan bashi, babu wanda be yi murna ba. Washe gari aka tashi da hadari a garin sai dai hakan ba hana ni saurin shiryawa yarana suka wuce makaranta ba, ni kuma na shirya na nufi gurin aiki ina ta Allah Allah kar  a sako da ruwa. Na yi sa'ar samun napep na shiga ina fada masa inda zai kai ni,   mu tsaka da tafiya ya soma nuna min wata mota da ke binmu mai motar na mana hannu da mu tsaya. A lokacin da na leka sai na gane Abraham ne na rasa yadda zan yi da shi, me zan masa ya fahimci bana son ganinsa ma balle saurarensa. Ban bar mai napep din ya tsaya ba sai da muka kusan isa kamfanin sannan na bukaci mai napep din ya sauke ni, mai napep din na yin parking Abraham ya faka gaba da mu kadan ko kudin shi ban bashi na nufi gurin da Abraham din yake rai a bace. Ko da na isa ya sauke gilashin motarsa aiko take na nufeshi da masifa.

“Me kake da bukata ne? Miyasa zaka rika bibiyarta? Bana son ganinka bana son wata alaka ta shiga tsakanina da kai, dan girman Allah ka kyale rayuwata na huta”


“Ihu fa kike yi? Ba ki tsaya kin saurare abunda zan fada miki ba, na san ba kya son ana ganina a gidanmu shiyasa na biyo napep din da kika hau”


Har na bude baki nai magan sai na ji tsayuwar mota a bayana, juyowar da zan yi na yi arba da Ahmad yana sauke gilashin motarsa.

“Lafiya?”


Sai na kalleshi na kalli Abraham sannan na sake kallonsa na ce.

“Lafiya kalau”


Ban san dalilinsa na tsare Abraham da ido ba, sannan ya sake kallon yace.

“Shine mutumen da yake bibiyarki?”


Na kalli Abraham wanda yai saurin tada gilashin motarsa yana mata key.

“A a makocin mu ne”


Be sake ce min komai ba ganin Abraham din ya bar wajen, sai shima yai ma motarsa key ya karasa cikin kamfanin, sai a lokacin na sallami mai napep din na karasa cikin kamfanin da kafa, ina shiga abokan aikina suk fara min murn wai an canja min aiki an bani wanda ba shi da wahala kuma mai albashi da mai tsoka, na yi murna kamar yadda su ma suke tayani murnar sannan na wuce office dina ina sanye da tufafin da na fi so kuma suka fi karbata wato abaya.

  Ganin Ahmad da nai a cikin office din tsaye jikin window ya bawa kofar baya hannayensa duka biyu zube a aljihu, gaba daya office din kamshin turarensa yake. A zatona ko na yi latti ne ko kuma wani abun na aikata ba daidai ba.

“Ina kwana ranka ya dade”


Be amsa min ba be kuma juyo ba, sai yai kamar be san da n shigo office din ba, wata kila kuma be san na shigo din ba, tun da ban yi knocked ba, hakan yasa na juya na fita daga office sai na tsaya daga bakin kofa nai knocked, ima ta jira ace na shigo amman shiru be ce min ba, ni ko na dage ina ta kwankwasa kofar a hankali. Can dai na gaji da tsayuwa sai na dan tura kofar a hankali da zimmar lekawa na ga ko ya nufo kofar ko kuma zama yai ko wani abun yake, kamar munafuka haka na leka office din kamar hadin baki sai muka yi ido hudu da shi ya juyo daga jikin window yana kallona da mamaki, saurin komawa nai na rufe kofar duk sai kunya ta kamani, amman hakan be saka na fasa knocked din ba, har lokacin kuma be ce min na shigo ba ko na tafi, lallai wannan mutum akwai girman kai tsinya, a gurin nai ta tsayuwa da na gaji na nemi guri na zauna, zan iya shiga yace na shigo ba tare da ya bani izini ba, tunda kamfaninsa ba, ko da yake na ga alamar kamar ya sauko daga yadda yake ba kamar da ba.

  Ina jikin kofar ya bude ta da dayan hannunsa yayinda dayan kuma yake cikin aljihu.

  Tsaye yai yana kallona ni kuma na tashi tsaye ina sadda kaina kasa.

STORY CONTINUES BELOW

“Office din nawa ne ko naki?”


“Amman ai kamfanin na ka ne, kai ke da ikon office din”


“Office din nawa ne ko naki?”


Ya sake tambaya.

“Nawa ne”


“Idan wani abu ya bata a office din nan ke za a tuhuma, ba a farin office bude kamar yadda kikai, ki rika kula da wanda zai shigo ko ya fita a office din”


Ya karasa yana nuna min security camera dake bakin kofar office din, sai a lokacin na lura da ita.

“Ke zaki bawa mutum izinin shiga office dinki ba wai ki tsaya jiran ya baki izini ba”


“To idan na shiga kace na maka ba daidai ba fa”


Barin jikin kofar yai ya karasa gaban teburin aikina yana duba wasu takardu dake wajen. Hakan yasa na shiga office din naja kujerata na zauna. 

“Me kake nema?”


Be amsa ni ba sai duba takardun yake har ya dauko wata takardar ya nuna min ita saitin fuska.

“Wannan.....”


Juyawa yai ya nufi kofa har zai fice sai kuma ya juyo ya kalleni da manyan idanuwansa masu daukar hankali.


“Miyasa ba ki yi reporting mutumen nan gurin police ba?”


“Shi ma ai dan sanda ne, kuma yace min ya tuba ya ba ni hakuri, kuma yace zai musulunta ya aureni”


“Dan sanda? Ya akai kika sani?”


“Ranar da naje kai kara a office din akan shi sai n same shi a office din kuma kamar shi ma yana da mukamin a cikinsu m dan oga ake kiransa”


Dawowa yai gaban teburin ya tsaya yana kallona.

“Fada min one good reason daya saka shi yi miki fyaden a wannan ranar byan kin ce dan sanda ne, da kakin ya tafi”


Kallonsa kawai nai na ki na amsa masa, shi kuma ya tsare da ido irin na babba da yaro, fuskarsa na nuna alamar ya fusata.

“Ok fine...”


Ya furta yana dauke idonsa daga kaina zuwa ga takadar da ke hannunsa.

“Fuska a rufe da bindiga mijina suka je nema a lokacin baya nan shine suka ce za su bar masa sako”


“So yanzu kin yafe mishi kenan? And you believe zai musulunta, kina ganin da gaske yayi nadamar da zai saka ya iya bayyana knsa a matsayin wanda yai miki fyade? Kina ganin zai yrda ya bar aikinsa da sana'ar saboda ke? Domin bayyana kansa a matsayin wanda yai miki fyade yana nufi rasa komai nasa ne, and what makes you think musulunci da gaske zai yi shi? Baki tunanin idan ya samu sa'arki zai iya aurenki ya dauke ki ya maidaki wani gurin inda baki isa ko harrarsa ki yi ba, addinin kuma sai yaga dama zai yi?”


Na yi shiru ina ta nazarin kalamansa.

“Fada min miyasa ya dawo gurinki?”


“Yace yana bukatar haihuwa, saboda zai iya mutuwa a ko yaushe”


“Hakan yana nufin yana neman haihuwa kenan be samu ba, sai da yai min miki fyade that's why ya kawo kansa, ina yar'uwar takardar nan?”


Ya karasa yana nuna min takardar, a take na shiga dubawa zuciyata cike da tunani, duk wani duba takardun da nake idonsa na kaina.


“Kin san wani abu? Kina da saurin yarda da mutane, kina da tsoron fushin wasu, kina iya shanye bakinciki dan wani yai farinciki, sune abubuwan da suke kara saka ki a damuwa, rayuwarki abar tausayi ce Wallahi, a yanzu ma za ki iya fadawa a wani tarkon”


Ya fada yana kallona kamar ba shi yai maganar ba, domin bubu alamun hakan a tare da shi.


“Ban ga takardar ba”


“Kije reception ki tambaya inda suka tura takardar ki karbo”


Yana fadar hakan na nemi guri ya zauna, ni kuma na saka kai na fice har an isa reception din suk fada min office din da zanje, wani bangare na kamfanin office din yake a lokacin da na isa tsayawa nai jikin kofar na kwankwasa har sai aka bani damar shiga sannan na shiga na gaisa da matar na fada mata abunda nake bukata sai ta dauko wasu files ya duba ta miko min takardar.

“Ke ce sabowar ma'aikaciyarmu ko?”


“Eh”


Na amsa mata, tare da mika mata hannuna kamar yadda take miko min nata.

“Yayi kyau sunana Zainab”


“Halima”


Sannan na jiyo na fito daga office din na nufo office dina, wannan karon ma sai da nai knocked sannan na shiga, jakata na tarar a bude hannunsa kuma rike da wayar da nake kyautata zaton tawa ce to me kuma ya kai shi a gurin jakata da har zai saka hannu ya dauko wayata, da sauri na kai hannu na fisge wayar ina bata fuska alamar ban jidadin abunda yai min ba.

Uffan be ce min ba sai kallona yake, kamar ance min na duba a saman tebur din sai na kyalla ido na hango wayata kusa da jakar, hakan na nufi wayar da na karba ba ta wa ba ce kenan tashi ce. Aiko ba shiri dora tashi wayar a saman tebur din na dauki tawa ina jin kamar kasa ta bude na shige ciki.

“Takardar...?”


Ya tambaya fuskarsa babu alamar dariya, sai a lokacin na tuna da abunda naje neman, mika masa takardar nai ya karba ya mike tsaye.

“Miye aikin shi da har yan fashi za su nemansa?”


Da gangan nai kamar ban ji shi ba badan komai ba sai dan ya fita ya bar min office din. Ban bashi amsa ba har ya kai hannu ya dauki wayarsa yana ta kallona ya fice.

  Sai a lokacin na samu natsuwa har na cire wayar tawa a password na, kamin na taba komai sako ya shigo min da wata bakuwar number.

“Fatar kina cikin koshin lafiya, na yi ta kira baki daga ba kina rejecting calls din, ko ba komai Halima ko dan yyanmu ai kya raga min ba kisan maganar da zan miki ba, izuwa yanzu idan ba rain kike son ya bar jikina ba ya kamata ace kin tausaya min, Wallahi kullum abunda na aikata yana damuna, na rasa samun sukuni idan har baki dawo gareni ba Halima ban san halin da zan kasance a gaba ba, tabbas Gobena zata zama mai rauni kuma abar tausayi”


Ina gama karanta sakon na goge, sai yanzu na gano dalilin dauko wayata ta Ahmad yai wata kila kiran yai yawa ne shiyasa ya dauko yana mim rejecting kamar na saka shi.

   Na yi aikina kamar jiya yau ma ban ci abincin sai dai na sha ruwan lemun da aka kawo min tare da takeaway.


Misalin biyar na tashi ban bar office din ba sai da nai sallah la'asar, daga office din na wuce gidan kawata Hajara, mun dade muna fira na labarta mata abubuwan da suka faru tun bayan rabuwarmu wato bayan zuwan da nai na karshen a gidanta.

Sai magariba na baro gidan, kamar koyaushe napep yar gidana na hau na doshi hanyar gida.

Ina fitowa daga napep din nai arba da Abraham dake tsaye jikin kofar gidanmu, sanye da riga da wando na shadda har da hula guluf din dake bakin kofarmu na haska fuskarsa tufafin sun masa kyau kamar ba shi ba, waiga nai ko'ina ban ga motarsa ba, ban ga alamunta ba, bayan na sallami kai napep din na nufi inda yake tsaye yana kallona na ce.

“Minene kuma?”


“Tambayarki na zo yi, bayan mutumen dazun? Wa kika fadawa na miki fyade kuma ina bibiyarki?”


Shine abunda ya fito daga bakinsa yana ta kallona fuskarsa babu alamar wasa.

“Babu shi ma kuma fada masa nai ba”


“To ya akai ya sani?”


Na masa shiru sai kallon mamaki nake masa.


“Waye kai Abraham ina son sanin tarihinka, waye kai?”


A maimakon ya bani amsa sai kawai ya amsa min da.

“Sirrina nawa ne ni kadai, sai ke ya kamata ki san da wannan”


Yana fadar hakan ya daga jikin kofar gidanmu ya nufi hanyar titi da kallo na bishi har na daina hangoshi, sannan na juya ina kokarin shiga gida Namra ta fito da saurinta ganina yasa ta tsaya.


“Momy yi sauri ga Daddy nan ya zo, ya mana siyayya har da ke”


“Kai Kai Kai..... Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Na furta da karfi ina dora hannu saman kai.....

Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 7 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...