GOBE NA CHAPTER 5 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 5 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 5 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

 GOBE NA CHAPTER 5 BY KHADIJACANDY             Www.bankinhausanovels.com.ng 
ABDALLAH POV.+

Tukin motar kawai yake zuciyarsa na sosuwa da kukan da Halimatu take yi, on the other part kuma maganar da Ahmad yai ta tsaya masa a rai. A iya tunaninsa duk mai kokarin cin mutunci Halima yana yi ne saboda yana ganin bata da mai tsaya mata kuma ana ganinta a mace mai rauni.

“Wata kaddarar, ta kan zabi wasu mutanen ta tare musu ko wane irin fada, ta tsaya musu ta hana ni ganin abun ki ko damuwa. Wata kaddarar kuma jefa wasu take a damuwa da bakinciki ta saka har duniya ta juya musu baya, mi yake damuna ne? Miyasa komai ni ce komai ni ce? Na gagara samun farinciki ko dan kankane dan kannen kamar haka...”


Ta nunawa Hafiza yatsanta tana hawaye.


“Komai ni ce, komai ni ni din dai Halimatu na fi kowa shiga cikin matsala, mutane gasu nan ina ganinsu suna farinciki amman ban da, kin gansu?”


Hafiza ta kasa ce mata komai sai kuka take yana rike mata hannu.

“Ga su nan fa ina kallo ke ba ki gansu ba?”


Ta fada tana nuna gilashin motar, da gaske mutane take gani kwakwalwarta na kawo mata abubuwa da yawa, ciki har da rayuwarda tai a baya duk abunda ya zo daga bakinta fada take, abubuwan da take fada ba komai ba ne sai damuwarta. Kuka take tai dariya a lokaci daya kamar wata tabbabiya.

Ta kalli Hafiza dake mata kallon tausayi tana hawaye.


“Wacece ke? Na baki labarina? Ni wata mace ce mai haduwa da abubuwa kala kala”


Sai kuma tai shiru ta sake kallon Hafiza ta kalli kanta.

“Wacece ni?”


Abdallah na jin hakan ya busar da iskar bakinsa ya faka motarsa gefen titi ya fita be dade ba sai gashi ya dawo rike da gorar ruwa ya bude motar ta gafen da Halima take ya cire murfin gorar ya kai mata ruwan a baki, a Hankali yake bata ruwan tana sha sannan ya cire gorar daga bakinta ya kai bakinsa ya kumda ruwan a bakinsa ya fesa mata a fuska, runtse ido tai na yan dakiku sannan ta bude kyakkawan idanuwanta sukai arba da na fuskar Abdallah.

“A ina muke miya faru?”


“Babu abunda ya faru”


Mikewa yai tsaye ya bayan ya bata amsa ya rufe motar ya zagaya ya shiga side dinsa ya tashi motar.

“Miya faru miyasa na jike ina zamu je?”


“Asibiti”


“Ka kai ni gida”


Ta fada kai tsaye.


“Kina da bukatar ganin likita”


“Bana bukata Abdallah bana bukatar kowa ya rabe ni a yanzu balle har ni na rabi wasu, duk wanda ya rabe ni sai wani abu ya faru da shi....”


Bata gama fadar abunda take fada ba ya daka mata tsawa.

“Ya isa haka kike sakawa kanki tunani kala kala har abun yana taba kwakwalwarki, I'm sure idan level din gushewar hankalinki ya wuce iya nan ko yayanki ba za su zauna da ke ba....”


Ta dago kanta ta kalli Abdallah ta madubin gaban mota idonta cike da kwalla.

“Ba ni da hankali kenan? Shiyasa na ke jin kamar ina bachi kamar na suma, ashe gushewar hankali ne? Kenan haukace ta kama ni?”


Ta lumshe ido ta a hawayen da Abdallah yake jin zubarsu har cikin zuciyarsa, har yaji ina ma be fada komai ba ina ma furta komai ba!

Har ya kai ta kofar gidan ta bude mota ta fita ta shiga gida be daina kallonta ba, sai ta shige gida sannan Hafiza ta bude motar ta fita sai ya kirata.

“Hafiza dan Allah a kula da ita, bana son nai mata cilas a zuwa asibitin ne yanzu, amman zuwa gobe zan turo direba ya maida ita kin ga ai ba su bata sallama ba kuma tana bukatar kulawar likitoci, and karki barta ita kadai pls shi ke kawo yawan tunani ku rika yi mata abunda zai sauke mata hankali”


STORY CONTINUES BELOW

“In-Sha-Allah, mun gode Ya Abdallah”


Be ce mata komai ba yai ribas ya dauki hanyar gidan Hajiyarsa zuciyarsa cike da tunani kala kala. Sai da ya faka motarsa harabar gidan maganar Halimatu ta fado masa a rai. Tabbas sukan kaddarar kyakkyawa ta musu rumfa ta tare musu ko wane fada, ta musu gata, bayan kuma ba zabin su ne ba hukunci na Allah. Idan auna yadda rayuwa ta shimfida musu kyakkyawar rayuwa da kuma rayuwar Halima sai ya ji imani da tsoron Allah ya kara kama shi, lallai ba yin kansa ba ne, domin yana da tabbaci da bawa ne yake zabawa kansa irin rayuwar da yake so da Halimatu bata zabi rayuwar da take a ciki ba a yanzu. A duk takunsa sunan Halimatu ke yawo a kansa, ko ina zai motsa tausayi ya mamaye shi, ya kasa ganin laifinta ya kasa samun hanyar rabuwa da ita a kullum kaddara kara kusanto masa da ita take.

Ko da ya shiga falon idonsa ya canja kala saboda damuwa. He got lucky Hajiya ce kadai a falon tana kallon wayarta. Sai da ya tsaya ya cire takalmin kafarsa sannan yai sallama ya shiga cikin falon, a kujerar da ke fuskantar ta Hajiya ya zauna yana gaisheta. Ta amsa masa tana aje wayar a gafenta domin ta hango damuwa a fuskar danta kamar yadda ko wace uwa mai kula take gane idan danta yana cikin bacin walwala ko kishiyar hakan.

“Husaini lafiyar ka yau kuwa?”


Dagowa yai ya kalleta a hankali.

“Ban san yadda za ki ji idan na tambaye ki ba, ban san ya zaki dauki tambayar ba, amman Hajiya kin taba tambayar kanki ko ki yi tunani miyasa Allah yai mu masu rufin asiri kamar haka?”


Sakin baki tai tana kallonsa kamin ta amsa.

“Ah Ah daman can Allah ya kaddara mu din masu arziki ne”


Ya gyada kai.

“Haka ne da yai mana arzikin kuma sai ya hada mana da farinciki, wasu kuma ya ba su arzikin ya hana su farinciki, wasu kuma ya ba su farincikin ya hana su arzikin, wasu kuma ya hana su arzikin ya hana su farinciki yadda ya so haka yake haka yake kasancewa, duk a cikin ikonsa ne”


“Wai miya faru ne, ban gane wannan maganar ba?”


“Halima Hajiya”


Yana fadar sunanta sai yai shiru kamar ba zai cigaba ba, Hajiya kuma ta gyada kai.

“Zancen kenan Halimatu Halimatu, ka kasa cire matar nan a ranka”


“Hajiya ta ya zan cire abunda ba ni na sakawa kaina shi ba? Da ina da iko da dama da ban bar zuciyata ta kamu da son Halimatu ba tun farko”


“Dan Allah na hada ka da girman Allah ka bar yarinyar nan, ka daina shiga zabgarta ka manta da ita a rayuwarka”


“Idan umarni ne zan bi, idan kuma shawara to zan amsa miki da cewar Wallahi ba zan iya ba Hajiya, Soyayyar Halimatu a zuciyata kaddara ce, Hajiya na san Halimatu tun kamin tai aure, amman Allah be dora min kaunarta sai da tai aure ta haifi yara biyu, da igiyar aurenta na kamu da sonta Hajiya, shim ba ki yi mamaki ba? A yanzu na tabbatar ba son ne kawai a kaddarar da ke tsakanina da ita ba, har da taimakon rayuwarta da tsaya mata a wasu abubuwa, kamar yadda Allah yake bawa wani bawa abinci a karkashin wani bawa, ko yai maka kyauta da hannun wani bawan”


Taso yai ya baro kujerarsa ya zauna kasa yana kallon mahaifiyarsa da duba irin na yaro mai neman dauki a gurin mahaifiyarsa.

“Dan Allah karki hana ni yi mata ko wane irin taimako Hajiya, yarinyar tana cikin damuwa tana bukatar mutane a kusa da ita”


“Halima ba yarinya ba ce, ka daina mata kallon yarinya, duk mace da zata haifi yara hudu ta san me take”


Hajiya ta fada tana kallon wani gurin fuskarta a hade.

“Yarinya ce Hajiya haihuwar da taima ta sauri ce, har yanzu Halimatu bata haura 26 ba, tana da rauni da yasa Hajiya, damuwa ta mata yawa yanzu har rasa tunaninta take, damuwarta kawai take iya karantowa idan tai losing memory ta”


STORY CONTINUES BELOW

“Ba damuwa bace matsalar Hassan ya fada ai, tana shaye-shaye kuma duk mai shaye-shaye dole ya hadu da irin wannan matsalar gasu nan muna gani sai haukacewa suke, ni ina mamakin wace irin damuwa ce da ba za abar wa Allah ba, damuwar me ma? Idan bayan cin amanar da tai Hassan ya sake ta... ”


Bata karasa Abdallah ya tafi numfashinta.


“Hajiya da gaske kin yarda Halimatu ta aikata abunda Abdulhamid yake zargi? Na rasa gane dalilin tsanar Halima da kike a yanzu, mace da za tai aure ba ta dace ba, ayi ma yarta fyade mijinta ya saketa saboda haka, ta dawo ta bar yayanta da aikinta ta auri d'anki da bashi da lafiya wata kaddarar ta fada mata a keta mata haddi da aurenta, kuma d'anki yai mata sakamako da saki a lokacin da take bukatarsa ki kasa ganin tausayinta? Wallahi na tabbatar da Abbah yana da da Abdulhamid be isa ya saki Halimatu ba, domin yana yawan fada yayansa ba su isasu taba masa yan'uwa ba, yan'uwan ma Baba Dahiru mutunen da be a shi da amini irinsa, duk inda Abbah ya saka kafa kafarsa tana nan, ina tuna lokacin da Abbah yake mana wasiya da son zumunci da taimakon masara shi, musamman Baba Dahiru, babu irin neman arzikin da ba su yi tare da Abbah ba, amman shi Allah be bashi ba, daga karshe ya koma ciwon kafafuwa ya tare a gida, sannan Allah be ba shi yaya maza ba sai a lokacin da tsufa ya kama shi balle su taimake shi, matan kuma babu wata mai tsiyayar sana'ar da zata iya taimaka masa sai Halimatu da take aiki kamin ta rasa aikin nata, yanzu macen da ta taso a irin wannan rayuwar bata baki tausayi ba?”


Tsawa Hajiya ta daka masa.

“Bata ba ni ba...! Bana kaunar yarinyar nan Husaini, ita kadai tasan bakin nufin da ke zuciyarta shiyasa take haduwa da abubuwa, da gangan ta taki soyayyarka ta auri dan'uwaka, ta barka kana ta wakenta, shi kuma yana can zuciya cike da kuncinta, ai ko dan hallacin da kake mata be kamata tai maka haka ba, ta san kana son ta kuma yar ta yarda ta auri dan'uwanka bayab kuma ta san ba da zuciya daya zata zauna da shi ba, ko da ma zaman ya yiyu da wane ido zata kalleka? Ina da tabbacin Halimatu taja Hassan a jikinta ne ta nuna masa zata aureshi saboda ta musguna maka, ashe ba kai kadai tai niyar ciwa mutunci ba duka ku biyun ne, ina da tabbacin Hassan ba zai taba yafe maka ba idan har ya gano ka taba sonta kuma ka bari ya aureta, taya zan so yarinyar Husaini ka fada min, ku yan biyu ne a mahaifa daya kuka rayu, ciki daya kuka fito a rana daya ta sani kuma ta aikata wannan abun? Ba yanzu ba, gaba na ke hange tsabanin da mahaifinku yake gudun kar ku samu kuna daf da rusgawa a wannan ramen matukar baka cire kanka daga dramar wannan matar ba”


Ya girgiza mata kai.

“A'a Hajiya, kaddarar ce a haka, ina da tabbacin da ni ta aura da ta samu jindadin da ta rasa har ma da doriya, amman wahala da bakinciki be kare mata ba shiyasa ta auri Abdulhamid sai waenan abubuwa suka faru da ita”


Wannan karon kallon tsoro Hajiya tai masa.

“Na bonu wannan wane irin abu ne Husaini? Wani irin so kake mata haka?”


Hajiya na masa tambayar ya lumshe ido ya dora kansa saman kafarta ta dama yana sauke ajiyar zuciya.


‘Wani irin so ne, wanda hannu be isa ya rubuta ba, ba ki ba zai iya furtawa ba, zuciya ta cika da kaunar Halimatu, rai na ta aikin begenta ta mamaye illahirin jiki da tausayinta, babu gurbin ganin laifinta, balle kiyayya ta samu muhalli...’


A zuciyarsa yake wannan maganar a fili kuma sai ya bude idon ya dago kansa ya kalli Hajiya ya ce.

“Tausayinta kawai na ke”


“Ka fara bani tsoro, duk yadda na ke tunanin abun nan ya wuce nan, sai dai ina gargadinka kar ka kuskura ka bar dan'uwanka ya san cewar wata alaka ta taba shiga tsakaninku”


Shiru yai na few minutes.


“Hajiya kin san miyasa na zo yanzu? So nake ki saka Abdulhamid ya maida aurensa da Halimatu”


STORY CONTINUES BELOW

Kallonsa Hajiya ta tsaya yi kamin ta mike tsaye.

“ Ada dai ina maka kallon mai hankali da tunani, to yanzu na gano baka da shi, Halimatu ta dauke ta tafi da shi, ai zamanta a gidan dan'uwanka ma hatsari gareku sai yanzu na gano, kuma Al-hamdulillah da ya saketa Allah ya hada kowa da rabonsa”


“Wallahi Hajiya tana bukatar Abdulhamid a kusa da ita, dazun ma da ya rasa tunaninta maganarsa take min, hannunwanta ta nuna min ce min take na kalla na ga yadda Abdulhamid ya rabu da ita, ya kasa yadda da ita ya kasa riketa....”


Tabe baki Hajiya tai.


“Wani makircin sai mata, kai miya kai ka gurinta?”


Be boye mata komai ba, ciki har da marin da Ahmad yai mata.


“To Allah ya kyauta yai mafita”


Shine abunda Hajiya ta fada ta shige dakinta, ta kasa samun muhallin da zata sake kaunar Halimatu a ranta, ada kam tana kaunarta sosai amman ban da yanzu da take ganin kamar Halimatu na son tarwatsa mata kan yaya ne. Sai 10 ya bar gidan bayan ya yanke shawarar tunkarar Abdulhamid kai tsaye da maganar.

AHMAD POV.

Ya kasa barin kowa yai jinyar yarsa ciki kuwa har da mahaifiyarsa, zuciyarsa ta cika da rauni har yake ganin idan ya daga kusa da Baby Namra zai iya rasata, mutuwar mahafiyarta yake tunawa and think he's not ready to bear the pain.

After yayi losing mahaifiyarta ace yanzu ita ma ya rasa ta? The pain was almost more than he could bear.

Tun da aka shigo da ita ICU bata motsa ba, yana ganin numfashinta yana tafiya yasan yarsa tana da rai, amman ba shi da tabbacin za ta tashi.

Iskar bakinsa ya busar yana neman ta inda iska zai shiga hancinsa ya huda zuciyarsa ya zauna ko ya samu sassauci. Be taba jin ya tsani wata hallita ba kamar yadda ruhinsa ya cika da tsanar Halimatu. Abubuwa mabanbanta zuciya take raya masa, wata kila wulakanta masa Y'a akai har ta kai ta je waje ta fada rijiya, wata kila ma tsawa tai mata shiyasa ta ji haushi ta fada rijiya, ko kuma ta koreta daga gidan ita kuma taje gurin rijiyar, what if yarta ce ta jefata? Ya mai akai ta fada rijiya?

“Ki yi addu'a kawai yata ta rayu, ya rabb pls save me”


Ya furta yana maida numfashi da karfi, sannan ya kalli tafin hannunsa, wanda tun a lokacin da ya mare Halimatu hannunsa yai sanyi har yanzu, maybe because be taba marin mace ba sai yanzu kusan shi a rayuwarsa ma be taba dukan kowa ba sai ita. Ji yake ya zama wani irin mugun mutum idan ya tuna ta, yadda zai sarrafa rayuwarta idan yarsa ta mutu kawai yake tunani, kamin ya kai hannun nasa ya rike hannun yarsa..........

Runtse ido yai be bude ba sai da Hajiya ta shigo tare da likitan da suka fita dazun.

“Gwarzo ya kamata kaje gida ka huta fa, 12 ta yi”


“Hajiya ina son na maida ita Abuja a akwai wata asibiti a can wata kila za ta fi samun kula fiye da nan”


Likitan ya matsa kusa da Namra da sauri ya taba ta, babu alamun numfashi a tare da ita, a take hankalinsa ya tashi ya fara bata taimakon gaggawa amman mai kira yayi kira wanda ya bada aro ya karbi kayansa, fita yai ya shigo da wasu likiton abunda ya kara tadawa Ahmad hankalin kenan, ta yadda ya ga fuskar ko wannensu da yadda suka ja zanen asibitin suka rufe ita sai ya zuba hannayensa aljihu ya daga kansa sama ya rumtse ido.

“Na yi imani da kai Allah, kai kake kashewa ka raya, La'ilaha illallahu..... ”


Ya furta yana jin kamar babu komai a zuciyarsa, duk kuwa da ya kasa gasgata yarsa ta tafi ta bar shi da gaske. hajiya kam fashewa tai da kuka tana ta salati har ta kasa tsayi sai da aka fito da ita daga dakin.

   Dafa shi da Doc Nura yai ne yasa shi bude ido ya kalleshi.


“I'm sorry Gwarzo take heart”


“Da gaske ta rasu?”


Ya gyada masa kai sai ya runtse ido, ya bude yana murmushi.

STORY CONTINUES BELOW

“Subhanallah”


Ya juya ya kalli gawar Baby Namra, sannan ya sake kallon Doc Nura.

“Dan Allah ka taimaka ka kaini gida i don't think zan iya driving”


Har zuwa lokacin da ya fadawa Doc Nura haka, be ji komai a ransa game da mutuwar yarsa ba, ya yarda ta mutu amman be ji zafi ko jin kewa ko tausayi a ransa ba, be kuma san da dalilin hakan ba. Wani yanayi yake jin kansa ba damuwa ba bakinciki.

A motar asibiti aka saka baby Namra, shi kuma ya shiga Motar Doc Nura Hajiya da darebanta kuma suka shiga nasu motar, aka baro motar Ahmad asibiti har sai da direban ya dawo ya dauka. Hajiya ce da kanwarsa suka kira familynsu suka sanar musu mutuwar Baby Namra. Hajiya na aikin hawaye yarta na rusa kuka wato kanwar Ahmad wacce ta shaku da Baby kamar wata kawarta,

Ahmad kam part dinsa ya shiga ya kwanta saman gadonsa rairaim ya lumshe idonsa yana maida numfashi a hankali. Wayoyinsa na ta ringing amman ya kasa ko da motsawa balle ya dauka....

AMINU POV.

Zaune yake Sa'adatu na kwance saman jikinsa hannunsa a cikin rigarta yana ta wasa da kirjinta, sam baya jin komai ba ya jin cewar abunda yake aikata akwai zunubi duk kuwa da kasancewar yasan sakamakon mu'amala da matan banza balle mace mai aure kuma kawar matarsa.

Haka yake a bangarenta bata jin cewar cin amanar mijinta take, ta dauki alhakin Allah da na mijinta ga kuma na yayanta hakan be taba damunta ba, taba taba jin ko ras a ranta zuciyarta tana nishadantuwa da alfasha kamar yadda shi ma yake ji.

“Wallahi na rasa kwarin guiwar da zan fada mata cewar zan dauko yayana”


“Wai kai wani irin tsoro kake mata ne? Tana matarka amman ko magana zaka mata sai ka rikice”


“Wallahi nima ban sani mugun tsoronta nake kamar mutuwa”


Ta tabe baki sannan ta tashi zaune.

“Ni dai dan Allah ka yi duk yadda za ka yi ka dawo da Halimatu, ta zauna cikin yayanta, daman can ban jidadin rabuwarku ba domin bana son naga ana raba mace da yayanta, dan tsabani kadan daga tambaya fita unguwa sai ka saketa”


Iskar bakinsa ya bursar domin yasan shi ya fada mata haka cewar ya saketa saboda ta fita unguwa ba da izininsa ba. Amman yanzu yana son ya dawo da ita ko dan arzikinsa ba yana jin kamar yafo samun natsuwa yayi yadda yake so a lokacin da yake auren Halimatu ba kamar yanzu ba, uwa uba kuma ga arzikinsa ance yana tare da ita. Wayarsa ya dauka ya soma lasawa yana fadin.

“Zan dawo da ita dole ma ne na dawo da ita, amman yaran zan fara karbewa tukuna yadda take da shegen son yara dole ta biyo su”


Bayan ya fadi haka ya kara wayar a kunne.

“Babyna ya kike”


“Lafiya kalau Baby kana ina?”


“Ina gurin aiki amman yanzu zan iso gida”

“Sai ka iso love you”


“Love you too”


Ya aje wayar yana tuna lokacin da yake auren Halimatu, at any time zai iya shiga gidansa kuma sai a time din da ya so dawowa zai dawo ba kamar yanzu ba, da wannan ta saka masa ka'idar indai zai dawo gida ya rika kiranta yana sanar mata, and be isa ya dawo pass 9 ba, a yanzu gida yake sallah isha'i wani lokacin har da magariba ma, be isa ya shirya tafiyar karya ba, balle har ya dauki wata macw su je tare, shi yake batawa Halimatu rai amman tai ta bashi hakuri, ba kamar wannan ba da ita zata bata masa ran kuma ya bata hakuri wani lokacin har da kukansa, gaba daya rayuwa ta masa juyin masa jindadi yai masa upside down. Shi kansa yanzu ya kasa gane kansa ga tsoronta ya cika masa zuciya ko magana zai mata fargaba yake.

Mikewa yai tsaye yana sauke ajiyar zuciya.


“Ya kamata na je gida yanzu, idan kin gama ki rufe dakin ki basu makullinsu”


“Okay”


Ta fada yana gyara rigarta.

STORY CONTINUES BELOW

****

Murja na aje wayar ta kalli Sadi tai saurin sauka ka gado.


“Gashi nan dawowa”


Shi ma zabura yai ya sauka daga kan gadon ya dauki rigar shaddarsa ya saka.

“Abunda muke fa nake tunanin wata rana asirinmu zai tonu, shiyasa na ce miki mu rika haduwa wani gurin kar wata be kira ba ya riske mu”


“Ni fa ba zan iya yawo boye boye ba sai a fara cewa ana ganina ina yawo, amman kai idan ka zo wa ya san abunda ya kawo ka gidan yayanka? Kai dai ko ka gaji da ni ne?”


Bakinsa ya kai yai mata kiss


“Ina zan gaji da ke Murja, tun kina waje ban gaji da ke ba balle yanzu da kike gidan yayana”


“To ka tafi dai kar ya tararda kai sai mun yi waya”


Ta fada tana turashi, ba musu ya dauki keys dinsa da wayarsa da ya saka a silent ya fice da sauri ita kuma ya nufi wardrobe ta dauko zane ta daura sannan ta bude karamar jakarta ta dauko kullin wani abu ta nufo kitchen da shi, kular miyar taushe ta bude ta kwance abun ta zuba kadan sannan ta saka spoon ta garwaye miyar ta fito da sauri ta maida maganin a muhallinsa ta shiga bandaki.


HALIMATU POV.

Me yake faruwa da ni? Da gaske hauka na ke a yanzu? Tsantsar damuwa ce ko kuma shaye-shaye da na fara ne ko kuma gamu nai? Har na shigo cikin gidan mu bana raba dayan biyu ba. Dare ne a lokacin amman a gidanky kamar rana, domin kowa yana farkewa cikin da har da yayana. Sannu kowa ke min suna ta min kallon tausayi, ni kuma na amsa na zauna q tabarmar da aka shimfida tsakar gidan.

“Momy...”


Muryar Namra ce da na kalleta sai ta kara boya bayan Aisha tana hawaye, can kuma ta leko.


“Momy dan Allah ki yi hakuri karki da ke ni, Wallahi ba ni na jefata rijiya ba, ita ce ta hau taba dirowa tana hawa shine murfin ya balle ta fada ciki Wallahi ba ni ba ce”


Ta fada cikin kuka kamin Inna ta karba mata.

“Dan Allah karki mata komai Halimatu, tun dazun take dakonki, ta kasa zaune ta kasa tsaye ta ce idan kika dawo yanka ta za ki yi, ki dauki abun nan a matsayin kaddara”


Idona ya cika da hawaye tausayin yata ya kama ni, sai na mika mata hannu alamar ta zo.


“Ba za ki min komai ba”


Na gyada mata kai sai ta tako ta zo gurin ta kama hannuna nawa ni kuma na jata jikina na rumgume, ni da ita muka fashe da kuka a tare. Ashe ba mu kadai ba, har sauran kanena da Inna sai da sukai hawaye ban lura sai da na tashi zan je dakin Mama.

Wani abum hamdallah a lokacin da na shiga dakin Mama sai na tararda ita a kwance magani a gafenta da ruwan zafi, daman can na san tana da hawan jini sai dai ba kasafai yake tashi ba sai idan wani abun ya faru ko ranta ya bace sosai, wannan karon na san tashin hawan jinin nata baya rasa nasaba da abunda ya faru. A gafen gadonta na na zauna kasa na dora kaina a saman gadon ina bachi ina kuka, Adnan ya shigo ya dora kansa saman cinyata sai kai hannu na dafa kansa.

“Bana da sa'ar komai a rayuwata, ko a lokacin da na haife ku mahaifinku ce min yai na tara masa yaya, zan tsofar da shi....”


Tuna ba ni kadai na ke ba yasa na yi saurin yin shiru sai dai hakan be hana Adnan fahimtar yarena ba.

“Kamar yaya Momy”


Hannu na kai na rufe bakina na hade yawu. Sai ya dago ya kalleni.

“Momy dan Allah ki daina kuka”


Ya fada yana kokarin fashewa da kukan. Hannu na kai na kama fuskarsa na rike.

“Adnan kai na fara haihuwa Allah ya raya min kai, ya inganta rayuwarka yai maka albarka ba baka ikon kula da kanenka ko bana raye”


“Ameen”


Mama ta amsa daga kwance da take tana kallona. Saurin share hasayena nai.


“Ashe kin farka ya jiki?”


“Ya na ki jikin?”


Shiru nai na wani lokacin ina kallonta kamin na amsa.


“Na ji sauki”


Sai ta tashi zaune cikin rashin kwarin jiki ta shiga bandakin da ke cikin dakin.a zaune nai bachi duk yadda Mama ta so na kwanta sai na kasa ko na kwanta ma bachi baya daukata hakan yasa na tashi nai alwala na raya daren da nafila. Misalin hudu da rabi nai sallamar karshe a lokacin da na daga hannuna na yi kirari ga Ubangijina nai salati ga annabi na sai na rasa mi zan fara roko, lafiyata ko ta Baby Namra ko farinciki ko gushewar damuwa?

“Allah ka min mafita ka tsaya min, ka isar min a komai da komai ka zama gatana, ka yafe min laifukana, ka sadani da rahamarka”


Bayan na gama na sake rufewa da salatin Annabi, ban tashi daga gurin ba har aka kira sallah asuba, bayan na gama sallah na dauko qur'ane na soma karantawa har bakwai da yan mintuna sannan na tashi, ina jin kaina na juya kafafuwana kuma sun yi nauyi kamar yadda idanuwa sukai.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Baby Namra ta rasu gashi ana sanarwa a Zamfara redio”


Shine abunda ya dira a kunne na da muryar Salma. Sai ni ma na karba mata a Hankali daga cikin dakin da nake tsaye.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Sai nai bayabaya har na kai jikin ginin dakin na jingina, hawaye suka ce min salamu alaiki......

Hannu na kai na rufe bakina, wannan karon ba kuka ido da baki kawai nake ba har da zuciya da kwakwalwa da jikina amsa amo yake. Kuka nake ta ko'ina irin kukan da ban taba yi ba, irin kukan da ban taba sani yana tare da ni ba karkawar nake kamar wacce ta shekara a cikin kankara hakorana na hadewa da juna suna wata kara, wani kalar hayaki nake ji a cikin kaina.+
“Ashe har yanzun kukan be kare ba Halimatu”

Mama ce tai maganar sai na dago na kalleta tsaye take jikin kofar dakin da nake ita ma kuka take kamar ni. Kai na gyada mata kamar wani abun arziki sai kuma na ji ana fisgata kafafuwana suka kasa daukata, wani farin haske ya baibaiye idona tashin hankali da nake ji a yanzu bana jin cewar ko daya daga cikin yayana ne ya mutu zan samu kaina a yadda na samu kaina a yanzu.
“Ki ce Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Mama ce take fada min abunda zan fada, ba dan ina ganin fuskarta ba, ba fuskarta kadai ba komai bana iya gani a yanzu sai dai ina jin hannunta a jikina tana rike da ni. Unkuri nai da zimmar na bude bakin na furta abunda ta umarce ni sai bakin yai min nauyi kamar ban taba magana da shi ba. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba sama nake kasa nake duniya nake ko a lahira ban sake sani ba, sai duniyar ta duburce min hankalin ya tafi numfashin ma yai min dogon zango....
AHMAD POV.
Tun bayan da aka kai Baby Namra a gidanta na gaskiya be sake zama a aje ba, duk wanda ya kira wayarsa ko ya zo gidan da sunan masa gaisuwa ba zai dauka ba ba kuma zai fito ba. Wani abu yake ji a tare da shi shi ba tsoro ba ba kuma fargaba ba, baya son ayi masa gaisuwar mutuwar yarsa, har yanzu kuma ya kasa saka komai a bakinsa bayan ruwa, ya kuma kasa jin komai a game da mutuwarta. Ita kanta Hajiya a yanzu tafi shiga tashin hankalin da gwarzo yake ciki fiye da jimamin mutuwar Baby Namra, ta fi kowa sanin danta yana da hakuri da juriya, sai dai wannan karon ta kasa banbance hakurin ne ko kuma damuwa? Ta san yadda yake son mahaifiyar yarsa balle kuma ita yartasa.

Yana tsaye gaban madubin dakinsa Hajiya tai sallama ta shigo jiki a sanyeye damuwa da bakinciki karara a fuskar uwa mai damuwa da ciwon danta. A bakin gadonsa ta zauna tana kallonsa har ta bude baki tai magana sai ya tari numfashinta.

“Hajiya Allah kadai yasan irin ihun da Baby tai kamin ta mutu, ita kadai ta san irin ciwon da ta ji”

Idonta ya cika da hawaye tana masa kallon tausayi.
“Ka fara jin zafin mutuwarta kenan”

Juyowa yai ya kalleta.

“Har yanzu dai, kawai na rasa dalilin da zai saka a kashe min ƴa ne”

Kallonsa Hajiya take da uwar ramarsa da rashin kuzari da yake fama da shi.
“Na kasa yarda cewar matar nan zata iya tura yarka a rijiya ta mutu bayan kai ka ceto ta ta yar, kullum mahaifinta da yan gidansu sai sun zo gaisuwa a gidan nan, babu yadda mahaifinta bw yi ba akan ya ganka amman saboda kace baka bukatar ayi maka gaisuwa na hana, ita kanta matar da kake zargi sun fada min cewar tana asibiti bata san inda kanta yake ba sanadin wannan abun”

Dan murmushi yai kadan na takaici.
“Hakan yana nuna da ganganta ta aikata, saboda ta ji nace zan daureta ne  shiyasa ta shirya ciwon karya”

Zuwa yai ya zauna kasa kusa da Hajiya ya dora kansa a saman cinyarta sai wasu hawaye masu zafi suka soma sauko masa.
“Hajiya kina iya tuna lokacin da take cewa bata son ta mutu ita kadai? Idan zata mutu zata tafi tare da ni da ke?...”
“Tana yawan fadar cewar bata son ta sha wahala idan zata mutu”

Hajiya ta karasa masa.
“Ta yi mutuwa mafi kaskanci Hajiya, ta samu rauniya ka dama, Allah kadai yasan wahalar da tasha kamin ta mutu”

STORY CONTINUES BELOW
Ya fada yana shafewa da kuka, for the first time bayan mutuwarta yau ya ji wani abu marar misaltuwa yana ratsa zuciyarsa, kewar yarsa yake ji a yanzu ji yake kamar ya rumtse ido ya bude ya ganta a kusa da shi, wani irin bakinciki ne ya soma rufe shi ta koina.

“Hajiya ina ma ace ba da gaske ba ne, mahaifiyar yarinyar nan ta tafi yanzu kuma..... ”

Sai ya kasa karasawa saboda kukan da ya ci karfinsa. Daga shi har Hajiya aka rasa mai rarrashin wani. Kanwarsa ce Siyama ta zo bakin kofar dakin ta tsaya tana kallonsu itama kukan take kamar su.
“Be kamata a kyale matar nan ba, ta raba mu da farincikinmu, ta dasa mana bakincikin da ba zai tana goguwa a zuciyarmu ba”

“Ba zan kyaleta ba, ba zan bar wannan abun ba Siyama”

Ya furta cikin mueyar kuka still kansa na kan cinyar hajiya kamar wani karamin yaro, ita kuma ta dora hannunta a saman kan nasa tana ta rarrashinsa.
“Ka dake ka daure ka shiga jama'a kuma ka amsa kiran wayarka, duk wanda akaiwa mutuwa yana jin babu dadi amman a haka yake daurewa, yau ake sadakan uku ya kamata ka fito cikin mutane ka zauna irin wannan kebancewar da kake kana kara bayyana rashin tawakalinka ga Allah ne, ya kamata mu yi imani da kaddara dukanmu”

Kuka yake ba dan kadan ba, kuka yake ba na wasa ba, kukan da be tana irinsa ba, kukan da be taba saka ran yinsa ba. Kukan da tun da Namra ta mutu be ji irinsa na kusanta shi ba, ko mutuwar matarsa be yi kuka haka kamar na Namra ba, tun Hajiya na taya shi kukan har ta share hawayenta ta koma bashi hakuri tana karfafa masa.
Daga karshe dukan maganganun Hajiya sun shiga jikinsa ya ji karfin hali da karfin zuciyar da yake jin zai iya fita ayi addu'a ukun yarsa da shi. Haka kuwa akai ya fita ya shiga mutane ana ta masa gaisuwa yana amsawa cikin karfin hali, sai dai a duk lokacin da akai masa gaisuwar sai yaji wani abu ya tsaya masa a zuciyarsa daker yake iya hada yawun bakinaa ya hade abun, tun yana iya hadewa da yawun har ta kai sai ya kurba ruwa yake jin abun ya wuce masa, wasa wasa ya fara jin numshinsa na yin kasa har sai da ya koma ambaton mahallincinsa. Babu wanda be tausaya masa ba, duba da irin shakuwar da ke tsakaninsa kuma sanin cewar ba shi da mata a yanzu, gashi mahaifiyar yarinyar itama ta rasu, ga wata uwar ramar da yai cikin kwana biyu kawai ya koma kamar wanda ya shekara kwance yana ciwo.
   Bayan sallah la'asar akai addu'a sai mutane suka fara watsewa, wasu kan so su sake masa gaisuwa sannan su wuce musamman wadanda ba su samu ganinsa ba sai a yau. A cikin mutanen har da mahaifin Halimatu wanda tun da akai mutuwar kullum da shi ake karbar gaisuwar. Da hannunsa ya turo wheelchair dinsa ya karasa kusa da Ahmad ya mika masa hannu Ahmad ya mika masa nasa hannun yana amsa gaisuwar da yake masa.

“Ni ne kakan abokiyar yarka Namra...”

Baba na rufe baki Ahmad ya tsaya cak yana kallonsa kamin yai saurin janye hannunsa.
“Me ka zo yi nan?”

Baba yai shiru kamar mai tunanin ta inda zai fara.
“Ka fada min cewar yarka bata da laifi? Ko kuma ka bani hakuri akan abunda tai? Ko kuma saboda ka yi min gaisuwa sai na ce na yafe mata...?”

“Da dai ka saurareni d’a na”

Baba ya fada cikin sanyayyiyar murya, a take Ahmad ya daga masa hannu yana mai jin baya ma bukatar saurarensa.

“Bana son jin komai daga bakinka, ka fadawa yarka ta jira kiran kotu, domin ba zan kyale wannan maganar ba, yarka kake kokarin karewa ni ma kuma kadin yata zan bi”

“Haba dai d'ana arzikin ba hauka ba ne ka saurareni mana”

“Ni ba danka ba ne da danka ne ni da yarka bata kashe min ya ba....”

Yana kawai nan ya juya a fucewa ya bar harabar gidan. Part dinsa ya shiga ya ya dauki wayarsa dake ringing sai ta ya fara amsa kiran amsu masa gaisuwa sannan ya samu damar kiran lauyansa.

STORY CONTINUES BELOW
***   ***    ***

Cikin tsananin damuwa Baba ya tura kekenasa ya fita daga gidan, daman haka yake idan zai tafiya mai nisa saboda baya iya taka kafa sai ya hau kekensa a maimaikon yai tafiyar da sanda, baya damuwa yace dole sai yaje da yayansa sun turashi ko su rika shi, ganin duk yayan nasa mata ne sa maza biyu da basu gama tasowa ba. Da kansa ya tari Napep bayan ta tsaya ya mike tsaye ya taka kafar a hankali ya shiga bayan ya fada masa inda zai kai shi, mai nepep din da kansa ya fito ya kama keken Baba ya nade ta ya saka ta a ciki sannan ya koma mazauninsa ya kunna napep din.
  Har suka isa gida Baba be daina tunanin maganar da Gwarzo ya fada masa ba, idan har da gaske yace zai daure Halimatu to dukansu suna cikin matsala domin za a kara mata wata damuwar ne bayan wacce take fama da ita a yanzu, ga kuma mahaifiyarta wacce ta koma sai an kwantar idan zata tashi ma sai an rikata saboda ciwonta na hawan jinin da ya saka ta a gaba. Cikin rashin kuzari ya isa gida sai da mai napep din ya fito masa da kekensa sannan ya ciro 200 naira ya mika masa bayan ya shi canja ya kwalawa dansa karami kiran.
“Abbah....”

Sai gashi ya fito da gudu.
“Shiga da wannan kujerar koma ciki ka dauko min sandata”

A nan ma da gudun ya shiga ya da keken ya dauko sandar ya kawowa mahaifinsa sannan suka shiga cikin gidan tare, a kishingide ya samu Mama saman tabarma Aisha na mata fita kofin fura a gefenta an saka kankara a ciki domin ita kada take iya sha a yanzu sai kuma maganin da aka rubuto mata asibiti. Daga inda take ta daga kanta ta kalli Baba tana ganin yanayinsa ta san ba zai bada labari mai dadi ba, sai ta maida kanta ya rufe ido.
“Sannu... ”

Baba ya fada sai ta daga masa kai a hankali, tana cizon baki tare da sauke ajiyar zuciya a hankali. Baba ya dubi Aisha
“Aisha kin dawo?”

“Eh Anty Hafiza da Husna da Inna suna can”

“Ya jikin Halimatu?”

“Wallahi Baba har yanzu bata magana, bata san wanda yazo kanta ba, ko motsi bata yi idan ba su likitocin suka juya ta ba sai dai tai ta kallon mutane ko kuma tai ta bachi”

“Al-hamdulillah Allah mun gode maka, a nan din ma ba wani sauki, ina ganin mutanen ba za su bar maganar nan ba, ya tabbatar min da bakinsa cewar sai ya kaita kotu”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Mama ta fada a hankali sannan ta bude idonta.
“Ka yi magana da shi?”

“Baya son saurarena”

“Ka yi magana da mahaifiyarsa?”

“Shi mai karar be saurareni ba taya kike tunanin mahaifiyarsa zata saurare ni?”

“Ita ai uwa ce zata fi shi hankali da tunani”

“Bana tunanin ba da sanin mahaifiyarsa ko izininta yake wannan abun ba”

“Idan ka yi min izini ni zanje nai magana da ita”

“Ba za su saurareki ba”

“Ba zan iya ganewa ba har sai na yi magana da ita, idan bata saurareni ba sai mu kai kararsu a gurin Allah”

“Taya za ki iya zuwa ki yi magana da ita Mama ke da baki da lafiya ma”

Aisha ta tambaya. Sai Mama ta unkura ta tashin zaune.
“Zan iya Aisha ciwon Halimatu ya fi ciwona damu na”

“Tashi ki taro napep mu tafi”

“Da dai za ki ji magana ta da kin zauna domin ba za su saurareki ba”

STORY CONTINUES BELOW
“Da dai ka bar ni na tafi hankalina zai fi kwanciya”

“To Allah ya sa'a a dace”

Shine abunda Baba ya fita da shi, sannan Aisha ta fita da kanta ta taro mai napep din ta dawo ita da Teema suka rika Mama suka saka ta a napep din. Kamin su isa har ta gaji saboda ciwon zuciya da ba jiki, ba a hana su shiga ba kusan gate din gidan ma a bude saboda masu zuwa gaisuwa da kuma wadanda ba su gama ficewa ba. Mama bata taba zuwa gidan ba sai yau saboda rashin lafiyar da ya same ta tun daga lokacin da aka kwantar da Halimatu asibiti, daga ita har Aisha da Teema daman Inna ce da su Hafiza suke jigilar zuwa gaisuwa kuma suje asibiti gurin Halimatu. Da taimakon mutane dake fitowa cikin gidan aka nuna musu kofar falon Hajiya har suka isa. Sun tararda falon a cike da mutane hakan yasa Mama ta fara gaisuwar ta kansu kamin ta kalli wacce take zaton matar gidance ta ce.
“Ke ce Hajiya”

“Aa ni yayarta ce Hajiya tana cikin bari a kira miki ita”

Wata budurwa dake kusa da ita zaune aka aika ta kira Hajiya, sai gata ta sauko babu dadewa waya makkale a kunnenta har ta zauna, sai da ta gama wayar sannan Mama ta mika mata gaisuwa tare da ta'aziya. Hajiya ta amsa tana mata kallon rashin sani.
“Hajiya zan iya kebancewa da ke? Magana nake son yi da ke”

Jimm Hajiya tai tana kallonta kamin ta mike tsaye ta nufi dakin baki da ke kasa.
“To sai ki biyo ni”

Hajiya na gaba Mama na biye da ita tare da Aisha wacce ta rikota har suka shiga dakin. Madaidacin daki ne mai dauke da gado da katifar kasa sai kuma wardrobe da yan kayan kwaliya kadan. A saman gadon Hajiya ta zauna mama kuma ta zauna a kasa sannan ta kalli Aisha tace.
“Je can waje ki jira ni”

“To Mama”

Amsa mata sannan ta juya ta fice sai ya rage daga Hajiya sai Mama ne kawai a dakin.
“Na san baki san ni ba Hajiya baki taba ganina ba, ba kisan inda na fito ba”

“Haka ne ban gane ki ba gaskiya”

Hajiya ta fada tana aje wayarta a gafen gadon tare da tattara dukan hankali ta fuskanci Mama.
“Ni mahaifiyar Halimatu wacce kuke zargin ta kashe muku jika....”

Shiru tai na dan wani lokaci tana shawaye kamin ta cigaba.
“Alfarma na zo nema gurinki Hajiya, kuma ba dan yata ta aikata abunda kuke zarginta ba, Wallahi yata mutuniyar kirkice ba, ba dab tana nawa ba sai dan zan iya shaidar halinta ko da ba yata ba ce, sannan na san ke uwa ce za ki iya jin abunda wata uwar take ji idan aka lakawa yarta sheri alhalin tana da gaskiya, kuna da arzikin da za ku iya hadawa da ni da ubanta duka ku daure amman ba shi nake son ki duba ba, adalci nake son ki yi danki kuma ki yi wa yata”

“Wane irin adalci? Dazun Gwarzo ya fada min cewar mahaifinta ya zo yana rokonsa ke kuma kin zo yanzu idan har da gaske bata aikata ba miyasa kuke ta magiya? Anya mai gaskiya zai yi haka?”

Mama ta daga kai ta kalli Hajiya hawaye na sauko mata.
“Za ki iya ba ni kur'ane na rantse Hajiya? Wallahi ina zaune tare da ita a lokacin da jakarki ta fada rijiya, yara suka shigo da gudu suka fada mana cewar Namra ta fada rijiya, Wata kaddara ce take bibiyar Halimatu wacce ban san yadda zan kwatanta miki ita ba, ina tausayi Halimatu fiye da duka yayan da na haifa ni kadai na san halin da yata take ciki, bani da tabbacin rayuwa wata kila zan iya mutuwa yanzu ko anjima ko gobe amman ina son kamin na mutu na tabbatar yata ba zata je gidan yari da laifin da bata aikata ba”

“Idan har da gaske bata aikata ba to kotu zata bata gaskiya mu ta bamu rashin gaskiyar”

Kai Mama ta girgiza ta sake duban Hajiya tace.
“Bari na baki wani labari Hajiya, kin taba haduwa da macen da akai mata fyade akai wa yarta kuma mijinta ya rabu da ita saboda tana kokarin kwatowa yarta hakkinta?”

A take fuskar Hajiya ta canja.
“Wa aka yi wa haka?”

“Halimatu Hajiya..... ”

Babu abunda Mama ta rage daga labarin Halimatu sai da ta fayyacewa Hajiya komai tun daga aurenta da irin kalubalen da ta fuskanta har zuwa yau da wannan kaddarar ta mutuwar Namra ta fada mata, ba mama kadai ke kuka ba, wannan karon har da Hajiya da ake ba labarin sai da tai hawaye.
“Amman kuma ita yarinyar kuka kasa kwato mata hakkinta?”

“Taya? Taya Hajiya? Taya za a kwato hakkin macen da mijinta ya karyatata ya gasgasta dan'uwansa akan yarsa? Mutun yarinyar kawai za a zubar a bata mata suna ita da mahaifiyarta”

Hajiya ta share hawayennta.

“Wannan ba hujja ba ce be kamata ku bar wannan maganar ba, kuka kokarin boyewa ne saboda gudun kunya, na tabbatar abunda kike kokarin boyewa na hana a bi wa yarinya hakkin kina kokarin daba wuka ne a ciwo, abun nan yana kasan zuciyarku ke da mahaifiyarta, miyasa za ku boye idan har za ayi wa mata da kananan yara fyade ana boyewa babu ranar da za a daina”

“Maganar ta dade da wucewa Hajiya, yanzu alfamar ki nake nema kar Halimatu ta sake shiga wani kunci”

“Zan yi mishi magana, za a samu mafita In-Sha-Allah”

“Na gode Allah ya kara sutura, Allah ya saka da alheri”

“Ita Halimatun tana can asibitin?”

“Tana can amman bata cikin hayyacinta”

“Gaskiya be kamata ku bar maganar nan ba, taya? Za a ketawa uwa haddi ayi ma ya kuma ku danne wannan bakincikin ku hade saboda gudun kunya?”

Mama ta unkura cike da karfin hali ta mike tsaye.
“Na gode Hajiya na gode Allah yasa ki rike min wannan sirrin”

Cikin karfin hali ta fara takawa zuciyarta na mata mugun nauyi ta fice daga dakiSai da suka gama tsara komai da lauyansa, sannan ya taso tare da shi suka shigo falon Hajiya, a lokacin 8 har da yan mintuna na dare. Da kansa ya tura kofar falon ya shiga Barrister na biye da shi a baya. Hajiya na zaune kasan center carpet Siyama ta dora kanta saman cinyar Hajiya ta lumshe ido kamar mai bachi, alhalin ba bachin take ba tsabagen ciwo kaina ya saka ta a gaba da damuwar rashin Baby Namra.
  Barrister ne yai sallama Hajiya ta amsa mi shi tana kallon danta, ramarsa ta yanzu har ta fi ta dazun da jiya ga wani rashin kuzari da yake fama da shi, ko be fada mata ba ta san abunda ya kawo lauyansa a gidan, ta saurari duk wani abun da Gwarzo da Barrister suka fada mata da kuma yadda suka tsara shigar da karar, bata katsi hanzanrinsu ba har suka yi suka gama, bayan barrister yai mata sallama ta kalli Gwarzo tace.
“Idan ka raka shi ka zo ina son magana da kai”

Ta okay ya amsa mata sannan ya mike tsaye suka fice tare da barrister. A harabar gidan ma sun kusan awa daya suna tattaunawa kamin yai masa sallama ya sake dawowa falon Hajiya ya zauna. Shiru shiru Hajiya bata ce masa komai ba tana da kallon plasma dake falon, har sai da ya kagara da kansa yai magana.
“Hajiya kin ce akwai maganar da kike son yi da ni?”

Juyowa tai a hankali ta kalli gefen da danta yake zaune a saman cushion.
“Zaka iya tuna lokacin da mahaifinku ya rasu?”

“Eh”

“Kana iya tuna silar mutuwarsa?”

“Ciwon suga ne”

“Matarka fa?”

“Hadarin mota ne”

“Miyasa ba kai karar likitan da ya duba mahaifinku ba a lokacin da ya rasu? Miyasa ba jai karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarka ba?”

Kallon rashin fahimta yai mata, why Hajiya zata bijiro masa da wannan maganar? Taya zai yi karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarsa? Taya zai yi karar likitan da ba shi ya kashe mahaifinsa ba?
“Fada min? Ko kuma ka fi son Baby Namra ne akan mahaifinka? Ko kuma ran Baby ya fi na Matarka daraja?”

“Ba... Ko... Daya...”

Ya amsa kamar ana matso maganar daga bakinsa.
“Then why zaka yi karar matar nan Gwarzo? Miyasa kake son dora mata laifi? Kana da wata hujja da ke nuna cewar ita ta kashe Baby Namra?”

Wani dogon numfashi ya ja ya sauke, sai a yanzu ya fahimci inda zancen Hajiya ya dosa.

“Saboda matar bata da mutunci ko kadan, kuma a yadda take da zafin zuciya zata iya aikatawa, kuma idan har bata aikata ba miyasa suke jin tsoro ita da iyayen?”

“Da zaka ji labarin matar nan da ka tausaya mata, kaddara ce ta fada mata kuma mahaifiyarta tai min rantsuwa....”

Saurin saukowa yai daga saman kujerar yana hade wani bakin abu daya tsaya masa a makoshi.
“Hajiya dan Allah? Bana son na ji duk wani abu da ya shafe ta, ba ina kokarin kai kararta ba ne saboda na danne mata hakki no hakki yata nake kokarin kwatowa?”

“Wace hujja kake da ita wacce ta nuna maka cewar matar nan ita ce ta kashe Baby? Haba Gwarzo ya kake neman zautuwa akan mutuwar da ba yau ta saba bakuntarka ba?”

Sakin baki yai da mamaki yana kallon Hajiya miyasa tai saurin canja har take kokarin hana shi bayan ita ma a da tana goyon bayan karar?
Siyama ce ta tashi zaune ta tana kallon Hajiya da mamaki.
“Hajiya be kamata a kyale wannan maganar ba, taya zata kashe Baby kuma a barta?”

Hajiya ta daka mata matsawa.
STORY CONTINUES BELOW
“Kar na sake jin bakinki ba ki san komai akan rayuwa ba, kuma idan manya suna magana karki sake tsoma bakinki”

“Amman gaskiya ta fada Hajiya indai suna da gaskiya kotu zata ba su gaskiyarsu mu kuma ta ba mu rashin gaskiyar”

Kallonsa Hajiya tai da kyau

“Mutuwar nan ta dauke mahaifinka ta dauke matarka, yanzu kuma ta dauke yarka, wata rana ni zata dauke kuma ta dauke kanwarka kamin ta dauke ka, wata rana zata zo da zaka rasa wanda zai hana ka aikata ba daidai ba balle ya fada maka kuskurenka....”

“Bana tunanin idan wannan ranar ta zo zan iya rayuwa Hajiya, na rasa babana na rayu na rasa matata yes na rayu yanzu kuma na rasa yata still zan rayu amman bana tunanin idan na rasa ki zan rayu, ku kadai kuka rage min a yanzu daga ke sai Siyama ku kadai nake da ku a yanzu, Allah ya min kyautar mata ya karbe, ya ba ni ya ya karbe, mahaifina ma ya karbi abunsa, ba ni da kowa a yanzu daga ke sai yar'uwata sai dangi”

Ya fada hawaye na sauko masa, sannan ya taso daga inda yake zaune ya nufa inda take ya rumgumeta.
“Na bar maganar nan har bada Hajiya, Wallahi na barta”

Hajiya ta lumshe idonuwanta dake cike da hawaye zuciyarta cike da tausayin danta.
“We're three mu kadai muka rage, babu Baby babu Daddy”

Cewar Siyama tana fashewa da kuka tare da rumgume Hajiya.
“Allah ya musu albarka”

Hajiya ta fada da muryar kuka, hakan yasa Gwarzo tashi ya bar falon yana share hawaye wasu na sauko masa.

HALIMATU POV.
Na ga abubuwa daya a cikin dogon bachi na, abubuwa mabanbanta, masu rikitarwa wadanda ba zan iya fassawaba, tabbas bachi da na dade ina yi a yau yana daure da mafarka kalakala. Ina ji a jikina kamar ban taba bachi mai nauyi irin wannan ba, domin ba jikina kadai ya mutu ba har fatar idona ji nake kamar ba zan iya budewa ba, numfashin ma idan ya fita daker ya ke dawowa, a duk lokacin daya dawo sai na ji wani bari da ban gama tantancewa daga ina yake fitowa ba, sai dai na sa tabbas ba na muhallina ba ne. A zuciyarta nake ta amboton mahallincina hakan ba karamin taimaka min yai har na samu karfin buden idon ba, sai kuma nai saurin maidawa na rufe sakamakon hasken da na ji yai min yawa idon har wani yaji na ji suna min. Cikin karfin hali na kai hannuna na murza idon sannan na sake budewa ina karewa dakin kallo sai a yanzu nake gane ko warin asibiti ne nake ji, amman miya kawo ni asibiti? Shi nake kokarin tunawa, a take kaina ya tsara na nemi duka tunani na rasa sai na sake rufe idon ina jin bakina da daci. Tuna abunda ya faru yasa ni saurin bude idon a nan abun neman ya samu hawaye suka fara aikinsu, unkurin tashi nai zaune amman na kasa saboda rashin kuzari. Hakan na cilasta min cigaba da karewa dakin kallo, ina haka aka turo kofar dakin wani ya leko ni sai kuma ya rufe dakin, da alama wani yake nema domin haka wasu suke idan suna neman wani sai su rika bibiyar daki suna lekawa. Har na lumshe idona sai kuma na sake jin an bude kofar a karo na biyu sai dai wannan karon na ji alamar shigowa duk kuwa da kasancewar idon nawa a rufe suke. Wani irin fitinannane kamshi turare na ji ya maye gurbin warin asibitin da nake ji hakan yasa ni saurin bude idon karaf nai arba da wani kyakkyawan farin mutum wanda ba zan iya kiransa da saurayin ba ba kuma zan ce masa mai aure ba tunda ban san gaibu ba, yana da manyan idanuwa ga dogon hanci, bakar rigar dake jikinsa ta haska fuskarsa gwanin daukar hankali. Matsowa yake ta yi kusa da ni yana kallon fuska kamar mai son tantance wani abu, van yarda a zahiri nake kallonsa ba har sai da na runtse ido na sake budewa, sai a yanzu na fahimci mutumen dazun ne da ya leko ni ya sake shigowa.
“Sannu.... ”

Ya furta min yana cigaba da kallona.

“Yauwa”

STORY CONTINUES BELOW
Na amsa daker, sai ya kalli kofa ya sake kallona.

“Ya jikin?”

“Al-hamdulillah kai likita ne?”

Jimm yai kamin ya bani amsa, hakan yasa ni tsaye na kare masa kallo da kyau, kusan a kuskure nai arba da sarkar cross din dake wuyansa wacce nake kyautata zaton ta zinari ce, kamar yadda hannunsa yake dauke da agogo da awarwaro na zinari haka ma zoben hannunsa, ba rigar jikinsa kadai ba har jean da ke jikinsa kana kallonsa kasan mai tsada ne.
“Yes ni Doctor ne how are you feeling now?”

Yana fadar hakan ya nufi gurin files dina ya bude yana dubawa sai dai babu alamar natsuwa a tare da shi in each seconds sai ya kalli kofa kamar mai tsoron shigowar wani. Ba zan iya karyata cewar shi din ba likita ba ne domin ban san a wace asibitin nakr ba, ba kuma zan iya gasgata cewar shi din likita ne ba domin ban ga alamun hakan a shigarsa da natsuwarsa ba, ko da yake likitoci ma sun fi saka kananan kaya.
“Ina mijinki?”

Ya tambaya yana kai hannunsa ya taba jikina.

“Miya faru?”

“Akwai maganar da nake son yi da shi”

Ya fada babu alamar wasa a tare da shi.
“Idan wani abun ne ka fada min likita ba ni da aure a yanzu zaman kaina ke”

Shiru yai yana kallon na dan wani lokaci kamin ya kai duka hannayensa ya rika ni ya tashe ni zaune, sai dai har lokacin ba shi da natsuwa.
“Haihuwarki nawa?”

“Hudu na samu miscarriage daya”

“When last kika samu miscarriage?”

“Ba a dade ba be wuce wata biyu zuwa uku ba”

“Mi kikai aka kawo ki asibiti mi yasa kike kuka?”

Hannu na kai na taba fuskata sai na ji sanyin hawayen dazun da ba su bushe ba.

“Wata yarinya ta fada rijiya kuma ta mutu shine abun ya firgita ni”

“Shiyasa kika samu kanki unconscious?”

Kallon rashin fahimta nai masa.
“Miyasa kake ta min wadannan tambayoyin?”

“Sun shafi lafiyarki ne, na duba files dinki na ga komai after that kina fama da cutar damuwa, kin sha maganinki yau?”

“Ban san an kawo ni asibitin ba sai yau”

Saurin tashi yai tsaye sai ya kai hannunsa a karo na uku ya taba fuska, sai kuma ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayar da ban taba irinta ba ya miko min.

“Saka min Number ki a nan zan, akwai bayanin da zan miki akan ciwonki yanzu sauri nake yi”

Tsakanin wayar da fuskarsa sai idanuwa suka kasa tsayawa kallon abu daya, fuskarsa ko kuma wayar ko tambayar da ta cika min zuciya? Mi zai saka likita ya tambayi number wayata? Wane irin bayani ne da ba zai iya yi min ba?
“Wane irin likita ne kai? Wane bayani ne da ba zaka iya yi min ba? Ni ban gane ba? Waye kai? Ka bar ni na ji da abunda yake damuna dan Allah”

“I'm sorry”

Ya fada sannan ya nufi kofar fita kamin ya fice ya sake waigo ya kalleni.
“i'm sorry”

Sannan ya fice, ni kuma na lumshe idona ina maida numfashi a hankali, tsakanin fitar Mutumen da ban san wanene da sake turo kofar dakin a shigo be wuce minti biyar da yan dakiku ba. Da sauri na sake bude idon a zato na shine ya sake dawowa sai ni arba da Abdallah ido cikin ido wani irin faduwar gaba na ji wanda ban taba jin irinsa ba, sai na ji yayi min wani irin kwarjini kimarsa ta cika ido, hakan yasa ni kawarda kaina daga barin kallonsa har ya karaso kusa da ni, yawo ya rika min da hannunsa a fuskata kamin ya kai hannunsa ya taba ni.
STORY CONTINUES BELOW
“Halimatu....”

“Na'am”

Na amsa ba tare da na kalleshi ba, ina iya jiyo sautin fitar iskar bakinsa kamin ya kai hannunsa ya daga idona.
“Sannu yaushe kika tashi?”

“Ban dade sosai ba”

“Okay”

Da kanshi ya shiga ba ni kulawa kamin ya fita ya hado min tea ya dawo. Ya mika min tea na saka hannu na karba idonaa na kaina, yana ta kallona kamar be taba ganina ba, har na gama shan tea na aje kofin be dauke idonsa daga gareni ba. Dagowa nai na kalleshi a zatona zai kawarda idonsa ne amman kamar jiran yake mu hada sai ya cigaba da kallona ido cikin ido, hakan yasa sai duk na ji na tsargu.
“Yan gidan mu basa nan?”

Sai ya gyada min kai still idonshi na kaina.

“Kwananki tara a nan sai yau kika farka”

Kwana tara? Kenan ba bachi nayi ba kamar yadda nake tunani suma nai? Na tambayi kaina kamin na sake kallonsa na ce.
“Da gaske Baby Namra ta rasu?”

Nan ma kan ya gyada min yana cigaba da yi min kallon da ban san na minene ba, shigowar wani likitan ne yasa shi saurin mikewa tsaye ya saka hannayensa aljihu yana yi Doc maraba.
“Ya jikin nata?”

“Da sauki.... ”

Haka Abdallah yai ta ba ni kulawa fiye da yadda na cancanta, sai dai hakan ba karamin taba ni yai ba, miyasa Abdallah zai yi ta bani kulawa bayan na zabi auren dan'uwansa sama da shi? Bayan na yi masa zargin shi yai fyade? Anya na cancanci girmamawa da kulawa daga gareshi?

Duka yan gidansu yan'uwa na kusa da kawaye na sun zo ganina ciki kuwa har da mahaifiyar Aminu, ban da mahaifiyata, ko baba da bashi da wadacacciyar lafiya sai da ya zo ganina amman ban ga mahaifiyata ba, idan na tambaya sai ace min tana gida tana miko min gaisuwa hankalina be kwanta ba sai da nai waya da ita muka gaisa sai dai a yanayin da na jita kamar ba lafiya ba. Aisha da Hafiza ne suka labarta min yadda Mama da Baba sukai da mahaifin Baby Namra da kuma zirga zirgar gaisuwar da suka rika zuwa yi.
Kwana na biyu asibitin aka ba ni takardar sallama, a ranar da aka sallame ni a ranar Aminu ya kawo min ziyara, ba karamin mamaki ya kamani ba da nai arba da fuskarsa, domin a yanzu bayan Mahaifin Baby Namra babu wanda na tsana kamar shi, su biyun nan bana kaunarsu a rayuwata. Be zo min hannu biyu ba yayi min siyayya mai yawa, bayan mun gaisa be sake ce min komai ba kamar mai kunyata sai wani sunsun da kai yake baya son kallona. Nima ta bangarena ban da kallon tsana babu abunda nake masa, ko ya jikin da ya ce min kasa amsawa nai sai Husna ce ta amsa masa shi kuma ya rike hannun Adnan yana ta wasa da shi gwanin kunya. Muna haka Abdallah ya shigo wani tsaya yai cak ya kalleni ya kalli Aminu.
“Waye wannan?”

“Mahaifinsu Namra ne?”

Aisha ta amsa masa.
“Daman Namra tana da uba? Miya kawo shi nan? Naga dai ba Namra ce bata da lafiya ba mi ka zo yi?”

Dagowa Aminu yai ya kalleshi.
“Na zo duba jikinta?”

“Sai yanzu kake damuwa da jikinta? Lokacin da take gidanka ka kula da ita ne? Dan Allah mana tashi ka fice ko na saka a wulakantaka yanzu nan”

“Akwai alaka a tsakanin mu ba ka isa ka raba wannan ba, so ko ka so ko ka ki dole ne alaka ta cigaba da tafiya har a bada saboda akwai yaya a tsakaninmu”

Aminu ya fada yana mikewa tsaye
“Yayan da baka damu da su ba? Yaran da kanenka ya lalata yarka ka kasa yin komai? Malam zo ka wuce”

STORY CONTINUES BELOW
A fusace Aminu ya fice daga dakin, aiko Abdallah kamar jira yake sai yai kaina da masifa kamar zai cinye ni.
“Tsakanin ke da shi ban san waya fi wani hauka ba, taya mutumen daya aureki ya raba ki da danginki ya kuma can ya wulakanta ki ya ci zafinki ke da yar ki  yanzu zai zo dubaki har ki saurareshi? Wace irin mahaukaciya ce ke? Ko sonshi kike ne? Son shi kike?”

Yana ta maimaita min tambayar son sa na ke yafi a kirga be yi shiru ba har sai da na amsa masa a fusace hawaye na sauko min zuciyarta cike da wani irin bacin rai da bakinciki marar misaltuwa.

“Eh son shi nake shikenan?”

Yawo yake da idonsa a fuskata kamin ya gyada min kai.
“Yes shikenan....!”

Ya fice ya bar a ni a dakin ni da Aisha ban san lokacin dana fashe da kuka ba.
ABDULHAMID POV.
A natse ya shigo ya falon ya zauna bayan sun gaisa da Hajiyarsa sai shiru ya biyo baya alamar akwai damuwa a tare da shi, sai dai Hajiya bata lura da hakan sai aikin motsa furarta take.
“Hajiya mi yasa baki taba fada min cewar Abdallah yana son Halimatu ba?”

Da sauri Hajiya ta juyo ta kalleshi.
“Wace irin magana ce wannan? Taya Hussein zai so matarka? Wacce ka rabu da ita”

“Wallahi Hajiya zan iya dafa miki al'qurane cewar Abdallah yana son Halimatu, sai dai abunda ban gane ba kamin na aure ta yake son ta ko kuma bayan na aureta? Ko kuma bayan rabuwarmu?”

Hajiya ta aje kofin furar tana dan murmushi tace.

“Ba haka ba ne Husaini yana tausayinta ne kuma.... ”

“Abunda yake mata ya wuce tausayi Hajiya, ni ba mahaukaci ba ne na fahimci komai yanzu, kuma na san ke ma kin sani”

“Ni ban san komai ba kuma Husaini ba son Halimatu yake ba, hasalima duk wani taimako ita ce take neman yai mata”

Hajiya na rufe baki Abdallah na shigowa dakin fuska babu annuri ya kwaso fushinsa na asibiti ya shigo gidanta da shi. Har ya zauna be cewa kowa uffan ba, kamar ya san zancen a ake, sai dai a badini kalaman Halimatu ne suka taba masa zuciya. Hajiya ta watsa mata wata uwar harara kamin ta rufe shi da fada.

“Daga ina kake?”

“Asibiti”

Ya fada yana dan sakin fuskarsa shi sai yanzu ma ya ankara da ya shigo babu sallama kuma be gaishe da Hajiya ba.
“Abunda kake yi wa Halimatu yayi yawa Husaini gashi nan har dan'uwanka ya fara zarginka.... ”

Abdulhamid yai saurin tarar numfashinnta.

“Ba zargi nake ba Hajiya zahiri na gani, kawai abunda na masa ganewa, shin kamin na aureta ne yake sonta ko kuma bayan na aureta ne?”

Abdallah ya kalli Abdulhamid with confused.

“Saboda kawai ina taimakonta sai ya zama ina sonta?”

A take Abdulhamid ya daka matsa tsawa abunda be taba ba.

“Sonta kake Abdallah, ni ba mahaukaci ba ne abunda kake mata ya wuce taimako, kuma abun kunya ne ace na saki mata ka koma kana bibiyarta”

Tabe baki Abdallah yai.

“Daga kai har Aminu ba ku dace da zama mata kamar Halimatu ba gaba daya ba ku da hali ba ku da tunani... Kuma ba ku da tausayi... ”

“Eh sai kai gwani, je kai yi campaign ta aure ka”

Abdallah ya mike tsaye a fusace.
“Wai miye damuwarka da taimakon da nake yi ma mata ne? Ka riga ka ji baka bukatar zama da ita ka sake ta, to miye damuwarka da ni ko ita? Baka san cewa ina taimakon Halimatu tun kamin ka aureta ba?”

Abdulhamid ma ta mike tsaye.
“That's mean kana sonta tun kamin na aureta kenan? Miyasa ka bari na aureta bayan ka san kana sonta?”

“Wai minene matsalar ka Abdulhamid? Abdulhamid?”

“Kai ne matsala Abdallah? Taya taya taya zan saki mata twins brother naya rika bibiyarta?”

Abdulhamid ya fada cikin daga murya.
“Haram nai ko kuma taimakon da nake mata ne ba dace ba?”

“Ana barin halak ko dan kunya, kuma ko dan gudun zagin mutane, kuma ni cin fuska ne a gareni kuma abun kunya a gareka”

“Bana gudun zagin mutane, kuma wata halak din take baruwa Abdulhamid, wata halak din...!”

“Husaini......! ”

Tsawar da Hajiya dakawa Abdallah ne yasa Abdulhamid ficewa daga falon a fusace.
“Enough is enough, so ba hauka ba ne kana ta wahala akan yarinyar da ta kasa daga kai ta kalli soyayyarta a idonka, da gangan ta take soyayyarka ta auri dan'uwaka, ba ka da hankali ne kai? Yanzu hakan da ran dan'uwanka ya bace ya maka dadi kenan? Baka da magana sai ta Halimatu baka da time sai na Halimatu, baku taba fada da junanku ba sai akan yarinyar, to ya isa haka an kai karshe”

Ta karasa hawaye na sauko mata, Abdallah dai be ce komai ba all what he try to do ya saukar da fushinsa ya samu natsuwa.
“Daga yau sai yau, ban yafe ka sake shiga safgar Halimatu ba, ban yafe ka sake taimakonta da komai ba”

A rikice ya girgiza mata kai da sauri sai ta daga masa hannu.
“Fita ka ba ni guri”

Hannunsa ya saka ya dafe kansa kamin ya juya da sauri ya fice daga gidan gaba daya....
Kai ma wani irin ka zama ne Aminu? Kamar ba kai ba? Har ka tsaya wani katon banza ya ci maka mutunci akan matarka ka kasa ramawa sai yanzu zaka zo nan kana wani huce haushi kana fada min? Haka yarinyar ta saka gaba wai ba zaka maida yaranka a gidanka ba kuma ka saka mata ido ya biye mata sai kace ba kai kake aurenta duk ka bi ka zama wani irin mutun”+

Uffan be ce ba har Hajiya ta gama yi masa fadan, shi kansa a yanzu ya san ba kamar da ba ne, duk wani kuzari da kazarkazar irin nasa yanzu babu shi a tare da shi, tun da ya auri murja komai nasa ya sauya ga tsoronta da yake kamar mutuwarsa, abubuwa sai fada masa suke.
“To idan ba zaka iya zuwa kai wa matar taka fada ba, ni zanje da kaina nai mata fadan kuma dole na yayanka su zauna a gidanka kamin uwarsu ta dawo, dan yara ba za su zauna suna ta gararanba a gari ba ba kamar marasa gata”

Da sauri ya dago kansa jin Hajiya tace zata je tai wa Murja fada.

“A'a Hajiya zan sake mata magana zan lalaba har ta yarda”

“Har da yarda? Ka lallabata? Uwarka ce ita? To ba zan lamunta ba, ba zan dauka ba, ko tana so ko bata so dole ne yara su dawo gidan ubansu, da har zance zan rika maka su amman yanzu na fasa ko zaku mutu sai sun zauna a gidan nan”

Cikin rashin jindadin ya kalli Hajiya.
“Hajiya komai dai a bi a hankali kin san ba ko wace mace ke son rikon yaran wata ba, kuma kin ga bata haihu ba so duk wani responsibility na yara bata san shi ba”

“Idan suka zauna gidan ka daukar musu mai kula da su, yaran ma ai da wayonsu kuma ba fata muke a wani dade ba mahaifiyarsu zata dawo, duk yadda za ayi sai ta dawo duk inda zan fita na shiga sai na yi amman Halimatu sai ta dawo maka, ko dan arzikinka ya dawo”

“Shine kawai abunda nake fata yanzu ni har abunda nake ganin yafi a bar yaran a hannunta idan zata dawo sai ta dawo tare da su gaba daya, sai na kama mata wani gidan ita da yara su zauna”

“Idan ba a karbe yaran ba taya za ayi? Ta dawo? Ai sai an karbe yaran shaukin sonsu da kaunarsu ya shiga zuciyarta sannan ta san muhimmancinsu ta dawo maka”

“To Hajiya idan Murja bata yarda da zamansu ba ai dole na hakura har ta dawo gaba daya..... ”

Ya karasa yana ciro wayarsa dake ringing daga cikin aljihun gaban rigarsa, ganin daga gurin aikinsu ne yasa shi hanzarin daukar wayar. After sun gaisa mutumen yake sanar masa ya zo yanzu ana nemansa.
“Okay gani nan zuwa, amman lafiya dai?”

“Ka zo dai”

Ya sake amsawa da okay sannan ya kashe wayar gabansa na mugun faduwa kamar yadda jikinsa yake fada masa ba lafiya ba.
“Wato yanzu sai ta aminta sannan yara za su zauna gidan lallai Aminu, kamar ba kai ba kamar an sauya ka Wallahi”

“Rayuwa dole ai tana sauyawa Hajiya, yanzu dai bari naje gurin aiki ana nemana”

Ya fada yana mikewa tsaye, Hajiya kam da kallon mamaki ta bishi har ya fice. Direban Hajiya yai ma magana ya sauke shi a gurin aikin na su da zimmar idan ya gama abunda yake sai ya samu wani cikin abokan aikinsa su sauke shi gida, tunda abun ya zame masa haka mota bata kaunarsa sabuwar da ya siya ya kashe mata kudi har ya gaji bata gyaru ba, idan ma ta tashi cikin kwana biyu zata sake samun wata matsalar.
  Cikin tsoro da tunani kala kala ya shiga ofishin shugaban na su, ya tararda wasu mutane a ciki hakan yasa shi neman guri ya zauna har sai da ya sallami bakin nasa sannan ya karasa gurin teburin ogan yaja kujera a daya daga cikin kujerun da mutanen suka tashi ya zauna yana mika masa gaisuwa.
“Makullin office dinka nake son ka ba ni da duk wasu takadar da suka shafi ma'aikatar da wadanda suke hannunka...!”

Tas tas tas gabansa yai mugun bugawa.
STORY CONTINUES BELOW
“Ranka ya dade lafiya dai?”

Wanda ya kira da ranka ya dade ya dauko wata takardar ya mika masa, sanyi jiki Aminu yai gurin karba kamar yasan abunda ke ciki ba alheri ba ne.
“Ranka ya dade takardar me ce?”

“Ka karanta ai ka yi boko”

Ya hade yawu yafi a kirga sannan ya bude zungureriyar takadar wacce ya kasa fahimta abunda aka rubuta a ciki ba dan kuma be iya karanta turancin ba sai dan baya cikin natsuwarsa.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ranka ya dade me nai aka kore ni? Kamar kora na ke gani ko?”

Ya tambaya jikinsa na bari bayan ya karanta takardar a galabaice ga wata uwar gumi daya tara a goshi.
“A gaskiya ni kai na ba zan fadar dalili ba abu ne daya taso daga sama”

“Amman ana sallamar mutum ba tare da yayi laifin komai ba ranka ya dade? Idan wani laifi nai a fada min sai na gyara, aikin nan shine rayuwata”

“To ina ganin abunda yafi ka koma gida sai ka rubuta apology letter sai ya aiko min ni kuma zan tura ta sama In-Sha-Allah, amman dai sun fi zarginka da wasa da aikin ga kuma rashin zuwa aikin akan lokacin”

“Allah yasa hakan shi yafi alheri, na gode”

Ya fada yana mikewa tsaye jiki a sanyaye zuciyarsa a daure. Office din nasa ya nufa a lokacin daya shiga sai ya rasa abunda zai yi a ciki sai kawai ya nemi gurina zauna ya rumtse ido, tunani yake son yayi ya kasa tunanin me zai yi? Kayansa da suke office din ya kwashe ko kuma tunanin gobensa? Ko tunanin laifin da ake tumarsa da shi? Anya wannan kawai ya isa ya saka a koreshi daga aikin da ya shafe shekaru yana yi? Ko dai akwai wani wanda yake masa makarkashiya yake bibiyarsa da sheri? Shigowar abokinsa ne yasa shi dago kai ya kalli kofar da idanuwansa da suka gama sauya kala.
“Tahir kaga abunda mutanen nan suka min?”

Ya fada yana nuna masa takardar kamar ya fasa kuka.

“Aminu sai hakuri idan mahassada suka saka mutun a gaba sai addu'a tun jiya aka bada takardar nan amman kowa ya kasa kawo maka shine yau bayan ka bar office yace a kira ka shi zai baka”

Ya busar da iskar bakinsa.
“Yace na rubuta takardar bada hakuri”

“Kai share banza ai duk da shi akai maka wannan sherin budurwarsa yake son dorawa a kujerarsa”

“Wacece Habiba?”

“No Jalila dai ba tare yake da ita ba”

Duk wata magana da yake yana yinta ne kawai cikin karfin hali amman ba dan yana da kuzari da karfin zuciya ba. Da taimakon Tahir ya hada duk wani abu daya san na shi ne ya kwashe a office din ya saka a kwali Tahir ya saka masa a motarsa, sannan ya koma office din shugaban na su ya mika masa keys din da wasu abubuwan da suja shafi ma'aikatar yai masa sallama ya fito.
  Tun da suka kamo hanyar gida Tahir ke ta ba shi magana yana nuna masa hanyar da zai bi a maida shi aikin da kuma manyan mutane da ya kamata yai ma magana. A cikin motar Tahir ya bar komai nasa ya fita daga motar ya shiga gidansa cikin damuwa da tunani kala kala, he wasn't surprised ganin motar Sadi a harabar gidan daman can ya saba zuwa gidan idan an kwana biyu wani lokacin kuma yana shigowa tare da shi, suna da kyakkyawar fahimta tsakaninsa da Murja ba kamar Halimatu da daman can tun a farkon fari basa samun jutuwa wanda ya samu asali daga Hajiya wacce bata son Halimatu. Tafiya yake yana jin kamar ba kasa yake takawa ba saboda damuwar data cika masa ruhi, a yau kam ba tare da ya kira murja ya sanar mata da zuwansa ba zai shiga gidansa duk kuwa da kasancewar tai masa gargdin cewar karya dawo gida babu notice, sai dai tashin hankalin dake tare da shi a yau ya mantar da shi dokarta, shi yanzu ma tsoronsa daya kar ya fada mata gaskiya ta guje masa, ko kuma ta juya masa baya, anya ma zai iya fada mata cewar an koreshi daga aiki bayan ko amarci bata gama ci ba? Duka duka ko shekara batai ba tana tunanin jindadi zai bijiro mata da wannan maganar? Har ya tura kofar falon ya shiga be yanke shawarar fada mata gaskiya ba ko kuma boye mata idan ma ya boye mata me boyewar zai haifar tunda dole ne wata rana sai ta san gaskiya. Ganin babu kowa a falo sai tv dake aikin watso labarai yasa shi mamaki, sai dai be kawo komai a zuciyarsa ba ya leka kitchen din dake bude nan ma wayan babu kowa kai tsaye ya nufi dakin Murja yana tabawa ya ji shi a kulle an saka masa key daga can ciki. Hakan yai mugun daga masa hankali har ya kai hannu yai knocked sai kuma wata zuciyarta hana shi, to ko dai Murja bata nan ne? Ta rufe dakin ta manta bata rufe falon ba? Idan kuma bata nan mi ya kawo motar Sadi a cikin gidan? Kuma ina Sadin yake? Juyawa yai da sauri ya fice daga falon ya zagaya ta can gurin windows dakin Murja da zimmar ya leka dakin sai ya samu windows din suma a rufe.

STORY CONTINUES BELOW
Dawowa yai falon ya zauna ya zubawa kofar dakin ido, yana ta kokarin hana zuciyarsa zargi yana ta kokarin kyautatawa matarsa da dan'uwansa zato! Sai me? Sai ya kasa natsuwa ya kasa sukuni gaba daya sai ya manta da zancen sallama hankalinsa gaba daya ya dawo a nan. Wata dabarar ce ta zo masa sai ya fita harabar gidan daga can inda ba za a jiyo muryarsa ya kira line ta da sunan da yai saving number ta sweetheart ringing tai har sai da ta kusan yankewa sannan tai picking.
“Hello Baby”

“Na'am ykk zan dawo gida yanzu”

“Okay sai ka iso i love you”

“I love you too”

Ya amsa mata yana maida numfashi. Sannan ya maida wayar aljihu ya nufo falon, har lokacin ba a bude dakin ba kuma be ji motsi ko alamar za a bude din ba hakan yasa shi jin sanyi a ransa sai hankalinsa ya fi karkarta da yarda cewar wata kila ta fita wani wajen ne? But wait idan ta fita ina Sadi? And me ya kawo motarsa a nan?
Ganin ba shi da amsar tambayar yasa shi sake nufar kofar dakin da zimmar knocked sai dai kamin ya karasa aka bude kofar daga can ciki ga mamaki Sadi ya fito daga dakin sanye da shadda yellow hullarsa a hannu yana gyarata. Kamar hoto haka Sadi yai tsaye a gurin ganin Amnu, kamar yadda Aminu ma yai tsaye kamar an dasa shi a gurin sai dai hakan be hana shi murmushin mamaki ba.
“I...na.. Mu...rja...”

Ya tambaya maganar na fitowa daga bakinsa daker. A rikice Sadi ya nuna masa dakin daya fito a take gumi ya karyo masa.
“Tana..... Ta... Na... Ci... Ki.... Al.... Al... Aljannunta.... Ne suka... Taso.. So... So... So”

Murja kamar jira take tana jin haka ta buga wani mahaukacin ihu ta fadi kasa ta soma murje murje....

HALIMATU POV.
Ban jidadin yadda na amsawa Abdallah cewar yes kaunar Aminu nake ba, bayan kuma ni kaina na san karya na fada na fada ne kawai cikin bacin rai sanadiyar maimaita min tambayar da yake ta yi, sai dai a yanzu ina jin cewar ko kallon banza be kamata ace ina yi ma Abdullah ba balle har na fada masa wata maganar marar dadi, na ji babu dadi sosai haka yasa na yanke shawarar kiransa idan na natsu na bashi hakuri, sai dai kuma ya cancanci na kira na bashi hakurin? Hakan ba janyo min wani abun ba? Idan kuma ban bashi hakurin ba zai iya daukar da gaske son Aminu nake, halin a yanzu ko sunansa bana son ji balle har a alakanta kalmar so da shi, no ba sai na kira shi ba indai Abdallah ne da zarar ya gama fushinsa ya sauka zai koma kamar komai be faru ba.
Haka dai muka isa gida a napep da sake sake kala kala a raina, na kulla wannan na kwance wacan har na fita daga napep din.
“Mai motar can fa tun dazun yake biye da mu”

Mai nepep din ya fada yana fito mana da kayan mu, da na daga kaina sai na hango wata kafirar bakar mota mai bakin gilashi wacce ban taba ganin irinta a fili ba sai a fina finai, mai motar kamar ni yake jiran na dago na kalleshi sai ya sauke gilashin motar a hankali, me zan gani? Mutumen nan ne wanda na taba gani a lokacin da na farka a asibiti kafirin nan, wani irin faduwa gabana yai a take na nemi natsuwata na rasa.

“Hasbiyallahu wani'imal wakeel”

Na furta ina cigaba da kallonsa kamar yadda shi ma yake kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Na sake furtawa daga Aisha har Husna kallona suke kamin su kalleshi sai yai sauri daga gilashin motar yai ribas ya juya inda ya fito.
“Kin san shi ne?”

Mai Napep din ya tambaya.

“No”

“To Allah ya sawwake yanzu mutane abun tsoro ne, garkuwa ake da mutane ta ko'ina”

Na dan tabe baki.
“Allah na tuba to ni idan an yi garkuwa da ni me za a tsinta?”

“Ai ba shi mutane suke dubawa ba, kuma ai akwai matsafa masu dauke mutane, sai dai kuma idan sonki yake”

Na sake duban mai napep din da kyau kamin nai murmushi na girgiza masa kai.
“Ni kan yanzu ai na girmi so”

“Ta ina? Ga ki kyakkyawa da jini a jika? ”

Daga ni har shi har kannen da muke tare dariya mukai, Maganarsa sai ta tuna min da wata maganar marar dadi da Aminu ya taba fada min.

“Look at you duk kin yi wani muni kin tsufa..... ”

Ajiyar zuciya na sauke na dauki wasu kayan na shiga da su cikin gida ni da Husna Aisha kuma ta tsaya sallamar mai napep din sarkin bargwanci.
Na jidadin ganin Mama da nai duk kuwa da kasancewar na ganta jikin nata sai a hankali amman hakan be hanani jindadin ganin farincikina ba, ba ita kadai ba kowa a gidan ya jidadin dawowata musamman ma yarana wadanda suka rika tsalle kamar na shekara bana gidan, Amal ta zo jikina ta zauna tana ta zuba min shagwaba.

ABDALLAH POV.
Luma biyu yai ya ji kamar ba zai iya cin abinci ba sai ya aje spoon din ya kurba ruwan dake gabansa.
“Lafiya kake yau?”

Ya dago a hankali ya kalli Suwaiba sai ya amsa mata a hankali tare da tashi ya bar mata dinning.
“Bana jin dadi ne”

Da kallo ta bishi ta tabe baki.
“Ai shine daidai da kai na san da ba haka nai maka ba ba zaka fita safgar wannan shegiyar Halimatun ba, amman yanzu da Abdulhamid ya san gaskiya ai dole ka kama kanka dan na san zai taka maka burki da wuri, tun da ku maza ba kunya ce da ku ba yanzu nan sai kace zaka aureta, idan anyi magana kace tausayinta kake to sannu sahabi.... ”

Ta cigaba da cin abincinta ranta fes duk kuwa da kasancewar bata san makasudin bacin ran mijin nata ba, sai dai ta san baya rasa nasaba da abunda ta fadawa Abdulhamid domin a yadda ta ga ransa ya bace ta san ba zai bar maganar ba!
Dakinsa ya shiga ya kwanta ya rasa abunda ke masa dadi, a duk lokacin da ya tuna maganar Hajiya ta gatangar da ta gina tsakanina da Halimatu sai yaji wani abu ya tokare masa zuciya, be tabbatar yana sonta da gaske ba sai a yanzu da yake jin kamar Hajiya na kokarin rabashi da ruhinsa ne. Ya rasa dalilin Hajiya na kin masa uzuri ya rasa dalilin hajiya na tsanar Halimatu tun daga lokacin da ta auri Abdulhamid, yes yasan tayi kuskure na auren Abdulhamid bayan kuma ta san yana sonta, amman ai itama mutun ce kamar kowa ko? Zata iya daidai zata iya akasin haka, then miyasa Hajiya ba zata kalli wannan tai mata uzuri ba? Ko da yake yanzu ba laifi Hajiya ba ne laifin Abdulhamid na yi mata maganar da nuna bacin ransa. Bayan kuma ba shi da wata hujja a yanzu domin da yana sonta kuma ta damu da ita da be sake ta da be juna mata baya ba. Hannunsa ya kai ya dafa zuciyarsa yana kara fadawa wani kogin tunanin.

Wai yanzu duk wani abu da yake yi ma Halimatu janye zai yi? Ba zai sake mata komai ba kenan? Babu wata alaka da zata sake shiga tsakaninsu? Ya tambaya kansa yana jin wani irin shauki da son ganin fuskarta.

______________________

Anya Abdullahi zai iya jurewa?
Da gaske Aljanun murja ne suka taso?
Waye yake bibiyar Halimatu kuma a yanzu?Kasa cewa komai yai  ya tsaya a gurin kamar an dasashi, Sadi kan sai gumi yake hadawa abun ka da marar gaskiya, Murja kuma na can dakinta tana aikin ihu kamar da gaske Aljanun ne suka ziyarce ta har da wani yare take shi ba yarbanci ba, ba kuma iyamuranci ba.+

“A kaita asibiti, no gurin malamai”

Fadi ya fada wiki wiki da ido, sai Aminu yai masa murmushi tare da gyada masa kai alamar gamsuwa.
“Za a kaita”

Ya amsa masa sannan ya nufi dakinsa jikinsa babu kwari, saman gadonsa ya zauna sai ya rasa abunda zai fara tunani, korarsa da akai a gurin aiki ko kuma tararda dan'uwansa tare da matarsa? Kwantawa yai saman gadon yana ta kallon silin.

“Aminu ka ji tsoro Allah abunda kake mana baka kyautawa, ka rika tunawa kana da yara kana da mata, ace magidanci kamar idan ya bar gida ba zai dawo ba sai karfe daya ko biyu na dare...?”

“Ke Halima a nan gidana ne ina da yancin shigowa a lokacin da nake so na fita na lokacin da na ke so, ba ki isa ki saka min doka a gidana ba”

“Ba doka nake son saka maka ba, abunda kake yi nake kokarin nuna maka illarsa, duk abunda kai wa matar wani sai an yi ma taka, kuma duk abunda kai wa yar wani sai an yi wa yarka....”

“Idan iskancin kike so ni ban hana ki yi ba, ga ki ga guri har kya fada min wani wai sai an yi ma yar wani matar wani dan baki da hankali”

“Allah ya tsare ni, ban aikata zina ina budurwa ba ba zan aikata da aurena ba, ga hakkin yayana ga na iyayena ga na mijina ga na ubangijina? Wallahi ba zan iya ba”

Ya fada tana share hawayenta sannan ta tashi ta bar masa dakin. Tuna wannan yasa shi share hawayensa ya rumgume hannayensa a kirjinsa. A yau na mallakawa murja komai, ita ke saka masa duk dokar da tai mata, be isa ya kai 9 a waje ba, be isa ya dawo gidan ba tare da saninta ba, amman hakan be hana ta cin amanarsa ba. Abunda be taba mafarki ba, domin a lokacin da zai aureta sai da yai bincike mai karfi aka tabbatar masa da tarbiyarta sannan ya aureta, sannan ya yaba da shigarta da hankalinta shiyasa ya aureta ashe be tsira daga abunda yake gudu ba, kuma ta rasa wanda zata aikata da shi sai dan'uwansa uwa daya uba daya! Wani irin abu yaji ya tsaya masa a kirji ya danne masa numfashi har sai da yai saurin kifewa a saman gadon ya runtse ido sannan ya samu  sassauci.
“Allah yasa ka gane kuskuren da kake aikatawa da wuri, ko dan yaranka..... ”

Maganar Halimatu ta sake dawo masa.

“Na gane Halimatu na gane......”

Ya fada yana fashewa da kuka wasu hawaye masu zafi suna sauko masa. Kamar an tsikare shi sai ya zabura tai saurin tashi zaune. So da gaske Halimatu take da fada masa cewar Sadi yai ma Namra fyade? Sadi ya daka masa wuka har sau biyu kenan? Yayi saurin tashi zaune, ji yai babu wanda yake bukatar gani a yanzu kamar Halimatu da yayanta.
Tashi yai ya fice daga gidan gaba daya, a bakin gate ya samu abun hawa ya fada masa unguwar su Halimatu, kamin su isa duk sai ya tsawalla kamar wanda ya shekara ba ga yaranba. Sai kuma yai rashin sa'a ya tarar bata gidan wai ta tafi dauko yaran daga School. Kai tsaye Scul din ya wuce a can ya sameta ta tana kokarin taron napep tana rike da hannun yaranta. Sai a lokacin yake jin rashin kyautawa ta ya zai barta ita kadai tana daukar responsibility ba yaransa bayan yana raye? Gaba daya sai jikinsa yai sanyi, karasa yai kusa da su, kallo daya tai masa ta dauke kai sai ya koma gaba Namra ya risina ya kai hannu ya shafa fuskarta yana murmushi.
“Daddy ina wuni?”

Kasa amsawa yai sai ya rumgume ta hawaye na sauko masa. Tun yana yi a hankali har ta kai mutane na kallonsa.
“Miye haka? A cikin jama'a muke fa, ka sake ta gida zamu je”

Sakinta yai ya dago kai yana kallon Halimatu wacce ke watsa masa wata uwar harara, kamin ya kai hannu ya shafa kan duka yayansa sannan ya mike tsaye ya share hawayensa, ita kuma taja yaranta sukai gaba, yana tsaye a bakin titin yana kallonsu har suka samu Napep suka shiga suka bar shi a gurin. Shi ma achaba ya hau ya dauki hanyar family house dinsu.
  Ko da be fada ba kana ganinsa kasan yana cikin tsakanin damuwa, kamar yadda mahaifiyarsa ta karanta a fuskarsa. Gashi ya shigo mata har dakin bachinta babu sallama balle gaisuwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Aminu lafiya kake?”

A lokacin daya dago kansa sai hawaye ta gani a fuskarsa.
“GOBENA Hajiya tunani nake yadda zata kara kasancewa....”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, miya faru kuma?”

“Hajiya yanzu na gane, ba dan na rabu da Halimatu na rabu da arzikina ba, saboda na cutar da ita ne, hakkinta ba zai bar ni ba, samun irinta a duniyar nan sai an tona, kullum nasiha take min bata tana nuna min gazawarta, da gangan Hajiya da gangan nake kauracewa Halimatu sai nai wata uku hudu ban neme ta ba kuma a haka take hakuri da ni......”

Ya fada yana fashewa da kuka kamar mace har zaman kujerar ya gagare shi sai da ya sauko kasa. Sai a yanzu yake jin wani irin zafi da bakincikin abunda Sadi yai ma yarsa da kuma matarsa ashe akwai zafi wani ya kusanci matarka, sai yanzu yasan zafin da uba yake ji idan aka lalata masa Y'a.

“Aminu ka fada min abunda yake faruwa mana, ka gada min hankali”

“Hajiya yau an kore ni gurin aiki... Amman bashi ya fi bata min rai kamar kama Sadi da nai da Matata Murja.... ”

Idan akwai abunda yafi sakin baki da mamaki sai da Hajiya ta yi shi.
“Kasan me kake fada kuwa Aminu?....”

A nan labarta mata komai idonsa ko gani basa yi daidai saboda hawaye. A take Hajiya ta saka kuka.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yanzu Sadi da matarsa da yaransa zai yi matar dan'uwansa haka?”

“Hajiya kin tuna lokacin da na saki Halimatu saboda ta fada min Sadi yai ma Namra fyade? Daga ni har ke ba mu tsaya mun yi tunani ba....”

Hajiya ta dafe zuciyarta tana hawaye.
“Indai har haka ne Sadi ba zai gama lafiya ba, wane irin da na haifa?”
A wunin ranar daga Hajiya har Aminu wuni sukai cikin jimami da damuwa, sai da Dare Sadi ya shigo gidan shi ma dan Hajiya ta kira shi ne, har lokacin ba shi da natsuwa da kwanciyar hankali, Hajiya ta rufe da fada tana kuka, amman sai kokarin kare kansa yake.
“Hajiya Wallahi Aljanunta ne suka gaso kuma tana fisge fisge shiyasa na kaita daki na kwantar da ita”

“Kaji tsiron Allah Sadi idan babu duniya akwai kiyamar Allah, wace irin lalacewa ace kana tare da matar aure mai auren ma matar yayanka? Bayan kai ma kanka kana da aure da yara? Ko ka amsa ka aikata ko kar amsa wannan maganar zata tsaya a tsakaninmu daga ni sai kai sai Aminu, ba zamu fitar da wannan sirrin ba”

Duk wani abu da Hajiya ke fada, Aminu dai be ce uffan ba, kansa n kasa har sai da Sadi zai tashi sannan ya dago ya kalleshi.
“Tun yaushe kuke tare?”

Jimmmmm yai kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya ce.
“Tun kamin ka aureta, class mate dita ce”

“Allah yai maka yadda kai min”

Ya fada masa sannan ya mike ya fice daga dakin ya bar su daga Sadi sai Hajiya.


HALIMATU POV.
Tsawon wata uku kenan ban sake saka Abdallah a ido na ba, hakan kuma ba karamin saka ni yai a damuwa ba, na rubuta masa sakon karta kwana na bashi hakuri amman be maido min da amsa ba, na kira wayarsa several times be yi picking ba.
Ba zan iya zuwa gidansa saboda na bashi hakurin abunda ya faru ba, sai dai ban abunda zan masa da zai saka ya sauko daga fushin da yake da ni ba, a iya zamana da Abdallah be taba fushi da ni na tsawon lokaci haka ba, ko da ban bashi hakuri ba yana saukowa da kansa balle har na bashi hakuri. Da kaina na zauna ina ta tunani da tariyo abunda ya faru so nake na gane idan maganar da na fada masa mai zafi ce sosai da har zata saka ya gujeni haka.
STORY CONTINUES BELOW
Amman kuma ai na huta da shi, ni da nake neman maraba ma? Dan ya nesance ni a yanzu ai na huta ko? Wata zuciyar ta aika min da tambaya, a maimakon na jidadi sai na ji akasin hakan, wata kila saboda na dan saba da shi ne shiyasa na ji babu dadi a yanzu, wata kila kuma saboda abunda na fada masa ne yasa nake jin babu dadi, haka dai nake ta sake sake na ni kadai na kulla wannan na wance wacan.
   Yau ma after na shiryawa yarana sun tafi school na shirya na fito da zimmar leka gidan kawata Hajara wacce na dade ban ziyarce ba, a yau can nake son zuwa yau so nake ba bude nata cikina ina son na ji irin shawarar da zata ba ni ina son na ji yadda zata kalli abun.
Na yi kyau matuka ni kaina na san na yi kyau domin bakar abaya ce a jikina wacce take yi ma ko wace mace kyau, gashi na tsirka da jan mayafi, sam ba zaka gan ni kace Halimatu bace domin na rame sosai ni kaina ina ji a jikina domin yanzu bana jin nauyin jikin kamar da kusan dukan tufafina sun min yawa. Napep na tara na shiga na fada masa inda zai kaini ina cikin napep din ina tunani ban san mun isa unguwar ba har sai da mai napep din ya tambayi inda zai sauke ni.
“Idan ka dan kara gaba kadan ya isa”

Na fada masa ina kallon wata motar da nake kyautata zaton mu take bibiya, ko na nace ni domin tun daga lokacin da nai arba da wannan mutumen ba kasafai bake fita ban ga mota tana bibiyata ba, kuma ba kalar mota daya ba, wani lokacin zai sauke gilashin motar ya kalleni amman ba zai ce min uffan ba, wani lokacin kuma ta cikin motar yake bibiyata, tun abun na bani tsoro har na fara sabawa, ban san mi yake nema a gareni ba, a iya sanina ban yi ma kowa komai ba balle ace wani ya saka ni a gaba dan ya cutar da ni. Bayan na biya nai napep din na tura gate din gidan na shiga sai da muka gaisa da mai gadin sannan na nufi cikin gidan.
  Na jidadin tararda ita ba tare da kowa ba, domin ko mijinta ya fita aiki balle kuma yara da sun tafi school. Tana ganina ta washe hakora
“Yau garinmu inji maki baki”

Da dariya na zauna saman cushion muka gaisa sai ta tashi ta hado min abun karyawa, ban musa ba na karba daman da safen nan koko kawai na sha, sai da na ji na koshi sannan muka dauko labaran duniya har take min zancen komawa makaranta na cigaba da karatuna.
“Ni yanzu ba wani karatu dake gabana, karatun da nai ya isheni aikin nake son samu, na dogara da kaina iyeyena ma suna bukatar taimako na ga yara a gabana ga kanena ga ni ni kaina, kuma kin san karatu dole sai da wanda ya tsaya maka...”

Ya janyo fillon kujera ta rumgume tana kallona.

“Zan tsaya miki ki yi karatu Halimatu, ko nawa ake kashewa zan kashe miki so nake ki yi karatu ki kai matakin da ko aiki zaki samu ba karami zaki samu ba sai babba wanda zai zama na har wasu ma'aikatan a karkashinki suke, ya zamana kina iya daukar nauyin yan'uwanki da ke kanki da iyayenki da kuma yaranki”

“Thanks for the opportunity amman har ga Allah a yanzu bana sha'awar karatu bana jin ma kwakwalwata zata iya daukar wani abu a yanzu”

“To aure kike so?”

“Bana da kudirin aure a yanzu Hajara, kin fi kowa sanin irin kalubalen da nake fuskanta a rayuwar aure, kwata kwata Yanzu aure baya burgeni, aiki dai nake son samu saboda na dogara da kaina domin bana da mai taimaka min a yanzu, Abdallah da nakr ganin yana dauke min wani nauyi shima ya fara guduna”

Fuskar mamaki tai
“Kamar ya?”

Ban rage ba ban kara ba daga abunda ya faru tsakanina da shi wanda nake ganin shine silar fushin da yake da ni.
“A gaskiya baki kyauta ba, amman shi kuma ya dauka da zafi”

“Na san ban kyauta ba, tun daga lokacin abun ke ta damuna har yanzu na ta masa sako na ta kiranshi amman be daga ba be kuma maido min da amsa ba, Wallahi abun yana da damuna”

STORY CONTINUES BELOW
Na fada idanuwa na taf da hawaye.
“Kina son Abdallah Halimatu....”

Wani kallo na watsa mata a kaikaice.
“Ko ki yarda ko karki yarda son Abdallah kike Halimatu kuma kin yi kuskure tun farko da kika auri Abdulhamid bayan kin san Abdallah yana sonki ga kuma tarin kyautatawar da yai ta miki, yanzu gashi zaki cutar da kanki”

“No ba ki gane ba ne, ba son Abdallah nake ba”

“To miyasa kike kuka saboda ya kaurace miki?”

Na kai hannu na share hawayen da suka zubo min.
“Ai ya kyautata min da yawa ko? So ya kamata na ji babu dadi idan ya kwaurace min ko?”

“Hakan be isa ya saki a damuwa ba, akwai son Abdallah a rayuwarki wata kila ba ki sani ba, wata kila kuma kina boyewa ne kawai, so abunda nake ganin yafi kije kai tsaye ki same ni a gidansa ai ba zai kyale ki a can ba, ki bashi hakuri idan ki kai hakan kin wanke kanki”

“Kina ganin idan naje matarsa ba zata zargi wani abu ba?”

“Ke fa jininsa ce Halimatu, taya matarsa zata yanke alakarku? Ke wai ni yar a manta ma ban fada miki ba kinji Aminu ya saki matarsa?”

“Haka Asma'u makociyata take fada min a chat, ko me hada su kuma?”

Hajara ta tabe baki.
“Me zai hada su kuwa ban da bakin halinsa, wace macen ce zata dauki abunda kike dauka? Ai babu macen da zata iya zama da Aminu”

Na yi murmushi ina tuna lokacin da yake ce min wai babu namijin da zai iya zama da ni sai shi saboda bakin halina da sa'idon da nake masa.
“Wata kila shiyasa ya fara munafurci, kin ga yadda yake kula da yaran nan a yanzu kamar ya lashe su? Wallahi idan ya gan ni har wani sunsun da kai yake kamar mazuru”

“To ko so yake ya dawo dai.... ”

Na tofar da yawun bakin.

“Allah ya kiyaye haba Hajara ai dai kya min fatar kwarai ko? Wallahi ni yanzu ko a kafa aka daura min Aminu ba zam iya jansa ba, ke idan na ganshi har wani tashin zuciya nake ji”

Na fada ina yatsina fuska sai Hajara ta saka dariya.

“Balle ya ga kin yi slim kin yi kyau abunki Ma-sha-Allah”

Mun dade muna fira da ita kamin na bijiro mata da zancen mutumen nan da ke bibiyata, ita ma kanta ga tsorata da lamarin har ta ce mai reporting ma yan sanda saboda gudun abunda zaije ya dawo, kuma ban ki ta taba domin dan'adam abun tsoro ne a yanzu. Na dauki shawararta na zuwa bawa Abdallah hakuri dan haka daga gidanta sai na wuce gidansa kai tsaye da kwarin guiwa na. Na dade ina knocked din kofar falon kamin matarsa Suwaiba ta bude min, muna hada ido sai yanayinta ya sauya.
“Ah ah ahhh Abun kuma yanzu har cikin gida Haba Halimatu?”

Ina ta tunin abunda zan fada mata sai na ji muryar Abdallah yana amsa mata.
“Ni nace ta zo....”

Sakin kofar tai wanda hakan ya bani damar shigowa cikin falon, sai na hango shi zaune saman sofa sanye da Jallabiya laptop a jikinsa da alama wani aikin yake. Daga inda nake nai tsaye na kasa cewa komai sai ya aje laptop din ya nufo ya ratsa gefena ya fito daga falon, sai nima na juya na fice a harabar gidan muka tsaya ni da shi, yana ta kallona kamar zai cinye ni, ni kuma na gagara ce masa komai na gagara daga ido na kalleshi kwarjinsa da kimarsa ta cika min ido ga wani uban faduwar gaba da nake ji kamar mai jin tsoro.
“Kin lalata komai Halimatu, kin aikata kuskure, taya zaki auri Abdulhamid bayan kin san ina sonki? Why? Saboda ki musguna min? Haka Hajiyata ta fada min, kin san me? Da Hajiya ta fi kowa son ki saboda ina sonki kuma gana ganin kamar kina so na, daga lokacin da kika ja ra'ayi Abdulhamid a kanki sai ta lamarin ya lalace, gashi yanzu aurensa be haifa miki da mai ido ba, kuma ya haifar mana da matsala gaba dayan mu, baki tunani idan za ki yi abu Halimatu baki tunani.... ”

Ya fada yana hada duka hannayensa ya daki kaina. Dagowa nai na kalleshi idona taf da hawaye zan yi magana ya tari numfashina.

“Sai kuka da an miki abu sai kuka.. ”

Yayi saurin juyawa sai kuma ya juyo.
“Ya akai? Miyasa kika zo nan?”

Na fara matsar yatsuna ina hawaye.
“Zuwa nai na baka hakuri akan abunda na fada maka a asibiti wanda ya saka kake fushi da ni....”

“Yanzu kin fara jin son na a cikin ranki? Shiyasa har kika damu da fushin da nake da ke? Bayan komai ya lalace?”

Ya juya ya fara tafiya.
“Ka yi hakuri dan Allah Wallahi ba abunda ke raina kenan ba”

Juyowa yai ya kalleni

“Ni bana fushi da ke ba zan iya fushi da ke ba....”

Haka kawai ya fada min ya cigaba da tafiyarsa har ya shige cikin falon. Ni kuma na juyo hawaye wasu na bin wasu na fito daga cikin gidan, ina tafiya ina jin ana bina a baya a lokacin sa na waiga sai sake arba da fuskar mutumen nan da ya saba bibiyata. Faka motarsa yai ya fito ya miko min handkerchief.
“Pls...”

“Waye kai? Me kake nema a gurina? Idan ma sace ni za kai ni bani da wanda zai karbo ni, idan kuma yarana zaka sace ban da kudin karbo su”

Murmushi na gani a kyakkyawar fuskarsa.

“Zaki iya shiga motana na kai ki gida, sai ki aminta da ni”

“Ba zan shiga ba, miye hadi n dake kai rista ni musulma”

“Soyayya ai babu ruwanta da addini, haka dai aka fada min mai irin addinin suna da kirki da karanci ba kamar yadda na same ki ba”

“Wani yayi amfani da hakuri na ya cutar da ni, wani yayi amfani da soyayyata ya cutar da ni, kai kuma kana son kai amfani da addinina ka cutar da ni, to ba zan yarda ba ban yi kowa komai ba ba zan yarda ayi ta cutar da ni ba”

Ina fada masa haka na cigaba da tafiyata.
“Idan cutar da ke na zo yi kar Allah ya bar ni da raina a yau”

Tsayawa nai cak kamin ya juyo na kalleshi da mamaki.
“Kai kuma daga ina?”

Matsowa yai kusa da ni ya miko min hannunsa.
“Sunana Abraham akwapo”

Tsayawa nai kallon hannunsa sake sanye da manyan zobuna sai dai ba irin wadanda can ba ne na zinari wasu kala ne na dabam sai dai duka alphabet dinsu A ne. Sai kuma na kalli fuskarsa.

“Ni musulma ce miyasa kake bibiyata? Zan kai report dinka a gurin police yau”

“Okay”

Ya juya ya shiga motarsa na yi zaton tafiya zai yi amman sai ya fito rike da wani kamin littafi yai rubutu akai ya mika min.
“Sunana Abraham ga number motata nan da number wayata da address din gidana ko da sun bukaci gani na”

Ni kan a tsaye da nake mamaki ya kusan kashe ni.
“Waye kai....?”

Sai yai murmushi ya saka hannayensa aljihu.

“Za ki ba ni damar kasancewa abokinki?”

Shiru da nai ban bashi amsa ba ban kuma daina masa kallon mamaki ba yasa shi sake sakar min murmushi.
“Ina mika kyakkyawar gaisuwata a gurin yaranki”
Sannan ya shiga motarsa yai mata key ya bar ni a gurin tsaye da mamaki....


Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 5 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...