DR TAHEER CHAPTER 6 BY UMMU ASHRAF - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DR TAHEER CHAPTER 6 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 6 BY UMMU ASHRAF

- - Post a Comment

DR TAHEER CHAPTER 6 BY UMMU ASHRAF              Www.bankinhausanovels.com.ng 


Yana gama rufe kofan ya juya tareda komawa cikin dakin..ya zauna kusada ita..fuska a tsuke yace"fadamin dalilin da yasa kike guduna baby..ko tsanar da kikamin ne yasa ko ganina baki sonyi"...Layla ta girgiza kai da sauri..har kwalla ya ciko idonta...Taheer ya sake hade rai yace"karki kuskura kimin kuka..kinsan banaso"..aiko ta hadiye kukan nata tareda Kai hanu tana goge hawayen dake kan fuskanta...yasa hanu tareda riko nata..idanunshi a kanta yace"ki fadamin baby..baki son ganina ne in dena zuwa inda kike"...Layla da kuka ke Shirin kufce Mata tace"ba haka nake nufi ba daddy..kawai dai"..kmr zata fada sai Kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya...yasa hannu yai cupping face dinta ya sake cewa"kiyi mgn baby..dare na karayi"...Saida ta lumshe idanuwanta snn tace"ni kunya nakeji daddy..Kuma inajin tsoro"...yai shiru na tsawon secs yana kallonta..sai can Kuma ya nisa yace"meyasa kikejin tsoro na Kuma..kina tunanin zanyi maki wani abun ne"...batace komai ba sai hawaye da takeyi...ya matso da fuskanshi ya hada da nata..hancinshi na gogan nata.. idanunshi shima a lumshe yace"idanma kina tunanin zanyi maki wani abun ne baby to ki dena..bazan taba yi maki abunda bakiso ba..I promise babu abinda zai shiga tsakanina dake sai da amincewarki..am not after that baby..am after your love..so ki dena jin tsorona ki saki jikinki dani don Allah"..Layla da idanunta ke lumshe har yanxu..tace mai"toh daddy"..ya dago fuskanshi yana share Mata hawaye yace"promise me daga yau baki kara guduna"...Layla ta saki murmushi snn tace"I promise"...yasa hanu ya janyota jikinshi sosae..idanunshi kan lips dinta da sukayi ja as a result of kukan da tayi..murya can kasan makoshi yace"saura kunyar..bari in cire maki itama kinga saik...bai karasa mgn ba Layla tai saurin dora hanu kan bakinshi dake gab da hadewa da nata...kirjinta na sama da qasa tace"shima na denaji daddy..bazan karaba"...wani malalacin

murmushi ya saki yana kallonta yace"are you sure baby..da ki bari kawai indan rage maki ita"...ta sake kai hanunta bakinshi tana girgiza kai kmr zatasa kuka tace"Allah na dena daddy..kayi hakuri pls"...Taheer yasa hannu ya sake manne ta da jikinshi yana smiling yace"na hakura my baby..amma daga yau duk kika sake cewa kunyana kikeji sai nayi..kin yadda"..ta daga mai Kai a hankali...ya dagota daga jikinshi yanata kallonta yace"alright na gode sosae baby..I love you"...Layla ta sake fadawa jikinshi tana murmushi..ta bude baki zatace I love you too sai Kuma ta maida bakin ta tsuke da sauri..murya can kasa tace"nayi missing dinka sosae"...ya dagota tareda kama cheeks dinta yace"and I missed you more...yanxu tashi kije ki kwanta tunda mun gama kar ummi ta farka taga bakya nan"...Layla murmushi ta saki data ayyano kawai ace suga ummi a kansu ynxu..ai tasan ba daddy ba ita kanta Allah ne kadai zai rabata da ita.

Taheer ya fara mikewa itama ta mike..ya kama hanunta suka fita daga dakin..ya rakata har kofar dakin ummi tareda yi Mata peck a goshi snn yace daita"sweet dreams"...tana murmushi itama ta gyada kanta tace"Allah ya tashemu lfy...Yana tsaye yana kallonta har ta bude kofar ta shiga..shima ya juya a hankali zuwa part dinshi...har ya fara missing dinta wlh..Allah dai ya dorashi kan ummi ta bashi matarshi su tafi gida abunsu.

+

Washegari ya kasance Monday..a ranar ne kuma Layla zata je school don fara registration dinta...ta gama shiri da wuri..tana zaune parlor itada umma Taheer din ya shigo...bayan sun gaisa da umma yace"baby I hope dai kin gama shiryawa don tafiya zamuyi yanxun nn"...Layla ta mike tsaye tana cewa"na gama tun dazu daddy..Ina kwana"...ya sakar mata smile snn yace"lfy qlou..how was ur night"...tace"Alhamdulillah"...Taheer ya dubi umma yace"ummi bata fito bane"...umma bata kaiga yin mgn ba ummin ta fito daga dakinta sanyeda hijabi..ta karaso parlon tana duban Layla tace"kin gama shiryawa ne"...Layla tace"eh na gama"...ummi ta wuce gaba tana fadin"to sai ku fito mu tafi"...Taheer ya wara idanun sosae yace"ummi unguwa Zakije ne"...ummi ta dakata da tafiyar da takeyi ta juyo tana mai wani kallo tace"ban gane unguwa zanje ba... registration zan rakata tayi Mana..ko da tunaninka zan bari ku tafi daga Kai sai ita ne"...Taheer da mamaki ya cikashi da kyar ya iya bude baki yace"ban gane me kike nufi ba ummi"...Yana rufe baki ummi tace"Ina nufin tare zamuje Taheer..haka kawai in bari ka fita da 'yar mutane kaje ka aikata abinda bashi knn ba..yanda ka lalace din nn ai bazan iya bari ka kebe da yarinyar nn ba wlh..Kai ba abin yadda bane"...Taheer ya dafa goshi sbb takaici ko mgn ya kasayi..idan yaso karban hakkinshi ne wajen Layla wlh yasan hanyar da zaibi ya karba Kuma ba tareda duk sun ganeba..saidai bayan abun ya faru su fahimta..amma meyasa ummi kemai haka for Goodness sake...ita kanta Laylan wnn karon bataji dadin abinda ummin tayi ba..ai yace mata shi ba abinda zaiyi mata meyasa ummi zatace haka...itama umma tana zaune ta zubama sarautar Allah ido..tana duban 'yar uwar tata tace"haba Yaya ya zakice haka... don Allah ki kyalesu suje su dawo ni nasan babu abunda zaiyi Mata wlh"...ummi ta saki wani murmushi tace"ai dama bazaki ganiba Aisha tunda bakison laifin danki"...umma ta mike tareda kamo hanun ummi suka zauna snn tace"don girman Allah Yaya kiyi hakuri ki barsu suyi tafiyarsu..ai yaji abinda kika fada Kuma nasan ko Yana da niyyan yin wani abun yanxu ya hakura..kiyi hakuri kar kice zaki bisu don Allah"...ummi tai shiru kawai kmr mai tunani...sai can Kuma tace"to ki gargadesa wlh..kar ya kuskura ya aikata abinda ba shknn ba don ranshi zaiyi mummunan baci"...da sauri umma tace"bazai ma aikata komai ba da izinin Allah"...ta dubi Taheer dake tsaye kmr gunki tace"wuce ku tafi Taheer..Allah ya bada saa"...Taheer kmr abinda yake jira knn ya fice daga parlon...itama Layla ta mike a hankali tabi bayanshi..cikin ranta ko dariya draman ummi ya bata wlh..wai ba abun yadda bane😹

STORY CONTINUES BELOW

Suna fita bank suka fara zuwa..sunyi saa Kuma basu samu layi sosae ba..nanda nn ya biya kudin daga nn Kuma suka wuce school.


Ya taimaka Mata sosae..duk abinda bata ganeba zai Mata bayani snn inda ya kamata suje tare ya rakata inda Kuma ya kamata taje ita kadai sai ya jirata daga waje...basu suka bar cikin Base ba sai around 3...Kai tsaye ya maidata gida shi Kuma ya wuce clinic.


Around 9:30 ya dawo gida..bayan ya kammala duk abunda yakeyi..sai ya dauki chocolates daya siyo Mata tun ranan da ta dawo ya nufi part din nasu...gaba dayansu suna parlor suna kallo..ya nemi wuri ya zauna shima snn ya gaisa da iyayen...Layla dake makale kusada ummi tace"daddy sannu da dawowa"yai Mata murmushi kawai kafin yai mgn yaga an jefo takadda da biro gabanshi..ya kallesu snn ya daga Kai ya kalli daga inda suka fito..ummi ce ta wurgo mai su idanunta a kanshi tace"rubuta sakin yarinyar nn ka bani yanxu..ai dama na ce maka idan bata sonka bazaayi Mata dole ba"...Taheer ya shiga bin ummin da kallo baki bude..he's totally speechless..kmr daga sama yaji Layla tace"ummi ni nace maki bana son zama dashi ne"...ummi ta juya tana kallon Layla tace"yo ai ba saikin fadaba 'yar nn..alamomi sun nuna ba sonshi kike yi ba"...tana rufe baki Layla tace"nidai ba cewa nai bana sonshi ba ummi..ni ban taba ce maki bana sonshi ba"..ummi ta shiga salati tana tafa hannaye tace"Ni Zaki bama kunya Layla..Ina kokarin in kwatar maki 'yancinki shine zaki watsamin qasa a ido"...itadai Layla bata sake cewa komai ba..ta turo baki kawai tareda dauke kanta gefe..umma dake kokarin yin dariya tace"kinga Yaya sai ki dena shiga harkansu yanxu..tunda ta nuna tanasonshi sai ki bashi matarshi suyi tafiyarsu can gidansu..muma mu huta"..ummi na girgiza kai tace"ko zan bashi yarinyar nn sai yayi Mata lefe wlh..duk wani abu da yasan anayi ma mace kafin a aureta sai yayi ya kawo..snn sai ayi biki ya dauki Matarshi su barmin gida"..Taheer daya kame kmr gunki sbd abubuwa biyu da suka sashi farin ciki da Kuma mamaki...na farko shine bai taba tunanin jin mgnr daya fito daga bakin Layla ba..knn hakan na nufin itama tana sonshi..na biyu Kuma dayaji ummk tace zata bashi matarshi..zai iya cewa rabonda yaji farin ciki irin wnn har ya manta...da sauri ya karaso inda ummin ke zaune ya zauna kusada legs dinta tareda Dora kanshi a kan laps dinta..ya lumshe ido yanajin wani extraordinary farin ciki har cikin zuciyarshi..murya can kasa yace"thank you so much ummina..Allah ya saka maki da alkhairi..ummi Allah ya faranta maki kmr yanda kika faranta min..you are the best"..ummi na shafa kanshi itama tana murmushi tace"lallai sannu majnoon"..umma ma na dubansu cikin farin ciki tace"kwarai kuwa Yaya ga Layla ga Majnoon..Allah yai muku albarka gaba dayanku"... Layla da duk kunya ya isheta ta mike zuwa dakinta..gaba daya batasan ya akai ta saki zance haka ba..sai yanzu takejin kunyar mgnr data fada..ga Kuma su umma suma suna Kara sata jin wani kunyan...Taheer ya bita da kallo bayan ta shiga dakin..ya dago kanshi daga cinyan ummi yana dubanta tace"gobe zanyi miki transfer ummi..sai ayi duk abunda ya kamata"..ummi tace to Allah ya kaimu...yace"Ameen"..snn ya mike zuwa inda ledan chocolates daya shigo dashi yake..ya dauka idonshi na kan ummi yana nuna Mata ledan yace"ummi don Allah in Kai Mata"...Ummi tabi ledan da yake nuna Mata da kallo kmr zatace aah sai Kuma tace"Kai Mata Amma karka dade"..wani dadi ya sake kama Taheer ya nufi dakin nata yana"yanzun nn zan fito ummi"...Ummin tabishi da kallo kawai tana murmushi...Saida ya shiga dakin snn ta dawo da kallonta kan umma tace"Ina sane nayi abunda nayi fa Aisha..nasan da zaunar da ita akai akace ta fada tana sonshi ko batasonshi bai zama lallai ta fada ba..yanzu da nayi haka kinga gashi ko tambayan ta baayi ba ta fada"...Umma ma na dariya tace"Kuma wlh kinyi hikima Yaya..da tambayan nata akai zataji nauyin fada..amma yanxu kiga yarinya kai tsaye ta fada abinda ke cikin ranta..Allah ya musu albarka ya basu zamn lfy"...ummi ta amsada ameen snn tace"yanxu sai mgnr biki.. don gsky bazai yiwu ace bikin Layla guda banyi taron biki ba..dagashi sai ita suka ragemin don haka ya zama dole inyi gagarumin biki kafin a bashi ita su tafi"...cikeda gamsuwa umma tace"hakan ma yayi ai Yaya..Allah ya nuna mana lokacin"..umma tace "ameen zanyi mgn da Alh Adam inyaso sai a tsayar da lokacin bikin"....a takaice dai sun dauki tsawon lokaci suna cigaba da tattauna yanda bikin zai kasance.


Layla kuwa na shiga daki ta fada kan gado tanata sakin murmushi..batasan meke sata murmushi haka ba..kawai ta tsinci kanta cikin excitement...a hankali Taheer ya turo kofar dakin ya shigo...tana ganinshi tasa hannayeta ta boye fuskanta dasu..har yanzu Kuma bata bar smiling ba...shima da murmushi a fuskarshi ya karaso inda take ya zauna..Yana kallon yanda ta boye face dinta yace"baby kunyan ya dawo knn"...ta cire hanun nata da sauri tana girgiza kai tace"no daddy ba kunya nakeji ba"...ya sake sakin wani murmushin Yana kallonta..sai ya bude hannayenshi idonshi cikin nata yace"come here baby"...ba musu Layla ta fada jikinshi tamkar dama abunda take jira knn...Taheer yasa hannunshi tareda matseta gam a jikin nashi..yanajin kanshi tamkar wanda yake cikin gajimare can sararin samaniya sbd tsabar farin cikin da yake ciki...daidai saitin kunnenta yace"thank you so much baby..you really save my heart from exploding..da ummi ta dage saina sakeki baby da ban San Ina zansa kainaba..thank you so much love..I love you sosae"...wani irin dadi Layla ta sakeji ya lullubeta..kalamanshi means alot to her..tanajin dadinsu sosae ba kadan ba...yasa hannu tareda dauko ledan dake ajiye gefenshi..yasa cikin hanunta yana cewa"this is yours..idan akwai wani abun da kikeso just name it..zan fita in nemo mikishi ko menene"...Layla ta dago daga jikinshi tareda bude ledan taga tulin chocolates ciki..ta zare ido sosai tana kallonsu..batasan lokacinda ta sake hugging dinshi tace"thank you so very much Daddy"...Taheer na shafa bayanta yace"no thanks baby..yanxu ki fadamin abunda kikeso"...ta sake dago kanta tana murmushi ta girgiza Kai tareda fadin"I want nothing daddyna..wnn din ma is enough..I really appreciate"...yasa hannu ya kamo fuskanta tareda manna mata slight kiss kan both cheeks dinta.. followed by forehead dinta...ya kwantar da ita kan gadon tareda ja Mata duvet ya lullubeta snn yace"ba cewa nai ki sasu a gaba kice Zaki cinye lokaci dayaba..da kadan kadan zakina ci coz banaso ya baki matsala idan period dinki yazo"...haka nn taji kunyar mgnr daya fada..ta lumshe idanunta kawai ba tareda tace komai ba...yana jan dogon hancinta yace"alright zanje in kwanta..sai da safe"...ta bude idon da sauri tace"baka yimin addu'a ba ai"...Taheer ya Kara sakin murmushi.. actually Yana sane dama ba mantawa yai ba..kawai yanason yaji ko zatayi mgnr ne gashi Kuma tayi...a hankali ya karanto adduan tareda shafeta dashi..ya tofa both sides snn ya mike tsaye yace Mata"good night..have a wonderful sleep"...ta daga mishi Kai tana murmushi itama..shi Kuma yasa kai ya fita daga dakin ba don yaso ba...har lokacin Kuma su ummi na parlon sunata discussing mgnr bikinsu..bai sake zama ba yai musu sallama kawai ya tafi part dinshi..he have to pray ya godema Allah da yake daidaita al'amuranshi one by one.. Alhamdulillah Ala kullu Haal.


Kmr yanda ummi ta fada..sunyi mgn da Alh Adam kan bikin da take sonyi..ya kumayi naam da mgnr tata..snn sun tsaida bikin nan da 4 weeks..sbd sunaso su kammala duk abunda ya kamata kafin zuwa lokacin biki..and ita kanta Laylan tana bukatar tutorials kan abubuwa da dama da suka shafi zaman aure..don haka dole sunada bukatan enough lokaci.

Wannan kenan

The following day ya kasance Tuesday..Layla suka sake komawa mkrnta don akwai abubuwanda bata kammala ba...ba yanda batayi da Taheer kan ya tafi aikinshi idan ta gama zata kirashi Amma Sam yaki tafiya..yace Mata zai jirata tunda he's on evening duty.Ganin time din sallah yayi Layla ta nufi female Majid tayi alwala snn ta shiga ciki don yin sallah..bayan ta idar tana addu'a wata yarinya da ko zata girmeta bai wuce da 2 or 3 yrs ba tazo ta zauna kusa daita..Saida ta shafa adduan snn ta dubi yarinyan dake kallonta da murmushi..ta mikama Layla hannu tace"sunana Hanna Umar Faruk"...Layla ma murmushin tayi snn ta Mika Mata nata hanun sukayi musabiha tace"Maryam Taheer Jakada"...yarinyar na gyada Kai tace"it's nice meeting you Jakada"..."nice to meet you too"..Layla ta fada itama tana murmushi...Layla ta fara mikewa..itama Hanna ta mike..suka jera a tare suka fita daga masjid din..Hanna tace"na ganki dazu a student affairs office..inata so in maki mgn Kuma sai na nemeki na rasa"...Layla tace"eh na fito inyi sallah ne"...Hanna na daga Kai tace"hakane..amma naga kmr course daya ma zamuyi dake..medicine right?...Layla tace"exactly..ashe course dinmu daya"...tace"yea and I hope zamu zama friends"..still Layla na murmushi tace"InshaAllah"...kafin wani ya sake mgn wayan Hanna dake hanunta ya fara ringing..ta dubi Layla da sauri tace"my Habibi is here to pick me up..kisamin number dinki sai mu na gaisawa kafin a fara lectures"...ba musu Layla ta amsa wayan da take Mika Mata..tasa Mata digits dinta snn sukai sallama ta tafi...itama ta karasa inda ta barshi sukayi gida Kuma.

+

Bayan Sati biyu...

Shirye shirye sosae su ummi suke ba kama kafar yaro...amarya na Shan gyara sosae don takanas aka dauko expert akan harkan gyaran amarya taketa kimtsata ciki da waje..lokaci guda ta Kara haske tayi wani irin kyau..skin dinta sai glowing yake...lokacin da suka fara lectures kullum Taheer ke kaita school..inta gama Kuma ya maidota gida..daga baya ummi ta hanashi kaita wai bata yadda dashi ba..haka kawai yanda yake rawar kan nn gani take ba abunda bazai iya aikatawa ba... dukda Taheer baiso ba amma haka ya hakura..ta wani bangaren shima taimakonshi akai..don duk suka kebe da ita wasu bakin al'amura yakeji na zagayawa cikin systems dinshi..yanda take glowing sai yayi da gaske yake iya controlling kanshi..ko makarantan ma da hijab dinta take zuwa har qasa.


Kmr yanda Taheer yace zaiyi musu transfer hakan yayi..ba bata lokaci Kuma suka fara siyen very unique and expensive kaya da sukasan zaima Layla kyau...duk sukayo siyayya umma zata janyo Taheer dakinta ta nuna mai kayanda suka siyo..haka zaita dubasu Yana comments.


Yauma suna duba kayan da suka siyo sai gashi ya shigo dakin...umma tace"yawwa karaso kaga kayan da Muka siyo"...ba musu ya karasa inda kayan suke a baje..umma ta shiga nuna mai inners din da suka siyo dazu...Taheer ya dinga dagawa yana kallonsu daya bayan daya..Saida ya gama kaf snn yana duban umma yace"wadan nn sun Mata kadan umma"...kafin umma tayi mgn ummi tace"ya zakace sunyi Mata kadan..sai kace wata uwar mata ace wnn breziern suyi ma Layla kadan"...ya sake cewa"Allah ummi sun Mata kadan..Kuma ki kai Mata ta gwada ki gani"...ba musu ummi ta dauki bra din ta fita dashi...ta samu Layla na karatu a dakinta..ta Mika Mata bra din tace"shiga bayi ki gwada yanxun nn inaso inga ko ya miki daidaine"...Layla batace komai ba tasa hanu ta amsa..ta shiga bayi for some secs sai fito..ta mikama ummi bra din tace"ummi yamin kadan wlh..ko shigana ma baiyi ba"...ummi da mamaki ya isheta ta karba kawai snn ta fice daga dakin...cikin ranta tana tunanin anya ko Taheer ba lalube yar mutane yakeyi ba..inba hakaba ta ina yai Mata saninda har ya haddace size dinta haka...tana komawa dakin ta mikama umma bra din tace"baiyi Mata daidan ba kuwa Aisha..yayi kadan"..sai Kuma ta juya ga Taheer tace"ka Fadi tsakaninka da Allah Taheer..anya ba lallabowa kakeyi cikin dare kana lalube 'yar nn ba kuwa"...Taheer da mgnr ummi ya bashi dariya da Kuma kunya yace"Kai ummi dn Allah..wani irin biyo dare Kuma ana zaune qlou"...a hasale ummi tace"yo biyo dare mana Taheer..ya koni da nake tareda ita ko yaushe ban iya haddace size dinta ba sai Kai da bama tare kuke kwana ba"...shiru kawai Taheer yai yana murmushi...umma ma mgnr ba karamin dariya ya bata ba..ta hade kan breziers din tareda Mika mai tace"gashi nn..zan baka receipt din inda Muka siyo sai ka maida musu ka dauko daidai size din nata..tashi ka tafi"...da sauri ya mike kmr jira yake ya fita daga dakin...umma na duban ummi tace"Kai yaya ai saiki bashi kunya..nasan ba wani lallabowa da yakeyi wlh..kawai dai Sabon da sukayi ne..kuma fa Yaya naga shi da kanshi ma yana siyo Mata inner wears..so ba wani abu bane dan ya haddace size dinta"...ummi dai bata tanka ba amma cikin ranta gani take da kyar idan ba lallabawa yakeyi wurin Layla ba😹

STORY CONTINUES BELOW

Bangaren amarya Layla kuwa zaace ba wani shirye shirye da takeyi Banda wanda ake Mata...kullum tana zuwa school abunta.


Yauma kmr kullum sun gama lectures dinsu gaba daya..suka fito don tafiya gida itada new friend dinta Hanna..sun saba sosae da ita kasancewarta mai surutu da Kuma saurin sabo..sai daga baya Hanna take fadama Layla cewan watanninta uku da aure...Layla tasha mamaki kam don bata taba tunanin Hannan tanada aure ba..snn bata taba nuna mata cewa itama tanada auren ba.


A hankali suke tafiya zuwa parking lots..don tasan maybe driver na can yana jiranta..itama Hanna maybe habibinta yazo yazo...kmr ance ta daga kai sukayi ido hudu dashi..yana jingine jikin motarshi ya rungume hannayenshi a kirji...ta wara ido sosae tana murmushi..snn ta kama hanun Hanna tana fadin"zo muje ki gaisa da daddy na"...yana kallonsu har suka karaso inda yake...tace"daddy sannu da zuwa...sai Kuma ta nuna mai Hanna tana fadin"meet my new friend..sunanta Hanna"...Taheer dake murmushi har yanxu yace"sannunki Hanna"...itama tana fara'a tace"daddy Ina yini"...ya amsa Mata"lfy Lou ya school"..tace"Alhamdulillah daddy"...ta dubi Layla tace"Jakada bari in karasa..ga Habibi can na hangoshi yana jirana"...Layla na daga Kai tace"alright bye..sai munyi waya"..itama tace daita"ba bye"snn ta juya ta tafi..Taheer ya bude Mata mota yana kallon yanda take sheki..Saida ta shiga ya rufe kofar snn ya zagaya shima ya shiga...yai ma motan key suka bar wurin.


Har suka danyi nisa a tafiya bai dena juyowa yana kallonta ba...she looks so takeaway..ji yake kmr daga nn kawai ya wuce da ita gidanshi...kasa hakura yai ya gangara gefen titi yai parking...ya juyo gaba daya Yana kallonta da idanunshi da suka canza launi..ya Mika Mata hanunshi alaman she should grab it..batai musu ba kuwa ta dora hanunta Kan nashi..ya janyota jikinshi sosae tareda dorata kan laps dinshi..ya matseta jikinshi yana sauke ajiyan zuciya a jere a jere...Layla kuwa lumshe idanunta tayi lub..tanajin yanda bubuwa da dama ke Kai kawo a kwakwalwarta..kirjinta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri...murya can kasa Taheer yace"baby I love you so much wlh..ni kaina ban San irin sonda nake maki ba..promise you'll never leave me har karshen rayuwata plss..idan kika barni baby mutuwa zanyi wlh"...Layla taji idanunta har sun ciko da hawayen tausayinshi..ba karamin tausayi yake bata ba yanxu..ta dago daga jikinshi kanta a kasa tace"InshaAllah bazan taba barinka ba daddy"...Taheer ya saki murmushin jin dadi snn ya manna mata peck a forehead dinta...da kanshi ya maidata seat dinta..har yanzu bai dena kallonta yana sakin murmushi ba..saida yaci gaba da driving snn yace"ummi fa bata san na taho daukanki ba..she was saying wai bata yadda dani ba..har ta turo driver umma tace kar yazo ni inzo"..ya kare mgnr still da murmushi..kafin ya sake cewa"umma really is a life saver u know..ba don itaba Allah nasan da yau bazan iya bacci ba..kawai mutum da matarshi duk anbi an hanashi ganinta"...ya karasa mgnr tareda pouting lips dinshi...Layla dake kallonshi ta saki dariya kawai tana girgiza Kai..


Bayan sun isa gida..yana gama parking ta shiga kokarin bude motan zata fita...Taheer yasa lock tareda komawa yai relaxing kan kujeran da yake.. idanunshi na kanta yace"ai ban sallameki ba"...Layla ta dena kokarin bude motan da take tareda komawa ta zauna itama...yadan daure face dinshi yace"baby banason kina zuwa makaranta a haka wlh..banaso"...Layla ta bude idonta sosae tace"hijab dina ya kai har qasa fa daddy"...tana rufe baki yace"to kuma fuskanki da kike yawo dashi a haka kowa na kalla fa..bakisan yanda kika koma ba koh"...Layla ta sauke ajiyar zuciya a hankali kafin tace"shknn..daga gobe zan fara sa niqab idan zan fita"...Taheer ya saki smile yace"good girl..May Allah bless you"..tace"Ameen Ameen..yanzu xn iya tafiya"...Saida ya cire lock din dayasa snn yace"yes ma'am..ki ajiye wayanki kusa..zan Kira".."toh"tace dashi snn ta bude motar ta fita..shi Kuma ya bita da kallo yanajin kmr ya bita cikin gidan..he can't get enough of her at all..son da yake mata is different.

Bangaren Hajia Anty Sameera kuwa..tayi bincike kmr yanda tace zatayi..an Kuma tabbatar Mata da Taheer ba kowa ya aura ba face Layla..wnn yarinyar me kama da aljanu..yarinyar da taji ta tsaneta dama from d beginning..ranar taci kuka ta godema Allah..don takaicin wai duk fadin duniya Taheer ya rasa wa zai aura sai wnn 'yar..wnn abar da ko ita kanta ta kusa haifanta...an tabbatar mata da yarinyan Base University take..snn bata tare gidan Taheer ba har kawo yanxu..wnn dalilin yasa ta kudiri aniyar shiga tsakaninsu nor matter what.

Wannan kenan..

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sati guda...

Zuwa yanxu abubuwa kadan ne basu kammala ba na shirye shiryen biki...Nafisa ma zata taho cikin satin nn..su kuma yaran sai gab da biki zasuzo tareda mahaifinsu.


A bangaren ummi ta dage kan lallai saita koyama Layla girki..duk ta dawo daga school da wuri dama zaa turata kitchen ace sai tayi girki..


Yauma tun safe ummi ta turata kitchen wai Mama hawwa ta koya mata yanda zatayi tuwon shinkafa da egusi soup...a karo na uku Layla ta sake fitowa daga kitchen hanunta rikeda ludayin miya tace"ummi don girman Allah kiyi hakuri..wlh karatu nakesonyi"..ummi tai Mata banza tana cigaba da ware cards din biki da aka kawo Mata..Layla har ta juya zata koma kitchen din taji Taheer yayi sallama..sai ta fasa komawan ta tsaya...shi Kuma ya karasa kusada umma ya zauna snn yace"umma gani"...ta miko mai cards din dake gefenta tana cewa"invitation cards ne dama aka kawo daxu..shine nace bari in baka ko zakayi inviting friends dinka..wnn na dinner ne..dayan Kuma na mother's Eve..kamu na Mata ne kawai so ba sai an baka ba"...Taheer ya rike cards din da take miko mai a hanunshi..idanunshi kan Layla da har yanxu ke tsaye da ludayi a hannu yace"lfy kuwa"..da sauri ummi ta dago tana dubanshi tace"lfy Mana..dambe ka samemu munayi da zata tambayemu ko lfy"...still idanunshi a kan Layla yace"baby me kikeyi a nan wurin"..wnn karon a kufule ummi tace"Kai wai Ina ruwanka da ita ne..girki nasata tayi..ko kana nufin haka zaa dauketa a kaita gidan nata ba tareda ta iya komai ba"...ummi na rufe baki yace"ummi indai don ni zaa koya mata girkin wlh na yafe...idan lokacin da zata koya yayi zata koya ai"...ummi na girgiza Kai tace"kasan wani abu Taheer..yarinyar nn dama da an likama wani ya aureta billahillazhi an cuceshi..yarinyar da bata iya komai ba sai shegen shagwaba kmr jaririya..amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane..sai ya manna maka kaje kayita fama da ita..dama ai ba wani ne ya lalata ba daya wuce kai..don haka ba Wanda ya kamata ya kwasheta sai kai din..sai kaje kaji idan dadi ne auran macen da bata iya girki ba"..Taheer da mgnr ummin ya bashi dariya..sai ya saki murmushi kawai yana cewa"eh naji koma menene ummi..ni ba girkinta na auraba..ita na aura"...ummi dai bata sake tanka shi ba..Yana duban Layla yace"jeki ajiye wnn abun a kitchen kije kici gaba da karatunki"...aiko da sauri ta koma kitchen din ta ajiye snn ta sake fitowa ta shige dakinta..umma dake sauraron draman nasu tana dariya tace"wai Kai haka ake rayuwa ne..ace duk wani abu daya kamata bazaka bari yarinyar nn ta koya ba..to idan bata iya girki ba kaine zakana zama kanayi muku girkin ko kuwa"...still Yana murmushi yace"sai in ringa siyowa umma..ko Kuma in dauki mai aiki da zatana yi mana girkin In biyata"...umma ta girgiza Kai tace"wato gak a majnoon koh..to ba gata kake yimata ba wlh..tun wuri ma in zaka canza ka canza"...bai sake cewa umma komai ba ya mike tareda ficewa daga dakin..ummi ta bishi da uwar harara tana dan rainin hankali kawai"😆


Yau Wednesday Layla sun fito daga class..ganin akwai sauran time kafin another lecture..suka nufi cafeteria don cin abinci itada Hanna...table daya suka zauna..Hanna na duban Layla tace"what will you like to have"...Layla ta fada mata abinda zataci snn ta bada order..

Bayan an kawo musu abinci sun faraci..sunadan hiransu jefi jefi..kmr daga sama sukaga mace a gabansu..a tare suka dago kawunansu suna kallonta..Layla ta zare ido sosae tace"Anty Sameera"..Sameera ta saki wani matsiyacin murmushi snn taja empty kujeran dake kusa dasu ta zauna...ta shiga bin Layla da wani kallo tana cewa"so kece kika shiga tsakanina da mijina koh"...da mamaki Layla ke binta da kallo..kafin tayi mgn Sameera ta sake cewa"let me give you this worning..daga yanxu..I mean as from today..ki fita harkan mijina..Taheer mijina ne ba naki ba..so kibar wani jin dadi don an aura masa ke a sadaka..idan Kuma bakiji Mena fada maki ba..wlh wlh kinji rantsuwar musulmi..baki isa ki zauna da doctor lfy ba..yanda kika sa ya fasa aurena sbd ke..kema baki isa ki zauna dashi matsayin miji ba..Taheer mijina ne ni kadai..Kuma babu wadda ta isa inyi sharing dinshi da ita"..da sauri Hanna ta mike tana fadin"Hey.. Hlow..wacece ke..who do you think you are da zakizo ki samemu haka kawai ki fara mana ihu a Kai..have you lost it..anya ko kinada lfy"..a fusace Sameera ta kalli Hanna tace"ba dake nake mgn ba..so stay away"..tana rufe baki itama Hannan tace"ko ba dani kikeba ai da aminiyata kike..yanxu qatotuwarki dake ko kunya bakiji ba..kixo kina fada da yarinya karama a kan namiji..wa yace kiyi sake har ta kwace maki shi din"...Sameer ta daga hannu zata Kai Mata mari kawai taji an rike hannun nata...Layla ta kama hanun Hanna ta shiga janta suka bar wurin...Sameera ta bisu da kallo zuciyarta na tafasa...Saida sukayi nisa da wurin sosae Hanna ta kwace hanunta tace"wai meye hakane Jakada..ya mace zatazo tana faffada maki maganganu Kuma kiyi banza da ita..snn ni da nake rama maki kin wani janyoni kin fito Dani daga wurin..what's wrong with you"...Layla batace komai ba..Saida ta samu wuri suka zauna snn tana kallon Hanna tareda dafa shoulder dinta tace"calm down mana babe..ni banga abun daukan zafi a nan ba"..Hanna ta ture hanun Layla dake kan kafadanta tana hararanta tace"ai bazaki gani ba dama..kawai mace tazo har inda muke ta raina mana hankali Kuma ki hanani ramawa...that aside..naji kmr tana mgnr kin kwace mata miji fa..Jakada kina nufin wai all this while kinada aure amma baki taba fadamun ba"...shiru Layla tayi na tsawon lokaci..batasan ta ina zata fara fada Mata cewa daddy is her hubby ba...Hanna ta dafa kafadanta tace"hlow..tunanin me kike Kuma"...Saida Layla ta sauke ajiyar zuciya snn ta shiga bata lbrin irin soyayyar da Taheer din ke Mata..alakar dake tsakaninta dashi..da yanda aurensu ya kasance da kuma shirye shiryen bikinsu da akeyi yanxu..da mugun mamaki Hanna ke kallonta tace"Amma gsky Jakada bakida kirki ko kadan..yanxu badon hakaba..da bazaki fadamin zaayi bikinki ba knn koh"..da sauri Layla na girgiza kai tace"wlh inata so in Fadi maki kawai bansan ta Ina zan fara bane"..ta bude bag dinta ta dauko cards da taketa faman yawo dasu ta Mika Mata tana cewa"take these..cards ne na gaba daya events din da zaayi..sun kusa sati cikin jaka na rasa ya zaai in baki..so ni waccan matar ma taimako na tayi"...Hanna tasa hannu ta amsa cards tana fadin"duk da haka baki kyauta min ba..amma kinsan wani abu..kwata kwata banyi mamaki da kikace daddy is your husband ba..don wani special kallo da naga yana jifanki dashi nasan dole Wanda akema tsanstar so akema wnn kallon"..Layla na murmushi ta girgiza kai tace"Hanna you are too much..dama sa mana iso kikeyi knn koh"...Hanna tace"no ba wani sa ido fa..abune da yake a fili..amma kinsan menene babe..ya kamata fa ki dage..ki kula da mijinki sosae..yanda kika samu yana maki irin wnn son..Nanda nn zaki mallake abinki a hannu..kinga ba ta yanda waccan witch din zata nemi shiga tsakaninki dashi"...Layla ta mike tareda kama hanunta tace"naji...yanzu ki mu tafi kar a fara lecture bamu komaba"...Hanna ta mike itama suka nufi hanyar clss dinsu tana cewa"gsky kina bukatn lecture akan yanda ake kula da miji Jakada..dole ma in baki sirrin yanda nake kulawa da Habibi na..shiyasa kikaga kullum Kara Sona yake"...Layla dariya kawai tayi tana girgiza Kai..ai Hanna sai a barta kawai..dama ya lafiyar kura..da can da batasan she's married bama kullum karatu take mata kan yanda zatai handling saurayi and everything..yanxu kuwa da ta san tanada auren ai sai inda manta ya kare..tasan idan aka fara Mata lectures din kmr yanda ta fada..har sai taji ya isheta ma gaba daya.


Yau saura kwana Hudu daidai a fara biki..gida ya fara cika da 'yan uwa na nesa...Nafisa ma ta dira...da yawa daga cikin family dinsu na kano ma duk sun hallara.

Da dare umma ta Kira Taheer kan yazo yaga kayan lefe..sun gama hada komai..don gobe ma idan wasu zasuje can gidan nashi..zaa tafi mata dasu...yana zaune umma nata aikin daga mai kayan yana kallo daya..ummi ta shigo dakin da sallama..ta dubi yanda umma keta nuna mai kayan sai tayi tsaki tace"yanxu Aisha da nace ba sai kin kirashi kin nuna mai ba Saida kika kirashin dai..idan sunje can karewan kallo ma a jikinta zata sa mai ya gani..to Kuma bai isaba sai an wani nuna mai kawai salon duk an gyara kaya a sake hargitsasu"..umma na ci gaba da nuna mai kayan tace"to Yaya mene laifi yanzu don an nuna mai..ai sai yaji dadi a ransa yaga shima yayi kokari"...a kufule ummi tace"au shine ma yayi kokari zakice..muda mukaita sintirin fita siyo kayan bamuyi kokari ba knn"..umma tace"ba haka nake nufi ba Yaya..kawai dai naga shima yayi kokarin bada kudi a wadace..kuma kayanda akai order wurin Amina Dubai duk ba shi yaje ya karbo su ba"...ummi tace"to ay shknn"..snn ta fice daga dakin...dakin Layla ta shiga tace Mata taje dakin umma itama wai taga kayanta..Layla tace"na riga na gansu ummi..ba sai na Kara ganiba"..ummi tace"ke kika sani dai..kema da baa maki gwaninta"tana gama mgn ta fice a dakin..Layla ta bita da kallo tana dariya..a fili ta furta"Hajia ummi rigima".

Taheer na gama ganin kayan dama part dinshi ya koma..tun safe yake son ganin Layla amma abu ya gagara..ga gidan ya fara cika da mutane da Kai tsaye dakinta zaije ya sameta wlh...bayan ya gama duk abubuwan da zaiyi..sai ya hau gado ya kwanta tareda daukan wayanshi ya shiga dialing number dinta...Layla na daki tana karatu call dinshi ya shigo..ta ajiye handout dake hanunta snn tayi picking call din...a daya bangaren Taheer ya wani narkan da murya Yana shafa tummy dinshi yace"baby am seriously sterving..ki kawomin abinci part dina dn Allah".. Layla ta zaro idanu kmr taga abun tsoro tace"daddy ummi bazata barni inzo ba ka sani"..tana rufe baki yace"ai ba cewa nai kije kice mata zaki kawomin abinci ba..kawai zuwa zakiyi kitchen ki dauki abincin sai ki faki idon kowa ki taho..kina zuwa zaki koma Allah ba wani abun zanyi maki ba..I just want to see you..yau duk mutanen nn sun hanani ganinki"...Layla dai tai shiru tana ayyana yanda zaai taje part dinshi ba tareda anyi noticing ba..a wani bangaren kuma tana tsoron abunda zai biyo baya idan taje din..ta fuskanci daddyn nn ba hakuri ne dashi ba..and bashi da kunya ko kadan...Taheer ya katse mata tunani da fadin"it's okay idan baki son zuwa baby..i won't force you..bari in fita waje kawai sai in nemi abinda zanc.."..tun kafin ya rufe baki tace"ai ba cewa nai bazan kawo ba daddy..zan kawo maka amma Ina zuwa zan wuce"..yace"na yadda baby..kiyi sauri Ina jira"..Yana gama fadin haka ya kashe wayar tareda ajiyeta nn gefe..sai doka murmushi yakeyi shi kadai.

Ita kuwa Layla suna gama waya ta mike tareda fitowa daga dakin..ta duba parlon Allah ya taimaketa ba kowa..don haka ta wuce kitchen da saurinta..ba bata lokaci ta hada komai kan tray snn ta dauki tray din ta fice daga kitchen din...sauri sauri take tafiya sbd kar a ganta..tana zuwa part dinshi ko knocking batai ba ta tura kofan ta shiga..ta wuce bedroom dinshi da abincin don tasan yana ciki..ko kallonshi batai ba..ta karasa ciki tareda ajiye tray din hanunta kan bedside drawer..ta juya da nufin zata tafi kawai taji ya riko hanunta..ta juyo fuska a kwabe tana kallonshi tace"daddy kace Ina zuwa zan koma fa..tsoron ummi nakeji wlh"..Taheer na murmushi ya janyota ta zauna gefen gadon..ya karyar da wuya yace"to kiyi serving dina mana..idan an kawoma miji abinci..zama akeyi ayi serving dinshi..Kuma sai an tabbatar da yaci snn ake tafiya"..Layla ta turo baki jin abin da ya fada..snn ta mike zuwa inda ta ajiye abincin..ta zuba mai a plate tareda sa spoon a ciki..sai ta juyo ta dora mai a kan cinya..ta sake juyawa zata tafi ya sake rikota ya zaunar gefenshi..ta sake turo baki da gani abu kadan take jira ta fashe da kuka...Taheer couldn't help it but laugh..yanda tai kicin kicin da fuska ba karamin dariya ya bashi ba wlh..ya dauke abincin data dire mai a cinya tareda ajiyeshi gefe..ya sake kallonta..yana son yin mgn amma dariya ta hanashi..rabon da yayi dariya haka har ya manta..Layla da bakin ciki ya isheta kawai sai tasa mai kuka..ya kunshe dariyan nashi da sauri..ya janyota jikinshi yace"ya Salam..menene abun kuka Kuma baby"...ta shiga kokarin kwace kanta amma ya riketa gam..har yanxu dariyan na cinshi amma ya daure ya sake cewa"ok ok am sorry..sorry for laughing at you..kiyi hakuri bazan Kara ba"..taki cemai komai tana cigaba da kukanta..sai ya dago fuskanta ya shiga share mata hawayen yace"I said am sorry baby..kukan ya isa mana"..sai ta dena kukan itama ta shiga goge tears din..still Taheer na murmushi yace"ur silly daddy is sorry okay?..yanxu ki bari muci abincin sai ki tafi"...ta zaro idanu tana girgiza kai kmr zata fashe da wani kukan tace"Allah idan ummi ta ganni fada zatai min..nidai ka barni in wuce plss"...Taheer ya mike tsaye Yana fadin"to muje in rakaki"..ta zare ido tace"Tabb niba saika rakani ba..ka zauna kaci abincinka"...yai shiru tareda tsura Mata ido kawai...sai Kuma ya bude Mata hannayenshi yace"alright give me a hug indai kinaso in barki ki tafi ke kadai"...bata San lokacinda ta galla mai harara ba..sai ya kwashe da dariya Yana fadin"naga wnn kallon baby thank you..saura hug din"...Saida ta dauke kanta gefe baki a tunzure snn ta taka a hankali tareda fadawa jikinshi...ya maida hannayenshi yai hugging dinta dasu...sun dauki almost 5 mins a haka snn ya saketa a hankali yace"you are free to go now..Saida safe"...ba tareda tace mai komai ba ta juya ta fice daga dakin..Taheer ya bita da kallo har ta fice snn ya koma ya zauna tareda daukan abincin ya faraci..har yanzu bai dena murmushi ba..she really is amazing.

STORY CONTINUES BELOW
Layla na shiga parlor taci karo da ummi tsaye cikin parlon idanunta a kan kofa kmr dai akwai Wanda take jira..ta sukuyar da kanta da sauri tanajin hawaye na gangarowa face dinta..ummi ta karasa inda take tareda kama hannunta..ta shiga janta har daki..a fusace take kallon Laylan tana cewa"bakida hankali koh..uban me ya kaiki bangarensa"..Layla na hawaye tace"cewa yai in Kai mai abinci"...ummi taja tsaki tace"sbd ke doluwa ce shine kika kwashi jiki kika bishi har bangarenshi..baki san namiji ba kunya ne dashi ba koh...shahsahsa shine zaki dauki kanki ki kai masa"..Layla na kuka wiwi tace"Ummi nifa na wani abun yayi min ba..abinci kawai na kaimai..ai dai bazan barshi ya kwana da yunwa ba"...ummi na salati tace"lallai kin zama abinda kika zama Layla..yanxu nidin kike cema bazaki barshi ya kwana da yunwa ba..ke 'yar dadi miji koh..to zancicci ubanku wlh daga ke har Taheer din..Allah ya kaimu gobe zaizo ya sameni"..tana gama fadanta ta fice daga dakin..Layla ta fada kan gado tana ci gaba da kukanta..abunda taketa gudu knn gashi nn ya ja Mata.
Washegari da safe ta gama Shirin tafiya school don tanada lecture 8...shima Taheer ya gama shiri da wuri don yanaso yayi dropping dinta a school din..yana shigowa parlon ko gaisawa baiyi dasu umma ba ummi ta hau shi da fada"yanzu Taheer sbd bakada kunya..baka San Annabi ya faku ba..shine ka kira yarinyar nn jiya bangarenka koh..wani wai ta kawo maka abinci..da uban wane ya hanaka cin abincin tun a nan..shine Saida dare ya tsala ka lallaba ka kirata wurinka sbd kawai ka samu damar kebewa da ita koh"...Taheer wani irin kunya yaji ya kamashi sbd bayan umma akwai Nafisa a parlon..Allah ya sani shidai yana jin nauyinta sosae..ko don ita ta haifi Laylan oho...Saida ya Kau da kanshi gefe snn yace"ummi abinci nace ta kawomin fa kawai..mene laifi a ciki fisabilillahi don ta kawo min abinci"...ummi tace"ai bazaka ga laifi ba dama..and this should be your last..kar ka kuskura ka sake kiranta bangarenka wlh..inba hakaba ranka sai yayi mummunan baci"...Taheer da kanshi ke qasa..cikin zuciyarshi yace"kwana nawa ne zamu bar maki gidan naki ma"..a fili Kuma yace"toh"...daidai nn Layla ta fito daga dakinta don driver na jiranta a waje..tana sanyeda hijab dinta har qasa..jakanta rataye a shoulder dinta sai handouts dinta data rungume a jikinta...ta karaso parlon..ummi na kallonta tace"wai don jaraba saura kwana uku a fara bikinki amma bazaki hakura da mkrntan nn ba..daga gobe dai ba inda zaki kara sa kafa ki fita sedai ko gidan mijinki"..itadai batace komai ba..bayan ta gaisa da kowa tai musu sallama ta fita daga parlon..Taheer ya bita da kallon mamaki don shi kadai ne bata gaisar ba a parlon..ya mike da sauri zai bita umma ta maidashi zaune da sauri..ya juyo yana kallon umman yace"umma fushi takeyi dani fa"...umma na daga kai tace"kyaleta"..ummi dai ta mike ta bar musu parlon..ya rage daga shi sai umma..sai Kuma Nafee dake gefe..Taheer na duban umma da mamki yace"in kyaleta Kuma umma..fushi tayi dani fa"...umma tadan bata rai tace"ka rabuda ita tayita fushinta Mana..ai ba Kaine kayi Mata fada ba Yaya ce..sbd taga kana damuwa shiyasa take maka wnn iskancin..da girmanka da komai ka tsaya qaramar yarinya tana caja maka Kai"...kafin yai mgn Nafee ma tace"umma gsky ta fada bro..ka rabu da ita don ubanta..duk ta gaji da fushin zata sauko..kuma bari ma ta dawo zanji ko kai din sa'an tane da zatana yi maka irin wnn iskancin"... girgiza kai Taheer yai snn a hankali yace"bazaku gane bane umma..ba wai zan bata hakuri sbd tafi karfina bane..No..zan bata hakurine sbd in samu peace of mind"..sai yai shiru tareda kama hanun umma cikin nashi..snn yacigaba"indai zata cigaba da fushi dani haka umma to wlh gaba daya ku kanku bazaku gane kaina ba..bazan iya samun nutsuwa ba in har nasan tana fushi dani haka..kuyi hakuri"..ya karasa mgnr cikeda rauni..da gani zakasan ba karamin azabtuwa yakeyi da soyayya ba...umma da tausayinshi ya kamata tace"to amma Taheer haka zaa ringa biye mata baa isa ayi mata fada ba knn..kadafa ka bari soyayyan nn da kake mata ya zama silar lalacewarta Kuma"..ya rufe bakin umma da sauri yace"in Allah ya yadda bazata lalace ba umma..idan tayi laifi ko banyi Mata fadaba ai nasan yanda nake treating dinta..Kuma batajin dadin hakan..so don Allah ki dena wnn mgnr kinji..babu abunda zai faru Bi'iznillah"...umma na gyada kai tace"shknn..amma ka ringa kokarin boye wnn son Taheer..ba koyaushe zakana nuna mata u can die for her ba"..yace"an gama umma..yanxu bari inxo in wuce office"..kafin umma tai mgn Nafisa tace"kodai ka wuce wurin Laylan taka ba.. Majnoon".. murmushi kawai ya saki kana yace"mind u..naji kina cewa zata dawo ta sameki to babu ruwanki da ita..wnn tsakaninmu ne"..dariya kawai tayi..tana binshi da kallo har ya fita snn tana duban umma tace"na rasa wnn wane irin soyayya ne umma..kmr a irin indian films din nn wlh"...umma tace"ba yanda Allah baya ikonsa ai..shi nashi jarabawan knn"
Taheer ko daya fita bai samu motan a cikin gidan ba..hakan ya tabbatar mai da cewa sun tafi..ya shiga mota shima ya tafi..ya zama dole ya bita har makarantan ya rarrashi abarshi..idan kuwa ba hakaba yau ko patients din bazai iya dubawa ba..and 10 zai shiga theatre..so dole ya lallabota kafin time din..kar yaje ya farka matar mutane yazo ya kasa dinkewa..lol😹

mintina qalilan suka kaishi school din..bayan yayi parking sai ya shiga Kiran wayanta...saida ya kusa katsewa tayi picking..a takaice yace da ita"Ina jiranki a parking lot baby"...bai jira me zata fada ba ya kashe wayan..ita Kuma ta dubi Hanna dake zaune kusada ita tace"babe bari in dan je waje pls..daddy na jirana"...Hanna ta saki wani dariya tana fadin"saikin dawo yammata..ai yanxu ke amarya ce..so dole ayi miki duk abinda kike so"..Layla na murmushi ta fita daga lecture hall din...tana isa inda motarshi ta bude ta shiga ciki...kanta a qasa tace mai"Good morning Daddy"...maimakon ya amsa sai cewa yai"fushi kikeyi dani koh baby..kiyi hakuri nasan it's my fault..da bance ki kawomin abinci jiyaba da ummi bazata yi maki fada ba"..Layla da har ta fara hawaye tace"ba laifinka bane daddy..ka dena apologizing..kawai mgnr da ummi ta fada ne banji dadinshi ba"...Taheer ya kamo hannayenta yace"duk da haka it's my fault..tunda kina zaman zamanki na Kira nace ki kawomin abinci..kiyi hakuri kinji..and ki dena hawayen nn"...tasa hannu tana goge tears din nata snn tace"it's ok ya wuce"...yaja kumatunta yace"to bakiyi dariya na gani ba"...ba musu ta sakin mai murmushi..shi kuma yai pecking dinta yana fadin"ko kefa..at least yanxu ina iya aikina cikin kwanciyar hankali..yanzu ki koma class abunki.. thank you"...har yanzu bata bar murmushi ba..ta bude motan ta fita..tana mai waving har ya tafi snn ta juya itama ta koma class.
Thursday..
Yau ya kama ranan kamu..tun jiya mai lalle tazo ta dandara ma amarya lalle na gani na fada..gidansu kuwa cike yake taf da mutane..'yan uwa da abokan arziki duk sun hallara.

Karfe 4 zaa fara kamun..don haka tun around 2 make up artist da zatai ma amarya tazo gidan...a nan compound din gidan zaayi kamun...so masu decorations suma na waje suna baje basirarsu na decorations...ko Ina ka waiga mutane ne abun baa cewa komai..

4:30 sharp aka gama yima amarya make up dinta..tana sanye cikin atampa super Holland fara mai zanen manyan flowers green...anyi mata irin traditional dinkin nn riga da plane zani..sai aka daura Mata zanin a kan rigan..head din dake kanta shima green.. likewise purse da kuma takalmin dake kafanta..kunneta da wuyanta kuwa..wani danqareren sarqa ne na gold..wanda ummi da kanta ta siya mata as wedding gift..haka ma Bangles da rings da suke hannunta...kallo daya zakayima Layla ka tabbatar da cewa amarya ce ko baa fada maka ba..sbd tsabar kyan da tayi..ni kaina garin kallonta saura kadan wayana ya fadi a qasa..😹

Ummi da Umma kuwa..anko sukai na atampa suma super England..dinkinsu irin dogon rigan nn A shape sai aka bajeta da stones tun daga sama har qasa..mayafan da suka yafa ma iri dayane haka komai da suka Sanya irinsu daya..sunyi kyau dasu kmr ba tsofaffi ba🙊😆

Sai Kuma Nafisa da Ramla..suma kaya iri daya sukasa..atamparsu iri daya da nasu ummi..sai dai color daya bambamta su..dinki ma iri daya akai musu..snn mayafi and everything suma iri daya sukasa..hakika duk Wanda ya kallesu dole yaji sun burgeshi.

Sai kannen amarya..su Ramadhan shadda sukasa brown..dinkinsu suma iri daya..sai Hibba da akai ma dogon riga da nata..sunyi kyau suma sosae..sun kuma fito a qannen amarya sakk.

Kasancewar taron ba maza..so iya Mata ne kadai a wurin..sai su Al'ameen din da suka kasance yara...kafin karfe 5 wuri ya cika sosae taro Kuma ya fara daukar harami..decor din wurin ba karamin kyau yayi ba..komai na gargajiya akayi..babu abinda ke tashi wurin sai kidan kwarya..😄

Amarya Layla na zaune inda aka tanadar Mata..daga kasa Kuma..inda aka tanadar ma friends dinta ne..Wanda most of them daga cikin family dinta suke..sai Kuma family friends don ba wasu kawaye gareta ba...Hanna na zaune a wurin itama..ta shiga cikinsu sai ka rantse ba yau suka fara haduwa ba.

Bayan an gama ciye ciye..su ummi suka fita domin yin kamun...aka sakar musu kida suka shiga..akaita fesheta da turaruka kala kala ana sakin guda..Saida suka gama snn aka bada filin rawa..nan fa mutane sukaita shiga suna cashewa..abun dai sai Wanda ya gani...nima daga baya maida wayata nai cikin jaka na shiga fili na dan taka snn nafito.
Can na hango mutanena..members na Dr.TAHEER Fans Group sunata tikan rawa a tsakiyar fili🤣

A takaice dai baa tashi daga wurin ba sai after magrib..kowa ya watse..Wanda zasu gidajensu suka tafi..Wanda zasu kwana a nn Kuma kowa ya nemi masaukinshi..amarya Layla ma da brides maids dinta suka nufi inda aka tanadar musu.
Wanda suke son zuwa biki suyi mgn don a tanadar musu cards dinsu😹Bayan Layla ta raka Hanna kofar gida sun tafi..ta koma ciki..tana kokarin kwanciya wayanta dake kasan pillow ya shiga vibrating...ta zauna gefen gado tareda janyo wayan daga inda take..gabanta ya yanke ya fadi ganin Taheer ne me Kiran..bata san me zaice ba yanxu Kuma..Saida ya kusa katsewa tai picking tareda Kara wayan a kunnenta...a daya bangaren Taheer yace"badai har kin fara bacci ba baby".. Layla ta wani kwantar da murya..ita a lallai mai jin bacci tace"yanxu dai zan kwanta"...ajiyan zuciya Taheer ya sauke snn yace"thank God tunda baki fara baccin ba..baby ki fito waje in ganki plss"...ta wani zare ido sosae tace"kasan dai ba barina zaayi in fito ba daddy"...Taheer yace"ai ba Wanda zai san kin fito..ta kofan kitchen zaki biyo..Ina jiranki back yard"...Layla ta turo baki snn tace"Allah daddy idan aka kamamu nidai ba ruwana"...Saida ya saki murmushi snn yace"Kai baby..wai idan aka kamamu sai kace wasu marasa gsky.. InshaAllah ma babu Wanda zai ganmu..kiyi sauri kizo kinji"...yana gama mgn yai hanging call din...Layla daketa faman turo baki ta mike tareda daukan katon mayafi ta yafa kan long rigan baccin dake jikinta..snn a hankali ta fito daga dakin..Sadaf Sadaf ta ringa tafiya har ta isa kitchen..Kai tsaye ta bude kofan da yace mata Yana ta nan din snn ta fita...ta shiga duba wurin amma bata ganshi ba..tana Shirin juyawa bayanta ta duba nan ma..kawai tajita a jikinshi..yai hugging dinta ta baya..ya sunkuyo da kanshi daidai kafadanta yana cewa"baby I missed you so much"...itadai bata iya cemai komai ba don ba karamin tsoro ya bata ba...bayan yayi breaking hug din..ya dauko kujeru biyu dake cikin plastic chairs dake ajiye can gefe..da alama Wanda sukai amfani dasu ne yau..ya zauna kan daya snn itama yace mata"sit"...ba musu ta zauna kan kujerar...Taheer ya zuba Mata narkakkun idanunshi Yana kallo..murya kasan makoshi yace mata"kinyi kyau"..ta dago idonta da sauri ta saukesu kanshi..sai Kuma tai murmushi kawai tana girgiza Kai...Taheer ya matso da kujeranshi gab da nata..har gwuiwanshi na gugan nata..still idanunshi kanta yace"Allah baby da gaske kinyi kyau..komai kikasa yana miki kyau baby..shiyasa nakeda kishi sosae a kanki..banso kowa yana kallon kyawunki sai ni kadai"...Layla da magangunshi ke sata murmushi itama ta kada baki tace"ai kaima me kyau ne daddy..duk kayan da kasa suna maka kyau..and you always look 30 not 40"..dariya sosae Taheer yayi kafin yace"baby yanxu dai kema kinaso kice nayi maki tsufa koh"...ta girgiza kai da sauri tana cewa"ni ba haka nake nufi ba..Ina nufin you are the perfect man for me"...Taheer bai san lokacinda ya sake hadata da jikinshi ba tsabar dadi..kalamanta ba karamin faranta mai sukai ba..ya Kai bakinshi saitin kunnenta murya can kasa yace"I love you so very much baby..I love you to the moon and back"...itama yau dai ta bude bakinta tace"l love you more"...Taheer ya dagota da sauri yana kallonta not believing his ears..did she just said she loves him..if he can recall rabonda ta bude baki tace mai I love you tun kafin ya furta yana sonta sai yau...yasa hanunshi yai cupping face dinta yace"what did you just said baby..say it again plss"...Layla na girgiza kai tareda boye face dinta a chest dinshi tace"ni kunya nakeji daddy"...Taheer ya shiga kokarin dago fuskan nata daga jikinshi yace"then lemme kiss you tunda kunyana kikace kinaji"...aiko da sauri ta bar jikinshi tana fadin"sorry ba kunya nakeji ba"...shima yana Mata murmushi yace"kin manta deal dinmu koh..daga yau duk kika sake cewa kinajin kunyana i must kiss you"...tana gyada Kai da sauri tace"na yadda"...Taheer ya mike tsaye tareda zira hannayenshi cikin aljihunshi yace"bari inzo in wuce baby tunda na ganki..yanxu xakiji wancan dan iskan ya fara damuna da waya"..itama ta mike tsaye tana fadin"to Saida safe"..yace"Allah ya kaimu..amma ki fara shiga tukuna sai Nima in tafi"..bata sake mgn ba ta bude kofar ta shiga..ya matso inda take tareda manna mata peck a goshi snn ya juya ya tafi...itama ta rufe kofar snn ta koma cikin gidan..Kai tsaye ta wuce dakinta..inda some of brides maids dinta ke kwance suna bacci..ta tsallakesu itama tareda kwanciya kan gado ta rungume pillow..tanata tunaninshi a haka har bacci yai gaba da ita.+

STORY CONTINUES BELOW
Shiko Taheer dama daga gidan Yusuf yazo..don tun jiya dayaga gidan ya cika taf..ya dauki duk abunda yasan zai bukata ya wuce gidan Yusuf inda some of abokanshi wanda ba cikin Abuja sukeba..suka sauka a boy's quaters na gidan Yusuf din..shima ya shiga cikinsu..don seriously bayason hayaniya.
Friday...
Yau ya kama zaayi dinner..duka bangarori shirye shiryen tafiya dinner din kawai akeyi.

A can gida kuwa..yauma kmr jiya da wuri make up artist ta iso gidan don yima amarya kwalliya.

Su umma suma  kmr dai jiya..yau wani dokakken lace sukasa purple color..dinki da komai nasu iri daya...yayinda Nafisa da Ramla kuwa sukasa irinshi amma nasu pink..daidai da dinkinsu iri dayane..sai hibba itama da akayi mata fitted gown dinta..akayi mata turban style a kanta..sai ta fito dass da ita kmr yammata.

Su Al'ameen kam yau getzner sukasa fara qal..hadda mahaifinsu..dinkinsu Kuma kaf iri daya.
8:pm daidai ango yazo daukan amarya domin tafiya wurin dinner din...da yawa daga cikin jama'ar dake gidan kuwa duk sun tafi wurin..'yan kadan suka rage Wanda basu tafi ba..amarya Layla dake sanye cikin wani dan ubansun gown..na material mai walwali..silver..head dintama silver..haka purse da shoe...wuyanta na sanyeda wata hadaddiyar diamond necklace ita kanta sai walwali takeyi... inshort amarya tayi kyau fiyeda ma jiya..ga gown dinta ya fito da ainihin shape dinta...tana takawa a hankali kmr wata queen yayinda Hanna da wasu mutum biyu daga friends dinta suka sanyata a tsakiya...har main kofan da zata fito daga parlor motan da zata dauketa yazo..Taheer dake cikin motar idanunshi na kan kofa..saida gabanshi ya Fadi da yaganta..don wurin akwai haske sosae...da sauri wani friend din Taheer mai suna Salim wanda shike driving motan nasu..ya fito tareda zagayawa ya bude mata motan...Hannunta rike cikin na Hanna har suka zagaya wurin...a hankali ta shiga cikin motan...Taheer ya lumshe idonshi da sauri jin wani fitinannen qamshi dake fita a jikinta..shima Yana sanye cikin dokakkiyar getzner dinshi ash colour..dinkin babban riga..tun daga kan hula dake kanshi..zuwa su wrist watch da takalmi duk matching clour ne...askin da yai sai ya maidashi kmr dan 35..fuskanshi ya Kara haske ga Kuma siririn sajenshi dayasha gyara suka hadu da gemunshi sai suka sake fito da asalin kyawunshi...bayan ta shiga Hanna ta rufe motan snn ta juya itama tareda sauran friends din suka nufi inda motar mijinta suka shiga..su suka fara fita daga gidan snn motan amarya da ango ma ya fita...Taheer da tunda ya runtse idanunshi bai sake budewa ba har yanzu..ya shiga karanto duk addu'ar dayazo bakinshi...yanajin yanda abubuwa biyu sukazo suka tsaya mai a makoshinsi..na farko dai kyawun da yaga tayi..sai yaji tamkar ya maidata cikinshi tsabar shaukin da yaji yana fizgarshi...na biyu kuma tsananin kishin yanda zata shiga cikin dubban mutane da irin wnn dressing ba tareda ko mayafi ba balle hijab...wnn abun yafi komai tsaya mai a rai...ita kuwa Layla tunda ta dago taga idanunshi rufe bata kawo komai a ranta ba har suka karasa wurin...tun daga waje dama zakasan hall din ba karamin hadadde bane tun ma kafin ka shiga ciki...bayan Salim yayi parking sai ya bude motan ya fita...shi Kuma Taheer ya shiga bude idonshi da yai jajir a hankali har ya saukesu a kanta...cikin karfin hali yace"baby kina nufin a haka Zaki shiga wurin nn wai"...Layla ta dago da kanta itama tana dubanshi tace"eh mana daddy..ko banyi kyau bane"..tun kafin ta rufe baki yace"mgnr kyau ma kikeyi baby..kin ganki kuwa"..sai ya shiga girgiza kai yana fadin"bansan tsaustayin daya kaini amincewa da dinner bama in the first place...da nasan haka zakizo dinnern baby da wlh ko kusa ma bazan taba amincewa ayi dinner ba"...Layla da magangunshi suka bata mamaki tace"wai me ya farune daddy..ban gane me kke nufi ba"...a dan fusace yace"baby babu inda zaki shiga a haka.. infact ko cikin motan nn bazaki fita ba"...ta zaro idanu tana fadin"wai me yake faruwa ne daddy..what's wrong plss"...da sauri Taheer yace"oh tambayana ma kike..baki san meya faru ba right?..just take a look at yourself..baby you look morethan beautiful..you look very ravishing baby ta ya zan bari ki shiga cikin Alrijalu haka..ko mayafi babu"..da ganin yanda ya karashe mgnr zakasan ba karamin ciwo abun yamai ba...mamaki sosae ya kama Layla tana binshi da kallo a hankali tace"amma daddy haka akeyi fa..Kuma f...bata karasa ba ya katseta da fadin"keep quiet..don haka akeyi ance maki you are thesame da sauran matane..you are different... you are mine don haka babu inda zakije daga cikin motan nn"...kafin tayi mgn taji ana knocking motar ta saitin da yake...a hankali yai winning glass din..sai yaga umma...tana dubansu tace"malamai ku fito mana..ga Wanda zasu shiga daku ciki nn sun shirya"...tana rufe baki Taheer yace"umma baby bazata shiga wurin nn a hakaba..kalleta fa ko mayafi babu"...umma na kallonshi baki bude tace"ban gane me kake nufi bafa Taheer"..ya sake cewa"umma ki kalleta fa kiga yanda tai kyau don Allah..ko mayafi batasa ba ga kayan jikinta sun matseta..ni da na san haka make up din yakema tun farko da bazaai Mata shiba wlh"...umma da mgnr shi ya kular da ita kawai sai ta bude motar tareda kamo hanunshi ta fito dashi...hanunshi na cikin nata ta zagaya inda Laylan take..itama ta fito da ita...ta jerasu wuri daya tareda sa hannun Laylan cikin nashi..tana mai mugun kallo tace"if you dare misbehave a wurin nn Taheer sai na saba maka wlh.. you'll see the other side of me"...Taheer ya bita da kallo kawai da idanuwanshi da suka sake yin jaa..itadai Layla ko tari batayi ba...saida aka sake arranging yanda zaa shiga da amarya da ango ...mace daya namiji daya snn a hankali suka fara tafiya zuwa cikin hall din..amarya da ango na tsakiya..Taheer na rikeda hanun Layla gam cikin nashi..sai mika hanu yake ta bayanta yana faman baza babban rigan jikinshi..wai a dole baiso a ga bayanta in tana tafiya...Saida umma ta sake dawowa ta gargadeshi da babbar murya snn ya dauke hanunshi.
Dj ya sakar musu waqan Bella Shmurda Ft Zlatan(Cash App)

"Ice on my neck....ice on my wrist....many days I neva sleep....Hotter Hotter....Hotter Hotter....everyday am chasing good life....Tire Tire....Tire Tire.... Rollercoaster Never Tire....I never Tire....yeah yeah....back to sender.... back to sender....you wish me bad....back to sender....yeah Mami....higher higher....higher higher....I never come down going higher....Shoni CC....load am....Cash App....Cash Out....Oni maga....bill am....small money....ball out....usain bolt run am....you get sure client lock am....if you no get money live am....EFCC Mbo japa"...ko ba komai Kun dan shaqata😜

A hankali suka fara shiga cikin hall din..suna tafe suna irin step dance haka..amarya da ango dai suna tsakiya...suna shigowa wurin kallo ya koma kansu... almost everybody was like"wow!!what a perfect couple"...babu Wanda basu burge ba a wurin...Layla dai kanta qasa..har yanxu Kuma hanunta na cikin na Taheer..har suka isa inda aka tanadan ma bride n groom suka zauna...brides maids ma suka zauna inda aka tanadar musu likewise grooms maids...bayan amarya da ango sun zauna Mc ya bukaci Hajia Nafisa da tazo ta bude musu taro da addu'a...Nafisa ta fito ta gabatar da addu'a snn ta koma seat dinta...Mc ya juya ga amarya da ango yana fuskantarsu snn ya fara mgn"ga Jakada angon Jakada...wato gskyr mgn tun da nake ban taba ganin amarya da angon da suka dace da juna kmr wadan nn ba...ango Dr.Taheer kayi Dace da zankadediyar amarya..son kowa kin Wanda ya rasa..Hajia Maryam farar mace alkyabbar Mata...ance idan kaga Zara zakaga wata...to yau ga Layla snn ga Majnoon dinta"..Taheer dake zaune yanajin yanda Mc ya dage sai koda mai Mata yake..sai yaji kmr yaje ya rufeshi da duka...shiko Mc da bai San ma yanayi ba..sai yaci gaba da sana'arsa"Hajia Maryam Jakada amarya a gidan Alhaji Taheer Jakada...Allah yasa shekara kmr haka mu dawo taron sunanku"...mutanen dake wurin suka shiga rige rigen fadin"Ameen..Ameen..Ameen"...Mc ya sake dubansu snn yace yanason ganinsu a tsakiyan fili..yanaso yaga  adadin masoyan da suke dashi...Taheer da har yanxu yakejin haushin Mc sbd koda mai Mata da yai..ya galla mai wata uwar harara a fakaice snn ya dauke Kai...Layla ce kadai taga abunda yayi...batasan lokacinda ta fara dariya ba...shima ya zuba Mata idanunshi kawai Yana kallon yanda ta dora hanunta kan bakinta tanata faman yin dariya...sai ya sunkuyo daidai kunnenta yace"you are laughing at me right?..don't worry Zaki shigo hannuna ne"..da sauri ta shiga girgiza kai ta matso saitin kunnenshi itama tace"am sorry plss..bazan Kara ba"...kmr daga sama sukaji Mc na fadin"don Allah amarya da ango idan an gama kus kus din sai a sakko muna jira..kaf mutanen wurin nn ku sukeson gani sbd dominku suka taru"..Taheer ne ya fara mikewa snn itama ta mike..Saida Taheer ya rikota jikinshi sosae snn suka shiga saukowa daga steps din...Mc na kallonsu yace"Allahu Akhbar kaga Layla da Majnoon iyayen kauna"...Taheer ya dan yatsine fuska..cikin ranshi ko cewa yake"waishi wnn Mcn bai iya komai bane sai mgn"..(what do u expect Dr..mutumin da sana'srshi ce mgnr😹)...ummi dake kallon abinda yai itama ta girgiza kai tana murmushi tace"mara kunya kawai"
Bayan sun sauko sun tsaya a wurin..sai Mc yacema Dj yanaso a samo waqan da zai dace da couple din nn ayi playing dinta... without wasting time kuwa Dj yai playing waqar Enisa(Love Cycle)...umma ce ta fara zuwa inda suke ta shiga yi musu barin kudi..snn ta rungumeshi gaba daya tana kokarin maida hawayen idonta...sai ummi ma ta taso..sai Nafisa da Ramla.. inshort a hankali mutane suka fara tasowa suna musu likin kudi...can na hango Hajia Amina maman Maimunatou tanata barin kudi kmr bata san ciwonsu ba😜abun dai sai Wanda ya gani.

Daga nn Kuma aka bada filin rawa..bayan amarya da ango sun koma mazauninsu...Hanna an dage sai tikan rawa ake..

Finally akazo cutting cake...Umma ta fito as uwar ango...ummi Kuma as uwar amarya..bayan an gama Mc ya sake Kiran amarya da ango stage...hakika dai Abu yayi kyau sai Wanda ya gani...anci ansha snn an dirki rawa.
inshort dai baa tashi a dinner ba sai after 11..shima sbd Taheer ya matsa wai lallai a tashi don shi ya gaji...su ummi basu tafiba Saida suka tabbatar da kowa ya samu mota snn suka wuce...amarya da ango ko dama tun dazu suka tafi...sauran friends dinshi sukaita jigilan daukan mutane suna maidasu gida.A hanyansu na komawa gida Taheer yai kicin kicin da fuska...itadai Layla bata kulashi ba don ta fuskanci kiris yake jira...saida suka shiga har cikin gidan snn Salim yai parking...maimakon ta bude motan ta fita sai ta juyo a hankali tana kallonshi...shima kallon nata yake..ta saki murmushi mai kyau snn tace"daddy I hope dai ba fushi kakeyi Dani ba..."murya a kasa yace"da zan iya fushi dake din ma ai da ba hakaba..haka nn kika kama kika sa wnn gown din..am sure babu Wanda bai kalleki ba a wurin nn"..Layla ta rausayar da kanta tareda kama kunnuwanta da hannu tace"am really sorry daddy..i don't mean to hurt you"...ya gyara zamanshi yana kallonta yace"kinaso in hakura"..ta daga mai Kai da sauri..shi Kuma ya saki wani smile yana nuna mata lips dinshi yace"kiss me indai so kike in hakura"...da sauri ta juyar da kanta tana fadin"you are not serious".. Taheer ya zare idanu yana dariya yace"ni kike cema am not serious koh..just wait and see"...yana gama fadin haka ya shiga kokarin janyota jikinshi..ta hade jikinta wuri guda itama tana dariya tace"ni da wasa nake ma fa daddy..kayi hakuri dn Allah"... Taheer ya koma inda yake ya zauna snn yace"toh indai kinaso in hakura abu daya kawai zakiyi"...tana kallonshi tace"and what's that"...Saida ya rungume hannayenshi a kirji snn yace"ki kirani da wani sunan apart from daddy"..ta zaro idanu tana faman girgiza kai tace"ni bazan iyaba gsky"...sai ya kwantar da kanshi kan kujeran motan yace"then sai muyi kwanan mu a nn"...kmr an fizgi mgnr daga bakinta tace"to hubby"...Saida ya saki wani malalacin smile snn ya mike zaune..idonshi kanta yace"you are free from me now..you can go sai da safe"...yana gama mgn ta bude motan ta fita tana turo baki..ko sallama bata yimai ba ta wuce ciki abunta..shi Kuma yai murmushi  yana girgiza Kai..Salim na ganin fitanta ta shigo motan shima snn ya jata suka wuce.
The following day suka tashi da Shirin mother's Eve.

Yau wani hadadden lace Layla ta sanya Red..head dinta da komai na jikinta ma is red..i think I don't have to tell you guys yanda kayan sukai suiting dinta..just imagine a very fair lady wearing deep Red clothe..kunsan ba karamin haskawa zatayi ba...
Shi Kuma angon nata milk din shadda yasa yau..yayi kyau shima sosae kmr ba tsoho ba🙊🤪

5pm sharp suka fara event din...qawayen ummi da yawa sunzo wurin..haka friends din umma ma sunzo all the way from kano..

Event din was very lovely..kowa ka gani zaka ga alaman yana enjoying abun...yau ma kememe Taheer ya hana Layla cashewa..duk yadda taso yin rawar hanata yayi..wai mutane zasu kalleta...sai daga karshe ummi da kanta ta jata sukai rawar tare..wnn Kam ba yanda ya iya dole yaja bakinshi ya tsuke yana binsu da kallo...baa tashi da wuri ba..don sai around 8 na dare suka tashi..

Daga yau kuma biki ya kare..waleema kadai zaayi gobe a nn cikin gidan nasu..zuwa dare kuma ango ya dauki amaryarshi su wuce don ba mutane ne zasu rakata ba.

Saturday...

Tun karfe 3 malama Aisha Ahmad wadda itace zata fadakar a wurin waleeman ta iso gidan...baa fara ba Kuma sai da akai sallhn asr.

Nan compound din gidan aka zuba kujeru..kowa ya zauna Kai..ita Kuma Malama Aysha tana daga dan wani wuri da akai matata danyi sama..yanda kowa dake wurin zai ganta zai kuma ji abun da zata fada.

Amarya Layla na sanye cikin lace fari qal..dinkin riga da skirt daya amshi jikinta sosae...sai aka kawo lafaya shima white  mai zanen black flowers a jiki..aka nannadeta cikin lafayan..ko fuskanta baa iya gani...tana zaune inda aka tanadar domin ita da kuma maids dinta.

Bayan an bude taro da addu'a malama Aysha ta ta dauki microphone dake kusa da ita snn ta fara kmr haka....."Rabbushrah lissadhri...wayasrili amri...wahlil uqlatan min lisani...yafqahu qauli..wa ba'ad Assalamu alaykum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu"...gaba daya mutane wurin suka hada baki wajen fadin"wa'alaikumusalam warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu"...snn malama Aysha taci gaba..."Muna godia ga Allah SWA daya hadamu a wnn wuri mai albarka...wadan nn ma'aurata da Muka taru dominsu muna fatan Ubangiji Allah ka Sanya Albarka a cikin aurensu...ubangiji ka kade dukkanin fitina dake cikin wnn aure...Ya Allah ka basu zaman lfy mai dorewa...ubangiji kasa abokan arxikin juna ne snn Allah ya basu zuri'a dayyiba Allah Kuma yasa zamansu zai dore har gidan aljannah"...nan ma mutane suka sake amsawa da Ameen...

STORY CONTINUES BELOW
Malama Aysha tace"to da farko dai amarya Maryam...inaso ki Sanya a ranki cewa shi aure bauta ne...snn ibada ne...idan kika Sanya a ranki cewa bauta zakije kiyi...da izinin Allah Zaki yaqi duk wata fitina da zata bullo cikin gidan aurenki...don kinsama ranki dama bauta kikazoyi....
Sannan da akwai wasu shika shikai guda biyar zan fadesu yanxu...Wanda duk wani aure da kika gani a duniya...wadann nan shika shikai da zan zayyano su yanxu...sune suke rikeda wnn auren..alal haqiqa Maryam in har kika dauki wadan nn abubuwa da zan fada Kuma kikayi amfani dasu a gidan aurenki...to tabbas baki ba matsala na zamantakewar aure da izinin Allah...bama ke kadai ba dukkanin yan uwa Mata ku saurareni da kyau...akwai shika shikai ko Kuma ince ginshikai da suke rike ragamar aure matukar mace ta daukesu snn take amfani dasu a gidan mijinta..Da Farko Akwai

1-Hakuri....yes Hakuri nada matukar muhimmanci a zamantakewar ma'aurata...Kuma idan akace hakuri ana nufin hakuri kan abubuwa da dama da zaki iya cin karo dasu a gidan aurenki...hakurin nn ya hada da...hakuri kan source of income na mijinki...maana ya zama dole mace tayi hakuri da yanayin yanda samun mijinta yake...walau me kudi ne walau Kuma akasin haka...duk abinda mijinki ya kawo..ki karba kiyi godia...snn ki nuna masa cewa wnn abun da yayi ba karamin faranta maki yai ba...hakan zaisa ko da yaushe mijinki ya ya ringa kokarin ya faranta miki shima...duk abunda ya samu zai ringa kokarin ya kawo maki don yasan you'll appreciate....snn hakuri na biyu shine...hakuri kan yanda yanayin halittar mijinki yake... Ma'ana ya zama tilas mace tayi hakuri kan yanda mijinta yake... kyakyawa ne ko akasin haka...Haram ne matar aure ta kalli wata siffa ta mijinta ta kusheta...ko Kuma tace bashida kyau or something like that...da yawa daga cikin matanmu na hausawa sunayin haka...wata Kuma wani zata gani a waje ta yabeshi... which is very bad...sbd haka don Allah Mata mu kiyaye....sai hakuri na uku...shi kuma Yana nufin kiyi hakuri da  halayyan mijinki...kunsan ance Dan Adam Tara yake bai cika goma ba...so dole mace zata samu mijinta nada wani hali Wanda ita ba haka takeso ba...to a nan ma sai kinyi hakuri dashi...matukar wnn halin ba sabon Allah bane...yakamata kiyi accepting mijinki a yanda yake...snn ki koyi zama dashi...forinstance wani namijin yanada fada...wani saurin fushi ne dashi...wani Kuma yanada hakuri...to ya zama dole mace ta fara sanin yanda halayyan mijinta yake..snn tayi hakurin zama dashi da wnn halin nashi...don kema bazaki rasa naki fault dinba....idan mijinki nada fada...kar ki kuskura ki daga murya lokacinda yake fadan... instead kiyi shiru sai kin bari ya gama sai ki tausasa murya ki bashi hakuri...ko Kuma kiyi masa bayanin abunda kika aikata yanda zai fahimceki...ta hakan ne kadai zaku samu dorewar zaman lfy a tsakaninku...idan Kuma namiji mai hakuri ne baa ce kije kiyita dirka rashin mutunchi ba...wai don kinsan mai hakurine...to kiyi a hankali don mai hakuri bai iya fushi ba...snn ki gujewa kanki daukan alhakinsa....sai hakuri na gaba shine...hakuri da dangin miji...idan akace dangin miji ya hada da mahaifi...mahaifiya...yayye...qanne...kowa da kowa daya danganci mijinki....ya zama dole suma kiyi hakuri dasu...ki kumayi kokari kowa ki koyi yanda Zaki zauna dashi...ki daukesu tamkar yan uwanki...iyayenshi ki daukesu tamkar naki...ba kyashi...ba rowa...Banda baqin ciki...kar kiga mijinki zaima mamanshi ko qannenshi wani abu ki hanashi...babu ruwanki instead kiyi encouraging dinshi...Banda daure fuska idan sunxo gidanki....ko kiyita bacin rai...snn banda gulma da munafurci...don nasan halinmu Mata akwai mu da gutsuri tsoma...don haka ayi kokari a kiyaye domin Allah.
Abu na biyu shine

2-Gaskia...gaskia nada matukar muhimmanci a zaman aure...kar ki kasance mai yima mijinki karya instead anaso ya kasance tsakaninki da mijinki kalamu Waheed...ya zamana duk mgnr da Zaki fada mai ki tabbatar gaskiyarki kika fada...idan kika saba da fadawa miji gsky wlh ko hadaki dashi akesonyi bai zama lallai yayi tasiri ba don kin riga kinyi winning trust dinshi...ko wani abu akace kinyi bazai yanke hukunci ba tareda yaji ta bakinki ba...duk mgnr da kika fada mai Kuma zai amince sbd ya yadda dake 💯Amma idan kika sake mijinki yayi miki shkedan karya...na farko bazakiyi qima a idonshi ba snn bazaki taba fadan mgn ya yadda dakeba koda gsky kika fada...amma idan kika saba fadan gsky kinci riba biyu...na farko kin kauce daga sabon Allah don kowa yasan karya sabon ubangiji ne...na biyu Kuma kinyi winning trust din mijinki wanda ba Wanda ya isa ya canxa hakan..
Abu na uku shine

3-Biyayya...itama tana taka muhimmiyar rawa a rayuwar ma'aurata...anaso mace ta kasance mai biyayya da duk wani umarni na mijinta...idan yace wance yi kaza...ki tabbatar da cewa kinyi wnn abun ko bakiso...haka idan yace wance banason abu kaza a denayi...kiyi iya bakin kokarinki kiga kin daina din koda shima bakyaso...hakan ba karamin kima da daraja zai Kara miki a wurin me gidaba...kuma ba wai kicema miji kin dena abu kaza snn kicigaba dayi a bayan idonshi ba...no..duk abinda kikace mai kin bari ya zama kin baryi knn for good...if not duk rananda ya gane baki bari dinba bayan Kuma kince kin Bari..mutunchinki kaff zai zube a idonshi and kinsan shi mitunci kmr Madara ne idan ya zube kasa bai kwasuwa...so don Allah ayi hattara Mata.
Sai Abu na gaba shine

4-Tsafta...itama tanada matukar muhimmanci a zamantakewar ma'aurata...anaso both mace da namiji su kasance cikin tsafta..amma yanxu Bari mu dauki na mace tunda shine maudhu'in mu...idan akace tsafta ana nufin tun daga kan tsaftar gida...tsaftan dakuna...tsaftan bandaki...tsaftan yara(idan kina dasu)...da Kuma tsaftan jikinki....kazanta ba karamin causing problem yake a rayuwar ma'aurata ba...anaso ya kasance kullum gidanki tsaf tsaf...tun daga kan toilet dinki zuwa su parlor da bedrooms da kitchen...sann tsafta jikinki ya hada da...yin wanka akai akai...yawan shafa turare ya kasance kullum cikin kamshi kike especially da dare...yawan sa kaya masu kyau...kiyi kwalliya sosae a gidanki snn ki kashe dauri...kibi duk wani lungu da saqo na jikinki da turare...zakisha mamakin yanda mijinki zaiyita binki da kallo kmr soko...we don't have enough time so inayi maku bayani ne in brief...snn akwai tsaftan abinci...anaso mace ta kasance mai kula sosae when it comes to girki...ki kula da duk wani abu da zakiyi when cooking for your hubby...idan akayi girki ba kula bazaa taba samun abunda ake bukata ba...it's either ki cika salt ko Maggi...ko mai...ko Kuma ma ayi abincin bai dahu ba ko baiyi dai yanda ake bukata ba...snn anaso mace ta kasance mai tattali...komai kudin mijinki maza basu son almubazzaranci wlh...yanaso yaga duk abinda ya kawo ki tattalashi...Banda wulakanta abinci...Kuma baa ce ki dinga rowa ba..no daidai daidai Zaki dinga alamuranki.
Sai Abu na karshe which is very important shine.

5-Soyayya da kulawa...yes...Mata Kuna Ina...anaso mace ta kasance ta iya soyayya...anaso mace ta kasance mai nunama mijinta tsananin soyayya da Kuma kulawa... there's different between soyayya da kulawa...bari mu danyishi brief

Soyayya...ana nufin mace taso mijinta kmr shine kadai abunda takeso a duniya...ki nuna mai kina sonshi qawata ba faduwa kikai ba...snn ki nuna kina son duk wani abu da yakeso..ki Kuma so duk wani abu daya danganceshi...tun daga kan 'yan uwanshi har zuwa kan abokanshi...idan yanada 'ya'ya Wanda ba naki ba suma ki sosu...kar ki sake kice Zaki muzgunawa yara wai don bake kika haifesu ba cox da na kowa ne and ke kanki bakisan wa zaki amfana a cikinsu ba..

Kulawa Kuma yana nufin ki kula da duk wasu al'amura da suka shafi rayuwrshi...ki kula da harkan aikinshi ko kasuwancinshi...ki kula da farin cikinshi da bacin ranshi...ki kula da gidanshi da yan uwanshi...ki kula da yaranshi da komai nashi...anaso duk wani abu daya shafeshi kiyi handling dinshi with care...snn kisan yanda zakina mai mgn...kar kizo kiyi sakeke a gabanshi kina mgn kmr namiji...ki tabbata kin tausasa murya kafin kiyi mgn da miji...ki kula da shimfidarshi...ki kula da cin abincinshi...ki kula da wankanshi...duk anaso wadan nn abubuwan ya kasance kina taimaka mai wajen yinsu...idan undies dinshi sunyi datti ki dauka ki wanke..wlh ba faduwa kikai ba...imagine wai mace matar aure ta dauki undies din miji ta bama mai aiki wai ta wanke...this is very very bad...idan zai fita hug him..kiss him..snn kimai addu'a Allah ya dawo miki dashi lfy...ya kasance koda kinyi tafiya mijinki duk abinda yazoyi sai tuno dake...idan yazo cin abinci ya tunoki...idan yazo yin wanka ya tuno dake...idan yazo shiryawa nan ma ya tuna dake...haka idan zai fita daga gida ko in ya dawo ya tuno dake...idan mace ta rike wadan nn abubuwan zata zauna da mijinta lfy da izinin ubangiji...sai sabani da na zaman tare wnn Kuma ya zama dole a sameshi in har zaa zauna tare...don haka yan uwana Mata don Allah mu kula...mu gyara rayuwar aurenmu don itace zata kaimu har aljannah...ubangiji Allah ya bamu ikon yin amfani da abubuwan da mukaji....sbd yanayin lokaci zamu tsaya a nan...amarya Maryam Jakada da Ango Dr.Taheer Jakada muna muku fatan alkhairi a rayuwar aurenku...Allah ya bada zaman lfy da zuri'a mai Albarka...subhanakallahumma...wabihamdika...ashhadu an...la'ilaha illa anta...astagfiruka wa atubu ilaik"

Daga nan waleema ta tashi...lokacin har an fara Kiran sallhan magrib...don haka ummi ta dauke amarya zuwa part din mahaifin Taheer don a shiryata a can...sbd cikin gidan cike yake da mutane..

Post a Comment for "DR TAHEER CHAPTER 6 BY UMMU ASHRAF"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...