GOBE NA CHAPTER 10 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 10 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 10 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

GOBE NA CHAPTER 10 BY KHADIJACANDY


               Www.bankinhausanovels.com.ng 
Red suit ne jikinsa babu abunda ke fita daga jikinsa sai kamshin turare, kallona kawai yake sai dai ba irin kallon da ya saba min kamar zai cinye ni ba, wannan karon ido a lumshe yake kallona kamar mai jin bachi. Nikam gaba daya jikina rawa yake ban tana ganin a fili ba ba a taba min irin haka ba ban kuma saka ran wani zai min ba, juyawa nai na karewa office din kallo na sake kallonsa daga ni sai shi ne a office din amman na kasa yarda cewar da ni nake, na kasa yarda ba mafarki nake ba har sai da na runtse ido ya bude na sake runtsewa na bude sannan na yarda ba mafarki nake ba, daman shine mamakin da yace zai ba ni? Na nuna kaina sai ya gyada min kai.1

“Will you be my wife for the rest of my life?”1


Ya fada da bakinsa still yana duke a gabana, hannunsa rike da dan karamin box da zobe ciki. Rasa nai abunda zan yi idan na ce masa no ransa ba zai masa dadi ba, sai dai be kamata yai min haka ba at least i need to think ina bukatar nai shawara, but what else i can say more YES.


“YES.....YES....YES...”12

Na maimaita har sau uku ina gyada masa kai idanuwana na cika da kwalla da ban san na minene ba, rashin ba ni damar yin tunani ko shawara ko kuma mamakin abun ko kuma amsawar babu shiri? Ko kuma na bakuntar sabon al'amari? Ba zan ce na murna ba dai domin a yanzu ban zan iya tantance a halin na ke ba farinciki ko akasin haka?3

“Oh Yes Babe my search is done”2


     Ya furta, gaba daya hannayensa ya hada ya matse sosai ya runtse idonsa yana wani irin murmushi da ba zan ina fassarasa ba, sannan ya mike tsaye ya kama hannuna for the first time ya yana kokarin saka min zoben da nake mamakin yadda akai ya san size din yatsuna, after ya saka min zoben mai haske da kyalli kamar na gold sai dai wannan zaiba ne, kallona yai ya dora hannunsa saitin zuciyarsa.2

“You're here in my heart, you're my destiny, you mean to be mine, so let's give love another life....”7

Faduwa yai gabana kamar mai neman gafara ya jimke hannayensa ya lumshe ido.

“Duk yadda zan fada miki irin farincikin da nake ciki a yanzu, to zan yi karya ne kawai, but i can promise you one thing nothing can keep us apart, all i want is to live with you, i will be someone that you can always turn to, i will be everything you want, you mean the way to me, i will fix what it broken, Lims i need you”4


Sai kuma ya mike tsaye yana kallona da murmushin da zan iya kiransa da dariya, ya zagaya bayana ya zagayo ya sake haka kusan sau hudu sannan ya sake tsawa a gabana yana sauke numfashi, har lokacin ina tsaye a gurin ina murza zoben da ya saka min, har lokacin bana jin murna farinciki, bakinciki damuwa ko akasin haka, I'm not happy kuma i'm not sad. The way da yake fadi wasu maganganu sai na ji kamar ba shi ba, domin a yadda yake a da zaka iya rantsewa Ahmad ba zai iya furtawa wata kalar so ba, watan kuma ni Halima, dana dago sai idanuwa suka sarke cikin nasa na saka kawarda nawa, shi kam daman kamar hakan yake so sai Murmushi yake sakar min, hawaye ne suka sauko min, sai ya matsa kusa da ni sosai.


“You should know this love i share was never mean to die, co's i don't wanna see you cry, i will never treat you bad, ban tana yarda so nake ba sai Lims kin san yadda nake ji a raina? Kamar na dauke ki na hade you're the queen of my heart, wani irin farinciki nake ji marar misaltuwa”3


Ya shafa kansa tare da daga kan sama yana busar da iskar bakinsa, ya nufi gurin windows office dina ya tsaya sai kuma ya juyo ya kalleni.

“Ba zan iya tuna ranar da wani farinciki ya same ni kamar haka ba....”


Maballin gaban suit din ya bude ya nufo inda nake ya kama hannuna ya dora saitin zuciyarsa.


“This where you belong, i hold you close to me”

Da gaske zuciyarsa bugawa take da mugun karfi kamar zata fado kasa, duk yadda nake jin bugun zuciyata nashi ya ninka nawa sau dari, janye hannun nawa nai har lokacin na kasa cewa komai, bakina yayi nauyi sosai a kaina kuma ina jin kamar babu wasu kalmomi ciki, a hankali na ji ana busa min iska a idona sai na lumshe ido ina shakar iskar bakinsa mai kamshin strawberry, har na daina jin iskar ban bude idon ba sai da na ji an bude kofa an fita sannan na bude idon a hankali, ban ganshi a gabana hakan ya tabbatar min da cewar ya fita daga dakin kenan. Kujera na nufa na dauke fulawar rose din ya zauna na rumgume ta a hannuna ina ta kallonta kamar ance min makomata tana ciki, na hade yawun bakina yafi a kirga kamin ya sake duba daya zauna a hannun kamar dan ni akai shi, kamar ance na juya na kalli windows sai na hango shi tsaye yana kallona. A wunin ranar kasa aikin komai nai sai jikina yai kamar wacce akai wa allurar rashin kuzari ga kuma magana da na kasa cewa komai, gaba daya sai m afka duniyar tunani, i think kuma ia say i will never fall in love, amman me kenan? Ko da yake ba zan ce ina son Ahmad ba kuma ba zance na tsane shi ba, amman makomar yarana fa? Shi ma zau dauke su kamar yayansa? Ko kuma zai yi min irin na Abdulhamid ne? Mahaifiyarsa za tai maraba da ni ko kuma dai ita ma kamar Hajiyar Aminu da ta Abdulhamid take? Da gaske zai iya rike ni tsakani da Allah ko kuma a a, ba zan iya gano haka a yanzu ba all what i have to do is nai Istihara na sanarwa Allah matsalata na kuka masa damuwata sannan na nemi mafita a gurinsa, na nemi zabinsa a tsakanin auren Ahmad ko akasin haka.

  Na sani duk yadda zan tsorata da auri ko na guji aure, shine dai matarba da cikar kamala ta, shine zai kare mutumcina yai min katanga daga duk wani abu da zai iya samuna a kafin igiyar aure, so ba ni da wani zabi da ya wuce na kaunaci sunnar manzo na nai bibiyaya ga Ubangijina, kuma na yarda da wannan kaddarar ko da kuwa ita ma kamar wadancan take domin shine cikar imanina.

  Kamar ance daga ki gani sai ganin mutum nai jikin kofar office din ya rumgume hannayensa yana kallona, sai murmushi yake kamar wanda be taba shiga damuwa ba, kamar jira yake na dago sai ya karaso ciki ya tsaya gaban teburina yana min kallo daya saba.2

“Za ki yi magana da Hajiya ta yanzu nan, tace tana son magana da ke, bata yarda da ni ba”


Ya fada min a hankali kamar mai magana da yaro karami yana son ya fahimta. Be jira cewata ba kamar yasan ba abunda zan fada din ya ciro wayarsa ya kira number ta ya saka a hands-free sannan ya kwanto jikin teburin yana cigaba da kallona, kamar wanda kallon nawa yake kara masa karfin ido. Ina jin lokacin data dauka sai yace.

“Hajiya ga ta”


Ya miko min wayar ni kuma na mika hannu na karba ina kallonsa kamar mai tunanin abunda zan yi da ita.

“Yata.... Da gaske ne abunda Gwarzo ya fada min? Wai kin amince za ki aure shi.....?”


“Eh haka ne...”


Kamar an matsi bakina haka maganar ta zo min subul da baka. Shi kuma sai ya turo bakinsa ya aiko min da kiss marar sauti daga inda yake tsaye.11

“Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah ya tabbatar da alheri a tsakaninku, ya kawardar fitina da sharin sheidan da na zuciya, ya kawar da idon makiya”


“Amin”


Wannan karon shi ya amsa yana wani lumshe ido.


“Yanzu kin yarda?”


“Na yarda kuma na fi kowa farinciki zan yi ma Siyama wannan albishir din, Allah ya maka albarka, kai da kanka ka nemo matar ka I'm very happy”


murmushi yai ya yanke wayar, ni kuma na mike tsaye na fara shirin tafiya.

“Daga yau idan na fito daga gida zan biyo na dauke ki, idan kin tashi aiki kuma ni zan kai ki”


“Amman....... ”


“Shiiiiiiiiii”


Ya dora hannunsa saman bakinsa yana min alama da nai shiru.

“Kuma idan kin je gida ki bar mahaifiyarki ta san abunda yake faruwa, nima zan yi magana da Hajiya zata sanarwa wadanda ya kamata ina son dai cikin satin nan na tabbatar da gaske kin zama tawa, idan an daura aure ban ki ba amman ba zan yarda sati ya shige ban biya sadakin wannan kyakkyawar Babyn ba”


The way da yake magana ban ga alamun da wasa yake ba, amman ya yake min haka kamar mai ba ni aiki? Ko dai ya manta ni bazawara ce? Wani irin biyan sadaki a yanzu kamar wanda ya matsu ko kuma nace wace aka gaji da ita? Anya yau Ahmad lafiya yake kuwa? Daga zancen saki aure sai kuma maganar manya su shiga lamarin kamar wani abunda ba gaske ba? Daman a cikin surprise dinsa har da wannan ko kuma yanzu idea ta zo masa? Kamar wacce yai ma wani magani sai na kasa ce masa komai sai kallonsa nake ina mamakin al'amarinsa.

Ban san abunda Hassan yake nema a duniyar nan ba, ban san wani abu da ya rasa ba, ban san kadarar da ta kai shi fadawa wannan mummunar sana'ar ba, na jama kansa masifa... Wata kila a kashe su wata kila a barsu su kasara rayuwar gidan kaso, amman ko da an sake su an kunyata su tun da an bayyana fuskokinsu kowa ya gansu, a lokacin da ya kamata ace ya samu farinciki sai kuma wannan kaddarar ta fado masa...”7

Hajiya ce take wannan maganar hawaye na fitowa daga idonta, wani irin abu ta ji ya tsaya mata a zuciya tun daga lokacin da gaskiya ta bayyana har yau yana nan tsaye ya tokare mata kirji. Abdallah ya sauke ajiyar zuciya, shi kanshi shi jidadin halin da dan'uwansa da mahaifiyarsa suke ciki ba, no matter how bad your blood is, jininka jininka ne, and idan akwai wanda zai yi blame me a yanzu Ahmad ne domin shine silar faruwar hakan, duk kuwa da yasan abunda Abdulhamid yake ba abun kwarai ba ne, amman yana tunanin ya tona masa asirine saboda ya saka Halima ta so shi kuma ta guje Abdallah, miyasa da ya gano haka ne be fadawa Halima a sirrance ba sai a san yadda za a bullowa lamarin, amman ya zabi ya tozarta shi haka wanda silar hakan ga mahaifiyarsa a kwance tana fama da jinya. Idan har Ahmad zai iya kitsa cuta a zuciyarsa kamar haka then be yi deserve ya aure Halimatu ba, domin shi ma ba a san iya abunda yake sakawa a zuciyarsa ba kuma ba a san abunda yake a karkashin kasa ba, ya fada masa sai ya nuna masa shi din ba kowa ba ne a gurin Halima that's for sure sai yayi, duk abunda yai ko zai yi zai tashi a tutar babu ne, ko mazan duniyar nan sun kare he don't think zai bar Halima ta auri Ahmad, rayuwarsa tana nuna masa babu wanda ya cancanci Halima sai shi, duk da ya san Hajiya ba zata bari ba a yanzu wata rana zata bari, so zai jira har zuwa lokacin da zata yarda but right now all what he want is yai magana da Halima. Tun da har Ahmad ya saka bakinciki a zuciyar mahaifiyarsa shi ma sai ya saka a tasa zuciyar, sai ya nuna nasa kudinsa da wata isarsa ba su isa su siya masa soyayyar Halima ba.28
“Duk yarinyar nan ce taja komai nasadinta komai ya faru, sam babu alheri a tare da ita, bata nufar mu da khairan ai sheran”2

Hajiya ta fada tana kokarin dora laifin akan Halima a ganinta sanadinta ne asirin Abdulhamid ya tonu har haka ya same shi, domin shi mutumen daya shige gaba akai bincike aka tona asiri saboda Halima yai dan haka komai ma ya faru ita ce sanadi. Abdallah dai be ce komai ba sai saurare kukan mahaifiyarsa yake.
“Da na san haka zai Faru Wallahi da tun farko ban bar shi ya aureta ba, Halima ta zame mana fitina a cikin iyali, ta lalata mana komai na rayuwa Allah ya isa tsakanina da ita, ban san me nai mata ba ta tattara duka farincikin nawa ta dauke, ta tarwatsa mana komai har ta kai yau ga ni kwance saboda bakincikinta”8

Sai a wannan karon Abdallah yace.

“Laifin wannan dan iskan ne, shine yai komai ai”

“Amman ai sanadin ne ko? Waya sani ko ita ta saka shi ma”

“Amman ai ba ita ta saka Abdulhamid a wannan harkar ba”2

“Ko ba ita ta saka shi ba, asirinsa saboda wa ya tonu? Allah yana son mai rufawa dan uwansa asiri, idan ba dan su kunyata mu ba taya za su nemi yi masa wannan cin mutuncin”2

Shiru yai yana jin tsanar Ahmad tana kara hauhauwa a zuciyarsa.2

AHMAD POV.
Be taba yarda da gaske yana son Halima ba sai yau, domin farinciki da yake ji a tare da shi ya wuce misali. Taya zai kwatanta yadda yake jinta a zuciyarsa na amincewarta kawai ashe daman tuni ba tausayinta kawai yake ba har da son ta, driving yake amman gaba daya hankalinsa yana gunta after every one minute sai ya kalleta with smile on his face. Wani irin abu yake jin yana masa zillo a zuciya babu abunda yake ayyana aransa sai idan ya kai kasance a mijinta ya zai tsinci kansa? A hankali ya busar da iskar bakinsa ya kalleta wannan karon idanuwansa sun samu masauki a cikin idonta, sai tai saurin kawardar idonta shi kuma yai murmushi ya cigaba da tukinsa har suka iso cikin unguwar.

STORY CONTINUES BELOW
“Ya isa”

“Why?”

“Ba sai ka kai ni kofar gida ba, zan sauka a nan”

“Okay Lims komai kike so shi zan miki”

A gafen hanyar ya faka motarsa yana kokarin fita ta bude mata tai saurin budewa ta fita, sai da ta rufe motar sai ya sauke gilashin motar ya kira sunanta.
“Lims...”

Jimm tai kamar ba zata juyo ba sai kuma ta waigo ta kalleshi a tsorace.
“I love you...... I love you so much.... And i know i love you.....”1

Kasa cewa komai tai kuma ta kasa matsawa daga inda take, kamar yadda ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa, kallonta yai for few seconds sannan yai reverse ya juya ya koma inda ya fito, sai da ya fita daga unguwar sannan ya dauki hanyar gidansu cikin wani irin farinciki marar misaltuwa, abunda be taba saka ran samu ba. After yayi parking habarbar gidan ya fito yana wasa da makullin hannunsa ya nufi part din Hajiya. Kamar ya san shi suke jira yana shiga Siyama ta taso ta sauri ya rumgume shi.
“Congratulations”

“Thank you Sis”

Ya saketa ya nufi gurin mahaifiyarsa kamin tace komai ya rumgume ta.
“Na gode Hajiya, you're such a wonderful Mom, thanks for everything”

Ya saketa ya zauna kusa da ita yana kallonta.
“Na fi kowa farinciki a yau, kasan saboda me? Ka nemo matarka da kanka, kuma wacce kake jin ta kwanta maka a rai, duk a baya ma ma san kana nemo amman sai matsala ta shiga ciki, to wannan karon bana fatar sake faruwar wani abu, a duk macen da zaka aura na kan jin kamar zata malleka ka ta kwace ka ne, amman wannan yarinyar ina jin natsuwa sosai a tare da ita, na dade ina maka fatar auren bazawara musamman irin wannan mai hakuri, domin wasu zaurawa wahala ce take fito da su daga gidanjen mazajensu wasu kuma kishiyoyine suke fito da su, duk mace da zata taba aure ta fito tai zaman zawarci ba tare da ta zubar da mutuncinta ba, hakika wannan matar abar girmamawace domin zawarci abu ne mai tsada kuma mai wuyar sha'ani, duk mace da tai zaman aure ta fito tai zaman zawarci to tayi rayuwa ne guda biyu mabanbanta, akwa challenges da yawa a rayuwarta, tun daga kan uwaye yan uwa masu neman aurenta yayanta mijin da ta fito gunss ko ya rasu, zaka tarar ta fuskanci kalubale, wanda a gaba idan za tai aure zata jure hakuri domin samun ribar auren, akwai fa'ida sosai a auren bazawara Gwarzo sai a yanzu zaka sani”

Ya hade yawun bakinta sannan ta sake kallonsa tana murmushi.
“Abu na biyu kuma ina tunanin lokaci yayi daya kamata ace na bar ku kun tafi duk inda kake so kai da matarka kui rayuwarku yadda kuke so”

Yayi saurin girgiza mata kai.
“Nonono Hajiya, Wallahi ba zan iya ba a yanzu ne kika fi bukatar na zauna a tare da ke, ko ba komai Siyama mace ce zata tai aure, gidan wani zata je ni kuma aurowa zan yi na kawo, akwai abubuwa da zaki bukata wanda dole ni ko matata ne za mu yi miki, ba ki da wani zabi daya wuce ki bar mu mu zauna a tare da ke”

“Idan kuma ita bata so fa? Wasu matan basa son zama da iyayen miji na sani, musamman ma irina”

“Me zai hana ta so? Halima tana da hankali, zata so zama da ke Hajiya, kuma ai kowa da part dinsa ba part daya ba ne, to me zai saka dukanku ku takura?”

Murmushi tai.
“Allah yai maka albarka ya hada kanku ya sa wannan auren alheri a tsakaninku”

Shi da Siyama suka amsa da amin.

“Na fada mata yai magana da mahaifiyarta domin sanarwa duk wanda ya dace, saboda ina son a cikin satin nan na san an tsayardar maganar”

“Ouhhhhh Yaya da sauri haka?

STORY CONTINUES BELOW
Cewar Siyama sai ya kalleta yana murmushi yace.
“I swear to Allah ji nake kamar da na yi sake kadan kamar haka zan iya rasata, idan son samu ne ma idan anje tambaya a daura auren a can, idan ya so duk wani shirye shiyen sai ya biyo daga baya, idan ma tace ba zata tare ba sai da da shekara ba ni da matsala”

Siyama ta tsire baki.
“Wannan Lims din dai ana ji da ita”

Hajiya ta yi murmushi tana kallonsa.
“Kana da abokin takata ne hala?”

“Yes Hajiya kin san mace ko bata da kyau ai bata rasa masoyi, balle ita kuma akwai wani cousin dinta da nake tsoron sherinsa kuma kin san cousins ba su da kyau”3

Gaba dayansu sukai dariya har shi.

HALIMATU POV.
Na manta rabon da wani ya furta min kalmar so haka kai tsaye, gaba daya sai na ji kamar ya sare ko wace gaba ta jikina, kalmar tai min nauyi a zuciya har ta sauko min a kirji. Gaba daya rayuwar yau ta zame min kamar mafarki at first na tafi office na tararda abunda ban yi zato ba kuma na amince ba akan cilas ba kuma ba dan zuciya tana ki ko tana so ba. Da kafa na karasa gida sai dai ban labarta wa kowa komai ba ciki kuwa har da mahaifiyata, to idan ma zan fada mata ta ina zan fara? Me zan fada mata? Yarana ya zan ce musu? Zai karbe su kamar ubansu? Ko kuma zai musu na Abdulhamid ne? Miyasa ban tambaye shi duk wannan ba na amince masa zan aure shi? I don't think na shirya yin wani auren na bar yarana.
  Har akai sallah isha'i ina ta tunani daya, bayan Mama ta sallame sallah na tashi na koma kusa da ita na zauna sai kuma na kasa cewa komai.
“Wata maganar kike son yi?”

Kasa nai da kaina gabana na faduwa sosai na ce.
“Mama yanzu idan nace zan yi aure be yi kusa?”

“Kin taba ganin mace tai kusa da aure ko ta makara?”

“Ba haka ba ne, ina tunanin rayuwar na da fito ne”

“Idan kina kallon rayuwarki ta baya, to har a bada gobenki ba zata taba yin kyau ba, ki yi fatar samun gobe mai kyau, ke a yanzu kamar kan titi kike idan kika ce za ki tsaya waiga bayanaki to mota zata zo ta gabanki ne ta kade ki ta takaki tai miki illa, amman idan kika fuskanci gaba sai rayuwarki tai kyau fiye da yadda kike tsammani, shi bawa ba a son yana yanke kauna daga rahamar Allah”

“Mama na yi wani abun da nake jin kamar ban yi daidai ba, Ahmad ya nemi aurena kuma na fada masa cewar na amince zan aure shi sai dai a yanzu ina ta jin damuwar amincewar da nai, saboda yarana...”

Ina kai aya na ga Mama na murmushi.

“Bayan kin amince kuma shaidan yake son raya miki wani abu a zuciya? Ko yanzu ai lokaci be wuce ba za ku iya yin magana, amman dai duk mutunen da zai rika yayana ai kana gane shi ne tun gida, bana tunanin Abdulhamid ya taba daukar yaranki ko sau daya ne a mota? Amman Abdallah da shi wannan har makaranta suka saka su, kina tunanin mutumen da zai san abunda ya faru da ke da halin rayuwar da kika tsinci kanki a ciki zai yi tunani saka ki cikin wani kunci?”

Kallonta nai a raunace na ce.
“Mama wasu maza suna da son kansu ne, kuma idonsu kan rufe har sai sun samu abunda suke so”3

“Haka ne, amman shi aure fahimtar juna ake so a ciki, za ki iya samunsa ku tattauna, idan ya aminta falillahil hamdu idan kuma ya nuna miki ba haka ba zai ki sake wata shawarar”

Mama tana da gaskiya matsalar yara mai sauki ce domin zan iya magana da shi akan. Har na bude baki an sake wata maganar sai muka ji sallamar Abdallah, daga uwar dakan da muke muka amsa masa yanayin yadda Mama ta kalleni kana gani kasan mamakin ganinsa take, ni kam na san da zuwansa. Tun da ya shigo idonsa na kaina har ya gaisa da Mama be daina kallona ba, idan sabo kuma na saba da irin wannan kallon daga gurin Abdallah. Bayan sun gaisa Mama ta tashi ta fice daga dakin sai ya rage daga ni sai shi ne a ciki. Shiru ne ya biyo baya be ce min komai ba ban ce masa ba, can ya ciro wayarsa ya soma latsawa.
STORY CONTINUES BELOW
“Me ke tsakaninki da Ahmad Gwarzo?”

Kamar daga sama na ji tambayar, ba zan yi mamaki ba idan Abdallah yai kishi daman ya saba kishina tun da yana so na.
“Babu komai”

“Yaushe muka fara haka da ke?”

Ya fada yana kallon irin kallon nan dake nuna da gaske yake.
“Ba karya nake ba, babu komai tsakanina da shi”3

“To idan ke baki da wata manufa akan shi shi yana da ita akan ki”

“Kamar yaya”

“Son ki yake mana ko be taba fada miki ba?”

Na yi shiru kamar na ce masa ya fada min a yau har ya nemi amincewar aure na kuma na amince sai kuma wata zuciyar ta hana ni domin na san abun ba zai yi ma Abdallah dadi ba.
“Be kamata ki karbi soyayyar wani ba a yanzu Halima, wanin ma kuma Ahmad Mutunen daya dora miki laifin kisa sanadin hakan kwakwalwarki ta tabu, a iya tunani yanzu kin yi hankali kina da tunanin ya kamata ki gane mai miki so ya gaskiya ki aure shi”4

“Kai kake min so n gaskiya Abdallah na sani, amman kuma aurenka abu ne da ba zai yiyu ba”2

Gyara zamansa yai yana kallona.
“Kamar dai ba ke ba Halima yau ke da kanki kike fadar aurena ba zai yiyu ba”2

“Saboda Hajiya da Abdulhamid”

“Hajiya idan zamu iya bata lokaci zata fahimta”3

“Ba zata taba so na ba Abdallah har kasa ta nade ba zan taba zama fara a gurin Hajiya ba, bana son na sake aikata wani kuskuren idan na aureka a yanzu mutane za su zage mu Abdulhamid kuma zai ga cewar bamu kyauta masa ba”1

“Gaba daya ya canja miki tunani Halima, ya dauke miki hankali, ya chusa miki wasu abubuwan da babusu akan ki, amman ya kamata ki yi tunani ko da ba zaki aure ni ba be kamata ki auri Ahmad ba, bakinsan komai akansa ba, Halima bana son alaka tana shiga tsakaninku, idan har zan roki wani abu ku yi a yanzu to zan roki ki aje aikin nan a kamfaninsa”

Ya fada da kamar fada har yana nuna ni, Yanzu kam bana jin Abdallah ya tsani Ahmad saboda ni kawai wata kila har da abunda yai ma dan'uwansa, sai dai duk kusanci ni na Ahmad be kai da Abdallah ba duk irin taimakon da zai min yana bayan na Abdallah, idan har Abdallah zai ce kar na auri Ahmad Wallahi zan iya ko dan na faranta masa ne balle kuma aje aiki wanda shi ya fi komai sauki a gurina tun da har ya bukaci haka, bana jin akwai wani abu da Abdallah zai bukata a duniyar nan na kasa masa ko da kuwa raina ne, balle abunda ran ya mallaka.16

“Zan aje aikin gobe In-Sha-Allah”

Na fada ina kallonsa, ina kallon lokacin daya ja dogon numfashi ya sauke sannan ya busar da iskar bakinsa ya mike tsaye ba tare da ya ce min komai ba ya nufi kofa, sai kuma ya juyo ya kalleni ido cikin ido.
“Wallahi ina son ki Halima”7

Wani tausayinsa ne ya kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya.
“Ba wai kaddarar mu ce kawai a haka ba, rayuwarmu ce, wata kila idan mu kai hakuri za mu iya cin ma nasara....”

Shine abunda ya fada sannan ya fice daga dakin, ni kuma sai na nemi jindadi na rasa, taya zan kalleshi na fada masa cewar zan auri Ahmad? Ya zai ji? Ya zai kalli abun? Zuciyarsa zata iya dauka? Ashe da na ce zan rayu da kaunarsa ba zan iya ba? Kar idona ya rufe na sake aikata abunda be dace ba, da gaske Ahmad ya cancanci zama abokin rayuwata ko kuma wata kaddarar ce take bibiyata? Gaba daya sai na kasa ganewa, kamin na ankaro hawaye ya fara wanke min fuska.
  Ban kwanta ba sai da nw labartawa Mama abunda Abdallah yake bukatar nai na aje aikin.
STORY CONTINUES BELOW
“Kuma za ki aje?”

“Mama kina tunanin akwai abunda Abdallah zai nema a gurina da ba zan masa ba?”

“Halima karki yarda ki sake aikata wani kuskuren, wannan karon bana jin kaddarar ce sai dai son zuciya, domin komai a bayyana yake auren Abdallah a gareki ba zai yiyu ba, ni kaina ba zan bari ba, ba zan hana ki aje aiki ba amman kar alakar Abdallah ta shafi alakar da ke tsakaninki da Ahmad, kar kuma ki bari alakar da ke tsakaninki da Ahmad ta shiga tsakaninki da Abdallah”1

Shine abunda ta fada min sannan tai shirin kwanciya. Ni kuma na tashi na koma dakina na kwanta cikin yarana, ina ganin kiran Ahmad na shigowa wayata amman ba kasa dauka. Washe gari ko su Namra ba su riga ni fita daga gidan ba ba dan zan aje aiki kadai ba sai dan na gujewa shiga motarsa kamar yadda ya fada zai rika kai ni yana dauko ni kullum wanda hakan na san ba karamar matsala zai ja min ba, ko da takwas tai ina cikin office dina sai dai yau an kwashe komai kamar ba gurin da aka jera rose ba a jiya. Na zauna saman kujera ina ta tunanin yadda zan fada ma Ahmad cewar zan aje aiki na san dole zai tambaye dalili. Ina jin wayata ta yi ringing na dauko ya duba number shi cikin sauri nai picking.

“Morning Lims”

“Morning too”

“Ga ni kofar gida fito muje”

“Ina office”

“Amman ba na fada miki ni zan rika kai ki ba?”

“Akwai maganar da nake son nai da kai mai muhimmanci”

“Okay Babe gani nan zuwa”3

Ya yanke kiran ni kuma na aje wayar ina ta kallon hoton yarana da ke screen din wayar. Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai ga shi ya turo kofar office din fuskarsa da annuri.
“Karki sake min irin wannan game din seriously bana son kina hawa Napep”

Uffan ban ce masa ba, duk kuwa da na san ba zan iya dauka ba taya za a ace kullum ya kawo ni aiki ya maida ni, ko da yake aje aikin ma zan yi na huta. Zaunawa yai a kujerar da ke fuskantar tawa yana kallon yanayina.
“Akwai damuwa a tare da ke, fada min minene”

“Ina son na aje aikina”

Na fada kai tsaye sai yai min kallon rashin fahimta mamaki karara a fuskarsa.
“As how...?”

“I want to resign”
“No i mean why?”

Na yi shiru kamar ba zan amsa shi ba.
“Saboda na ce zan rika kai ki kullum na dauko ki? Idan ba kya ra'ayi that's normal we can talk, kin san bana son bacin ran ki i won't force you”

“Ba Saboda shi ba ne, Abdallah ya bukaci haka.....”2

Mikewa yai tsaye yana murmushin da zan iya kiransa da dariya.
“That stupid guy ko?....”

“He's not stupid, Abdallah yana da muhimmanci a rayuwata...”4

“How dare you.......!”3

Ban karasa ba ya daka min wata mahaukaciyar tsawa ya ture desktop din dake saman teburina ta fadi kasa har wani zaro ido yake kamar mai aljanu yana maida numfashi da karfi. Tsorata nai garin na mike tsaye kujerar da ke kai ta kade ni na fadi ni da ita, kamar yana jira sai ya zagayo inda nake ya risino kusa da ni ya nuna da yatsa.
“Ba a maganar wani namijin a gabana matukar ina son mace, ina da kishi ki kiyaye wannan, bana lamuntar ki kira wani namijin da muhimanci a rayuwarki idan ba mahaifinki ko dan ki ba”

STORY CONTINUES BELOW
Sai da ya fada min hakan sannan ya mike tsaye ya fice daga office din a fusace, nikam daman jira nake yana fita na tashi tsaye na dauke wayata da jakata na fito daga kamfanin gaba daya na dawo gida. Da daren ranar sai ga shi ya kira ni yana ta bani hakuri akan abunda yai min, na yi zaton ko zai yi magana akan aje aikin da nace zan yi ko kuma Abdallah amman be min ko daya ba sai da zamu yi sallama sannan yace min.
“Ki yi ma Mama magana, ta fadawa wadanda ya kamata sai su saka mana rana da za su zo”

“To”

Shine abunda na ce sannan ya aje wayar, na fada mata kamar yadda ya bukata sai dai maganar yarana na kasa masa ita kuma abun ya tsaya min a rai.  Da aka fadawa kanen mahaifina sai suka nuna jindadinsu suka tambaye waye shi miye sana'ar shi a ina iyayensa suke duk na fadawa Mama ta fada musu, the following day suka saka musu rana assabar wato jibi kenan.
Kamin ranar Ahmad ya zo shi da abokansa biyu suka gaishe da Mama da Inna suka kawo musu alheri mai yawa da kudi. Tun daga ranar a kowa wane karshen dare wato misalin hudu da rabi ko hudu na kan tashi nai alwala nai sallah nafila raka biyu raka ta farko zan karanta fatiha da kulya'ayu sau goma, a raka ta biyu kuma na karanta fatiha da kulhuwallahu sau goma sha daya, bayan na sallame sai na sake sujada na yi salati sau goma, nai Subhanallahi walhamdulillahi har zuwa karshe sau goma, sai rabbana attina fidduniya hasana wafil'ahherati har zuwa karshe sau goma sannan na fadawa Allah bukatata na auren Ahmad idan akwai alheri a cikin Allah ya tabbatar ya bani ikon amincewa kuma ya saka min natsuwa, idan kuma babu alherin Allah ya kawo min mafi alherin shi ma ya zaba masa wata. Haka na jera rana ku nan kullum sai na yi sallah nan na roki Allah.
A iya tunani idan sun je za su gaishe da iyayene kawai wato kanen mahaifina da yayyensa, da kuma neman izinin zuwa fira kamar yadda ya fada min ashe ba haka ba ne. Da goma suka ce masu za su hadu misalin sha daya saura sai ga kiran kanen mahaifina ya shigo wayar Mama, be ce mata komai ba kawai yace ta ba ni wayar.
Na karba na kara a kunne ina masa sallama sai ya amsa min yai na mika masa gaisuwa ita kan be karba min ba yace.
“Ba ki fada mana idan sun zo za ayi daurin aure ba? Haka nan ake abu ba a fadawa sauran yan'uwa ba ba ayi komai ba? Gasu nan sun zo da mota kusan biyar da mutane da goron daurin aure da alawa da dabino”

Kasa magana nai, sai na ji abun wani iri wai daurin aure haka nan kawai daga zuwa tambaya sai kace na fado daga sama, to me ni ma zan ce? Nace a a karya yake ban ce a daura auren ba? Ko kuma na ce ban amince da hakan ba? Ban gama tunanin abunda zan fada ba na ji muryarsa yana fadin.
“Ke nake saurare Halimatu”

“Baba duk yadda kuka yi daidai ne”

“A a ke muke saurare, ke kika turo shi ai idan kin amince sai a daura ni ba mu da matsala idan kuma ba ki amince ba sai ya nemi sasanci a gurinki”

Gaba daya sai na zama kamar wata kurma, na kasa cewa na amince ko kuma a a ban amince ba, zuciyata tai wani irin nauyi kamar wacce bata tana aure ba.
“Na amince Baba”2

Na fada hawaye na sauko min ina numfashi daker.
“To Ma-sha-Allah, Allah yasa alheri sadakin fa nawa za a yanka masa?”

“Baba duk yadda kikai daidai ne”

“To Allah yai miki albarka”

“Amin....”

Na amsa ina fashewa da kuka, ji nake kamar ban taba auren ba gaba daya abun ya zame min bakon al'amari, da gaske kuka nake sosai kamar wata karamar yarinyar da akai wa auren dole, Mama tai yi ta tambayar dalilin kukan nawa na kasa fada mata saboda kukan da nake ji nake zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito waje, idan aka tambaye ni dalilin kukana ba zan iya fada ba domin nima ban san abunda ya saka ni kukan ba.
Abu kamar wasa bayan minti talatin Kanen mahaifina ya kira ya fadawa Mama cewar an daura aure ne, ijiyar auren Ahmad uku ta hau kaina, a lokacin ne kuka yace dazun ban ci komai ba yanzu zan yi shi, kowa ya cika da tsananin mamaki a gidan sai dai dukansu suna murna sanin cewar alheri ne wannan karon yai musu bazata ba sheri ba, duk wanda ya tambayi mi nake yi ma kuka sai na ce ban sani ba domin har ga Allah ni kaina bansan dalilin hawayen ba.
Bayan kamar awa daya kanen mahaifina suka kawo goro da alawa da dabinon dauren aure sannan ya ciro dakina a aljihunsa ya rika hannuna ya danka min.
“Ga sadakin nan Halimatu, mun ce su bada 30k sai suka ce one million za su biya, babu yadda ba mu yi ba akan su rage amman suka ki, ina addu'a wannan aure yasa ya sanya nasa albarka ya saka alheri yasa gidan zamanki ne”4

Da gaske miliyan daya nake gani a matsayin sadakina, ni Halimatu abunda ban tana gani ba ban kuma tana ji ba an biya sadakin bazawara har haka kuma bazawarar ma mai aure biyu da yaya hudu. Dana karba sai na bawa Mama na ce ta aje min, ita kuma ta kulla goron da alawa da dabino ta bada aka kai makota wai a fada musu an daura auren Halimatu yau.
  A lokacin da su Namra suka dawo daga islamiya sai ta dame ni da tambaya.
“Momy aure kika yi?”

Na gyada mata kai.
“Momy da wa? Da wa? Da wa?”

Sai na kasa masa nata ita kuma ta kasa daina tambaya har sai da Aisha ta daka mata tsawa.
“Haba Namra wannan tambaya haka?”

“Momy Daddy kika aura?”

Na girgiza mata kai alamar a'a sai ta fashe da kuka sosai.
“Momy tafiya za ki sake yi?”

A gurin ta fadi da uniform dinta na islamiya tana ta kuka. Babu wanda ya rarrashe ta sai Hafiza ita ta fada mata wanda na aura kuma ta fada mata wannan karon ba zan tafi na bar su ba ne tare za mu tafi.
  Har akai sallah la'asar ban daina ganin kamar mafarki nake ba, kuma ban daina hawayen ba, ina zaune saman carpet din dana kare sallah ina yi ma Allah godiya kuma ina kara rokon ya tabbatar da alheri a tsakaninmu, sai ga kiran Abdallah ya shigo, rawa jikina ya fara yi na fara kallon wayar kamar na ga wani dodo, na kasa daukar kiran har ya katse, lokaci daya na fashe da kuka marar sauti, na san duk inda yake a yanzu ya samu labarin daurin aurena wanda hakan ba zai masa dadi ba.
  Bayan sallah magariba aka daf da sallah isha'i wani gurin ma har an fara yaron ya doko sallama ya shigo gidanmu da manyan ledodi.

“Wai gashi in ji Ahmad kuma yace yana sallama da Halima a waje”

Wani irin faduwa gabana yai sai naji kamar ban taba arba da shi ba, kamar wani bako na ji shi, har nai kamar ba zan je ba sai dai yadda Mama ta matsa min yasa dole na zari Hijab dina na saka na nufi kofar fita jikina ba kwari gabana sai faduwa yake. Can nesa da gidanmu na hango motarsa a fake sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na doshi gurin, kamin na karasa na ji an rumgume ni ta baya ya dora kansa saman wuyana.

“Al-hamdulillah...... Lims you're finally mine....”

“Mutane za su iya ganinmu”

Na fada ina hango daidaikun mutanen da ke can nesa da mu suna sha'aninsu wasu kuma na alwala. Sai ya sake ni ya juyo da ni yai kissing goshina kana ya hade goshinsa da nawa yana goga min hancinsa a hankali sai kallon cikin idona yake.5

“Why are you crying?”

Ban ma san da hawayen sun zubo min ba sai da yai maganar, shiru nai ban amsa shi ba.
“Lims do you love me....?”

“Ban sani ba...”

Na fada da iyakar gaskiyata, wasu hawayen na sauko min, halshensa na ji a saman kunci na yana lasar hawayena.
“Wannan hawayen mai sanyi ne, ni na san kina so na Lims....”

Ya fada bakinsa na taba nawa murya can kasa kasa kamar mai rada, saurin lumshe idona nai muna ta shakar numashin juna....Raba jikina nai da nasa.+
“Mutane za su iya ganinmu”

Be ce min komai ba yaja hannuna ya karasa gurin motar da ni ya bude gidan baya na shiga sannan shima ya zagayo ya shigo ya rufe sannan ya rika hannayena ya soma murzawa yana kallon fuskata.
“Ban miyasa nake jin ki a zuciyata fiye da kima ba, ina jin cewar na fi kowa dace a duniyar nan, a yanzu bani da wani buri sai na aurenki kuma ya cika ina son sosai, irin son da bana jin wani namiji ya taba miki shi, bana tunanin akwai namijin da ya fi ni son ki”

Ya sumbanci hannun nawa.

“Kamin na aureki, idan wani ya fada min zan aureki zan karyata shi kuma na fusata, amman a yau da Yayan mahaifin yai min albishir da cewar an daura aurena da ke sai na rasa inda zan saka kaina dan murna, na rasa abunda zan bashi na kyautata masa na goron abunda ya fada min, na gode da kika amince min na gode da kika ba ni damar shiga rayuwarki, na gode da kika karbe ni a duniyarki”

Ya karasa tare da kai hannunsa yana shafa fuskata, sai kuma ya jani jikinsa ya kwantar da ni ya rumgume ni sosai kamar ba gobe.
“I love you so much Lims”

Ya fada calmly kissing my forehead, dayan hannunsa kuma yana mutsa yan yatsun hannuna. Mu kai shiru kamar babu mu a cikin motar baka jin komai sai saukar numfashinmu, can ya saka hannunsa ya dago kaina ya dora bakinsa a saman nawa kamar zai tsosa sai kuma ya bar shi a haka yana ta kallon idona da na rufe, ji nai an busa min iska a saman idon hakan yasa na bude muna hada ido sai ya hade bakinsa da nawa, a hankali yake kissing din lisp dina sai kuma ya cire bakinsa a nawa ya kai gurin tsinin hancina ya tsosa sannan yai kissing forehead dina ya sake rumgume ni a kirjinsa tsantsa yana sauke ajiyar zuciya.9
“What else i can say more than Al-hamdulillah, you're finally mine”4

Muna haka na hango mota ta faka a kofar gidanmu, ina ganin motar na san cewa Abdallah ne, Ahmad kam be gane shi ba har sai da ya fito daga cikin motar ya jingina yana lasa. Wayar da ke hannuna tai ringing kiransa ya shigo, kallon wayar nai na kalli Ahmad sai na kasa daga kiran.
“Me ya zo yi?”

“Wata kila yana son magana da ni ne”

Bude motar yai yace min na fito muje, abunda ban so ba ke nan domin nasan ganin mu a tare da Ahmad ba karamin bata ran Abdallah zai yi ba, ba zan iya musa ma Ahmad ba kamar yadda ba zan so Ahmad yai abunda zai kara batawa Abdallah rai ba. Ya rufe motar sannan ya rika hannuna muka nufi gurin da Abdallah yake tsaye, daga inda yake tsayen ya dago idonsa yana kallon mu har muka iso, na kasa ce masa komai shi ma be ce min ba Ahmad ma be masa magana ba, sai kallon juna suke kana ganinsu kasan da akwai abunda kowa ya aje kasan zuciyarsa, Ahmad murmushi yake yana ta lilo da hannuna duk yadda na so na kwace hannun sai ya ki saki, na yi tunanin Abdallah zai yi wani abun ne ko kuma ya fada masa bakar magana amman ga mamakina sai ya sakar wa Ahmad murmushi ya mika masa hannunsa.2
“Congratulations, that's good daman ka ce zaka nuna min ko waye kai a gurin Halimatu ko? Na gani yanzu ina taya ka murna”4

Sai da Ahmad ya kalli hannunsa nasa sannan shima ya mika masa nasa.

“Thank you”

A lokacin ne Abdallah ya kalleni da murmushin a fuskarsa yace min.
“Ina taya ki murna”

Ni kam kasa amsawa nai sai Ahmad ne ya sake ce masa

“mun gode”

Sai ya bude motarsa ya shiga yai ribas ya juya ya bar mu a gurin tsaye ina bin motarsa da kallo.
STORY CONTINUES BELOW
“Kun taba yin wata magana ne da shi?”

“Eh lokacin da mahaifiyarsa ta saka aka kamaki ba, yace min wai ni waye ne a gurinki da har zan nuna masa isa, sai na ce masa zan nuna masa ko ni wanenen nan da dan lokaci”

Na yi shiru bance komai ba, hakan yana nufin shi da Abdallah sun yi sa'insa kenan, wata kila shiya saka Abdallah ya nemi na bar aikin a kamfanin dan ya nuna masa ya isa da ni. Ji nai ya saki hannuna ya juyo gabana yana kallona.
“Bari na barki ki huta, ki yi list din duk abunda kike so kin san yanzu hakkinki da na yaranki yana kaina, da safe zan zo na karba”2

Ya fada sannan ya shafa fuskata, har ya juya sai kuma ya juyo.
“Ba ni line wayarki”

“Why....”

“Just”

Ban musa masa ba na ciro line ya mika masa.

“Amman akwai numbers din yan'uwa da kawaye na a ciki”

“Okay idan na dawo gobe zan zo da sabon line sai ki dauki numbers din a ciki”

Kai na gyada masa sai ya juya can kuma ya sake juyowa a karo na biyu yai min alama da na zo, sai na karasa kusa da shi kamar yadda ya bukata, saitin kunnena ya kai bakinsa ya rada min

“Muje ki min sallama”

Ko be fada kai tsaye ba na san abunda yake nufi maybe he want to kiss me or hug, ko something like that, ni kuma bana son mutane su fara saka mana ido ace mun fara yin abunda be dace ba a bainar jama'a.
“Akwai mutane fa”

“To muje zauren gidanku”

“Nan ma za a iya saka mana ido, ka bari har ka dawo”

“Ba zan bari ba....”

Ya fada yana wuce ni ya nufi cikin zauren gidan a dole na bishi a baya, ko da na shiga har ya jingina da bangon gurin yana jiran shigowata, hannunsa ya kai ya kama kwankwaso na ya rike ya hade fuskarsa da tawa.
“So this woman here is mine”4

Ya fada da sigar da babu wanda zai ji sai ni, ni dai hankali yana kan kofar gida kar wani ya fito daga cikin gida ya gan mu. Bakinsa ya saka cikin nawa ya tsosa iya yadda yake jin ya samu natsuwa sannan ya sake ni, kamar an masa shocking haka ya zabura da karfi ya bankare sai kuma ya runtse ido, kamin ya bude su a hankali ya kalleni.
“Good night Sweetheart”

Ya fada yana kissing kumatuna sannan ya juya ya fita daga zauren, hakan kawai na samu kaina da son kallonsa, haka n leko a zaune ina ta kallonsa har ya karasa gurin motarsa ya bude ya shiga yai mata key ya fice.
  Wata irin natsuwa da sakewar zuciyata da nishadi ne suka ziyarce, rumgumar da yai min sai na ji kamar mu kasance a haka har a bada, gaba daya jikina kamshin turarensa yake murmushi ya maye gurbin hawayen da nake, ina jin a raina kamar na yi dace duk da ban tabbatar din ba, sai a yanzu nake jin wata irin natsuwa da farincikin amincewa da nai, wata kila dazun ba kukan bakinciki nake ba, kukan farinciki nake ban gane ba, da kuma yadda abun ya zo min a bazata.3
“I love you so much Lims”

Na yi murmushi ina jindadin tuna kalmar daya fada min a dazun, har yanzu bana jin ina son sa kamar yadda bana jin tsanarsa ko kasan a raina, amman am happy I'm now officially Mrs hakan ma wata martaba ce babba, na juyo na nufo cikin gida, sai da na gama sallah isha'i sannan na bude ledodin da ya kawo min, kaza ce babba har guda biyu da lemu sai kayan tea da katon burodi da kuma ku a cikin farar takarda 20k.
Washe garin ranar na tashi cikin walwala ba laifi ina ta jin nishadi a raina, bayan su Namra sun tafi Islamiya sai ga Aminu ya sallamo ya shigo cikin gidan, kamin ya karaso falon Mama nai saurin dauko Hijabinta na saka ya rufe jikina sannan na dawo falon na zauna. Ya shigo da sallama na amsa masa ina murmushi kamar ba ni ba. Shi ma murmushin ne kwance a fuskarsa sai dai ba irin murmushin nan na jindadi ba irin murmushin nan mai kamar na dole.14
STORY CONTINUES BELOW
“Ina kwana”

“Lfy kalau”

Ya amsa yana ta kallona kamar be taba ganina ba, a raina na raya cewar da ace Ahmad nan Aminu yake min kallon nan da yanzu wani abun ya faru, ban san lokacin da wani murmushin ya subuce min ba har sai da na ji Aminu na tambayar.
“Me kike yi wa murmushi?”

“Ba komai”

“Na ga alamar dai kina cikin farinciki”

Na yi kasa da kaina ban ce masa komai ba.
“Daman na zo ne na taya murna, na ji abunda ya faru ance kin yi aure jiya, shine nace abun babu gayyata”

“Nima abun ya zo min bazata ne shiyasa”

“To congratulations Allah yasa alheri Allah yasa wanda zai rike ki amana ne”

Yanayin yadda maganar ta fito daga bakinsa kana ji kasan ba dadi ya fade ta ba. Ni dai na amsa da Amin.
“Nima na zo na fada miki ne zan maida Murja”

Kallon Mamaki nai masa.
“Murja da wacce ta ci amanarka?”

“To ya za'ayi? Nima ba amanar wasu na ci ba? Kin mutum mai irin matsala ba ko wace mace yake aure ba, kuma idan nace zan nemi mace mai irin ciwona na aura, ban fallasa sirrina ne kawai, kara dai mu rufawa juna asiri ni da ita mu yi zama na tsakani da Allah”

“Allah yasa hakan shi ya fi alheri”

Na fada cike da tausayawa.
“Amin ina fatar dai yarana ba su san da maganar nan ba”

“Ban fada musu ba, kuma ba zan taba fada musu ba In-Sha-Allah”

“Na gode”

Ya ciro kudin da za su kai 30k ya miko min.
“Ga wannan kwai siye wani abu”

“A a muna da komai”

“Haba dai hakkina ne ai”

Na kai hannuna na karba sai ya sakar min murmushi.
“Ina taya wanda ya aureki murna, hakika ya samu mata mai kawaici, mai hakuri, kuma kyakkyawa”

A yau Aminu da kansa ne yake fadar ina da kawaice abunda be taba fada ba a lokacin da nake gidansa, a yau shi da kansa yake kina da kyakkyawa kyau da ya kasa gani a lokacin da nake kusa da shi.
“Ina fatar mutumen da kika aura zai rike miki yaranki”

“Ka yafe mushi su ne?”

“A irin wannan condition din dole nai nesa nesa da su, kuma kin san masu irin matsalar mu musamman maza ba wani dadewa suke a duniya ba, bana son na mutu na barki da dawainiya, ina son ko da zan mutu at least ace kina samun wanda zai taimaka miki wajen kula da su, maybe ma su ne kadai yayan da Allah zai ba ni a duniya i don't know”2

Ya karasa hawaye na cika idonsa.
“Cuta ba mutuwa ba ce Aminu...”

“Tawa ta mutuwa ce Halima, kawai dai ki yi ta saka musu albarka”

Ya mike tsaye.
“I wish you all the best”

“Na gode”

Murmushi yai min as respond sannan ya saka kai ya fice, ni kuma na tashi na nufi dakina na saka kudin a cikin jakata, sannan na fito na fara gyare gyare dakina da dakin Mama daman Aisha ta share dakin Inna.
Da azahar aminiyata Hajara ta shigo gidanmu da murnarta kamar zata cinye ni, wai ita babu abunda yai mata dadi kamar yadda Ahmad yafi dukan mazanjen da na aura rufin asiri, domin da ce wani makaskanci na aura da yanzu makiya sun saka min dariya amman duk wanda yaji ga wanda na aura sai yace hakurin da nai ne Allah yai min wannan sakamakon, ni kan har ta ci ta shude ban ji komai araina ba wai dan Ahmad yana da arziki, wata kila saboda dukiyar tasa bata gabana ne, ni yi mamakin inda ta ji domin ban fada mata ba gashi line ma yana hannun Ahmad balle nace ko kiranta nai, ashe abun har ya fita da goron da aka raba a makota da kuma can family mu wannan ya fada wancan jin babban mutum ne nn da nan maganar ta yadu ita ma gurin wata kawarta tace wacce ita kuma yar'uwarmu ce.
STORY CONTINUES BELOW
Sai yamma ta tafi gida, bayan Abban Afrah ya zo daukarta da kansa har da shi yake min murna wai ya ji na yi aure Allah ya sa alheri, a wunin ranar na damu matuka da ban ji daga Ahmad ba, duk be wani saba min sosai da kira ba amman a yanzu ai ni matarsa ce ya kamata ace ya kira ya ji tashina, ko da yake line yana can hannunsa kuma ban san uzurinsa ba.
  Can da la'asar sai ga Siyama ta shigo gidanmu, sai da ta gaisa da kowa sannan ta bukaci ganina aka fada mata ina dakin Inna, ina zaune a dakin ta shigo sanye da atamfa mayafinta a hannunta tare da jakarta, da sauri ta zo ta rumgume ni.

“Matar Yaya”

Na yi dariya ina dan jin kunyarta sai ta zauna kusa da ni muka gaisa cikin far'a.
“Hajiya tace tana gaishe ki”

“Ina amsawa”

“Yaya yace ya zo na karbi takardar idan kin rubuta”

Sam ni na ma manta da zancen wani rubuta abubuwan da muke bukata sai a yanzu.

“Wallahi ban rubuta na manta”

“Ayyah za ki iya rubutawa a yanzu?”

“Ko kuma mu bari har gobe ko jini saboda ko na rubuta wani abun zan iya mantawa da wani a yanzu”

“Okay to ba matsala”

Ta saka hannunta a jaka ta dauko sabon line ta miko min.
“Ga line yace ki saka zai kira ki”

“Okay lafiya yake”

Na tambaya bayan na karba.
“Lafiya kalau”

Sai ta mike tsaye
“Ni zan tafi in-law Allah ya baki ikon rike min brother na da gaskiya, because yayana yana son ki sosai, Hajiya da ni duka muna son ki Allah yasa kar ki ba mu kunya”

“Allah ya bani ikon kula da ku duka”

Na fada ina murmushi sai ta amsa da amin ta fice rike da makullin motarta. Ban tashi daga inda nake ba na kira Aiman ya dauko min wayata na saka line ciki, ina kunnawa kiransa na shigowata sai nai picking na kara a kunne tare da sallama.
“Tun dazun nake ta kiran line ne ina son ki saka na ji muryarki, ya kike?”

“Ina lafiya, Siyama ta kawo min shi yanzu nan”

“Na sani kin bata list din”

Yanayin yadda yake amsa min kamar a wahale, ni kuma na amsa masa cikin sanyi jikina.

“Aa na manta ban rubuta ba sai gobe”

“Ba ki da matsala Queen, za mu yi waya anjima”

Daga haka ya kashe wayar.


ABDALLAH POV.
Har a yanzu bana ganin laifin Halima a iya abunda yake gani Ahmad kamar ya mata cilas ne tun da gashi abun daga sama suka ji daurin auren.
  Zai iya rasa komai ya hakura ban da Halima, in his own life ya san Halima ba son Ahmad take ba, kuma yana ganin Ahmad kamar ba zai iya rike Halima da gaskiya.
  Duk kuwa da irin kirarin da mahaifiyarsa take na cewar wai daman can Halima haka take so ta bata alakar da ke tsakaninsa da dan'uwansa yanzu kuma ta hana dan'uwansa aure kuma ita ta yi aurenta, a yanzu babu abunda Hajiya bata sani ba na abunda Abdulhamid ya aikata da alakarsu da Ahmad amman saboda bakar kiyayay ta kasa daina ganin laifin Halima, a ganinta ai saboda ita asirin Abdulhamid din ya tonu gashi ta kassarasa masa rayuwa ita ta gyara nata. Abdulhamid ma da Hajiya ta kai masa labarin auren Halima kam yayi farinciki da ba Abdallah da aura ba duk kuwa da ya san Hajiya ba zata bari ba amman auren Abdallah zai fi komai tsaya masa a rai idan har ace haka din ta kasance. Babu abunda yafi yi ma Hajiya ciwo kamar sanin cewa mutunen da Halima ta aura a yanzu yafi yayanta rufi asiri, babu abunda take fata take kuma son ganin kamar lalacewar auren ko kuma Halima ta shiga wani hali. A ranar da za a fara shiga kotu da Abdulhamid da Abraham da wasu mutane hudu babu irin kukan da Hajiya ba tai ba sai ta ji kamar ta hade zuciyata ta mutu dan bakinciki.


6
STORY CONTINUES BELOW
AHMAD POV.
A ranar da ya bar gidansu Halima be iya kai kansa gida ba, saboda wani irin azababben ciwo da ya rika jin yana masa yawo a jiki, a dole ya faka motarsa gefen titi ya kira driver din gidansi yace ya zo ya tuka shi. Da suka isa gida sai ya wuce part dinsa ya kwanta yana ta jin abun na masa yawo a cikin jiki sai dai hannunsa ya fi ko'ina yi masa zafi domin yai masa nauyi kuma ya masa kamar an dora shi akan garwashin wuta. Duk yadda yake da juriya da iya dakewa a daren kasa hakuri yai idan yai tsaye ya zauna ya tashi haka yai ta yi har garin Allah ya waye. Da asuba ma kasa sallah asuba yai saboda bala'in ciwon da hannun yake masa, gumi sai ke to masa yake ta ko'ina kamar wanda maciji ya tsara, kamin haske ya dan shigo Hajiya ta shigo part dinsa ganin shi be fito ba har jin yai kamar ba zai rayu ba. Tana ganin halin da danta yake hankalinta yai mugun tashi da taimakon mutanen gidan suka saka shi mota aka nufi asibiti da shi, wani abun mamaki da aka yi kwaje kwaje aka duba hannu ba a same shi da komai ba, amman Ahmad azabar ciwo yake masa sosai idan ya samu sauki sai idan an masa allurar kashe ciwo sannan zai ji abun ya kwanta masa amman ko allurar bachi aka masa baya jin sauki domin ciwon baya bashirin bachi.
  Sai dai likitocin sun fada masa yawan yi masa allurar matsala tun da ba aiki za ayi masa ba, hakan yasa shi da kansa ya shirya fita waje ganin likita, ko da wasa be fadawa Hajiya cewar tun daga lokacin daya gaisa da Abdallah abun ya sameshi ba domin baya son tai blamed Lims dinsa, secondly kuma ya hana kowa ya fadawa Halima halin da yake ciki saboda kar hankalinta ya tashe kuma kar canfin da take na cewar duk wanda ya kusance ta sai wani abu ya same shi ya tabbata, yana son ganinta amman ba dama sai dai ya kirata a waya, ko video call be son yi da ita saboda kar ta fahimci halin da yake ciki.

24
HALIMATU POV.
Wasawasa aka kwashe kwana takwas ban saka Ahmad a ido ba hakan kuma ba karamin damuwata yai ba, domin sai na ji kamar na saba da shi a kullum ne, zai kira ni a waya da safe da rana haka ma da dare amman hakan be wadatar ta da ni ba. Ya aiko an karbi list din duk abunda na rubuta an siyo har ma da wanda ban rubuta ba duk an siyo kuma ba kadan ba da yawa aka siyo wanda zai dauke mu tsawon lokaci muma amfani da shi.
  A iya sanina yadda Ahmad yake nuna min kauna kamar ba zai iya kwana biyu be saka ni a ido ba balle kuma yanzu da nake matarsa, amman miyasa ya dauke min kafa tun daga wacan ranar? Ko dai shi ma mahaifiyarsa bata so? Ko kuma wani abun ne? Ina tsaka da tunanin nan wayata tai ringing ganin kiransa ne yasa nai hanzarin dauka.
“Hey Babe na ykk”

“Ina lafiya”

“How are my kids?”

“Suna lafiya”

“Na kira na ji muryarki, kuma na miki albishir cewar Kabir yana ta samun sauki ana tunanin end of this month ma su sallame shi, domin an masa tiyata an kwashe jinin daya taba kwakwalwarsa yanzu sun dora shi akan magani ne”

“Ma-sha-Allah Allah ya saka da alheri”

Na fada cikin rashin far'a kamar ba labarin nake son ji ba, ban san abunda ya hana ni jindadi ko murnar samun lafiyar Kabir ba bayan kuma na dade ina fatar samun haka.
“And... I think gobe ko jibi zan je United Kingdom wato London for some works”

Na y shiru ban ce komai ba, domin ban san abunda zan ce ba gaba daya jikina sai ya ba ni kamar ba lafiya ba.
“Idan akwai abunda kike bukata ki fada min”

“Kai nake bukatar gani Ahmad i need to see you”

Daga can cikin wayar ya jiyo sautin murmushinsa mai kama da dariya.

“Wow i got lucky Matata tana so na da yawa haka nan, idan na dawo zan zo In-Sha-Allah”

“Ba zaka zo mu yi sallama ba?”

“Ba zai yiyu ba ne yanzu haka ina Abuja, daga can zan wuce i'm ban fada miki ba, but karki damu next time tare za mu tafi In-Sha-Allah”

Jin na yi shiru yasa shi cewa.

“Kin ji Baby na? Are you there”

“Allah ya tsare”

“Amin i love you”

Na aje wayar ina ta kallon screen din, idan har da gaske wani aikin ne zai kai shi da sai yaje da ni, ko dai shi ma mahaifiyarsa ta masa katanga da ni ne? Ko ba da amincewarta ya aure ni ba? Tun da akai auren ba ban taba gaisawa da ita ba, ni kam dai ina rashin dace da in-laws, but wait miyasa zan zargi mahaifiyarsa? What if ba shi da lafiya? Domin a duk lokacin da nake waya da shi ina jin muryarsa ba a yadda na saba jinta ba. A take gabana ya fadi hankalina yai mugun tashin da sauri na dauki wayar na aika masa da kira amman haka tai ringing har ta katse be dauka ba.....
Kwance take a dakinta tana kallon windows din dakinta da suke bude, pillow na rumgume a kirjinta babu abunda ke fita daga idonta sai hawaye masu zafi.
  Mai aikinsu ce Hindatu ta turo kofar dakin ta shigo da sallama.+
“Assalamu Alaikum, Siyama Hajiya na nemanki”

“Ki ce zan zo”

Ta amsa ta ba tare da ta juyo ta kalleta ba. After like one hour Hajiya ta turo kofar dakin ta shigo.

“Siyama....”

Sai a lokacin ta fara kokarin yin kamar bachi take, hakan yasa Hajiya ta karasa kusa da gadon ta zauna leken fuskarta da hawaye ya gama yi mata kwalliya.
“Miye abun kuka kuma? Me yake damunki?”

Juyowa tai da kyau ta kalli Hajiya wasu hawayen na cika mata ido.
“Hajiya...”

Sai kuma tai shiru ta tashi zaune tana matsar yatsun hannunta.
“Ba ki fito kin ci abinci ba, ko yau ba kya zuwa makarantar ne?”

“Hajiya bana son na sake rasa kowa”

Ta fada cikin hawaye.
“To wa za ku rasa?”

“Ban sani ba, amman yanzu idan ciwo ya kama wani a cikinmu sai na rika ganin kamar zan rasa shi ne, i don't want to be alone....”

Ta fashe da kuka, tana kwantawa jikin Hajiya.
“Babu abunda zai samu yayanki zai samu sauki In-Sha-Allah, ki daina tada hankalinki kin ga nima kina daga min nawa, da kuzari da karfin zuciya da nake da shi sai ki sa ya karye”

“Hajiya ina jin tsoro”

“Ki daina kawai ki yi masa addu'a, ki tashi ki wanke bakinki ki fito ki yi breakfast”

Ta gyada kai tana share hawayenta Hajiya ma ta yi saurin tashi tana tare hawayen da ke son zubo mata, cikin rashin kuzari ta fita daga dakin ba Siyama kadai ba ita kanta abun ya bata tsoro jin cewar ba a ga komai ba kuma gashi yace yana jin ciwo, tun daga lokacin da ciwon ya same shi baya iya komai daga zaune sai tsaye sai kwance wani lokacin kuma ya kan dan zagaya cikin asibitin amman fa sai idan am masa allurar kashe ciwo, ga shi baya wani iya cin abu mai nauyi daga lemu sai ruwa sai tea shi ma can ba a rasa ba, sai dai tana addu'a kuma tana fatar idan an je check up din nan a gano matsalarsa. A dinning din take zaune amman ta kasa taba komai balle ta ci kamar ba ita ta dafa abun karyawar ba, yadda yake fito daga part dinsa ya zo part dinta su karya ko kuma idan ba shi da lokaci sai ya dauki breakfast din ya tafi da shi ko mug ne abunda yafi tsaya mata a rai, yau kusan 7 days yana asibiti mutumen da bata bari yai nisa da ita, and the most saddest part is aurensa aka daura yana cikin farinciki wannan abun ya same shi.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta dora hannayenta saman dinning din ta dafe kanta kamin ta kike tsaye ta nufi upstairs dan jin tai bata bukatar cin komai.
HALIMATU POV.
Ba karamin tsoro ne ya kama ni ba, na san ban tana kiran Ahmad ba tun da nake a rayuwata, amman mi zai saka yanzu na kira shi yaki dagawa? Amman ya kamata nai masa uzuri, after like seven minutes a sake gwadawa still be daga ba na sake gwadawa be daga ba haka nai ta yi har kusan 20 miss calls amman be yi picking ba, a lokacin ne fargabana ya karu tsoro ya auri zuciyata na fara sake sake kala kala, ji nai bana da natsuwa kwata kwata a rayuwata jikina ya bani cewar akwai abunda Ahmad yake boye min.
Tashin nai na shiga dakina na canja tufafin jikina na saka wata rigar yadi na dauki medium veil na yafa na saka talkamina na dauki yar purse dita cikin dabara na fice na bar gidan domin na san idan nace zan fadawa Mama zata iya cewa ba zan fita ba tare da izinin mijina ba, tun da ba fada mata zan yi gurinsa zan je ba, ina tafe ina waige waige kar wani dan gidan mu ya gan ni kamar wata marar gaskiya, Allah ko ya bani sa'a har na tari napep na hau ban hadu da kowa ba, zuciyata bata raya min na je ko'ina ba sai gidansu Ahmad, duk kuwa na san hakan be dace ba amman ba ni da wata mafita wacce ta fi wannan ko dan samun natsuwar zuciya dole naje na ga halin da yake ciki, tun da yanzu yamma ta yi ba na san baya kamfaninsa.
  Sai da mai napep din ya kai ni har kofar gidan na sallame shi sannan nai knocked din gate din gidan cikin sa'a kuwa mai gadin ya bude min, sai da muka gaisa da shi sannan na tambaye shi ko masu gidan suna ciki, ya amsa min da suna ciki har ma da bude min kofar, sai da na doshi harabar gidan sannan na soma tambayar kaina to idan na shiga ciki me zan fada musu? Idan ma mahaifiyarsa ce tai masa katanga da ni fa? Kuma gashi na shigo har cikin gidan anya shi ma kansa zai jidadi? No wait idan ma babu duk wannan anya ban yi rashin kunya ba na tukari idansu kai tsaye? A take duk na ji wani iri hakan yasa ban karasa ba na juyo na dawo gurin mai gadin.
STORY CONTINUES BELOW
“Dan Allah Malam ko zaka shiga ciki kace ana sallama da Ahmad?”

“Wai Alhaji... Alhaji ai.... ”

Sai kuma yai shiru ya kalleni.
“To bari a fada musu”

Ya nufi cikin gidan ni kuma na bude gate din daker saboda shegen nauyinsa na fita daga waje na tsaya, kamin ya fito har na matsu bugun zuciyata ya karu ga tsoro ga fargaba da tunanin rashin dacewar zuwana sai suka taru suka tsaya min a rai. A tsammanina Ahmad din zai fito ko mai gadin amman ga mamakina sai kanwarsa ta fito waton Siyama, tana ganina ta saki far'a ta karaso ta rike hannuna.
“Laaaaa In-law shine kika tsaya a waje"

Nima nai mata murmushin daya kasa boye damuwata cike da kunya na ce.
“Bana son shiga ciki ne”

Sai taja hannuna tana fadin.
“Dan Allah shigo ciki magana, sai ku gaisa da Hajiya”

“A a dan Allah ki bari, ba sai na shiga ciki ba amman Ahmad na zo....”

Sai kuma kunya tasa na kasa karasawa, sai tai murmushi.

“Ai baya nan ya tafi jos.....”

Da sauri na kalleta domin ni ba jos yace min ba.
“Jos kuma?”

“Amman ba can yace min ya tafi ba”

Wani abu tai da ido tana yar dariya kamar marar gaskiya.
“Eh na tuna daga jos zai wuce can garin da yace miki zai tafi...”

“Wane gari?”

Na sake tambaya ina ta kokarin gano gaskiyarta, sai ta fara kame kame wanda hakan yasa hankalina ya kara tashi.
“Can inda yace miki, Kadu.... Na....”

“Ni Abuja yace min”

“Eh eh daga Jos din zai je Kaduna da Abuja, daman Abujar ya kamata nace tun dazun sai na fadi wani gari”

Ta karasa tana murmushin rashin gaskiya. Hannayenta na kama biyu na rike cikin wata irin siga ta magiya na shiga rokonta.
“Dan Siyama idan akwai wata matsala ki fada min”

A iya abunda zuciyata ta raya min Ahmad na cikin gidan yace ace baya nan, hakan na nufin Hajiyarsa ta hana shi ganina kenan ko kuma wata matsalar ce ta dabam daga sashenta. Sakin hannayen nawa tai tace.
“Ina zuwa”

Juyawa tai ta koma cikin gidan, ni kuma na tsaya a gurin zuciyata kamar zata fito, hawaye sai wanke min fuska yake ina sharewa, a yanzu kam idan har ta tabbata Hajiyarsa ta shiga tsakanina da Ahmad ban san ya zan yi ba, wata kila akwai matar da take son ya aura ba ni ba shi kuma ya aure ni ba d amincewarta ba, indan sabon da tsanar uwar miji na saba sai dai bana jin cewar zan iya jure wannan idan har ya tabbata abunda nake zargi ne.
 
“In-law Hajiya tace ki shigo”1

Dagowa nai na kalleta idona da hawaye na girgiza mata kai.
“A a zan tafi dai, ki ce ina gaishe da Ahmad din”

“Ba zata jidadi ba idan kika tafi ba ki shigo ba, bayan kuma ita da kanta ta bukaci haka”

“Ina tsoro kuma ina jin kunya”

“Akwai maganar da Hajiya take son fada miki dan Allah ki shigo ko kuma naje na kirata”

Na yi saurin dakatarta ita.
“A a dan Allah”

“To muje”

A dole na bita a baya bayan na share hawayena, babu abunda zuciyata take raya min sai irin cin mutuncin da Hajiya zata min ko kuma gargadi, a lokacin ne naji ina ma ace ban zo ba, kamar wata marar gaskiya haka na shiga falon sai na tsaya daga bakin kofar na zauna jikin wata karanar kujera mai kamar ta kwalliya dake jikin kofar, ita kuma Siyama ta nufi dakin Hajiyar, ni kam gabana sai faduwa yake har yawun bakina daker nake hade su, ina jin motsin saukowar Hajiyar gabana ya kara faduwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Ahhhh Haba dai Siyama ya zaki barta a bakin kofa? Yanzu idan Yayan ki yana nan Wallahi kin san sai yace mun wulakanta masa mata”

“A a Hajiya ita ta zauna a can daker ma fa ta shigo cikin falon nan”

Siyamar ta fada tana rigan Hajiya zaunawa. Hakan yasa na dan dago kadan na kalli Hajiya tare da mika mata gaisuwa sai ta amsa min da murmushi.
“Lafiya kalau taso dawo nan Yata”

Ta fada tana taba kujerar da take zaune wacce ta zaman mutum uku ce, ban iya musa mata ba na tashi na koma a inda ta bukata wato kusa da ita na zauna a kasa wata irin kunya na kara rufe ni, ai kam da kunya ace na so neman miji har gidansu!
 
“Kawo mata abinci da lemu Siyama”

Umarnin Hajiya Siyama ta bi a gabana ta jera min kula biyu wacce nake kyautata zaton tuwo da miya ne ko shinkafa da miya, sannan ta kawo min lemu da ruwa da kofuna ita da kanta ta bude lemun ta zuba min a kofi sannan ta koma ta zauna. Kunya ta hanani ko da kallon nemun balle na dauka na sha.
“Hajiya zan tafi”

Na fada ina mikewa tsaye cike da kunya.

“A a ko abincin ba ki ci ba?”

“A a koshe nake”

“Ba Ahmad kika zo nema ba? Zauna mana”

Hakan da tace sai yasa kunya ta kara rufe ni.
“A a daman... ”1

“Zauna Yata ke ma kina da hakkin sani”

Cewar kina da hakkin sani yasa na koma na zauna cike da son jin ko minene.
“Yata... Mijinki ba shi da lafiya Siyama ta fada min cewar yace miki ya tafi Abuja, be je ko'ina ba yana asibiti, yace miki haka ne saboda baya son a tashi hankalinki, ni da Siyama duk ya roki kar mu fada miki halin da yake ciki, sai dai na fada miki ne saboda ke matarsa ce kuma kina da hakkin sani, na san ya mace na da kunya da kawaici tun da har kika iya zuwa nan dan jin lafiyarsa aiko kin nuna mana kauna, ya kamata ke ma ki san halin da yake ciki”

Tun da ta fara maganar na ji zazzabi ya rufe ni, a razane na kalleta.
“Hajiya me ya same shi? Dan Allah ku fada min”

Na juya gurin Siyama ina hawaye.
“Rashin lafiya ce ki kwantar da hankalinki da sauki ai sosai, yanzu haka na gama shirin fitar da shi waje jibi zamu tafi”

A take jikina yai sanyi gaba daya sai na nemi kunyar da nake ji na rasa na kama kafafuwan Hajiyar na rike.
“Dan Allah ku kai ni na gan shi, ina bukatar ganinsa dan Allah”

“Siyama tashi ki kaita”

Hajiya ta fada ita ma hawaye na sauko mata kamar yadda Siyamar ma take balle kuma ni da kuka ya zame min abinci. Da sauri Siyama ta tashi ta nufi dakin da nake kyautata zaton nata ne bata dade ba ta fito rike da dan mayafi da makullin mota, ni kam jiki na rawa na tashi na bi bayanta, kusan a tare muka shiga motar domin zuciyata sa ya soma raya min abubuwa marasa dadi. Wayarsa na soma kira wannan karon ma sai da tai ringing ta katse ba a daga ba.
“Idan yana cikin azabar ciwon baya iya daukar kira”

Siyama ta fada tana tuka motar tana kallon sunan yayanta dake gaban wayata, ji nai kamar ba zan iya hakura ba sai na sake kiran na ci sa'a ya daga.
“Hello Lims...”

Sai na kasa magana saboda bana son yaji kukana.

“Lims.... Lims.... Lims....”

STORY CONTINUES BELOW
Haka yai ta kirana amman na kasa amsawa daga karshe na kashe wayar gaba daya, sannan na kalli Siyama na ce.
“Tun yaushe ne ba shi da lafiya”

“Wacan asabar din da ta wuce, yace ya ji abun yana driving be ma iya kawo kansa gida ba sai da ya kira driver ya tuka shi ya kawo shi gida saboda hannun da ke masa ciwo, yace mana be yi kwana ba saboda azabar ciwo kuma da aka je asibiti aka auna sai aka ce ba a ga komai ba”

“Mi yake damunsa?”

“Ciwon Hannuna ne, wani lokacin har cikin jikinsa yace yana jin abu, idan ya taso masa sai an daure ko kuma an masa allura sannan yake samun sauki”

“Hannun ya bugu da wani abu ne?”

“Mu dai be fada mana ba gaskiya, yace cikin dare ya soma jin abun”

A gurin da aka tanada dan aje motoci ta aje motarta muka fita kusan har na fita sauri ma duk da ban san inda yake ba har sai da ta shiga dakin da kanta ina binta a baya. A zaune muka same shi an daure hannunsa na dama da belt dayan hannunsa kuma rike da waya. Yana ganina ya watsawa Siyama wata muguwar harara wacce ta saka ta kasa karasa cikin dakin.
“Zuwa kikayi kika dauko ta ko?”

“A a Wallahi ita ta zo...”

“Shut up.... Ban fada miki kar a fada mata ba? Ko ban fada miki tana da hawan jinin ba?”

“Yes amman..... ”

“Fita ki ba ni waje.... And if wani abu ya samu matata i swear sai kin yabawa aya zakinta”

Cikin tsawa sosai yake mata fadan ya ma kasa tsayawa ya saurareta, da sauri ta juya ta fice tana kuka. Nima da nake tsaye bakin kofar kuka nake ina kallonsa yayi wani irin mugun rama sosai kuma kana ganinsa kasan ba shi da wani kuzari.5

“Kin gani ko? Saboda kukan nan yasa nace kar a fada miki yanzu sai ki tashi hankalinki....”

“Amman ina da hakkin sani, ni matarka ce, a iya tunanina babu wani boye boye a tsakaninmu, be kamata ka boye min wannan ba.... ”

Na fada cikin kuka, sai ya aje wayar ya miko min hannunsa na hagu, ni kuma na taka na karasa kusa da shi na kama hannun na rike.
“Can you please hug your husband”

Na rumgume shi kamar yadda ya bukata ina fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya. Da dayan hannun ya rika shafa bayana yana min magana a hankali kamar yadda ya saba.
“Babe please kukan kin nan yana taba min zuciya, bana son wata damuwa ta same ki shiyasa na ce kar a fada miki”

“Daman na sani.... Shiyasa nake tsoron rabar mutane ko kuma mutane su rabe ni... Saboda wani.... ”

Ban karasa ba yasa hannunsa na hagu ya dago fuskata ya hade bakina da nashi, we spend more than 5 minutes muna abu daya kamin ya cire bakinsa ya hade goshinsa da nasa.
“I miss you....”

Ya fada cikin rada.

“Daman can ina fama da ciwon kirji kuma kin sani, to shine yanzu ya sauko min har a hannu, so ki daina canfa kanki idan kina haka haka ne zai ta sakancewa da ke, Allah yasa dai baki fadawa Hajiya wannan maganar ba? Kar ki sa ta fara zargi ta tsorata ta dauka da gaske ne”

Na girgiza kai a hankali hawaye na sauko min.
“Ban fada ba... Amman....”

“Amman.... ”

Yaja hancina sannan ya saka hannun ya share min shawaye.
“Karki sake irin wannan maganar, tun before na aure ki nake jin wannan ciwon yafi min tsanani a yanzu kawai pls smile”

STORY CONTINUES BELOW
Ya fada yana jan kumatuna, all what i try to do is na tsayardar zubar hawayena. Tashi nai na zauna saman gadon kusa da shi, a yau kam ni nake masa irin kallon da yake min wani irin jinsa nake a raina gaba daya tausayinsa ya gama mamaye min zuciya. Kissing forehead dina yai sannan ya saka hannunsa na hagu ya kama hannuna ya rike gam.
“Sarkin kuka i love you”

Kwantar da kaina nai kafadarsa ta hagu ina jin wani sabon kukan na son fito min. A hankali na fara jin yana motsi da na kalleshi sai na ga ya rufe ido yana cizon baki, a take hankali yai mugun tashi cikin sauri na mike tsaye ina tunanin abunda zan yi, dayan hannunsa yasa ya rike hannunsa na dama yana wani irin nishi yana ambaton Allah.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Shine abunda na furta ina fashewa da kuka, a yanayin yadda nake ganin fuskarsa da kuma yadda ya rike hannun ya isa ya sanar min da irin azabar da yake ji, wacce nake jin kamar ace akwai abunda zan iya a dauke masa ciwo gaba daya, da sauri na fito daga dakin da zimmar zuwa dakin da Doc Nura yake domin na san asibiti tun da ba yau na fara shigowa ba, a kujerar dake kusa da dakin na yi arba da Siyama zaune tana latsa wayarta tana ganina ta mike tsaye.
“Ciwon ya tashi kenan?”

Ban ko kula ta ba na nufi hanyar da zata sadani da dakin likita ina kuka, kamin na karasa mutumen da ke gadin kofar office din ya tare ni.
“Likita nake nema ciwon Ahmad ya tashi”

“Baya office dinsa tun dazun ya fita”

Juyawa nai da gudu na koma dakin sai na samu likitan da wasu likitoci biyu suna tsaye a kansa, Siyama kuma tana gefe tsaye tana kuka, belt din suka kwance suka sake saka masa wani sannan sukai masa allura.
“Dan Allah ku je waje..... ”

Ni da ita muka fito daga dakin muka tsaya a waje, ita kuka ni hawaye.

“Ki yi hakuri zai samu lafiya in Allah ya yarda”
Na fada ina dafata domin a yadda ita take kuka dole ne ni tasa ni na hade nawa kukan na zama jaruma na lallashe ta.

“Ina fatar hakan, baya son muna zuwa kusa da shi saboda kar mu ga halin da yake ciki, tsoro na ke ji ina jin kamar.... kamar.... Yaya mutuwa zai yi.....”

Na yi saurin rufe mata baki.

“Haba dai cuta ai ba mutuwa ba ce, zai samu sauki In-Sha-Allah”

A lokacin ne wani kukan ya zo min, tana da gaskiya ni da ita za mu iya rasa shi, saboda haka suka rasa yarsa, idan har ya kasance ni ce sila fa? What if ya kamu da wannan ciwon ne saboda ya aure ni? Ban raba dayan biyu ba Doc Nura ya fito daga dakin, ya nufo inda nake tsaye ni da Siyama yai mana maganar da zata kwantar mana da hankali cewar Ahmad zai samu sauki. Sai da ya wuce zuwa wani gurin sannan Siyama ta bude dakin ta shiga, ni kuma na bi bayan likita na cika kafa kamin ya shige na cin masa.
“Doc dan Allah ina son magana da kai”

Juyowa yai ya kalleni.
“Ina jin”

“Dan Allah miye abunda yake damun Ahmad?”

Shiru yai kamar mai nazari.

“Hajiya bata fada miki ba?”

“Ta fada min tace ba a san ko minene ba amman ina son kara ji daga bakinka”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.

“Gaskiya ne, an yi duk wani hoto daya kamata amman ba a ga komai ba, kuma shi yace yana jin ciwo yana masa yawo a hannun”

“Amman tun yaushe abun ya fara?”

STORY CONTINUES BELOW
“Yace min ranar assabar da dare, ya fito daga gurin abokinsa da dare, wai be iya kai kansa gida ba sai da ya kira direbansu ya kawo shi, na tambaye shi ko ya ci wani abu ne ko kuma hannun ya bugu da wani abu? Yace min a a yanzu jibi za a fita da shi, asibitin da za a kai shi tana da kyau tana daya daga cikin asibitoci masu kyau da iya aiki a duniya, ina sa ran ko minene za su gano In-Sha-Allah ki kwantar da hankalinki”

Na gyada masa kai sannan na juyo na fara tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa, babu komai a zuciyata sai tausayin Ahmad da kuma zargin kaina domin a wannan assabar din guri ya fito, ban san ko ya biya ta wani gurin ba, amman tabbas na san ranar ce abun ya same shi. Jinginawa nai jikin wani gini ina hawaye, wayata tai ringing da na duba sai na ga number Hafiza, share hawayen nai na dauki kiran.
“Hello”

“Halima kina ina?”

“Dan Allah kina kusa da Mama?”

“Eh ita tace a kira ki ai ta duba bata gan ki ba”

“Bata wayar”

Ina jin sallamar ta a kunnena sai na fashe da kuka.
“Mama na fita na zo nan asibiti Ahmad ba shi da lafiya”

“Subhanallahi miya same shi?”

“Hannun shi ke ciwo, kuma likitan yace ba a gano matsalar shi ba an yi hoto ba aga komai ba, Mama tun ranar assabar din daya bar gurin be sake lafiya ba har yau”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, kina asibitin ne?”

“Eh Mama tsoro nake ji”

Na fada ina kuka domin har ga Allah tsoron nake ji.

“Ikon Allah abu kamar na iska? Ki kwantar da hankalinki za ku zo yanzu In-Sha-Allah”

“To”

Na kashe wayar ina share hawayena, sannan na nufi dakin da yake na tura na shiga, ban samu Siyama a dakin ba shi kadai na samu a zaune kamar dazun, a take hawaye suka fara wanke min fuska amman shi murmushi yake min wanda zai kwantar min da hankali, karasa nai kusa da shi na saka hananyena duka biyu na rika fuskarsa ina ta kallonsa har ga Allah ban tana jin son sa da tausayinsa a raina ba irin yau.

“Tun ranar da ka bar gurina baka sake lafiya ba, ba a gano dalilin ciwon nan naka ba, Ahmad ba zan daina zargin kaina ba, idan wannan ciwon be barka ba zan yafewa kaina ba, na dade ina jin tsoro bana son mutane suna samu matsala saboda ni, kuma ina ji a jikina cewar ni ce sila....”

“Shiiiiiiiiiiiiiiiiii”

Ya dora hannunsa saman bakina.
“Ke baki dogara da Allah ba ne? Kin gani saboda gudun hakan yasa nace kar a fada miki, zaki saka damuwa a ranki har ciwonki ya taso, sannan za ki so ki fara magana marar kyau har ki sa a fara zargin wani abu, musamman ma Hajiya ta ko Siyama, dan Allah Lims ki bar wannan a matsayin sirrin mu, bana son wani yace zai ga laifinki ko ya tsane ki a yanzu, kina bukatar farinciki ko bana raye, and I'm sure idan ba ki samu a gurina ba Hajiya da Siyama za su ba ki, saboda sun san ina son matata sosai...”

Ya karasa yana sumbatar hannuna. Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rumgume shi ina jin kamar akwai abunda Ahmad ya boye min, har ga Allah ba zan daina zargin kaina a kan ciwon Ahmad ba domin a lokacin da be aure ni ba abun ba haka yake ba, why sai yanzu? Ko dai ni din ba alheri ba ce a gurin jama'a? Sanadina ya rasa yarsa, yanzu kuma ace ya zama mijina kuma ta kamu da ciwo?  Ina kokarin tsayar da kukana zancen Siyama da na Doc Nura ya fado min a rai, cewar a daren assabar din data gabata abun ya same shi and a wannan assabar din yana tare da ni ai kuma daga ita ne be dawo ba, hakan na nufin a ranar ne ya kasa kai kansa gida? Kuma a wannan ranar he hold my hand wata kila daga nan abun ya same shi.

“Abu kamar na iska”1

Maganar Mama ta dawo min, no wait a daren ma ai ya gaisa da Abdallah, kuma Abdallah zai iya masa wani kofi, indai har ransa ya bace, i can remember ni ma ya taba min a lokacin da ya bukaci na shiga motarsa na ki sai an rasa mai napep din da zai dauke ni, and i lokacin da na auri Abdulhamid ma ya taba min na kasa girki, ya taba min wayata tsage ba tare da ta fadi ba, and yayi ma Abdulhamid ma, tabbas zai iya yi ma Ahmad inda har za a duba ace ba a ga komai ba tabbas Abdallah ne.
  Shine abunda zuciyata ta raya min kai tsaye, domin a wannan ranar Ahmad ya rike hannuna har gaban Abdallah kuma na san hakan ba dadi zai masa ba, secondly the way da ya ba Ahmad hannu su gaisa ba dan Allah bane, how Abdallah zai yi wani murna ya aure ni? Wanin ma wanda ya bukaci na daina aiki a kamfaninsa saboda baya son taraiya mu...
Ban san lokacin da na mike tsaye da sauri ba hankalina yai mugun tashi.

“What...?”

“Ya kamata naje gida ba su san na zo nan ba gashi yamma ta yi”

Kallona yai from head to toe.
“Ji veil din da kika fito da shi Lims, nasa doguwar riga ce amman ina bukatar ki rika rufe min jikina”

“Zan saka next time, zan dawo anjima kadan...”

Na fada ina nufar kofa da sauri sai ya kira ni.
“Hey Lims are you okay?”

“I'm fine”

Na fada ina kokarin kwantar da hankali.
“Okay come here and kiss me”

Dawowa nai na yi kissing dinsa sai ya rumgume ni da dayan hannun nasa.
“I love you”

Ya rada min sannan na sake shi na mike tsaye na dauki purse dita na fice daga dakin. A phone list dina na shiga na nemo numbersa da ke kan gmail nawa na danna masa kira da sabon line na, ringing rai sai da ta kusa katsewa sannan ya daga da muryar da ke nuna be san mai magana.

“Abdallah kana ina?”

Yana jin muryarta ya gane ni ce mai magana.
“Halima.....”

Yayi shiru sai kuma ya amsa.
“Ina gida”

“Wane gidan?”

“Gurin Hajiya”
Kashe wayar nai na nufi hanyar fita daga ward din ina ta sauri kar na hadu da su Mama.For the first time a yau zan tunkari Abdallah da maganganu a cikin gidan Hajiya babu tsoro ko fargaba a tare da ni, sai dai ga dukan alamu shi din ya kasa natsuwa sai kiran wayata yake ni kuma na ki na dauka domin face to face nake son ganinsa ba ta waya ba, kamin mai napep din ya isa har na matsu, yana saukeni na biyashi kudinshi na buga gate din sai na ji shi a bude, hakan yasa na tura kofar na shiga babu kowa a harabar gidan sai motoci ina ganin motarsa na tabbatar da lallai yana gida kamar yadda ya fada min. Kai tsaye na nufi kofar falon nai knocked sai na ja na tsaya, after some seconds ma sake kwankwasawa. A hankali aka bude kofar Abdallah ne ya fito daga cikin falon ya janyo kofar ya rufe yana kallona da mamaki a fuskarsa.2
“Halima lafiya?”

Ya tambaya a hankali kamar mai rarrashin yarinya. A yau da na kalleshi sai na ganshi kamar ba Abdallah ba, duk wata kima da matarta da mutunci da nake ganinsa da ita a yau sai na nemeta na rasa.
“Ina mamakin yadda zaka fada min abunda ba shine a ranka ba, ina mamakin yadda ka tozarta yardar da nai da kai ka watsar da amincin da nai maka”

Karara mamaki da al'ajab suka bayyana a fuskarsa.
“Halima are you okay?”

“No I'm not, me yasa zaka fada min abunda ba shine a ranka ba, akan me zaka ce kana son farincikina bayan ba haka ba ne a ranka?”

Matsowa yai kusa da ni ganin yadda nake daga murya, idanuwana kuma na nuna tsantsar bakin raina.
“Wace irin magana ce wannan? Me yake damunki?”

Ya fada murya kasakasa.

“Kaine damuwata Abdallah, kai ne matsalata”

“What happen?”

“Ka rantse min baka san abunda yake faruwa ba....!”

Murmushi yai ya lumshe ido ya bude.

“Wai wannan banza... Ai...”

“Shi ba banza ba ne mijina ne na sunna!”2

Na fada cikin wani irin zafin rai da ban taba sanin ina da shi ba. Sai ya sake yin murmushi.
“Na sani ne ai, har na taya shi murna remember?”

“Yes a ranar ka cije shi a hannu”

“Maye ni ne ko aljani da zan masa wani abun?”

“No amman kai kana da kofi, kai ka yi wa Abdulhamid ya kasa aure, ka taba min ba sau daya ba ba sau biyu ba, Abdallah na sani zaka iya kullatar Ahmad a rai”

“Yes...”

Ya amsa min kai tsaye yana hade fuska kamar ba shi ba.
“Ya fada min zai nuna min matsayinsa a gurinki, kuma ya fada ya cika na sani yayi forcing din ki ya aure ki, he deceive you ba ki san waye shi ba, how could he? Ya aure ki by force and ya holding hannunki a gabana bayan ya san na fi kowa son ki? How dare he?”2

“No how dare you....! Ahmad be aure ni ba sai da amincewa ta, abunda kai masa ya nuna baka son farincikina, domin yan'uwansa da danginsa ni zarsu zarga idan hakan ta faru ya kake tunanin zan kasance?”2

“Amman Halima ba son shi kike ba, ta ya za ki auri mutumen da ya laka miki laifin kisan kai? Ko kin manta ne? Mutumen daya tashi sakawa a rufe ki gidan yari? Babu kalar maganar da be fada miki ba, Ina son ki Halima kin sani ina da kudurora akanki, i just want you to get a better life, kuma idan mu kai jira na wani lokaci wata kila Allah zai cika mana burinmu”2

“Jiran shekara dubu nawa? Jiran ranar da Hajiya za ta so ni har ta amince na aure ka? Ko jiran ranar da Abdulhamid da bakinsa zai roki na aure ka? Ko jiran ranar da mutane za su ga dacewar haka su ba mu shawara aikatawa? Ba so na kake ba Abdallah kana son ka ne, a lokacin da na ke auren Aminu ka sani mijine uban yayana amman kullum sai ka fada min aibinsa, kullum sai ka fada min abunda zai bata min rai saboda na rabu da shi na aure ka, ka sani neman auren matar aure haramun ne Annabi ya hana amman ka nace kana ta min campaign kanka, babu abunda baka min dan na kashe aurena na aureka, wannan dalili ya hana ni auren shiyasa na zabi na aure dan'uwanka domin shi be taba min haka ba, duk kuwa da kasancewar shi ya fara so na kamin kowa, yana sane nai aure amman be taba ce min Halima ki kashe aurenki ki aure ni, Abdulhamid ya fika zuciya mai kyau, domin shi be taba cutar da ni ba, kawai ya kasa aminta da ni ne a lokacin da kaddara ta fada min, and now na sake auren wani ba kai ba, so kake na kashe auren na fito aure ka? Saboda ka cika son kanka kuma ka kasa yarda da kaddara, miye laifin Ahmad idan na aure shi kuma zan samu farinciki a gidansa? Ashe ba farinciki kake min fatar samu ba?”2

STORY CONTINUES BELOW
Na karasa a tsawace hawaye na sauko min.

“Halima kamar ba ke ba”

“Ni ce dai, na zo na gargade ka ne, idan wani abu ya samu mijina...! Ba zan taba yafe maka ba, kuma hakan ba zai saka ya sake ni ba ba zan taba rabuwa da shi ba har a abada...! Domin ni na yarda da abunda ka kasa yarda da shi KADDDARA”1
Na kare ina nuna shi da yatsa, sai ya girgiza min kai ya kara matsowa kusa da ni

“Haba Halima kina da raunin tunani, ta yadda idan wani ya kisa miki wata maganar sai ki hau ki zauna akanta, ki rika kokarin samawa wasu farinciki ba kanki ba, yanzu duniya ta wuce wannan kowa kansa ya sani, kamar kin manta waye Ahmad? Miya zai kitsa miki abubuwa a kaina kuma yardar da mutumen da kika gani a jiya sama da ni?”1

“So kake GOBE NA ta lalace, so kake mutane su fara guduna suna ganina kamar wata annoba? So kullum nai ta dauwama a bakinciki da damuwa? Na gaji i deserve happiness”1

“Shi nake kokarin ba ki, i promise you za ki samu farinciki a tare da ni, dukannin mafarkina da burina akanki ne, Halima ina miki son da wani da'namiji be taba miki shi ba....”2

Yana karasa Hajiya ta bude kofar falon ta fito, a yanayin yadda na ganta da kuma yadda fuskarta ya nuna ta ji komai. A gabansa ta tsaya yana kallonsa shi ma kallonta yai sai yai kasa da idonsa.
“Da gaske kai ne silar ciwon Hassan?”

Ta masa tambayar tana masa wani irin mugun kallo, sai yai shiru ya kasa amsawa kuma ya kasa daga ido ya kalleta.

“Ka amsa min? Eh ko a a?”

Ta daka matsa tsawa jikinta har bari yake.
“Eh....”

Tasss ta wanke masa fuska da mari kamar daman jiran take ya amsa mata da eh din, hakan kuma be wadatar da ita ba har sai da ta sake marin dayan baren fuskar.

“Amman baka da tausayi baka da imani Husaini.... Allah ya wadaranka....”

Cikin kuka take mishi wannan maganar, shi kuma har lokacin be motsa daga inda yake ba. Sai kuma ta juyo ta kalleni tana hawaye.
“Fita ki bar min gida, ba ke ba yaya har abada, ko bana raye ka auri Halima ban yafe maka ba.....!”2

Ta karasa tana nuna shi da yatsa, a rikice Abdallah ya kalleta ya kalleni sai ya fadi kasa ya rike kafafuwanta ya fashe da kuka kamar ba shi ba.
“Noooooooo Hajiya dan Allah..... Hajiya dan Allah, Hajiya dan Allah.... Hajiya dan Allah.... Hajiya dan Allah...”

Ya maimaita hakan ya fi a kirga yana rike da kafafuwanta yana kallona kuka yake sosai kamar ba namiji ba, sai kuma ya mike tsaye ya rike hannayenta.
“Hajiya ina son Halima Wallahi baki san kudurina ba dan Allah karki shiga tsakaninmu haka....”

A take ta fisge hannunta ta sake wanka masa kyakkyawan mari. A lokacin ne yai shiru ya runtse ido.

“Ka gani ko? Dan Allah ka kyale min mijina.... Ina son abuna”

Na fada ina hade hannayena nima hawaye nake kamar shi, sai ya bude ido ya kalleni kamin ya juya yana kallon mutanen da suka fito daga falon suna tambayar ba'asi, Hajiyar kuma ya koma cikin falon tana kuka. Ni kuma na juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fara tafiya ina jin wani abu marar dadi. Sai da na kai gate din sannan na juyo na kalleshi har lokacin yana tsaye a inda yake yana kallona, juyawa nai na bude gate din na fita. Sai da nai tafiya mai nisa sannan na samu napep na shiga ta mayardar da ni asibitin ko da na isa ana kiran sallah magariba, kai tsaye na nufi ward din da Ahmad yake ina isa na tura kofar dakin na shiga, sai na samu Mama da Inna zaune a dakin ga Hajiyarsa da Kanwarsa Siyama da wata wasu mata hudu da ban wayance su ba, sai dai ina kyautata zaton yan'uwan Ahmad din ne, shi kuma yana zaune saman gadon wani kallo kawai yake aiko min wanda ke nuna ba lafiya ba. A sanyaye na shiga muka gaisa da mahaifiyarsa sai ta gabatar da ni a gurin matan, sannan tace min.
STORY CONTINUES BELOW
“Kin gwangwanin Gwarzo nan”

Hakan yasa na sake mika musu gaisuwa sannan na tsaya a kusa da Inna sai dai a duk lokacin da na kalli Ahmad sai ya dan harare ni kasa kasa, sannan ya sauko saman gadon ya shiga bandaki yai alwala ya fito, Hajiyarsa ta umarce ni da na shimfida masa carpet su kuma suka tashi suka fita tare da bakin. Inna da Mama suka mike tsaye Inna na ce min.
“To mu kan mun tafi Halimatu sai kin dawo Allah ya kara sauki”

“Amin inna sai na zo”

Sai da suka juya sannan ya kawo kunnensa kusa da nawa ya rada min.
“Ki ce musu nan za ki kwana”

Na lake kafada alamar ba zan fada ba, shi kuma ya kware min ido kamar mai yi da karamar yarinya. Sai da suka fice sannan na shiga bandakin nai alwala na fito na zauna bakin gado har sai da ya gama sannan ya tashi ya dawo saman gadon ni kuma na hau carpet din nai sallah, babu komai a addu'a ta sai nemawa Ahmad lafiya da rokon Allah ya tsare min shi. Sai da na shafa addu'ar sai ya miko min hannunsa na hagu, na rika na tashi tsaye sai ya dawo da ni kusa da shi na zauna, sai ya saka hannunsa saitin kwankwaso na yana ta wasa da shi, ya dora gemunsa saman wuyana sai yasa ta bakinsa ya janye mayafin kaina ya sauko kasa, bakinsa saitin kunnena.
“Na fadawa Hajiya ta sa a shirya miki ticket mu tafi tare”

“Amman Ahmad tun da ance ba a ga komai ba why not a yi addu'a kasan wani lokacin iska da kandu suna yin haka fa”

“Ba laifi ya zama iska ba, kin san Nigeria ba mu da irin wannan cigaban yanzu za a iya zuwa a can su yi gwaje gwajensu kuma a gano matsalar”

“No ba na asibiti ba ne”

“How do u know?”

Kamar mai rada haka yake min magana in each word sai ya tsotsi kunnena sannan yake fadarta wani sa'in kuma sai ya busa min iska a kunnen. A kalleshi a natse na ce.
“Baka fada min tun daga lokacin da ka gaisa da Abdallah ne abun ya same ka ba”

Sakina yai yasa hannun nasa ya rike fuskata.
“Ina kika je dazun?”

Na yi shiru.
“Ba gida kika je ba, na sani dominbda suka zo sun tambaye ki kuma Mama tace kin buga mata waya kina kuka, i suspect something fada min ina kika je? Don't lie to me”

“Magana nai da Abdallah....”

A take fuskarsa ta canja.
“As how?”

“Akan ciwon ka ne”

“Oh ya Allah, taya za ki je ki yi magana da shi? Kin san ko tunawa nai akwai son ki a zuciyarsa sai naji kamar na kone, akan me za ki je ki yi magana da shi? Lims why? Is not allowed ya ji muryarki ma ji drees dinki ma, gown ce fa sai mayafi Babe why?”

Ya karasa kamar yai kuka, hakan kadai ya isa ya karantar da ni irin zafin kishin da Ahmad yake da shi, so idan har zan zauna da shi dole nai tsaka tsantsan da rayuwarsa.2
“Saboda na san shi yai maka kofi, kuma da na masa maganar ya amsa min da cewar shi din ne, tun da yana jin haushinka na san dole zai maka, shiyasa na ce maka ba na asibiti ba ne, ya yi ma dan'uwansa kuma ni ma ya sha min”

“Ba kofin ya dame ni ba, maganar da kika yi da shi ta dame ni, Allah kadai ya san abunda ya ce miki kila ma yace Halima ina son ki”

Na dan zaro ido.
“Aa be ce ba fada fa mukai da shi”

“Fada did he touch you”

“Oh oh No ba irin wacan fadan ba, fada na baki”

STORY CONTINUES BELOW
Ture ni yai daga jikinsa.
“Daga ni dan Allah”

“I'm sorry, amman na damu da halin da kake ciki ne”

Ya fada ina kada kafata domin tafiyar abu nake ji kamar ƙuda, ina jijjiga kafar na ji abu ya fado mai nauyi, saurin mikewa nai tsaye sai ganin kunamu nai har uku a inda kafafuwana suke, ban san lokacin da na daka tsalle na dale saman gadon ba ina ihu.

“Ka gani ko? Ya fusata da ni shine yai min kunamu nan”6

“Shiiiiiiiiiiii karki bari Hajiya ta ji maganar nan”

Ya fada yana rufe min baki.
“Shiyasa na fada maka cewar ciwon hannunka nan ba na asibiti ba ne, ayi maka addu'a zai fi sai ka mu sauki”

Na fada kamar zan fashe da kuka, jana yai jikinsa ya rumgume.
“Amman kin san yanzu an riga an gama shirya komai Hajiya ba zata yarda a fasa ba, kuma zuwan ma yana da amfani ko ba kuma hakan zai kara tabbatar da maganarki kuma Hajiya ba zata zargi komai ba”

“Amman taya za a samu maganin kofi a asibiti? Ahmad kai tunani mana”

“Okay fine zan yi magana da Hajiya sai nace mata a hada da addu'a hakan ya miki?”

“Eh ni ma kuma za ki rika maka fatiha kafa bakwai kullum da safe a ruwa kana sha idan zaka iya shan yawuna”

“Hmmmm har abunda ya fi yawunki ma zan iya sha, kin san minene”

Ya fada yana shinshinata tare da dora hannunsa saman cinyata.
“A a bana son sani”

Sai yai murmushi ya sauka saman gadon ya dauki takalminsa da hannunsa na hagu ya kashe kumamun dake ta yawo a cikin dakin sannan ya dawo ya zauna a inda nake yana kokarin kai hannunsa kirjina aka tana kofar da sauri na dauki mayafina na rufe kaina shi kuma ya dauke hannunsa daga jikina.
Yunus ne ya shigo rike da ledodi a hannunsa, after sun gaisa da Ahmad ya gaisa da ni sai kuma ya soma zolayata.
“Amarya ashe ashe ba mu sani ba....”

Wani kallo Ahmad yai min hakan yasa ban biyewa wasan da yake min ba.

“Yunus ka fa san ni bana son wasa da iyalina please take note”

The way da yai masa maganar babu wasa ko kadan a tare da shi, sai dai hakan be hana Yunus din yin dariya ba.
“Daman na zo ne na dauke ta ayi mata hoto Hajiya tace a shirya mata komai da ita za a je”

“Ban gane ka dauke ta ayi mata hoto ba? Ta dai baka hotonka karami ko?”

“Ba shi kadai ba ka san za a mata passport”

“Okay kuma kai zaka kaita ayi mata”

“Alhaji bana da matsala idan kai zaka shige gaba ayi mata komai, yanzu dai ya jikin naka?”

“Al-hamdulillah zan mata komai”

Ya fada yana kallona. Sun dan dade suna fira kamin yai mana sallama ya tafi. A lokacin ne na zuba mana abincin a plate daya ni da shi, be wani ci sosai ba hakan yasa nima na ji ba zan iya ci ba, ya bukaci na hada masa tea.

“Shiyasa ka rame baka cin abinci”

“Sai na samu lafiya zan ci abinci na koshi na more”

“Ba gashi na zuba maka yanzu ba ka ci ba”

“Ba wannan abincin ba, wacan abincin wanda aka dade ba a hadu ba, kuma na yi marmari da yawa”2

Murmushi nai ba tare da na kalleshi ba na cigaba da hada masa tea, da na kawo masa masa be karba ba sai yace na bashi da kaina, haka na rika ba shi tea kamar wani karamin yaro.
STORY CONTINUES BELOW
“Sha mana”

Na kurba kadan na bashi ya sha, bayan ya gama mukai sallah isha'i. Ban tashi daga saman carpet din ba sai ga Hajiyarsa ta shigo tana tambayar ko akwai abunda muke bukata.
“Sai dai ko shi ni ai gidan zan tafi”

“A a nan za ki kwana, wannan kuka da kuka min dazun idan kika je gida ai sai ki yi mafarkin kukan kuma”

Ta fada tana murmushi ni kuma nai kasa da kaina kunya ta rufe ni, Ahmad kan dariya yasa kamar ba shi ba.
“Ashe dai ana so na”

Kasakasa na wasa masa harara. Sai Hajiya tai murmushi.
“Allah dai yai muku albarka kuma ya ba ka lafiya ka koma gida cikin iyalinka”

Daga ni har shi muka amsa da amin, sannan tai mana sallama ta fice. Duk yadda na so ya kwanta saman gadon ni na kwanta kasa sai yaki, ala dole sai dai mu kwanta saman gadon a tare ko kuma shi ya sauko kasa mu kwanta.
“Gadon ai ba zai dauke mu ba”

“Ai ba dole sai mun wadata ba, ko kuma mu kwanta kasa”

“Ya za'ayi kana rashin lafiya ka dawo kasa ka kwanta?”

“Kin san dai ba zai yiyu mu kwana daki daya kuma a daban daban ma wannan ai haramun ne ma”

“Inji wa?”

“Inji ni”

Ya nuna kansa, ban san lokacin da na saka dariya ba. A dolen dole muka kwanta kasa ni da shi, muka lulluba da Bedsheet daya yadda ya rumgume ni a jikinsa yana shafa ni kai ka rantse da Allah ba ciwo yake ba.
Da asuba sai da na dumama masa ruwa yai wanka ni kuma na shiga nai alwala ko da ya fito na gama sallah na gaishe shi na shimfida masa carpet din yai sallah bayan ya gama na karanta masa fatihar ya sha sannan na hada masa tea.
  Misalin bakwai da wani abu direbansu ya kawo mana breakfast ba laifi nan ma da na zuba mana ya ci wata kila saboda mun ci tare ne ko kuma dan na yi magane jiya yasa yau ya ci oho. Sai tara da wani abu mahaifiyarsa ta shigo, ni kuma na fita na basu waje. Ina tafiya wayata tai kara alamar shigowar sako, number Abdallah ce.
“Ina fatar mijin da kika aura ya rike ki amana Halima, i wish you all the best
....”9

Shine abunda ke rubuce a cikin sakon, ban miya sa ba sai duk na ji wani iri. Har na koma dakin jikina a sanyaye yake.
“Na yi magana da Hajiya akan ko a daga tafiyar nan har gaba sai ce ba zai yiyu ba, amman dai ta aminta za a saka da addu'a din”

Ban ce masa komai ba na hau saman gadon na zauna na dora kaina sama wuyansa.
“Babe are you okay?”

Na kalleshi.
“I'm fine, Allah ya baka ikon rike ni amana”

“Amin”

Ya sumbaci goshina.

“Ba zako taba kuka da ni ba In-Sha-Allah i love you so so so much”

Ya fada try to hug me with both hands.
“Baka jin ciwo ne?”

“Da sauki dai gaskiya”

Murmushi nai na rumgume shi. Ban dauka da gaske yake ba har sai da muka je tare da shi aka min komai na tafiyarmu a yadda nake ganinsa na jidadi domin baya nuna alamar ciwon ko da akwai ma yana boye min, domin ya fada min duk bayan awa uku sai hannun ya taso masa da ciwo amman yanzu kam Al-hamdulillah.
Tare da shi da direban da ke jan mu ya sauke ni kofar gida, sannan shi kuma ya wuce. Da na shiga gida sai Hafiza ta rika zolayata kamar ba kanwata ba iskanci kala kala ko kunyar Mama da Inna bata ji, ko da yake daman can Hafiza ba wata doguwar kunya ce da ita ba. After na yi wanka na canja tufafin jikina ina gyarawa su Amal kayansu Inna ta shigo tana tambayar wai da gaske ne taji a gurin mama cewar da ni za a tafi.

“A a aiko hakan yayi Allah ya bashi lafiya”

“Amin”

“Inna”

“Na'am”

Har ta juya na kirata ta juyo.

“Dan zauna dan Allah”

Ba musu ta zauna saman katifar da muke bachi, a nan labarta mata abunda nake zargi a ciwon Ahmad da kuma a abunda ya faru tsakanina da Abdallah a maimakon ta yaba min sai ta rufe ni da fada.
“Sakaryar banza sha sha ba, marar tunani, komai Abdallah yai miki kar karki manta dan'uwanki ne kuma saboda yana son ki yai, ai ko a munafurce mutum ya nuna maka kauna ya fi wanda ya fito kirkiri yace baya son ka”2

“Amman Inna shine fa yai masa wannan kofin”

“Idan shi din ne ai sai ki bishi da lalama ba da hauka ba, Abdallah ya gama miki komai a rayuwarki Halimatu be cancanta ki saka masa da wannan ba, ke dai kan baki da tunani sam sakarya kawai”

A fusace ta fice ta bar dakin ni kuma sai duk na ji babu dadi, na rasa abunda zan yi na ji sanyi a raina na rasa tunanin da zai nuna min na yi daidai ko akasin hakan.


ABDALLAH POV.
Tun da Hajiya tai furucin nan sai ya ji kamar an zare masa rai a cikin jiki, har lokacin kuma ya kasa ganin laifin Halima, iya abunda yake tunani Ahmad ya kira mata abubuwa ne akansa ita kuma ta yarda shiyasa ta zo har cikin gidan Hajiya tai masa kalamai marasa dadi.
Sai dai daga lokacin da Hajiya tai masa furucin cewar ko bayan ranka ya auri Halima bata yafe masa ma ya cire zancen aurenta ya aje a gafe, hakan kuma ba zai saka kaunarta ta goge a zuciyarsa ba, sai dai yana da yakinin idan ba Halima ya aura ba ba zai taba samun cikar burinsa ba na haihuwar da namiji, a iya kwallafa rai ya kallafa mata rai da zato da kuma tunanin idan ya aureta burinsa zai cika na haihuwa da namiji kuma zai samu damar kusanci da abar son sa.2

“Yanzu na gane ba laifinta ba ne, har da naka kana da son ka Abdallah taya zaka runtse ido ka tsaya kai da fata akan cewar sai ka aureta? Matar da dan'uwanka ya saka? Kuma dan'uwan naka ma twins brother dinka? Kuma yana raye? Bayan kasan bana son yarinyar nan, hakika na tsorota da lamarinka, idan har zaka ita cutar da dan'uwanka to ni ma zaka iya cutar da ni”

“Subhanallahi Hajiya wace irin magana ce wannan? Abdulhamid shi ya fara cutar da ni, domin yayi min kofin ba zan taba haihuwar da namiji ba, kuma Hajiya kin san yadda nake son namiji, yana daya daga cikin dalilin da yasa nake son na auri Halima”

“Kum illata kanku kun cutar da kanku, amman kai kafi cutar da dan'uwanka, ko da baka haifi namiji ba ai kai ka yi auren har ka haihuwa? Shi fa? Dubi inda ya kare yanzu da yana ko ya ce da ban kalli yar na ji sanyi ba? Amman damuwarsa bata dame ba ka, kai neman da namiji kawai kake? Babu ruwanka da matsalarsa, kana kallon yadda yake ta fafutukar neman magani amman baka taba tausaya masa ba Allah ya wadaranka Abdallah, ka so matar aure, kuma matar dan'uwanka saboda selfishness reasons, Halima ce kawai mata a duniya? No saboda ka musguna ma dan'uwanka ne kuma kana ganin idan ka aure ta zata iya haifa maka namiji tun da last child dinta mace ce kuma tana haihuwar maza da mata ne, Wallahi karya kake kai baka isa kai abunda Allah be yi ba, komai kofin ka ba zaka iya yi wa kowa abunda Allah be masa ba, ashe ba laifin Halima ne kawai ba har da kai, ta yi tunani a lokacin da ki aurenka ta auri dan'uwanka ko ni ce haka zan aikata domin kai abun tsoro na, ka maida kanka wani kalar mutum dukanku kun zamar min wasu iri”1

Ta karasa tana fashewa da kuka, sai yai sauri sauka daga saman kujerar da yake zaune ya matsa kusa da ita ya kama hannayenta yana hawaye.
“Hajiya dan Allah ki yi hakuri, Wallahi na bar zancen Halima har abada, kuma In-Sha-Allah zan nemi maganin kofin zan karya shi, dan Allah karki kuka saboda ni”

Kawarda fuskarta tai tana share hawayenta.
“Da bakincikinka zan ji ko da na dan'uwanka? Tun jiya na kasa bachi saboda abunda na ji, na rasa wane kai din wane iri ne?”

“Zan canja Hajiya i promise you this”

Ya fada yana kokarin kwantar mata da hankali.


Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 10 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...