GOBE NA CHAPTER 6 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 6 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 6 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

 GOBE NA CHAPTER 6 BY KHADIJACANDY


              Www.bankinhausanovels.com.ng 


Na kasa jefarda takardar kuma na kasa fadawa kowa cewar ya bani takardar kamar yadda na kasa fadawa yan sanda. Shi kuma be fasa chusa kansa a cikina ba, har kara ma da bibiyata kawai yake amman a yanzu har yarana yake yi ma siyayya ta kudi mai yawa ya kai musu a scul a gida kuma ya aiko min da ita, a kullum ina fargabar idan Mama ta tambayi wanene shi wa zan fada mata ba? Bayan karyar da nai mata cewar wani ne dana hadu da shi yake min haka yai ma su Namra, amman idan aka samu akasi yarana ko kuma Mama da kanta ta ganshi fa? Duk wanda ya gan ni da kafiri zai yi mamaki abunda ya hada ni da shi ina diyar musulmai.

Sai dai a yadda na fahimta kamar shima yana gudun mutane domin baya min magana a inda yakr ganin jama'a da yawa, sai idan ina a kebance kamar idan zan hau napep ko na sauka ko zanje wani gurin sai kuma da dare zai aika yace ana min sallama. Duk kuwa da ban tana fitowa da sunan amsa sallamar da yake min ba, hakan be hana shi aiko min lokaci zuwa lokaci ba, kamar yadda yake yawan bibiyata yana rokon na saurareshi.

Ni kuma na kasa saurarensa saboda bana jin aminci a tare da shi wata kila saboda ba addinin mu daya da shi ba oho, sai dai a yadda na lura yana da kamun kai da taka tsantsan da kuma natsuwa wacce ba ko a musulman mu ba kowa kake samu da wannan ba.

  Ba ni da wata fargaba a yanzu sai ta abubuwa uku,wannan Abraham din sai kuma Aminu wanda shi ma ya saka ni a gaba da yawan bugo min waya da sunan zai gaisa da yayansa tun yana kira ina dagawa na bawa yaransa har ta kai yanzu idan ma ya kirani sai dai na mika musu wayar su su yi magana da shi, hakan kuma be hana idan ya kare magana da su yace su ba ni wayar idan ni kadai ce ko kuma da kanen sai na yanke kiran idan a gaban Mama ne kuma na kan dauka saboda ta gargade ni cewar na daina kin karbar wayarsa ko dan darajar yarana, ina yi mamata biyaya ne kawai saboda ina gudun bacin ranta gudun kar tace ban dauki shawararta ba, amman har ga Allah bana kaunar jin sunan Aminu ma balle jin muryarsa, shi kuma yanzu har wani zillon rashin kunya yake domin wani sa'in har cikin gida yake shigowa ya gaishe da Mama da Baba sannan ya fita, ga wata bakar al'ada da ya tsiro ta daukar yaran yana tafiya da su gidansa ko wani gurin daban su wuni can sai dare zai kawo su gida. Idan na nuna zan hana sai Mama tace min ba haka ba. Wani lokacin sai dai nai ta jin haushin a zuciyata kawai amman ban isa na nuna a fili ba saboda kar mama tace saboda ita nake yi.

  Na tattara komai a yanzu na aje a gafe, babu da bukakata da damuwa kamar abu na ukun nan wato neman aiki, duk inda naji wata ma'aikata ko wani kamfani sai na mika takarduna, sannan na saka addu'a a gaba nai ta yi ko Allah zai saka a dace.!3

Bayan na gama sallah isha'i ina rike da wayata ina latse latsena kamshin turaren Abdallah yai min sallama kamin muryarsa ta daki dodon kunnena, a take na nemi natsuwata na rasa sai na ji duk na kwadaitu da son ganinsa fuskarsa a take na aje wayar na unkura ina gyara Hijab dina na mike tsaye ina juyowa sai nai arba da mutum, faduwar gaba ta same ni a lokacin wacce take yayin yin haka a duk lokacin da nai arba da Abdallah, abun ka da wacce ta rude sai na kasa komawa na zauna daman dakin babu kowa sai ni kadai da aljanuna idan ma ina da su, ratsawa nai gefensa na da zimmar na fita domin a bakin kofar yake tsaye ya zuba min idonsa kamar ya cinye ni, ban san yadda akai ba na kasa lura da kyau har na buga kaina da garun kofar a take goshina ya fara zogi ni kuma na saka hannu ina murzawa jikina na ta rawa kamar marar gaskiya, har lokacin be dauke idonsa daga kaina ba kuma be kauce daga kofar ba. A dole na koma na zauna saman kujerar da ke kusa da inda nai sallah, amman me sai na gagara samun natsuwa domin jikina na bani cewar idonsa na kaina. Sai da ya ji muryar Inna ta doso dakin tana masa lale marhabun sannan ya karaso cikin dakin ya zauna a saman carpet din da na tashi wanda nai sallah, idonsa ya koma gurin kafafauwa ya sakar musu ido kamar mai son tantance abu, ni kau na daga abuna sama na dora saman kujera na lullube su da hijab, sai kallon ya koma gurin hannayena, su ma na nade abu cikin hijab din sannan ya kalli Inna wacce ta shigo ta zauna.

“Abdallah yaushe rabonka da gidan nan”


“Bana samun zama ne sosai yanzu shiyasa aikin yana min yawa, ya gida ya kwana biyu?”


STORY CONTINUES BELOW

“Lafiya kalau ya gurin su Hajiya?”


“Tana lafiya tana gaishe ku”


“Muna amsawa mun kwana biyu ba muje ba itama bata zo ba, ina Suwaiba da su Inteesar?”


“Duka suna lafiya, na ga Baba a waje ai mun gaisa ina Mama?”


“Ta dan zagaya makota jikin ne idan yai mata nauyi sai ta zagaya saboda asibiti ma ance ta rika dan takawa tana shiga mutane”


“Allah sarki gidan yau ku ne akwai a ciki? Duk ina yan matan Baba?”


“Wallahi duk sun tafi wankin Amaryar da ake nan makota, kawarsu ce take aure kuma ta zama kamar yar gidan nan har yaran duk suna can shiyasa ka ga gidan babu kowa”


“Okay”


Ya amsa yana maida dubansa gurin wayata wacce ke kusa da shi, kamar na kai hannu na dauka sai ganin nai ya dauki wayar yana ta shafa screen din domin tana da password ba zai iya bude ta ba, ganin shiru yayi yawa yasa Inna ta tashi ta bar mana dakin daga ni sai shi sai fankar sama da ke ta aiki ba mu iska kasancewar akwai nepa.

“Zan nemawa su Namra transfer zuwa government schools”


Ya fada ba tare da ya kalleni ba, kamar yasan zan tambayi dalili sai ya ce.

“Saboda na san ba za ki iya cigaba da biya musu school fees a wannan private school ba”


Har ga Allah na ji babu dadi amman ban nuna masa ba, domin ban san dalilinsa na yin hakan ba, wata kila ya gaji da taimakon da yake ba ni ne a yanzu ganin kamar ba zan taba aurensa ba.

“Allah yasa hakan shi ya fi alheri”


Na fada da muryata da ke nuna lamarin be min dadi ba. Sai ya kalle ni kamar yana mamakin jin haka daga bakina.

“Ba zaki tambayi miyasa nai haka ba? Ba ki damu ki san dalili ba?”


“A lokaci da ka shige musu gaba har suka samu karatu a wannan makarantar ban tambayi dalili ba saia yanzu da zaka canja musu? Ka yi min alheri da yawa Abdallah wanda ni na san har na mutu ba zan taba iya biyanka shi ba.... Ba zan zarge ka da komai ba”


Mikewa yai tsaye ya jefo min wayata tare da jan tsaki.

“Ba ki hadu ba Halima....”


Yana fadar hakan ya fice, ban ce masa komai ba na fiddo hannuna dake cikin hijab na dauki wayata, ko da na kunna sai ganin screen din nai ya tsaga. Hakan da Abdallah yai be karamin komai ba sai kuzarin neman na kaina, kamin aikin ya samu ina son mai amfani da kudin hannuna na fara sa'a domin zaman banza ba nawa ba ne a yanzu.

Kwana uku da faruwar hakan ya kawo min takardar transfer dinsu har gida, a ranar Mama take tambayata dalilinsa na yin hakan nima na ce mata ban sani ba, sai da na labarta abunda ya faru asibiti.

“A duk yadda akai ba a iya yanke alakarki da Aminu saboda yaya sun shiga tsakaninku yaran har hudu ba ko daya ba”


“Za a iya yankewa mana Mama, Aminu ai be damu da yaran nan ba tun suna gidansa balle yanzu da ba sa tare da su”


“Ai yanzu ne yake sanin darajarsu Halimatu, ba ki lura da yadda Aminu ya canja ba? Ba ki lura da irin kulawar da yake bawa yaransa ba?”


Hafiza ta tsire baki.

“Ni fa ina ganin kamar so yake yace Halimatu ta koma masa...”


Ni ko nai karaf na ce.

“Allah ya kiyeye gatari da saran shuka, ni da Aminu a lahira idan na shiga aljanna wata kila na hango shi a bakin kofar wuta, dan yana da wahala idan Allaj ba kona shi ba akan zalincin da yai min”

STORY CONTINUES BELOW

“Halimatu kenan kina kara girma amman har yanzu hankali ya ki zuwa miki, kin kasa duban yaran dake gabanki ko dan su ai kya kyautata wasu kalaman akan mahaifinsu”


“Mama har yanzu ban gama warkewa daga tabun Aminu ba, saboda shi na samu kaina a duk wani hali da nake ciki a yanzu, mutumen da zai dube ni ya kira ni da mummuna yace ina ta haifa masa yara saboda na tsufar da shi, ya sake ni saboda na fada masa cewar dan'uwansa yana neman lalata yarsa? Sannan yai taraiya da kawata? Haba mama wace irin mutunci kike tunani zai shiga tsakani na da Aminu? Ni kadai na san irin kalubane da na fuskanta a gidansa”


Na karasa idananuwana na cika da kwalla, sannan na unkura na tashi na nufi inda jakata take na dauka daman da shirina na fito.

“Mama idan ko Hafiza idan su Namra sun dawo daga scul ki fada musu ba za su sake zuwa ba daga yau, saboda kar su saka rai, zan bawa Aisha kudin Napep ta je ta dauko su dan nasan kamin na dawo lokacin dawowarsu daga school yayi”


“To Allah ya bada sa'a ya tsare”


Cewar Mama. Hafiza kuma ta kalleni daga sama har kasa tace


“Allah yasa mai kamfanin yana kallonki yace ya samu mata”


Ni kuma nai dariya.

“Ai na girmi aure yanzu, ko nawa za a bani ba zan iya aure a yanzu ba, mun dai yi kuma gama da yarda Allah”


“Kara dai da kika ce da yardar Allah, aure ai shine martabar mace, kuma kin san ba ido zan saka miki kina zama a gida ba ko? Mutanen unguwa ma sai su yi ta yi da ke, musamman idan kika fara aikin nan wani ba tunanin alheri zai miki ba, yanzu sai ki ji an fara tsegumi, daman can ana lissafa mu na yan mata wai mun ki aurarda su.... ”


Mama ta tari numfashina tana ta kora bayani, ni dai kan uffan ban sake cewa ba, nai musu sallama na fice, har nai addu'a fita daga gida, ban daina mamaki da sake sake a raina ba, na kin ganin laifin da Aminu da Mama take da kokarin wankeshi a idanuwana, ga kuma zancen aure da take kokarin bijiro min da shi, anya ya gama da warke daga radadin azabar kunar da Abdulhamid da Aminu suka min da har zan yi tunanin aure? Ko da ma ace yana gabana ballantana yanzu da bana sha'awarsa.

  Na isa gurin da zanje cikin lokaci domin na tsarawa kaina isa gurin da misalin tara na safe sai ga ni na isa takwas da rabi da yan dakiku a kai, duk kuwa da kasancewar babu wanda ya san da zuwana a kamfanin hasalima ni kaina ban san mai kamfanin ba ban san tsari da dokokin kamfanin ba amman ina kyautata zaton a lokacin ne za a samu duk wani wanda ake tsammani samu a kamfani.


Kamar dai ko wane kamfani shi ma wannan yana da masu gadi dake sanye da uniform mai sunan kamfanin wato Crown Company Limited. Sai dai ba su kadai ba har da Sojoji a gurin.

             Sai da suka auna jikina idan bana dauke da bom sannan suka ba ni damar shiga ciki, ba ni kadai suke yi wa haka ba, har masu mota sai sun bude musu bayan mota sun duba sannan su basu damar wuce ciki.

A iya zamana garin gusau ban taba shiga cikin kamfanin ba, to me ma zai kaini tun da ba siye ko siyarwa zan yi ba, a yanzu ma dan ina neman aiki ne kamar yadda nake cewar kamfanin yana neman ma'aikata yan boko wadanda za su iya communicating da wasu mutanen amman da yalshen nasara wato turanci.

Sai dai ban san inda ake bi a shiga kamfanin ba, domin na lura da kofar kamfanin ta kasu gida uku wasu na fita da shiga a ta farkon wasu a ta biyu wasu a ta uku, tsaye nai a gurin ina ta tunanin wacce zan shiga, ta farko haka zuciyata ta raya min dan haka na nufi kofar gadan gadan, a nan ma wasu matsaran ne rike da abun awonsu kamar dai na bakin gate.

  Sai dai da alama su basa barin mutum ya shiga sai idan ya nuna musu wata yar takardar wacce nake ganin kowa yana ba su su duba kamin su barshi ya shiga ciki. Hakan yasa ban karasa a gurin ba sai na juyo na nufi kofar tsakiya wacce mutane suka fi fitowa a cikin, wani abun burgewa ma kofar ita take bude kanta sai jujjuyawa take gwanin sha'awa, ina kokarin kutsa kai na shiga cikin kamfanin na Abban Baby Namra ya fito daga ciki yana sanye da shadda mai ruwan madara, ba laifi na dan saki fuskata domin har ga Allah na yi nufin gaisheshi sai kawai na ga ya hade fuska kamar bakin hadari daman can fuskar tashi ba a washe take ba, balle yanzu da ganina yasa ya kara hade ta kamar yaga mala'ikan mutuwa. Hakan kuma be hana na mika masa gaisuwa ba,  amman sai yai min banza ya wuce abun shi, a take na ji duk na muzanta domin akwai mutane a kofar kuma na san wasu sun ji gaisuwar da na mika masa. Sai kuma duk na ji haushin kaina, miyasa na gaishe shi tun da farko ma? Miyasa ban kyale shi ba na yi tafiyata? Why na nuna na sanshi ma?

STORY CONTINUES BELOW

“Miya kawo ki nan?”


Kamar daga sama na ji tambayarsa da wata bakar murya tashi, har daka min tsawa yake kamar wata yarshi.


“Ban sani ba”


Na fada cikin tsiwa ba tare da na kalleshi ba na cigaba da tafiyata ina jin haushin kaina, na gaishe shi ne saboda ina ganin kamar akwai mutunci a tsakani ko dan abokatar da ke tsakanin Baby Namra da Namra, ko da yake daman daga ganinsa ba zai yi mutunci ba sai wani jijji da kai sai kace shi yafi kowa arziki a gari, Allah kadai ya san abunda ya kawo shi kamfani ma wata kila shi ma wata alfamar ya zo nema amman sai son nuna isa.

“Wai miya kawo ki nan”


Na fada a fili ina tsire baki har wani namijin da ke reception din ya dago ya kalleni.

“Na'am....”


Sai na dan saki fuskata nai masa murmushi.

“Sannu dai Malam daman na ji kamar ance kamfanin ku yana neman ma'aikata”


“Eh amman ba zuwa ake ba, ta email ake turo mana sako”


“Minene mail dinku?”


Ya fada min sannan na sake ce masa.

“Sai dai matsalar ban taba zuwa kamfanin ba, ban kuma san tsare tsaren kamfanin ba ban san mi kamfanin yake ba”


“Kamfanin mu yana siye da siyar da zinari tare da narkawar da kuma saffarashi ta hanyar yin abun wuya dan kulleni ko kuma wani abun na kayan ado na jiki ko na riguna”


“Na gode sosai, ta mail din zan tura cv na?”


“Yes idan sun duba suka ga kin cancanta za a kira sai ki zo”


“Na gode”


Na fada masa ina dariya.

“Your welcome.”


Tare da murmushi as respond. Ni kuma na jiyo na fito daga kamfanin, abun ka damai salo sai da nai ma security guard din sallama sannan na kama hanya, ban yi wata tafiya mai nisa ba na hango Kabir zaune a gafen hanya tufafin jikinsa sun yi datti ga surar kansa ta taru gaba daya ya soma canjawa ga wani abun datti da jikinsa yai. Karasa gurinsa nai da sauri ina kiran sunansa sai ya dago kansa da sauri ya kalleni ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Hannu na saka a jakata na dauko dubu biyu na mika masa, be karba ba ba kuma yi min alamar zai karba ba, hakan yasa na risina na aje masa kudin na soma tafiya ina hawaye ina waigensa, har na tari napep na shiga be daina kallona ba kuma be kai hannu ya dauki kudin ba.

Gaba daya rayuwarsa ta baya sai ta dawo min sabuwa, Kabir mutum ne mai tsafta ga far'a da son mutane, musamman ni yana kula da ni yana nuna min kauna, duk kuwa da yake haramtacciyar kauna na nemana bayan yasan ina da aure.

  Na fi alakanta ganin da nai a haka da rashin mahaifiya a raye domin na tabbatar da ace mahaifiyarsa tana raye ba zata bar danta a haka ba, domin ba duka yake ba balle ace ana gudunsa ba zagi yake ba, kusan sun ta haukar nan ta same shi ko magana baya yi.

  Wallahi har na isa gida hawaye ba su daina zubar min ba, sai da zan fitaa napep din sannan na share hawayena na sallame shi na shiga gida, ashe wani kukan zan tarar a gidan mu, na shiga n samu hankalin kowa a tashe, ka rasa wanda zai fada min cewar Amal ta samu hatsari.


“Wai miya faru ne?”


Na tambaya ganin kowa yana ta bina da kallo.

“Amal ta samu hatsari”


Inna ta fada min muryarta a hankali.

“Ko dai ta mutu? Ku fada min?”


“Ba mutuwa tai ba tana asibiti ma”


Hafiza ta amsa min.

“Garin ya ta samu hatsarin?”


“Aisha taje daukarsu daga school sai ta tarar wai Aminu ya dauke su, sai ga kanwarsa ta zo yanzu ta fada mana wai Amal ta samu

Hatsari, so yake ya kashe miki yayan”


STORY CONTINUES BELOW

“Wace asibiti?”


“Wai Yarima bakura yanzu yanzu ta bar gidan”


Ko jakata ban aje ba na ja kanwata Husna muka nufi asibitin domin an fada min Mama da Aisha suna can sun tafi, haka muka shiga cikin asibitin mukai yawon duniya muka gama ba mu gane inda aka kwantar da Amal ba, daga karshe n yanke shawarar kiran Aminu a kan dole na tambaye shi, shi ma nai ta kiran wayarsa ya ki ya daga har yamma.

  Ga shi daga Mama har Aisha babu mai waya balle na kira su, hankali yai mugun tashi, wata zuciyar na ce min naje gidansu Hajiyarsa na tambaya sai kuma na ji kamar ba zan iya zuwa ba, ba hatsarin Amal ne kawai ya daga min hankali ba har da rashin ganin Adnan Aiman Namra da ban yi ba domin ance suna can tare da shi.

“To ko kuma din sun samu hatsarin ne?”


“Waya sanar mishi? Mu dai kar ya kai mana uwa ya halaka”


“Wai ina ka kai min yara ne Aminu.....”


Kamar hadin baki ina rufe baki sai ga kiransa ya shigo a wayata. Da sauri na daga jikin har ba ri yake.

“Ina Amal din ina yarana...”


“Muna nan Royal Hospital tare da su”


Tsakanin akatse kiran wayar da mikewa ta tsaye bana jin ya ci dakika daya ma, cikin sauri na fita cikin gidan na isa titi na hau achaba na nufi asibiti. Sai da na sake kiransa na tambaye shi gurin sannan na karasa, a waje na samu Mama da Hajiyarsa suna zaune kamar abun arziki, Hajiyarsa na ganina ta taso ta tare ni da yar far'arta ni kam ko kula ta ban yi ba na tura dakin na shiga. Daga Aiman har Adnan da Namra da Aminu da kuma Aisha suna cikin dakin, Amal na kwance an saka mata bandeji akai sannan an saka mata wani karfe a baki an kware bakin ga halshenta da dinki.

“Miya same ta me kai mata?”


Na tambaya a tsawace ina kallonsa. Sai ya kalleni a sanyaye ya kasa ce min komai. Sai mahaifiyarsa ce ta amsa min.

“Ya dauko su daga Scul ne yana kokarin tsallaka titi da su sai wani mai Napep ya hade Amal”


“Momi kuma halshenta ya cire yanzu aka dinke mata shi..... ”


Aiman ya karasa mata, ban san lokacin da na kalli Amal ba na sake kallon Aminu ya ce.

“Kaga abunda ka ja min a gurin ya ko? Miya kaika daukar min yara?”


“Mhaifinsu ne ni Halima ki rika tunawa da wannan... ”


Ya fada ido raurau kamar zai fashe da kuka.

“Sai yanzu ka san kai mahaifinsu ne? Sai yanxu kasan su din yayanka ne?....”


“Haba Halimatu”


Mahaifiyarsa ta tari numfashinta sai yai saurin daga mata hannu.

“Barta ta fadi duk abunda take son fada Hajiya...”


Wannan karon nuna shi nai da yatsa.

“Ba fada kawai zan yi ba, gargadin ka zan yi akan yarana? Karka sake kula su ko kallonsu karka sake yi balle har ka dauke zuwa wani gurin karka sake nuna hada jini da ni...”


“Ba zan yi abunda zai jefasu a matsala ba, abunda ya faru kaddara ce wacce ko wane dan'adam be isa ya wuce ta ba, kuma ina son ki rika tunawa cewar har gobe ni mijinki ne domin akwai yaya a tsakanin mu kuma ba a san abunda gaba zata haifar ba..... ”


Taba sanin cewar kiyayya Aminu a zuciya ta kai min makura ba sai a wannan lokacin, tasss na wanke masa fuska da mari, mari daya be min ba har sai da na kara masa na biyu ina kokarin yin na uku Namra ta rike min hannu tana kuka sai ta rumgume Babanta. kasa cewa komai nai na fice daga dakin ina hawayen da ban san na minene ba. Ko da na fito ana ta kiraye kirayen sallah mutane waje kowa harama yake hakan yasa na nufi gurin da aka tanada dan aje motoci na zauna saman wani tebur da wasu maza suka tashi, a lokacin da na zauna sai na saka kaina cikin kafafuwan na rushe da sabon kuka, ji nai an zauna a saman tebur din da nake zaune da sauri na dago kaina na kalli gefena. Abraham ne sanye da blue T-shirt da facing cap black kamar yadda wandonsa yake, ko da wasa be kalli inda nake ba sai raba ido yake yana kallon harabar asibitin, Bluetooth din dake gefen kunnensa na ta balli da jar wuta.

“Mi kike yiwa kuka?”


Kawar dai nai wasu hawayen na sauko min.

“Abubuwa da yawa da yawa da yawa... ”


Na kasa daina fadin da yawa din har sai da ya kalleni.

“Kamar me da me?”


“Ba za su lissafu ba, idan na fita daga wannan na shiga wannan na gaji da rayuwar nan, na rasa yadda zan yi.... ”


Ji nai ya rika hannuna...

“I will be safe in this hand of mine, fada min matsalarki kuma ki fada min wanda ya saka ki a damuwa yanzu nan... I can give you another life..... ”


Kamar an min shocking haka nai saurin fisge hannuna na mikewa tsaye ina kallonsa. Kamar yadda shi ma yake kallona.


“I will take the pain,.... take it away....”


Hannu na saka na share hawayena na nufi inda na fito da sauri na barshi a gurin zaune.

ABDALLAH POV.+


After ya bar gidansu Halimatu ya koma office, sai dai ya kasa natsuwa da abunda Hajiya ta saka shi ya aikata kuma yana ganin be kyautawa Halimatu ba, yanzu dawainiya za tai mata yawa. Haka dai yai aikin da tunaninta a ransa kamar kullum bayan ya tashi office yai sallah masallacin asibitin sannan ya nufi gidan Hajiyarsa.

A yau harabar gidan ya tararda ita ta shinfida katuwar tabarma ita da yar aikinta suna ta fira. Kusa da inda suke zaune yai parking sannan ya fito daga cikin motar fuskarsa na nuna alamar akwai damuwa a tare da shi, tun kan ya karaso mai aiki ta miko masa gaisuwa sannan ta tashi ta koma cikin gidan.


"Hajiya sannu da hutawa"


"Yauwa"


Ta amsawa tana kokarin kawarda fuskarta daga damuwarsa, shi kuma ya zauna kusa da ita sosai ya soma mata magana a hankali.

"Hajiya da dai zaki duba maganar"


"Maganar Halimatu ko? Ko gaisawa ba mu gama yi ba za ka dauko min zancenta"


"Wallahi Hajiya tun daga lokacin da kika shaya mana katanga a tsakani sai na shiga cikin damuwa, ba aurenta zan yi ai Hajiya, bayan soyayya akwai tausayinta a zuciyata wanda shine makasodin karuwar soyayyarta a raina, hanani taimakonta da kika yi sai ya jefani cikin damuwa"


"Indai kana neman albarka ka bi umarnina ka huta"


"Amman Hajiya harda yaranta?"


"Har da su...."


Ta amsa masa da karfi alamar ta fusata sosai. Sai yai kasa da kansa, na wani lokacin kamin ya tashi ya saka takalminsa.

"Hajiya zanje gida na huta, a tashi lafiya"


Shine last word dinsa da ita sannan ya nufi motarsa ya shiga, a maimakon ya nufi gidan kamar yadda ya fada sai ya juyarda motarsa zuwa gidan iyayen Halimatu, hakuri yake son ya bata akan abunda ya faru dazun, if ba zai iya taimakonta a yanzu then ba shi da yancin fada mata bakar ji yake kamar yai mata wani aibi, daya bayan daya yake ta tunanin maganganun da yai da ita dazun a lokacin da yaje kai mata takardar transfer dinsu Namra, even if be fada mata bakar magana ya kamata yai mata wata maganar da hankalinta zai kwanta ba wai ya barta a cikin duhu ba za tai ta zarge zarge akansa hakan kuma ba karamin jefata zai yi magana damuwa ba.

Yana isa ya fita daga motar cike da gwarin guiwa ya nufi cikin gidan, sai da gaisa da kanenta sannan ya nufi dakin Mama.


"Mama bata nan Halimatu ma bata nan sun tafi asibiti"


Ya juyo yana kallon Ramla wacce ke masa maganar.

"Waye ba lafiya?"


"Amal ce aka ce ta samu accident on their way back to school"


"Subhanallahi suna wace asibitin?"


"Royal"


Da sauri ya fice daga gidan be ko tsaya gaisawa da Inna ba, hankalinsa ya tashi sosai a take tausayin Halimatu ya kara kamashi.

"Oh Allah.... "


Ya furta yana hannunsa na hagu saman kai. Tunanin halin da Halimatu take ciki yake gashi ba shi da halin taimaka mata a yanzu. Ya busar da iskar bakinsa yana girgiza kai.

Sai ya shiga cikin asibitin sannan ya ciro wayarsa ya kira Halimatu domin sanin a inda suke, a maimakon ya ji muryar Halimatu sai muryar Aisha ta daki dodon kunnensa, itace ta kwantanta masa inda suke ya karasa gurin da kuzarinsa, sai dai yana bude kofar dakin ya shiga idonsa sukai arba da Aminu sai wani rashin jindadi da walwala ya mamaye masa zuciya. Da Mama kawai ya gaisa sai Aisha da ta miko masa da gaisu, ko da wasa be kalli inda Aminu yake ba balle mahaifiyar Aminu da ke binsa da kallo.


"Mama garin haka ya faru?"

"Wallahi suna kokarin tsallaka titi ne wani mai achaba ya kade ta"


"Subhanallahi"


STORY CONTINUES BELOW

Ya karasa kusa da Amal yana dubata, sai Aiman ya zo ya kama hannunsa yana kiran Uncle. Dan murmushi kadan Abdallah yai masa domin yau babu walwala da far'a a tare da shi, hannu ya kai zai shafa kansa sai Aminu ya kai nasa hannun ya fisgo Aiman yana jin wani irin kishi da kiyayyar Abdallah na taso masa. Da gangan Abdallah yai masa wani shegen kallo na uku saura kwata, kamar zai yi masa dariyar abunda yai sai kuma ya dauke kai ya kalli Mama.

"Allah ya saukewa Mama, ya kamata a saka ido sosai akan yaran nan, a samu wanda zai rika kaisu ya dauko su zai fi...."


"Ba sai ka fada mana ba, can baya da ake kula da su kai kake kula da su ne? Ba yara ba ne mu da zaka fada mana abunda za mu yi"


Aminu ya fada cikin fusata da daga murya. Ko da wasa Abdallah be kalli inda yake ba sai yai kamar be ji abunda yake fada ba, har sai da ya duba agogon hannunsa sannan yai masa wani kallon wulakanci, cikin wata irin isa da jin kai ya zuba hannayensa aljihu yana fadin.

"Magana kake Malam Aminu... Ai ban lura da kai bane Aminu... Ashe kana gurin..."

Maganar Abdallah bata karawa Aminu komai ba sai fusata da kawo zuci kusa har launin idonsa ya canja.

"Ya za ayi ka lura da ni ka shigo hankalinka sama"


Dariya Abdallah yai kamar ba komai sai kuma ya juya ya kalli Hajiya.

"Ikon Allah ashe har da mahaifiyarka ma, Na shigo hankalina yana gurin Amal ne, ka san ni Allah ya saka min son yaya musamnan na Halimatu, to sannu Hajiya"


Ya karasa yana da risinawa kamar da gatse, sannan ya kalli Mama still with murmushi a fuskarsa ya ce.

"Mama zan fita sai na sake dawowo"


Har Aminu ya bude baki ya sake fadar wani abun sai Hajiya tai masa hani da ido, hakan yasa shi hade maganar tare da bacin ransa. Abdallah ya nufi kofar fita yana kallon Aminu fuskarsa da murmushi mugunta.

HALIMATU POV.

Har na yi nisa sai kuma ya juyo na dawo gurin da yake da sauri, ban same shi a gurin ba hakan yasa na daga kaina na fara waige waige a gurin, kamar yasan shi nake nema sai ya dago min hannu daga can inda yake tsaye jikin wata kotuwar mota mai ruwan toka, kamar kar na karasa a inda yake, sai dai kuma akwai tarin tambayoyin da shi kadai zai amsa min ba, akwai abubuwan da nake son a banbance min, ina son ko wane launi da zanen kaddarata ya fito min a kalarsa, fari yai fari fes bakin yai baki wulik ta yadda zai fuskanci alkibila ta, ina son sanin wanene shi, a yau ina son nai ninkaya a duniyar tarihinsa, ina son na bazama a duniyar mafarkinsa a kaina na wanzu da burinsa da dalilin bibiyata da yake.

"For the last time waye kai?"


Ita ce tambayar da na fara aika masa tun kamim na isa daf da shi, ina ta yawo da idanuwa a fuskarsa.

"Kina da bukatar hutu, ya kamata ki huta daga baya sai mu yi maganar"


"Hutu? Hutu a duniyar macen da ta zo bauta? Hutu a rayuwar matar da manta da jindadi a rayuwarta? Fada min waye kai...!"


Na fada da iyakar karfina har sai da ya soma tsorata ta yanayi na.


"Sunana Abraham zauna a ciki sai mu yi magana"


Ya fada yana bude min motarsa.


"Sunanka baya min dadi ka daina maimaita min abunda na riga na haddace, kasan me nake nufi ka bani amsa kawai"


"Idan na baki amsa ba zaki guje ni ba? Idan na fada miki waye ni ba zaki kyamace ni ba? Ki min alkawari cewar fada miki waye ni ba zai kawo kiyayya a tsakaninmu ba"


Kallon mamaki nake masa.

"No wait.... Why all this?"


"Saboda na taba cutar da ke.... "


Har lokacin da yake maganar ban kawo komai a raina har sai da ya fadi kalmarsa ta karshe, zuciyarta ta fara raya min wani abun da ban taba mafarkin faruwarsa, lalabe na fara yi a duniyar tunani na, sautin wacan muryar nake hada da wannan, ina ta kokarin siffanta surar wacan da wannan, farat daya na nemi duniyar tunanin nawa na rasa, abubuwan da nake kokarin hadawa duk suka watse, sai na ji kan nawa kamar babu komai a ciki. Tafiya nai bayabaya kamar zan fadi sai yai saurin kai hannunsa zai kamani.


"Dan.... Allah... Kar.. Ka... Taba... Ni... "


Na fada a wahale, wasu zafafan hawaye na sauko min, kamar yadda shi ma idanuwansa suka fara fitar da hawayen.

"I can't hide it anymore yanzu, ba zan iya cewa ba da gangan na aikata ba, i rape you amman ban tsammanci zan dawo gareki ba, and on that very night da kika fada min kin samu cikina ban iya bachi ba a ranar saboda tunani da farinciki jin haka, daga lokacin na samu kaina da kaunar ki da kuma son rayuwa da ke, because my only hope and pray is na samu haihu kamin na mutu, na san zan iya mutu at any moment, but i want to make my parents proud, and ina son ko na mutu na bar carbon copy na...."

Ya karasa muryarsa a dakishe saboda kuka. Risinawa nai gabansa na hade hannayena kamar neman gafara.


"Why do you rape me? Mi mai maka?"


Sai shi ma ya risino saitin fuskata yana share hawayensa.


"I don't know why, na san dai mijinki na je nema a wannan daren.... "


Be gama maganar ba na mike tsaye na juyo tafiya na fara yi kamar mai ciwon kafafuwa, ko wace dagawa da takawa tana min nauyi, ga nauyin zuciya da ya danne min kirji har yana neman numfashina, ina tafe wasu hawaye masu zafi suna sauko min yawun bakin gaba daya ya canja gumi na ta karyo min har kasan marata murdawa yake, ina ta girgiza kai alamar a'a a'a ban daina ba har sai da na hango Abdallah ya fito daga cikin emergency sanye da shadda hannayensa duka biyu zube a aljihu... Tsayawa nai cak ina kallonsa, a yau ji nai kamar an halittoni ne kawai domin kallonsa, kaunarsa da tausayin kazafin da nai masa wanda har ya kai ni ga furta masa. Babu kamar kai Abdallah Wallahi babu irinka, mutumen da ya kasa nuna min kyama balle yayana, mutumen da ke bani taimako da kowace hanya, mutumen da idan nai gudu naje gunsa da bukatuna da damuwata zai tara hannayensa biyu ya karbe ni, na yi kuskure tabbas na aikata kuskure na barin mutune da ya dace da zama abokin rayuwata....


"Kullum cikin kuka kike please smile...."


Maganarsa ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da nake, ashe ya karaso kusa da ni ya ban sani ba, fuskarsa da murmushi yana min alama da nai murmushi da yatsan hannunsa biyu kamar yadda murmushin yake a fuskarsa.

Ban tana jin kaunarsa Abdallah sai yau ban taba jin kimar Abdallah ba sai yau ba, ban taba jinjina abunda yake min ba sai yau. Murmushin nai ina hawaye.

"That's my girl...."1


Ya furta sannan ya maida hannun aljihu yai gaba abunsa, kamshin turarensa ya daki hancina har sai da ma lumshe idanuwana....

Na samu dakika biyar a haka kamin na juya ina kallon tafiyarsa cike da kaunarsa, wata kila jikinsa ne ya bashi cewa ina kallonsa sai ya juyo ya kalleni tare da aiko min da kyakkyawan murmushin wanda ya sanyaya min zuciya ji nai kamar na ruga na rumgume shi na fada masa cewar yau Ni Halimatu ina kaunarsa.....

Ban koma cikin dakin ba, a harabar da amsu jinya suke zama na samu butar wata matar nai alwala ta bani carpet nai sallah nai addu'a sannan na tashi na nufi wani bangare na asibiti gurin da aka kawata da furanni da kuma hasken fitulun kasancewar hudu ya fara. Tsaye nai a gurin ina ta kallon sama wata iska mai dadi na kadawa hawayen idona na ta aikinsu, babu abunda nake tunani sai Abdallah babu wanda nake hangowa a tare da ni sai a yanzu nake ganin dacewar tarairaya ta da Abdallah.

“Uhmm na san na bata miki akan maganar da nai dazun amman iya gaskiyata nake fada, kina da damar da za ki ji haushi na ki tsaneni kuma zan jira har zuwa lokacin da zaki warke daga raunin da nai miki.... ”


Juyowa nai a hankali na kalli Aminu wanda ke min maganar, sai a yanzu nake kallonsa da kyau ya rame sosai ya dan yi duhu. Dan murmushi nai na nufi wata karamar balcony na zauna sai shi ma ya tako ya zo ya zauna kusa da ni. Magana na fara yi ba tare da na kalle shi ba

“A lokacin da nake budurwa idan mai ma mahaifiyata ko mahaifina wani aiki ko abunda ya faranta musu rai, sukan ce min Allah yai miki albarka ya baki miji na gari, ni kaina ina yawan addu'ar a sallah ta, a lokacin da ka zo kace kana so na ka aureni sai na ji cewar Allah ya amsa addu'o'inmu, bayan na yi haihuwar farko ka juya min baya, sai na fara addu'a ina ta fata da ganin kamar wata rana zaka daina, da nai haihuwa ta biyu sai na fara karaya, daga lokacin ne na dauka cewar aurenka yana cikin mummunar kaddarata, domin zama da mazinacin namiji ba abu ne mai sauki ba, kullum ina cikin fargaba, kullum ina cikin addu'a, kamin wani lokaci sai alakar auratayyarmu ta canja, na kuma maka kamar bakin maciji, idan nai kwaliya ina jiran ka dawo ka yaba min, ba zaka dawo ba sai tsakiyar dare, a maimakon idan ka kalleni kace na yi kyau sai ka fada min cewar siraran mata suna can suna can waje suna jiranka, a gabana kake yabon wasu mata a wayarka ko a tv saboda kawai na ji zafi, bayan ka san a lokacin da ka aureni ba haka nake ba, kyau jikina na daya daga cikin abunda ya dauki hankalinka har ka zo gurina ka nuna kana son aurena, a gidanka halitta ta canja Aminu saboda yayan da na haifa maka yasa jikina ya bude, halitta ta tashi daga budurwa zuwa matar aure,  na bar iyayena na bar yan'uwa da kowa nawa na koma gidanka cikin yan'uwana da zama, amaimakon ka tausaya min ka mutunta ni sai na zama abar wulakantawa, kai ka yi min mahaifiyarka tai min yan'uwanka su yi min, ka dinga fada kana cewa na haifa maka yara da yawa zan tsofar da kai, hakan yasa na fara tunanin planning, kace na ciki kiba kai ba haka kake son mace ba ka fi son siririya, babu irin kudin da ban kashe ba akan nai slimming amman ban samu sa'a ba duka ka san saboda me? Saboda na faranta maka saboda na gyara rayuwar aurena, wani lokacin idan na unkura sai na ji kamar ba zan iya fita na bar yayana ba, hakan yasa na yarda aurenka yana cikin kaddarata, wasu akan jarabesu da kiyayyar uwar miji, ko yan'uwansa, wasu kishiya wasu mijin wasu yaya wasu rashin abinci wasu rashin lafiya, to sai aka jarrabe ni da abubuwada yawa, da gangan kake kin siyo mana abu mai dadi ko na marmari wanda za mu ci mu jidadi saboda kawai ka musgun min, ka dauki karan tsana ka dora min saboda kawai na aureka na haifa maka a yaya, a ranar da na tambaye ka 2k ka hana ni a ranar na ga alert dinka na turawa wata 30k+ ka tuna....?”+


Tun da na fara naganar yake hawaye har na kai aya, be iya bani amsar tambayar ba ko kallona sai ya kasa yi. Hannu na saka na share hawayena ba tare da sun bar zuba ba.

“A kowa ce rayuwar aure akwai kalubale, na sani shiyasa na jure zama da kai a wacan lokacin. Amman wani abun mamaki a lokacin da kake ki na kaka nuna min kiyayya a lokacin ne Abdallah ya nuna yana so na, bashi kadai ba a duk inda na shiga maza basa dauke ido a kaina amman nawa mijin....”


Kasa karawa nai saboda kukan da ya ci karfina.

“Na yi miki abubuwa da yawa Halimatu, a lokacin ina jin kamar ke din matsala ce a rayuwata, ban gane muhimmancin ki ba sai bayan na rasu da ke, duk abunda zan fada miki a yanzu na san ba yarda za ki yi ba, amman Wallahi zuciyata babu wanda take mamari take kauna sai ke, na aikata babban kuskure na rabu da nai da ke, amman ko a wacan lokacin ina son ki Halima, kawai dai sherin zuciya ne da na shaidan. Amman a yanzu na canja Wallahi duk wani hali marar kyau nawa yanzu babu shi..... ”


STORY CONTINUES BELOW

Sai a lokacin ya kalleni ya sauko daga zaunen da yake ya risina gabana.


“Ki dubi girman Allah ki yafe min, ki duba yayanmu ko dan su ki yafe min, ni da Hajiya duka mun yi nadama, Wallahi babu daren da bana kukan rashinki Halima....”


“Kana son na yafe maka?”


Yayi saurin gyada min kai jikinsa har rawa yake kamar ba shi ba.

“To ka maka dan'uwanka a kotu, ka tsaya da kafafuwanka har sai ka kwatowa yarka yancinta......”


Ina fadar hakan na mike tsaye ina share hawaye na kauce daga gabansa na fara tafiya....

“Idan nai hakan zaki yafe min ki dawo ki zauna da ni da yayana?”


Juyowa nai na kalleshi.

“Wata kila dai zan iya yafe maka na goge sunanka daga bakar takardar da na rubuta shi, amman zancen zama aure a tsakanin ni da kai wannan har abada ne, sai dai wata mai sunana amman ba ni ba....”


Ban tsaya jiran abunda zai fito daga bakinsa ba na nufi dakin da su Amal suke, har a lokacin Mama da Hajiyarsa suna dakin a zaune, kusa da Amal na karasa na zauna ina tambayar Aisha wayata.

“Yaya Abdallah ya zo nan”


“Eh mun gaisa da shi”


Na fada ina yin kasa da idona saboda jan da sukai.

“Halimatu ayi hakuri da rayuwa, mun san mun yi kuskure mun laifi amman a dubi girman Allah a yafe mana wallahi yanzu Aminu yayi nadama

......”


Kaina na daga na kalli Hajiyar Aminu wacce ke maganar murya kasa kasa kamar za tai kuka, sai na kalli Mama nace.


“A nan za ki kwana? Ko ni zan tsaya na kula da ita?”


Sai Hajiyar Aminu tai karaf tace.

“A a ni zan kwana nan kuje ku hutarwarku”


Jin hakan yasa na mike tsaye nai musu sallama na fice. A daren ranar kasa bachi nai saboda tunanin rayuwar da nai a gidan Aminu, tabbas na fuskanci kalubale wanda ba ko wace mace ce zata iya jurewa ba. Da asuba bayan na yi sallah na dora da karatun qur'ane, misalin shida da yan mintuna na sha ruwa na koma bachi, bayan begen Abdallah da zuciyata ta kwanta da shi har da mafarkinsa sai da nai a bachin nan nawa na safe. Kiran waya ne ya farkar da ni duk kuwa da kasancewar bakuwar number ce hakan be hana ni dauka ba. Tun da sallamar matar ta daki dodon kunnena na gane mahaifiyar Aminu ce, ita ta fara miko min gaisuwa ni kuma na amsa mata da ina gajiya. Ta fada min wai kar a dafa komai tasa an kawo musu daga gida, ni dai da to kawai na amsa mata na aje wayar.

  Misalin tara na shirya na cikin bakar abaya kamar yadda na fi son sakata a duk tufafina na fita da zimmar idan na bar gidan Abdallah na je asibiti, so nake na tafi na bawa Abdallah hakuri kuma na fada masa labarin mutumen nan, and i got lucky na tarar ya shirya cikin kananan kaya na shirin zuwa office. And wani karin farincikin kuma shi ya bude min kofar da kansa yana rike da mug.2

“Ina kwana?”


Na gaishe shi ina murmushi sai ya amsa min fuskarsa ba yaboba fallasa.

“Ya kai?”


“Zan iya shigowa magana nake son yin da kai.....”


Daga can bayansa na jiyo muryar Suwaiba tana da fada.

“To wannan abun ya wuce gona da iri, ya zama iskanci da cin fuska, kuma Wallahi ba zan dauka ba ke bakya ma jin munya bibiyar kanen tsohon mijinki... Kai tirr Halima kin yi abun kunya.... ”2


Da muryar da na san zata iya jiiyoni na ke fada masa cewar.

“Ka ce tai hakuri na san babu dadi, amman babu abunda zai yanke alaka a tsakaninmu...”


STORY CONTINUES BELOW

“Muje waje mu yi maganar”


Shine abunda ya fito bakinsa, bakin nasa nake ta kallo kamin nai backwards na fita daga falon, wanda hakan ya bashi damar fitowa ya janyo kofar ya rufe.

“Ya kai....”


Yan yatsuna na fara murzawa sai hawaye.


“Daman na zo ne na baka hakuri akan abunda ya faru..... ”


“Ai na ce miki ya wuce ko? Ni ban rike ki da komai ba tun wacan karon na ce na yafe miki”


“Ba shi ba, akan duka abubuwa da nai maka”


“Na yafe miki Halimatu....”


Na kalleshi cike da kaunarsa wacce ta mamaye qalbina take taraiya da numfashina a yanzu, kai na gyada masa alamar gamzu.


“Kuma ina son ma fada maka wani abu....”


Sai yai hanzarin katseni.


“Bana son jin komai a yanzu pls”


Na sake gyada kan a karo na biyu ina hade yawuna.

“Amman magana ce mai muhimmanci akan maganar fyaden..... ”


“Oh Please haba dai bana son jin komai a yanzu”


“Shikenan, zan jira har zuwa lokacin da kake son ji, zan tafi amman dan Allah ka rika daukar wayata idan na kiraka kuma ka rika min reply idan ka ga sakona pls dan Allah”


Be ce min uffan ba har na juyo na fara tafiya, sai jin mutum nai a gafena yana takawa tare da ni.

“Dan Allah Halimatu ki cire komai a ranki, ki nemi aiki ko wata sana'a zaki iya tallafawa kanki ki rage damuwa kin ji? Ki cire kowa a ranki”


Tsayawa nai na kalleshi.


“Babu kowa a raina a yanzu, na cire komai na fahimci komai, babu wanda yake cikin raina Abdallah sai kai....”


Kallon mamaki yake min is like kamar be yarda da ni ba, juyawa yai ya kalli bayansa kamin ya nuna kansa. Ni kuwa na gyada masa kai cike da kuzari, can ya busar da iskar bakinsa.

“Ya rabb, wato baki daina shayeshayen nan da na ce ki daina ba ko?”3


Na matso kusa da shi ina girgiza masa kai.

“Ban sha komai ba Wallahi a hayyacina nake”


“No Halima ba zata fadi haka a hayyacinta ba, ko dai damuwar nan ta dawo miki ko kuma kin koma ma shaye shayen”


“Wallahi ban sha komai ba”


Na fada ina masa magiya kamar zan fasa kuka.

“Shikenan ki tafi gida”


“Zan tafi duk abunda ka ce zan yi Abdallah”


Kamar umarninsa nake jira sai na juya da sauri na fice daga gidan.


AHMAD POV.

Glass cup ne a hannunsa yana kurba lemun a hankali, while idanuwansa suna watching plasma but his heart is one where else. Yana jin tsananin damuwa da kadaici a rashin Baby Namra da Matarsa da kuma mahaifinsa a rayuwarsa, sai dai his try be strong for him mother and his sister Siyama, domin su kadai suka rage masa a yanzu, he feels like da ace mahaifinsa yana raye da abubuwan sun masa sauki, kamar yadda da ace Baby Namra tana nan wata kila da be shiga damuwa haka ba damuwar da ke taba lafiyarsa ta taba rayuwarsa, he missed his wife his father his daughter. Be dawo daga duniyar tunanin Gobensa ba har sai da Hajiya ta soma magana da shi ayayinda take zaune saman sofa Siyama na kasa tana matsa mata kafafuwanta.

“Dazun Laraba ta kirani tace wai dan Allah a taimaka mata a dauki danta aiki a kamfaninku...”


A hankali ya juyo ya kalleta.


“Ai ba irin su muke dauka ba, yan boko, kuma kin san Attahiru ba wani boko yai mai zurfi ba, idan ma yayi ba zai wuce secondary school ba”


“To a duba masa dai haka nan tunda har ta roka sai a samu inda aka laba shi”


“Hajiya ki dai fada mata masu ilmi muke dauka saboda kamfanin a yanzu yana bukatar gogaggun.....”


Be marasa ba ya fara tari da sauri ya aje lemun hannunsa ya ciro handkerchief dinsa ya tari jinin da ya fito daga bakinsa. The white handkerchief din ya bawa Hajiya da Siyama damar ganin jinin da kyau, daga Hajiya har Siyama sai ka rasa wanene hankalinsa ya fi tashi...

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Mi zan gani haka?...”


Cewar Hajiya. Sai yai murmushi yana nuna mata cewar ba komai ba ne.

“Habo na ke yi, daji ne ya kamani da mura ba wani abu ba”


“Brother yaushe ka fara haka?”


Siyama ta tambaya hawaye na sauko mata, kallonta yai he know he can't hide anything from her domin karatun likita take kuma ta fi kowa sanin waye dan'uwanta.


“Can we talk private?”


Hajiya tai saurin amsawa tana girgiza kai tana kuka.

“No I'm your mother be kamata ka boye min komai ba, how do you expect your own mother to live after you death? How? Ku kadai kuka rage min daga kai sai wannan”


Ta nuna Siyama hannunta na rawa tana fashewa da kuka. Da sauri tashi yai ya koma gabata.


“Wallahi Hajiya ina shan magani kuma i believe zan ji sauki, duka duka ban hi sati da fara wannan tarin jinin ba, kuma na ga different doctors sun bani magani ina kan sha”


Siyama ce ta taso ta zo bayansa ta rumgume shi ta fashe da kuka.

“Please Brother we love you..... ”


He feel so hopeless, so emotional but a haka yake kokarin ganin ya zama very strong for them.

Tun daga lokacin da Hajiya ta lura da halin da danta yake ciki bata sake yarda ta barshi ya zauna shi kadai ba indai yana gidan to yana falo tare da ita ko kuma yana harabar gidan suna fira, a ganinta sakewarsa zai taimaka masa fiye da kadaicewar da zai yi shi kadai yana tunani da saka kansa a damuwa.

  Kamar yadda ta saba masa after dinner suna zaune dinning ta dauko masa zancen aure domin shi ne abunda ta fi son taga yayi a yanzu ko zai rage masa damuwa har ma ya kawo masa farincikin samun wata haihuwar.

“Tun kwanan baya na maka magana akan aure kace zaka yi tunani ba ka ce min komai ba”


Ya kurba ruwan da ke gabansa kadan yana dan murmushi.

“Hajiya bana son zancen aure a yanzu”


“Saboda me? If saboda ni ne zaka iya zama a wajen gidan nan da matarka, and ba zan cilasta maka auren Ikilima ba, sai ka dauko budurwa da kake so ka aura”


“No ba wai Budurwa ko bazarawa ba, a halin yanzu mace bata gabana, ni ban ki na mutu a haka ba”


“Saboda me? Ni bana son ganin jikanka ne? Ku kadai Allah ya bani ai zan so ku yi aure ku yi juri'a da yawa ba kamar ni ba”


“Kawai ina ganin kamar idan na sake haihuwa rasata zan yi, ni kuma bana son abunda zai sake kasani a damuwa yanzu”


Hajiya ta yi murmushi.

“Baka da karfi zuciya sai kace ba namiji ba”


“Hajiya ba zaki san abunda nake ji ba, babu wanda zai shiga a irin halin da nake ciki a yanzu ace be samu kansa a damuwa ba”


“Yes dole na ka damu an sani ai, amman ka rika sassautawa rayuwarka, ita daman rayuwa tana tafe da kalubale kala kala, wani mai sauki wani mai wahala, sai dai duk halin da zaka shiha ka rika tunawa akwai wadanda suka fika shigarsa, idan arziki ne akwai wadanda suka fika, idan talauci ne da damuwa akwai wadanda suka wankeka suka shanye, kai mata kawai ka rasa sai ya kuma uba, akwai wata macen da na gani na ita tana da uwar a raye uba a raye dukan ya'yanta suna nan, amman kalubalen rayuwar da ta shiga ko kan akaifarta baka shiga ba, tun daga lokacin da na ji labarin matar nan abun ya tsaya min a rai”


“Indai har tana da kowa a raye mi zai saka ta a damuwa”


Har Hajiya ta bude baki ta fara labarta masa labarin Halimatu sai ga Siyama ta dauko fuskarta dauke da damuwa taja kujera ta zauna tana fadin.

“Ni kam i don't think zanje gaskiya”


Ahmad ya kalleta.

“Why? Saboda Baby bata nan? Mu da Hajiya za mu je kamar yadda muka saba a kowace shekara”


Yana fadar hakan ya mike tsaye ya bar dinning table din ya nufi hanyar da zata fitar da shi daga falon zuwa part dinsa. Hajiya ta kalli yarta cikin kwarin guiwa tace.

“Idan ba mu karfafa masa ya manta da komai ba, taya za mu taimaka masa wajen tunawa da abunda zai tsaya masa arai, a kowa ce shekara shi yake bada kaso 50 a cikin dari na wannan wasa da ake na children day, 25% daga kamfaninsa ne, 25% daga makarantarsa ne, sauran al'umma da kamfanonu su dauki 50%, taya mutun zai yi wannan aiki kuma ya kasa halarta taron da yake talarta duk shekara, saboda kawai yarsa ta rasu sai yace ba zai je ba”


“Nifa ban ce kar yaje ba”


“Shi kike nuna masa mana saboda babu Baby Namra sai ya kasa jurewa ya nunawa duniya yana cikin damuwar rashinta har yanzu, ya kamata ki karfafi dan'uwanki shiga irin abubuwan nan zai rage masa damuwa, ko a lokacin dq Baby take raye wannan children game din yana cikin abunda tafi so fiye da komai a rayuwarta,to yanzu dan bata da rai kike tunanin mahaifinta ba zai je ba?”


“No Hajiya ina jin ba dadi ne, kusan every year tana cikin mutanen da suke bada award wa wadanda sukai nasara, kuma tana zaune tare da shi....”


STORY CONTINUES BELOW

Ta karasa tana fashewa da kuka, Hajiya ta tashi daga kujerar da Siyama take zaune tana rarrashinta.

“Haka Allah yake ikonsa, haka na rasa mahaifinku a lokacin da nafi tsananin bukatarsa, amman da nai hakuri sai komai ya wuce, na koma ina farinciki kamar ba ni ba, idan muka yi hakuri sai ki ga Allah ya sauya mana da wani abun na daban”


Siyama ta rike hannun Hajiya tana ta kuka, haka take a duk lokacin data suna Baby, domin ta zame mata kamar kawa kusan abubuwa da yawa a tare suke duk kuwa da kasancewar ta girma sosai amman ta dauke ta kamar kawarta.

Magani ne first abunda ya fara sha a lokacin da ya shiga part dinsa sannan ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwa, ya fi karfin 30m ruwan na dukan kansa sannan yai wanka ya fito daure da towel, zuwa yai gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa. Ba rama kadai ba har bakin rai mutuwar Baby Namra ta kara masa daman can dariya ba babinsa bace balle yanzu da yake jin abune mai wahala wani abun dariya ya kusance shi balle har yai ta, a nan ma ya dade yana kallon kansa kamin ya saka kayan bachi ya kwanta.


Da wuri ya farka saboda akwai abunda yake son yi a office, ko da ya fito part dinsa cikin shirin zuwa office ya fito ya shiga part din Hajiyarsa 7:13am. A kitchen ya sameta tana hada musu breakfast, tana da mai aikin amman ta fi ra'ayin girka musu da kanta musamman shi da tasan ba ko wane abincin yake ci ba, gashi da kyama komai tsaftar mace idan hankalinsa ba kwanta ba sai yace ba zai ci abunda ta dafa ba.

 

“Yau da wuri ka tashi gashi ban gama hadawa ba”


“Akwai abunda nake son yin a office fin ne shiyasa”


Ya fada yana daukar cup ya hadawa kansa tea.

“Zan tafi yanzu idan komai ya zama Ready a fada min na aiko direba ko kuma na dawo na ci”


“Okay Allah ya maka albarka”


“Amin”


Ya amsa da dan murmushi kadan a fuskarsa sannan ya fito cire da kofin tea ya nufi motarsa ya bude ya shiga, yana mata key mai gadin ya bude masa gate ya fice, da hannu daya yake driving dayan hannun kuma na rike da  cup din yana kurbawa a hankali.

Yana kusan isa kamfaninsa ya rage gudun da yake yana ta kallon Halimatu ta cikin bakin gilashin motarsa, shi be san abunda take a nan ba kusan kullum indai yayi sammako sai ya ganta idan kuma zai tashi ma yana ganinta tana bawa mahaukacin nan abinci, ko miye alakarsu oho! Ko da yake ita din ma ai kallon mahaukaciya yake mata, shi ganinta da yake kusa da kamfaninsa ma bata masa rai yake domin bayan mutuwarsa babu wacce ya tsana irinta, sai dai duk haka idan ya ganta a gurin sai ya tsaya ya kalleta sai dai idan ya ganta ya rika jin haushinta yana jin haushin kansa, duk ranar da be ganta ba har jira yake ga ko zata zo ta bawa mahaukacin abinci.

To ko shine uban yayanta? Wata zuciyar ta tambaye shi. Oho mata ma ko wanene can ita ta sani Allah yasa ma wata rana ya makureta.... Ayyana a ransa sannan ya karasa kamfanin da kansa ya shiga cikin ana ta miko masa gaisuwa amman ko kallonsu be yi ba balle ya amsa sai wani sham kamshi yake.


HALIMATU POV.

6 MONTHS LATER.....

Al-hamdulillah Al-hamdulillah Al-hamdulillah, da sannu rayuwa ta soma sauya min ta inda ban zata ba, domin ko a mafarkina ban kawo cewar zan samu aiki a kamfanin nan ba, duba da irin mutanen da sukai applying sai dai komai na Allah ne cikin ikon da yarda ya amince aka dauke ni aiki a kamfani, aiki a gurin yamin dadi ba dan komai ba sai dan Kabir kusan ko wace Safiya ta Allah nakan siye abinci a hanya ko kuma na siyo na dafa naje masa da shi idan zanje aikin, haka ma idan na dawo indai akwai canji a jikina zan siya masa abinci na tsare shi sai an tabbatar ya ci ya koshi sannan na dawo gida, hakan kuma na karamin faranta min rai yake ba, har ta kai a yanzu idan ya gama cin abinci na tashi sai ya tashi ya bi har bakin gate din kamfanin sai idan security din sun hana shi shiga sannan ya zauna a gurin ko kuma ya koma can a inda ya saba zama ya zauna har sai na gama aikin ya fito na bashi abincin.

STORY CONTINUES BELOW

Wani irin dadi nake ji, a taimakon abincin da nake bashi a yanzu, ina jin cewar na bawa wani mai bukatar taimako taimako na,  a kamfanin ma kowa yana mutunta ni kamar yadda nima nake bawa kowa girmansa, bana da matsala da kowa ga wasa da dariya sai kace daman can mun dade tare a aikin, bana fuskantar wata matsala a aikina sai dai fargabar abu daya, wato Mahaifin Baby Namra, tun daga lokacin da na fara aiki a kamfanin aka bani takardu da da magazine din kamfanin sai na gane cewar shine mai kamfani kamar yadda na lura da cewar shine mai makarantar da can da Abdallah ya cire su Namra domin a can mna ganshi kamar yadda na taba ganinsa a wannan kamfanin aau daya, domin hotonshi ne a jiki an rubuta masa shugaban kamfanin Ahmad Muhammad Gwarzo, sai dai ba kowa ya san haka ba kasancewar ba a saka hotonsa a kamfanin ba balle sunansa, kusan tun da na zo ban taba ganinsa ba, sai wacan ganin da nai masa a farkon zuwana kamfanin neman aiki.

  A yanzu kam kullum a cikin fargaba nake ina karanta masa hasbunallahu da rokon kar Allah yasa ya ganni har na samu wani aikin na bar masa kamfaninsa, domin ina ji a jikina cewar duk ranar da ya gano ina aiki a karkashinsa sai ya wulakanta ni ya ci min mutumci kamin ya koreni.

    Bayan shi ba ni da wata fargaba kuma ina jindadin aikina, ko ba komai kamfanin yana kusa da inda Abdallah yake aiki, hakan yasa na daukarwa kaina kullum da misalin karfe biyu na rana sai saka order an kaiwa Abdallah abincin rana a office dinsa, tun ina zuwa kullum na kai kudin har na fara biyan na wata wata, sai dai duk da haka Abdallah be taba kira wayata da sunan ya min godiya ko ya nuna min ya jidadin abunda nake masa ba, ko kuma ya gargade ni akan na daina ba, sai dai mai kai abinci ya fada min be taba cewa a daina kawo masa ba, tun daga lokacin da na fara aiki a kamfanin kusan kullum sai na turawa Abdallah sakon Barka da Safiya abun har ya xame min kamar ibada sai dai shi be taba maido min da amsa ba, idan na masa magana a whaspp ko fb sai ya karanta amman ba zai ce min komai ba, tun ina jin babu dadi har na soma sabawa da wannan sabon halin nashi.

Haka zai shigo gaishe da su Mama da Baba gida, ba zai ko kalle inda nake ba haka ba kuma ba zai hana na yi masa magana ba, wani lokacin ya kan amsa min sai dai idan na matsa da magana sai yai mana sallama ya tafiyarsa.

  Gaba daya ya canja min taimakon da yake ba ni ya daina, sai dai ba shi ya dame ni ba kamar rashi sakin fuskarsa da kula ni da yake a yanzu, ga shi Allah ya dauki soyayyarsa da kaunarsa da tausayinsa ya cika min zuciya da su. A yanzu ta kai idan ba zancen Abdallah ba bana son labarin ko wane namiji, duk wata soyayya da nai wa Aminu da Abdulhamid a baya ashe ta karya ce a yanzu nake soyayyar da gaske, haka zan raya dare da begensa a zuciyata da tunanin abubuwan alherin da yai, da girma da yaraba hudu amman tunanin soyayyar wani ta hanani sukuni, idan na ga wani da sunansa sai na ji ya burgeni saboda kawai Abdallah.

  Sai a yanzu na gane cewar na aikata kuskure babba na zabar Abdulhamid na bar Abdallah, a yanzu kam ina ganin laifin Abdallah kadan na cewa yana so a lokacin da igiyar aure take saman kaina, da farko ina daukar cewar fushi yake da ni daga baya kuma sai na fahimcin cewar kamar kokarin cireni yake a ransa ya nesanta kansa da ni, wanda hakan ba mai yiyuwa ba ni a tsakanin ni da shi, har ga Allah na tabbatar Abdallah yana so na, kamar yadda nake jin a yanzu da a raba ni da soyayyarsa kara a raba ni da raina.

  Ko da Abdallah ba zai aureni ba ina son na saka masa da soyayyar da ya nuna min ni da yayana.

“Wai da gaske kike za ki shiga gasar nan?”


Kaina na dago na kalli Hafiza wacce tai min maganar ina murmushi domin na lura kamar bata yarda da zancen da nai na cewar zan shiga tare da yara a wasar da za'ayi Next Week ta children day ba.+


“Why not? Ko dan farincikin yarana ai zan shiga, bani da matsala da kowa yanzu ba aure ke kaina ba balle na ce”


“Amman gaskiya matan hausawa ba sh cika shiga irin wannan ba”


“Ai dai mata suna shiga ko? To nima zan shiga idan na saka wando zan dora abaya a sama na saka karamin hijab dina”


Na fada ina jin cewar har a raina zan yi domin farincikin yarana kawai, domin a yanzu bani da damuwa sai ta yarana da iyayena sai kuma tawa, na tattara komai na aje a gefe, Aminu ma da ya matsa min na fada masa kotu zan kai shi idan be daga min kafa ba, sannan na jadadda masa matukar be saka Sadi a kotu an kwatarwa Namra hakkinta ba ba zan taba yafe masa ba, wanda nake tunanin abu nai wahala yai hakan ko dan Hajiyarsa na san ba zata bari ba.

 

“Yes Momy kuma mu za mu cinye....”


STORY CONTINUES BELOW

Aiman ya fada yana daga hannu tare da dariya, sai na gyada masa kai.


“In-Sha-Allah kuma idan mun yi ta daya, zan yi amfani da kudin na saka ku a wata makaranta private school so that ku samu karatu mai kyau, sauran kudin na rika juyawa ga aikina kamin lokacin biyan wasu yai na san zan samu na biya”


Namra ta yi karaf tace.

“Momy pls ki siya mana kayan wasa kuma pls”


“Zan iya muku, ki yi addu'a Allah yasa mu yi na daya”


“Amin kullum zan yi addu'a idan na yi sallah”


“Da alama dai wanda ya siya miki ticket din nan ke da yaranki yana ji da ke sosai, ko mother letter din nan fa kusan 20k ake bada ita”


Hafiza ta fada tana dago min wata farar takardar mai zagen kamar abun zinari.

“Kuma kin ga ticket ma na shiga gurin kawai 10k ne na shiga game kuma 30 domin ko baka ci ba za su baka wani abu wanda kuma yai na daya million daya da award da kallon azurfa, haka dai na biyu har zuwa na biyar, muma na ga alamar shi wannan bawan Allah da yake ta wahala da ke kamar ba ma sonshi kike ba, oh maza akwai daukarwa kai wahala”


Ta sake fada tana tabe baki


“Baki san waye shi ba, kin taba ganinsa?”


“No kawai dai naga yana ta kashe miki kudi ne hakan nan, ko jiya sai da Mama tai magana har tace zata same ki ku yi magana indai  a aurenshi za ko yi ba, to ki sallame shi kar dawo daga baya yace sai an biyashi”


Shiru nai na dan wani lokacin, idan har Mama ta same ni da zancen ban san me zan fada mata ba, idan har taji cewar kafiri ne zata tsorota ta kuma nemi hanani kulawa wanda na daina tuntuni amman shi ya kasa janye kansa daga jikin kullum sai neman kara shiga jikina yake, na rasa yadda zan yi da shi babu bakar maganar daban fada masa ba babu irin gargadin da ban masa ba amman babu abunda ya canja.

“Yana da kyau Momy amma yana saka sarkar cross kuma yana sawan cin chewing gum....”


Na yi saurin rufewa Namra baki.


“Kar naji maganar nan gurin wani, duk wanda ya fadeta a cikinku sai na dokeshi, tashi ku shiga ciki... ”


A tsawa na yi musu maganar fuskarta babu alamar wasa hakan yasa duk suka tsorata har Amal suka tashi suka shige daki suka bar mu a waje ni da Hafiza, a kokarin dauke hankalinta daga zance na dauko mother letter din na rike ina tambayarta.

“Me ake da wannan hala?”


“Uwa ce zata rubuta tahirin rayuwarta da kuma yadda take kula da yayanta daga karshe sai ta rubuta daga uwar su wane da wane, sai ta saka a cikin dan box din wasika, idan mc ya zo shi zai karanta sai ya fada cewar daga uwar su wane idan anji an san ko su waye ake nufi”


“Wow abun ya kayatar”


Na fada ina jin cewar ni ma zan rubuta komai na rayuwarta a cikin wasikar da kuma yadda nake kula da yarana sai dai na zan fadi sunan da suna yara ba ba, ba so nake a san ni ba kawai dai ina son nao sharing tarihin rayuwata ga wadansu iyayene musamman abunda ya shafi Namra domin kawai ya zame musu darasi su kula da yaransa da kyau, ba kamar yadda ni nai sake har haka ta faru da yata ba, zan rubuta komai nawa a cikin har da rayuwar aurena a gidan Aminu da auren Abdulhamid da soyayyata da Abdallah, haukacewar da Kabir yai da kuma mutuwar Baby Namra fyaden da akai min akaiwa yata, sai dai ba zan fadi sunan kowa a ciki ba.


“Ke fada min ina kike hadu da shi?”


Ta tanbayeni daman na san za a rina, a banza ma Hafiza tai gulma balle wannan mai dalili. Abunka da yar'uwa duk kuwa da kasancewar ba uwar ma daya ba uba ne kawai amman bama boyewa juna abu idan ma ba wanda ya sani ba ba zai taba sanin cewar ni da Hafiza yan uba ne ba, domin a gidan m ba zaka taba sanin yan dakin Mama da kuma yan dakin Inna ba, kowa uwarmu ce idan Mama bata nan bama da matsala ko damuwa mun san Inna zata mana kamai, kusan Hafiza ma a dakin Mama take komai nata a can take yi wani lokacin ita da Mama har sirri suke babu wanda ya sani sai idan sun fada.

Kamin na gama bata labarin har mararta ta cika da fitsari, tsoro duk ya bayyana a idonta da jikinta.


STORY CONTINUES BELOW

“Bari nai fitsari na dawo”


Da gudu ta nufi bandakin da ke tsakar gidamu tai fitsari sannan ta dawo ta zauna tana zaro ido.


“Dan Allah ki ce kin yafe masa mana, Wallahi zai iya fusata ya zo ya halbemu, kin ga dai ni ko dan karatun ban gama ba, balle na ci moriyarsa, ga yaranki kanana, Baba Lafiya ma bata isheshi ba, dan Allah ki yafe masa kar ya zo ya halbe mu dan Allah kema zai iya halbeki Wallahi...”


Da farko dai na dauki maganarta serious daga karshe kuma sai ta bani dariya domin na lura tsoro ya gama cika mata ciki, ina cikin dariya Baba ya shigo bakinsa a haushe yana da far'a.

“Kun ji abun Allah yanzu fa sallamar da kai min ina fita wani ya bani 100k kyauta”


Ni da Hafiza muka hada ido kamin su Inna da Mama su fito daga dakin da murnarsu, gaba dayan gidan sai ya kaure da murna abunka da talaka mai neman na yau da gobe ya samu kyautar 100k a rana daya ina bakin yan gidanmu zai rufu, ni kaina na nuna murna kuma na jidadi ganin yadda Mama da Baba da Inna suke ta murna suna masa addu'a, sai dai ni na san mutum daya zai iya wannan abun wato Abraham.


“Amman Baba kai kadai ya bawa kyautar?”


“Gaskiya bani kadai ba ina tsaye da Malam Isuhu ya min sallama ya miko min 100k shi kuma Isuhu ya ba shi 5k”


“Baba yaro ne?”


“Aa dattijo ne amman ba zai kaini tsufa ba gaskiya, yana cikin wata bakar mota mai kyau kana ganinta ka san mai kudi ne sosai, shi dai mai ja masa motar ne matashi”


“Uhmm”


Na fada ina rafka uban tagumi tare da kallon Inna da ke fadi.


“Allah mai iko sai ka ji wani yayi kyautar abu kamar banza yanzu har dubu dari ka bayar kyauta, wasu Allah yai musu arziki”


Mama ta taya ta.

“Ina jin dai zakka ce, ko kuma irin masu kudin nan da ke bin gidajem talakawa suna ba su kudi”


“Ko dai minene mun gode Allah shi kuma Allah ya saka masa da alheri, daman an kwana biyu ba mu girki da nama ba gobe da safe idan Allah ya kai mu sai a samu mana nama mu ci”


Cewar Baba, sai duk suka dariya ban da ni da ke ta wani tunanin na dabam. Har aka isha'i babu abunda nake sai tunanin yadda zan bullowa lamarin nan, wata zuciyar na fada min cewar na sanar da police kawai n huta ko kuma na sanar dasu Mama idan kuma nai hakan hankalinsu zai tashi, idan kuma na kyale shi abun nan kara gaba zai yi.

Misalin takwas da rabi yaro ya shigo wai an sallama da ni ba waje, da farko na dauka Aminu ne domin shi ma yana min hakan ganin bana daukar wayarsa sai kawai ya aiko kirana kai tsaye sai idan na fita na ganshi, sai dai mafi akari Abraham ya fi min haka, domin shi be tana kirana a waya ba ma, be tana ce min na bashi number ta ba.

Aiko kamar jira nake na zari hijabi na saka na bi bayan yaron da ya aiko kirana, ko da n fita yana can nesa da gidanmu kamar yadda ya saba tsayawa, hango ni yasa shi fitowa daga motar ya rike gambun motar yana ta kallona har n karaso.

“Me kake so? Kana ta bibiyar rayuwata, na fada ka fita daga hanyata, bana kaunar ganinka Abraham kai ne silar lalacewar aurena ba baka aikata abunda ka aikata min ba da har yanzu in zaune tare da mijina... To me kake nema a yanzu?”


“Yafiyarki mana, na rasa gane wace irin mace ce Halimatu, me zan yi ki yafe min? Fyaden da nai miki kuskure ne, na yarda na lalata miki rayuwar aure, amman haka ba ya kara fito da kalar mijinki ne kawai, na nuna miki cewar ba zai iya zama da ke idan wani abun ya same ki ba, and I'm here for you, na ji na aikata laifi amman yafiyarki nake nema, and i promise you zan dauki nauyin yaranki da iyayenki da kanenki, zan inganta rayuwarki”


“Da kudin haram? Kudin da kuke tare mutane masu hakki ku karbe musu abu? To bana so kuma karka sake bawa mahaifin kudinka na haram”


“Su waye muke tarewa muna kwace musu hakki? Halima har addinina n ce zan bari na shiga na ki saboda kawai ina kaunarki amman kin ki aminta why? Daman haka musulmai kuke?”


“Karka kuskura ka kasa zancen addinina a ciki maganarka, kuma tirr da kai ni ba zan auri dan fashi ba dan fashin ma wanda ya keta min haddi”


Ya gyara tsayuwarsa yana kallon.

“Waya ce miki ni dan fashi ne?”


“Miya hada ka da bindiga a wacan daren?”


“Saboda kawai n rike bindiga sai ya nuna ni dan fashi ne, a yanzu ma ina da ita a mota, ke dai ba kisan komai a game da ni ba, ba ki san waye ni ba, iyakar abunda kika sani na miki fyade sai sunana sai kuma bibiyarki da neman yafiyarki da nake”


“Idan na yafe maka zaka daina kula ni zaka daina bibiyata zaka daina zuwa kofar gidan nan zaka daina bibiyar yarana?”


“No ai yafen min da za ki yi shine ki aure ni, ki haifa min yara.....”


Da sauri na rumtse idona ji nai kamar ace akwai wani makami a kusa da ni na daba masa a kirji ya mutu a gurin, saboda zafin da maganarsa tai min, taya mutun zai keta min haddi da aurena kuma yana kafiri ina yar musulma sannan yanzu ya dawo yana min maganar aure har da haifar masa yara, saboda kawai ni Halimatu ai komai nawa dabam ne.... Ji nai an haska fuskata hakan yasa na bude ido ashe wayarsa ce ya haska min a fuska ganin ina hawaye yasa shi ce min.

“I'm sorry ban zo nan dan na saka ki kuka ba, zan tafi see you at Children's Day”


Yana fadar hakan ya koma cikin motarsa yai mata key ya bar ni a gurin tsaye ina hawaye.

“Ba zan je ba, saboda kai ka siyo min ticket din”


Na furta a fili ina ayyanawa a raina cewar ba zanje din ba....

_____________


Wai ashe Abraham yana da team 🤐

  Who can guess what will happen next? 🤗

Hakan nan yau yake sha'awar zuwa gurin aiki da wuri, daman kuma ya tashi ya ji jikinsa sai a hankali so yana bukatar yai aiki da wuri ya dawo gida if possible. And he like to wear a suit today like always sai dai wani lokacin yana saka shadda dan yafi jinsa more comfortable fiye da suit.

  Bayan ya gama shiryawa ya shigo bangaren Hajiyarsa still ya same ta tana aikin hada masa breakfast sai dai yau ba ita kadai ba har da Siyama. As he already knows siyama bata tashi da wuri sai idan makaranta zata je, amman ga a kitchen tare da Hajiyarsa da mai aikinsu har ma da cousin dinsa Khadija wacce kwararriyar banker baker ce. +

“Yau me kuka hadawa haka ne?”

Da sauri dukansu suka juya suka kalleshi domin ba su san da zuwansa ba sai ganinsa da kai a kofar kitchen yana ta kamshin turare.

“Amman Bro you wake early”


Cewar Siyama tana nufo inda yake. Agogon hannunsa ya duba wanda ya nuna masa bakwai da yan mintuna.

“Yeah ina son naje aiki da wuri ne”


“Oh bro i wanted to surprise you.....”


Ta fada tana bata fuska, sai Khadija ta tari numfashinta tana murmushi.

“We can still surprised him dear... ”


Ya kalli Khadija da fuskar rashin fahimta. Sai ta jango masa kujerar kitchen din ta aje bayansa.

“Dan zauna”


Be zauna ba be kuma nuna alamar zai zauna din ba balle har ya furta wani abu. Siyama know him well, he is no nonsense at all, hakan yasa ta hade hannayenta.

“Pls”


Sai da ya kalli Hajiyarsa wace ita ma tai masa alama da ya zauna din sannan ya zauna yana binsu da kallo. Da gudu Khadija da Siyama suka fita daga kitchen din, like 6 minutes suka dawo sai Hajiya ya fita.

“Close your eyes pls”


Be musa ba tunda Siyama ce tai masa maganar, a take ya rufe idon sai ta kama hannunsa yana masa jagora a hankali har suka fita daga kitchen din, gaban dinning area ta nufa shi sannan ta saki hannunsa.

“Now open your eyes....”


A hankali ya bude idon, by surprise yai arba da katon birthday cake mai hotonsa.

“Wow”


Ya furta yana kallon mahaifiyarsa da ke Murmushi kamin ya rumgumi Siyama wacce ke ce masa happy birthday.

“Thank you Blood, Thank you Mom, thanks Sis”


Ya fadawa Siyama Hajiya and Khadija wacce tai masa respond da murmushi.

“So duk kun san yau birthday na kenan, ni na manta sam”


“Taya za ayi na manta ranar da na maifi Ahmad Gwarzo...”


Cewar Hajiya tana murmushi, sai yai murmushi ya kai hannunsa ya debi cake din ya kaiwa Hajiya a baki.

“I love you Hajiya ta”


One after the other ya bisu ya saka musu cake din a baki har Khadija, sannan suma suka ba shi, daga bisani Siyama ta ciko hannunta da cake din zata shafa masa sai yai saurin rike mata hannu ya murda har sai da ta kai kasa tana ihu.

“Wayyo Hajiya....”


“Gwarzo karka kare min ya”


“Hajiya ba zan bari ta bata min tufafi ba today is special day for me...”


Sai duk suka saka dariya har ita Siyamar sannan ya sake ta ya dauki tissue ya goge hannunsa.


“Yau din nan ko? I very very special day for us, i call your friend on phone and i told him ya saka kowa yai surprise dinka da wani abu each and every person a kamfaninka, so karkaje ka dinga musu fada ni na saka su”


STORY CONTINUES BELOW

“Kina da hankali Siyama?”


“No sam sam Hankali wala gare ni a yau, la la la and in the laila akwai celebration... ”


Ta fada tana rawa.


“Hajiya yau yarki bata da hankali”


Ya fada sound so serious domin gani yake yau Siyana hauka take ji how zata kira company su tace kowa yai surprising dinsa, and now tana gaya mishi akwai celebration, shi rabon da yai celebration din birthday sa tun matarsa Halima na da rai.


“Tana da hankali she's just celebrating her brother birthday”


Khadija ta fada tana murmushi Siyama tace.

“Louder pls”


“No ina ganinki da hankali Khadija karki biye wannan”


Daga haka ya juya ya fice yana murmushi, sai kuma ya juyo yana kallon Hajiyarsa.


“A saka min cake dina a fridge pls”


“Okay Breakfast fa”


“Zanje office din na san kamin na dawo kun hada sai na ci, akwai wanda nake son meeting da shi a 8”


“Okay Allah ya tsare”


Sai da ya amsa da min sannan ya fice daga falon ya nufa haravar gidan gurin da ake aje motoci. He choose ya black kalar suit dinsa sannan ya shiga.

   Sai ya kusa isa kamfanin sannan ya rage gudun da yake, like always dan kawai ya gani idan ma din ma Halimatu zata bawa mahaukacin nan da be san alakarsu ba abinci, to his surprise yau be ganta ba sai dai mahaukacin na nan a zaune, haka nan kawai ya faka motarsa gefen titi yana ta kallon mahaukacin he just wanted to see idan zata ba shi abinci yau, ko ma bata ba shi ba shi miye nasa a ciki? Yaja tsaki a maimakon yaja motarsa yai gaba sai ya dauko wayarsa ya shiga whatsapp yana duba status din Siyama wacce ta sika status din da hotonsa tana masa kalamaina na kauna irin na yar'uwa da dan'uwanta, sai da ya dora hotonsa a status dinsa ya rubuta happy birthday to me sannan ya shiga duba na sauran yan'uwansa da abokansa, daga lokacin ne n banks dinsa suka shigo sai kuma fb da sukai masa happy birthday.

Ya fi karfin minti talatin a gurin sannan yai ma motarsa key ya karasa office din, hakan nan yaji baya son fita daga motar ma and he don't know why sai kawai ya ciro wayarsa amininsa kuma abokin aikinsa.

“Happy birthday Boss”


“Thank you, Salim ya ganar Inuwa? Kana ganin zai samu zuwa yau kuwa”


“Yes ai ba zai tsaba alkawari ba amman na san yau rana ce mai muhimmanci a gareka, zan masa jagoran komai kai sai ka huta”


“Thank you zan fito amman sai anjima”


“Okay”


Daga haka ya aje wayar yai reverse ya koma hanyar gida, still sai ya sake tsayawa yana kallon mahaukacin na tsawon five minutes sannan ya cigaba da tukinsa.

HALIMATU POV.

Bayan tafiyar Abraham wani tunanin ya fado min a rai, a iya tunani be kamata na kyale shi a haka nan yana ta bibiyar rayuwata ba, ya kamata na kai shi gurin yan sanda su mana tsakani ko ba komai zan samu salama kuma zan fada musu cewar dan fashi ne ko zai kashe ni sai dai ya kashe ni.

Ban sanarwa kowa ba sai dai na kudirci abun a zuciyata, a daren ban yi bachi ba sai pass 12, ina ta tunanin irin matakin da ya dace na dauk domin na san nan gaba kadan iyayena za su bukaci saninsa to sai na ce musu me?

  Da wuri na shiryawa yarana sannan na karya bayan su ma sun karya suka kama hanyar makarantar wacce ta kasance nesa da unguwarmu kadan, yau ban basu kudin tara ba saboda ina son dafa musu indomie tare da Kabir, da kaina na nufi shagon unguwarmu na siyo indomin sai ya rage naira goma ce kawai canji dan haka na bukaci ya bani chewing gum da ita idan ma na karbar na san rigima kawai zata zama tsakamin Namra da Aiman da Amal kara Adnan yana dan daga kafa wani lokacin baya biyesu.

  Sai da na dafa indomie na zuba musu a cularsu sannan na dauko leda na kwashe ragowar indomin na zuba ciki, a gaggauwace na nufi bandaki nai wanka na shirya sai dai hakan be hana ni shafa janbaki da hoda ba har da kwalli kamar yadda na saba,  riga da zane na atamfa na dauko na saka sannan na saka hijab dina ya saka wayata da a jaka na fito ina yi ma su Mama da Inna sallama.

Sai da na karanta addu'ar fita daga gida sannan na fita, ina karasa titi nai sa'a da mai adaidaita babu kowa a ciki bayan na tare na fada masa ya kai ni police station da ke can unguwar kwaza, wata zuciyar na fada min kar ka kai maganar gurin yan sanda saboda gudun abunda zata zame min, amman kuma idan ban kai ba me zan yi? Haka zan zuba masa ido yana ta bibiyata? Bayan na fada min ko na yafe masa idan ban aureshi ba ba zai daina bibiyata ba. Nesa da station din aka sauke ni domin masu napep ko abu hawa basa karasa har gaban gurin, bayan na bashi kudin na shiga ciki, gabana sai faduwa yake kamar marar gaskiya, abunka da wacce bata saba zuwa gurin yan sanda ba. Kai tsaye na shiga ciki har da yar sallama ta suka amsa min wanda na ganin da yar fuska far'a na nufa na fada masa abunda ya kawo ni a gurin, ba shi kadai ba ko su sauran da suke sauraren labarin nawa sai da sukai mamaki.

STORY CONTINUES BELOW

“Amman kuma ba ki san shi ba?”


“Ban san shi ba ba ni da alaka da shi, kawai dai yace yana so na ni kuma na nuna masa bana sonsa hakan kuma be saka shi ya daina bibiyata ba, and jiya ma sai ga kudi an aikowa mahaifina ina zaton shi ya bada yace a bashi amman shi mahaifin nawa be sani ba, kuma ni ina tsoro kar abun yai nisa ya zame min fitina”


“Kin ce kin taba ganinsa da bindiga?”


“Eh a motarsa ba, ina tunanin dan bashi ne”


“Ko dan kidnapped ba, wannan babban case ne gaskiya, ina ganin abunda ya kamata a fadawa PRo sai ta shiga tai masa bayani”


“No kai ta gurin oga direct zai fi, idan ya hannatawa Pro shikenan, mu sai mu rubuta statement”


Atsakaninsu su uku suke wannan shawarar, kamin dayan ya shiga ciki be dade b ya fito ya ce akwai case din da yake idan ya gama sai na shiga, haka na samu guri a gurin na zauna ina ta kallon wasu mutane da ke shigarda kara da wadanda ake saurarensu suna kare kansu.

Bayan kamar minti talati ya sake lekawa ya fito yace min na shiga, shi yai min jagora ciki har da bude min kofar na shiga sannan ya janyota ya rufe, mutumen da na tarar  yana zaune a irin kujerar nan ta office mai lilo, ya bani baya wanda hakan ya bani damar daga kaina saman ina kallon office din, kamin ya kare wayar ya juyo ya kalleni arba nai da abunda ban tana tunani ba abunda ban taba tsammani ba, a take jakar hannuna ta subuce ta fadi, nai baya da sauri kirjina na mugun bugawa kamar zai fito.

“Ya akai?”


Ya tambaya ni fuskarsa ba yabo ba fallasa.


“Ni ban gane ba, tagwaye ne ku, kama ce, ko kuma kai din ne dai?”


Murmushi yai.

“Ni din ne dai, wa kika kawo kara? Ni ko wani?”1


“Daman kai dan sanda ne kuma kake fashi da makami?....”


“Shiiiiiiiiiiiiiiiiiii”


Ya furta tare da saurin mikewa tsaye ya nufo inda nake, kan ya karaso har na kai hannu na bude kofar na fita da sauri jikina sai rawa yake, ina fitowa na nufi gurin kular abincin yarana zan dauka sai dayan yace.

“Kin masa bayani”


“No waya yake, yace naje na dawo, bari na kaiwa yarana abincinsu a makaranta na dawo”


“Okay ba matsala”


Daga haka na samu na fita daga station din, mamaki ya saka ni mike hanya ina ta tafiya ba tare da na tari abun hawa ba, sam hankalina be bani a gafen titi nake ba har sai da nake tsallakawa ba tare da na saurari horn din da motocin ke min ba. Ban ankara ba na ji abu ya buge bugu bana wasa ba, har sai da nai bayabaya na fadi kan kwalbatin da ke gefen titi.


“Ba ki da hankali ana miki horn amman sai kokari tsallaka titi kike kurma ce ke?”2


Iyakar kokarin da nai na fita daga kwalbatin ne kamin na dago na kalli mai motar wanda ya rufe da fada babu ko tausayi.  Muna hada ido yaja wani bugun tsaki ya koma cikin motarsa da ke bude ko inda nake be sake kallo ba.

“Wawa kai ne mahaukaci tun da baka iya tsayawa ka duba mutane ba, ko tokin be iya ba sai jin kai kamar wani Governor, ko titi na gidanku ne....!”


Be sake ce min uffan ba har yaja motarsa ya bar gurin.

Wani mai acahaba ne ya tsaya yana tambayar idan ban ji ciwo ba.

“Ban jimu ba faduwar kawai nai”


Na fada domin bana jin ciwo komai a jikina.


“Dan Allah ki rika kula idan za ki tsallaka titi irin wadannan ba imani garesu ba”


STORY CONTINUES BELOW

“Na gode”


Na fada idona na cika da kwalla, lallai a yau na tabbatar Ahmad gwarzo be da imani kuma be da mutunci, taya zaka buge mutum ka wuce ba tare da ka duba lafiyarsa ba, ko da yake ni mai laifi da nai kokarin tsallaka titi ba tare da na duba ba, amman duk da hakan da ace mutum ne mai imani da zai tsaya ya duba idan be jimi ciwo ba, wata kila saboda yaga ni ce yasa yai min haka ko kuwa daman can halinsa haka yake?

  Ban bar gurin ba sai da na tari mai napep na fada masa makarantar da zai kaini ta su Namra, wacce ya kamata ace can na fara zuwa kamin na je station din amman saboda gudun kar nai latti yasa na fara zuwa can zuwa da be amfani da komai ba.

  Tsayar da mai napep din nai na nufi shagon da ke kusa da makaranta na siye musu pure water shiga har cikin makarantar na kai musu abincinsu tare da ruwan sannan na fito, na sake karbar wani ruwan na Kabir na fadawa Mai napep din inda zai kaini.

  Daidai kusa da Kabir ya aje ni na biyashi kudinshi sannan na fita na nufi gurin Kabir din na ciro indomie da ke jakata na bashi sai da na tabbatar ya saka hannunsa ya ci ya koshi sannan na bashi ruwa ya sha, ni kuma na mike na fara takawa da kafar da sai a yanzu nake jin tana min wani irin mugun ciwo, kaina sai sarawa yake ina dan jin jiri kadan-kadan. Cike da karfin hali na karasa kamfanin, ba laifi na gaisa da masu gadin gurin kamar yadda muka saba sannan na karasa cikin kamfanin ina tsinginta saboda zafin da kafar take min idan na taka. Duk wanda ke magana da ni idan ya gan ni sai ya tambaya me ya samu kafar sai na ce fadawa nai kwalbati. Haka na nufi bangaren mu na tura kofar na shiga sai na samu Yunus yana musu wani bayani da ban fahimci me yake nufi ba, har sai da ya gama musu sannan ya juyo yana min bayani.

“Yau dai kin zo late, daman ina musu bayani ne akan yau birthday shugabanku, so yana da kanwa Siyama ta kira ni ta ce tana bukatar kowa da kowa yai masa kyau komai kankantarta, na san ba abu mai yiyuwa ba, domin yawa ma'aikatan kamfanin bata sunansu ba ne shiyasa tace haka, so ni kuma na zabi ku da kuke sabbin dauka ku yi masa haka”


Bance komai ba har yai gama fadar abunda zai fada, ina jin a rain kamar ba zan iya ba, taya zan bawa wanda baya kaunar ganina kyauta, amman kuma ai be san wanda ya shi ba, sai dai ni kuma hankali ba zai kaunata ba matukar nai masa kyautar, ho me ma zan bashi me nake da shi da zan bashi.

“Kamar me za mu bada...?”


Abokin aikina ya tambaya.


“Komai kake da shi zaka iya ba shi, ko biro ne idan kuma akwai mai kudi a cikinku sai ku siyo wani abu a nan waje ku bashi, mu na dai son kamin ya shigo mu yi masa kyautar”

Dukanmu muka amsa da to ni dai ba dan raina ya so ba, wasu suka rika fita suna siyo masa abun da ya samu ban da ni da na rasa abunda zan bashi kuma bana jin zan saka kudi na siya masa komai. Kusan duk a tare muna doshi office din nasa, wanda ban taba zuwa ba sai yau, tun daga muka doshi inda office dinsa yake sai na zama bakauya yadda kaban taba ganin kamfanin ba haka na zama, wata kalar wallpaper ce aka kawata gurin da ita mai wani irin daukar ido da kyau, ga wani uban sanyi ac mai ratsa jiki, sai da muk shiga office biyu ko wane da ma'aikaci a ciki sannan muka isa office dinsa, wanda kanshin air freshener mai dadi ya fara yi mana marhabun, ya kawata office din da hotunansa wani gurin yana tare da mahaifiyarsa wani gurin da Baby Namra sai kuma wanda sukai wani a gurin meeting wani da turawa, tebur biyu ke cikin katon office din daya a yana fuskantar kofar shigowa wanda shine babba, sai kuma karami dayake gefe mai dauke da desktop computer har guda biyu bayan laptop din dake saman babban tebur din, sai kuma wata doguwar durowa mai cike da littafan da kuma numbobin karammawa. A kasa gaban teburin aka umarce mu da aje duk abunda muka kawo masa kusan mu goma sha daya, wasu suka aje biron kamar yadda ha fada wasu littafi wasu kuma sun rufe kyautarsu da irin ledar nan mai kyali.


“Ku yi hakuri is like kamar na yi force dinku, tun jiya ya kamata na fada muku amman ba samu dama ba yau din ma sai da na dub status dinta sannan na tuna”


Duk muka shiga nuna masa cewar babu komai ai kyautatawa, duk wanda ya aje juyawa yake ya fita, har ya zama ni ce ta karshe, hannu na saka na cire agogon hannun duk kuwa da kasancewar na mata ne na aje a saka tare da chewing gum daya sannan na juya na fita ina aynnawa a raina cewar wata kila zubdasu zai yi.

    Har na dawo na fara aikina ban daina jin kafata da kaina suna min ciwo ba, hakan yasa na nemi izini na fita daga ward din mu da zimnar na kai kaina titi gurin mai chemist din nan na siyo magani.

Ina kawowa reception nai arba da Ahmad ana nuna masa abu a katuwar plasma dake gurin, wani irin mugu faduwa gabana yai domin na san yadda ya tsane ni balle ace yau ya gano ina aiki karkashinsa.

Da kallo ya bini har na kusan ficewa sai na ji an daga min tsawa da wani irin karfi.


STORY CONTINUES BELOW

“Keeeeeeeeeeee!”


Ba ni kadai ce mace a gurin ba, amman ina jin muryarsa na san da ni yake, hakan yasa na juyo na kalleshi.

“Me kike anan?”


Shiru nai na kasa cewa komai har sai da mutumen da ke kusa da shi ya amsa da.

“A nan take aiki tana cikin sabobin ma'aikatan da aka dauka, zo nan”


Mutanen ya karasa yana min alama dana karaso gurin da hannu. Ba musu na karaso gurin.


“Ku sallameta”


Da sauri na daga kai na kalleshi idona cike da hawaye, tabbas yau da ace Ahmad shi ke da kamfanin nan da sai na yi masa wankin babban bargo, amman ba wannan damar.


“Ka taimaka min dan Allah ina da bukatar aikin nan....”


Na roka ba dan komai b sai dan na san idan har wannan aikin ya subuce min kamin na sake samun wani aiki ne a gareni.

“Ranka ya dade tana da takardunta fa, duka ma'aikatan da aka dauka suna da takardu”


“Ku aje ta reception....”


Shine kawai abunda ya fada har ya juya sai kuma ya juyo yana kallona


“Karki shigo min kamfani da kwaliya, ba dandali ba ne nan”


Kai na gyada masa alamar okay ina share hawayena sannan ya juya ya wuce ya bar a gurin tsaye mutanen da ke gurin na ta kallona. Ji nai ba zan iya zuwa siyen maganin ba saboda kunya da kukan da ya rufe ni na wulakancin da Ahmad yai min a yau. Sai na koma ward din aikinmu na zauna, tsakanin shigowata da zamana be kai minti goma ba wani ya shigo ya canja min gurin aiki zuwa reception.

AHMAD POV.

A hanyarsa ta karasawa gida ne ya kade Halimatu at first ya fito da fada a cikin motar sai dai ganin ita dince yasa shi jan tsaki ya koma cikin motarsa duk kuwa da irin bakaken maganganun da take fada masa, ya kyaleta ne kawai saboda ita din macece baya fada mata yana daukar namiji mai fada da mata ragon namiji, balle kuma ita da ba shi da lokacinta.

  Gida ya koma ya karya sannan ya dawo kamfanin, a reception ya tararda ma'aikatansa a gaban katon plasma dake gurin suna kallon harin da aka kai barno, sai dai ganinsa ya saka kowa ya kama gabansa, ban da Rilwal dake labarta masa abunda ke faruwa. Uffan be cewa Rirwal ba, yana kokarin kama hanyar office dinsa sai ga Halimatu ta fito daga wani bangare na kamfani abunda ya bashi mugun mamaki, kararsa ta kawo? Ko kuma wani nata ne a ciki? Ko wani abun ta zo yi? Da kallo mamaki ya bita har sai da ta kusa ficewa daga gurin sannan ya daka mata tsawa, ta juyo jikin a sanyaye.


“Mi kike a nan?”


Ya tambaya co's idan ma zuwa take kamar yadda ya ganta a wacan karon yai mata warning kar ta sake zuwa masa kamfani yo his surprise sai rirwal yai masa bayanin aiki take a gurin, a take ya bada umarnin a koreta. Sai dai yadda ta marairaice fuska tana hawaye tana rokonshi, yasa shi canja mata position a maimaikon korar gaba daya.


Kai tsaye ya nufi office dinsa ya bar a gurin tsaye tana hawaye da suka saka shi jin babu dadi, yana tura kofar office din farko mutane da ke office din ya mike tsaye yana gaisheshi, haka ma na biyu sannan ya shiga office dinsa.

  Sam ya manta da zancen da Siyama tai masa cewar tasa ayi kowa ya bashi gift sai da yaga taren abubuwan da ba zai iya tsayawa ya tantace ko kiye da miye ne a gurin ba. Gaban teburisa ya karasa ya zauna, hannu ta kai ya danna telephone dinsa.


“Zo”


Shine kawai abunda ya fada ya sannan ya mike tsaye ya cire rigar dake jikinsa ya dorata a bayan kujera. Mutane da ke office na biyu ne ya shigo da sauri sai Ahmad ya nuna masa kayan dake kasan tebur din.

“Kwashen abun nan ka san inda zaka kai su... ”


Ya fada yana masa nuna da baki idonsa na kaiwa akan wani agogo da chewing gum kwara daya dake gefe agogon. He don't know why he find it so intereste to touch.

“Mi komin wannan agogon”1


Mutumen ya dauko ya miko masa, sai ya karba yana dubawa agogo chewing gum diary na daya daga cikin abubuwan da his late wife Halima take bashi as a gift a idan yai birthday, tun kamin ta aureshi har bayan aurensu. Ji yai ba dadi tunawa da matarsa da yai, da kansa ya duka ya dauko cingon da wani karamin diary dake can gefe ya nufi kujera ya zauna.

“Kasan wa ya min kyautar agogon nan da diary nan da chewing gum din nan?”


“Wallahi ban sani ba ranka ya dade, su da yawa suka shigo kuma ban san waye ba cikinsu dan ba gabana suka aje ba”


“Okay take the rest”


Dorowarsa ya bude ya saka diary da agogon a ciki sannan ya bude chewing gum ya kai bakinsa. He can't remember when last na ci chewing gum sai yau hakan yasa ya ji ya masa tauri, or maybe saboda wannan karami ne ba irin mai tsada da ya saba ci ba. Haka nan kawai Halima ta fado masa a rai, did she deserved to work a kamfaninsa? Bayan dazu dazun nan ma ta gama zaginsa, ashe kuma ta san a kamfaninsa take aiko amman ta ci masa mutunci? Ko da yake shi ya kadeta kuma be tsaya ya dubata ba yai tafiyarsa, amman duk da haka ai be kamata tai masa rashin mutumci ba. Laptop dinsa ya janyo ya bude ya fara duba wasu abubuwan.

  After like 40 minutes Yunus ya shigo masa da wasu takardu, after ya gama masa bayani yake tambayarsa.

“So ka biye shiriritar Siyama kasa am bata min office da gift ko?”


Yunus yayi dariya.

At least ai an saka ka farinciki, tunda birthday ka ne, ban saka kowa yayi ba amman dai na saka sabbin ma'aikatan mu ne su baka abunda ya samu”


“Nope ka san ba komai ke burge ni ba”


Har ya dauke kai sai kuma ya juyo da sauri.

“Sabbin ma'aikata? Har da wannan farar mata tana nan ciki....”


“Wace farar mata?”


“Wacce na saka aka canjawa position dazun baka nan?”


“Yeah amman na samu labari, har da ita dukansu na saka ai ita ta aje maka chewing gum da agogo”


Jimmm Ahmad yai.

“O.... Okay....”


Ta fada yana daina tauna chewing gum tare da yatsuna fuska...Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 6 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...